*Allahumma munzilal kitab, sari'al hisab, ahzamil ahzab, allahummah zimhum wa zalzilhum
Allahummah inna naj'aluka finnuhurihim, wana'uzu bika min shururihim, Allahummak finihim bima shi'ita*
"Matuƙar kariƙe wuɗannan addu'o'in da suka fito daga bakin fiyayyen halitta to tabbas sai kayi galaba akansu kuma sai Allah ya baka kariya ga dukkanin abinda zasu yimaka". Ta ƙare zancen tana sake nanata masa addu'o'in, suna zaune mahaifin Aryan ya shigo ta labarta masa abinda yafaru bayan yafito wanka yaci abincin, kiran Mutallab ya sake yi ya tambayesa menene gaskiyar zance ya sake faɗa masa kamar yanda Ummie ta sanar dashi, haƙuri shima ya sake bashi sannan ya tabbatar masa da cewa In sha Allah zai je yayi magana da mahaifinsa kuma yasan zai haƙura.
Godiya Mutallab yayi masu sosai kafin yakoma ɗakin Aryaan dake zaune yana cike wasu takardu, wayarsa ya ciro ya sake kiran Jalil akaro na ba adadi ya tambayesa jikin Afrah ya shaida masa data samu sauƙi amma har yanzu bacci takeyi, nasiha ya sake yimasa akan sha'anin gidan kafin yafaɗa masa cewa yana tare da Aryan in Sha Allah gobe zai zo su duba jikin Afrah sannan sukayi sallama. A daren dai baiyi bacci ba sai saƙawa yakeyi da kuma kwancewa akan tunanin makomarsa yana jin ya zame masa dole yaƙara zage damtse ya tashi ya nema ko don rayuwar Afrah da Jalil da duk duniya yanzu bayada kowa da zai kalla yaji sanyi sama dasu.
Washe gari Afrah taji sauƙi sai dai fa har yanzun kuka takeyi akan sai ankaita wajen ya Mutallab, sai da Jalil yakira mata shi a waya sukayi magana yace tagyara Jalil yaraka tatafi makaranta in zata iya zai sameta acan yadubata, ai kuwa cike da farinciki duk da bata jin ƙarfin jikin nata ta miƙe tahau shiri, Jalil dake tsaye yana kallonta bayan ta gama shiryawar ya zungure mata kai haɗe da cewa, "Wato kinfi son ya Mutallab akaina shiyasa ko ganina bakyayi kike nema ki takani kiwuce ke mai yaya ko?" Langaɓe kai tayi haɗe da cewa, "Ya Jalil ina son ka fa! But na ya Mutallab yafi yawa gaskiya". Taƙare zancen ganin yanda ya ɗaure fuska tana tuntsurewa da dariya haɗe da ficewa da gudu ta sauka ƙasa shi kuma yabi bayanta da yana dariya, koda suka fito sashen Abba Jalil ya rakata ta gaishesa ya amsa mata ciki-ciki ba tare daya damu da rashin lafiyar data ƙwana da ita ba yana cewa, "next time idan kika sake maimaita haukan da kika yimani bisa duk hukuncin dana zartar acikin gidana to tabbas sai shafeki kin ji ko?" Yaƙare zancen a tsawace tare da ɗagowa yana kallonta, da sauri Afrah da tsoron Mahifinnata yafara shigarta ta ɓuya bayan ya Jalil dake tsaye gefe yayi folding hannayensa akan ƙirji fuska a murtuƙe tana faɗin, "Abba kayi haƙuri?"
"Kufice mun daga ɗaki". Yafaɗa yana jeho mata kuɗin daya saba bata na break don ƴan uwanta tun ɗazu sun wuce, da ita baza taje ba saboda yanayin jikinta amma jin ya Mutallab zaije ya dubata acan yasata shiryawa tatafi don ma tasoma makara, Jalil ne ya duƙa ya ɗauki kuɗin ba tare daya damu da hararar da Abba keyi masa ba yaja hannunta suka fice, sai daya rakata har makarantar sannan ya juyo ya dawo gida, ya Mutallab kuwa saboda zuwa wajenta yasa Aryan jiransa bai tafi wajen aiki ba har sai da tara da rabi tayi lokacin sun fito breakfast, biskit dasu chacculate ya tsaya ya sai mata a wani shago sannan suka nufi makarantar, office ɗin shugabar makarantar suka je aka kira masu ita, da gudu tazo ta rungume ya Mutallab lokaci ɗaya tana dariya da kuma hawaye, murmushi ya saki ya ɗago kanta yana share mata hawayen haɗe da cewa, "to menene Afrah ba gani ba?"
