son shi, yarinya marainiyar Allah nazo na aura masa ita taje can su taru shi da matarsa sun ƙuntata mata." Ja Jalil yai ya tsaya yana kallon Dada data wacce hannunta daga riƙon da yai mata tana masifa kafin yace, "Haba Dada! Bai kamata kifaɗi hakan ba, a ganina ke mai iya ba wani labari ne akan ya Mutallab, shi ɗin ba irin mazan da kike tunani bane, jajirtacce ne akan duk abinda ya saka agabansa, a ɓangaren kiyaye haƙƙi kuma ke sheda ce akan wannan ɗabiarsa ce, dan Allah Dada kibarsa ya auri yarinyar nan tunda yana sonta."
"Jalil kenan! Kayi tunani da duka-duka auren nasa yaushe akayi da zai ɗauko zancen ƙara aure? Yasan matsalar tara mata kuwa?" "Ya sani mana Dada tunda mun taso cikin irin rayuwar, amma ita zuciya bata tuna wannan, burinta kawai abata abinda take so, sannan ban taɓa ganin ya Mutallab yanar damuwar da zata cutar dashi har haka ba aransa ba inba soyayyar Aïcha ba, yana matuƙar sonta sosai Dada, ko don ya samu kwanciyar hankali da sassauci agidan aurensa ki barshi ya aureta." Harara ta maka masa haɗe da cewa, "Shiya faɗa maka baya da kwanciyar hankali ne agidan nasa?" "Bai faɗa ba Dada amma nasan komai tunda awaje ɗaya muke zaune, yaya Mutallab nason zama kusa da iyalinsa aduk inda ya tsinci kansa hakan yasa ya tsara wannan tafiyar tare da matarsa amma taki amincewa ta biyowa duk da tarin matsaltsalun da take dasu da yai fatali dasu gefe..." Nan Mutallab ya kwashe komai ya faɗa wa Dada akan Meenal cike da son ta amincewa yayan nasa ya auri Aïcha ganin yadda yake tsananin sonta. Shiru Dada tayi kafin ta sauke ajiyar zuciya cikin jajantawa jikan nata tace, "Shikenan Jalil, idan har sun dai-daita kansu taji tana sonsa daga baya zan amince ta auresa, idan kuma bataso tofah bazan tilasta mata ba saboda amana take a hannuna, zan kuma yi ƙoƙari naga ta soshi ɗin dan karan kanta ba tare da shi ya tirsasa mata ba." "Yawwa Dadanmu ko kefa, hajjin bana dake za'a je in Sha Allah ni zan biya maki muje mu suke farali." Jalil yafaɗa yana dariya cikin jin daɗin ganin yai convencing ɗinta, Dada kuwa harara ta maka masa tana cewa, "indai cin hanci ne bana so kabari jikan ya biya Mani." Cewa da Mutallab ɗin.
A can ɓangaren su Aïcha kuwa su Dada nafita Mutallab ya tashi zaune yana cewa, "Wato ma dariya kika saka kina son Dada tasake kwantar dani idan ta gudur mani dake?" Murmushi ta saki tana sadda kanta ƙasa tare da cewa, "Tunda dai batayi hakan ba ai sai ka tashi muje kaba bayin Allah nan sadakar dan su samu su rage matsaltsalunsu ko?" Kafaɗa ya maƙe mata haɗe da cewa, "Afara rage nawa matsaltsalun tukuna Baby pls". Yana kwaɓe fuska tare da haɗe hannaye waje ɗaya, wannan karon dariya Aïcha tayi data bayyanar da duka haƙwaranta kafin tace, "To bari naji ya Mutallab meye taka matsalar?" Idanuwansa cikin nata yake cewa, "So ne matsalata Aïcha, ba kuma son kowa ba face naki ke kaɗai kamar yadda na faɗa maki, ki taimakeni ki tausayawa raunannar zuciyata dake cike da ƙaunarki." "Baka ganin cewa babu dacewa tsakaninmu kuma idan nayi hakan nayi sonkai?" "So baya duba dace Aïcha haka kuma idan kin so kanki bakiyi laifi ba wajena domin shi na aikata wajen zaɓoki acikin ƴan mata." Murmushi ya kuccewa Aïcha jin abinda ya faɗa tare da cewa, "Yanzu dai mu ajiye wannan a gefe ya Mutallab muyi abinda yakamata in yaso daga baya nayi wannan zancen ko kuwa?" Baya da zaɓin daya wuce yai yadda tace saboda bazai iya musa mata ba ko kaɗan, cikin ƙarfin hali ya janye duvet ɗin dake lulluɓe da rabin jikinsa ya zuro ƙafafuwansa ƙasa, takalman dake gefen gadon ta janyo masa yasa sannan yafara ƙoƙarin miƙewa