Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tare da juyawa yana sake ba Alhaji Tanimu haƙuri, shi kuwa Mutallab bayan sun gama wayar ɗaukar ruwan daya saya ya wanke hannunsa yau sannan yasha yabar wajen yanufi shagon Alhaji Tanimu, yana zuwa Idris ya taso da sauri ya riƙo hannunsa haɗe da cewa, "muje kafara ba Alhaji haƙuri sannan muyi aikin dan naga ya hasala sosai". Ba musu Mutallab ya bishi ya gaida Alhaji Tanimu da sai faman cika yakeyi yana batsewa dan abu kaɗan yake jira Mutallab ɗin yayi yaci masa mutunci ya koresa, bai amsa ba amma duk da haka Mutallab ya ɗan russuna gabansa haɗe da cewa, "Kayi haƙuri Alhaji bansan da zuwan customers ɗin ba shiyasa natafi wajen wani aikin ganin ba wani aikin da zanyi a lokacin". Hohoho ina wuta Alhaji Tanimu ya kaɗa Mutallab ya balbalesa da masifa hadda cewa wai yana yimasa muguwar fatar rashin customers aniyarsa ta bishi, aiki ne dai tunda zari yayi masa yawa yay wannan yay wancan har yakai baida lokacin tsayawa yayi masa nashi aikin a shago yana nema yakore masa customers to yatafi ya sallameshi baya son ya sake leƙo masa koda abakin shagonsa ne, haƙuri Mutallab yafara ƙoƙarin bashi cikin daka tsawa ya nuna masa hanyar fita shagon yana cewa, "Bana son ban haƙurinka kawai kafitar mun daga shago kada na sake ganinka tunda bakasan arziƙi ba, kuma wlh ta Allah bazaka taɓa zuwa kace zaka gini arziki ba dan wannan sana'ar tawa gada nayi naci gaba da bunƙasata har na zama haka, shine kai da kazo jiya kace kana so kafini tako halin ƙaƙa".              (Ikon Allah! Kai kuwa Alhaji Tanimu arziƙinnan ba Allah ke rabashi ba da kake wannan tunanin har kace zaka koresa dan kada yazo yafika arziƙi?🤔 Gaskiya wasu mutanen sam basa da man kai😓). Kasa cewa komai Mutallab yayi duba da yadda yaga Alhajin yana wulaƙantashi gaban mutane har suna neman taruwa, ɗan haka sai kawai ya juya yafice masa daga shagonsa kamar yanda ya buƙata, Idris ne ya tsaya yana tayiwa Alhaji Tanimu magiya da ban haƙuri amma yayi banza dashi, dole shima ya haƙura ya taso yabi bayan Mutallab da gabaɗaya zuciyarsa tagama cunkushewa da ɓacin ran baƙaƙen maganganun da Alhaji Tanimu ya faffaɗa masa sai kace wanda ke jiraye dashi, don dai ya tabbata wannan ɗan laifin daya aikata bai isa yasa Alhaji yayi masa irin wannan wulaƙancin a abainar jama'a, #Mutallab Asad #Tagwaye Biyar #Billy s fari #Nana Diso.   SHAFI NA ASHIRIN DA BIYAR. *MUTALLAB ASAD*      Arewabook:- billysfari       Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.   *RUBUTUN ƳAN TAGWAYE BIYAR.* NA *NANA DISO** & *BILLY S FARI* ____Darasi Na HUDU____ *MAGANIN KARIN GIRMAN NONO* GARIN ALKAMA GWANGWNI 2 GARIN WAKEN SUYA GWANGWANI 2 GARIN DANYAR FARAR SHINKAFA GWANGWANI 2 SUKARI GWANGWANI DAYA *KI HADESU KIDINGA SHA DA MADARA KO NONO KO KIDAMA KAMAR KUNU*. _____ Sai da Mutallab yamiƙe zaune yana dafe kansa sannan yace, "Am sorry Aryan daƙyar idan zan iya zuwa, yanzu haka ina gida zuciyata babu daɗi ko ƙadan na dawo gida nasamu kuɗinnan da nake baka labari ina tarawa saboda wani buri dana barwa zuciyata na samu anfasa bankin gabaɗaya ankwashemun su". "What! Innalillahi an kwashe fa kace? Garin yaya MAM? Hazbunallahu waniimal wakeel, Yanzu wai