wannan babban ofishin, ya gane cewa abu mai girma zai faru a CashTalk FM, kuma kowa yana ɗokin ganin irin canjin da Amal za ta kawo.
Meeting ɗin ya cigaba da tattaunawa akan projects, schedules, da objectives na kamfanin, dukkan ma’aikata suna nuna professional attitude, suna sha’awar sabuwar mataimakiya ta Maleekh.
Amal ta tsaya a bakin office ɗin Maleekh, tana kallon babban room ɗin, dukkan na’urorin zamani suna nan, computers, monitors, da smart boards. Ta ɗauki ajanda da pen a hannu, tana jin ɗan tsoro amma a lokaci guda cikin excitement.
Maleekh ya ce:
"Alright, Amal, yau zaki fara da tasks ɗin yau da safe. Zan nuna miki workflow ɗin kamfani, sannan zamu duba schedules, emails, da projects ɗin da muke yi."
Amal ta yi murmushi:
"Yes, Sir. I’m ready."
Maleekh ya ɗauki tablet ɗinsa ya fara nuna mata:
"CashTalk FM is structured in departments. Marketing, Finance, HR, IT, and Content Production. I expect you to assist me directly, manage appointments, and also liaise with department heads when needed."
Amal ta rubuta kowanne word a ajandanta.
Daga nan suka fara zagaye office, suna zuwa departments ɗin daban-daban:
Marketing: Amal ta gaisa da Ahmed, ya nuna mata ongoing campaigns.
Finance: Fatima ta yi mata briefing akan budget reports.
IT: Chike ya nuna mata dashboard na live broadcast da recordings.
Manager: Ibrahim ya gaisa da Amal, sannan ya bayyana mata aikinsa:
Yace shi ne ke da alhakin tsara ayyukan sassan daban-daban da tabbatar da cewa kowanne yana aiki bisa manufa.
Ya nuna mata yadda yake tracking progress ta weekly reports daga kowane department.
Ya kuma gaya mata cewa duk lokacin da akwai matsala ko shawarwari, shi ne first point of contact kafin su kai wa CEO. Amma tinda ta bayyana a matsayin assistant of CEO yanzu ita za'ana sanar wa komai kafin ta kai wa CEO..
Daga ƙarshe ya nuna mata wani project board da yake amfani da shi wajen saka deadlines da monitoring...
Maleekh ya kalle ta cike da murmushi ya ɗora da cewa:
Assistant COE tana taimaka wa shugaban kai tsaye. Ita ce hannun damarsa wajen kula da abubuwa na yau da kullum, tana sauƙe masa nauyi da yin follow-up akan departments.
Manager kuma suya kula da departments (Marketing, Finance, IT, HR, da sauransu)...
Maleekh ya cigaba da sanar mata cewa:
Tana karɓar rahotanni daga Managers, ta tace su kafin su je wurin COE.
Tana iya jagorantar meeting idan COE baya nan.
Tana taimaka wajen tsara strategies da implementation, musamman idan COE ya fi kula da babban vision.
Ita ke sa ido akan discipline da compliance kafin rahoto ya kai ga babban boss.
Wato Manager → ya kula da department.
Assistant CEO → ta haɗa rahotanni daga Managers, ta tace, ta duba, sannan ta kai wa COE.
COE → ya yanke manyan hukunci da policies...
⚖️ Idan babu Assistant CEO, to duk Managers za su rinƙa damun CEO da ƙananan bayanai, hakan zai cika mun kai da workload.....
Maleekh yana lura da Amal, yanda take ta zabga murmushi, cikin dariya ya ce:
"You’re catching up fast, Amal. I knew you’d be able to handle this."
Amal ta yi murmushi sannan ta ce
"Thank you, Sir. I’ll do my best."
Bayan zagaye, suka koma office tare da hutawa a babban office na Maleekh, inda Amal zata fara handling emails, scheduling meetings, da drafting reports.
Yayin da take aiki, wasu ma’aikata suka zo suna tambayar ta:
"Amal, how are you finding your first day?"
Amal ta ce:
"It’s exciting! Everyone is so professional, and I feel welcomed."
Maleekh yana kallonta, yana murmushi ya ce
"Good. That’s exactly what I like to see. Confidence, poise, and professionalism."
