batayi karatun addini ba da tabbas kuwa sai tayi abunda yafi abunda iyayen nata suke sakatayi "Aicha muyi bakin kasuwa anfi samu acan". Taji má pére ɗin ta ya faɗa. "Ni dai bana son zuwa bakin kasuwa fa ƴan iskane suyita kirana wai naje". "Ke jimun ja'irar yarinya unga nan Aîcha ƙaniyarki nace kinji ko, wai me yasa bakida mutunci Aîcha kike yimani baƙinciki? Wato ke kike korar mani kasuwa, ga dai kyakyawar ɗiya anfani amma kuma mara hankali har ana ce miki kije kina ƙi ko Aicha?"
"Haba má pére haramun ne fa, Allah ko kasuwar da muke shiga ina cuɗanya tsakanina dasu a islamiya ance ba kyau yin haka, musamman macce da namiji balle wanda ba muharraminta ba yakiraka, to so kakeyi naje?".
"Eh Aîcha kije sai me? Ai kuɗi zamu samu".
"Hm'em lalle má pére to wallahi ni bazan je ba da yardar Allah tunda kai kafison kuɗi akaina". tafaɗa wasu hawayen takaici na zubo mata". Tsaki yaja kafin can su ɗan ƙara tafiya suji wani yana faɗin, "ke karɓi wannan ƴar fara kyakkyawa". ya miƙo mata Naira 20 yana wani lashe baki, tsayenta tayi má pére ya turata yana cewa, "jeki karɓi mana Aîcha yau munfito a sa'a kenan!" Harara ta gallawa mutumen kafin tace, "wane Sa'a má pére da Naira 20". Turata ya shiga yi takarɓa tana hawaye haɗe da miƙa hannu zata karɓi kuɗin, ai kuwa mutumin ya riƙo da hannunta yana shasshafawa. Fizge hannunta tayi da sauri tana dallah masa harara tare da cillar da ashirin din tana faɗin, "Allah ya sakamin mugu azzalumi ban yafe ba". Sannan ta nufi inda má pére nata yake, duk yadda yakai gurin tambayarta nawa suka bayar banza tayi masa har sai da ya buga mata sanda sannan tace bai bata komai ba, ai kuwa má pére ya hau bakinsa yanata masifa da ita saman hanya tayi masa banza kamar bata ji ba, Tafiya sukayi mai shegen nisa kamin su isa bakin kasuwa, tun ahanya taji cikinta ya rarake cikin muryar dake nuna ta gaji sosai tace, "Má pére ka kawo in ƙarbo mana tuwo".
"Da muka samu nawa shashasha, ai tunda bakida tausayi Aicha sisi bazan baki ba, kuma ma yaushe muka fito da har zakice yunwa kikeji? Kofa sadaka daya bamu samu ba kinyi mana ɓakin cikin wancan na farkon daya tashi bamu".
Matso ƙwalla tayi haɗe da cewa, "To má pére yanzu da yunwa zan zauna".
"Shi ne daidai ke, kinga idan aka bada sadaka dole kike ki karɓo mana ko dan kisamu kici abinci". Cikin muryar kuka tace, "Ɗan Allah má pére". Banza yayi mata tare da samun waje yayi zamansa, hakan yasa itama tana hawaye ta samu kusa da inda ya zauna ta zauna tana ɗora kanta saman kafaɗarsa hawaye na zubo mata ba tare data damu da ranar dake dukanta ba....
#Mutallab Asad
#Tagwaye Biyar
#Nana Diso
#Billy S Fari
*MUTALLAB ASAD*
*PAID BOOK #500*
*TAGWAYE BIYAR.*
NA
*BILLY S FARI*
&
*NANA DISO*
36.
