Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kukan Shagwaɓan bazata dena shiba, Sarkin kuka ita ko gajiya batayi". Ganin yaƙi kulawa duk da tsokanar daya yimata sai kukan takeyi yasa Mutallab riƙo hannunta suka shiga daga cikin daƙin nasa, Jalil ne ya rufo ƙofar ya tsaya jiki zuciyarsa na masa wani zafi cikin ɓacin rai yace, "Ince wani kalar wani zaluncen ne aka ƙara yimiki ko? Wallahi yaya kai kake sakani nayi shiru akan abubuwan da ake yiwa Afrah ko tausayinta basa ji..." "Is ok Jalil, What are you trying to do? Becareful!" Mutallab yafaɗa cike da gargaɗi yana kallonsa, wani abu ne Jalil yaji ya taso masa amma sai ya haɗiye don yasan ko waye yayan nasa yayi ƙasa da kansa yana cewa "Am sorry ya Mutallab". Don har lokacin idanuwansa na akansa, juyowa Mutallab yayi ba tare daya amsa shi ba yana kallon fuskar Afrah yace, "Ya isa haka shalelen ya Jalil, faɗamun menene?." Kuɗin hannunta ta miƙo masa tana cewa, "Kaga fa Abba 500 yabani ɗaya dasu Khalid ita kuma Jidda ya bata dubu ɗaya.." Nan ta kwashe komai har shigowar Umma a daƙinta ta gaya masa, "Allah yasaka maki" Jalil yafaɗa cikin zafin rai, ɗago kai Mutallab yayi ya kallesa ba tare daya ce komai ba ya ɗagata yana cewa, "wannan ai bakomai bane Afrah, dama can ita yakamata kibawa kayan tunda basuda wani sauran amfani awajenki, kuɗi kuma nasan ba abinda zakiyi dasu tunda a ƙoshe kike ajiyewa kaɗai zakiyi su kuma na tabbata kashewa zasuyi, kinga anan ma kin fisu saboda kina da ɗari biyar ajiye su kuma suna da zero ko ba haka ba?" Murmushi tasaki tare da ɗaga masa kai yaja hannunta yana cewa, "Muje narakaki makarantar yau ma kin makara, amma ba damuwa bane tunda dama yau zaki fara zuwa, idan kin dawo kuma zuwa dare sai mu dinga lesson, kuɗin da Abba yabaki kuma idan kinyi amfani da wanda zakiyi sauran kina ajiyewa koda wani buƙatar zai taso maki bama nan sai kiyi amfani dasu, Allah yasa musu albarka."  Ta amsa da Amin sannan sukayi gaba Jalil na biye dasu a baya, kasancewar Mutallab ya saki hannunta yana amsa waya yasa ta tsaya har Jalil yaƙaraso kusa da ita ta riƙon hannunsa ta saka mashi kuɗin tana cewat "Kaga ka saka mana su a bankin kuɗinmu". Da yake akwai asusun da sukeyi ita da Jalil ɗin ba tare da Mutallab ya sani ba wai zasu bashi, wanda Jalil ɗin ne ya kawo shawarar saboda ya hana Afrah ɗin kashin kuɗi any how kamar yanda su Jidda keyi, girgiza mata kai yayi yaƙi karɓa haɗe da cewa "A'a Afrah kije dasu kawai kinga ba'a baki breakfast ba yau ganin makarantarku kusa take da gida". Murmushi tayi ta sake riƙon hannunsa ta danƙa masa kuɗin sannan tayi gaba jin Ya mutallab yana kiranta. Goge idonsa Jalil yayi ganin hawaye na bin fuskarsa cike da tausayinsa, duk da yanda ya Mutallab ke kula dasu tare dajin tausayinsa ko kaɗan bai kai Afrah tausayi ba, wataƙil don zamowarta a jinsa mata da suke da matuƙar rauni shiyasa duka tafisu tausayi, don idan yau taga ɗayansu kwance ba lafiya ta riƙa kuka kenan, da ita za'ayi jinyar har a gaba, haka ma idan abune take dashi duk soyayyarta dashi taga ɗaya su na buƙata ko baiyi magana ba haka take haƙura tabashi, ba suba kuwa hatta dasu Khalid da Jiddah duka haka take dasu. " Ya Allah kafimu sanin dalilin karɓe rayuwar mahaifiyarmu zuwa gareka Allah ka zame mana duk wata gata da zata bamu idan tana raye muda ƴar ƙanwarmu". Yafaɗa yana juyawa tare da komawa ɗakinsa.  