da goshinta, tana mamakin irin kalaman da ɗanta ya zuba wa Farha a gaban Amal..
Amal kuwa tana tsaye a gefe tana kallon Maleekh, zuciyarta na tafarfasa da soyayya da alfahari da irin yadda yake tsaya mata.
Farha ta riƙe kirjinta tana rawar jiki, hawaye na zuba kamar ruwan sama. Tana faɗin cikin kuka:
“Don Allah kayi haƙuri Ya Maleekh… Na yi kuskure ne saboda sonka… Wallahi sonka ya rufe mun ido… Na rasa tunani saboda kai…”
Maleekh ya yi wani tsaki mai ƙarfi, idonsa jajir kamar wuta.
“Sonka fa kike cewa? Wannan abin kunya da kika yi ne soyayya? Kulle ni cikin ɗaki kamar zakin da aka saka a keji? Ki hana ni zuwa masallaci? Ki hana ni aiki? Ki hana ni zuwa ga masoyiyata? Wannan ba soyayya bace, hauka ce, haukar banza!”
Farha ta fara matsawa baya tana girgiza kai, hawaye na kwaranya.
“Wallahi ban yi nufin cutar da kai ba…”
Maleekh ya katseta da cewa
“Karya kike! Ba wai cutar da ni ba kawai kika yi ba, kin cutar da Amal! Kin je gidanta, kin je kin tada mata hankali, kin saka mata fargaba, har kin sa aka ɗauke ta zuwa police station saboda sharrinki! Yanzu ki gaya min, menene laifinta? Menene kuskurenta da za ki wahalar da ita haka?!”
Farha ta kasa magana, tana kallonsa da idanuwanta da suka kumbura da kuka.
Maleekh ya matso kusa da ita, muryarsa ta sake kaɗawa cikin ɗaki:
“Na rantse da Allah Farha, kin gama da ni. Kada ki sake furta sunana, kada ki sake bibiyata, ka da ki sake kusantar Amal. Wallahi idan kika sake kusantar ta ko da a mafarki ne zan sa kiyi kuka na gaske. Na gama da ke, kuma kema kin gama da ni!”
Farha tana kwance a gado, tana ɗaure da drip. Maleekh yana tsaye da fuskar ɓacin rai, yana ɗaga murya:
Ya ci gaba da faɗin
“Farha! Yanzu na gane baki da hankali ne ko kaɗan, Wannan wautar takin tasa kin zubar da mutuncina. Kin raina ni saboda me?”
Yana nuna ta da yatsa cikin hargowa. Farha ta runtse idonta, ta kasa magana..
Ammy ta katse shi a fusace
“Maleekhhh!!!”
Ɗakin ya ɗan ɗauki shiru. Kafin ya ankara Ammy ta zabga masa mari mai ƙarfi.
Ammy tana faɗin
“Kada ka sake ɗaga mata murya haka! Ka manta marar lafiya ce? Ka manta asibiti muke? Maleekh bana son wulakanci irin wannan!”
Ta tsaya tana huci.
Maleekh ya dafe kuncinsa yana kallonta da mamaki.
Ammy ta cigaba da cewa
“Ka sani yau, auranka da Farha ba fashi! Babu wata Amal da za ka aura! Wannan yarinya ta kulle ka ne saboda soyayya, ba saboda ƙiyayya ba!”
Farha ta fara kuka cikin rauni.
Sai a nan Doctor ya shigo da file a hannunsa, ya tsaya daga bakin ƙofa, yana kallon hayaniyar.
Doctor a tausashe ya ce
“Excuse me… kuyi hak’uri. Wannan asibiti ne, akwai majinyata da basa son hayaniya..”
Suka yi shiru. Sai Doctor ya juya ya kalli Farha, sannan ya buɗe file ɗin.
Doctor cikin girmamawa da muhimmanci ya ce
“Yanzu dai za mu faɗa muku ainihin matsalar. Dalilin da yasa Farha ta faɗi dogon suma saboda ƙaramin abu shi ne, jikinta ya raunana… saboda tana amfani da wasu miyagun kwayoyi na maye.”
Ya ɗan ja numfashi.
Sannan Doctor ya cigaba da faɗin
“Mun gano tana shaye-shaye kafin rikicin ya faru. Wannan shi ne ya jawo suma, kuma idan ba’a kula ba, yana iya fara taɓar mata kwakwalwa. Don haka ku sani, matsalar tana da girma sosai.”
