tunda taji ya ɗauko zancen anbiyawa Sadeek jikanta amma shi da yake ɗan sa yaƙi biya masa, Daga nan bai tsaya ba yafita daga gidan shima ya wuce can gurin abokinsa dake yin kayan printing yana so ya yiwa wata amarya data basa ayi mata memo's da kuma deary da sticker na aurenta.
******
Washe gari kowannen su bai samu tashi dawuri ba sai wajejen karfe 12 na rana saboda gajiyar jita, Uwar gayya meenal ko motsawa batayi ba don ko sallar asuba da Mommy ta tada ita komawa tayi tayi kwanciyarta, A gagguce Mommy tayi wanka sannan ta ɗakko wani yadinta mai ɗan sauki tasaka ta shafa mai da ɗan lipstick sannan ta nufi kitchen, Ganin masu aikin sun gama komai yasata nufar daƙin Dady tana tuna farincikin daya sakata juya wajen birthday ɗin Meenal, murmushi ta saki tare da ƙarasawa bakin ƙofar ɗakin tana tura ƙofar, ga mamakinta Dady bayanan da alama yafita kenan tana bacci kuma bai karya ba, gaba ɗaya duk sai taji babu daɗi, toilet ta wuce ta wanke masa shi tas sannan tafito ta gyare ɗakin ta turare da room freshner masu ƙamshi daga nan sai ta haye sama zuwa ɗakin Meenal ta iskota kwance tayi ɗai-ɗai a gado daga ita sai wata banzar rigar bacci, sakkowa kasa tayi don kar ta tada ita cibi ya zama ƙari ta zauna ta shiga ƙaryawa, tana cikin karyawar wayarta ta shiga ringing, murmushi ta saki lokacin da kallonta yakai ga screen ɗin wayar tana kallon lambar *KAMAL* dake yawo akai don ba laifi shi tana ɗan shiri dashi, kawai shi dai kabarshi da saurin fushi....
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
#Mutallab Asad
#Ƴan Tagwaye
#Billy S Fari
#Nana Diso.
*MUTALLAB ASAD*
(Labari mai taɓa zuciya)
NA
*BILLY S FARI*
&
*NANA DISO*
ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU
TAGIYAR BIYU TAFI ƊAYA.
SHAFI NA GOMA SHA HUƊU
_______
https://www.tiktok.com/@maims_kiddies
"Lallai Dr irin wannan kyau haka tamkar kunzo daga ƙasar UK? Gaskiya kayan jikin su Hanan sunyi matukar kyau, amma dai ba'a ƙasar nan kuka siya ba?" Cikin dariya Dr Aisha tace. "A ƙasar nan muka siya, sai dai kamar yadda kika ce ɗin haka ne, duk wannan kayan da kika gani a jikin yaran nan na ƙasar UK ne da *@Maims_kiddie* take sai da su a cikin Nigeria, muma a wajanta muka siya kuma ba tare da munje inda take ba, kayan na gani a Instagram account ɗin ta na *KIDS THRIFTY/OKRIKA STORE.* Kayane masu kyau da kwari daki bari kenan malam Khadija dan tun da na fara siyan kayan yara a wajanta shikenan na dena ganin kyawun na ko'ina. Kema/kuma zaku iya nemanta a Instagram link ɗin dake sama. Za kuma ku iya samunta a WhatsApp ta wannan link ɗin dake ƙasa. Ko lambar wayarta.
https://Wa.me//08101378616
________________
Ɗaga kiran tayi tana dariya ƙasa-ƙasa don tasan daƙyar in bai fara dayi mata ƙorafi ba don tunda ya wuce Egypt ɗin sau biyu kacal sukayi waya da shi".
"Mutan Egypt ya kake ya ƙarfin jiki?".
"Momcy bazan amsa ba tunda kin kasa nemana, sai dai dana gaji juya na daure nakira Dady yake cemun wai duk kunyi bacci"
"Bari kawai KAMAL duk mun gaji yarinyata tayi celebrating na birthday ɗinta".