"Ya Please comeback home". Ta faɗa tana sake ƙwaɓe fuska zatayi kuka haɗe da kallonsa, dariya ta bashi yasa hannu ya share mata hawaye haɗe da cewa, "in Sha Allah zan dawo kin ji ko, wannan kukan ne kaɗai naki bana so idan baki daina ba ni kuma bazan dawo ba". da sauri tasa hannuwa ta share guntayen hawayen da suka sake zubo mata sannan ta gaishesa, bayan ya amsa ta juya ta gaida Aryan da tun ɗazu idanuwansa ke kanta, shi har yau yana sake mamakin irin kyan da Allah ya zubawa yarinyar da ita har yayan nata da kamarsu ɗaya, sai kace ba jinin hausawa ba yana mai addu'a cikin ransa Allah ya mallaka masa yarinyar dan ya jima da mutuwa akan sonta. Shiyasa ma da yaji Mutallab yace zai je wajenta yaƙi fita aiki ya zauna zaman jiransa da sunan zai rakata don kawai ya ganeta.
Murmushi ya sakar mata haɗe da amsawa yayi mata ya jiki da kuma ya karatu ta amsa sannan ya basu waje na mintuna uku, da zasu tafi ya Mutallab ya bata ledar bisciut da chacculate daya siyo mata shi kuma Aryan ya ciro dubu biyu ya miƙa mata, ƙin karɓa tayi har sai da Mutallab yace mata takarɓa sannan, bayan Aryan da yake ji tamkar kada ya tafi yabarta yawuce Mutallab yace mata data Isa gida kada ta shiga ciki har sai ta kaiwa Jalil kuɗin ya ajiye mata dan kada asamu wata matsalar itama idan aka ganta dasu, amsa masa da to tayi sannan suka wuce ya Aryan ya ajiyesa kasuwa shi kuma ya wuce wajen aikinsa.
Acikin kwanakin nan ba ƙaramin wahala mutallab yake sha ba dan kullum yini yakeyi a kasuwa, kusan shaguna 7 yanzu yakeyiwa dako, ganin yadda Allah ya rufa masa asiri yanzu sai yasakawa ransa nutsuwa bakamar kwankin baya ba da bashida wata nutsuwa aransa ko kadan, amma duba da yadda Aryan da ummie ke jansa ajiki kai kayi tunanin ɗan gidan ne yasaka Mutallab kwantar da hankalinsa sosai, yau ma bai dawo ba sai wajejen karfe 10 na dare dan ya saro gwanjo na kusan dubu talatin yana kasawa agefen titi yana siyarwa cikin ikon Allah ranar da yafara sarowa mutum biyu ne kadai suka siya, da har yace ya haƙura da cinikin amma ganin yadda Idris ke sake ƙarfafa masa gwuiwa ya sakashi haƙura ya cigaba da kasawa haɗe da ƙara dagewa da mai da hanƙali, yau alhamdulillah don gabaɗaya aka siye kayan shiyasa ma yayi dare, cikin farinciki yake mamakin cinikin da yayi na kusan dubu arba'in da biyar don yasamu riba har ta kusan dubu goma sha biyar, zama yayi yana sake lissafa kuɗin sai ga Aryan yashigo "MAM ka daga min hankali wallahi har Ummie tayi bacci tana tambayar lafiya kuwa baka dawo ba? Tukuna ma ina ka tsaya sannan wannan wane irin aiki ne kakeyi haka? Ka ganka kuwa sai kace wani ɗan dako? Kullum idan ka dawo naganeka a haka ina so na tambayeki amma sai na manta, wane irin aiki ne kakeyi haka?" Ɗagowa yayi ya zubawa abokin nasa idanu kafin yace, "Meye laifin idan ma shine, ko ɗan dako ba mutum bane? What ever dai nima itace sana'ar da nakeyi yanzu!" Ya ƙare zancen in i don't care yana ɗage kafaɗa, da mugun mamaki Aryan ya kalleshi yace "What! MAA dako kakeyi? Haba wasa dai kakeyi don