Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
*🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 61 to 62 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Monday morning.. Zaman kotu na biyu rana mai cike da alhini (public trial) Babban kotun tarayya. A babban ɗakin shari’a, kujeru sun cika, ‘yan jarida, jama’a, manyan mutane, da kuma masoyan ɓangarori biyu. Ana shirye-shiryen zaman sauraren shari’a: an zaɓi majalisa, alkalai uku, da lauyoyi a shirye. Farha da Doctor an kawo su cikin tsaron ‘yan sanda, suna zaune a gaban masu tuhuma. Fuskokin mutane sun cika bege da kuma kallo da sauraron hukunci; ƴan jaridu suna ta ɗaukan videos da photuna.. An Fara shari’a lauyoyi masu ƙara sun gabatar da hujjoji. Chief Prosecutor (wani lauyan gwamnati): ya tsaya, ya juya ya dubi kotu tare da faɗin. “Mai girma Alkalinmu, al’ummar nan sun shaida yadda ake shirin halaka sunan wannan yarinya; akwai bidiyoyi, sakonni, rubuce-rubuce, takardun labo na asibiti da aka canza; akwai shaida daga admissions na club; kuma akwai shaida daga bakin wanda ya yi wannan manufa. Mun gabatar da manyan hujjoji guda uku: (1) shaidun bidiyo da aka tura wanda Farha ta sa. (2) canza result na doctor wanda ke nuna akwai zubar ciki (wanda asali ba haka ba ne), (3) confession na wasu masu laifi da aka kama a hannu akwai rubutu da hotunan da suka nuna Farha ta shirya wannan aikin tare da mata kawayenta..” Alkali yana gyara takardun ya ce: “Mu fara sauraren shaida daga witnesses. Kawo shaidu.” Shaidu na farko Security na club, mai gidan club da witness na farko Wanda yake kula da tsaro a club ya hau tambari; ya bada labari yadda Amal ta shigo, yadda wasu ‘yan mata suka bata drink ta sha, yadda suka kulle ta a male’s toilet, yadda suka yi injection da kuma yadda aka samu jini da kayan zubar da ciki a wurin. Ya bada hotuna da videos, domin akwai CCTV... Kwamitin Mutane a kotu suka cika da mamaki; Farha ta lumshe idanu, ta zamo kalar tausayi.. Shaida na biyu wanda ya gano bidiyon (friend/informer) Wanda ya samu video mai ɗauke da kisan sunan Amal ya bada labarin yadda Farha ta umarci asa a social media... Shaida na uku Doctor yayi confession A nan an kawo doctor. Lauyan karewa ya yi ƙoƙari ya kare shi; amma bayan gagarumin hujja (jakar kudi, record maganganun da suka yi da Farha a office daga wata nurse da ta saurara, saƙonnin waya daga Farha), doctor ya soma faɗa cikin ƙarar sa. Bayan an yi masa tambayoyi mai ƙarfi, an sami confession, doctor ya tabbatar da canza sakamakon (falsifying medical report) saboda kuɗin da Farha ta kawo... Doctor cikin rawar murya ya ce: “Na karɓi kuɗin. Na canza sakamakon. Na yi laifi. Ina roƙon Allah gafara; na yi kuskure babba.” A wannan lokaci, ofishin kotu yayi shiru sosai, mutane suna girgiza kai cike da mamaki da baƙin ciki.. Shaida na hudu Amal ta yi bayanin abin da ta fahimta Amal ta hau, tana ƙanƙancewa cikin sanyin jiki, ta gaishe kotu, ta yi shaida: labarin tafiyarta zuwa club (shin ta tuna wani abu?), yadda ta tarar da kanta a male’s toilet, yadda jinin ya ratsa jikinta, yadda take samun hotuna a social media, yadda abin ya