Ɗakin ya ɗauki shiru. Ammy ta yi diri-diri tana kallon Farha. Maleekh ya zaro ido, ya kasa magana. Farha ta rufe fuska da hannunta tana kuka.
Maleekh a firgice ya tsaya cak sannan ya ce
“Shaye–shaye??”
Ya runtse ido yana jin tamkar asibitin ya juye akansa.
Ammy ta ce
“Wannan ba gaskiya bane! Ba zai yiwu Farha ke shan miyagun kwayoyi ba! Doctor, ka tabbatar da abinda kake cewa kuwa?!”
Doctor cikin nutsuwa ya ce
“Mun tabbatar, ta sha kafin rikicin ya faru kuma ta daɗe tana sha. Wannan dalilin ne yasa jikinta ya raunana da sauri, kuma suma ta tsawon lokaci fiye da yadda ake tsammani.”
Farha ta fashe da kuka tana girgiza kai:
Fcikin kuka take faɗin
“Wallahi ba da son raina nake sha ba… wallahi! Na shiga cikin wannan abu ne saboda matsin rayuwa… saboda… saboda nake jin bana da kowa sai soyayyar Maleekh. Amma na kasa daina…”
Ammy ta dafe kirjinta cikin tashin hankali ta ce
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un! Farha… shaye–shaye kuma?!”
Ta matso kusa da Farha tana riƙeta, amma a fili tana jin kunya da takaicin halin da Farha take ciki...sannan tana tunanin idan iyayenta suka san da wannan maganar ya zata yi..
Maleekh ya nuna ta cikin fushi da zafi ya ce
“Shiyasa kika kulle ni a ɗaki? Shiyasa kika jefa ni cikin tashin hankali? wannan itace ‘soyayyar’ da kike ikirari? Wauta da lalaci!”
Ya juya kamar zai fita.
Ammy da ƙarfi tana tsawatar masa ta ce
“Maleekh! Idan baka amince da auren ta ba, ka sani ka karya mini zuciya. Wannan yarinya zata zama matar ka, ko da kuwa kana so ko baka so. Ka taimaka mata, ka gyara ta, ka ceci rayuwarta. Wannan shine nauyin ka a kanta.”
Farha tana kuka sosai tana girgiza kai.
Cikin kuka mai nauyi
“Ban cancanci ka taimake ni ba Maleekh… amma wallahi bana so in rasa ka. Kai kaɗai nake da kai a duniya.”
Doctor ya kalle su duka da tausayi, ya ja numfashi sannan ya ce
“Idan har kuna so ku ceci rayuwarta, sai an saka ta a rehabilitation program. Idan ba haka ba… wannan al’ada zata ƙara tsananta, kuma tana iya zama tabin hankali gaba ɗaya.”
Ɗakin ya sake yin shiru. Amal ta tsaya gefe tana kallon komai da idanu cike da hawaye, zuciyarta cike da tausayi da kuma rikici.
Maleekh ya fice daga ɗakin cikin fushi, yana riƙe da kansa kamar zai fashe da kuka. Zuciyarsa cike da fushi, takaici, da ruɗani.
Maleekh yana furta a ransa cikin zafi.
“Ni aure da mai shaye–shaye? Wannan abin kunya ne, wulakanci ne! Ammy har ta mare ni saboda ta kare ta?!”
Amal ta bi shi a baya da sauri tana ƙiran sunansa:
Amal cikin tsoro da tausayawa ta ce
“Maleekh… please, ka tsaya… don Allah ka saurare ni.”
Ya tsaya cak, ya juya da hanzari, idonsa jawur saboda fushi da takaici.
Cikin tsawa ya ce
“Me kike so in saurara Amal? Ba ki ga halin da ake ciki ba?! Saboda an raina ni, a gaban mutane ake cewa in auri wacce take shaye–shaye! Za'a naɗa min ballagaza mai dattin shaye-shaye?!”
Ya dafe bango, zuciyarsa tana tafarfasa. Amal ta matso kusa da shi da nutsuwa, ta ɗora hannunta a kan kafadarsa ta ce.
“Na san wannan abu ya girgiza ka… amma ka kwantar da hankalinka. Idan kana son yin hukunci a yanzu, zai iya zama a cikin fushi. Ka bari ka nutsu kafin ka ɗauki mataki.”