wallahi kafi ƙarfinsa". "Hmmm Aryan kenan! Anaka tunanin kake ganin kamar nafi karfinsa amma ni agurina babu abunda yafi dacewa dani sai shi, ba ruwana da kuɗi mahaifina tunda ba nawa bane ƙara natashi na zage dantse na nemi nakaina tare da rufin asirin Allah, karatun ma da nayi yanzu haka bani da rabo acikinsa, ƙilan rabon nawa acikin dakon da nakeyi yake, don haka ni fatana kawai na rufama kaina asiri". Atake idanuwan Aryan suka ciko da kwallah yana jin tausayin abokin nasa har cikin zuciyarsa, ganin shima yafara karaya yasashi miƙewa yashige toilet yana tunanin gobe ma ina sha Allah zai fara zuwa ya koyi ɗinkin maza da mata, dan yana jin ɗazu yadda wani costumer ɗinsu ke tambayar Alhaji ina ma ace suna irin dinkunan nan na mata da maza da yashiga dasu Niger yaga irin arziƙin da ake samu dasu. Jin wannan hirar yasa Idris dashi suka yanke shawarar fara zuwa koyan ɗinkin ko Allah zaisa sunada rabo don mai nema fa baya gajiya kuma mutum bai san inda rabonsa yake ba.
Sai da Mutallab yayi sati biyu a gidan su Aryan sannan mahaifin Aryan yaje ya bawa Abba haƙuri akan abinda ya faru dan dama ya bari ne har ya huce daga fushin da yayi, ya kuma samu daƙyar ya haƙura sannan yace ya amince Mutallab ya dawo masa gida amma bisa sharaɗin kar ya sake shigar masa cikin gida inda iyalinsa suke, ya tsaya anan kaɗai sashensa, sannan kuma bazai sake cimasa abincin gida ba yaje can yanema da kansa, sosai maganar ta girgiza mahaifin Aryan ganin tarin arziƙin da Abba ke dashi amma yake yankewa ɗan nasa irin wannan hukunci, amma da yake maslaha yazo nemawa yaron kuma yasan baida mahaifiya acikin gidan balle ya damu don a hanasa shiga ciki, ƴar uwarsa kuwa yana iya sa akirata nan waje aduk lokacin da yake son ganinta yasa yacewa Abba ya amince da sharaɗin....
#Mutallab Asad
#Ƴan Tagwaye
#Billy S Fari
#Nana Diso.
SHAFI NA ASHIRIN DA BIYU.
*MUTALLAB ASAD*
Arewabook:- billysfari
Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.
bayan tafiyarsa umma tashiga bugar cikin abba jin wani baƙone yazo , anan yake sanar mata baban aryan ne abokin mutallab yazo bashi haƙuri akan abinda yafaru, "Kuma shikenan ka haƙura Abbansu? Gaskiya da saurin sakkowa kake yanzu kenan yaron nan yaci kuɗinnan abanza saboda Allah dan baisan zafinsu da yadda akeji ba?"
"Ya zanyi? Ai hannunka baya ruɓewa ka yanke kayar, kuma banda abunki ai ba kai tsaye na amince ba har sai dana saka masa sharaɗin hanashi shigowa gidana yanzu na kuma soke abashi abincin gidana daga yanzu dan haka zama ne da zaiyi acan kurkukun daƙinsa, kinga kuwa dawowar tasa ma ba tada amfani acikin gidannan? Wlh Mutallab tunda wannan abun yafaru naji naƙara tsanarsa kuma yafice mani a zuciya bana jinsa cikin raina kamar yanda nake jin sauran ƴaƴana" Murmushi Umma tayi haɗe da cewa "Wannan mataki daka ɗauka shine daidai ubangiji Allah yaƙara maka lafiya". Ya amsa da "Ameen ya Allah ko zaki kawomin farau farau?"
"Eh to amma inaga babu gasarar ta ƙare sai dai nasaka ƴan aiki suyi maka kafin mugama fira sun gama".