lalata mata suna. Kuma ta bayyana yadda ta kasance ba ciki, yadda doctor ya canza sakamakon... Amal cikin kuka da ƙarfin hali ta ce. “Ina neman adalci. Don Allah a hukunta wadanda suka shirya wannan sharri.” Lauyoyin kare Farha da doctor sun yi ƙoƙarin kare su: sun nuna dalilai, gargaɗi, zancen ko an tilasta doctor ko kuwa an yaudare shi. Amma lauyoyin gwamnati sun tada hujjoji masu nauyi: hotunan, bidiyon, confession, shaidu, saƙonnin waya. Kotun ta ci gaba da watsi da rawar karewa. Jawabin Alkali Bayan an rufe shari’a da hujjoji, alkali ya ɗauki lokaci kaɗan, ya tsaya ya dubi duk wanda ke gaban kotu. Alkali cikin murya mai nauyi ya ce. “Mun ji hujjoji. Mun ga bidiyo, takardu, shaidu. Wannan ba ƙaramin laifi ba ne kisan suna, kokarin halaka mutum, da conspiring to defraud, da tampering with medical records. Wannan al’amari ba kawai laifi ba ne, har ma cin amanar rayuwa ce. A bisa hujjojin da aka gabatar, kotu tana ganin akwai isasshen hujja da ke nuna laifin Farha da Dr Khalid.” Ya dubi fuskar Farha da doctor sannan ya ce: “A yanzu ina yanke hukunci na masu laifi: Farha an same ki da laifin conspiring, defamation, conspiracy to harm, attempt to cause grievous bodily harm. Doctor an same ka da laifin forging medical records, accepting bribe, and conspiracy. Kotun na hukunta Farha da shekara 5 a gidan yari, tara tarar kuɗi, kuma an umarci a yi mata restitution. Doctor kuma an hukunta shi da shekara 2 a gidan yari, ya rasa lasisin aiki na dindindin (revocation), da kuma toshe sunansa daga aiki a asibiti... ” Sauran masu hannu a ciki (kawayen Farha) an gudanar da ƙarin bincike. Kotun ta umurci social media da jaridu su share duk wani abu game da rashawa da zargi da suka tura (injunction), kuma an bayar da umarnin a dawo da mutuncin Amal, tare da neman a biya ta diyya don asarar sunanta. Sannan gargaɗi ya zo daga Alkali: “Wannan hukunci ne na riga. Duk wanda ya taimaka a wannan sharrin zai fuskanci hukuncin da ya dace.” Farha ta zunduma ihu, iyayenta suna faman rarrashi tare da ƙarfafa mata gwiwa cewa zata fito nan da wata ɗaya.... Jama’a sun yi yabon adalci, wasu na jin takaici, wasu na tausayawa Amal. Amal ta faɗi ƙasa tana kuka domin bata yi farin cikin wannan hukunci ba saboda tasan yanzu ba ita ba auran Maleekh, Inna ta rungume ta tana bata hak'uri, Maleekh ya tsaya a gefe yana kallonta ya kasa furta komai... Bayan an watse, Abbah, Maleekh, Amal da Inna sun zauna a wajen kotu. Abbah yana rarrashin Amal: Abbah yana riƙe da hannunta ya ce: “An yi adalci yau. Ban ce duniya ta koma kyakkyawa ba amma wannan hukunci zai yi mana amfani. Ki yi haƙuri...” Maleekh ya matsa kusa da Amal yana murmushi mai rauni ya ce. “Beb, ni nayi ƙoƙarina Inma baki ga hakan ba. Na yi alƙawarin zan share miki hawaye. Wannan hukunci zai zama misali ga duk masu son yin sharri a rayukan mutane.” Amal ta kallesa, idanuwanta sun yi sanyi ta ce “Na gode. Amma akwai abin da ke damu na a raina...” Inna ta yi murmushi kaɗan, ta dubi Maleekh da kallon godiya, ta ce: “Allah ya kawo mana wannan rana. Na yi nadama da abubuwan da na ce a baya amma yanzu zan gyara komai. Mabud'in