Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kuwa kullum cikin damunsa take da kira da kuma text message, yana gani zai yi banza da ita dan shi ko kaɗan bayan jin zai iya amsa tayin nata. Sanin irin yanayin gidan yasa Mutallab keyi komai nasa bisa tsari da kuma taku don baya nuna masu irin samun da yakeyi, dan tuni ya sayi fili anfara yimasa gini haka kuma ya sayi mota ta matsakaitan kuɗi da har yanzu ma bata iso ba yana sa ran sai wani wata don bai ƙarasa biyan kuɗin ba. ******** A duk lokacin da numfashi ke jikin bawa to tabbas tafiyar lokaci baya tsayawa har sai idan wannan numfashin naka ne ya tsaya idan lokacinka yaƙare, kimanin shekara biyu kenan har da watanni da yaɗuwar Meenal da Mutallab data ƙwallafa ranta kanshi, abubuwa da dama sun shuɗe acikin rayuwar kowanensu na farinciki da kuma akasin haka, yayin da har yanzu Meenal takasa haƙura da Mutallab shi kuma yakasa bata dama daidai data girman ƙofar allura duk da tarin ƙaunar da take ƙoƙarin nuna masa, duk wani abu da zatayi dan ganin ta burgesa tanayi ko ma nace tana janyo amma ko yaushe abun zame mata yakeyi tamkar kuwa baya ga yaƙi. Haka ma a ɓangaren gidansu Mutallab abubuwa da dama sunfaru na daɗi da akasin haka, wasu abayyane wasu a ɓoye yayin da samun ɗaukakar Mutallab taci gaba da bunƙasa ta yanda yakasa dakatar da bayyanar hakan a zahirance, ita kuma rayuwa kuwa dama tana tafiya ne akan sumun wani daidai yake da cirewar rigar ɗaukakar wan, don tuni labari ya fara sauyawa daga ainahin ɗaukakar tarin arziƙin baban Mutallab da aka sani zuwa arziƙin ɗan nasa Mutallab da ayanzu ya fara amsakuwar karaɗe garin baki ɗaya, hakan kuwa baisa Mutallab sauyawa daga ainahin ko waye shi ba acikin gidan har sai zuwa lokacin daya tsara bayyana hakan da kansa, duk da fa tuni su Mommy labari yakai kunnensu daga su har Abba amma rashin samun tabbacin haka daga wajensa da rashin gani da idanuwansu yasa suka dauki abun almara kuma suke ganin kamar ba gaskiya bane, shi kuma yaja bakinsa yay shiru yaci gaba da rayuwarsa a yanda ya sabayi a gidan, dan har yanzu shi yake yiwa yaran gidan lesson... #Mutallab Asad #Tagwaye Biyar #Billy S Fari #Nana Diso *MUTALLAB ASAD* *PAID BOOK #500* *TAGWAYE BIYAR.* NA *NANA DISO** & *BILLY S FARI* 27. Yau ya kama ranar litinin, yadda yake jin jikinsa wani iri da mararsa dake faman ƙulle masa ya tabbatar masa da yanayin buƙatuwa da iyali, sai dai taya tunda har yanzu bai samu macce data kwanta masa ba balle har ayi zancen aure ya samu damar sauke abinda ke cikin mararsa dan wannan yanayi a yanzu ya riga daya aureshi fiye da tunaninsa, kallo ɗaya zakayi masa ka tabbatar ya amsa sunansa na cikakken namiji, namijin ma irin wuɗanda akeyiwa laƙabi da jarumai mana dan gabaɗaya gaɓɓan jikinsa sake murɗewa sukeyi suna bayyanar da zaton surarsa na zama cikakken ɗa namiji, Ajiyar zuciya yayi ganin ƙarfe takwas tayi, yanzu ne idan yaƙara minti ɗaya baije wajen gyaran ɗakin mahaifin nasa da har yanzu yaƙi ɗauke masa ba to tabbas shi yana tafe wajen kiransa tare da sauke masa kwandon faɗan daya saba yimasa, dan har yanzu matansa sunƙi gyarawa suyi masa yanda yake so shi kuma yaƙi dena sakashi yayi masa, gashi Abban yanzu girma ke ƙara sauka jikinsa wasu abubuwan baya iya aiwatar