Aunty Amarya kuwa tana ƙoƙarin shiga sashenta bayan yaran sun wuce makaranta Abba ya gama breakfast ɗinsa ta haɗa masa ruwan wanka ya shiga tafito taji zancen da Umma da Jamil keyi data rakosa zai fita, hankalinta ne yayi mugun tashi taƙara laɓewa har saida tagama sauraren maganar tasu tas sannan tawuce ɗakinta wani zufa na sauko mata ta ɗauki waya takira mahaifiyarta, suna gama gaisawa tace, "Hajiya na shiga uku wlh, gidan nan fa idan ba dagaske nayi ba wallahi baza tabarni na zaunashi ba saboda yadda Alhaji ke nuna bambanci ƙarara, shiyasa nace miki kada asake ayi sanya akan malaman nan da muke bi, idan ba haka ba wannan mashurikar matar tasa sai ta fiddamu daga gidan nan dani har ƴaƴana, kiji fa iskanci wai ɗan Jamil Sadeeq za'a kai karatu kuma karatun ma har america bayan ɗawainiyar da yake yimusu saboda Allah." tafaɗa cike da takaici tana jan tsaki, Ata ɗaya ɓangaren Hajiyar tata tace, "to ke kuwa me yayi miki zafi, Menene naki aciki da zaki dami kanki? In yana iyawa yabiyawa uwarsu ma, kedai kiyi takanki da ƴaƴanki, yanzu duk yadda zakiyi kiyi ki ƙara samun koda shagon Rumfar kasuwa ne ya mallakawa yaranki kamar yadda yayiwa ƴayan nata maza da mata, ina su sauran yaran bororin gidan?" Taɓa baki Aunty Amarya tayi kafin tace, "Hmm...Ai Hajiya sai kinyi musu kuka babu wani mai saffa saffa acikinsu wallahi, ni uwarsu ta riga data saka mani tsanarsa wlh shiyasa bama shan inuwa ɗaya dasu, shi kuma sam bayayi dasu har da ƴar macen Afrah haka suke ganin wulaƙanci kala-kala, kinsan makaranta ma sai da shigeyar matarnan makira tasa aka cireta inda sauranmu keyi? Yayunta kuma suna nan zaune suna zaman banza, shi wannan mai girman kan tsiya Mutallab ya gama karatu ba aiki, shi kuma Jalil mara kunya bai ƙarasa makarantar ba yaƙi ya biya masa kuɗin registration wai ya gaji da kashe kuɗinsa a banza". "Allah ya sawaƙe ni dai ban goyi bayan kiraba yara da ubansa ba har abada, ba ruwanki da matsalar su, uwarsu ce Allah kuma ya rabaki da ita don haka kiji da matarsa dake gabanki, itama in zan baki shawara tashi tsaye zakiyi ki mallaki mijinki kamar yanda tayi, yanzu haka na jiyo wani sabon malami acan ɓangaren kudu gobe zanyi sammakon hanya in tafi in sha Allahu, sai ki turo da abinda ke hannunki aƙara dashi". "Yawwa Hajiyata yanzu nan kuwa". Aunty amarya tafaɗa cike da farinciki ta kashe wayar tare da turawa Hajiyar Tata kuɗin data buƙata tana jin wani irin sanyi a ranta, don har ga Allah Umma ta tsaya mata a wuya ita bata fito ba ita bata wuce ciki ba... Mutallab Asad #Tagwaye Biyar #Nana Diso #Billy S Fari. _ Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only Zaki biya ta wannan account ɗin👇🏻 *ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *MUTALLAB ASAD MUTALLAB*                 (MAM) NA BILLY S FARI & NANA DISO    *SHAFI NA GOMA SHADAYA.