Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Aicha tayi tace " Kiyi hakuri mama dare nayi shine na biya gidan dada." " wai menene haka ke? Daga shigowarta zaki fara zaginta." " Yanzu fa kagama tambayata ina take har kana min wa'azi yanzu kuma tashigo ina hukuntata kacemin wai meye haka." Sannu da zuwa dada Kawu yafada yana bata gurin." Tsaki dada tayi tace " Wai kai kuwa wanne irin mata katara ko gani idanuna ai tarage sababi." " Ayi hakuri dada ashe gidanki tabiya." " To idan na sakarci ba a aiko yarinya da yamma ris antaɓa haka? Kuma kun ajiye budurwa gabanku babu ilimi antaba haka?" " kiyi hakuri dada danAllah wallahi Nidai banda karfin rikon ne inadayi ne Amma makaranta ban iya sakata suma sauran yaran iyayen su." " To ita datakeyiwa wahala bata sakata." " Au karata taje takai miki to billahilaxi ban iya wannan rikon munafuka kawai taje can gidan karuwan da suka kama itada karuwar yayarta taje tacigaba da zama." Kawu da hankalinsa yatashi yace " DanAllah kiyi hakuri maman mukhtar." " Wallahi bazan riketa ba tsinanniyar yarinya mahaukaciya yar mabarata irinki masu tahirin abun kunya." Sosai Aicha tashiga raira kuka. Tashi mama tayi ta shiga dakin shirgi ta dakko bakko ta cillowa Aicha ga kayanki nan kishige ki barmin gida fitararriya." Sai da ta gama sannan Dada taka ajiyar zuciya tace " Daman zuwan danayi kabani ita shiyasa nazo dakaina ni zanyi kula ita zan kuma riketa tunda ku kunkasa baza'abar marainiyar Allah tana wulaknta ba." " Wallahi kitafi da'ita dada na amince dari bisa dari idan tasamu mijima tayi aurenta danAllah kowa ya huta." Mamakine ya kama dada sosai da wannan zumuncin na zamanin nan. " Tashi muje Aicha." Cikin shahekar kuja tace " Kawu nagode Allah yasaka da Alkhairi kawu." " Ameen Allah ya kiyaye sai ki kama kanki dan idan kika rasata bana tunanin kinada wani matsugunen." Tsaki mama tayi tashige daƙi tana faɗin " Ayi dai mugani idan ma baƙin cikin tallan datakemun ne akeyi zan iya abuna da kaina mutane sai munafurci, jinin tsiya ma irin Aicha." Ke dakata kada ki gayan magana." Shigewarta mama tayi ita kuma Aicha tana kuka sukayi sallama da kawu suka huce a hanya ma sai da dada tayi kuka, " Yunusa idan kasame shagon siyayya zamu tsaya ni zanyi aikin ladan Allah yatayani rikon marainiya, haka kuwa akayi ɗan suna karasowa shagon dada taja hannun Aicha suka shige ciki Nan tayi mata siyayya mai yawa dab Aicha kuka tasaka mata saboda mamakin lamarin sai daga nan suka ɗauki hanyar gida. Safiyyou ina dada tashiga ne? " Nidai tacemun tashiga kauye." " kauye kuma?" Fita yayi ransa abace daman zuwa yayi yayimata fanfo akan tasaka baki Mutallab ya aure daya daga ciƙin yaransa kuma gashi batanan. Wajejen ƙarfe 12 mahmud yazo suka shiga cikin kauye dan sintirin gidan su aicha, gaba daya yakasa sukuni, wani irin ƙaunar yarinyar yakeji, ko da suka karasa gidan Ansanar musu ai masu gidan sun daɗe da rasuwa nan yashiga dubawa amma kuma duk inda suke tunanin zance daya ne ai sundade da rasuwa "Yadda Mahmoud ya hango tsantsar damuwa cikin idanuwan Mutallab ya sashi dafa kafaɗarsa cikin son lallashinsa yana cewa, "calm down Mutallab, zamu samesu duk inda suke". "When? Where Mahmoud? Wallahi ina don Aïcha so mai tsanani, ina buƙatar sanin meya samesu kuma a ina suka shiga?". "Duka zaka sani Mutallab, amma dole sai munbi abun a hankali, nifa ina tsoron wannan wutar ma idan bada su