Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dinkin albarma nagani nafada duba da za'a kaiwa abokanan ango abinci haka kawayenta sukayi sai da suka kaimusu sannan suka dawo lokacin da mutallab yashigo kasa motsawa yayi sabida yadda yaga matar tasa ta kara wani kyau mashaa Allah a dan hankali yashiga gaishe gaishe har yakarasa inda take tsaye itama tashiga kallonsa sai kuma ta dan murmusa tana faɗin " Sannu da zuwa." Tabbas yayarda soyayya gaskiyace yanzu dan suk wani zafin da ransa yake masa bisa abunda meenal tayi sai yaga ya kau gaba daya karshe ma jawota yayi gaban mutanen dake ta musu hotuja kala kala." " Mrs Mutallab asada." Murmushi kawai tayi dan ta daukarwa kanta alkawarin faranta masa ko da ita bataso dan abunda su dada sukayi mata bazata taba watsamusu kasa a ido ba dan haka sai tace masa " Aïcha mari (mijin aich). Murmushi yayi har hakoransa na bayyana nan sukashiga hotuna kala kala daga baya kuma yayi gurin dada. #Mutallab Asad #Ƴan Tagwaye #Nana Diso #Billy s fari MUTALLAB ASAD Na Billy s fari Nana diso 87. Wata irin ƙara Meenal ta daka tare da duƙewa wajen kafin cikin ɓacin rai Mutallab ya kalleta yana cewa, "Ni ba irin shashashan mazan da zasu riƙa zaunawa mata nayi masu wannan dabbancin da hauka bane, I know it's very painful alokacin da matarka taji zaka ƙara mata abokiyar zama shiyasa nake ɗaga maki ƙafa Meenal nake kuma cigaba da haƙurin zama dake, amma idan kina tunanin duk waɗannan abubuwan da kikeyi zasu iya dakatar dani ga ƙarin auren da nake da niyar yi to kici gaba karki fasa ni kuma zan nuna Mani negative side ɗina." Yana gama faɗar hakan ya wuce bedroom ɗinsa rai a ɓace, toilet ya shiga ya cire kayan ya watsa cikin washing machine sannan ya sakarwa kanshi ruwa yana jin zuciyarsa ba daɗi, bai fito ba har sai da yayi wankan ya gama sannan ya ɗauro arwala yafito ya shirya, yana gamawa ya fice daga gidan gabaɗaya, a can tsakiyar farfajiyar dake tsakanin mension ɗinsa dana Jalil ya nemi ɗaya daga cikin kujerun dake kakkafe a wajen ya zauna yana shaƙar daddaɗan ƙamshin fulawowin dake tashi wajen haɗe da lumshe idanuwa ya faɗa duniyar tunani akan makomar auren daya ɗauko idan har sukaci gaba da wannan zaman da Meenal, dan ya tabbata tunda har bata raga masa ba shi da ƴan uwansa to tabbas bazata ragawa Aïcha ba. Da wannan tunanin Jalil dake ƙoƙarin fita har zai shiga mota ya hangosa tare da fasa fitar ya riskesa a wajen, "Ya Mutallab." Jalil ya faɗa har kusan sau uku bakiji ya amsa masa ba saboda yadda yai nisa a tunanin da yakeyi sai daya sake kiransa da ɗan ƙarfi a karo na huɗu sannan firgigit ya dawo hayyacinsa haɗe da amsa masa, kujerar dake gefensa Jalil yafara zama yana kallonsa cike da mamaki kafin yace, "Yaya lafiya kuwa kazo nan ka zauna kana irin wannan tunanin da sam baida wani alfanu ga lafiyar mutum?". Sai daya furzar da iska cikin yanayin damuwa ya ɗago kai ya kalli ɗan uwan nasa, kafin yakai ga cewa wani abu Jalil dake karantar yanayinsa yace, "Meenal ce ko?", "Kusan haka Jalil", ɗan ɗauke fuska Jalil yai yana sauke numfashinsa haɗe da juyar da kai gefe yace, "Kayi haƙuri da abinda zan faɗa Yaya wallahi bakayi sa'ar mata ba, astagfirulla amma bansan wane kuskuren kayiwa ubangiji ba daya jarabceka da