"Ince Afrah ta iya?" Atake annurin zuciyarta yaɓace dan batason ko kaɗan taji yana ambatar sunan ɗaya daga cikin yaran, musamman yarinyar da Mutallab da duk kwanan duniya inta kallesu take hango fuskar shegiyar uwarsu atare dasu saboda kamar da sukeyi da ita, dan haka cikin ɓacin rai tayi saurin faɗan, "kai kuwa ina Afrah ina kamu Abbansu? Ai wannan aikin larai ne bari yanzu zata haɗa zuwa anjima nasan ya kwanta gobe sai a haɗa maka ko?"
"To madallah ba damuwa amma kuma nasan itama Afrah ɗin ta iya tunda ina ganinta tare dasu a kitchen indai tana gida". Umma tayi kamar bata kisa ba tare da ɗauki masa wata firar don yau daga ita sai shine agidan saboda Aunty Amarya ta tafi gidan mahaifiyarta bayan ta shantakawa Abba ƙarya akan asubiti zataje dubo wata ƙawarta da batada lafiya sannan yabarta, hakan yasata samun mai Napeep dan bata fita da driver ba gudun su dawo Abba yatambayesa yace ai gidansu yakaita, tana shiga gidansu ta tarar da mahaifiyarta a palour tana cewa, "taso Hajiya na samo kuɗin nan daƙyar tun satin daya wuce, nabari ƙura ta kafa ne dan kar a fahimci ni na ɗauka shiyasa kika ganni sai yau, hmmm Hajiya wai kinsan ta yadda na shiga damuwa akan satar kuɗin nan? Wallahi rayuka sun ɓaci sosai don daga ƙarshe waccan shashashar da bata fahimci komai ba ta tayani muka ƙalawa Mutallab satar saboda ya taka sawun ɓarawo". Cikin rashin damuwa da abinda Aunty Amarya ka faɗa Hajiyarta tace "Ke dallah ni bani nan zaki tsaya shirman naki har wani yazo ya gani, Me ruwanki da wanda aka ƙalawa tunda Allah yasa bake aka kama ba to menene abun damuwa kuma? Yanzu idan million ɗaya kikace Alhaji yabaki zai baki ne? Kina zaune da mashurika acikin gida ai dole muyi da gaske ita tsafi ɗanta tsafi babu tsoron Allah ko guda acikin ransu, yanzu million nawane a nan?".
"Million biyu ne har da rabi".
Murmushi dattijuwar tayi tana cewa "Kai Masha Allah, Kice da karbar fili nan kusa gurin mijinki". Dariya Aunty Amarya tayi tace, "Banda haufi da damuwa indai da ranki mahaifiyata".
"Ahh to ina zakiga damuwa kullum muna tafe yarinya, da azaune muke kina tunanin da wannan matar bata fitar dake ba tuntuni".
"Tuni ma Hajiya ai ni nasan hakan". Aunty Amarya tafaɗa tare da miƙewa saman kujera zuciyarta cike da farinciki itama zata kame alhajin nata a hannu.
Shikuwa Mahaifin Aryan ko daya koma ya sanar da Mutallab sharaɗin da Abba ya gindaya akansa ya matuƙar girgiza dajin sharaɗin musamman na rashin shigarsa cikin gidan, ba tunaninsa irin wane abu zai faru da Afrah acikin gidan ba tare daya sani ba alhalin suna zaune a waje guda, ƙarfafa masa Ummie da Aryan sukayi akan ya amince yakoma ɗin ko don ya samu natsuwa a ransa, dole ya amince da sharaɗin na mahaifinsa washe gari Abban Aryan ya ɗaukesa da kanshi ya maidashi gidan ya kuma sa yaba mahaifinsa haƙuri duk da yasan beda laifi, jaddada masa yayi akan bashi