kana nufin bankin aka fasa aka kwashe maka kuɗin daka wahala da zufanka saboda Allah? Wannan abu gaskiya yafara yawa MAM yakamata ka ɗauki mataki wannan ai mugunta ce da zalunci". Aryan yafada cikin ɓaci rai ɗan abun ya matuƙar ƙona masa rai, Mutallab yayi Murmushin da yafi kuka ciwo haɗe da cewa, "To na ɗauki mataki wa wa Aryan? Su wa kake so na zarga? Bayan wanda duk suka shiga daƙin jinina". " Hmmm wani jinin fa yafi guba MAM! Am sorry amma baka gani ko wannan shashan yayan naka ne Jamil ko kuma..." Bai ƙarara ba Mutallab yace, "Koma waye na riga nabarwa Allah Aryan yana ji kuma yana gani, na ambaci sunansa domin ya kawo Mani gudun nawa da kuma ɗauki acikin lamarina, ɗan haka mubar zancen kawai". "Shikenan, amma kodai waye Allah yasaka mana dan wallahi BAZAMU yafe ba, guminka ne fa". "Ba komai, Allah yayi mani wata lafiyar" "Amin, zan shigo da daddaren daman yau akayimuna albashi, zan baka 100k ɗin kayi wani abun dasu da zai taimaka maka ni kuma sai nayi amfani da 80k ɗin." Sai da Mutallab yayi Murmushin jindadin kalaman aminin nasa kafin yace, "A'a wallahi bazan karɓa Aryan, kulawarka kaɗai da kasancewarsa agefena aduk lokacin da nake acikin damuwa yawadatar, Allah dai yadda mana nagode sosai aminina". Shiru Aryan yay Dan baiji daɗin saurin rantsuwar da Mutallab yayi ba kafin daga bisani yace, "What a friend's mean MAM? Gaskiya banji daɗin wannan rantsuwar da kayi ba dan ni a gurbin ɗan uwama nake kallonka ba aboki ba". "Afuwan kayi haƙuri". "Shikenan zan shigo da daren but yanada kyau kayi bincike ko dan gaba". "Ok in Sha Allah zanyi hakan". Mutallab ya faɗa bawai dan zai yi ba ɗin sai don yakawar da zancen, yaƙare maganar yana kashe wayar yana sake jin zafin faruwar al'amarin aransa tare da gogewa hawayen da suka sake zubo masa karo na biyu a fuska, Ringing wayar tasa ta sakeyi a yana dubawa yaga shiga Idris ne, wannan tashin hankalin gabaɗaya ma yasashi mantawa da zancen da sukayi da kuma abinda ya maidoshi gidan, yana ɗagawa Idris yace, "Wai ina ka shige ne kaganni nan inata faman dubaka cikin kasuwar nan banganka ba, gashinan nasamo mana wani dako da zamu samu alkhairi sosai". Mutallab da yaji gabaɗaya ma dakon yafice masa arai yace, "Kawai kayi Idris ni ina gida ma bazan iya fitowa ba". "Subhanallahi wani abun ne ya faru Mutallab ko dai har yanzu abunda Alhaji ne yayi  maka ya kasa fice maka azuciya? To tsakani da Allah bari na faɗa maka gaskiya, ita fa kasuwa tagaji hakan wataran tazo maka da daɗi wataran kuma tazo maka da akasin hakan, kuma wannan abun daya faru kaɗan daga cikin ƙalubalen kasuwa ne, dan haka kada ka sawa kanka damuwa kowa rabonsa zai samu kuma ai kansa yayiwa tunda Allah ya baka rai da lafiya zaka iya zuwa duk inda kake son aiki ƙanena". "Ko ɗaya ba wannan bane Idris, kuɗin da kabani shawara akan na tara ne fa ko dana dawo gida na isko a ɗauke babu ko sisi kuma fa har cikin ɗakina akazo aka fasa bankin aka ɗauke". Sosai shima Idris ya girgiza da zancen tunda yasan tsawon lokacin daya ɗauka yana asusun, amma don ya karfafa masa guiwa yace,  "kayi hakuri Mutallab wannan ma jarabawace da Allah yayi alƙawarin yiwa masu imani, in Sha Allah Allah zai musanya maka da lunkinsa, wanda ya ɗauka