Kyaleta yayi ya cigaba da kwasowa Afrah sauran tarkacenta zuciyarsa na yimasa wani irin ƙuna, Umma ce Jiddah taje tayowa gulma sai gata tafito daga dakinta dai-dai lokacin da suka sauko ƙasa tana cewa, "A'a har tafiya Afrah babu sallama?" Murmushi Afrah tayi haɗe da cewa, " Umma yanzu dama zan shigo tunda mun kammala haɗa kayan". tafaɗa tana riƙe wasu hawaye baƙin ciki dake son sauko mata, cike da izgilanci Umma tace, "Yau kuma sai cikin Sahara ko? Gaskiya banji daɗin wannan hukuncin da Alhaji yayanke muku ba, haba yara sai kace ƴan riƙo ba haihuwarsa akayi cikin gidan ba? Wannan abu ai yayi tsauri da yawa wallahi, sai dai ya zamuyi tunda muma a ƙarƙashinsa muke kuma bamayi masa mummunan zato ba wataƙil akwai abunda ya hango ko kuma dalilinsa nayin haka! to yanzu sai aurenki daɗa idan mun samu zarahin zuwa ko?" Jalil da ya harzuka zai yi magana Afrah tasake riƙe masa hannu akaro na biyu tana girgiza masa kai hawaye na sauko mata, cikin ɓacin rai ya ƙwace hannunsa yana nunata kamar zai mareta yace, "Sau ɗaya dai kimayar masu da magana ko kyaji sanyi a ranki ba kizauna kina wannan kukan na sakarci ba". Yayi gaba aunsa tare da jan hannunta suka wuce, sai da suka kai bakin ƙofa sannan ya juyo yana kallon tare Umma yace, "Ki godewa Allah da baki taɓa shiga gonata ba har zan bar wannan gidan, da nayi maki abinda baƙin ciki zaisa ki haɗiye zuciya kimutu wallahi". Yaƙare zancen tare da jan hannun Afrah suka ƙarasa ficewa daga cikin palourn, Aunty Amarya dama tana ɗakinta, yau ne karan farko data fara tsorata da lamarin Umma, kuma yasan tabbas idan tafito babu abinda zai hana tausayinsu Afrah yasa ta mayar mata da maganganu, gashi da alama kaɗan maigidan nata ke jiran tayi abu itama yakorata, dan haka dole tayi da gaske wajen ganin batayi wani kuskuren da zaisa Abba yakorata ba har zuwa lokacin da Hajiyarta zata koma wajen bokansu suma, a cewarta hatsabibancin irin na Umma tsaf zata iya sa har su Walid a koresu ba tare data dubi ƙarancin su ba, .Afrah da Jalil kuwa ɓangaren Abba suka nufa suna kawowa yaya Jamil yakawo shima yace kada su shigo su jira har sai yagama magana da mahaifinsa, haka kuwa akayi kusan mintuna talatin kamin kuma yafito yanata dariya saboda zancen da yaji Umma har taje tana faɗawa Abba wai Jalil ya zageta yayi mata rashin kunya, shine abban kecewa ta ƙyaleshi ai ya rigana yagama hukuntasu tunda bar masa gida zasuyi, "Jalil korar ashe har dakai? Kai ƙin..ƙin..ƙin gaskiya abun babu daɗi amma kawai kuyi haƙuri, idan kuɗin da yayan naku ke tutiya dasu sun ƙare kaga cikin sauƙi zai koma dakonsa kai kuma sai ku wuce wajen bara Afrah nayi maka ƴar jagora, gaskiya abunnan zainfa kawo show...." kafin yarufe baki Jalil ya shaƙo wuyansa ya haɗa da gini ya maƙuresa har sai da idanuwansa suka fito yafara kakari yana biɗar taimako Jalil yace, saurin basarwa Jalil yayi daga wannan tunanin da yakeyi na nunawa ya'yan nasa zallar rashin kunyarsa tare da shigewarsa ɗakin Abban ba tare da sunce masa komai ba, "To marar kunya nima zuwa kayi kai mani rashin kunyar? Zaman me kuma zakuyi anan maza kutashi kuwuce bana don ganinku". Abba yafaɗa ganin suna ƙoƙarin neman wuri su zauna, duk da maganganun da yakeyi hakan bai hana Jalil zaunar da Afrah ba shima ya zauna yana kallon mahaifin nasu yace, "gamu to agabanka ka kashemu mana tunda baka don ganinmu, ko kace mutafi Abba ai dai kabari muyi sallama ko? Kuma duk rintsi dai mahaifinmu kake dole muyi maka sallama indai yaran kirki ne mu duk da kafifita wasu ɗaya akanmu ka koremu daga gidanka".
"To naji munyi sallama kutashi kuje". Umma dake gefe ta taɓa baki tare da kallon Abban tace, "A'a Alhaji katsaya ka sauraresu mana".