ba abincin gidansa kuma kada ya kuskura yaga ƙafarsa aciki ya tsaya nan sashensu baya buƙatar ganinsa tare da iyalinsa ya amsa mashi da to sannan mahaifin Aryan yayi masu sallama ya tafi shi kuma ya wuce ɗakinsa yana sauke ajiyar zuciya, a gyare ya iskoshi tsaf tamkar yana nan don kullum sai Jalil ya gyara masa shi ya kuma share, don haka kan katifarsa kawai ya faɗa tare da rufe idanuwansa a hankali yana tunani abinda zai kuma zo masa anan gaba bayan ya tsallake wannan jarabawar, bayan ya huta yamiƙe ya nufi ɗakin Jalil ya iskoshi a rufe don haka yayi tafiyarsa kasuwa, sai da yabiya gurin koyan ɗinkin inda ya samu Idris acan, awansa ɗaya kamin yawuce wajen aikinsa na dako, yauma sun gama kenan sukayi baƙon costumers tunda yayi siyayyar yagana yake satar kallon Mutallab daga baya dai yakasa rike abunda zai faɗa yana ta kallon yadda Mutallab ɗin ke kwasar kaya akansa yana nufar motar da zata ɗaukar masa kayan yace da Alhaji Tanimu, "Alhaji ina kasamu wannan yaron mai hazaƙa haka? Irin yaran nan idan ba'a bi hattara ba himmarsu kesa suzo sufi ubanningidansu kuɗi, Atake ciwon hasada ya taso ya dunƙulewa Alhaji Tanimu zuciyarsa ta karaya yana kara maimaita maganar costumer ɗin nasa yana kallon Mutallab daketa jidar kaya har yagama yazo ya rissina wajen Alhajin ya sheda masa sun gama. Kalmar sannu da yake yawan gayamasa yau baice masa komai ba sai yayi masa banza hakan yasa Mutallab ɗin ya fahimci ƙilan akwai abinda ke samun Alhajin, ɗan haka saboda kada ya takurasa sai yayi gaba kawai yaje ya kasa gonjansa na yara da mata da maza wannan karan kayan dubu hamsin yasiya, ganin yadda ake masa ciniki yasashi jin daɗi ragowar dayayi sai yashiga kasuwa yana zazzagawa dasu, ganin ƙarfe 4 tayi ya sashi ajiye kayan yaje yayi Alwala yayi Sallah, yana dawowa ya tadda inda ya ajiye ragowar kayan nasa da zasu kai na kusan dubu biyar ba komai an ɗauke yayita nema amma ya rasa har kusan lokacin sallah yashiga yana cigiya amma kowa sai yace masa shifa baiga kullin buhu ba, zuciyarsa babu daɗi yaje yayi Sallah tare da addu'ar Allah ya bayyana masasu idan kuma ba rabonsa bane Allah ya mayar masa da alkhairi, ko dayagama sallar sai da yayi azkar ɗinsa sannan yakara cigiya amma shiru, ganin lokacin dakonsa yashiga yasashi komawa shagon Alhajin, Nan fa Alhajin yashiga surfa masa masifa ta ba gaura ba dalili yana faɗin idan yagaji yagaya masa sai ya sallameshi amma akan wani dalili zai tafi yawonsa bayan yasan Akwai mutanen da zai kwasarwa kaya".
Cikin ƴar damuwa Mutallab yace, "Dan Allah Alhaji kayi haƙuri kayan da nake kasawa ne aka ɗaukemun shine nashiga dubawa kayi hakuri bazan ƙara makaraba".
Tsaki yaja yace "Gwara da aka ɗauke ai kafiya hadama naga shaguna 4 yanzu kakeyiwa aiki shine yanzu kuma kasiyo gwanjo kana siyarwa, mtsee... ku dama fulany badai son kuɗi daga zuwa sai kuce sai kunfi ɗan gari kuɗi".