aurenta." "Jalil kenan shiyasa ban fiye son sannar dakai damuwata ba, shi ubangiji ai ba sai anyi masa kuskure ba yake jarabtar bayinsa, auren Meenal nayi imani cewa ƙaddarata ce kawai a haka shiyasa ka ganmu a inuwa ɗaya." Kallon yayan nasa yai haɗe da cewa, "To Yaya wai ya zancen Aïcha ne? Yakamata ku daidaita ka samu ka auretako kaji sanyi ta ɓangaren ta." "Zancen da muka gama yi da kawu kenan yake sanar dani ta amince na tura iyayena da har Meenal taji ta tada rigima." "And so Yaya? Taje tayita rigimarta amma tunda har Aïcha ta amince kaje kuyi magana dasu baffa (mahaifin Imam) kawai a wuce wajen, ƙara ayi komai agama kahuta wallahi." Murmushi Mutallab yai yana kallon Jalil haɗe da cewa, "Wane hutu Jalil cikin ajiye mata biyu, ai sai dai asamu ladar dake ciki amma kai kasan idan har ba'a huta ba a mace ɗaya to biyun ma sai anyi da gaske." "A'a ranka shi daɗe, mace ɗaya ma ana hutawa idan aka dace, ba gani ba ga kuma Walid, duka mata ɗaya muke dasu kuma daidai gwargwado alhamdulillah, ka cire tunanin ƙaruwar matsala a auren nan, jikina na bani cewa warwarewar matsaltsalunka ne in Sha Allah shiyasa Allah ya saka maka da masifar son ita Aïcha ɗin saboda kasamu sauyin rayuwa anan gaba..." Haka Jalil yaita karfafa masa guiwa sosai akan zancen Aïcha ɗin kafin sukayi sallama ya fice zuwa inda zashi, Mutallab kuwa ƙarin guiwar daya samu daga ɗan uwan nasa ya bashi karsashin iya ciro wayarsa daga aljihu, lambar Aïcha ya kamo ya kira haɗe da karawa a kunne, kusan kira uku yai mata tana tsinkewa ba tare daya ɗaga ba, dole ya haƙura ya tura mata message sannan ya mayarda wayar a aljihu. Ita kuwa Meenal kuka ta dinga yi sosai kamar ranta zai fita dan Allah ma ya sani bazata jiri ganin mijinta da wata maccen ba, zuciyarta bugawa zatayi tayadda bazata koma moriyar gangar jikinta ba, miƙewa tayi ta ɗauko wayarta takira Umma, wani miskilin murmushi umma ta saki lokacin da sautin kukan Meenal ya dira acikin kunnuwanta dan haka ba ƙaramin faranta zuciyarta yakeyi ba sanin babu kwanciyar hankali kenan tsakaninta da mijinta, ita kuwa dama burinta kenan bata ƙaunar duk wani abu da zai haifar da zaman lafiya acikin gidan Mutallab balle har ya samu natsuwa a ransa, sai data yatsine fuska sannan tace, "Ƴatah wai lafiya kika kirani kina wannan kukan kin kasa magana?" "Nashiga uku na lalace Umma wallahi ƙarya Mutallab keyi bai fasa auren nan ba, yanzunnan suka gama magana wai zai tura iyayensa aje anemo masa auren tsinanniyar yarinyar nan." "Tirƙashi! Garin ya hakan tafaru bayan da bakinsa yai maki alƙawarin cewa yafasa auren? Kenan yana nufin bazai iya cikawa ba shiyasa ya karya?" Ita dai Meenal banda kuka babu abinda takeyi dan ta tabbata Umma tasan amsar tambayoyin nan data jefo mata, dan idan har Mutallab bai karya alƙawarina ba taya zai amsar wannan zancen gaban idanuwanta, Muryar Umma taji tana cewa, "Hmm ai duk laifinki ne, abu ɗaya kin kasa samowa ba dole ki kasa mallakar mijinki ba, kina ganin ko ni da nake matsayin uwarki sai abinda nace ubansa yayi yakeyi kamar yadda uwarsa tayi mana a farko." "Umma bazaki gane ba, wallahi duk yadda nasaka araina zan ɗebo abunnan sai Allah ya mantar dani har ayi komai agama kuma bana tunawa sai bayan nafito wanka." "To ai Shikenan