shi kuma kansa yayiwa, don Allah idan zaka iya kadawo muyi aikin nan zamu samu alkhairi ciki, ka jure mana saboda kafara dauƙar hanya cimma nasara. Kakata tana yawan gayamin cewa aduk lokacin da Allah ya karɓe maka wani abu daga hannunka to ka kyautata masa zaton cewa yayi hakan ne dan yabaka wanda yafishi, kayi haƙuri kataso idan mungama aikin sai mu tattauna yanda zamu ɓullowa lamarin anan gaba". Cikin jin dadin maganganun sa Mutallab yaji wani ƙwarin guiwa ya shigesa dan haka ya amsa masa da gashinan zuwa tare da miƙewa bayan ya kashe wayar ya jefa cikin aljihu, sai daya shiga toilet ya rage cikinsa yayi arwala sannan ya haɗe kayan gwanjonsa guri ɗaya ya ɗauka yafice daga gidan zuwa kasuwa, yanzu in banda Naira dubu ɗayar dake jikinsa bashida ko sisi gida da waje, ganin ana jiransa ya sakashi shiga abun hawa dan ya isa kasuwar dawuri, yana isa yakira Idris awaya ya sanar masa inda yake sannan ya ajiye gwanjonsa inda ya saba ajiyarsu  ya shiga masallaci yayi sallar azahar daga nan kuma suka haɗe suka tafi gurin mutumin da zasu yiwa aiki, sun ɗauki lokaci sunayi har akayi sallar la'asar basu gama ba, da yake wannan shagon na ƴan china ne daya taɓa ɗaukar wa Alhaji Tanimu kayi suka lodama wani da yayi sayayya shima a shagon kayansa a trelar, suna gamawa bayan ya sallamesu matar da itace shugabar wajen tace zata ɗauki Mutallab aiki, ɗan ita tun ganin farkonta dashi taji tana da sha'awar ɗaukar da aiki, amma da tayi bincike taji Alhaji Tanimu yake yiwa aiki a shagonsa sai ta haƙura, ɗazu ne take ji ana fira cikin yaran da suka zo ɗaukarwa wani alhajin kaya cewa wai yakori mutallab, shine fa tasa aka nemo mata Idris don tasa atare suke ta haɗa su da wannan alhakin da suka gama yiwa aiki, bayan sun kammala ta bijirowa Mutallab da buƙatarta, abunda dukansu daga shi har Idris basu taɓa kawowa aransu ba saboda ma'aikatan dake yimata aiki na musamman ne wasu ma farar fata ne ɗaiɗaiku ne baƙaƙe daga cikinsu, kuma suna jin labarin irin kyautatawar da takeyiwa ma'aikatan musamman wuɗanda suka riƙe mata amana, cikin garin hausarta take ce musu taji abinda yafaru ne tsakaninsa da Alhaji Tanimu shiyasa take so ta taimakesa in zai iya yimata aiki kuma ya rike mata amana to ita batada matsala in sha Allahu zaiji daɗin aiki da'ita, da farko tsoro Mutallab yaji ya kasa amsa mata har sai da Idris ya nuna masa wannan wani musayar alkhairi ne da yake faɗa masa ɗazu tun dawuri Allah yafara yimasa, ɗan haka kawai ya yarda dama ce babba Allah yayi masa kada yayi wasa da ita, nan ya faɗa mata cewa ya amince cikin harshen turancin daya fahimci tana ganewa sama da Hausa, wanda ba Idris ba hatta ita kanta mr. Jennifer sai da tayi mamakin yanda zallar turancin kefita a bakinsa, saboda a kallo ɗaya bazaka yimasa tsammanin ya iya ba tunda bai taɓa yiba, asali ma yanayin shigar da yakeyi tasa yakoma tamkar irin Fulanin nan da zaka iya cewa ko taho kasheni basu sani ba, wannan ya sake ƙarara mata cewa tabbas zai iya yimata aikin da take so ba tare da wani haifi ba tare da bata natsuwa da kuma kwantar mata da hankali akansa, sai dai ya faɗa mata cewa zai dinga yimata aikinta da safe amma zuwa 12 na rana shima zai je ya kasa kayansa na gwanjo da