Daga bisani, Maleekh ya ce:
"Amal, today is just an introduction. By tomorrow, I want you to handle your first mini project, liaise with HR, and prepare a short report for me."
Amal ta amsa da kwarin gwiwa:
"I’ll make sure it’s done, Sir."
Cikin wannan first day, Amal ta fara samun gaskiyar ƙwarewa akan aiki, tana ganin yadda take iya organizing schedules, communicating da manyan ma’aikata, da handling tasks efficiently.
Maleekh yana kallonta daga ɗaya gefe na office, yana jin alfahari da yadda take sarrafa aiki, sannan yana shirin ganin yadda zata ƙara bunkasa a CashTalk FM.
Meeting ɗin farko da Amal ta jagoranta (kodayake ƙaramin program ne) ya nuna cewa kowa ya fara yaba mata da kwarewarta, har ma da ma’aikatan da suka fara kallonta da mamaki.
By the end of the day, Amal ta gama dukkan tasks nata da kyau, Maleekh ya yi mata brief:
"Well done, Amal. I’m impressed. Keep this momentum, and soon you’ll be fully managing executive tasks on your own."
Amal ta yi murmushi, tana jin confidence da excitement: wannan shine farkon babban tafiyarta a CashTalk FM.
An tashi daga aiki ƙarfe 6 na yamma, tun safe karfe 7 ake fara aiki. Amal ta ɗauki jakanta ta fita daga CashTalk FM cikin nishaɗi, tana jan motarta zuwa gida, zuciyarta cike da farin ciki da excitement; tana tunanin yadda ma’aikatan suka karɓe ta hannu bibbiyu, kuma yadda Maleekh yake lura da ita a office.
Da ta isa gida, ta tarar da Inna a falo tana shan tea. Amal ta sauri ta rungumi Inna tana faɗin
"Inna! Today was amazing! Kowa a office ya yaba da ni, da aiki na, har Maleekh ya nuna jin daɗinsa sosai."
Inna ta yi rawar hannu, ta girgiza jikinta, sannan ta ce cikin farin ciki:
"Allah! Ashe ya tabbata aikin, ya kamata kiyi farin ciki, yarinya ta. Ina ta tunanin yanda zaki je wurin aikin nan ki burge su duka."
Amal ta yi dariya tare da faɗin:
"Yes Inna! Duk suna kallona da mamaki, sun yaba min sosai. Amma Maleekh… Inna, Maleekh yana kallona ne har a office da yanda nake gudanar da aiki, yana lura da ni sosai."
Inna ta rungume ta da dariya:
"Ai yarinya, ki more wannan lokacin, ki nuna kwarewa sosai."
Maleekh ma ya koma gida cikin annashuwa da farin ciki...
Abu ɗaya ne yake ɗaga masa hankali da zaran ya koma gida shine..
Kullum batun mahaifiyarsa Ammy akan Auren Farha ne, damuwarta Maleekh ya amince da Auren Farha in yana son farin cikinta..
Shi kuwa ya dage akan baya sonta, baya kaunarta....ƙalubalen dake damunsa kenam..
Bayan ya koma gida, ya wuce part ɗinsa..zama yayi
yana kallon wayarsa, yana rubuta wasu notes game da projects na Amal da CashTalk, amma a zuciyarsa har yanzu akwai damuwa akan Farha da mahaifiyarsa...
Maleekh ya ɗaga kai ya yi murmushi sannan ya furta
"Amal… yanzu ke ce zaki cike min office da farin ciki. Kullum ina son ganin irin wannan ƙwarewa a tattare da ke."
A gefe guda, Amal tana gida tana ta shaƙe da labaran aikin nata, tana jin confidence da motivation, wannan shine farkon babban tafiyarta a CashTalk FM, kuma ranar Monday ya kasance mai cike da nishaɗi da farin ciki ga dukkan su biyu.
🌹🌹🌹
Ammy ce ta fara knocking a ƙofar Maleekh jin dawowarsa..
Ba jumawa yazo ya buɗe mata, ta shigo tana yatsine ta zauna cikin izzah sannan tace da Maleekh shima ya zauna..
Ya zauna yana fuskantar Ammy yasan batun ta baya wuce akan Farha...
Ammy ta ce cikin tsanani..