* _RUBUTUN ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU._ _TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA_     A ɓangaren Jamil ma dake buƙatar wasu maƙudan kuɗaɗe agun Abba ya yi yawa Umma magana takarɓarmasa amma taƙi saboda takaicin idan ma takarɓar masa matarsa zai ba ita kuma bazata lamunci hakan ba, zaune yake gaban wani babban malaminsa na tsibbo ya tanƙwashe ƙafafuwa tamkar mai roƙon gafara yana cewa, "Yanzu Malam babu yadda zakayi akan maganar karbar kuɗinnan gurin Abba? Ina da buƙatar kuɗinne sosai in ma wani yanka ko surƙulle ake buƙata duka zanyi" "Wannan karon ba abinda zanyi maka Jamilu tunda idan nayi maka aiki baka cika min alkawari, haka kasa nayi aiki akan ɗan uwanka Mutallab saboda kar ya samu aiki mukayi kuma yarasa aikin har yanzu amma baka cikamuna kuɗin aikinmu ba". "Tuna nakeyi malam na gayamaka matsala aka samu wata yarinya ce ta damfareni shiyasa amma kayi haƙuri zan cika nabaka har na wannan aikin da za'ayi mun." "To Shikenan babu laifi zan ƙara yimaka akaro na ƙarshe, idan ka saɓa to tabbas duk abinda ya biyo bayanka kai kajiyo, yanzu faɗa mun menene kake da buƙata kake so ayi maka aiki akansa?" Murmushin jin daɗi Jamil yayi haɗe da cewa, "Malam kuɗi nakeso na karɓa masu ɗan banzan tsoka agun Abba ina so a rufe masa baki yakasa musamin ko tambayata me zanyi dasu". "Shikenan angama ka ɗauka buƙatarka ta biya ko akwai wani abu bayan shi?" "A yanzu dai ita kenan sai kuma na sake juyowa da wata". "Babu damuwa tashi kaje, amma ranar asabar kasamu alawa ka bawa yaran da basu fara magana ba katabbatar sun sha indai har kabayar to mahaifinka zai baka duk wani abu daka buƙata daga gurinsa batare da yace uffan ba kamar yadda yaran nan basa magana haka shima bazai ce maka ƙanzil ba balle har ya tambayeka, sauran aikin kuma kabarshi hannuna". "Huhuhu sai malam ilya." Jamil ya saki wani irin farinciki cike dajin daɗi". Malam Iliya yayi dariyar shima lokaci ɗaya ya ɗauke fuska haɗe da cewa, "tashi kaje yau zanfara aikin zuwa gobe, jibi kuma na kammala sai kayi abinda nace". "To Nagode malam" Jamil ya faɗa yanata faman murmushi hangowa kansa sabbin ƴammata da zaiyi, dan shi kam gaba ɗaya dukiyarsa acan take ƙarewa, ko zancen zuwan Sadeeq makaranta ƙarya ce ya sheƙa ya aza zai samu kuɗin a hannu yayi bushasharsa yace an ɗauke, sai gashi abban yace ayi shirye shiryen komai zai tura kuɗin kai tsaye, matarsa kuma ganin dukiyar da suke ci ƙarƙashin Abba yasa ta bazama malamai itama ta hanashi ƙara auren tare da juyashi duk yanda take so, shiyasa yake masifar tsoronta dan duk iskancin da yakeyi a ɓoye yake bada sabunta, wanda ko nawa ke ga account ɗinsa zai iya zubewa macce su ya kwanta da ita ta lashe su tas. Da wannan tunanin ya ƙara so gida, yana ƙoƙarin wucewa sashensa ya hango Mutallab nafitowa daga sashensu zai fita, sake da fuskar da yake son nuna masa shi alallai yaga ɗan uwansa yaja ya tsayanan, cikin ransa kuwa jinsa yakeyi kamar ya kashe Mutallab ya huta saboda yanda ya tsanesa. Tun kafin Mutallab ya ƙaraso Jamil ya sake takowa ya iso gunshi yana faɗin "Barka da marece ƙanina wai Menene sirrin naga kwana biyun nan sai wani sheƙi kakeyi kana ƙara kyau? Ko dai ansamu aikin ne?" Murmushi Mutallab ya saki na gefen baki yana ɗan sosa ƙeyar kansa dan kuwa ayanzu ya fahimce ko wanene Ya Jamil, sai dai kawai ya kalleshi, ada yana matuƙar bashi gida saboda nuna damuwar da yakeyi dashi ashe