yanzu baya karya alƙawarinsa ba ya ɓata maki rai? Saboda haka tunda shima yana son cikin jikinki sosai sai kizubar dashi ki ɓata masa ransa shima, kinga dole ya gane kuskurensa kuma in har yana sonki ya janye ƙudurinsa dan yasamu ki sake ɗaukar masa wani tunda yana son haihuwar, idan Asiya zata zo zan bata maganin da zaki sha cikin sauƙi ya zube ba sai kiyi wahalar zuwa asibiti ba balle wani yagane ke kika zubar da cikin." "Wallahi Umma ni ko agabansa ma zan iya zubar dashi ai tunfarko nafaɗa masa gaskiya." "Shikenan, an jima zan kiraki." "To Umma." Meenal tafaɗa tare da katse kiran tana share ƙwalla, da sauri tánte dake ƙoƙarin shiga part ɗin saboda bincikar lafiyarta data jiyo kukanta takoma baya, ba komai ne taji inba kalmar zubar da ciki ba da kuma sunan Umma data ambata, taso ta sanar da Mutallab amma rashin gamsashhiyar hujja yasa batayi ba, sai dai tayi alkawarin zuba mata idanuwa tare da kiyaye duk wani motsinta daga wannan lokacin dan tasan irin yadda Mutallab ya ƙwallafa rai akan ɗan cikin nasa. Mutallab kuwa daya gaji da zaman miƙewa yayi ya nufi wajen motarsa ya zura makullan ya buɗe sannan ya shiga ciki ya tayar haɗe da yiwa mai gadi horn yafice daga gidan, kasuwa ya nufa wajen Idris yaga yadda harkokin ɓangaren nasa ke tafiya, kasancewar Idris mutum ne mai riƙon amana yasa komai sai sake haɓɓaka yakeyi dan tuni Mutallab ya sake buɗe masa wani katafaren shago na zallar boutique, kayan manya da yara maza da mata inda shi kuma Idris ɗin ya barwa yaronsa ɓangaren kayan gwanjo da har yanzu ake sauke masu diloli suna ba ƴan kasuwa, sun jima suna fira inda yake sanar dashi cewa Alhajin da sukayi zama a shagonsa yai gobara shagon nasa ya ƙone gabaɗaya, yanzu haka yana asibiti ya kamu da hawan jini, sosai Mutallab ya tausaya masa tare da jajanta masa yana mai addu'ar Allah yamayar masa da alkhairi, sai da akayi sallar la'asar sannan suka bar shagon shida Idris yace ya rakasa asibitin su dubosa, kallonsa Idris yai cike da mamaki kafin yace, "Alhaji kaje dubosa fa kace? Ko ka manta da abinda yayi maka ne a shekarun baya?" "Ban manta ba Idris, amma idan har zan riƙe abinda yai Mani araina meye amfanin tarin ni'imomin da Allah yayi mani? Shi musulmi tafiya aka sanshi da ita ba riƙo ba, dan haka ba komai Ni a wajena tuni komai ya wuce." "Gaskiya Alhaji Mutallab dole ka ɗauka, ba kowane mutum ne keda irin zuciyarka ba ta yafiya." Murmushi kawai Mutallab yai sannan suka nufi asibiti, sosai Alhajin yaji kunyar ganin Mutallab da kuma nadamar abinda yai masa, musamman daya alƙawarta masa cewa zaisa a gyara masa shagon nasa sannan ya bashi kyautar million ɗaya yace ya sake gwada wani karin dasu Allah ya bashi lafiya. Kuka Alhajin ya fashe dashi tare da cewa, "Tabbas nayi kuskure kuma wani bawa bai isa yace zai dakatar da samun wani bawan ba koda a ƙarƙashinsa yake dan Allah Alhaji Mutallab kayi haƙuri kayafe mani, wancan lokacin ma dana koreka dasa hannun.." saurin daga masa hannu Mutallab yai haɗe da cewa, "dan Allah Alhaji kamanta da komai ya wuce, kai kaɗai ne mutum na farko daka fara taimakona lokacin dana shiga kasuwar ina neman aiki, shiyasa bazan manta da wannan alkhairin naka ba na ɗauki kuskuren daka yimani ba." Wata kunyar ce ta sake rufe