"Ya batun maganar mu akan auren?.."
Maleekh ya ce
"Auren wa Ammy?.."
"Ammy ta ce
"Kar ka raina mun wayo mana, ka manta maganar mu akan Farha ne?.."
Maleekh ya ce "Na riga da na sanar mik, kullum batun ki ɗaya kuma nima amsar da nake baki ɗaya ne Ammy, bana sonta taya zan aure ta?.."
Ammy tana harararsa ta ce
"Maleekh! Ka saurara da kyau. Ka fahimci cewa dole ne ka auri Farha, idan har kana son ganin farin cikina. Bazan zauna lafiya ba har sai ka yarda da wannan!"
Maleekh ya ɗaga kai, fuskar sa tana nuna ƙwarin guiwa da natsuwa, cikin murya mai ƙarfi ya ce:
"Ammy… na fahimci damuwarki, kuma ina son farin cikinki sosai. Amma ki saurara da kyau: bazan taɓa auran Farha ba, ko mata sun ƙare a duniya. Ko zata mutu… ba zan yi hakan ba."
Ammy ta wurga masa wani kallo ta taja numfashi mai ƙarfi, tana ƙoƙarin ɗaukar hankali daga fushin da take ciki ta ce
"Maleekh! Kai kasan me kike yi ne kuwa? Kai ba yaro bane, amma kana wasa da rayuwata! Ni ina son ganin Farha a gidanka. Kuma dole sai ka aure ta!"
Maleekh ya yi murmushi mai sanyi, ya matsa kusa da ita, amma bai bari ya nuna fushi ba ya ce:
"Ammy… Ina sonki. Amma ba zan auri matar da ba na ƙauna ba.… Farha bata da wani wuri a rayuwata. Ki fahimta cewa ni ba mutum ne mai yin wasa da soyayya ba."
Ammy ta ɗaga kai tana ƙoƙarin faɗar wani abu..kafin ta furta Maleekh ya ɗaga hannunsa da sauri ya toshe mata baki yana girgiza kai, cikin raunin murya kamar zaiyi kuka ya ce
"Ki yi haƙuri, mahaifiyata… Wannan shine gaskiya, kuma ba zan taɓa boye miki ba. Ina sonki, amma na san inda zuciyata take."
Ammy ta yi shiru, idonta cike da hawaye, amma zuciyarta ta fahimci cewa Maleekh yana da nufinsa. Duk da haka, fushinta da damuwa basu sauƙa ba gaba ɗaya.
Ammy kiyi haƙuri da abin da zance..
"Ni yanzu zan huta. Amma ki san cewa zuciyata ba zata canza ba, kuma Farha ba zata shiga gidan nan a matsayin matar Maleekh ba."
Ammy ta tsaya kallon sa, zuciyarta cike da rikici da rashin jin daɗi...
A fusace Ammy ta miƙe tare da barin ɗakin...
A wannan rana, duk da nishaɗin da Maleekh ya samu daga Amal da fara gudanar da aikin, gidan ya kasance cike da damuwa da tashin hankali saboda batun Farha da tsananin kishi da damuwar Ammy...
Yana zaune ya kifar da kansa akan gwiwarsa lokaci guda yaji wani irin zafaffen hawaye yana zubo masa...
Haka ya kwana a zaune bai runtsa ba, yana tunanin kalmar da zata fito daga bakin Ammy ya haka, a hankali ya furta..
"Zan tsi.....!."
Wannan kalmar ce ta tsaya nasa a rai, yana mamakin Ammy zata iya tsine masa akan Farha...?
_Washegari da safe,_
Amal ta fito daga gidansu cikin tsararren motarta, Kalar motar ta saje da kayan jikinta: brown colored abaya mai bubu ya sha kwalliya, da golden eyeglasses akan dara-daran idanuwanta, da takalmi mai tudu. Handbag da wayarta a hannu ɗaya, lokaci da ta iso company kowa yana bata girmanta da gaisuwa na musamman...
Security a mashigar kamfanin suka buɗe mata ƙofofi tare da miƙa gaisuwa:
"Good morning, Miss Abdulsamaad," suka ce, suna nuna girmamawa.
Amal ta murmusa cikin ladabi:
"Good morning, sir. Thank you."
Tayi parking motar ta a wurin parked..