shi ya maidashi sakarai yayi ta nunawa yana sonshi, sai gashi ranar da yafara samun aiki yaji yana waya yana cewa kora wane hali a tabbatar masa da kuskurene akayi aka bashi upper ɗin wani akoreshi, sai gashi yana zuwa kuma haka ta tattabata, Tun daga ranar yaka kansa dashi ya kuma san irin zaman da zai cigaba dayi dashi. "Am barka da safiya Babban yaya, kaima kasan ai bazan samu Aiki ba batare dana kawo maka ba kasaka mini Albarka". Ya ƙare zancen yana sake karantar fuskar Jamil, shi kuwa cikin nuna iya ƙwarewa da makirci daya gado agun Mahaifiyarsa yace, "Haka ne Mutallab karka damu kaci gaba da ƙokartawa wataƙil zaka iya samu ƙanina, komai ai lokaci ne dashi." Murmushi Mutallab yayi yana mamakin yadda ɗan uwan nasa ke cigaba da pretending nuna damuwarsa akansa afili wacce acikin ransa ya tabbata ba haka bane sannan yace, "Ameen babban yaya nagode da ƙarfafamin gwuiwa da kakeyi akoda yaushe, yanzu ma da ƙoƙan barata nazo ya Jamil ko zaka samarmin koda gurine a shagonka sai na zauna?". Farko Jamil yafara ƙoƙarin sauya fuska ya aza taimakon nema masa aiki ne Mutallab zai buƙata, amma ɗaya ji cewa ƙasƙantar da kaine Mutallab zai yi agunsa kamar yanda yake tunani sai yace, "Afwan Mutallab nayi tunanin hakan wallahi abunda yasa banyi maka magana ba ƙannen abokina ke zama shagon yanzu, sai dai kaje kasamu Abba kayi masa magana yabaka ɗaya daga cikin shagunansa ko tsaron gidan mansa sai a matsayin manager". Jamil yayi maganar yana dariya a ƙasan ransa don yasan ko sama da ƙasa zasu haɗe Abba bazai masa ko ɗaya acii ba, Mutallab daya gama fahimtar kamar gatse ne yayan nasa keyi masa kawai sai yace, "ka kawo shawara ya Jamil amma kasa baki mana". Yayi hakan ne duka don ya sake tabbatar da abinda ya jiyo ɗan uwan nasa nayi masa na zagon ƙasa, Ganin kamar Mutallab ɗin na nema yaƙureshi ya sashi cewa, "Bakada damuwa kaje ka sameshi kuyi magana,nima zanyi magar dashi". Cikin girmamawa yayi masa godiya sannan yabar gurin, Da harara Jamil ya rakasa yana faɗin, "Ni ɗan iska ne da zan saka baki ga cibanka? Ai ina nan dakai ba wani aiki da zakayi ko sana'a sama da shaye-shaye da neman mata, shine target ɗina dakai na ƙarshe ta yanda kai da Abban zan shiga tsakaninku har abada, munafuki kawai".  ***** ABNU EVENT CENTER   8:00 Na Dare. Babban gurine da aka ƙawata tun daga farƙon gate har zuwa ainahin inda aka tanada saboda uwar taro wato Meenal Abdul-aziz, zaka fahimci wannan gurin na masu ƙasa ne masu hannu da shin ko kuma hamshaƙan ƴan siyasa duba da yadda ma'aikatan ke tafiyar da komai cikin tsari da kuma girmama mutanen da suka halarci wajen, A tsarin da aka yiwa wajen bayan ka wuce gate na farko wasu haɗaɗɗun bishiyoni dake dauƙe da wasu kalar fitilu masu saka idanuwa motsawa saboda salon fitar haskawarsu dake cike da ƙayatarwa, sai tamfatsetsen kafet dake zagaye da filin inda wata fitila ke sake hasko kyakkyawan rubutun dake rubuce a jikin ginin ansa, MEENAL ABDULAZIZ BIRTHDAY @21!!! Ga wani irin sauti dake tashi tun daga bakin shiga cikin Hall ɗin da faɗar yadda aka tsara shi da wasu irin abun decoration ɓata lokaci ne don duk yanda za'a faɗa tsarin ya zarce haka, kusan kowa ya gama halarta wajen birthdaygirl kaɗai