tana tsaye gefe tana kallonsa, da gangan yai baya kamar zai daɗi tayi saurin miƙa hannu ta riƙosa tana cewa, "kayi a hankali ya Mutallab". Ɗago kansa yai yana kallonta tare da sakin murmushi yana ƙoƙarin zare hannun nasa daga riƙon da tayi masa tace, "Ni kabari na taimaka maka." Taƙare zancen tana bada step ɗaya tare da kallon yadda shima ya ɗaya ƙafar tasa zai taka, wani lumshe idanuwa Mutallab yai yana jin wani abu na tsirga masa tun daga ƙasan tafin ƙafarsa har zuwa tsakiyar kansa, a hankali take takawa dashi har suka fito daga cikin room ɗin da yake, kasancewar ba nisa da Male Medical word yasa suka nufi can, dogon ɗaki ne jere da gadajen marasa lafiya suna kawowa ya janye hannunsa daga cikin nata yana cewa, "tsaya daga nan bari na shiga kada su kalle mani ke". Ya ƙare zancen yana kallon yadda abayar jikinta ta lafe mata tare da jin tsikar jikinsa na zuba, janye idanuwansa yai ya karɓiledar kuɗin a hannunta sannan ya nufi ciki, yana kaiwa bakin ƙofa Jalil daya taso lokcin ɗaya hangosu ya ƙaraso wajen tare da riƙasa yana faɗin, "Ranka ya daɗe sannu ya jikin?" Sai da Mutallab ya ɗago kai suka kalli juna sannan yana ɗauke kai yace, "Yawwa Jalil, ashe baku wuce ba?" "Eh." "Ina Dada ne?" "Ta zagaya duba marasa lafiya." Daga haka bai sake cewa komai ba suka shiga suka dinga zagayawa gadajen marasa lafiyar Jalil riƙe da ledar kuɗin yana miƙowa Mutallab shi kuma yana ba marasa lafiya haɗe da yimasu ya jiki, haka suka ci gaba da zagayawa ward by ward Aïcha na biye dasu har sai da kuɗin suka ƙare tas sannan suka dawo, kallon Jalil yai haɗe da cewa, "kaje kacire wasu koda makarantun almajirai uku ne a sake kaiwa ayi sadaka." "Ok ranka ya daɗe, Allah yaƙara sauƙi." Jalil ya faɗa yana yimasa sallama sannan yabar ɗakin, kallon Aïcha yai yace, "Sannu da ƙoƙari, kin sha yawo ko?" "Ba komai ai na saba dan muna yin fiye da haka ni da mà pèrè, kai dai nake jiyowa idan ba sai ka sake wata jinyar ba ta ƙafafuwan." "Ai kasancewarki a damana bai sani jin gajiya ba ko kaɗan." Kafin tabashi amsa wayarsa ta ɗauki ƙara, hannu ya miƙa yaga Meenal ce mai kirar, kamar bazai ɗaga ba sai kuma ya ɗaga tare da jan ajiyar zuciya yana saukewa, tun kafin ya ƙarara kai wayar a kunnensa yaji cikin ɗaga muryar tana cewa, "Wallahi tallahi Mutallab ina nan ina jiranka kaje ka dawo ka sameni kai da munafukan ƴan uwan naka dake tare dakai, sai na nuna maka kuskurenka na bijiro mani da zancen ƙarin aure bayan ko watanni huɗu bamu rufe ba, sai na saka dana sanin ba wata maccen damar shiga zuciyarka har tayi tunanin takara dani a soyayyarka." "Meenal wannan itace soyayya? Itace soyayyar da kike yimani da zaki kirani ina kan gadon asibiti kina faɗa Mani magana don ranki?" "Mtss wannan kuma matsalar kace ba tawa ba, Ina nan ina jiran duk shegiyar data yi kuskuren aurenka tare da biyoka dan wallahi sai takoma inda tafito ita kaɗai." "To Shikenan naji, Ba'a faɗa maki banda lafiya bane?" "An faɗa mani amma me zanzo nayi maka? Kaje wacce ka shirya aura sai ta kula dakai." "Haka kika ce?" "Eh naɗa". Meenal tafaɗa kai tsaye tana jin haushinsa, ƙit taji ya kashe wayarsa kansa na wani sara masa, kansa ya shiga tambaya meyasa ya kasa gujewa abinda ya tsa arayuwarsa? Me yasa Meenal ta sauya masa haka zuwa irin matan da yafi tsana arayuwarsa da basu san darajar mazajensu ba? Ɗago kansa yai yana furta Allah ya sawaƙe acikin zuciyarsa, ga mamakinsa sai yaga Aïcha bata cikin ɗakin dan tunda tafahimci da iyalinsa yake waya yanar ɗakin, ajiyar zuciya yaja ya sauke sannan ya ɗan yi baya ya kwanta zuciyarsa cike da da damuwa akan Meenal.