Alhaji ya shiga yiwa Mutallab godiya sannan Mutallab yai masa sallama suka wuce, daga nan asibiti sukayi sallama da Idris ya koma shago shi kuma ya wuce gidan baffansu, bayan sun gaisa yayi masa bayanin abinda ke tafe dashi, fatar alkhairi yai masa kafin ya ajiye masa kudi yatafi. Gidansu ya wuce kai tsaye ya samu mahaifinsa yai masa bayanin cewa iyayen Aïcha sun bashi damar turowa kuma ya samu baffa yayi masa magana, nan suka kai ƙarshe dashi akan jibi baffan da kuma wani abokin Abba da nan take yakirasa yayi masa magana zasu tafi nema masa auren Aïcha ɗin, bai bar gidan ba sai da suka naga shirya komai da mahaifinsa har abinda za'a buƙata masu tafiyar idan anje sannan yayi masa sallama ya wuce. Akan hanya ya fara tsayawa yayi take away ɗin abinda zai ci, har yanzu haushin abinda Meenal tayi masa yake ji amma tunawa da babynsa dake jikinta yasa ya haƙura itama ya siya mata abinda zata ci dan ya tabbata ko yaje ba abinda ta dafa, yana isa gida ya nufi sashenta kai tsaye, zaune ya sameta a saman kujera yai sallama tare da haɗa yawu daƙyar saboda wani tsami dake tashi acikin palourn ya ƙaraso tsakiyar palourn ya ajiye mata ledar take away ɗin akan center table sannan yafice ba tare daya sake kallon inda take zaune ba daga ita sai ɗaura gaba, cike da takaicinsa cikin ƴar ɗaya murya yanda zai jiyota Meenal tace, "kazo ka kwashi tsiyarka bana ci, mugu kawai azzalumi wallahi nayi dana sanin aurenka." Yana jiyo abinda take faɗa amma yayi banza da ita wuce sashensa yaci nasa abincin sannan ya miƙe yawuce sashensu tánte, zaune ya samesu suna kallo ita da Afrah ya samu waje shima ya zauna bayan yayi masu sallama, gaida tánte yayi kafin Afrah ta gaidashi shima, abinci tante tace Afrah taje takawo masa ya girgiza kai yana cewa, "a ƙoshe nake tánte alhamdulillah." "To masha Allahu, yawwa Mutallab nace dan Allah kadena biyewa yarinyar nan kaga juna biyu ne da ita dole mai ciki ana hakuri dashi." "To tánte." Mutallab yafaɗa dan baya don zancen gabaɗaya, har yanzu tánte batasan gaskiyar kalar zamansa yakeyi da Meenal ba shiyasa take cewa haka, yafaɗa aransa kafin ya shiga yiwa tante bayanin zancen tafiyarsu baffa Niger jini nema masa auren Aïcha da sukayi da mahaifinsa, hamdala tánte tayi kafin Afrah tayi tsalle haɗe da cewa, "wayyo yayana naji daɗi wallahi, Finally dai sister ta amince zata zama matar yayana Allah ya tabbatar da alkhairi." Mutallab dake murmushi suka amsa da 'amin' shi da tánte kowanensu na hasaso wani abun a zuciyarsa game da shigowar Aïcha gidan. #Mutallab Asad #Ƴan Tagwaye #Nana Diso #Billy s fari SHAFI NA TAMANIN DA TAKWAS *MUTALLAB ASAD*      Arewabook:- billysfari       Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne. Washegari ko da yatashi bayan sallah asuba yanema musu abunda zasuci awane manyan restaurant sai da yakaiwa meenal nata duk da tijarar da takeyi masa bai kulata ba har tagama yafita ya ajiye mata abincin nan bai tsaya koina ba sai sashen sa nan yazauna dan akwai abunda yakeson aikawata awayarsa bai jima da farawa ba kawai yaji an juye masa abincin ajiƙinsa wanda hakan bakaramin razanashi yayi hakan yasa yana mikewa ya saukewa meenal zazzafan narin da sai da takusa waduwa saboda tsabar azaba cikin hargagi da bacin rai da