duka ta haɗa ta ƙune ba Mutallab". Wani irin fizgo kansa Mutallab yai yana masa wani irin kallo haɗe da cewa, "meyasa bakinka bazai faɗi alkhairi ba Mahmoud? Kasan matsayinta a zuciyata da kake yimata fatan mutuwa sai kace baka don farincikina!" "Wannan wace irin magana ce haka kakeyi Mutallab? Akan ƴar mabarata kake kallon fuskata kace bana son farincikinka? Me kake nufi da hakan?" Mutallab da kansa ke jingine a jikin kujerar da yake zaune idanuwansa a rufe ba tare daya buɗe ba yace, "Abinda duk zuciyarka ta raya maka kuma bana son sake jin kalma ɗaya akan Aïcha daga bakinka matuƙar ba alkhairi zaka faɗa ba". Cike da mamkinsa Mahmoud yace, "ƴar mabaratan Mutallab? Wai ko mantawa kakeyi kana da mata, kana da wacce tafita komai agidanka ƴar masu arziƙi da zaka wani tada hankalinka akan ƴar matsiya.." kafin ya ƙarasa Mutallab ya daka masa tsawa yana cewa, "get out in my car". "Mutallab!" "I said get out Mahmoud ko kana so kaga negative side ɗina ne?" Cije baki Mahmoud yai yana kallonsa haɗe da buɗe motar yafita tare da rufo masa marfin ƙofar da ƙarfi, wayarsa ce tafara ringing kamar bazai ɗaga ba sai kuma ya miƙa hannu saman kan stearing wheel ɗin motar ya ɗauko ya ɗaya yakai kunnensa har lokacin idanuwansa na arufe, "hello Yayana!" Meenal tafaɗa a shagwaɓe tamkar zatayi kuka, Mutallab dake jin kansa cikin wani yanayin da gabaɗaya baya yimasa daɗi yace, "Na'am Meenal sai yanzu zaki nemeni? Bayan abunda kikayimun jiya anyway kina lafiya?" "Lafiya kalau yayana, sai dai zuciyata sam bata yimani daɗi saboda wani mummunan mafarki dana tashi dashi wai ka kafara son wata mace bayan ni har kafara zuwa zance wajenta an kuma saka maku ranar aure! Yayana wallahi mutuwa zanyi dan bazan iya jurar ganin wata macce tare dakai ba! Bazan iya lamuntar karaba mana soyayya ni da wata maccen ba, bazan iya ba yayana". Taƙare zancen tare da saka mashi wani irin kuka daya sake jefasa cikin wani yanayin, a hankali ya buɗe idanuwansa da suka wani kaɗa masa tare da cewa... MUTALLAB ASAD   (labari mai taɓa zuciya) Na Billy s fari Nana diso      RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU.    TAFIYAR BIYU TAFI DAYA   SHAFI NA SABA'IN DA BAKWAI. "Meenal wai duk wannan kukan na meye? Daga mafarki sai akace maki ya zama gaskiya? Kuma idan ma hakan ne ai bai kamata ki tayar da hankalinki ba saboda kin kasa tsayawa ki bani irin cikakkiyar kulawar da nake buƙata, Please dan Allah dan Allah Meenal kibari naji da halin da nake ciki". Wani kukan ta sake saka masa haɗe da cewa, "Me kake so kasanar dani yanzun? Kenan soyayyar da nake yimaka na gaza? Duk iya jurewa tarin buƙatarka da a kullum baka gajiya da nakeyi duka a banza ne kuma ba kulawa bace?" Runtse idanuwansa yai ciwon kan dake damunsa na sake tarar masa haɗe da cewa, "Bance kin gaza ba Meenal amma kisani kowane namiji ba soyayya kaɗai yake buƙata ba awajen matarsa, yana don tattali kulawa, martabawa, tsaftace muhalli sa, kalamai masu daɗi, jansa ajiki, kula da cinsa shansa da suturarsa idan ya nemo ya ajiye maki da dai sauransu, wuɗannan abubuwan sune ke zama ginshiƙin dake ƙarfafa tsayuwar ginin da akayiwa soyayya tare da ƙawatata da kuma ƙarfafata ta yadda shi kansa auren zaiyi ƙarko, rashin samun su kuwa Meenal kan raunata soyayya da kuma lalata aure". "Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun kana so kafaɗa Mani cewa soyayyar da kake yimani ta