******
A ɓangaren Meenal kuwa tana jin ya kashe wayar tayi jifa da wayarta tafashe da wani irin kuka, me tayiwa Mutallab da zai saka mata da haka? Me yasa ya zaɓi tozartata a cikin ƙawayenta da zasuji labarin kawo mata kishiya cikin watanni huɗu da aurenta?,me mutanen gari zasu ce akanta na ƙarin auren mijinta? Baya sonta ne ko kuma dai wata ya gani a waje wacce tafita? Tambayoyin data riƙa jefowa kanta kenan tana kuka har Asiya ta shigo ɗakin ta iskota a haka..
#Mutallab Asad
#Ƴan Tagwaye
#Nana Diso
#Billy S Fari
SHAFI NA TAMANIN DA UKU
*MUTALLAB ASAD*
Arewabook:- billysfari
Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.
Da sauri Asiya ta ƙaraso wajenta tana Dafata, "Meenal lafiya? Kukan me kikeyi haka." "Asiya me zanyi inba kuka ba, aure fa Mutallab zai yi, wata maccen fa zai aura bayan ni Asiya na shiga uku." Harara Asiya ta dalla mata cikin ranta tana cewa, 'Ai baki shiga uku ba yanzu dai zaki shigeta tunda Allah ya haɗaka da umma.' a zahiri kuwa cewa tayi, "Kiyi haƙuri Meenal ki kwantar da hankalinki, ki saka aranki ƴar aiki ce zai kawo maku dan ba'a hannunki kaɗai ba har a hannunmu dana Umma sai taci ubanta, sai tayinadamar shigowa gidanki wallahi." "Asiya bazaki gane ba, nifa ko a mafarki sam bana don Mutallab yai tarayya da wata macen balle a zahiri, wayyo Allah na nono na lalace." Meenal tafaɗa cikin kuka tana sake fashewa da wani kukan.
Haka Asiya taci gaba da zugata tana jure mata kunne akan abubuwan da zata yiwa Mutallab ta huce baƙincikin da zai yi mata haɗe da tuggu da makircin da zasu shiryawa amaryar idan ankawota, hakan yasa Meenal ta ɗan ji sanyi a ranta tare da sakin jikinta sannan Asiya tamiƙe tana cewa, "Yau me zan dafa mana?" Dan tuni tadawo nan da zama a ɗayan ɗakin Meenal take zaune, "Duk abinda kika dafa Asiya." Meenal ta bata amsa tana zamewa kan kujerar da take zaune ta kwanta, kitchen Asiya ta nufa ta ɗora masu dahuwar taliy a'a shaf-shaf da kofin gwangwani ta dafa ƙwai guda huɗu ta zubo mata nata ga plate ta azo mata ƙwai ƙwaya ɗaya akai bayan ta baɗe abincin da maganin da Umma ta bata takawo mata sannan takoma kitchen ta zubo nata ta ɗoro sauran ƙwan guda uku ta nemi waje ta zauna tana ci.