shine hakuri da addu’a.” A wannan ranar Farha da Doctor sun tafi gidan yari, duk da yiwuwar daukaka ƙara, amma shaidun sun yi masu yawa. Amal ta samu diyya da umarni na shari’a: a farfaɗo da kundin da aka wallafa a social media, a share hotuna, a biya mata diyya... Al’umma sun koyi darasi, shari’a ta nuna cewa ba za a bari zalunci ya yi galaba ba. Bayan Amal da Inna sun tafi a motarta.. Abbah shima ya shiga motarsa ya tafi. Maleekh yana shirin shiga motarsa cikin nutsuwa, fuskarsa cike da gajiya da tunani. Sai ji yayi an furta sunansa da ƙarfi, Zayd ne ya nufo wurinsa fuska a ɓace, zuciyarsa cike da fushi... Zayd yana huci, ya kai hannu ya shaƙo kwalar rigar Maleekh, tare da haɗin. "Ka bani mamaki, Maleekh! Baka da imani! Sannan baka da kunya! Ka kai ƴar uwata gidan yari saboda mace?! Saboda wancan yarinyar nan Amal?!" Maleekh yana ƙoƙarin kwace kansa daga riƙon, yana magana cikin natsuwa amma idonsa na nuna haushi tunzura ya ce: "Ka sake ni, Zayd... ka sake ni kafin in manta kai ɗan uwana ne...! Ka sauƙe hannunka da kyau kafin kayi nadama." Zayd yana dariya mai zafi ya ce: "Nadama? Kai zaka sa ni nadama?! Kai wanda ka lalata sunan mu gaba ɗaya saboda soyayya? Kai wanda ka tozarta iyayenmu saboda mace marar asali? Wallahi baka cancanci ƙiran ɗan family ba!" Maleekh ya fisge hannunsa daga kwalar da yayi masa, yana fuskantarsa, murya ta dushe cikin ƙarfin zuciya ya ce: "Yau pretty ɗinka ce marar asali Zayd? Yau ita kake ƙira da wannan kalmar?… to kada ka sake! Idan baka san darajarta a gurina ba, ka fara koya daga yau! Amal bata da laifi, ku ne masu zuciyar duhu, kuna ganin ƙimar mutum tamkar bola..." Zayd yana jijjiga hannunsa cikin ɓacin rai ya ce: "Kai ɗan wulakanci ne Maleekh! Ƴar uwarka ta wulakanta saboda kai! Ko ka manta Farha ƴar uwarka ce? Kayi mata wannan tozarci saboda ƙalilan ɗin mace da ta iyayenka basa na'am da ita...! Kana da tabbaci zaka aure ta ne? Impossible.." Maleekh ya bugi ƙirjinsa da ƙarfi, yana nuna masa yatsa ya ce: "Banaso yanzu a ga laifina da yawa saboda na dake ka akan wacce nake so, saboda haka ka ƙyale ni da wani batun Farha! Farha ita ta jawo akanta, ba ni ba! Kai kuma, kar ka sake ce min na tozarta ƴar uwata saboda ban taɓa wulakanta ta ba, kawai na kare wanda ba kowa ke iya kareta ba!" Zayd yana ɗaga hannu kamar zai mare shi ya ce: "Wallahi idan baka daina wannan haukar soyayyar ba sai na nuna maka ni ɗan family ne, ba kai ba!" Maleekh yana girgiza kai ya ce: Bana sa'in sa da mutum saboda nafi ƙarfin haka, don haka ka tafi ka bani wuri, ni ba sa'anka bane.." Zayd ya saki numfashi da ƙarfi, yana nuna shi da yatsa cikin fushi. "Wallahi wannan soyayyar zata hallaka ka, Maleekh. Kai kaɗai kake tunanin kana da iko, amma ba zaka iya cin karo da dangi ba!" Maleekh ya ƙare shi da kallo mai tsanani, ya ce cikin zafin rai. "Dangin banza da wofi, akan su nake rayuwa ne? Ko zan mutu in ba su? To ka je kace wa Dangi basa gaban Maleekh, ni ba ta su nake ba, da su da babu su duk ɗaya ne a guna, Iyayena waɗanda suka haife ni sune rayuwata... That's all...." Zayd ya tsaya kallonsa cikin mamaki da takaici, zuciyarsa na tafasa, kafin ya juya ya tafi yana bugan ƙasa da ƙarfi... Maleekh ya tsaya da numfashi mai nauyi, ya rufe idonsa yana furta cikin sirri: "Ku tsane ni gaba ɗaya... amma soyayyata da Amal... ba wanda zai iya raba ta."