ake jira dake can wajen makeup tana jiran special man ɗinta da zai ɗaukota sai Mommy da har yanzu itama bata ƙara so ba saboda tsayawa jiran ƴarta Asiya da kuma Shukura da tayi, cikin mintuna bakwai sai ga Mommy ta ƙaraso wajen tasamu gurin parking suka fito itada da yaranta sunyi shigar baƙar abaya sai Mommy ita kuma tayi shigar wata irin danƙareriyar atamfa da akayi mata ɗinkin Abuja gown da kuɗin atamfar kaɗai zai kai 2hundredK sai tsadadden mayafinta data yafa daya matuƙar fito da kyanta don tabbas itama ɗin kyakkyawa ce gata matar manya daka gani, Shukura ce dake faman baza idanuwanta tana kallon wajen tace, "Tirƙashi! Gaskiya Mommy wannan yarinyar kun sangartata iya sangartawa wlh, wai wannan birthday ne aka nark dukiya haka? Laaa...kalli fa turawa ne suke welcoming ɗinmu." Murmushi kawai Mommy tayi don ba tada abun cewa tunda lamarin yafi ƙarfinta, magana kawai zatayi ace baƙi ciki takeyi bata ƙaunar yarinyar, Asiya ta kalli Shukura tace, "kema dai kya faɗa Yaya shukrah dan ma bakiga komai ba, wallahi Allah Meenal cikakkiyar sangartaciya ce da ba'a magana". "Kai ya isa haka ku shige muje mana." Mommy tafaɗa cike da son dakatar dasu don bataga amfanin maganar ba kafin suka iso bakin wajen, kowannen su scanning katinsu akayi masa ya nuna wani green Abu sannan aka buɗe masu ƙofa suka shige, duk da tun ta jikin glass ɗin dake zagaye da ganin wajen zaka hango ƙawatuwar cikin hall ɗin suna shigowa su Asiya suka saki baki suna kallon ikon Allah, manya manyan yara ne agurin kama daga ƴaƴan ministoci da kuma manyan ƴan siyasa, ganin mawaƙan dake tashe a lokacin sukayi kowanne akan hamshaqiyar kujerarsa sai kuma wata lafiyayyar kujera da akayiwa ado da kalar baby pink wacce ke nuni da ta birthday girl ce, tun kafin su zauna Mommy data hango grandama da Maamah ta nufi wajensu suka gaisa, daƙyar Maamah ta amsa mata tana ƙara jin tsanarta a zuciyarta musamman da idanuwanta suka ganar mata kalar shigar dake jikinta, batare da Mommy ta damu ba ta juya zuwa inda yaranta suke sunata surutu da mamakin haɗuwa irin yadda aka tsara wajen, bayan mintuna biyar da isowarsu Mommy mc yayi sanarwar shigowar Birthday girl da ƙawayenta dake tare da ita suma cikin shigar Baby pink da sukayi anko, sakin wata zazzafar waƙar dj yayi kafin ƙawayenta su fara shigowa gurin suna wani irin taku haɗe da bada kyakkyawan step ɗaya matuƙar burge kowa wajen sannan itama ta shigo hannunta cikin na AAB yaro mai tashe haɗe da lokaci yaro ɗan gidan babban dan majalisa wanda yake ɗaya tilo a gurin mahaifinsa, Ihu ƴan matan dake wajen suka saka haɗe da tafi  shiga tun kamin su ƙaraso ciki, yadda yake riƙe da hannunta sai ka rantse mijinta ne ko kuma diner ɗin aurensu akayi, duk da kana kallonsu kasan sam babu wata dacewa tsakaninsu kawai neman sunane, ba tare data ji kunyar kwa ba sukaci gaba da ratsowa ciki zuwa wajen zaman da aka tanadar mata, sai alokacin Mommy ta ɗago kanta tana kallon hannun Meenal dake cikin na AAB sanye da wata haɗaɗɗiyar gown dark pink da taji adon duwatsu tundaga sama har ƙasa, kanta an zuba mata attachment ga Nail da akasaka mata tayi matuƙar kyau makeup ɗin yaƙara fito da ainahin kyanta, a hankali Mommy tabi hannuwanmu