A ɓangaren Umma kuwa yanzu abubuwa sun fara sauyawa ta ɓangaren Abba da Aunty Amarya saboda yadda Aunty amarya ta dage da azkhar na safiya da marece, haka ma idan zata kwanta tana tofe jikinta da addu'o'in tsari da Imam (matar Walid) idan tazo take koya mata, dan yarinyar akwai natsuwa da kuma girmama manya hakan yasa ta dauki Aunty amarya tamkar tata mahaifiyar kuma da yake duniya makaranta Aunty Amarya tayi karatun ta natsu yanzu sai ta jata ajikinta itama ba tare da tasa girman kai ba take zaunawa suyi hira abunsu tana faɗa mata addu'o'in tana rubutawa har ta soma haddace wasu daga ciki tana yi ba dare ba rana kuma tana yiwa Abba Togo ga abinci shima yana ci, idan ta samu keɓewa dashi kuma ina Umma tafita takan sheda masa ya tashi tsaye ga ibada da kuma azkhar, sai gashi Allah ya taimaka yafara dawowa cikin hayyacinsa har yana iya tirjewa ga wasu abubuwan da Umma ke sashi musamman ta fannin Aunty amarya daya fara nuna mata cewa matarsa ce bata isa ta saka masa shamaki da ita ba, haka itama Aunty amarya duk wani tsoron Umma da kwarjinin da takeyi mata tana bautar da ita ya fara cirewa sai baka rasa ba, Imam kuma banda gaisuwa ba abinda ke shiga tsakaninta da Umma don dangin Abba kaf babu wanda bai san halinta ba, shiyasa mahaifinta da yake ƙanen Abbane ya gargaɗeta da duk wani abu da zai haɗata da Umma ɗin ta kiyayeshi baya so, wannan dalilin yasa duk yadda Umma taso ta jata ga jiki ta kasa sai ta ɗora mata karan tsana, Walid kuwa tuni Mutallab ya ajiyesa a daya shagonsa na kayan abinci yana tsaro idan ya taso makaranta, sosai Imam da Fannah ke shiri tsakaninsu kasancewar halinsu yazo ɗaya, shiyasa ba wanda yasan tsakaninsu hatta mazansu zasu kashe su binne ba wanda ya sani wajen ƙoƙarin ganin yanda zasu faranta ranmazajrnsu, wannan yasaka zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidajen aurensu sosai, dan daga Jalil ɗin har Walid sun ɗan ƙara ƙiba da haske alamun suna cikin kwanciyar hankali kuma suna samun kulawa awajen matayen nasu.
*************
Mutallab kuwa kwanansu huɗu a asibiti kafin aka basu sallama, acikin kwanaki huɗun nan duk wata hanya da zai bi ya nunawa Aïcha tsantsar ƙauna da soyayyar da yakeyi mata sai daya bi saboda yadda ta sake shiga ransa duba da irin kulawar da take basa, wata irin shaƙuwa da kusanci yayita ƙoƙarin sanyawa tsakaninsu sai dai ita sam takasa sake jiki da hakan, baya iya ɓoye soyayyar da yakeyi mata agaban kowa, Dada kuwa aduk lokacin da taga Mutallab ya fiye zaƙewa akan lamarin Aïcha haka zata dinga masifa dashi tana cewa yafita harkar jikarta tunda tace bata son shi, tanayin hakan ne duk dan ta tabbatar idan har Aïcha ɗin tafara son shi ko kuma tariƙa nuna mata cewa ai akwai mijin data yimata zaɓi kuma ta tabbata idan taganesa itama zata so shi, A duk lokacin da Dada tafaɗi hakan sai Aïcha bata cewa komai sai dai ta tashi tabar wajen tana jin ba daɗi ranta wanda batasan dalilin hakan ba tunda dai tasan babu soyayyarsa a ranta, Dada kuwa da kallo take rakata tana mai addu'a Allah ya tabbatar mata da alkhairi yasa tazama mai sharewa jikan nata hawaye dan yanzu ko dan ita Aïcha ɗin