"Hajiya Umma ba buƙatar hakan ai, mudai zamubi yayanmu kuma ubanmu mutafi, in sha Allah kuma yanda aka koremu sai andawo an nememu" yafaɗa tare da miƙewa yayi ƙofar fita Afrah tabi bayansa, Muryar Umma ta dakatar dashi dake cewa, "To Kadai bi ahankali Jalil dan kuɗin ɗan uwan naku ba'a san daga ina yake samuba ko danfara yafara kokuma kuɗin.." sai kuma tayi shiru tana dafe baki ganin yanda ya juyo yana kallonta cikin wani yanayi na ɓacin rai, sai dai duk da haka fa sai da takai aya tace, "Wai tsoronta kada akama da kai idan takwaɓe". Dariya Jalil ya saki kamar ba shiba har da kama ciki kafin yace, "Hajiya Umma kenan! Yanzu ɗan Allah banda abinki taya ba'a kama Jamil ba kike tunanin za'a kama ya Mutallab ko ni, gaskiya kike asibiti ƙwaƙwalwarki tafara taɓuwa?" Yagama maganar yana dariya tare da ficewa abunsa, ita kanta Afrah sai da tayi murmushi jin maganar da ya Jalil ya mayarwa da Umma, Umma da zuciyarta tayi zafi tace "Kana kallon mara kunyar yaron nan ko Alhaji, har ni yake faɗa wa haka agabanka amma shine bazaka ɗauki mataki ba?"
"kiyi haƙuri tunda dai sun riga sun tafi, yanzu dai muyi magana yaushe ne kika ce masu don Jidda zasu zo kawo kayan lefe nufa nawa Yakamata akashe tunda dai ƴan gidan girmane." Dariya Umma tayi dan dama indai akan zancen kuɗine to za'a gama da ita duk yadda aka ɓata mata rai, saboda haka tana jin yayi zancen nawa za'a kashe tace, "Gobe ne zasu zo kuma inaga ai kuɗin baza su wuce 300k ba tunda kaga har da snacks akeyi kuma a siya kaji tunda harkar girma ce".
"Eh haka ne amma 300k ɗin kinaga zasu isa?"
"To ko kabada da hamsin?"
"Tohm shikenan bari kawai abada 400k ɗin ai yafi". yafaɗa yana miƙewa tare da buɗe wani safe ya ɗauki mata rafar ƴan dubu dubu guda huɗu yamiƙa mata haɗe da kwantawa saman gadon yace bari ya ɗanyi bacci na mintuna kafin anjima yafita.
Mutallab kuwa bayan Jalil ya gama zuba duka kayansu a Boot ɗin mota tafito daga ɗakinsa cikin wata kyalleliyar shadda milk color yana zuba ƙamshi kamar bashi ba, daga Jalil har Afrah tsaye sukayi bauɗe da baki suna kallon ya Mutallab ɗin su da acikin mintuna ya bala'in sauyawa haɗe dayi masu wani irin mugun kwarjini, dama ƴan kayansa da suka kasance na mahaifiyarsu na ɗaki yayi waya da Idris yasa daga kasuwa anturo masa akori kura motar ɗaukar kaya kenan da zata kwashe, yana fitowa yaba masu ɗaukar kayan izinin shiga su kwaso masu duk kayan har na ɗakin Jalil, kyauta mai tsoka yayiwa bana mai gadi dake ji kamar ya ajiye aikin shima ya bisu, amma tunawa da halaccin da Abba yayi masa a shekarun baya kafin ya sauya ya sashi haƙura, lokacin da Mutallab ya ƙaraso gaban motarsa key ya kaɗawa Jalil a fuska saboda yanda ya shagala da kallonsa, cikin ƙwarewa da rashin ji irin nasa wataran ya ɗaya hannu ya buge ƙafa yana cewa, "Yes sir". Duk sukayi murmushi ɗan kana kallonsu kasan dukansu ƙarfin hali ne kawai ne sukeyi akwai babbar damuwa a ƙasan idanuwansa, alama Mutallab yayiwa Afrah ta buɗe baya ta shiga, Jalil kuma ya buɗe gaba gefen driver ya shiga, shi kuma yayi tsaye yana ƙarewa gidan nasu kallo kafin ya shiga ya tayar da motar su wuce, abun mamaki sai sukaga yayi hanyar bayan gidan nasu duk da akwai ƴar tafiya kaɗan, a bakin wani babban gate sukaga yatsaya mai gadin dake bakin ƙofa ya taso ya gaidashi cikin girmamawa sannan ya miƙa masa mukullan cikin gidan tare da komawa ya wangale masu gare suka shiga, baki suka saki dukkansu suna kallon haɗuwar gidan da tsaruwarsa kafin Afrah datakasa hanƙuri tace, "yaya gidan wanene Nan?" Bayan sun firfito cikin motar, Jalil ya nuna mata da key ɗin motar dake hannunsa haɗe da cewa