... Da yamma gidan Abbah ya cika da hayaniya... Hajiya Sa’adatu mahaifiyar Farha tana zaune a kujerar falo, tana jijjiga ƙafafunta cike da ɓacin rai. Gidan ya cika da manyan ‘yan uwa, wasu daga ciki daga Kaduna suke wasu daga Kano wasu daga Borno, duk an hallara, saboda jin labarin abin da Maleekh ya aikata... Hajiya Sa’adatu tana ɗaga murya cikin ɓacin rai, tana faɗin: "Wallahi wannan abin kunya Maleekh ya jawo mana! Yaro kwata-kwata bai san darajar kowa ba, duk irin ƙaunar da ake nuna masa, yanzu saboda wata matsiyaciyar yarinya ƴar talakawa sai ya tozarta ƴar uwarsa?!" Uban Farha, Alhaji Wadata ya ce: "Duk duniya babu wanda ya tozarta ni kamar Maleekh, kuma bazan taɓa yarda da wannan abu ba. Maleekh bai san darajar asalin iyayensa ba. Ko da jini ɗaya ne tsakaninsa da Farha, wannan wulakanci da ya nuna ya isa a raba zumunci!" Zayd kuwa yana gefe yana share hawaye, yana kallon mahaifiyarsa da mahaifinsa, ya ce: "Wallahi Mom, ban taɓa tsammanin Maleekh zai zubar mana da mutunci haka ba. Ina alfahari da shi a matsayin ɗan uwa, amma yanzu na tsani jin sunansa ma." A gefe kuma Ammy mahaifiyar Maleekh ta shigo cikin falon cikin tsantsar fushi. Ta gama jin duk complain da ƴan uwa suke yi. Ta zauna tare da faɗin: "Ni ma dai na gaji! Na yarda da ku gaba ɗaya. Wannan yaron yanzu ya fita daga kulawata. Tinda ya iya hukunta ƴar uwarsa saboda mace, to ni bana da ɗa mai irin wannan hali! Wallahi ba zai taɓa auren waccan ƴar talakawar yarinya ba." Duk falon suka ɗauki hayaniya suna maimaita kalma ɗaya, wasu suna girgiza kai saboda baƙin ciki.. Daga can gefe, Islam da Arfat suna tsaye suna sauraron maganar cikin mamaki. Islam ta ce a hankali: "Wai duk saboda Yaya Maleekh ake so a lalata dangantaka? Kowa da abinda zai ce akansa, haba dallah, daman can basa sonsa, kuma wai har da Ammy wacce ta haife shi ake kushe shi..maimakon ta tausayawa ɗanta.." Arfat ta ce cikin tausayi: "Ai Yaya Maleekh yana cikin rikici... amma yanzu fa komai ya lalace..." Ana cikin wannan hayaniyar sai ga Abbah ya sauƙo daga upstairs, yana sanye da farar jallabiya, ya tsaya a tsakiyar falo yana kallon kowa... Kafin ya zauna, ya ce cikin natsuwa: "Ku saurare ni! Duk kun manta ne?, Maleekh ɗin nan fa ɗana ne, jinin jikina kuma ɗa namiji a guna ɗaya tilo. Kuma in har inada rai babu wanda zai kore shi daga wannan family, idan kuma kun ce a raba zumunci saboda shi to na amince nima a cire ni daga dangi, zan kula da shi da kaina. Tin da ni na haife shi to bazan taɓa gudun sa ba, bazan taɓa kushe shi ba a ko ina, saboda haka idan zaku ƙi ɗana to ku ƙi mu gaba ɗaya da sauran ƙannensa su biyu waɗanda suke jini ɗaya, domin mahaifiyarsa ma ba ƙaunarsa take ba, gata nan shiyasa za'a haɗu da ita a zage shi tasss..." Hajiya Sa’adatu ta ce tana turo baki: "To Alhaji, idan haka ne, mu dai bazamu ƙara zuwa yanda kuke ba. Tinda kana son ƙiyayya ta cigaba tsakanin yara." Sai ta ɗauki