"Woow..shegiya Meeneluwa shine kota faɗa mani, Momcy ya bukin nasan dai dole akwai zafaffun babies agurin ko?" Ɗan ɗaure fuska Mommy tayi haɗe da cewa, "Wai kai Kamal har yau baka natsu ba ka dena wannan shashancin? Yaushe nafara wasa dakai?" Dariya yayi haɗe da cewa,
"Sorry Momcy babies ɗinnan fa duniya ne wlh".
"To Allah yaƙara shirya mani kai ya nan Egypt ɗin kuma yaushe zaka dawo?" Dariya Kamal ya sake saki haɗe da cewa "Momcy Egypt so nice Baki ganeni ba gaba ɗaya na koma jiki duk madara, na karayin fresh Momcy sai ma kin ganni, wayyo Allah bari na gaya maki Momcy ingayamiki ina nan ƴammatan etophia da india ke mun wanka bakiga yanda suke kulawa dani ba wannan ta shafa kai wannan ta shafa ƙirji abun gwanin burgewa to ta ina zan yarda na dawo, kallon macce ma kafiye yi sai ace ka zama ɗan iska, ga inda za'a lundeka da mai Momcy ayi maka Rauda ba wanda ya damu dakai, ai dawowata ba nan kusa ba". Cike da tashin hankali Mommy da taji abinda yake daɗi tace,
"Subhanallahi Kamal menene haka kake faɗa sai kace ba ɗan musulmi ba Musulmin ma ɗan Hausa fulani? Da gyara Kamal zamanka wajen nan sam babu alkhairi don haka dole a tattaro inaka-inaka ka dawo".
"What! Mommcy ina wannan shaƙatawar haɗe da wataya ina jin daɗi na? Kawai kibar wannan zancen don yadda babies ɗin nan ke kula dani suna wani lailayani Momcy kamar jariri bazan iya dawowa ba, karatuna ma anan zancewa Abba zan ƙarara shi kawai naci gaba da morewata".
"A'uzubillahi Kamal ubangiji Allah ya shiryaka, sam hakan bazata saɓuba ba Kamal daga jinya Shikenan sai kafara Waɗan nan ƙazaman zantukan, ni yanzu ina karyawa idan nagama mayi waya muƙarasa maganar". Mommy tafaɗa ganin abun karin nata na nema ya huce, a ɓangare Kamal cewa yayi, "Easy Momcy naji kin wani tayar da hankali ki, bada wani abun bane amma Shikenan zan miki video call later bye." Yana katse wayar Mommy ta ture abincin dake gabanta taji tama kasa ci zuciyarta sai wani raɗaɗi takeyi, innalilahi wainna illahirrajiun ya zatayi? Idan fa ɗaya ne baza tayi shiru ba batare data sanarwa da mahaifinsaba?, Don haka koma me Dady zai ce dole ta sanar masa da cewa yasa Kamal ya dawo gida hakanan tunda ya samu sauƙi koda Abban bazai fahimceta ba, Tana cikin wannan tunanin haka taji sallamar Dady yana shigowa palourn yaransa sun riƙo masa ledojin da yatawo dasu, miƙewa tayi tana yimasa sannu da zuwa tare da ƙarasowa ta karɓi hularsa da babbar rigarsa da yake cirewa, dining ya nufa don yunwa yake ji lalurar gaggawa ce kawai ta fidda shi da sanyin safiya ya zauna kan dinning table ɗin, sai da takai kayan ɗakinsa ta dawo sannan tace, "Me zan zuba maka ranka ya daɗi?" Sai daya saki murmushi yana kallon benen yace, "Duk abinda na samu, ina Meenal har yanzu bata tashi ba?"
"Wlh kuwa sai biyu ina zuwa dubota a gani ko ta tashi kasan akwai gajiya tattare da ita shiyasa". Taƙare zancen tana zuba masa abun karin nasa data san yana matuƙar so, wato haɗin cowleg da kuma soyayyen buredi sai ruwan tea, har yagama tana can tana tunanin kamala tare da haɗa zantukan da zata fuskanci mahaifin nasu dasu ya fahimceta yayi abinda yadace ga ɗansa don wannan ba maganar da za'a wofantarwa bace, idan ta kamo wancan zancen ya kucce mata ta sake komo wani shima ya kucce, ganin hankalinta sam yau baya kansa kamar yanda ta saba yana cin abinci tana yimasa fira ya sashi cewa, "Lafiya kuwa mansura ko wani abun yafaru ne?" Firgigit tafito daga tunanin haɗe jan Numfashi kafin tace, "Dady dan Allah Kamal yadawo gida haka tunda ya samu sauƙin, kasan fa shine abokin firata Allah nafara kewarsa".