Maleekh ya kalleta sosai, kamar idanunsa za su cinye ta ya ce
“Amal… ba ki gane bane. Ammy ta ce dole ne in aure ta. Ke fa? Kina nufin ke za ki zama a gefe…? laifin me kika yi da aka sa ki cikin wannan azabar?!”
Hawaye ya taru a idon Amal, ta runtse ido tana jin nauyin kalmarsa.
Amal a hankali, cikin murya mai rauni ta ce
“Ban san dalilin da yasa duniya ta ɗora min wannan nauyin ba… Amma duk da haka, ina nan tare da kai. Ka tuna ka ce min ni matar da zaka aura ce. Wannan magana taka tana bani ƙwarin gwiwa, duk da abinda nake fuskanta.”
Maleekh ya yi shiru. Numfashinsa yana nauyi, yana kallonta tamkar yana son ya rungumeta amma zuciyarsa tana cikin rikici saboda maganar Ammy.
Sai ya ɗan matsa gefe, ya furta da ƙarfi:
“Na rantse da Allah Amal, ko da meye, ba zan taɓa yarda a tilasta min auren Farha ba! Ko da hakan zai sa na yi gaba da mahaifiyata.”
Ya ja numfashi ya wuce gaba yana tafiya cikin hanzari. Amal ta tsaya a wurin, idonta cike da hawaye...itama ta bi bayansa
Maleekh ya shiga mota cikin hanzari, ya tada engine da ƙarfin zuciya. Fuskar sa cike da fushi, numfashinsa yana tsananta. Amal ta shige a gefensa, ta dafa ƙafarsa a hankali tana kallonsa.
Shiru ne ya mamaye motar, sai karar AC da numfashinsu kawai ake ji.
Amal ta juyo da nutsuwa tana kallon Maleekh.
A hankali cikin murya mai rauni da ƙarfi a zuciya ta ce
“Maleekh… akwai kalmar da ka furta ta yi nauyi a zuciyata.”
Maleekh ya ɗan kalleta cikin mamaki, ya ce da ita.
“Me na ce? Na fa yi magana ne cikin fushi Amal.”
Amal ta ce
“Ka ce koda hakan zai sa ka yi gaba da mahaifiyarka.”
Ta ɗan sauƙe ajiyar zuciya, hawaye ya taru a idonta saboda nauyin kalmar.
Amal ta ci gaba da cewa.
“Maleekh, mahaifiya darajarta babba ce a rayuwarmu. Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce: ‘Ku bi uwa! Ku bi uwa!! Ku bi uwa!!! Har sau uku, sannan ya ce ku bi uba.’ Wannan ya nuna mana uwa ita ce ginshiƙin rayuwa, ita ce hanyar rahamar Allah gare mu.
Allah Maɗaukakin Sarki ma ya umarce mu a cikin Alkur’ani: ‘Mu yi wa iyaye biyayya da kyautatawa, musamman uwa da ta ɗauki ciki da wahala, ta haife ka da zafi, ta shayar da kai da ƙauna.’ (Suratul Luqman: 14).”
Ta ɗan kama hannunsa da ƙarfi.
“Wallahi Maleekh, ko da mahaifiyarka ta yi kuskure, bai kamata ka furta kalmar gaba da ita ba. Ka yi haƙuri, ka nemi hanyar da zaka yi magana cikin hikima da ladabi. Wannan shi ne darajar da musulunci ya ɗora mana akan uwa.”
Maleekh ya yi shiru. Hannunsa a kan sitiyari ya ɗan yi sanyi, zuciyarsa ta fara raguwa daga zafin da take. Ya kalli Amal cikin mamaki, yana ji kalmarta tana shiga zuciyarsa kamar ruwa mai sanyaya wuta.
Maleekh a hankali ya furta.
“Amal… kin yi gaskiya, Kin tuna min darajar uwa, na ji a raina… Wallahi bana nufin in yi gaba da ita. Fushin ne kawai ya rinjaye ni.”
Amal ta yi murmushi mai taushi, ta share hawayenta sannan ta ce
“Haka nake so na ji daga gare ka. Fushi baya ƙara mana komai sai haɗari. Amma idan ka daidaita kalmomin ka da addini ya koyar mana, zaka kasance cikin nasara. Ka roƙi Allah ya yi maka jagora wajen kyautatawa uwa da yin adalci tsakanin soyayyata da ita.”