jakarta ta fice da mijinta. Ammy ta tsaya tana huci, tana faɗin: "To da kyau! Ku tafi. Ni ma daga yau ba zan sake kula Maleekh ba!" Abbah ya ce "Oh bazaki ƙara kula shi ba? To ai ba amfanin zamanki a gidan nan tinda gidan mahaifinsa ne, kuma ina sonsa sosai, don haka kema kama hanya kiyi tafiyarki bana buƙatar ganin maƙiyan ɗana, zan nema masa wata uwa mai ƙaunarsa ba ke ba..." Haka kowa ke fita waɗanda suka zo daga wani gari, duk Abbah ya kore su. Islam da Arfat ne suke roƙon Abbah akan ya bar Ammy ta zauna, da ƙyar ya barta.. Ammy tana kuka ta nufi ɗakin ta.. Abbah ya zauna a kujerarsa cikin nutsuwa, yana murɗa agogo, sannan ya ce a hankali: "Soyayya ta zama jaraba....." A ɓangaren Amal kuwa, Hajiya Sa’adatu mahaifiyar Farha ce ta ziyarce ta bayan barinta gidansu Maleekh da sauran ƴan uwanta... Inna tana zaune a falo tana lissafin abubuwa sai ga ƙarar horn ɗin mota ta dawo da ita daga cikin tunani. Kafin a ankara, motoci uku suka tsaya a harabar gidan bayan maigadi ya buɗe musu. An buɗe ƙofar mota, sai ga Hajiya Sa’adatu, mahaifiyar Farha, ta fito cikin hargowa da matsananciyar fushi. Tare da ita akwai wasu ‘yan uwa mata guda su biyar, duk sanye da kayan alfarma, amma fuskokinsu cike da ƙyama da hargowa. Maigadi ya yi gaggawar ƙarasowa yana tambaya, “Hajiya lafiya kuwa?” Ta ce da ƙarfi, “Ina Amal take? Muna son ganinta yanzu haka! Idan ba ta fito ba sai na sa an fito da ita da ƙarfi.!” Inna ta fito da sauri tana murmushi cikin tsoro, “Hajiya sannu da zuwa… lafiya kuwa?” Hajiya Sa’adatu ta ce cikin tsawa, “Lafiya? Lafiya ce bayan yarinyar nan ta jefa ‘yata cikin tashin hankali?! Ke kike zaune lafiya ita kuma Farha tana kwana a cikin kurkuku saboda irin ɗabi’un wannan yarinyar..!” Inna ta tsaya cak, ta kasa cewa komai. Sai Amal ta fito daga ɗaki cikin sanyin jiki, ta tsaya a bakin ƙofa tana kallonsu. Hajiya Sa’adatu ta kalle ta sama da ƙasa sannan ta matsa kusa da ita tana nuna ta da yatsa tana faɗin, “Ke ce Amal ko? Ke ce dalilin da yasa Farha take cikin wahala yanzu ko? Wallahi idan har ba ki sa Maleekh ya je yasa an yafewa ‘yata ba, rayuwarki zata zama ɗaya daga cikin ƙalubalen da ba za ki iya jurewa ba!” Amal ta ɗaga kanta a hankali, ta ce cikin murya mai rauni, “Wallahi Hajiya ba ni na saka Farha ta shiga gidan yari ba… komai da ya faru…” Hajiya Sa’adatu ta katse ta da cewa, “Karya kike yi! Ba sai kin faɗa min komai ba! Amma zan faɗa miki abu guda indai ba ki tsugunna kika nemi yafiyar farha ba, ki sa yaron nan Maleekh ya je ya sa Farha ta fito daga kurkuku ba, to zan tabbatar da kin fuskanci bacin rai da wahala da ba ta da misali!” Daya daga cikin matan da suka zo tare da ita ta ce, “Ai irin wannan yarinya ya kamata a koya mata darasi, saboda ta manta da asalinta! Tana ganin ta sami soyayyar ɗan masu kudi sai ta fara raina mutane.” Inna ta tsala kuka tana roƙon su da su yi hakuri, “Don Allah kuyi hakuri, wannan ba hanyar warware matsala bace..." Hajiya Sa’adatu ta ce "Daman ce miki akayi munzo warware matsala ne? Ai mu duk yanda matsala take nan muke tunkara, mu da kika ganmu nan bama son zaman lafiya ko kaɗan, idan har Amal