"Shi kuwa yama manta dake don yace na tura masa kuɗi yaci gaba da karatunsa acan". Dady ya faɗa cike da farin ciki da jin daɗin yanda ta nuna damuwa ga ɗansa yana dariya, Murmushin yaƙe tayi tare da cewa, "Kamal ai bazai manta dani ba, in da dai shalelenka ce".
"Ita da kika tsana bakya so ko? To ta Allah ba taki ba, shi kuma tunda acan yake don karatunsa ai sai yayita zama". Yafaɗa tamkar bashi yagama dariya yanzu ba, Mommy kuwa tsananin tashin hankali batasan lokacin da tace,
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun, kada kayi hakan Dady tamkar kasa hannunsa wajen lalata masa rayuwa".
"Oh da yake ba ɗanki bane dole kice hakayadawo hakanan kinyi kewarsa ashe duk munafurci ne? Wai don Allah me isa kike hakane mansura? Me yarana suka tare maki fisabilillahi". Runtse idanuwa Mommy tayi tana jin zafin kalaman dake fita a bakinsa da inda sabo izuwa yanzu yaci ace ta saba dasu, cikin sanyin murya da kuma kwantar dakai don nuna masa abinda yake zargi ba haka bane tace, "haba Dady shikenan banida damar faɗar gaskiya akan yarannan sai ka fassarani kana cewa ina baƙin ciki? Akan me maida keda ƴaƴanta kuma dukiyar taka ce akan me zanji baƙin cikinsu don kayiwa abunka hidima? Yanzun nan ya kirani fa yake gayamin wai yana nan ƴan matan etophia da india suna masa wanka..." Ta kwashe firar da sukayi tsaf ta faɗa masa, ga mamakinta ba abinda Dady zai cewa lokacin daya zuba mata idanuwansa ransa a ɓace zuciyarsa na ƙuna sai, "Duk sharrin da zaki yiwa ƴaƴana kiyi masu Mansura amma ban yarda kiyi masu na bin mata ba ko zina, kinga! Tunda bakinki bazai faɗi alkhairi ba ga ƴaƴana tashi kibani guri? Yafada a tsawace ransa na mugun ɓaci tare da dukan dining table ɗin, jiki a sanyaye Mommy ta miƙa dama tasan za'a rina Batare da tace komai ba tatashi tabar masa gurin ta shige daƙinta, shima fuuu.. yamiƙe yafice gidan gabaɗaya dan yana da meeting ɗin da zai gabatar nan da mintuna ashirin duk da yanda yake son ganin ya ƴar tasa Meenal ta tashi"
Meenal kam tana tashi tayi wanka sannan tasaka wasu ƙananan kaya a gurguje ta gyara saboda kiranta da bestie yakeyi, ba tare da Mommy ta sani ba kawai ta sauko cikin hanzari tabar gidan don gab ake da kiran sallar magarib kada ta ganta ta ɓata mata lokaci da banzan surutunta da nasihohinta na islamiya ta saka kai tafice. Ba ita ta samu ta isa hotel ɗin ba sai wajejen isha'i shima tana isa ta danna masa waya, fitowa yayi ya riƙo hannunta suka huce ciki. "Bestie i miss you". Yafaɗa yana ɗan hugging ɗinta, zaiyi kissing ɗinta tace "No bestie na gayamaka bana son wannan abun ko?" Kallonta yayi cike da mayata yana lashe lips ɗinsa na ƙasa yace, "Haba besty menene haka wai? Meye bambancinsa da hugging ɗin da kika barni?" Cire jikinta tayi daga rungumar daya yimata tana jan tsaki tace "To shima bana so kada ka sake". Sanin halin Meenal kar ya sashi saurin riƙe hannunta a ɗan ruɗe yace, "Bazan kiri wannan hukuncin ba Meenal don Allah kada kice haka besty, wai ko kin manta natsuwar AAB gaba ɗaya na tattare dake ne?". Ɗan harararsa tayi cike da soyayyar da suke alaƙantawa da besty kafin ta saki dariya tana janye hannunta tace, "matsoraci! Kai ɗin ne kamar baka gane zancena wani lokacin Allah bana son abunnan is not good at all, bayan haka Ni ƙazantarsa nake ji sosai s please stop it!"