Maleekh ya ɗan kai mata hannu ya kama nata da ƙarfi, yana jin zuciyarsa ta yi sanyi sosai.
Ya ce
“Na gode Amal. Zan kiyaye kalamaina. Kuma zan nemi hanyar da ba zata cutar da ke ba, ba kuma zata ɓata wa uwa zuciya ba.”
Suka cigaba da tafiya, kowannensu yana jin wani irin salama a zuciya.
A ƙarshe motar ta tsaya a kofar gidan Amal. Amal ta sauƙa cikin nutsuwa, ta juya ta sake kallon Maleekh.
Ta ce cikin sanyin murya
“Ka tuna… uwa ita ce aljannah ko wuta a gare mu...”
Maleekh ya gyaɗa kai da ladabi, zuciyarsa cike da tunani mai zurfi...
Maleekh ya dawo gida da dare, fuskar sa cike da nutsuwa duk da zuciyarsa tana ɗauke da zafi. Ya shigo falon da sallama cikin ladabi.
Ammy tana zaune a kan kujera mai faɗi, tana jiran dawowarsa. Fuskar ta a ɗaure, ta ɗago kai ta kalleshi cikin tsananin fushi ta ce.
“Maleekh! Kaje asibiti ka yi hayaniya, ka rufe wa mutane ido, ka ɓata mana suna. To yanzu, a nan gidan, ka gaya min gaskiya. Wannan miskilar yarinyar Amal ce ta rufe maka ido har ka yi min tawaye?!”
Maleekh ya durƙusa a gabanta, ya dafa ƙafafunta cikin ladabi, yana kallonta da idanu masu cike da hawaye.
“Ammy… bana son ɓata miki rai. Uwa ke ce ginshiƙina, ina girmamaki sama da komai. Amma wallahi Ammy, akan batun Farha, ina roƙonki ki fahimce ni. Bazan iya aurenta ba.”
Ammy ta fizgi ƙafarta daga hannunsa cikin bacin rai
tana ɗaga murya ta ce
“Ka yi mun shiru! Kai ɗana ne, kuma kai ne farin cikina. Amma idan ka yi tawaye a kaina, kai da kanka zaka yi asarar wannan uwar takan. Aure ne da Farha, kuma dole ne! Ka ji ni kuwa?!”
Maleekh ya haɗiye yawu, cikin ladabi ya ce
“Ammy, ki gafarta mun. Ni ɗanki ne tabbas, ban isa in yi musayar yawu dake ba. Amma ki duba gaskiya da adalci, ki duba irin halayen Farha. Kin ga abinda ya faru a asibiti, kin ji da kanki likita ya ce tana shaye-shaye. Ina jin tsoron aure da mace irin wannan, Ammy. Wannan ba ƙiyayya ba ce, gaskiya ce.”
Ammy ta yi shiru na ɗan lokaci, zuciyarta na tafasa. Sai ta juya ido gefe, tana jin kalamansa amma ta ƙi sassauta wa, ta ce
“Ko shaye-shaye take, ni ce na ɗora ta a kanka. Kuma ni mahaifiyarka ce. Idan kana son ka nuna kana mun biyayya, to ka ɗauke ta da halinta. Idan ba haka ba… to ka sani, bana goyon bayanka akan Amal!”
Maleekh ya lumshe ido, zuciyarsa na tsananin girgiza. Ya share hawayen da ya taru a idanunsa.
“Ammy, zan yi biyayya a kanki akan duk wani abu. Zan baki girmanki da darajarki. Amma akan wannan aure… zan yi addu’a Allah ya sa ki fahimce ni. Bazan iya ɗaukar Farha a matsayin mata ba. Ki yi hakuri.”
Ya durƙusa har kasa, ya gaisheta da kyau sannan ya miƙe cikin nutsuwa ya fice daga falon, zuciyarsa cike da nauyin kalmomin ta, kai tsaye part ɗinsa ya wuce..
Hospital – ɗakin da Farha take..
Washegari
Ammy ta dawo hospital, ta shigo ɗakin da Farha take kwance, ta barta da Arfat ne akan ta taya ta kwana, bayan sun gaishe da Ammy, Ammy zama tayi a kujerar gefen gadon tana ɗauke da saƙon da zai girgiza zuciyar Farha....
Farha ta zaro ido tana jiran jin abinda Maleekh ya ce.