yarufe masa idanuwa yace Ni sa'anki ne? Yafada yana huce haɗe da rawar jiƙi akan abunda tayimasa, zuciyarsa gaba daya ta jagule yakasa samun sukuni wannan wacce kalar masifa yake ciki tunda yayi aure bai samu nutsuwa ba wacce kalar macce shiƙam ya aurane? Yagaji yagaji wallahi. Sautin kukanta da maganganunta ne ya dawo dashi dag duniyar da yashiga " Ni kamara Mutallab akan gaskiyata nacewa baza'ayimun kishiyaba? Akan wata yar gidan matsiyata jinin bara da tozarci shine ka mareni, good for you Narantse da Allah sai na zubar da ciƙin dake jikina idan yaso kayi uwar dazakayi nagayamaka wacce kalar rayuwa nakeyi da bakin munafuki irinka." Da mugun mamaki ya kalleta yana dago idanuwansa da suka canza launi saboda bacin rai jiƙinsa ne yayi mugun sanyi saboda tafaɗi weakness dinsa. " meenal stop yafaɗa yana kokarin nufarta ita kuma tayi hanyar waje tana faɗin " You can't stop me wallahi nagayamaka sai nayi abortion kaje kayi aurenka an marina da kayi kajira kaga abunda zanyi." Cikin zafin rai yace " Do whatever you want to do but never touch my baby danAllah yafaɗa da wata murya rarrauna da gaba daya jiƙinsa ya rikice masa." " To hell with your baby tafada tana fita shikuma samun kansa yayi da komawa ƙan kujera yanajin zafaffan hawayen da raban da yajisu yabanta sukafara zuba saurin saka hannunsa yayi yanajin tsantsan bakin ciki da damuwa yaa hayyu yaa Qayyum ka taimakamin kashiga lamarina kakawomin mafita, jin numfashin nakokarin gushewa yasa wayarsa yakira jalil da ya tabbatar yana gida shima cikin ƙankanin lokaci yashigo bangaren nasa har saman nasa babban palour din da yake ciki ganinsa zaune jiƙinsa da miya jalil yaji ransa yayi mugun baci dan yadda ya lura dole abunda yake tunani ne yafaru. " Yaya mutallab zama da wannan matar taka bazaiyihu ba how..." " Is okay jalil muje please bari nacamza kaya angama haɗa lefen ne?" Duk da zuciyarsa tana daci ganin halin da ɗan uwansa yake ciki yasashi kasa magana saboda halin da yaga dan uwansa yana ciki yazame musu bangon farin cikin rayuwarsu Amma shikuma baisamu wacce zata sakashi farin ciki ba babban baƙin cikinsa da bazai iyq sawwake mata ba ga mata nan sai wacce yazama yagani yanaso Ko bai fada masa ba yasan watsa masa miyar tayi ajikinsa." Mutallab da har yanzu yake ciƙin bacin rai yace " Muje jalil inason su kawo furniture din zuwa Friday." Murmushi yayi akan fuskarsa yace " dada ta turamin kudi har 3m yaya wai asiyawa yarinyarta kayan daki." Baice komai ba sai da suka shiga mota sannan yace " Ai nagayamaka zanmata komai kada ta turo kudin dan haka ka aikamata da abinta i will makesure nafaranta mata insha Allahu." Da dan mamamki ya kalle yayan nasa har suka fita daga gidan. Ni za'a mayar yar iska ni za'a wulakanta Wallahilazim karyane nafada nakara karyane tafada tana jan mayafinta da mukullin motarta yau bata da lokacin kiran umma ma tunda tasan gidan malaman datake kaita dan haka directly can tayi batare da ta tsaya ba bakin cikin da take ciki bazai faduba yadda zuciyarta take zafi bazai faduba sai tayi duk abunda zatayi batare da anyi auren nan ba, Tafiya tayi mai nisa kamin ta faka motarta tayi k'okarin parking tafito. Ada idan suna zuwa da umma takanji tsoro da fargaba amma yanzu zuciyarta ta