da kallo cike da tashin hankali saboda bata taɓa tsammanin rashin kunyar Meenal ɗin zata kaita ga aikata hakan ba agaban idanuwan mutane da kuma uwayenta, kallo ɗaya zaka yiwa yaron kasan idan shekarunsu basu zo ɗaya ba to tabbas Meenal zata ɗan girmemasa, sai ɗaya kaita har kujerar da zata zauna sannan ya juya da niyar barin wajen ta ɗan ɓata rai haɗe da cewa, "Besty ina zaka je?" Daidai kunnen mc ai kuwa yayi caraf cikin kwantar da murya haɗe da shaƙiyanci yace "where are you going Bestyyy! Comeback pls kafara taya  birthday girl murna kafin kafita, dj aba besty sautinsa na musamman". Wani kalar kiɗa dj ya saka a take AAB  ya fiddo rafar Naira dubu-dubu ya shiga zubesu akanta har sai da suka ƙare sannan yafita don babu namiji ko ɗaya a wajen, take waje ya ruɗe da shewa da ihun ƴan mata, nan kuma akaci gaba da gudanar da shagalin kowane mawaƙi nafitowa da baitukansa yana tayata mura har aka kammala, daga nan aka wuce inda ake serve your self kwa ya ɗin abinda yake so yaci, bayan an kammala kuma wasu turawa da kana kallonsu kasan ma'aikatan wajen ne suka shigo da wani abu kamar mota yana tafiya suna controlling nasa da remote ɗauke da wani irin haɗaɗen cake daya sha ado sosai har suka ƙaraso gaban kujerar da Meenal take zaune zata yanka, take family and friends suka zagayeta wanda hakan yayi daidai da isowar mahaifinta data azawa rigimar yazo ta yanka cake tare dashi, take wasu turawa suka fara busa wani irin sautin dake fita da waƙar HAPPY BIRTHDAY TO YOU.. HAPPY BIRTHDAY MEENAL..HAPPY BIRTHDAY BIG GIRL HAPPY BIRTHDAY DADY GIRLLLL... A lokaci ɗaya suma mutane na rera waƙar, suna gamawa Meenal na bushe wutar candle ɗin dake jikin cake ɗin tare da yankawa akasa tafi, ɗibowa tayi ta kaiwa Dady abaki sannan takai sauran abakin Maamah da wani irin farinciki ya rufeta, duk da soyayyar da Dady keyiwa Meenal sai yaga rashin kyautawarta dako kallon gefen da Mommy take tsaye batayi ba, cake ɗin ya ɗebo ya kaiwa Meenal abaki sauran kuma yaba Mommy da ba zato ba tsammani taga hannunsa riƙe da cake ɗin a bakinta, hakan ya bala'in burge mutane suka hau tafi suna dariya, ya kuma janyowa Mommy girman sosai a wajen da Meenal taso ta walaƙantata, inda wasu suke ganin Dady yayi daidai wasu kuma suke ganin kawai dai Mommy ta gama shanye Dady shiyasa yakasa ɓoye hakan agaban mutane, musamman Maamah da sauran danganta da suka halarci wajen, inda da suka bar wajen cike da wannan tunanin bayan an kammala taron kowa ya tafi da abubuwan da aka rarraba, Mommy da motarta suka wuce gida ita da yaran, Dady kuma shiga ɗauki Meenal da wasu ƙawayenta suka wuce gida don ɗazu da motar AAB aka kawota, shima kuma bai bar wajen ba har saida Meenal ta gabatarwa da Dady shi a matsayin Besty ɗinta yayi masa godiya shima aka cika masa mota da kayan Birthday ɗin nata sannan ya wuce.      (Hmm...besty!🙄 Muje zuwa ƴar gidan Dady Happy birthday to you big girl). _ Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only Zaki biya ta wannan account ɗin👇🏻 *ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *MUTALLAB ASAD MUTALLAB* (Labari mai taba zuciya) NA *BILLY S FARI* & *NANA DISO* RUBUTUN ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU TAFIYAR BIYU TAFI DAYA *SHAFI NA GOMA SHA BIYU* Mutallab na fita yaga Aryan na ƙoƙarin tsaida motarsa a ƙofar gidan nasu, ƙarasawa yayi yana masa sallama haɗe da bashi hannu suka gaisa yana cewa. "MAM kaga aiki ya ɓoyeni kwana biyu ko? Bari kawai ko jiya tsabar gajiya tasa muna chat bacci yakwasheni, wannan aikin na office is not Easy at All MAM".  