Farha da rawar murya ta ce
“Ammy… Yaya Maleekh fa? Yanzu ya yarda da aurenmu ko?”
Ammy ta zauna kusa da gadon, ta dafa hannunta tana sauƙe numfashi ta ce
“Farha, ki kwantar da hankalinki. Na yi magana da Maleekh. Yana girmama ni sosai, amma… akan aure… sai dai na ce miki, ya ƙi.”
Farha ta zaro ido, zuciyarta ta buga da ƙarfi.
Ta ce
“Ya ƙi?! Ammy kina gaya min da bakinki cewa shi da kansa ya ce ba zai aure ni ba?! To wai ni waye zan Aura idan ba Maleekh ba? Me yasa ya raina ni haka bayan duk irin ƙoƙarin da nayi?!”
Ta fashe da kuka tana bugun ƙirji, tana murɗa hannayenta.
Ammy cikin lallashi ta ce
“Ki natsu Farha. Na rantse, zan tilasta masa. Aure ba fashi. Kin ji na rantse. Maleekh ɗana ne, bai isa ya ƙi mun biyayya ba. Ki daina kuka.”
Farha cike da tsananin fushi ta ce
“Ammy ki saurara! Idan Maleekh ya ci gaba da bijirewa, sai na ɗauki fansa akan shi da waccan matsiyaciyar yarinyar Amal! Wallahi sai na nuna musu babu wanda zai yi min wulakanci a duniya!”
Ta share hawayenta da hannun rigarta, idanuwanta suka canza launi kamar wacce take cikin hauka, tana ta huci da kishi da tsanar Amal...
Ammy ta ɗan ja da baya tana kallonta da mamaki, zuciyarta na tunanin “Ko dai shaye-shayen nan ya fara shafar kwakwalwarta?”
Arfat itama bakin ƙofa taje ta tsaya ganin yanda Farha take wani irin huci kamar mayunwacin kare...
NEXT NEXT NEXT....
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 29 to 30
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
Ɓangaren Amal kuwa bayan ta koma gida..
Tana shiga cikin falon gidan da sallama, zuciyarta cike da gajiyawar rai, sai ga Inna da ke zaune tayi tagumi, idonta cike da hawaye. Da jin muryar Amal ta firgita, ta miƙe da sauri kamar za ta faɗi.
Inna da kuka, ta rungumi Amal da ƙarfi tana faɗin
“Alhamdulillahi, Alhamdulillahi! Na san ai dole Maliku ya karɓo ki daga hannun waɗancan ƴan sandan nan. Allah ya tsare ki, Amal na… Wallahi ina tsoron kada wani abu ya same ki!”
Amal ta ji jikinta ya ɗan yi sanyi, ta rungumi Inna sosai kamar ƙaramar yarinya da ta dawo jikin uwa. Hawaye suna zuba daga idonta, tana goge wa Inna hawaye..
Ƴan aikin gidan da ke cikin kitchen suka fito da gudu, kowacce ta rungumi Amal, suka ce cikin farin ciki
“Alhamdulillah! Mun yi kewarki Hajiya Amal! Kin dawo lafiya, mun gode wa Allah!”
Falon ya cika da hawaye na farin ciki da godiya wa Allah, kamar ba su da abin da zasu ce sai
“Alhamdulillah”.
Amal ta zauna a kujerar falon, tana goge hawaye, ta dubi kowa da murmushi cikin kuka, ta ce:
“Ku daina damuwa, ku kwantar da hankalinku. Ni dai Allah ya ceto ni, wallahi idan ba saboda Maleekh ba, da yanzu ban san halin da nake ciki ba…”
Kowa ya jinjina kai, falon ya koma cikin shiru na tausayawa, amma a zuciyar Amal akwai wani irin nauyi da ƙuduri na cewa dole ta fuskanci wannan ƙalubalen da karfin imani.
A can hospital kuwa..
An sallami Farha daga asibiti, an dawo da ita gida. ta shiga ɗakinta ta zauna Ammy itama ta shigo tare da zama a kusa da ita... Fuskar Farha cike take da damuwa, koda yake har yanzu akwai ɗan murmushi saboda farin cikin samun kulawar Ammy..
Farha ta ɗago ta dubi Ammy cikin raunin murya ta ce
"Ammy, dan Allah yanzu ya zanyi in shawo kan Maleekh zuwa gare ni..? Kullum sai gudu na yake..."