"An gama Besty bazan sake ba" yaɗa yana dariya tare da janyota ya sake haɗawa da jikinsa, hira suka sha sosai kafin yayi musu order wine da abinci, taci abincin sosai don tana jin yunwa ta ture wine ɗin a gefe tana cewa, "Kai da tare da Mommy kake rayuwa tabbas saita kasheka wataran saboda rashin fahimtar dai-dai ko akasin haka, ina itama wannan ɗin nasha gayamaka bana so, ban iya shaye shaye ba kuma bazan fara yanzu ba saboda kai, ko da zanyi to zanyi ne a lokacin dani na saka kaina bawai wani ya saka ni ba".
"Saboda me Meenal komai ke bakyayi? Akan wani dalili?" Wani kallo tayi masa kafin yamiƙe ta ɗauki jakarta tana cewa
"That's not your bussiness AAB, think is 12 yanzu dare yafara yi abeg matsa na tafi" don zaune yake a gabanta inda zata i ta wuce, marairaice fuska yayi yace, "Haba Besty yanzu ko ɗan romancing baza muyi ba?" A razane Meenal ta ɗago ta kalleshi haɗe da cewa, "To hell with you AAB, Anya ƙasan real definition na besty kuwa? Kula, kyautatawa, rufe sirrin juna And so on, wannan shine besty bawai bawa juna jikinkunanku ba sai kace wasu aladu, our bodies besty is main for our spouses, don haka kada ka sake furta mani irin wannan ƙazamiyar kalmar".
Tana ƙare faɗa haka ta karkata abunta tafice daga ɗakin ranta a ɓace....
**********
Mutallab kuwa bai iso gida ba sai ƙarfe shida dai-dai na marece, yana ƙaraso a harabar gidan nasu yaga mutanen gidan kowa a tsai tsaye sun taki Dady da dama tafiyar marece zai yi zuwa ƙasar Jordan da wani business zai kaiwa jirgi su zai tashi ƙarfe bakwai dai-dai, ƙarasawa yayi yaba Ya jamil hannu dake kusa dashi suka gaisa sannan yace, "Barka da marece Abba tafiya zakayi ne?" Wani kallo yayi masa duk da yasan bai sanar dashi zancen tafiyar ba amma haushinsa da yake ji aduk lokacin daya bayyana agabansa yasashi cewa "Zama zanyi Mutallab, nace zama zanyi shashashan yaro daga gidan uban wa kake tun ɗari naketa faman nemanka baka ba labarinka?" Kai tsaye Mutallab yace, "Kayi haƙuri Abba naje wajen dako ne". Yana jin wasu hawaye na tarar masa cikin idanuwa, Dariya Ya Jamil yayi har Umma na tayasa. Muryar Dady suka ji yace "Da kyau haka kayi dai-dai Nagode". yana shigewa motarsa. Da sauri Mutallab ya nufi wajen motar jin yanayi maganar mahaifin nasa cikin ɓaci rai yana cewa, "Abba.." kafin ya ƙarasa Abba ya rufe marfin motar da ƙarfe ba tare daya saurarensa ba, hawayen da yake ƙoƙarin riƙewa yaji suna sauko masa ganin irin fushinsa mahaifin nasa yayi da kuma yanda ya muzanta a wajen, da haka Jamil ya ƙaraso kusa dashi haɗe da dafa kafaɗarsa yace, "Karka damu ƙanina, Abba zai sauko amma ina kai ina dako kana ɗan gidan attajiri kamar Abba..." Bai rufe baki ba Jalil daya kai ƙololuwar hasala jin abinda ya Jamil ke faɗa sai kace bashi ne ya ɗora shi akan wannan shawarar ba don ranar yana jinsu yana bayan window ɗin ɗalibai yana wanki, ganin kawai sukayi yaja hannun Mutallab yana watsa masu wani banzar kallo su duka yace, "Munafurcin banza Munafurcin wofi, in Sha Allah ta Allah ba taku ba.." bai ƙarara ba shima yaji saukar mari a fuskarsa da Mutallab yayi masa jin abinda ya faɗa, dukkanninsu Murmushi sukayi tare da sauke ajiyar ganin abinda Mutallab ɗin yayi cike da jin daɗi, Afrah kawai ce ta runtse idanuwa tana kauda kanta gefe, "Su ɗin iyayenmu ne shi kuma yayanmu ne, dole ka girmamasu ka kuma san irin maganar da zaka faɗa akansu". Mutallab yafaɗa a ɗan zafafe sannan ya juya ya nufi ɗakinsa yana share ƙwalla tare da jin zafin marin da yayiwa ɗan uwan nasa, hakan ne kawai zaiyi masa ya kubutar dashi daga sharrinsu da kuma makircinsu na ganin sun cutar dashi saboda tsaurin idanuwansa da baisan inda ya samo su ba..