Murmushi mutallab yayi haɗe da cewa, "Haba Aryan! Kawai kaci gaba da godewa Allah tare da jajircewa, kana kallo mugashi munata tsalle guri ɗaya har yanzu abun ya gagara mun rasa aikin yi". Aryan yayi dariya kafin yace, "Lallai MAM bazaka gane ba fitar nan ta tunda sassafe ba daɗi ne da iitaa ba, sannan kawuni kana ƙarar da lokacinka can ba damar ɗagawa kabar office ɗin saboda tarin aiki, shiyasa yau nace musu sai after 2 zan shigo saboda ina son ganinka tunda kai ko ƴar irin ziyarar nan mutum bai samu daga wajenka, if not da yanzu ina can gaban system ina fama, ya kake, hope kuna lapya?". "Lafiya klw Alhamdulillah" "Yawwa zancen aikinka nazo muyi, kaga har yanzu dai ta bangaren nawa dasu yaya ke nemamaka ba'a dace ba, ya labarin ta ɓangaren naka?" "Shima dai kusan hakan?" Mutallab ya faɗa fuskarsa cike da damuwa, Aryan yayi shiru shima yana jin damuwar abun a ransa kafin yace, "To yanzu haka zakaci gaba zama MAM babu aiki? Gaskiya inaga yakamata ko wata ƙaramar sana'arce kafara nema kayi, zaman a haka sam baida amfani kuma ma bazai yihu ba". "Tunanin dana gamayi kenan yau da safe, kuma in sha Allahu zan tashi tsaye na nemi sana'a Aryan don nima bana son zaman hakan, idan dama taƙiya sai a koma hagu tunda kana ganin dai yadda nadinga neman aikin Allah bai yi zan samu ba". "Nasani MAM in sha Allah Allah zai  kawo babban rabo ni bari na huce idan Allah yakaimu gobe zan shigo." "To babu damuwa abokina Nagode Agaida mutan gidan." Mutallab ya faɗa yana boɗe masa ƙofar, har Aryan zai tada motar bayan ya shiga ya zauna sai kuma yafasa yana turo kansa ta jikin tagar motar haɗe da cewa, "Ina ƴar ƙanwata Afrah kwana biyu zuwa uku kenan duk nazo bana ganinta, hop dai ba jikin ba?" Murmushi Mutallab yayi tare da cewa, "A'a kwanannan ai ta ɗan samu sauƙi sosai tunda gashi almost 2weeks tana zuwa makarantaranta lafiya klw". "Masha Allah Allah yaƙara mata lafiya, Allah MAM bana don ciwon Afrah ya tashi har cikin ƙoƙon raina nake jinsa". Yaƙare zancen haɗe da tayar da motar Mutallab na faɗin, "Ya muka iya aryan, jarabawace Allah ya bamu ikon canyeta" ya amsa mashi da Amin sannan yaja motarshi yabar wajen, shi kuma ya juya yakoma cikin gidan nasu yana jin wata irin damuwa na taso masa, shashin mahaifin nasu ya nufa yayi Sallama aka bashi izinin shiga, Umma da Anty Amarya dake zaune tare da Dady suka ɗago suna kallonsa, fuskarsa kaɗai suka kalli suka ji yayi masu wani mugun kwarjini daya sa hatta Abban nasu da yaɗago kai yana kallonsa sai daya kauda kansa yana jin wani abu na motsa acikin ransa, ƙarasowa yayi yace "Abba barka da safiya". "Sai yanzu kaga damar zuwa gaisheni Mutallab? Ai nazata ni kake jira nazo na gaisheka, ace tun ɗazu kai ba aiki ba kai ba sana'a ba amma yanzu kake zuwa gaisheni? Kai kenan kwanciya a ɗaki kana zaman kashe wando". Ƴar sauke ajiyar

Chapter 7 of 54