Ta shiga cikin babban lobby, tayi amfani da elevator zuwa office floor inda Maleekh yake, dake ta wurin Office ɗinsa yake, amma sai ta fara shiga office ɗin Maleekh kafin ta shiga nata....
Bayan ta isa office, ta gaishe shi cikin girmamawa. Maleekh ya fita daga corner office ɗinsa tare da murmushi ya ce
"Beb, ready for your first executive tasks?"
Amal ta amsa cikin ladabi da nishaɗi:
"Yes, Yaya Maleekh. Ina so in tabbatar da zan yi aiki kamar yadda aka sa ran."
Maleekh ya ce:
"Good. Zan fara da showing you the operations, sannan za ki fara handling some executive emails da scheduling."
Fita suka yi zuwa office ɗinta..
Ma’aikatan kamfanin suna kallonta, suna murmushi da mamaki saboda yadda take tsaye da ladabi, da yadda take professional a kowa da kowa.
Bayan sun shiga office ɗinta.
Maleekh ya nuna mata babban conference table:
"Ga kujerunka a nan, ga computer ɗinki, sannan ga dukkan files da za ki fara aiki da su."
Amal ta zauna, ta fara sorting emails, scheduling meetings, da drafting documents. Maleekh yana tsaye kusa da ita, yana bayar da guidance:
"Always respond professionally, and ensure no detail is missed. This is how we maintain CashTalk’s standards."
Amal ta ɗauki notes, tana fahimtar kowanne abu da kyau. duk ma’aikata sun lura da yadda take indispensable assistant, wani daga cikin ma'aikata sun shigo office ya ce
"Wow, Miss Amal, you are very organized. I can see why CEO appointed you," wani ma’aikaci ya faɗa.
Maleekh ya miƙe, ya yi murmushi sannan ya ce
"I told you she’s talented. And you’ll see… she’s going to make life much easier for all of us."
Amal ta murmusa cikin nutsuwa, tana jin ƙwarin guiwa saboda support daga Maleekh da yarda daga ma’aikata.
A ƙarshen ranar, Maleekh ya yi mata private discussion a his office, suna zaune kusa da glass window ya ce
"Beb, I am impressed with your performance today. You really understood the flow fast."
Amal ta murmusa, tana jin daɗi:
"Thank you, Yaya Maleekh. Na yi ƙoƙari sosai koh?."
Maleekh ya faɗa da nishaɗi:
"Keep this up, and soon everyone will know you as my indispensable assistant."
Amal ta kalle shi da murmushi, tana jin cewa ya amince da ita sosai.
Bayan wannan, Amal ta fita daga office, tana jin nishaɗi da ƙwarin guiwa saboda first successful day a CashTalk.
_Washegari_
Bayan ta iso cikin girmamawa..
Amal ta shiga office ɗinta a CashTalk. Tana duba emails, schedules, da reports da Maleekh ya tura mata. Ta fara tsara appointments, ta yi organize client meetings, kuma ta fara ƙirga budgets da spreadsheets cikin sauri da kyau.
Maleekh ya shigo office ɗinta, yana murmushi ya ce
"Beb, yau zamu fara strategy meeting ɗin mu, kafin ma’aikatan su iso."
Amal ta miƙe, ta ɗaga kai, ta ce:
"Shiryashi nake, Yaya Maleekh. Duk wani task da kake buƙata, zan tsara shi yadda kowa zai fahimta."
Maleekh ya dubeta, yana murmushi.
"Kin tabbata zaki iya komai da kanki. Ina jin daɗin hakan."..
(In aka zo office ba batun soyayya domin daga CEO har assistant ba lokaci😅😅)
Suna zaune, suna tattauna private projects da clients, suna shirya budgets, da deadlines. Maleekh yana dariya, yana cewa:
"Tin da kina matsayin assistant, babu wani project da zai tsaya a CashTalk."..
Amal ta yi murmushi ta ce
"Ko shakka babu, Yaya Maleekh, za mu tabbatar da cewa duk clients da tasks suna tafiya smoothly."
Bayan wasu lokaci, ma’aikatan sun shiga office don team briefing. Amal ta jagoranci wasu questions, tana bayar da guidance ga staff. Duk wanda ya tambaye ta, tana ba da amsa cikin nutsuwa da fahimta, har ma wasu staff suka yi dariya da nishaɗi akan irin attitude ɗinta da professionalism.