tasamu inda zata huta tana burin auren nasu ya tabbata. Yau ma kwance take ɗakin Dada dawowarta kenan daga islamiya Mutallab ya shigo ɗan jikin nasa yai kyau sosai dan ya samu sauƙi, tana jin sallamarsa ta tashi da gudu ta wuce uwar ɗakin Dada, a tsakar gida ya tadda Dada dan haka ya fara gaisawa da ita sannan ya shiga raba idanuwa yana cewa, "Dada ina Aïcha ne?" "Tana ciki injin dai ko lafiya?" Shafa kansa yai yana murmushi kafin yace, "Lafiya kalau Dada laifi ne idan na tambayi matata." Harara ta maka masa haɗe da cewa, "Kafita idanuwana Mutallab, wai yarinyar nan bazaka ƙyaleta bane tunda tace bata sonka?" "Haba Dada kina so na sake komawa gadon asibiti kenan." Ya ƙare maganar tare da miƙewa ya nufi cikin ɗakinta yana murmushi ba tare daya jira amsar da zata bashi ba, yana shiga cikin palourn tana fitowa daga cikin uwar ɗakin sanye da dogon hijabinta har ƙasa, jingina yai ajikin ƙofar yai folding hannayensa akan ƙirji tare da tsareta da idanuwa, kanta ta sunkuyar ƙasa tana wasa da zoben hannunta haɗe da cewa, "Sannu da zuwa ya Mutallab ina wuni?" "Bazan amsa wannan gaisuwar taki ba Baby saboda kin mun laifi". Ɗago kanta tayi tana ɗan zaro idanuwa haɗe da kallonsa tace, "laifi kuma ya Mutallab?" "Eh mana, waya faɗa maki haka ake jinya da ansallami mutum daga asibiti sai afita batunsa ko ƴar dubiyar nan taya jikinsa baza a koma ayi masa ba." Dariya ya bata dan haka ta ɗan murmusa tare da cewa, "kaji tsoron Allah ya Mutallab jiya-jiya fa aka sallamoka asibiti, yau kuma baka ga rana tafaɗi bamu je dubaka ba amma har kazo kana ƙorafi." "Dole nayi hakan Aïcha naga ankasa bani irin kulawar da kike bani ina shirin mutuwa maraya. Shiyasa nace bari dai nazo nakawo maki kaina." "To baruwana kai da Dada kuwa." Taƙare zancen tana ƙoƙarin raɓawa tafito ɗakin, kasancewar yana abakin ƙofar tsaye yasa ya gyara tsayuwarsa sosai yadda faffaɗan ƙirjinsa ya tare wajen da zata raɓa tawuce, kanta ta ɗago idanuwanta suka sauka cikin nasa da yake kallonta, "Barka da rana kyakkyawata kin wuni lafiya?" Yafaɗa yana kallonta, tace "Lafiya klw ya jiki?" "Alhamdulillah." Shiru tayi ita bata wuce ba ita bata koma ciki ba tana sadda kanta ƙasa, bara naje nakawo maka ruwa." "No nagode dawo ki zauna muyi magana." Ya ƙare zancen yana ƙara sawa cikin palourn ya samu ɗaya daga cikin kujerun y zauna, hakan yasa itama dawowa ta zauna a ɗaya e kujerar dake fuskantar tasa tare da sunkuyar da kanta ƙasa, Allah ma ya sani wani irin kwarjini yakeyi mata aduk lokacin da suka haɗa idanuwa shiyasa take dauke kanta daga garesa, shi kuma ta lura yana son yimata, ko yanzu tana jin yadda idanuwansa ke yawo akanta wanda hakan ya haifar mata da kasa natsuwa sai mutsumutsu takeyi saboda yadda ta tsari, shi kuwa Mutallab ji yake wata irin soyayyarta na fizgarsa tamkar yaje ya rungumota a jikinsa ko zai samu sassaucin yanayin da yake jin kansa aciki, a halin yanzu amincewarta kaɗai yake buƙata shiyasa yazo gidan dan ya sake fitowa a matsayin masoyinta a karo na biyu agaban iyayenta, dan tun abinda yafaru kwanaki aka jingine zancen dake tsakaninsu da ita tunda tace bata so bai sake ɗauki masu