Ammy ta kalleta da idanu masu cike da ƙauna da kuma tsananin ƙuduri, ta kama hannun Farha tana shafa shi ta ce:
"Ina so ne, Farha, nasa ranar baikon ku. Ba zan wani ɓata lokaci ba."
Idon Farha ya cika da walƙiya na farin ciki, ta sau murmushi na jin daɗi, ta rungumi pillow tana jin kamar mafarki take, ta ce
"Ammy, idan har da gaske haka ne, ai yana da kyau mu haɗa ranar baiko da ranar birthday ɗinsa. Kin manta kuwa? Jibi ne birthday ɗinsa..."
Ammy ta yi dariya cikin jin daɗi, ta girgiza kai:
"Taya zan manta shekarun yarona? Tabbas jibi zai cika shekara talatin cifff. A ranar birthday ɗin, bayan kowa ya taru, zan mayar da ita rana ta musamman ranar baikon ku ke da shi. Zan ƙira dangi, abokan arziki, har da iyayenki daga London."
Farha ta zaro ido cike da murna, ta riƙe hannun Ammy tana murza shi tare da faɗin
"Ammy, wannan fa bazai zama abin alfahari ba kawai, zai zama mafarkin rayuwata! Amma shi zai yadda da wannan baikon? Kinsan fa Ya Maleekh baya ƙaunata kamar yanda yake faɗa..."
Ammy ta danne murmushi, ta yi ƙwafa, sannan ta jinjina kai cikin girmamawa da girman kai irin na uwa mai iko ta ce
"Farha, ki bar wannan damuwar a hannuna. Zan tilasta shi. Daga yau za a fara shirye-shiryen birthday ɗinsa. Zan sanar masa ya fara gayyatar abokansa da sauran jama’a. Amma maganar baiko? Wannan sirrinmu ne. Ba za mu sanar masa ba sai a ranar birthday ɗin. A lokacin, babu yanda zai yi domin bazai iya bijirewa ba, saboda kowa zai taru, sai dai ya amince dole."
Farha ta sake dariya cikin farin ciki, ta jingina kanta a kafaɗar Ammy tana furta cikin sirri:
"Ammy… kina da hikima sosai. Wallahi ina sonki da zuciyata dukkaninta."
Ammy ta shafa gashinta a hankali, tana murmushi mai cike da annashuwa ta ce
"Ni ma ina sonki, ƴata. Ki kwantar da hankalinki. Jibi rana ce da ba za ki taɓa mantawa da ita ba."
A haka Farha ta kwanta saman gado tana ta tunanin yadda wannan ranar zata zame mata babban nasara, zuciyarta na cike da mafarki da buri. Ita kam Ammy kuwa, zuciyarta na daɗa ƙarfafa cewa zata cimma burinta na ganin ɗanta ya auri Farha, ko da kuwa hakan ba da yardarsa ba.
Bayan Ammy ta bar ɗakin Farha, part ɗin Maleekh ta nufa...
Tana zuwa ta fara knocking, a hankali yazo ya buɗe mata...
Ta shiga sannan ta zauna akan sofas falonsa, ta bashi umarnin ya zauna kusa da ita, shima zama yayi, Ammy ta riƙe hannunsa tana murmushi ta ce
"Suprise my son.."
Maleekh yace "Suprise ɗin me?.."
Ammy ta ce
"Jibi birthday ɗinka, za'a haɗa dinner party na musamman, zan sa a shirya mana hall mai girman gaske, a shirya komai zuwa jibi.."
Maleekh ya ce
"congratulation to me.."
Ammy ta ce
"Inaso ka gayyato abokanka na kasashen waje dana nan Nigeria....sannan iyayen Farha zasu zo daga London.."
Maleekh ya ce "Shikenan idan sun zo, sai su ɗauki ƴarsu su tafi da ita, domin bazata lalace da shaye-shaye anan gaban mu ba, mutane zasu ce don ba ke kika haifeta ba shiyasa kika barta ta lalace, kinga daga shaye-shaye zata fara bin maza..."
Ammy ta ce
"Ya isa haka Maleekh, dan Allah kada idan iyayenta sun zo ka nuna musu ƙiyayyar da kake yiwa ƴarsu.."
Maleekh ya jinjina kai yana kallon gefe..