"Gidan Jalil Asad Mutallab ne". Yaƙare zancen yana murmushi tare da kallon Jalil daya kusa mutuwar tsaye, Afrah kuwa tsalle tayi tace, "wayyo haduwa Masha Allah tabarakallah ya Wai da gaske kakeyi?" Tayi maganar tana kallon Mutallab, lumshe idanuwa yayi ya buɗe yana jinjina mata kai alamun tabbatar mata da haka ne kafin yaci gaba da cewa, "Ban kammala nawa ginin ba shiyasa zaku zauna ana Jalil tunda shi an kammalasa, sai ku zauna da mà tánte Sajida idan ta iso tunda zata kwana biyu kafin takoma, in yaso sai kaje yau kasiyo maku furnitures a saita ɗakunan da zaku zauna, wannan makullin na hannunka kuma dana baka ɗazu kaga waccan accord ɗin?" dake gefe rufe da riga a filin gidan, yaci gaba da cewa, "takace naga zirga-zirgan nan tana maka yawa sai kariƙa amfani da ita". Da hannu ya nuna masu wani babban part can gefe da aketa gini har yanzu zai lunka gidan Jalil ɗin sau biyu har da rabi yace masu shine gidansa da ba'a kammala ba da ciki zasu zauna, wasu hawaye ne suka zubo a fuskar Jalil da tun ɗazu mamaki ya gama kashewa yace, "Me zance maka ya Mutallab? Babban gida da mota Yaya duka wani kaɗai?"
"Ina da wani wanda yafiƙa ne Jalil? Duk da wahalar neman kuɗin nan tare mukeyi dakai, taya kake tunanin zan so kaina nikaɗai nabarka ka wahala a banza? Bazan iya ba wannan kusan duka da guminsa aciki dan haka kama dena cewa na gina maka gida, kai ka gani abunka.." wata rin runguma Jalil ya kaimasa kafin ya rufe baki yana fashewa da kukan jin daɗi, itama Afrah rngumesu tayi gama ɗaya tana cewa, ""Allah ka tsare mani babana da kuma mamata yaƙara rufa maku asiri, yaya muna godiya sosai". Yanda tayi maganar yasa Mutallab yin dariya tare da ɗago Jalil a jikinsa yace, "Afrah Baba da mama kuma anan?" Ta ɗaya masa kai yayi murmushi yace, "To waye baba kuma waye mama?" Shi tauna matsayin Baba Jalil kuma ta nuna shi a matsayin Mama tana dariya, ai kuwa ya nufota yana faɗin, "lallai yarinyar nan ni zaki maida macce ma". Ta riga ya bita suka riƙa zagaye motar har ta samu ta ɓuya a bayan Mutallab, Jalil na sauke ajiyar zuciya tare da tsayawa gaban Mutallab ɗin dake yimasu dariya yace, "Kin sha yarinya".
Cikin gidan suka nufa Jalil nafaɗin, "Wallahi ya Mutallab ko jiya na wuce ta gaban gidannan a zuciyata har nake cewa ko wane attajirin ke ginin gidajen nan ba ƙananan kuɗine da shiba dan irin wannan ginin a zamanin nan da muke ciki da tsadar rayuwa tayi yawa sai wanda ya tara, ashe ban sani ba harda da nawa gidan ina ƙara godiya babban yaya Allah ya saka da alkhairi". Ya amsa da Amin yana nunnuna masu ko ina sannan suka dawo suka cire kayansu dake cikin motarsa yace masu zaije yadawo,ke kuma ki hada kayanki ga trolly can nasiyomiki tana motata, kihada harda nawa guri daya tare zamuyi tafiyar. sannan zai turawa Jalil number má tánte Sajida idanta iso takirasa sai yaje ya ɗakkota, daidai motar akori kura data kwaso masu kayansu a gidan Abba ta shigo yace su shigar da komai ciki kuma su taimaka masu asaka komai inda ya dace sannan ya sallami ma'aikatan dake shisshigo da kayan nasu ya wuce.