zancen ba sai dai ƙoƙarin bayyana mata irin soyayyar da yake yimata da yai, gyaran murya yafara yi sannan yace, "Aïcha muyi maganar gaskiya nifa har yau ban haƙura da soyayyarki ba, kuma nasan kema kinfi kowa sanin haka tunda kinga yadda sonki ke galabaitar dani, ki bani dama kafin nawuce Nigeria nan da kwanaki uku bukin abokina Aryan a tsaida magana, na roƙeki dan Allah kada kice a'a a wannan karon kinji." "Ya Mutallab me kake so nace? Nifa ina jin tsoron.." kafin taƙarasa yace, "Tsoron me Aïcha? Matata ko kuma meye?" "Kai dai ya Mutallab ba matarka ba." zaro idanuwa yai haɗe da cewa, "Ni kuma Aïcha! Saboda me?" "Abubuwa da dama ciki akwai rashin dacewar mu." Wani matsanancin faɗuwar gaba yaji jin kalmar daya tsana tafaɗa na fitowa daga bakinta. "Oh my God! Aïcha sai yaushe zaki dena faɗar haka ne wai? Kawai dai kice bakya sona ne amma shi so ina ruwan shi da dacewa." "Da ruwansa ya Mutallab kamanta me bahaushe ke cewa? Ƙwarya tabi ƙwarya saboda haka kai ɗin ba Sa'ar aurena bane takowace fuska baka dace dani ba." Wani ɓacin rai yaji ya taso masa ta ƙasa zuciya yana kallonta yace, "ok na fahimta." Haɗe da miƙewa cikin fushi ya nufi ƙofar fita, "Ya Mutallab..." Runtse idanuwansa yai tare da ja ya tsaya yana ɗaga mata hannu yace, "Ya isa haka Aïcha zan tafi tunda bakya sona babu wani sauran abinda zaki sake faɗa mun, dan haka nagode da iya kulawar da kika bani." Yana kaiwa nan ya fice ransa a ɓace ba tare dako Dada ya yiwa sallama ba, a tunaninsa ko yane yakamata ace Aïcha tayi masa mazauni acikin zuciyarta, ya ɗauka duka kulawar data bashi a asibiti dan tana sonsa ne, ashe kawai yaudarar kansa yakeyi har yanzu bayada muhalli a zuciyarta, da wannan tunanin ya isa wajen motarsa ya shiga ya ja da ƙarfi yabar ƙofar gidan ransa nayi masa wani irin sululi da kuma ƙuna. Aïcha ta jima a zaune tana mamakin fushin nasa dan ita bataga abinda tafaɗa ba da har zai sashi fushi dan duk abunda tafaɗa gaskiya ne, miƙewa tayi tana sauke ajiyar zuciya hankali kwance ta cire hijabin sannan tafiya inda Dada take zaune tsakar gida ta fiddo alayyahu tana gyara, kallonta tayi cike da mamakin yadda Mutallab ɗin yafita cikin ɓaci rai ko sallama baiyi mata ba tana cewa, "ke Aïcha lafiya?" "Lafiya kalau Dada kawo na tayaki." Ganin ba alamar komai a fuskar Aïcha na ɓaci rai yasa ta jawo wayarta dake gefenta takira lambar Mutallab lokacin yana tuƙi dan taji eye sanadiyar fushin nasa, yana ganin kiran Dada yakasa ɗagawa tare da sake ba motarsa wuta. "innalillahi wa'inna ilaihirrajiun, ke wai uban me yafaru naga yafita yana fushi kuma nakira wayarsa yaƙi ɗagawa, me kika yimasa ne?" "Dada wai me zan yimasa ne?" tafaɗa cikin halin ko inkula tana cigaba da gyaran alayyahunta, "Ikon Allah, Ni wannan lamari naku akwai ban mamaki aciki, ke kin dage bakya sonsa shi kuma yaƙi ya haƙura dake, ban san ya kuke so ayi ba." Da haka Aïcha ta gama gyara alayyahun ta yanke ta miƙa ta nufi kitchen dashi tana wankewa, ita kuma Dada ta shiga tunanin meye mafita yanzu dan tafahimci ba kaɗan jikan nata ke sonta ba ita kuma bazata taɓa yiwa Aïcha auren dole dashi ba idan har bata sonsa.