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
#Mutallab Asad
#Ƴan Tagwaye
#Billy S Fari
#Nana Diso.
*MUTALLAB ASAD*
(Labari mai taɓa zuciya)
NA
*BILLY S FARI*
&
*NANA DISO*
ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU
TAGIYAR BIYU TAFI ƊAYA.
SHAFI NA GOMA SHA BIYAR
Tunda Jalil ya shige ɗakinsa ya kulle Tsananin zafin da ransa yake masa ba zai misaltu ba, me yasa akowanne lokaci laifinsa ya Mutallab yake gani? Hakan bakaramin taɓa masa zuciya yakeyi ba, har dare bai koma fitowa ba yana zaune a daƙinsa, daga sallar magrib har isha idan yaje masallaci baya bari su haɗu da ya Mutallab saboda yadda yake jin zafi a zuciyarsa na yaƙi tsayawa ya fahimci ko suwaye matan uban nasu da kuma Ya Jamil, ban banci da rashin kaunarsu karara yaƙe azuƙatan mutanen nan, sai dai abinda bai sani ba Mutallab na sane da yadda kowannen cikin iyayen nasa da ƴan uwan nasa suka ɗaukesu, kawai baya so ne su lalata tarbiyyar da mahaifiyarsu ta ɗorasu akai adalilin waɗannan abubuwan da ake yi masu, ya tabbata wataran duk wucewa zasuyi kuma zai zama tahiri duk da ganin wucewar sai an ƙara haɗawa da haƙuri da juriya harma da kauda kai.
Sai da Mutallab yayi shirin kwanciya sannan ya nufi ɗakin ɗan uwan nasa, cikin sa'a kuwa ya tadda ɗakin a buɗe don dawowarsa kenan daga bakin gate ya kaiwa maigadi takeaway ɗin da Afrah ta kawo masa da yaya Mutallab ya sawo masu a kasuwa saboda gudun kar ya lalace tunda baici ba, dama haka yake idan yana fushi har abincin fushi yakeyi dashi sai daga baya idan yunwa ta nuna masa ta fishi taurin rai tukuna yake nema yaci.
Cikin kamewa Mutallab ya tura ƙofar ɗaƙin ya shiga bakinsa ɗauke da sallama, abakin ƙofar ya tsaya yana jingina a jikinta tare da naɗe hannayensa a ƙirji ya yi crossing ƙafafuwansa yana kallon Jalil dake zaune bakin katifarsa yana rubutu a wani littafi, ɗago kai ya yi ya kalli ya Mutallab sannan ya mayar da idanuwan nasa ga littafin da yake rubutu akai yana cewa,
"Barka da dare ya Mutallab".
Mutallab yasan fushi yakeyi dashi akan abinda ya faru ɗazu, so yakeyi ya nuna masa kuskurensa hakan yasa bai tanka masa ba yayi kamar ma bai ji me yace ba yaci gaba da kallonsa kawai, a hankali Jalil yaja ajiyar zuciya ya sauke tare da saka abun rubutun da yakeyi a tsakiyar littafin dake hannunsa sannan ya rufe ya ajiyesa gefen katifar tasa, cikin sanyin murya yafara magana ba tare daya ɗago kansa ba yake cewa, "Duk da abubuwan da suke yimana ban taɓa yi masu wani kallo ba sama dana matan mahaifina kuma iyayena, haka ma ya Jamil ako yaushe ina ƙoƙarin ganin na bashi girmansa da kuma matsayinsa na babban yaya acikin gidan nan, sai dai ko sau ɗaya zuciyata bazata taɓa iya jurar ganin ɓacin ranka ba kona Afrah, wulaƙancin nasu yafara yawa ya Mutallab akwai buƙatar ko da sau ɗaya ne muriƙa nuna masu muma fa ƴaƴane acikin gidannan ba bayi ba!"