*********
Tun yau da daddare Mutallab yafara shirye-shiryen tafiyarsu da yake so ya wuce gobe don komai yayi ready, saida yagama siya musu komai da zasu buƙata, sosai ransa yaɓaci samun labarin da yayi wai an samu wani yazo yana ɓata masa suna kuma ana tsammanin kamar kamar ɗan uwansa ne, duk da hakan bai samesa ba sai daya shiga tunanin waye zai zo yayi masa haka, baya son zargi dan idan da sabo yakamata ace yanzu yasaba da wannan abubuwan da akeyi masa dan ɓata masa suna ko kasuwa tunda ba yau aka fara ba, yana zaune má tánte Sajida takira ta sanar masa da zuwanta ɗan ya manta bai tura mata lambar Jalil ba, nan yakira Jalil bayan ya tura masa lambarta yace suje su ɗaukota tasha lambarta na nan ya turo masa, har ya kashe ya sake kiransa ya gayamasa sunan tashar sannan ya kashe wayar.
#Mutallab Asad
#Tagwaye Biyar
#Nana Diso
#Billy S Fari
MUTALLAB ASAD MUTALLAB
(Labari mai taba zuciya)
NA
BILLY S FARI
NANA DISO
RUBUTUN ƳAN TAGWAYE BIYAR ZANGO NA BIYU.
TAFIYAR BIYU TAFI DAYA
SHAFI NA ARBA'IN
Kasancewa jirgin yawo suka hau cikin wasu awanni suka sauka a kasar Ethiopia daga Nan kuma suka hau wani jirgin domin karasawa madinatul munawwara (ubangiji Allah duk wanda baije wannan guriba Allah ka kaishi wanda yaje kuma ka maimaita masa dan tsarkin mulkin ka yaa hayyu yaa qayyum). Kallon Afrah Mutallab yayi ya saƙarmata murmushi itama murmushi ta sakar masa tana faɗin " Yayana wannan Ac Tayimun sanyi da yawa wallahi kaga bamu saba ba." Kallonta yayi yana murmusawa kamin yasaka hannunsa ya rufe abundake busa Ac din." Ƴar dariya ce ta suɓuce masa duba da shima dai bai taba shiga jirgi ba sai wannan karan dan Abbansu duk zuwan da zaiyi da yaya jamil yake tafiya sai da yafara kasuwanci yakan dan shiga kasar cana da turkey suma baya huce kwana goma ya dawo kasa mai tsarki dai bai taba zuwa ba. " Yaya Nakasa cin Abincin Nan babu daɗi." " Haba afrah bakiga shinkafa aciki ba da dadi kici." Dariya tasaka tace taci cake ɗin ciki da lemon nan Da ruwa sai coffee Amma dai wannan abinci bansaba cinsa ba tsakani da Allah." " Zaki saba Inshaa Allahu." Ahaka dai kowannen su yayi shiru duba da suna tsakiyar gajimare jirginma inbanda dan bayanin ma'aikatan na jefi zuwa jefi bakajin surutun kowa.