riga ta bushe bata tunanin zata iya daga kafa yanzu akan lamarin mutallah babu maccen datakeso ta rabeshi har takarasa tsakiyar dajin da tashiga kiran sunan boka tana fadin " tsinanne Nakaraso da bukatuna ina neman kabiyamini." Ihun dataji da dariya yasata karasawa inda bukkan take nan taganshi zaune.kamin takara tayi magana yayi saurin faɗin basai kince komai ba basai kin furta ba Nagani na kuma saurara nakuma amince Amma bazamu iya aiki akan kowannen su ba sai dai in har sun kasance basa addu'a akwai wata addu'a da akeyi safe da yamma da Aljanun mu basa samun tasirin aiki akan duk wacce yayita sannan bazajin dadin zama ajikin mai zama da alwalah aure sai anyi duk inda zakije gashinan ma nagani." " Yanzu boka babu yadda za'ayi?" Dariya yayi yana kallon meenal yace " Zaki iya kwana anan? Kwanadaya zakiyi zan sakamiki aikin ajiƙinki da bazai taba iya tarayya da daya matar tasa ba." Gabanta ne yabuga sai kuma tatuna wani labari da kawarta tabata nafaɗin bokane yataba sakawa wata mata kanjamau sai kuma cikinta ya kada tace " Zanyi tunani boka." Daga nan takara gaba batare da ta waiwayo ba dan bazata iya zina ba komai zatayi Amma ita batajin zata iya hakan taje yacuceta bayan yariga yagayamata sai anyi auren, a hanya tasiya takeaway duba da yunwar dake cikinta daga nan ta nufi wani babban pharmacy tasamu manager haɗe da cin hanci yabata wani magani dazata sha sau biyu cikin zai zube. Cike da murna da farinciki ta karba ta Nufi gidan nata zuciyarta babu dadi. Ko data karasa bata nufi ko'ina ba sai daƙinta. A kwana biyun nan tsakaninsa da meenal yaga lafiyarta wanda indai yaje bangaren nashi karshenta asamu matsala kokuma ta nemi zaginsa shikuma ya kau da ƙansa saboda cikin jiƙinta da yake mutuƙar kauna da so yanzu ma yashiga bayan sallar isha'i duba da gobe zai tafi Niger gobe za'a daura masa aure da wacce yake kira da farincikin rayuwarsa sallama yayi yashiga inda yasamu guri yazauna duk da da alama asiya ta gyara mata gurin kallonta yayi yace " ya jikinki?" Banza tayi masa batace komai ba. " Kamar yadda nagayamiki gobe zan tafi Niger idan zaki bimu to kishirya sai mutafi tare gobe inshaa Allahu za'a daura auren mu da Aicha." " To sai uban Me nace sai Me? Idan kaga dama kayi uku take wannan matsalarka ce tafada tana jan tsaki dan bayan da yabar gida rannan kai tsaye mumy yakira yasanar da'ita komai dake faruwa nan tabashi hakuri tace kuma zatayiwa Abban meenal din magana yayi mata fada hakan yasaka Abba yakira meenal yayi mata tatas har yakai da faɗin idan har tabar gidanta batare da mijin ne yace tabari ba to tabbas bazai taba yafemata ba shine dalilin da yasa ma ta shiga taitayinta. " ki kula da Kanki da kuma babyna idan kuna bukatar wani abun ki dauki Atm din gurin Afrah kiyi amfani dashi." " Tsaki taja ta barmasa gurin shikuma ya girgiza kai batare da yace mata komai na yakoma bangaren su tante nan yaga yadda suka shirya komai nasu tunda tare zasu tafi. " Alhaji mutallab sannu da zuwa nace ko akawomaka abinci ne?" " Ai dazu dayake gidan jalil naje munci tare ma mama yafada cike da kaunarta." " To mashaa Allahu inataso in maka magana umar fa sunfara daidaitawa da Afrah har yafara mata maganar yaushe ne zai turo." Da dan mamaki ya kalleta yace " Au