dasu, shiyasa kullum ɗan nasa da yafiso yanzu cikin jawo masa asara mai yawa acikin dukiyarsa yake!. Kauda wannan tunanin yayi ya miƙe yashiga wanka ya dauki akallah mintuna ashirin yana wanke jikinsa, daga bisani kuma yafito riƙe da towel yana goge jikinsa da sai faman tashi tsigar jikin nasa keyi, a gaggauce ya shiga shafa mai ya kammala haɗe dasa jallabiyarsa ya nufi sashen mahaifinsa ya gyaro masa ɗakinsa, bayan ya kammala ya koma ɗauki da dan yayi shirin zuwa kasuwa, yana shiga wayarsa tafara ringing ya duba yaga mai kiran nasa daga babban shagonsa ne da yake mallakinsa wato MAM GENERAL ENTERPRISES, shine  babba daga cikin shagunan da yake dasu a kasuwar guda huɗu, biyu na kayan abinci ɗaya na harkar gwanjo sai ɗaya na ɗinki, yanzu haka wani na nan da yake ƙoƙarin buɗewa da zai zuba ƙwararrin maɗunkan zamani na maza, wanda shi yasai filin yake kuma ginawa da kuɗinsa, dan a harkar ɗinki kam ba abinda zai ce sai masha Allah dan tana kawo masa kuɗi sosai ɗan manyan gari da ƴan kasuwa yake yiwa ɗinki. Sai da kiran ya katse sannan ya kira da kansa aka ɗaga,"Oga barka da safiya kaya sunzo mun gama fitarwa harma an kasafta wanda sukeso sun siye yanzu mun haɗa kuɗaɗen duka shine nace zan saka a account ne akai banki ko kuma ajira har ka ƙaraso". Sai daya ja iska ya furzar ta bakinsa sannan yace, "Jalil! Jalil! Wai har sai yaushe zaka daina kirana da oga ko nafara wasa dakai ne?" "Afuwan ya Mutallab". Jalil ɗin ya faɗa yana dariya, "Kai dai ka sani,  Yaushe kafita ina cikin gidan nan ban sani ba?" "Tun ɗazu oga! Au afuwan sunan ne nake ganin ya cancanta dakai ranka ya daɗe". "Allah to ya shiryaka, yan sun nan zan shigo in sha Allah, inaga kawai kariƙe kuɗin a hannunka, idan bukatarsu ta tashi zan iya nemanka, but ina fatar komai yatafi daidai?" "Sosai Oga sai ka iso". Girgiza kai Mutallab yayi haɗe da cew, "Kaji dashi, ai dama nasan ba denawa zakayi ba". Ya ƙare zancen tare da kashe wayarsa ya ajiye gefe sannan yaci gaba da shiryawa. Bubbuga ƙofarsa aka shigayi yasan dayan biyu ne ko Afrah ko kuma wannan mayyar yarinyar data addabawa rayuwarsa, don yanzu Meenal duk inda tasan zata samesa bibiyarsa takeyi. muryar Afrah yaji ta katsesa da faɗin, "Yaya may i come in?" Yace "Yes my lovely sister, shigo mana". yana maida hankalinsa kan takalminsa da yake sawa. Tana shigowa ta sakar masa murmushi tana cewa, "Good morning ya Mutallab". "Morning Afrah ya jikin naki?" Yafaɗa yana kallonta cike da kulawa, "alhamdulillah yaya naji sauƙi, dama cewa nayi ko zaka ajiyeni school ina da 8-10". Ɗan yanzu Afrah sun kammala secondary har sun shiga jami'a kuma shike ɗaukar nauyinta kasancewar Abba yace shi bashida halin sakasu duka su biyu ita da Jiddah, sai kawai ya saka Jiddah ɗin ita kuma ya ƙyaleta sai dai shi Mutallab ɗin ya sakata yana yimata duk wani abun ɗaya shafi makarantar kama daga biyan kuɗi har sauran ƙananun buƙatu irin su sayen handout da sauransu, nan ma aka sanya tsegumi wai ya raba ɗaya biyu ita da Jiddah da ƙanwarsa kawai yake kula, kallonta yayi kafin yace, "me zai hana ƙanwata ai da gudu zan ajiyeni, burkina kawai ki natsu kiyi karatu sosai kin ji ko? Dama yau zan buɗe sabuwar motata da aka kawo jiya da daddare, kinga sai kiriga kowa fara ɗanawa". Cike