bata sa an ciro mun ƴata ba to wallahi sai mun ƙona gidan nan da ku kan ku...." Daga nan tayi shiru domin ta san abun da ya faru da iyayen Amal kenam... Inna ta ji kanta ya fara juyawa tana tunanin ɗanta da yanda aka ƙona su da azabar wuta... haka jikinta ya fara rawa, gaba ɗaya ta gama tsurewa... Hajiya Hauwa’u wacce aka taho da ita ta ƙara da cewa: “Idan ba ki gaggauta ganin Farha ta fito ba, wallahi za ki ga tashin hankali a rayuwarki, aure? Ki manta da shi! Rayuwa? Zamu tabbatar kin shiga wahala fiye da ta Farha!” Inna ta shige tsakani cikin fushi ta ce: “Ku ji tsoron Allah! Wannan wane irin hari ne haka a gidan mu? Me yarinya tayi muku da kuka zo da cin mutunci haka? Saboda Kuna da ikon raina kowa? To wallahi Amal tafi ƙarfinku, idan baku ƙona mu ba, baku cika mutane ba...!” Hajiya Sa’adatu ta kalli Inna sama da ƙasa cikin raini, ta ce: “Ke ma tsohuwa, ki kula da bakinki! Idan ba ki koyar da ita hankali ba, zamu koya mata da hannunmu!” Sai ta juya tana nuna Amal da yatsa, muryarta tana rawar fushi: “Idan har kika wuce sati biyu ba’a saki Farha daga kurkuku ba, ki shirya da Inna taki! Rayuwarku za ta zama darasi ga masu taɓa mu!” Suka juya suka shiga motarsu suna ta harara da cizon baki, suka bar Amal da Inna cikin firgici da hawaye. Amal ta durƙusa ta dafe ƙirji tana faɗin cikin kuka: “Ya Allah… me yasa rayuwata ta zama irin haka?.. Ina zan saka kaina yanzu?” Inna ta zauna kusa da ita tana share mata hawaye tana faɗin: “Ki kwantar da hankalinki yarinyata… Allah ne kawai zai kareki daga mugayen mutane, ki dage da addu’a…” ☆☆☆☆☆☆☆ Maleekh bai dawo gida ba sai dare misalin ƙarfe 12. A falo ya tarar da Abbah yana zaman jiransa. Abbah yayi saurin miƙe wa tare da faɗin. "Maleekh aina ka tsaya haka sai yanzu? Baka saba kaiwa wannan lokaci a waje ba meyasa yanzu?..." Maleekh yana lumshe idanu alamun bacci yake ji sosai, ya ce "Abbah saboda gudun matsala ne yasa ban dawo da wuri ba, kowa jira yake yayi magana dani ni kuwa duk girman mutum bai isa ya shiga gonata na gyale ba in ba iyayena ba, ni nasan kaina ba hak'uri ne dani ba hakan yasa na dawo yanzu..." Abbah ya ce "okay to wuce ka je ka kwanta. .." Kowa ya kama part ɗinsa.... _WASHEGARI DA SAFE_ Maleekh ya fita office da wuri... An kunna AC, fitilun ofis suna haskawa cikin sanyin yanayi. Maleekh yana sanye da farin suit, yana kallon cikin laptop ɗinsa, idonsa na cike da gajiya da tunani. Sai kawai ƙofar ta buɗe da ƙarfi, Amal ta shigo cikin hanzari, idanunta sun kumbura saboda kuka. Hannunta na riƙe da jakarta da waya alamun yanzu isowarta, ko office ɗinta bata samu shiga ba, tana murɗa zoben hannunta cikin damuwa... Ta ce da sauti mai rauni, tana rawar murya: "Please... Maleekh... in har kana sona da gaske, to ka taimaka, ka sa a fito da Farha... don Allah..." Maleekh ya ɗago da mamaki, yana kallonta kai tsaye: "Amal, me kika ce? Na fito da Farha? Wannan magana ba a hannuna take ba, kin ji ko?." Amal ta matso kusa da tebur ɗin, tana kuka ta ce: "Na sani... amma kai mai faɗa a ji ne, kai ɗan babban mutum ne, kai ɗan hamshaki mai faɗa a ji ne. Kai zaka iya faɗa su janye ƙarar, ko su jawo