yake sayarwa zuwa ƙarfe huɗu sai ya dawo, koyon ɗinkinsa kuma ya barshi sai irin bayan sallar isha har zuwa ƙarfe goman dare, ta amince da tsarin daya faɗa mata saboda tana son aiki dashi sosai wanda atake tace masa idan yana buƙata anan gefen ƙaton shagon nata ma tabashi dama yakasa kayansa ba tada damuwa da hakan indai zai mata aikinta kuma shima ya amince da hakan. Bayan kwana biyu Mutallab ya fara zuwa aiki inda ya ɗan fara sarauta shiga saboda ganin fuskokin manyan mutanen da zai riƙa mu'amala dasu, bayan haka ma akwai kaya na usamman da yaran wajen ke amfani dasu amma da yake lokacin daya je suna magana ya sanar da ita cewa ai business administration ya karanta kawai sai ta bashi muƙamin cashier mai kula da ƙididdigar kayan da suka shiga da fita a shagon, ya matuƙar jin dadin hakan tare da yimata godiya inda yafara yimata aiki tuƙuru, cikin ɗan ƙanƙanen lokacin da bai haura sati ɗaya ba tafara ganin cigaba da sauyi sosai a shagon nata don ko kaɗan Mutallab bai yarda da maguɗi ko cin hanci da yaudara ba acikin aikinsa, kafin kace me cikin wata ɗaya mutallab ya maida lunkin kuɗaɗen da aka sace masa, dama kuma tuni washe gari da akayi awa satar Afrah da Jalil sun fashe nasu bankin da suke tari aciki gaban Mutallab ɗin da mamakinsu gal ya cika masa zuciya, ana ƙidaya kuɗin su kai dubu sittin har da wani abu suka miƙa masa wai yaƙara yaja jari, yaji daɗi sosai tare da kara jin ƙaunar ƴan uwan nasa wanda atake bisa shawarar Idris yaje ya buɗe masu account su duka, ya kuma zuba masu kuɗaɗensu aciki ba tare da sun sani ba kasancewar yariga daya samu wata madafar. ************ A ɓangaren mahaifiyar Meenal kuwa duk wani abu da zasu iya na sharri ko makirci akan Mommy tabar gidan sunyi amma fa abun ya faskara, sun gwada zuwa wajen malamai amma a sanar dasu cewa duk abinda zasuyi bazasu taɓa iya galaba akantaba saboda a tsaye take ga ibada, dole sukayi haƙuri ganin Kamal ya dawo suka fara tunanin janyowa ajiki dan ƙarara masu aikin da suke ganin Meenal takasa, yau ma tunda sassafe Kamal yafito shinda Meenal Wai zasu je dubo Mahma ba lafiya, sun tsaya sayen fruit akan titi wani tsoho yazo yana bara agabansu, Kamal bai kulasa ba Meenal kuma dama latsar wayarta takeyi suna chart da Nancy dake cemata zasu shigo mata yau akwai story, suna gama sayayyar ta juyo da nufin komawa cikin mota sukayi karo da tsohon nan mai bara dake ta faman roƙonsu tamkar zai shige cikinsu har sai da wayar Meenal iPhone 16proma tafaɗi glass ɗin ta na gaba da baya duka ya fashe, ai kuwa tana ɗagowa ta kwashe tsohon nan mari har sau biyu haɗe da cukuikuye masa wuya tana faɗin sai ya biyata wayarta, take mutane suka fara taruwa ana ba Meenal hakuri amma taƙi haƙura sai zagin tsohon da duka kansa furfura ne takeyi, Kamal kuwa na a mota yay zamansa a cewarsa daidai take tunda tanada feedom akan haƙkinta, sai da yaga abun yayi yawa sannan yafito ya nufi wajen yana bata haƙuri amma shima taki saurararsa don tsabar masifa har ɗan kwalin kanta ya cire, janta yakeyi tana sake komawa tana cukumo wuyan tsohon tana jijjiga, hakan yasa Kamal sa hannuwa ya tallabota tana shusshura ƙafafuwan cike da son kaima tsohon ɗaya gama galabaita shuri, Mutallab dake cikin