Shi kuwa Mutallab na isa gida yawuce sashen tánte Sajida ya samu tana sallah, zaunawa yai har sai data sallame sannan ya gaisheta yana cewa, "Tánte ina ganin ku shirya gobe zamu wuce tare da Jalil dama a goben yake don wucewa ni na tsaida shi akan yabari sai zuwa jibi in an kwana biyu muwuce tare saboda bukin Aryan." "To in Jin dai lafiya kuma ka sauya shawara." "Lafiya kalau tánte kawai ku zama cikin shiri gobe in sha Allah zamu wuce." Ya ƙare zancen yana miƙewa haɗe da barin wajen, "Allah yakaimu." Tafaɗa tana karantar yanayin da yake ciki haɗe da girgiza kai. Aïcha kuwa wayarta ta ɗauko tana son kiran shi dan dama shi ya samata lambarsa a wayarta yai saving amma kuma sai takasa sai jujjuya wayar takeyi zuciyarta na gargaɗinta da kada tayi hakan, da wannan shawarar ta ajiye wayar tafita ta shiga wata sabgar haɗe da taya Dada aiki.
*********
Shirye-shiryen buki akeyi sosai na gani na faɗa dan duk wata bidia ta cikakkun wayayyi sai da Aryan da amaryarsa suka shirya, ana gobe ɗaurin aure ranar da akeyin dinner Mutallab da tánte Sajida da Jalil da Mahmoud daya biyosu don tun bukin Mutallab suka zama aminai shi da Aryan suka iso garin dan Afrah cewa tayi bazata biyosu ba zata zauna wajen Dada har ya Jalil da tánte na tsokanarta wai kishi takeyi Aryan zaiyi aure, bata rabasu da uffan ba ta haɗa kayanta ya Jalil ya sauketa can gidan Dada bayan ya shiga sun gaisa da ita sannan yawuce suka kamo hanya, duk da Aryan na fushi da Mutallab na rashin isowarsa wajen hidimarsa har sai da aka kusa gama programs gaba ɗaya dan sati aka ɗauka anayi yaji daɗin isowarsa, a ƙalla zaiji daɗi tunda ya samu halarta wajen dinner da za'ayi gobe kuma ɗaurin aure.
#Mutallab Asad
#Ƴan Tagwaye
#Nana Diso
#Billy s Fari
SHAFI NA TAMANIN DA UKU
*MUTALLAB ASAD*
Arewabook:- billysfari
Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.
Shi kanshi yasan ba ƙaramar ɗaukaka bace agunsa ace mutum mai muhimmanci kamar Mutallab Asad yaje bukinsa, shiyasa yai burin ace gabaɗaya ma ya samu halartar bukukuwan nasa dan yai alfahari da hakan. Mutallab kuwa koda ya iso Meenal bata gida kuma ya kirata ya sanar da ita zancen dawowarsa, shiru yai yana bin gidannasa gabaɗaya daya haukace sai kace gidan da aka shekara babu mutane aciki, wani baƙinciki da sululi ya taso masa a rai yawuce sashensa, ga mamakinsa shima a hargitse da alama tana amfani dashi kuma bata damu data gyara ba, kansa ya shiga juyawa lokacin daya wuce toilet bayan ya gama rage kayan jikinsa da niyar watso ruwa, da sauri ya dawo baya saboda wani irin ƙarni daya bugi hancinsa, ba ƙaramin wari toilet ɗin keyi ba ya samu gefen gado ya zauna haɗe dasa hannayensa ya dafe kansa, wayarsa yaciro ya kamo lambarta yakira, sai da tayi kusan missed call huɗu kafin ta ɗaga a na biyar lokacin suna fitowa daga cikin wani daji ita da Umma data sanarwar zancen dawowarsa tace ta shirya takaita wajen wani malami da zai bata maganin da zatayi amfani dashi idan ya iso saboda zancen auren ya watse, murya a daƙile ta ɗaga tana cewa, "ka iso ne?" Sai daya danne zuciyarsa sannan ya amsa mata da , "Eh na iso kina ina?" "Naɗan fita ne gani nan ƙarasowa." "Fita kuma ina kika je bada izinin a ba ko kin tambayeni?" "Ka tambayeni ne kai daka yanke hukuncin ƙari mani kishiya balle kasa ran zan tsaya tambayarka ko amincewarta idan zanyi wani abun?" "Ni kike faɗawa haka?" "Sama da haka kafaɗa mun Mutallab dan haka kada kayi mamakin jin fiye da hakan daga bakina." Tana kaiwa nan takashe
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 47 Chapter of 54