Ya ƙarasa maganar tare da ɗago kai idanuwansa cike tab da ƙwalla yana kallon ya Mutallab, ganin har lokacin bai tanka masa ba yasa yaci gaba da cewa, "Taya kake tunanin zan iya riƙe fushina akan yaya Jamil bayan nasan shine ya baka shawarar zuwa kayi dako amma yazo yana faɗa maka maganar banza har anayi maka dariya? Nasan har cikin zuciyarka ka amshi shawarar tasa dan kana shigowa na hango tsananin gajiya da kasala atattare da kai, na lura da yanda jikinka yayi sanyi saboda tsananin wahala, haka hannuwanka ma ko kaɗan basu ɓoye tsantsar jigatar da sukayi ba wajen aikin da kayi, na hango haka lokacin da ka meƙawa afrah ledar dake hannunka daƙyar kake iya ɗagasa". Shiru yayi kafin cikin raunanniyar muryar da kuka yaci ƙarfinta yaci gaba da cewa "Bazan iya haƙuri ko kauda kai ba ko kaɗan koda me zai faruwa dani, na yarda suyita nuna mana bambanci dasu har Abba, amma ban yarda da cin zarafinka ba ko kaɗan, meye baka musu ko meye ka tsare musu da zasu tsaneka haka? Duk da wanzuwar su acikin gidan nan a matsayin matan mahaifinmu amma ako da yaushe kaine wanke banɗakin Abba, kaine gyara masa daƙinsa da duk wani aike nasa komai wahalarsa, wahala kakeyi da kowa kaf a gidan nan har ni amma kaine abun wulaƙantawa, sau ɗaya an kasa faranta maka agidan nan kuma kace inyi shiru har kana huƙuntani agabansu bayan kasan hakan faranta masu zai yi? Har ga Allah ni zuciyata bazata iya ɗauka ba wallahi, bazan iya ba ya". Yaƙarasa yana mai kara sakin kuka".
Atake Mutallab yaji zuciyarsa ta karye, lokaci ɗaya yanayinsa yaƙara canzawa ganin yadda Jalil ke kuka, cikin son ɓoye damuwarsa yace,
"Kenan ka zaɓi a matsayina na yayanka gazawata tafito fili ta hanyar kasa baku kariya daga cutarwar da za'a iya yimaku akan haƙuri da duk wani abun da zai janyo acutar mani daku?" Yayi maganar a tausashe cike da kulawa, ɗago kai Jalil yayi haɗe da cewa,
"Kai ɗin ba rago bane ya Mutallab balle gazawarka agaremu ta iya bayyana, sau ɗaya dai kabari ina taka masu burki ga wasu abubuwan idan kai bazaka iya ba, hakan zaisa su fahimci bawai tsoronsu muke ji ba, tarbiyar mahaifiya ce dake gudana a cikin jinin mu kesa muna ɗaga masu ƙafa, idan suna ganin zasu iya galaba akan Abban mu da asirce-asircensu to mu bazasu taɓa iyayin komai akan mu ba tunda mun riƙe Allah mun kuma rike addu'oin safe da marece kowanne lokaci".