soyayya suke yana dan murmushi da afrah ta rufe fuska MashaaAllah to babu damuwa Allah yasa alkhairi zamuyi magana da baba idan nafuta inshaa Allahu. Sai maganar da nakeso nayi dake mama akan zaman aicha acan Nida nace ita tazauna waccen gidan Amma kuma duba da harkokina sunfi yawa Anan sai nake ganin kamar dai gwara tadawo nan din." " Eh to hakan yayi amma ashawarata kabarta can har tagama karatun nata tunda kaga ancemun jami'a zata fara yanzu ko kuma karatunsu yafi nanan sauki idan tagama idan kanada ra'ayi sai kadawo daita nan din idan kuma kaji can din yafi sai kabarta can din. " Eh to hakane yafada yana mikewa yana sanar musu da Asubahi zasu tashi." Duk yadda Mumy tayiwa meenal fada da nuna mata kada ta sake ta zubar da ciƙinta da nuna mata irin matsananciyar matsalar fa zai iya haifar mata Amma ina sai data zubar da duk wata shawara da Mumy tayi mata karshe ma sai ta tashi ta dauki maganin batasha biyu ba sai ta saka duk ukun ta zauna tana kallo wanda tun bayan shanta da wasu awanni tashi cikin tashin hankalin da bata taba tsintar kanta ciki ba dan matsanancin ciwo ne nabaya ya sarketa haɗe da mararta ga wani irin zazzabi da yarufe. Kuka tasaka Amma sanin abunda tayi sai yasaka bata kira kowa ba sai tayi shiru fa baƙinta. ****** Wai kukan me kike yabi da tazo yar uwar mahaifarsu ce daga chadi suna shiri sosai da maman su aicha dan su aichan kusan suna zuwa idan takama duba da yadda yabi ke son mahaifiyarsu da kuma kaunarta dan ko da taji mutuwar tafi kowa girgiza nan ta tubure sai an bata yaran duba da wani rikice da ya barke akasar shine Allah bai bata damar zuwa ba har sai watan da yahuce tana gidan da dada duba da mahaifiyarta da ta dada daya tasha nono ta sakarwa daya, ta fada tana dallawa aicha harara." " Banason rabuwa da dada Mama yabi.." " Kiji wata shegantaka tafada tana dariya." " Yabi kinfa takurawa yarinyar nan wallahi kin takuramata menene haka." " Takura ta ina mama? Bayan rigima irin da aicha saboda Allah wannan kyauta datasamu ai abun ta godewa Allah ne Nan afrah tacemun matarsa bata cika macce ba dan babu abunda ta'iya ita kuma tasamu damar nan sai kuma akace tayi wasa da'ita soyayya ai daman a hankali take shiga to nidai wallahi zangayamiki gaskiya idan zaki zauna ki gyara rayuwar aurenki ki kula da mijinki to kiyi idan kuma zaki tsaya shirme ne da shiririta to sai kiyitayi babu ruwan kowa kinganin yan uwan uwarki da uban naki basu tsinana komai ba kishiga gidanki kirufawa kanki asiri kiyi hakurinki dan zama sai da hakuri ko da wa kuwa zaka zauna koda kai ka haifi mutum sai kayi hakuri dashi ballantana zaman da akace ibada." Murmushi dada tayi tana kuma kara godewa Allah da yakawo mata yabi dan takasa yiwa aicha fadan komai duba da ganin kamar zata takurawa marainiyar Allah " Ni bari naje kamin masu kayan abincin can suzo." " To mama sai nafito na kama aikin." A hankali aicha tariko hannun mama yabi tace " Ina tsoro mama ina tsoron komai har da matarsa da shikamsa gwara yan uwansa sun nuna suna sona." Murmushi yabi tayi tace " Taba aicha sai kace ba diyar mamanki ba wacece zata baki tsoro? Kishiya? Kishiyar da anriga angayamiki tayiwa kanta tikas agurin mujinta? Ai bari in gayamiki duk wasu salo na girmama

Chapter 50 of 54