da jin daɗi tace, "wow Masha Allah Yaya Allah yaƙara buɗi kuma ya tsare, saura ɗaki Yaya dan Allah kacanza komai na daƙin nan naka?" "Ba yanzu ba Afrah, ni dake gini ina naga ta gyaran ɗaki yanzu? banda lokacin canza komai har sai na kammala idan na samo maki aunty zamu koma can kinga sai nayi mana komai sabo ko?" Murna tayi tana masa fatan Alkhairi suka fito zuwa harabar gidan inda aka ajiye masa  motar tasa jiya sabuwa fil Toyota venza v6 2010 Red. Kasancewar yana fitowa maigadi ya taso da sauri ya cire mata rigar da aka rufeta da ita Afrah ta zaro ido tana cewa, "Wowww ya Mutallab motar nan ta azabantu dakyau". Tanayi tana shafa jikin motar, murmushi yayi tare da ɗaya kai yana kallon Umma dake zare idanuwa itama ganin yana ƙoƙarin buɗe motar, wannan shine plan ɗinsa na farko da yake son fara yimasu bazata wajen bayyana masu ko waye shi yanzu, tabbas sauƙin da yake son isarwa Umma ya isa dan sai da yaji wani abu ya dokar mata zuciya, dan a tsammaninta motar ta ɗaya daga cikin aboķanan Abba ne suka kawo ajiya, ga mamakinta kawai sai taga ashe ta Mutallab ce, bata sake shiga wani mamakin ba sai da taga ya zuwa makullin motar ya buɗe zai shiga baya ya buɗewa Afrah gefenta itama, kaɗan ya rage jiri ya ɗebeta tafaɗo ta saman dan tsananin tashin hankalin daya shiga, kenan dai ta tabbata arzikin da ake cewa Mutallab ya tara a waje da gaskene, da hanzari ta shiga saukowa daga saman ɗaƙin ta nufi shashin Abba. Cike da farinciki Afrah ta juyo ta kalli yayan nata dake ƙoƙarin tada motar tace, "ya Mutallab motar nan tayi mani kyau sosai". "Sha kuruminki kema zan siya mako idan Allah yaƙara buɗowa". "Allah yayi buɗi na alkhairi yaya, daman dukkanin mahaƙurci mawadaci ne, yau gashi kai da aka ɗauka ba bakin komai ba Allah ya ɗauka..." bata ƙarara ba yace, "kiyi shiru haka Afrah mana". Dan shi baya don irin waɗannan maganganun. Yana ƙoƙarin tada motar Abba da Umma tayowa zuga yafito da ɗan saurinsa yana faɗin, "kai Mutallab dakata ina zaka je ne? Motar uban waye haka ka ɗauki ka kawa kanka masifa? To ni baruwana kaji na faɗa maka, maganin kar ayi tofa kar afara". Kashe motar Mutallab da har ya tayar yayi haɗe da fitowa yace, "Ba abinda zai faru Abba mota tace musanya mani albarka". "A gidan ubanwa ka samu kuɗin diyan irin wannan motar Mutallab? Ko dai ka koma satar daka ɗaukowa rayuwarka yi abaya?" Wannan karon kasa cewa komai yayi jin yadda Abba ke magana kamar bashi ya haifesa ba yana kallon tashin hankali ƙarara a fuskarsa sai kace baisan abinda zai iya ba da wanda bazai iya ba, Aunty Amarya ce da ya Jamil suka fito yanzu jin maganganun Dady itama cikin tashin hankali, Umma kuma dama tare suka iso wajen ita da Dady, Jamil da dama lamarin Mutallab yake bashi tsoro akwanankin nan yanda labari sa ke yawo a gari amma su basuga komai ba sai yanzu yace, "Hmmmm wlh biri yayi kama da mutum, dama gari nata yawo da zancen yaron nan ya samo maƙudan kuɗi amma ya biye ɗan kar muci yaƙi nunawa, to bari kaji nakasa wasu sama damu a duniya kuma inhar gaskiya ne ka samu kuɗi tofa abincike ka don idan jin tsoron samun kuɗi a lokaci ɗaya in ba maza kaķe bi ba, ko ba haka ba  Abba? Tunda yanzu ina Mutallab ina motar million kisan bakwai fisabilillahi?" Runtse ido Mutallab