Maleekh ya tsaya a gefe yana kallonta, yana jin nishaɗi sosai ya ce
"Yau Beb ta tabbatar min, ita ba kawai assistant ba, har da driving force ga kamfanin mu."
Daga nan, ma’aikatan suka jinjina mata. Amal ta yi musu murmurshi, tare da cewa:
"Ku yi aiki da ni kamar team ɗaya, insha Allah zamu samu nasarori da yawa."
Washegari da safe, Amal ta dawo CashTalk cikin tsararren motarta...
Ta isa office ɗin kamfanin, tana shiryawa don babban show broadcast da za ta jagoranta a TV, domin ta nuna cigaba da nasarorin kamfani.
A TV studio ɗin kamfanin, Amal ta shige, ta duba lighting, cameras da microphones tare da technical team. Ta tabbatar komai na aiki lafiya kafin ta fara jawabi.
Daidai lokacin broadcast ya fara. Amal ta tsaya a gaban camera, murmushi tayi, sai ta fara jawabi:
"Assalamu alaikum, masu kallo. Ni ce Amal Abdulsamaad, mataimakiyar shugaban kamfani CashTalk, CEO Maleekh Abdul-Majeed. Yau zamu kawo muku labarin cigaba da nasarorin kamfanin mu, tare da gabatar da sabbin ayyuka da muka fara."
Voice ɗinta ya cika da kwarjini da natsuwa, kamar yadda take jarida, kowa a TV yana sauraro da kulawa. Ta fara gabatar da wasu statistics, projects, da sabbin initiatives na kamfani. Duk lokacin da take magana, ma’aikatan da ke kusa da ita suna kallonta da mamaki, suna dariya da jinjina mata.
Maleekh daga office ɗinsa na kallo a TV, yana sipping coffee, yana murmushi, yana cewa:
"Beb na, yanzu duk duniya suna ganin iya aikinki. Wannan shine voice ɗin da nake son ji a kamfani na."
A gida kuwa, Ammy da Farha suna zaune a falon gidan su, suna kallon TV. Gaba ɗaya fuskokinsu cike da haushi da kishi. Ammy ta ce:
"Maleekh, wannan yarinya ta kama ka sosai, tana aiki a kamfaninka, kuma yanzu duk duniya suna ganin ta, wani irin asiri tayi wa yarona? Domin na tabbata ba haka kawai ta barshi ba, gaba ɗaya ta haukatar mun da yaro, yaron da baya kula ko wace mace, wanda zaman sa yafi yinsa a England amma yanzu saboda ita yaƙi komawa sannan saboda ita yake bijire mun..."
Farha tana tafa hannu da ƙarfi, tana cewa:
"Ya Allah! Wannan ya fi ƙarfin zuciyata! Haka Female ɗan talaka ke cin nasara a cikin rayuwar matashin mai kuɗi!? Bazata taɓa kyale shi ba daman, ta gama da shi..."
Amal kuwa a TV tana ci gaba da jawabi, tana gabatar da sabbin projects, tana nuna professionalism da charisma. Voice ɗinta ta cika da kwarjini, tana ba da labarin kamfani da sabbin initiatives. Kowa da kowa a CashTalk ya shaida cewa Amal ta zama indispensable assistant.
A ƙarshen broadcast, Amal ta yi murmushi, ta ce:
"Na gode sosai, kuma insha Allah za mu ci gaba da kawo cigaba da nasara ga kamfanin mu."
Maleekh daga office ɗinsa ya tura hannu yana yi mata thumbs up, murmushi yayi, yana jin nishaɗi sosai...
Ammy da Farha sun ci gaba da kallon TV, zuciyarsu cike da kishi da haushi, yayin da Amal take haskakawa a matsayin tauraruwa a kamfanin Maleekh....