Daga nan Ammy ta fice a ɗakin ba tare da ta sanar masa maganar baikonsa da Farha ba...
Washegari Ammy ta sa an fara shirye-shiryen party birthday ɗin Maleekh...
RANAR BIRTHDAY DINNER, PARTY NA MALEEKH
An kai ga ranar da Ammy ta sha alwashin ta zamarwa ɗanta suprise. Tun daga safe gidan ya cika da hayaniya da shirye-shirye. Ana shiga ana fita, an ɗauko masu kwalliya, decorators, caterers, DJs, da security.
An zaɓi Hilton Event Center a cikin Abuja, hall ɗin da aka san shi da girma da walwala. Aka kawata wurin da gold da white. Daga ƙofar shiga har zuwa ciki, aka shimfiɗa red carpet, tare da golden lights da balloons masu kyau.
A tsakiya an kafa manyan LED Screens suna nuna hotunan Maleekh tun yana ƙarami har zuwa girmansa. A gefe kuma aka kafa photo booth da aka rubuta:
✨ “Maleekh @30 – The King’s Birthday Dinner” ✨
An shirya teburori masu kyau da gilashi mai ƙyalli, aka sa fresh roses da candles a tsakiyarsu. Kowa da aka gayyata yana samun invitation card mai golden foil, saboda VIP event ne.
Lokacin da manyan baƙi suka zauna, aka kunna background music. Aka kashe wutar hall ɗin gaba ɗaya, sai fitilu masu colour suka fara haskawa.
Sai jin ƙarar horn ɗin motor daga wajen hall, alamar cewa Lamborghini Urus mai launin black-gold ta iso.
Security masu baƙin suits suka buɗe masa hanya.. Cameramen ne suke ta ɗaukar hotuna, dron ɗin sama yana capturing cinematic entry ɗinsa.
Maleekh ya fito cikin royal tuxedo mai launin navy blue da golden tie, yana tafiya a kan red carpet kamar sarkin da ake masa coronation. Duk hall ɗin ya tashi da tafi da murna.
PROGRAM ENTERTAINMENT
MC (AY) ya ɗauki mic yana yiwa kowa barkwanci cikin annashuwa... Sai kuma DJ mai suna DJ Neptune ya saka kiɗa mai armashi.
Live Band suka fara rera waƙa domin Maleekh, suna cewa “Happy Birthday, The King @30”.
An yi special dance presentation daga ƙungiyar rawa cikin uniform mai kyau.
Wani celebrity singer, Davido, ya rera waƙa ta musamman domin bikin birthday...
Bayan shagalin farko, aka buɗe buffet. An kawo abinci kala-kala:
Nigerian Dishes: jollof rice, fried rice, tuwo da miya.
Intercontinental: Chinese noodles, pizza, pasta.
Seafood section: prawns, shrimps, lobsters.
Dessert corner: ice cream, chocolate fountain, cake slices, da fruits carving.
Drinks kuma kala-kala: mocktails, cocktails, champagne popping, har da tiger nuts da zobo ga masu avoiding alcohol.
(Kan bala'iiii har da ni a wurin cin Abinci domin mu acici ba'a barin mu a baya🤣🤣)
BIRTHDAY CAKE
An shigo da cake mai layers 7, mai launin gold da white, wanda aka kawata shi da diamonds designs. A kan cake aka rubuta
🎂 “Happy 30th Birthday, Maleekh The King” 🎂
Maleekh ya yanka cake tare da Ammy da Farha a ɗayan gefensa, aka kunna fireworks a cikin hall...
Bayan an gama didimar Birthday sai kuma
SURPRISE ANNOUNCEMENT 😳😳
Bayan kowa ya zauna cikin farin ciki, Ammy ta miƙe tsaye da mic a hannunta. Tana murmushi cikin nishaɗi, ta ce:
“Alhamdulillah. Yau rana ce ta farin ciki a gareni da iyalaina. Na ga ɗana ya kai shekara 30, kuma Allah ya yi masa arziki, lafiya, da daraja. Amma wannan ba kawai birthday bane…”
Kowa a hall ɗin ya ɗaga kai cikin mamaki.
“…bayan birthday sai kuma ranar baiko a yau. Ina farin cikin sanar da ku cewa yau ɗana, Maleekh, zai ɗaura baiko da Farha.”
Hall ɗin ya ɗauki ihu da mamaki. Wasu suka tashi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 62