yayi jin kalmar da ɗan uwansa ke jifarsa dashi kafin can yaji Umma tace "Gaskiya abinciki lamarin nan,  wallahi shiyasa bana samun bacci wadataccen bacci kwana biyu kada ace amanar Allah zamuci bama kula da tarbiyar yaranmu azo yana aikata abunda sunan ahalinmu zai ɓaci." A daidai wannan gaɓar sosai ran Mutallab ya ɓaci ya shiga kallonsu ɗaya bayan ɗaya kafin yace da mahaifinsa, "Abba akwai abunda zanmaka ne?" Yayi maganar jijiyoyin kansa na mimmiƙewa "Babu Amma kaji tsoron Allah kuma idan kadawo inason ganinka?" Abban ya bashi amsa sannan ya juya ya koma watsa ciki gida, Dukkansu mamaki ya kashesu da amsar da Abba ya bayar don ba haka suka so ba, musamman Umma data yo zuga sosai, ita a ƴan kwanakin nan ma ta lura Abba baya iya yimasa cin mutunci kamar da, aikuwa dole tamiƙe zama bai ganta zata koma bazama gurin malamanta har sai taga wannan tsinannen yaron ya lalace, Jamil ne yace, "Abba kada fa kabari tafiya da motar nan kada zargina ya zama gaskiya, irin wuɗan nan kuɗin Abba dole fa a tsananta bincike". Ko juyowa Abba baiyi ba ya ƙarasa shigewarsa, dan yanzu bai san me yasa ba wata irin tsanar Jamil ɗin yake ji a ransa.    (Ehmm waya sani ko ƙaiƙayi koma kan mashekiya ne🏃) Mutallab kuwa bai sake bi takansu ba ya shigewarsa ya tada motarsa bakinsa ɗauke da addu'a suka fice ya barsu sake da baki bakin ciki kamar zai kashesu. ******    Kuka takeyi sosai ɗare-ɗare a saman cinyar Kamal yana lallshinta, aikin data wuni yi kenan a yau tun safe har yanzu karfe sha biyu na rana, palourn  yayi tsit sai sautin kukanta da yake tashi Abba daya kasa fita tsaye yana kallonta, Mommy ma dai idanuwa ne nata tana kallon ikon Allah ace balagaggiyar yarinya ta tashi hankalin kowa tun safe kuma an zauna anbiye mata, ita bnama haushinta kamar irin wannan kusancin yayan da ƙanwar dake nema ya kazanta tsakaninsu, tana jiye musu shaiɗan watarana dan shi babu ruwansa da gida ɗaya jini ɗaya ko uwa ɗaya uba ɗaya indai tsakanin macce dana mijine. Kallonta Kamal yayi da kukan nata yafara sha masa kai haɗe da cewa, "Wallahi zan ɓallaki Meeneluwa ko kitashi kibani waje, tun ɗazu anyi magana kin ƙyale mutane to wai wannan kukan uban me ne kikeyi mana?" "Haba Kamal ƴar uwarka ce fa kayi mata a hankali". Dady yafaɗa da ɗan ɓacin rai haɗe da damuwa a saman fuskarsa, duka banza tayi masu har aka kwashe kusan mintuna goma sannan tace, "Dady anya kai ka haifemu? Kana gani fa cutar don Mutallab zata kasheni ka kasa yin komai". Cikin sigar lallashi yace, "Haba Babyn Dady na gayamiki yau ɗin nan ba sai gobe ba zanje muyi magana da mahaifinsa tunda mun gano ko ɗan gidan waye, babansa amininsa ne sosai ba abinda zan nema a wajensa n rasa, ɗan haka ki kwantar da hankalinki saboda wannan kukan naki ni ɗaga mani hankali yakeyi, zan je muyi magana da mahaifinsa kinji ko?" Tana share ƙwalla ta ɗaya masa kai tare da tasowa ta rungumesa tana cewa, "i love You Dadyna". "I love You too Babyn Dady". Ya Bata amsa yana rungumeta ajikinsa tsam yana jin wani sanyi acikin ransa ganin ta samu farinciki... #Mutallab Asad #Tagwaye Biyar #Billy S Fari #Nana Diso *MUTALLAB ASAD* *PAID BOOK #500* *TAGWAYE BIYAR.