maganar kotu a sake ta! Farha tana can a kurkuku saboda ni, saboda soyayyata da kai!" Maleekh ya miƙe tsaye, yana jujjuya alkalami a hannunsa ya ce: "Kin manta me Farha ta aikata? Kotun ce ta yanke hukunci, ba ni ba. Ba zan iya tsoma baki a cikin hukuncin doka ba, Amal." Amal tana girgiza kai, cikin kuka ta ce: "Zaka iya komai idan kana so... za ka iya sa duniya ta motsa idan ka buƙata, to me yasa baza ka iya ceto Farha ba? Ka ji yadda nake jin wannan a raina? Taya zanyi farin ciki idan na san yar’uwarka tana can cikin wahala saboda ni?" Maleekh ya ɗan dafa tebur, yana kallonta cikin ƙunci ya ce: "Kin san ba Farha ba ce kawai ta shiga matsala saboda ke, har ni ma... duk gidan mu ya rikice saboda soyayyar nan, Amal. Amma inaso ki ji kalmomi na, ba ni da iko akan kotu, ba ni da iko akan dokar ƙasa." Amal ta share hawaye, ta ce da muryar raɗa: "To me kake da iko akai, Maleekh? In baka iya kare Farha ba, in baka iya kare soyayyarmu daga iyayenka ba, to me yasa kake cewa kana sona?.." Maleekh ya ɗauke kai, yana riƙe kansa da hannu ya ce: "Amal... kada ki faɗi haka... bana son ki rikita ni da wannan zancen." Amal ta ce cikin ɓacin rai. "To sai ka tabbatar da kalmarka... idan kai kaine Maleekh ɗin da nake so, ka je ka fitar da Farha saboda ita yar’uwarka ce, kuma saboda kai ne dalilin da yasa take cikin wannan hali..." Ta juya a hankali, ta kama ƙofar zata fita, tana kuka sosai. Sai kawai Maleekh ya ƙira sunanta cikin raunannen murya. "Amal..." Ta tsaya, bata juyo ba. Ya ce: "Zan yi iya ƙoƙarina... amma ki sani, ba komai a hannuna yake ba. Ki yarda dani..." Amal ta amsa ba tare da juyo ba: "Na daina yarda da ƙoƙarinka idan bata ceto waɗanda suka shafe rayuwata ba..." Ta fita, ƙofar ta rufe da ƙarfi... Maleekh ya tsaya cikin shiru, yana kallon ƙofar, zuciyarsa cike da tashin hankali da soyayya mai zafi. Ya jingina da bango, yana maimaita a hankali: "Farha... Amal......" _BAYAN SATI GUDA_ Amal da Maleekh sun daina mu'amala kamar yanda suka saba, Amal yanzu tunaninta da damuwarta shine Maleekh yasa a fito da Farha...amma samm ya ƙi, hakan yasa kullum suke cikin samun matsala... Falon Amal yana ɗauke da hasken wuta mai launin zinariya, wanda ke ba da sanyi da natsuwa... Amal tana kwance akan kujerar falo, ta lullube kanta da blanket. Idonta a rufe, amma zuciyarta tana tafasa da tunanin Farha da kuma barazanar mahaifiyarta.... “Farha tana gidan yari saboda ni… Ko da kuwa ta tozarta ni, bai kamata hakan ya kai ta wurin hukuma ba. Kuma Maleekh… meyasa yake jin haushin ta haka?” Sai ta lumshe ido, hawaye ya zubo. Cikin zuciyarta tana fadin: “Allah ka sa duk abinda ke tsakaninmu ya warware lafiya… bana son ganin ɓacin ran kowa saboda ni.” Cikin wannan tunanin sai ta ji ƙarar bugun ƙofa, ƙarar da ta firgita mata zuciya. Ta miƙe a firgice, ta nufi ƙofar. Kafin ta kai hannu ta buɗe, sai aka ƙara buga ƙofar da ƙarfi.... “Subhanallah! Waye ne haka?” ta furta cikin tsoro. Kafin ta ankara, Zayd ya shigo cikin huci da fushi, idonsa a rufe da ɓacin rai. Hannunsa na motsawa kamar wanda yake neman abinda zai bugawa mutum. Amal a tsorace ta ce:

Chapter 41 of 62