Shi dai Mutallab baice komai ba duk da dariyar da yaji mutanen dake saurarar faɗa da Alhaji keyi masa nayi, haka yakarɓi aikin da zaiyi yaƙarasa amma ga mamakinsa yau sallamarsu dubu takwas aka basu, hakan ba ƙaramin sosa ran Mutallab yayi ba ganin asarar daya tabka ta kayansa da aka ɗauke yanzu kumab anwafce masu har dubu biyu cikin sallamarsu, Baice komai ba duk da haka ya saka kuɗinsa aljihu sannan yayi shigewarsa sauran inda yake aiki, bai tashi ba sai kusan isha'i ya shiga can cikin kasuwa inda yake sarin gwanjo yaje yay na dubu Arba'in, wajen mai abinci yafara tsayawa yaci sannan ya ƙarasa gaban wata doka da yaga anbuɗe ya siyawa Afrah pant da breziya dan ya lura yadda take yawo kamar tana da buƙatar su, tunanin siyawa Jiddah yayi sai ya tuna ai ita tanada mahaifiya ta siya mata, masu kyau ya tsintar mata duk da bashida tabbacin zasuyi mata ko bazasuyi ba! Yatsaya shago yasiya mata brush da sabulu da pad sannan ya ɗora kayansa akansa ya nufi gida, Ganin uwar asarar da ya tafka yau ga ɓatan kayansa ga ragin kusan dubu uku da Alhaji yayi masa sai yacewa mai Napep ya ajiyeshi nan kasansu ya ƙarasa takowa aƙasa duk da nisan dake tsakaninsa da gida, Amma saboda yanzu ya riga daya saba bayajin tafiyar ko kaɗan, Ko da yakaraso baƙin gate din yaya Jamil yagani da abokanansa saman motcinsu na lfarma suna fira, sauke kayan yayi yace "Barka da yamma ya Jamil". Sannan yawuce abunsa duk suka rakasa da idanuwa, ɗaya daga cikinsu ne ya kalli Jamil yace "wannan fa! Hala dan aikin gidanku ne dubeshi ɗan Allah wani ƙazami tmeye ya ɗauki maku a wancan ruɓaɓɓen buhun?" Dariya ya jamil yayi yace ku manta guz wai ƙanena ne a haka, suka sake tuntsure masa da dariya, Murmushi Mutallab kawai dake jiyosu yayi ya shigewarsa ɓangarensa ya ajiye kayansa gefe guda, sabulun da yazo dasu da omo ya ɗauko ya kwaso kayansa ba tare da yaji gajiya ba ya shiga wankewa ganin haka mai gadinsu ya taso ya nufo wajen yana cewa, "Haba ranka yadade da kanka? Ko zaka riƙa kawo sai na dinga wanke maka tunda kaga bana komai" Tunani yazowa Mutallab sai yace, "To anawa zaka dinga wanke mun?"
"To gaskiya zan faɗa maka ranka ya daɗe a kyauta zan riƙa yimaka don bazan iya karɓar kuɗi ka ba mai sunan manya". Murmushi Mutallab yayi don shi kama a yanzu yasan yanda jiki ke wahala wajen neman halaliyarsa don haka yace, "A'a kaga baza muyi haka, duk set ɗaya zan riƙa biyanka Naira ashirin idan ka wanke mun kai ma ka samu karage wasu abubuwan".
"Baza ayi haka ba to kabada Naira 10 dai ko tunda kaga ba siyan ruwa muke ba kuma kai zaka bada sabulunka".
"To Shikenan nagode". Da haka yasa hannu ya tayasa wankin sunaci gaba da firarsu har suka gama yayi masa godiya sannan Mutallab yashiga daga ciki yayi wanka yayi sallah ganin karfe takwas tara na dare yasashi fitowa kofar bangaren nasu daga nisa ya hango Afrah da littafan ta ta tawo, zama tayi kusa da daddumarsa suka shiga karatu sai da ya koya mata assignment ɗinta sanna yashiga kara mata karatun kur'ani cikin sautin muryarsa mai shiga rai itama tana maimaitawa yana kara mata, fitowar Abba kenan dan zuwa ɗakin Mutallab ɗin yagaya masa gobe yazo ya gyra masa daƙinsa dan yagaji da kazantar matan nasa gashi yacewa Jamil yazo yayi yace masa yanada aikin yi, jin yadda suke karatun shi da ƴar uwarsa sai da zuciyar Abba ta taɓu. Sautin muryar Abba ce ta sasu dakatawa yana faɗin, "kai Mutallab damab bakada mutunci? Nace bakada ta ido? Yar'uwar taka ita kadai zaka tasa gaba kadinga koya mata karatu? Wai kaima ka iya ƴan ubanci? Me isa zuciyarka batada kyau ne? Ke kuma Afrah me yasa bakya kirawo Jiddah idan zaki zo kuyi tare? Dayake kema kin iya munafurcin ko?". Afrah da ayanzu tafara jin haushin abinda Abban nasu keyi tashiga kumbure kumbure Mutallab yace, "Abba kayi haƙuri zan dinga kiransu bansan sunaso ba". Umma da ihun faɗa da Abba keyi yafito da ita da Aunty amarya tace, "Gwara dai da kayi masa magana ko yafi jin taka? Yaran nan dai Allah yariga ya haɗasu babu wanda zai raba uba ɗaya ai ba wasa bane, haka yakeyi ba tun yau ba shiyasa Afrah duk fashinta na makaranta bata taɓa ɗaukan ƙasa da ta ɗaya ba saboda ashe yana sata loko yana koyamata". Anty amarya tayi caraf tace, "Kuma fa yana sane da walid baya gane karatu amma ɓakin hali yasa bazai iya haɗawa yakoyar dasu gabaɗaya ba" Kallonsa Abba yayi yace, "Daga yanzu kadinga yimasu su duka ai kaima ni nabiya maka kuɗin da kayi karatun ko ba haka ba?"