*TO PAH ZAN YI WANI ƊAN COMMENT NIMA....*
*A YANZU ZA'A FAHIMCI CEWA KWAKWALWAR MACE DA NAMIJI SUN BANBANTA, KAMAR YANDA AKE CEWA TUNANIN MACE DA NAMIJI BA ƊAYA BANE, TABBAS HAKANE NAMIJI YAFI MACE ZURFIN TUNANI DA WAYO...*
*MEYASA NACE HAKA?..*
*SABODA A LOKACIN DA AMAL TAKE TASHEN TA A GIDAN RADIO KOWA DA KOWA YANA YINTA, A LOKACIN MALEEKH YAKE TA NACI AKAN JAWO TA KAMFANINSA DA TAYIN MAKUDAN KU'DADE, YA BADA CHECK NA BILLIONS DOMIN TA DAWO AIKI KARKASHINSA TAƘI, AMMA GASHI A RUWAN SANYI YA SHIGE JIKINTA, TA HANYAR SOYAYYA YA JAWOTA KAMFANIN BA TARE DA CHECK BA😢😢*
*KUƊIN DA ZATA IYA GUDANAR DA RAYUWARTA DA SHI AMMA TAYI LOSING, DUK DA MUTUMIN BA BUTULU BANE TANA CIN MORIYARSA DUK DA HAKA 😅😅😅*
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 35 to 36
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
Inna Ta Ziyarci Amal a CashTalk
Ranar yau ta kasance ta musamman ga Amal, domin Inna ta zo kamfanin CashTalk domin ta ga inda jikarta ke aiki.
Daga bakin get ɗin kamfanin aka shigo da ita, security suka yi mata iso cike da girmamawa, suka nuna ma ta hanya har zuwa cikin compound. Amal da Maleekh suna tsaye a tsakiya suka tare ta.
Inna tana ƙare kamfanin da kallo, idanunta suna yawo daga sama har ƙasa, sai ta ce cikin mamaki:
“Oh ikon Allah… yo dubi wuri kamar aljanna…!”
Ganin tagogi da ƙofofi duk na glass mai ƙarfi, ginin kuwa tsaye sama sama, har sai da ta ɗaga kanta sosai kafin ta hango ƙarshen sa. Tsayin ginin ya wuce misali, hawa goma sha takwas kacal ga office na Maleekh, sai kuma hawan biyu da aka ƙara a saman wanda aka tanada domin ma’ajiyar kuɗaɗe.
Wurin ma’ajiyar kuwa an kafa masa tsaro na musamman – security na ko’ina, ga ƙofar shiga da sai an danna code sannan ta buɗe. Idan kuma aka sa wrong code, nan take robot zai zabura da ƙarar jiniya kamar karar wuta, robot ɗin kofar tsaron zai ɗauka duk wanda ya yi kuskure number to ya shigo a matsayin ɓarawo ne...
Inna sai kallo take yi tana faɗin:
“Subhanallah… wallahi duniya ta lalace, yanzu haka aka zubar da kuɗaɗe tamkar a bola ake d'ibar su...!”
Maleekh da Amal suka saka Inna a tsakiya suka nufi stairs ɗin escalator.
Da suka iso wajen, Inna ta tsaya cak tana kallon matakala yana motsi da kansa kamar maciji. Da sauri ta zaro ido tana faɗin:
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Amal, wannan menene kuma? Matakala ne ko maciji ne yake tafiya da kansa haka?”
Amal dariya take yi, tana ce mata:
“Inna wannan ba komai bane, escalator ake ƙiransa. Zai tafi da mu sama da kansa.”
Da ƙyar ta ɗora ƙafar Inna kan stairs ɗin, Maleekh kuma ya tallafe ta tare da ɗago ta kan benin. Suka taka nan da nan escalator ya fara tafiya.
Inna ta firgita! Ta daka ihu tana faɗin
“Wayyo Allah na! Mutuwa ta iso! Amatu, Maliku ku kama ni, ku riƙe ni!”...
Tana rawar jiki ta tsuguna, daga nan ta kwanta bisa escalator ɗin, ta rungume shi tamkar zai tafi da ita. Escalator kuwa bai tsaya ba sai tafiya yake da ita a kwance, tana zunduma ihu, yayin da Amal da Maleekh suke tsaye suna dariya kamar ba za su tsaya ba.
Sauran mutane da ke hawa da sauƙa suna ta kallonta suna dariya.. Escalator dai an yi shi biyu bangaren hawa sama, da bangaren sauƙa ƙasa amma hankalin kowa ya koma kan Inna...