* NA *NANA DISO** & *BILLY S FARI* 29. Tafewa sukayi da juna suna dariya Abba na nunasa haɗe da cewa, "Kai ko? bazaka taɓa canzawa ba". yariƙe hannun nasa suka nufi cikin wata ƙawatacciyar ƴar runfa dake can gefe zagaye da kujeru, taku biyu sukayi babban yaron Dady ya biyo bayansu, juyowa yayi ya ɗaaa masa hannu alamun a'a sannan suka cigaba da tafiya suna gaisawa har lokacin Abba nariƙe da hannun Dady. Bayan sun samu waje sun zauna tare da tambayar junansu kasuwa da yaushe rabo Dady ya kalli Abba haɗe da cewa, "Alhaji Asad wannan tafiyar ta ƴarka Meenal ce, ita tasani zuwa saboda ɗana Mutallab da take so". wani faɗuwa gaban Abba yayi jin an ambaci Mutallab, ba abinda ya zo masa arai sai motar daya gansa da ita ɗazu, Allah yasa bata ƴar wajensa bace ya ɗauko kar yaja masa abun kunya da abun faɗi, dan gaba ɗaya baima tsaya ya ƙarasa jin zancen ba, ɗago idanuwansa yayi haɗe da kallon Dady yace, "subhanallahi injin ba wani abu yayi mata ba? kasan ƴaƴan yau ka haifesu baka haifi halinsu ba". murmushi Dady ya saki tare da cewa, "Haba Alhaji, baki me nake faɗa maka ba? Sata ce kawai yayiwa ƴar taka amma fa ta zuciya.." nan ma dai Abba baibari yaƙarasa jin kalaman Dady na ƙarshe ba, kalmar sata daya ji kawai yasa shi cewa, "innalillahi wa inna ilaihirrajiun, dama ni nasan wannan motar ta mutanece ya ɗauko". "kamar ya Alhaji? bafa zancen ɗaukar mota nakeyi ba, ina magana akan zancen sace zuciyarta da yay kai kuma kana zancen ya ɗauki mota, haba Alhaji mi akai akayi mota ai indai yaronka ne kowace iri ce yafi ƙarfin ta". ajiyar zuciya Abba yayi tunawa da halin Dady nason barkwanci a wasu lokutan haɗe da cewa, "Dole kaji nafaɗi haka Alhaji Abdulmalik saboda yaran yanzu da kake gani kana zaman-zamanka zasu ɗauko maka rigima, amma alhamdulillah tunda ba abinda nake tunani bane". "Haka ne amma a ɓangaren shi yaronka shi ba haka yake ba dan sai da nasa aka binciko mani ko shi waye? Ɗabi'unsa, aikinsa da kuma halayyar da kuma duka alhamdulillah bai yarba a halayyarka don anan ma nagano cewa ɗan ka ne, Meenal na tsananin sonshi kuma ta tabbatar mani da cewa matuƙar bata auresa ba zata iya rasa ranta, Kullum cikin kuka take akan soyayyarsa duk ta su suce ta zama abun tausayi, ni kuma duk duniya bani da wata ƴa inba ita ba shiyasa duk abinda take so nima nake son shi haɗe da ƙoƙarin nemomata shi, sai dai ga dukkan alama shi yaron naka hankalinsa baya kanta dan duk wannan tsawon lokacin da suka ɗauka ta kasa shawo kansa, ba tada aiki kullum sai kuka saboda yaƙi saurararta kwatakwata, to dana sa akayi mani bincike na gano ashe yaron ɗan wajenka ne, shine nace bari nazo da ƙoƙon barana agabanka Alhaji Asad akan muhaɗa wannan auren ko dan ƙarfafa zumuncin dake tsakaninmu". Abba ya kallesa cike dajin daɗin zancen daya zo masa dashi yace, "Ikon Allah! Alhaji Abdulmalik wannan ai ba wani abu bane, kirana kaɗai idan kayi akan wannan maganar sai muyita mugama asaka lokaci kawai tunda kasanni na sanka tun muna yara, kuma banda shirmensa ma ai kamata yayi yaji daɗin wannan lamarin saboda na tabbata zata bashi farinciki tunda tana sonsa, dan haka ka ɗauka wannan abun kamar anyi angama, kuma ina sha Allah zanyi magana dashi zai zo har nan gida ya sameta su daidaita, wannan ai ba wani abun damuwa bane ko kuka". Dady da dama yasan kalar kirkin Abba shiyasa har ya samu ƙwarin guiwar