mota zaune shi da Aryan suna jiran motar su Kamal data tare masu tabasu hanya ya tsareta da idanuwa, ƙamari dai kullum yarinyar nance da bazai manta fuskarta ba a waccan ranar yauma cikin wata banzar shiga da zai iya rantsewa ƙara shigar ranar akan ta yau ɗin, abun ban haushin ma yanda yaga wani ƙato ya cicciɓeta tana faman zillewa, wanda yana kallo dakyau kamar ma da gayya yaron ke kai hannayensa aƙasan ƙirjinta yana janta zuwa mota, iska ya ja a baki haɗe da kauda kai gefe yana jin wata irin tsanar yarinyar a ransa, yanzu haka ji yakeyi tamkar yaje daga ita har yaron ya rufe su da duka, yaja tsaki yafi aƙirga har sai da Aryan ya juyo ya tambayesa ko lafiya yayi masa banza tunda baisan me zai ce masa ba akan abinda bai shafesa ba. Daƙyar da suɗin goshi Kamal ya samu ya tura Meenal a cikin mota ya dawo ya kwashe mata ɗan kwalinta data zubar da wayar yakai mata sannan ya zagaya ya buɗe yashiga shima yaja motar sukabar wajen... #Mutallab Asad #Tagwaye Biyar #Billy S Fari #Nana Diso *MUTALLAB ASAD* *PAID BOOK #500* *TAGWAYE BIYAR.* NA *NANA DISO** & *BILLY S FARI* 26. Bayan sati biyu da faruwar haka sai gashi kuma sun sake haɗuwa da Meenal ɗin a wajen wata dinner abokin Aryan da aka gayyacesu, bai so zuwa ba amma matsayin Aryan a wurinsa ya shi shiryawa suka je, can gefe ya samu waje acikin hall ɗin ya zauna yana kallon bidirin da akeyi, can d.j ya saki wani sauti na abokanan amarya, a take ya hango waccan yarinyar da takeyiwa laƙabi da fitsararriya tsakiyar filin, yau kam kace ne a jikinta ɗinkin doguwar riga amma gabaɗaya ya matseta ga wata tsaguwa da akayiwa rigar a baya, rabin ƙirjinta kuwa duka a buɗe yake, yayin da hannuwanta da saman ƙirjinta basuda maraba da abuɗe suke suma saboda net ne aka ƙawata wajen dasu tasha kitson attach sosai an zuboshi abaya sai kwasar rawa takeyi ita da su Nancy da sauran abokananta, lumshe idanuwa yayi yana dafe goshinsa haɗe da cewa, "yau ma dai ita ɗin ce anan? Hazbunallahu waniimal".  Tunda ya noce kansa ƙasa yana shafa goshinsa cike da takaici bai ɗago ba har sai da yaji sautin kidan ya tsaya, wata game aka fara gudanarwa tsakanin maza da mata abokanan ango da amarya zasuyi, wacce mazane zasu fara acikin minti ɗaya kacal ake so kowane yaje ya ɗauko jikkar duk wanda ya samu acikin taron ƴan matan, wanda ya kasa kawowa kuma za'a ciwa tara, bayan sun gama aka dawo kan mata, su kuma cikin minti ɗaya ake so su ciro duk hular da suka samu akan abokanan ango, duk wacce ta kasa dole tabiya tara itama, kasancewar ɗinkin dake jikin Meenal bazai iya bata damar yin gudu ba yasa har ƴan matan suka gama ciro hulunan akan samarin ita bata samu wanda zata ciro tashi ba duk duka a cire masu hulunan ana dariya, kamar ance ta juya gefenta inda Mutallab yake zaune ai kuwa tanufi wajensa, kai tsaye ba tare daya tarar ba sai dai yaji hannunta akan hularsa tana ƙoƙarin cirewa, hannu yasa ya dafe hularsa yana watsa mata wani mugun kallo dake cike da tsana, ba tare da Meenal ta damu ba tayi ƙoƙarin cire hular tasa cikin ƙarfi, takaici da tsanar mugayen ɗabiun nata yasa bai san lokacin daya mike ba ya turata gefe da ƙarfi har sai da tafaɗi saboda tsinin takalmin dake ƙafarta, cikin ɓacin rai yake