"Hakane Abba kayi hakuri duka zamu dingayi daga yau". Umma tayi murmushi tana jin daɗi daga ƙarshe da zai ƙare tamkar bawa agidan tunda zai zama teacher ɗin yaransu, takalli Abba haɗe da cewa, "Abbansu sai asamu asiyo musu chair da board ai ko?"
"Eh Gobe da safe sai asiyo kai kuma sai ka kiyaye". Yawuce ba tare da yayi masa maganar data fito dashi wajensa ba, dariya umma tasaka haɗe da cewa, "wa yaga teacher ba salary." Afrah zatayi magana yace, "tashi kije ki kwanta Afrah ba komai" har zata wuce ya tuna da kayan daya siyo mata daya ɓoye a gefe ya kirata ya ɗauko ya miƙata, karɓa tayi ta shiga yimasa godiya tana ganin abinda ke ciki takasa ƙarasa godiyar saboda kunya ta wuce cikin gida da gudu shi kuma yasa mata dariya don dama yasan hakan zata faru indai Afrah ce,
Ɗakinsa ya nufa yana shiga ya tadda wayansa na ƙara dubawa yayi yaga Aryan ne ke kira, sai daya nemi gefen katifarsa ya zauna sannan ya ɗaya haɗe dayin sallama, "hello MAM". Aryan dake kwance saman kujera a palourn Ummie yafaɗa idanuwansa arufe yana tunano fuskar Afrah da yau tunaninta ya hanashi shaƙat a office, Mutallab ya amsa masa da, "Na'am Aryan ya kuke yasu Ummie?"
"Lafiya ƙalau gatanan ita tace sai nakira mata ɗanta taji lafiyarsa". Murmushi mutallab yayi yace, "kafaɗawa Ummina ina nan lafiya kalau ina fatan itama tana lafiya?" Kasancewar Aryan ya miƙawa Ummie wayar sai yaji tace,
"Lafiya kalau nake Mutallab hop dai komai na tafiya normal yanzu?"
"Eh Ummie kusan hakan sai ɗan abinda ba'a rasa ba".
"To kaci gaba da haƙuri watarana komai zai zama labari, kada kuma ka kosa da yiwa mahaifinka biyayya in sha Allahu komai zaizo ƙarshe, ubangiji Allah yayi maku albarka".
"Amin Ummie In sha Allahu zan ɗauki duk shawarwarin da kika bani kuma zanyi aiki dasu Allah yaƙara miki lafiya".
"To madallah Amin sai da safe ka gaida ƴan uwan naka?"
"Zasu ji" Muryar Aryan ɗaya karɓi wayar yaji yana cewa
"MAM yajikin Afrah?"
"Haba ai Afrah ta ware tuni, ni narasa ina takoyo wannan ƙulafucin nata tare da saka abu arai haka, bansan ya zamuyi da ita ba idan zatayi aure?"
"Ɗaukarka zamuyi muhaɗa da ita mubawa mijin gaba ɗaya". Dariya Mutallab ya saka sosai haɗe da cewa, "Angaisheku masu ƙanwa, kace kawai na shirya zama ɗan zaman ɗakin Afrah?" Shima Aryan yasa dariya haɗe da cewa, "Ƙwarai da gaske amma kayi addu'a Allah yasa ba nibane don in nine bazan lamunci hakan ba ka takura mu, ina take ne mu gaisa". Mutallab da bai dauke maganar komai ba yace, "yanzun nan ta shiga gida mun gama karatu sai dai gobe".
"To Allah yakaimu lafiya, dan Allah adinga koyamata sosai yadda zata gane kada kuma a wahalar da ita our humble teacher." Murmhshi MAM yayi tare da cewa, "Indai wannan kalmar ce anrigaka, zaka ma iya ƙarawa da cewa teacher with out salary". Suka sake sa dariya sannan sukayi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 54