Aciƙin awannin da bazasu gaza biyar ba suka sauka akasar datafi kowacce kasa, Afrah yi sauri mana, murmushi tayi tana ƙallon hasken dake bayyani jiƙin wani abu kamar TV An rubuta مرحبا بكم في المدينة المنورة (barkanku da zuwa madinatul munawwara) wani sautin murna tasaki tace yayana Ubangiji Allah yayi maka tukwici da Jannatul firdausi jina nakeyi kamar ba afrah ba." Murmushi yayi yace Nima jina nakeyi Kamar ba Mutallab ba." Murmushi tayi tarike musu karamar jakarsu inda shikuma yacigaba da gara trolly din hannunsa sai da suka karasa akayi musu checking da sauran Abubuwan kamin suna fita wata taxi tataresu takarasa dasu Masauƙinsu. Daga kofar babban Hotel din ta ajiyesu, daga kansa da zaiyi yaga An rubuta Al taiba hotel MashaaAllah Alhamdulillah ya Ambata aciƙin ransa kamin kuma ya sauki wata ajiyar zuciya ajajjere kayansu suka shiga dasu inda suka ƙarbi mukulllin daƙinsu " Afrah ga wannan yarinyar tare zaku zauna sunanta Amal kinji." To yaya Tafada tana gaida Wanda yaya Mutallab suke gaisawa." " itace ƙanwar tamu mutumin yafaɗa yana dan kallon Afrah karo na uku dan tunda tashigo yake binta da kallo." " Ina yini " Tafada taba sunƙuyar da ƙanta." " Afrah Wannan ɗan aboƙin dadyne sunansa umar." Ciƙin dan tsarguwa tace " Yaya umar sannu." " Sannunmu Amal kuje sai ku huta kunga asabah taƙusa munason samun Sallah." Tunda suka isa daƙunansu wanka kawai Mutallab yayi yasaka wani yadinsa Ash sannan ya ɗan kishingida kamin cikin mintuna Ashirin suji Ankira sallah haƙan yasasu saurin miƙewa sai da sukaje suka tawo dasu Afrah sannan suka huce masallaci Tundaga ƙan hanya Afrah ke hamdala tana godiyawa Allah da yaNufita da zuwa kasancewa Amal ita tasaba zuwa dan ita tariƙe hannun Afrah suka huce can ciƙin masallaci kasancewa ba'a cikaba Shigarsu keda wuya Askarawa mata sukafara hana shigowa duba da cancikin masallacin ma Akwai guri, kuka sosai Afrah takeyi yau gata garin manzon Allah saw. Yau Nice masallacin Annabi saw. Shima ta bangaren Mutallab haka yaƙasance dan baisan sanda yashiga Nafila ba yana Karantowa ƙansa addu'oi kala kala daga neman tsari Har zuri'a tagari Arzuki mai Albarka har ma da lafiya." Ko da suka idar daga sallah rauda suka tafi sun danyi zaman jira kamin abude musu wasu Na shiga da gudu wasu Na Tafiya a hankali gurin masoyi tunda mutallab yasaka ƙafarsa yashiga faɗin " Assalamu Alaika ya rasullilahi habibullahi rasulilahi saw" yafashe da kuka ahaka suka karasa rauda suka sha Addu'a da sallama da gaisuwa ga masoyin mu Annabi Muhammad saw. Ko da suka fito gida suka Nufa dukansu har su Afrah da idonta ya canza saboda kuka. " yayana bantabajin Dadi Araina ba kamar danaganni aciƙin rauda yayana kai da kayi sanadiyar kawoni Allah ya yafema kurakuranka yayana Allah yasaka Mamanmu A Aljannah." " Afrah Addu'ar Nan tayi yawa ƙinji jiki ku huta ƙinji." Umar dake sauraronsu ƙallonta yayi yanajin wani sanyi aransa kamin yacewa Mutallab wannan addua dama Ni Na sameta." Murmushi yayi masa suka shige.
********
Wasa-wasa sai ga ciwo ya sake kwantar da Meenal akaro na biyu bayan kwana uku da tafiyar su Mutallab, gabaɗaya Dady ya ruɗe ya rasa yanda zaiyi saboda tuni natsuwarsa ta daɗe da barin gangar jikinsa, ko ina ma ya dena fita kullum yana gida yana aikin lallashin Shalelen tasa, haka ma Mommy tana iya ƙoƙarinta wajen ganin ta kwantar mata da hankali, sai dai har yanzu abun ya cutura dan kamar sake yin gaba ciwon nata keyi, musamman aduk lokacin data lalabi numbobin wayar tasa duka ta kasa samu, gashi takasa haƙura data daina kiran nasa saboda ganin takeyi kamar hakan na nufin ta rabu dashi kenan har abada, cikin kwanaki ukun tayi wani baƙi ta rame sosai tamkar ba ita ba, babu abinda take iya tsinanawa kanta daga kwanci sai kuka, sai kuma sallah da sam bata wasa da ita saboda yadda Mommy tanuna mata muhimmancin yinta musamman a halin da take ciki yanzu, amma zancen wanka ko cin abinci ta ciresu cikin tsarinta sai Mommy ta matsa mata take tashi tayi ko kuma taci, yau bayan ya Kamal ya shiga dubata yafito dan tana tare da Mommy kuma kwana biyun ma Meenal ta dena sake masa fuskar shiga ya zauna mata a ɗaki kamar yanda Mommy tayi mata faɗa, kai tsaye gidan Grandama ya nufa yaje ya sanar masu da halin da Meenal ɗin ke ciki, nan hankalin Mahma ya tashi tace ya jirata tashirya suwuce tare ta dubota, cikin mintunan da basu wuce goma ba ta shiryo tafito, kallonta Grandma tayi haɗe da cewa, "ya naganki haka hannu biyu?" Kallon kanta tayi tana gyara mayafin data rufe jikinta dashi tare da cewa, "Kamar ya grandama?"