nunata da hannu kafin yace, "Sau ɗaya dai kiyi ƙoƙarin sauya halayenki da wannan muguwar shigar da kikeyi kafin ranar nadama tazo maki". Yana gamawa ya fice daga hall ɗin gabaɗaya ita kuma aka saka mata dariya, ganin abun zai koma wani abun tashin hankali yasa dj ya tada sauti don maido hankalin mutane ga abinda ya tarasu wajen. Meenal kuwa binsa da kallo tayi har ya fice duk da raɗaɗin da take ji a kafarta don kuwa ta gwabce, bata fahimci akan ba sai da tayi yunƙurin tashi takasa, kuka ta saka sai da su Nancy suka riƙata bayan angama dinner ɗin suka kaita gida, Mutallab kuwa dama cikin motar Aryan ya koma ya shige yaci gaba da latsar wayarsa da ayanzu ya canza tunda ba laifi yana samu, yana zaune Aryan yazo ya buɗe motar ya shigo tare da kallonsa yace, "Haba MAM! meka aikatawa yarinyar mutane haka? Abun nan fa is just a game Amma kazo banda yarfata da kayi ka goce mata ƙafa". Mutallaf bai tankasa ba har ya ƙaraci surutunsa ya gama, dole ya tashi motar suka wuce suna ba tare daya sake cemasa komai ba.... Meenal kuwa koda takoma gida har ƙafarta tafara kumbura, Kamal ya ɗauketa ya kaita asibiti aka gyaro mata tasha kuka har ta godema Allah, Mommy kam sannu kawai ta haɗata da ita tare da addu'ar Allah yabata lafiya, Dady baya nan yayi tafiya don haka rakin nata da shagwaɓar duk sai suka koma akan yayan nata shi kuma yana faman lallaɓata tare da manneta ajikinsa ɗan hakan nayi masa daɗi, sosai wannan ɗabiar ke ciwa Mommy rai amma ba yanda ta iya ta zuba masu idanuwa, ranar kam a ɗakin Meenal Kamal ya kwana da sunan jinya ba tare da Mommy ta sani ba, washe gari da Dady ya dawo ya tadda halin da Shalelen nasa ke ciki sunga ruwan masifa da tashin hankali, ɗan cewa yayi a nemo masa ko ɗan gidan uban waye sai ya dauresa, Mommy kuma ya balbaleta da faɗa akan me tun jiya bata kirasa tasanar dashi abinda ke faruwa da ƴar tasa ba tayi shiru, ita dai bata rabashi da guda ba har ya gama ta bashi haƙuri tamiƙe ta shige ɗakinta. Sunan hall ɗin da akayi dinner ɗin Dady ya tambayeta tafaɗa masa, tana ganin ya janyo waya ta turo baki haɗe da karɓe wayar tace, "Me zakayi Dady?" "Police zankira suje su bincika agano mani kowaye yaron a ɗauke mani shi, wannan abun ai cin zalin ne da rashin sanin darajar ɗan adam yayi maki". A shagwaɓe ta kwantar da kanta saman kafaɗar Dady tana cewa, "A'a Dady ka ƙyalesa, laifin ai nawa ne". Da mamaki Dady ya kalleta haɗe da cewa, "laifinki Babyn Dady? Me kikayi masa?" Tura kanta tayi cikin jikinsa cike da jin kunya tace, "Nidai Dady kada kace komai nace a ƙyalesa dan gaskiya ina sonsa". Taƙare zancen tana sake haɗawa da rufe fuskarta da tafin hannunta, murmushi Dady ya saki haɗe da cewa, "Ahhh lallai babyna ta girma, ai sai ki faɗa mani faɗan na soyayya ne, waye shi ɗan gidan waye?" "Dady nima ban sani ba, yau nafara ganinsa kuma ni shi nake so na aura". Buɗe baki dady yayi haɗe dayin dariya kafin yace, "Allah babyna da gaske kikeyi?" Ta ɗaya masa kai tana wasa da yatsun hannuwanta. Shafa kanta Dady yayi haɗe da cewa, "To ki kwantar da hankalinki ki gano ko ɗan gidan waye shi, kin auresa kin gama in Sha Allah". Hugging Dady Meenal tayi cike da farinciki tace, "thank you Dady you're d best ever". Yayi