Mutallab daya fara jin maganganun Jalil na neman jefasa a wani tunanin ya lumshe idanuwa haɗe da buɗe su lokaci ɗaya yace, "Ya isa haka Jalil, don Allah kabarsu suyi duk abinda zasuyi, zagi ko cin mutunci bazasu laƙe mana ajiki ba, ina sane da duk abun da sukeyi kuma da gangan nakeyi tamkar bana fahimtar su saboda hakan na hasko mani hanyar da zamu bi ne mugyara gobenmu, damuwata ɗaya kada su cutar mani daku, hakan ba ƙaramin raunata zuciyata zai yi ba shiyasa nake ƙoƙarin dakatar dakai akoda yaushe, don dukkansu zasu iya maido idanuwansu akanka kai kaɗai, ni kuma bana buƙatar hakan Jalil ya kamata ka fahimta". Ajiyar zuciya Jalil ya sake saki akaro na biyu tare da cewa,
"Shikenan ya Mutallab in Sha Allah zan kiyaye, kayi haƙuri bazan kuma ba koda naji zuciyata bazata iya ɗauka ba zanyi ƙoƙari na kauda kaina ko kuma nabar gurin atake kada na aikata abunda zaka koma jin babu daɗi." Sosai Mutallab yaji daɗin yadda Jalil ya fahimci abinda yafi buƙatar yariƙayi yace,
"Am sorry too, kaci abinci?" Shafa kai Jalil yayi don kuwa koda yace yaci ɗin ba gaskiya yafaɗa ba kuma ba yarda ya Mutallab ɗin zaiyi ba tunda yasan halin shi, murmushi ya Mutallab ya saki tare da girgiza kai kawai ya juya yana cewa, "ka rufo ɗakin naka ka sameni a waje". sannan ya fice
Da ƙafa suka taka sosai shi da Jalil suna ci gaba da tattaunawa akan matsaltsalun gidan nasu har suka kusa fita anguwar tasu, wajen wani mai saida shayi suka nufa sukayi sallama Mutallab ya miƙa masa hannu suka gaisa sannan yaja bencin dake gefe suka zauna bayan shima Jalil sun gaisa Mutallab yace a haɗa masa tea da bread na ɗari biyar da soyayyen ƙwai guda biyu, ba ɓata lokaci aka haɗa aka kawo masu ya turawa Jalil gabansa yana cewa, "Tunda Allah ya taimaka gimbiyar taka ta sauka sai ka taimaka kaba ciki nashi haƙƙin shima".
"Yaya kaifa?"
"Alhamdulillah sai da naci nawa muka fito, kasan mutumena akayi, kai kuma nasan yau ko ruwan gidan ba lallaine kasha ba".
Murmushi Jalil ya saki yana shafa ƙeyar kansa sannan ya soma shan tea da bread ɗin, sai daya canye komai tas wani irin zufa na keto masa alamun yunwa ta gama fita haɗe dayin gyatsa, murmushi Mutallab ya saki har haƙoransa na bayyana cike da tsokana yace, "Sannu malam Jalil mai fushi da abinci, gaskiya kayi ragon azanci fushi da ɗa'ami dan ni bazan iya wannan shirmen nakaba". Ya miƙe tare da ciro Naira dubu ya miƙawa mai shayi yace ya ƙara soya masa wani ƙwai guda biyu, suna tsaye ya gama soya ƙwan ya saka a leda ya miƙa masu tare da canjin Naira hamsin, ledar ƙwan kaɗai Jalil ya karɓa canjin kuma ya Mutallab yakarɓa yana maidawa a aljihunsa, suna isa Mutallab ya karɓi ledar a hannun Jalil ya wuce ɗakinsa shi kuma ya wuce cikin gidan, yana shiga cikin babban palourn ya hango Afrah na saukowa riƙe da littafinta, da alama wajensa ta nufa yayi tsaye har sai data ƙarasa saukowa, fuskarta ɗauke da murmushi tace, "laa ya Mutallab da fa wajenka zan je, ina wuni?"
"Lafiya klw Afrah". Ya faɗa shima yanayi mata Murmushin haɗe da cewa, "To gani injin ba laifi nayi ba aka zo mani takakka?" Littafin hannunta ta saka ta rufe fuskarta tana dariya tace, "Kai yaya waya isa? Ai baka laifi inda dai boss ne". Cewa da yaya Jalil, zaro idanuwa yayi yana nuna mata bayansa da hannu cike da tsokana irin ai Jalil ɗin na bayansa, ba shiri kuwa ta juya da nufin guduwa dan tasan zai iya riƙata ya mammaketa tunda dama yau cikin fushi yake, dariya Mutallab ya saki haɗe da cewa, "dawo matsoraciya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 54