zuwa ya fuskancesa da maganar ya saki murmushi haɗe da cewa, "Alhamdulillah naji daɗin wannan magana taka, shiyasa tunda nagano cewa yaron ɗan wajenka ne nayi alfahari da zaɓin nata saboda na tabbata barewa baza tayi gudu ɗanta yayi rarrafe ba". da haka sukaci gaba da tattaunawa kafin Dady yayi masa sallama cike da farincikin magancewa ƴar tasa matsalarta. Abba kuwa koda ya koma cikin gida Umma data samu labarin zancen baƙin da yayi ta tarbesa da zancen ko kallonta baiyi ba saboda takaicin abinda Jamil ɗin yay masa daya tabbata da saninta hakan tafaru, a halin yanzu gabaɗaya da ita har yaran nata kallonsu kawai yakeyi saboda ya fara gano irin abubuwan da sukeyi ba tare da saninsa ba, musamman shi Jamil ɗin. Ganin haka yasa dole Umma ta sha jininta cike da mamaki taja bakinta tayi shiru duk kuwa da yanda ta matsu da son sanin ko suwaye da abinda yakawo su, Aunty amarya taji ya ƙwalowa kira saboda yanzu ita take murza sitarinta acikin gidan dan kuwa aikin da mahaifiyarta taje tayo mata yayi yanda suke so, Abba baida wata abokiyar fira ko shawara sama da Aunty amaryar, kuma kuɗi ko nawa take so bata yakeyi, ga wata masifaffiyar kulawa da soyayya da yake nuna mata daga ita har ƴaƴanta, Umma na tsaye Aunty Amarya tazo tagabanta tawuce tana mata wani kallo, wani ashar Umma ta lailayo ta ajiye tare da cewa, "lallai rashin mage a cikin gida shi kesa ƴan kusa daddagi, amma kin takalowa kanki tsuliyar dodo dan faɗa da aljani sai an shirya kuma wallahi sai na hanaki runtsawa, sai na nuna maki kinyi kuskuren ja dani yarinya". taƙare zancen tana cije baki haɗe dayin kwafa sannan tabar wajen. Ko data koma ɗaki sintiri ta dingayi tana daddagar tafin hannunta tare da tauna laɓɓanta, dama ta daɗi tana zargin akwai makircin da Aunty Amarya ke shiryawa da yasa Abba yafara juya mata baya, saboda a ƴan kwanakin nan ya canza mata gaba ɗaya duk abinda tayi masa bata burgesa, tabbas yanzu aiki ya zamo mata guda biyu a, dan haka dole da safe tayi sakko ta Ziyarci malam nakan ruwa. ********** Mutallab kuwa ko daya tashi daga kasuwa shagon ɗinkinsa ya wuce, basu baro shagon ba shi da Jalil sai kusan ƙarfe goma na dare dan gaba ɗaya yama manta da zancen Abba daya ce yana son ganinsa da safe, yana daidaita parking ɗin motarsa tare da fitowa Abba dake tsaye yana kai da komowa a harabar gidan yayi gyaran murya dan tun ɗazu yake zaman jiran dawowarsa, hakan ya alamtawa Mutallab ɗin cewa shi yake jira tunowa da ɗazu yace yana nemansa idan ya dawo, dan haka kai tsaye suka nufi inda yake suka gaishesa cikin girmamawa daga shi har Jalil, ba tare daya amsa ba yace, "Wato reni yafara shiga tsakanina dakai ko Mutallab? me nafaɗa maka da zaka fita?" "kayi haƙuri Abba namanta ne na tsaya a shagona na ɗinki?" "Meye tsakaninka da ƴar gidan Hon. Abdulmalik Mu'azzam?" Mutallab yaji kamar daga sama mahaifin nasa ya jeho masa tambayar, kansa ya ɗago ya kalli mahaifin nasa da sam babu alamun wasa atattare dashi ya sauke ajiyar zuciya yana gyara tsayuwarsa sannan yace, "Babu komai tsakanina da ita..." bai ƙarasa maganar ba cikin ɓacin rai Abba yace, "Karka rena mani da wayau Mutallab, idan har ba wani abu tsakaninka da ita a ina kasanta da har ka iya bani amsar cewa ba komai tsakaninku? to bari