murmushi sannan yamiƙe ya wuce ɗakinsa cike da mamakin yau Meenal ce ke furta kalmar aure da bakinta? Ai kuwa zai yi alfahari da ganin wannan ranar koya huta da karan tsanar da Mommy ta ɗora mata idan ta tafiyarta ɗakinta. Tun daga wannan ranar Meenal ta bazama neman Mutallab ta hanyar wayoyi bayan ta warke kuma da kanta take binciken inda zata haɗu dashi, kimanin wata huɗu kenan batayi nasarar samun wani ƙwaƙƙwaran bincike akansa ba, lambar wayarsa kaɗai ta iya samu hannun angon da akayi bikinshi ranar shima kuma Aryan yakira yace ya bashi lambar abokinsa, baiyi wani tunanin komai ba ya bayar ƙasar Tata takirata ta amsa saboda yanda duk tabi ta takurasu ta uzzura masu da kira.... Ba tare da wata kwanakwana ba cike da farinciki Meenal takira lambarsa kai tsaye, lokacin suna jera kaya a sabon shagonsa daya buɗe na kayan abinci da taimakon mr. Jannifer data yarje zata riƙa bashi komai yana dubawa aciki yana fitar mata da kuɗi ta shi kuma yana cire ribarsa, kai tsaye Meenal ta gabatar masa da kanta ba tare data ɓoye masa kowaye ita ba yanda zai ganota ta kuma shaida masa tunda ta ɗora idanuwanta akansa lokacin da yakeyi mata masifa wajen dinner taji duk duniya ba namijin da take so sama dashi kuma ita ba soyayya kaɗai take son shi da ita ba aurenshi take so tayi, dariya ta bawa Mutallab sosai har yana samun wajen zama jin soki bututun da takeyi masa, ɗan gabaɗaya ma yarasa me zai ce mata jin yanda take jero magana sai kace ita ɗin ce namiji shi kuma mace, sai da yayi dariyarsa mai isarshi sannan yace, "Your not serious kije kiga likita yarinya". Sannan ya kashe wayarsa yana jan dogon tsaki, ɗan a yanda yake jin tsanarta a ransa baya tunanin koda duka matan duniya zasu ƙare zai iya aurenta. Da wannan tunanin ya watsar da zancenta a gefe yaci gaba da harkokinsa, inda tuni arziki ya fara buɗe masa a ta ɗaya ɓangaren kuma yana ci gaba da koyon ɗunkinsa, yanzu haka ko bai zo cikin sahu na farko ba acikin ƙwararrin maɗunkan da suka ƙware a ɗunkunan na maza to zai zo na biyu ko na uku, nan take kuma ya sake buɗe wani shagon ɗunki ya sayi keken ɗunki guda uku ya zuba, lokacin Jalil ya gama makaranta don haka sai ya kawoshi shagon yana koya masa ɗinkin shima idan ya samu lokaci, wani lokacin kuma sai ya saka aminta cin yaransa guda biyu daya saka a shagon, su suke amfani da keken ɗinkin guda biyu, ɗayar kuma shi yake hawanta, da Jalil yafara iya ɗinkin sai shima ya sawo mata tashi keken yana hawa a hankali har ya iya. A ɓangaren saida gwanjo ma bai saki sana'ar ba ganin yanda ta karɓesa, dan haka sai yakama hayar wani shago yana ɗauko dila-dila ana kwancewa cikin farashi mai sauƙi, inda nan take ya nemi Idris da su haɗa hannun jari wajen ɗauko gwanjona inyaso sai su saka yaron da zai rika kula masu da shagon, Idris ya amince sai dai yaroƙesa da yabarshi shi ya zauna ya tsare shagon da kansa tunda har yanzu shi ba wata cikakkiyar sana'a yake da ita ba. Dama duk wanda ya nema zai samu kuma sana'a bataga raggo kamar yanda hausawa akoda yaushe suke faɗa cewa babu maraya sai rago, dan a yanzu Mutallab ya tsaya da ƙafafuwan sa har yana taimakawa wasu suma kamar yanda mr. Jennifer ta taimakesa, a ɓangaren Meenal

Chapter 16 of 54