"Mtsss matsalata dake kenan duk lokacin da dama ta sameki watsi kikeyi da ita, kin san dai duk inda muka buga da yarinyar nan abun ya gagaremu saboda ba tsaye take ba ita, dan haka yanzu amfani zamuyi da wannan damar ki ɗibi kayanki kije gidan ki zauna kiyi jinyar ƴarki ki kula da ita, da haka sai kisan yanda zaki sake janyo hankalin mahaifin nasu gareki ko kuma kiyi makircin da zaisa tafita tabar gidan".
Kamal dake jinsu daga zaunen da yake yana latsar wayarsa ya ɗago kai ya kalli mahaifiyar tasa da tunanin shawarar grandma tafara shiga kanta ya jefa wayarsa a aljihu sannan yamiƙe tsaye yana cewa, "Mahma muje ko". Harara ta maka masa kafin tamiƙa masa handbag ɗin ta data ɗauki tana cewa, "Jeka mota kajirani ko bakaji magana mukeyi da Grandama ba". Wani kallo yai wa Grandama dan basu fiye shiri da ita kafin ya karɓi jakar hannun Mahma yana cewa, "Mah kada fa ki daɗe akwai inda
zanje".
"Sakarai kawai in kana iyawa kar ma kajiratan kaje duk inda zaka je, idan ma kaso mafi ruwa gudu". Grandma tafaɗa itama tana maka masa harara, bai tsaya bi takanta ba yawuce abunsa yana jefa ƙafa irin na gayun nan, tsaki grandama ta saki haɗe da cewa, "wannan ɗan iskan yaron naki idan baki tashi tsaye ba akansa watarana sai ya janyo maki abun kunya, yaro a kallo ɗaya zaka gane tatacce ne shi, dubi wata tafiya da yakeyi wato shi ga gaye ko?"
"Kai grandma ni dai mubar wannan zancen ya kike ganin zancen tafiyar nan tawa? Kina ganin babu wata matsala?" Sake da baki grandama tabita da kallo kafin tace, "matsala kuma? Kamar ya ina ƴarki kika je jinya tunda ba iya kula maki da ita zatayi da kyau ba, kina ji da kunnenki yaron nan yace Meenal ɗin duk tayi rama tayi baƙi ko?"
"Eh amma Grandma ina jin tsoron mahaifin nan nasu kada fa yazo ya kunyatani agaban matarsa kuma kesan wallahi bazan ɗauka ba".
"To Alhamdulillah tunda dai bazaki ɗauki hakan ba, maza jeki kihaɗo kayanki kuwuce kafin wancan fitsararren ɗan naki yatafi yabarki". Grandama tafaɗa cikin ƙarfafawa Mahma guiwa, nan ta juya ta koma ɗakinta ta haɗo kayanta a trollybag tafito sukayi sallama da grandama tana nanata mata abubuwan ɗaya kamata tariƙayi dan ɗaukewa Dadyn Meenal ɗin hankali sannan suka wuce.
Kasancewar weekend ne Dady bai tashi bacci ba sai kusan ƙarfe goma sha ɗaya na safe yasa suna shigowa gidan lokacin yake breakfast, sallama ɗauke abakinsu suka shigo palourn ya Kamal na gaba ɗauke da akwatin Mahma ɗin ita kuma tana biye dashi abaya, kusan atare Daddy da Mommyn suka juyo lokacin daya ƙaraso tsakiyar palourn har suna haɗa baki wajen jeho masa tambaya ina yafito da jikka, kasa ƙarasawa Mommy tayi ganin mahaifiyar tasu tsaye acan bakin ƙafa Kamal ya juya yana ce mata, "Mahma Shigo daga ciki mana". Dady da mamaki ya cika na ganin wacce baiyi tunanin zata sake tako ƙafarta cikin gidansa ba tun gargaɗin da yayi mata a shekarun baya yamiƙe cikin ɓacin rai yana cewa, "Maryam me yakawoki cikin gidana?" Kafin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 54