Da suka sauƙa daga saman escalator, Inna ta fara sauƙe ajiyar zuciya tana jijjiga kanta ta ce:
“Amal! Wallahi na gaji da wannan kamfanin nakun. Ni ba zan iya shiga sama ba, ku sauƙar da ni ƙasa, na koma gida tun yanzu.”
Amal ta tsaya tana kallonta, ganin Inna ba wani nutsuwa zata yi ba yasa ta ce cikin lallashi..
“Inna mu je na saka ki taxi ya maidar da ke gida. Kada ki damu.”
Inna kuwa ta ce cikin rawar murya:
“Amatu, ki yi wa Allah da Annabi, kar ki ƙara saka ni kan wannan matakala mai tafiya da kansa. Wannan ai ba na mutane bane, na aljanu ne. Na rantse idan na koma gida yau, in kin ƙara ganina a nan ki yanke mun ƙafa.”
Amal ta buɗe baki da mamaki ta ce
“Haba Inna, wannan wane irin kauyanci ne kuma?”
Maleekh yana gefe ya kasa riƙe dariyarsa, yana ce mata:
“Amal, ku bar escalator, sai ku bi ta elevator. Wannan ya fi sauƙi gareta.”
Amal ta yi murmushi, ta ce:
“To shikenan Inna, muje.”
Suka nufi elevator. Amal ta danna, ƙofar ta buɗe.
Inna ta yi baya da sauri tana zaro ido ta ce:
“Ikon Allah! To nan kuma wane irin duniya ne za ku saka ni ciki? Wallahi Amal wannan ai kurkuku ne.”
Amal ta kwashe da dariya ta ce:
“Inna, ba kurkuku bane. Elevator ne ake ƙiransa. Shi ne zai sauƙar da mu ƙasa.”
Da ƙyar ta ja hannun Inna suka shiga ciki. Da ƙofar ta rufe, Inna ta fara zabga salati da addu’o’i, tana kankame Amal da hannunta na rawar jiki. Da elevator ya fara motsi ƙasa, Inna ta fashe da kuka.
“Wayyo mutuwa! Amal wannan ina yake kai ni!? Na rantse yau dai na shiga tarkon aljanu!”
Har sai da suka isa ƙasa, suka fita daga ciki.
Inna tana share hawayenta, ta tsaya cak ta ce:
“Amatu, idan kin ƙara ganina a wannan shegen kamfanin naku, ki yanke mun kafafu! Allah ya haneni dawowa, wuri kamar gidan sihiri.”
Amal ta girgiza kai cikin dariya, sannan ta ƙira wani security ya taimaka ya saka Inna a taxi ta koma gida.
Amal kuwa ta juya cikin kamfanin, tana ɗan murmushi, tana tunanin irin abun dariyar da Inna ta nuna yau.
☆☆☆☆☆☆
Bayan Amal ta raka Inna har ta fita daga kamfanin, sai ta juya ta dawo ciki. Amma kafin ta shiga office ɗinta, zuciyarta ta ja ta kai kai tsaye wurin Maleekh.
Ta ɗan tura ƙofar office ɗinsa a hankali, sai ta shiga da murmushi a fuskarta. Maleekh kuwa yana zaune a kan kujerarsa mai juyawa, yana kallonta cikin sanyi, kamar ya san ita ce zata shigo.
Amal ta zauna a kusa da shi tana lumshe ido, kafin ta buɗe baki ta ce cikin shagwaɓa:
“Yaya Maleekh…”
Da sauri ya katse ta, ya ɗaga yatsarsa yana dariya kaɗan ya ce
“Kada ki sake ƙirana da haka, haba kamar wata bakauyiya. Kin manta muna soyayya? Ga sunayen soyayya kala-kala, amma sai ki kirani Yaya Maleekh…”
Amal ta yi shagwaɓar gyara murya, ta ce:
“To my love…”
Ya girgiza kai yana murmushi ya ce
“Tsohon suna kenan. Ba zan amince da shi ba.”
Ta yi dariya, tana gyara zama a kujerar da ta matsa kusa da shi sannan ta ce
“To my chocolate…”
Sai ya dafe goshinsa, yana yin kamar ya ji haushi ya ce
“A’a, wannan ma bai yi mun ba. Chocolate kuma ai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 62