na faɗa maka ni ba ƙaramin yaro bane da zaka ɗauka bansan abinda nakeyi ba, dama nagaji da kallonka haka cikin gidana ƙato dakai ba aure, dan haka koma meye kaje ka daidaita da ita saboda mun riga da mun gama magana da mahaifinta zamu haɗaku aurenku nan da ɗan lokaci, kuma dole gobe mu zauna kafaɗa mani a ina kasamo kuɗin da kaje dasu kana ƙarya har yarinyar nan ta liƙe maka" yana ƙare zancen ya juya, taku ɗaya baiyi ba yaji muryar Mutallab na cewa, "Kayi haƙuri Abba babu inda zan je saboda bana sonta". da ɗan ƙarfi Abba ya juyo yana kallonsa cike da mamakin furucin daya fito daga bakinsa, shima Mutallab ɗin shi yake kallo, dan Abba ya tabbatar shi yay maganar ba Jalil ba yace, "Me naji kace Mutallab". "Bazan je ba Abba saboda ban sonta bazan iya aurenta ba". Abba dake nunasa cikin ɓacin rai yace, "Ni kake faɗawa haka Mutallab? to bari kaji ya zama dole kaje ko kana so ko baka so, wannan umurni ne nabaka ba shawara ba". Mutallab yaja numfashi tare da cewa, "Abba nifa ba yaro bane da za'a ce a aura mani wacce zuciyata bata so saboda ni zan zauna da ita ba wani ba, dan haka ni bazan je ba". ya ƙare maganar cikin fushi haɗe da tabbatarwa Abba ɗin tabbas bazai je ba ɗin sannan yabar wajen yana jin wani ɓacin rai na sake rufeshi, mahaifinsa bai san kowaye Meenal ba shiyasa yake ƙoƙarin cewa sai ya aureta, shi kuwa ko sama da ƙasa zasu haɗe bazai taɓa ɗaukowa ƴaƴansa uwa irin Meenal ba da zata janyo masu gori watarana saboda mugayen halayenta da ɗabi'unta, waye ita waye mahaifinta shi duk hakan bai samesa ba. Mamakine yakusan kashe Abba jin yadda Mutallab ɗin ya mayar masa da magana kai tsaye kuma cikin fushi da zafin da bai taɓa ganin yayi masa ba. Hakan yasaka jikin Abba yin sanyi sosai ya koma cikin part ɗinsa cike da jinjina kansa da tabbatarwa da kansa zaiyi maganin Abun tunda wuri kafin yazo yafi ƙarfinsa Jalil dake zaune bakin ƙofar ɗakinsa ya kasa ya tsare yana jin duk abinda akeyi ya saki murmushi jin hukuncin da yayan nasa ya yanke na ƙarshe sannan ya tashi ya shige ɗakinsa, yau ne karo na farko da ɗan uwan nasa yayi abinda ya burgesa acikin gidan akan abubuwan da akeyi masu. haka yayita murmushi shi kaɗai a ɗakin duk dako yadda yake ɗan jin tausayin kalar bibiyar da Meenal kewa yayan nasa da irin son da take nuna masa agaban kowa. Mutallab kuwa koda ya baro wajen Abba ɗin jin zuciyarsa yayi gabaɗaya a cunkushe, har zai shiga dakinsa yaga yaga Jamil zaune saman mota, kamar shi yake jira yana ganinsa ya fito daga kan motar ya nufi wajensa, yi Mutallab yayi kamar bai gansa ba ya wuce abinsa batare da ya kulashi ba dan ya lura sai yatashi tsaye yanzu agidannan wulaƙancin nasu kuma yafara yin yawa. "Yawwa Mutallab kai fa nake zaman jira shine zaka zo ka wuce babu ko yar gaisuwa kamar baka ganni ba". Cikin ɗan ɓacin rai dake zuciyar Mutallab ya juyo ya kalleshi haɗe da cewa, "Kake jirana sabida me? Ko cin mutuncin da kagama yimun ne da safe bai isheka ba sai kazo har inda nake kwana ka ƙara yimun wani?" Mamaki ne ya cika Jamil dan ko da wasa bai taɓa yimasa haka ba sabida wannan sam ba ɗabi'arsa bace, da dai Jalil ne yayi furucin to tabbas bazaiyi mamaki ba dan yaron na shige masa hanci shiyasa baya shiga shirginsa, kallonsa Mutallab

Chapter 17 of 54