raunata? Kana so kace mani aurenmu ya lalace kenan bayan kasan irin tarin ƙauna da soyayyar da nake yimaka?". Jin da Mutallab yai sam bazata fahimcesa ba saima sake saka masa kukan da takeyi tayi ya sashi sauke ajiyar zuciya a hankali don ya soma gajiya da kukan nata tare da sanyaya muryarsa ya ce, "Soulmate duka ni ba haka nake nufi ba kuma mafarkinki ba gaskiya bane, kiyi haƙuri ki kuma kwantar da hankalinki domin yayanki na matukar sonki a zuciyarsa, ina cikin wata ƴar damuwa ne yanzu kiyi mani addu'a anjima zamuyi waya In sha Allah kin ji ko?" Sai data ja majina ta hancinta cikin kukan sannan ta iya cewa, "Toh" Murmushin ƙarfin hali ya sakar mata haɗe da cewa, "I love you". Nan ma da "Toh". Kaɗai ta sake amsa shi kafin ya iya kashe wayar zuciyarsa cike da takaici, wai ɗan i love you ɗin nan ma bazata iya maida masa ba sai dai Toh, baisan lokacin da ya saki tsaki ba yana tada motar yabar wajen, shagunansa ya wuce yaga tadada komai na tafiya dai-dai yadda ya kamata. A can yai sallar azahar da la'asar sannan yabar wajen, anguwar su Aïcha ya sake komawa yaci gaba da tambayar mutane ko Allah zaisa ya dace da wanda yasan inda suka koma amma har lokacin ba'a dace ba, gefe ya koma ya kifa kansa da jikin stearing wheel na motar haɗe da faɗawa duniyar tunani, Allah ya sani yana da matuƙar buƙatar wata maccen a gefensa dan kaucewa faɗa wa halaka amma yana matuƙar jin tsoron kar ya sake zuwa ya ɗaukowa kansa irin Meenal, shiyasa zuciyarsa takasa haƙura da Aïcha duk da itama ɗin bayada tabbaci akan zai samu komai ɗari bisa ɗari agunta amma zuciyarsa na faɗa masa zai sau kaso tis'in bisa ɗari a wajenta, wanda hakan kaɗai ya wadatar dashi idan ya haɗa da kaso ashirin bisa ɗari da yake samu agun Meenal. Har akayi kiraye-kirayen sallar magrib yana wajen ya buɗe motarsa yafito ya rufe,  kasancewar akwai masallaci acan gaba ya nufi wajen ya ɗauki buta ya ɗebi ruwa yai arwala mutanen anguwar sai faman kallonsa sukeyi ganin baƙon mutum da kallo ɗaya zakayi masa kasan akwai tarin arziƙi da wadata atattare dashi acikin anguwar tasu, bai kula su ba har yaƙare arwalarsa ya shige cikin Masallacin aka tada sallah, bayan angama ya miƙe yai nafila raka'a biyu kamar yadda ya saba ya sallame ya ɗaga hannu yayi addu'o'insa da azkhar ya shafa, hannu ya miƙawa na kusa dashi suka gaisa haɗe da cewa, "Bawan Allah tambaya nakeyi dan Allah." Isah mai shayi dake kokarin miƙewa yaje yafara haɗa wutar dafuwar shayinsa saboda ya makara yau yace, "Allah yasa na sani ranka ya daɗe amma muje daga waje ko." Ya kama hanyar fita shima Mutallab ɗin ya miƙe yabi bayanshi suka fita, sake gaisawa sukayi Mutallab ya gabatar masa da kansa kafin ya ɗora da cewa, "Nazo anguwar nan a watannin baya da suka wuce a wancan gidan wajen wata yarinya da mahaifinta ke bara tare da ita akan zan sake dawowa muyi magana dasu, sai dai yanzu naga kamar basu bane acikin gidan dana tambaya sai akace mani sunyi gobara sun ƙone." "Eh haka ne amma akwai ƴarsu ƙwayar ɗaya data rage dan ƴar uwar tata itama Allah yai mata rasuwa bayan mutuwar iyayensu." a razane  Mutallab ya ɗago kai yana kallonsa haɗe da cewa, "wacce daga cikinsu ke raye." "Aïcha ce ranka ya daɗe." Wata gauruwar ajiyar zuciya Mutallab ya sauke jin Aïcha na raye yana mai jin sanyi da kuma tausayinta azuciyarta kafin yace, "Allah sarki, ubangiji yai masu rahama ya kuma gafarta masu." "Amin ya Allah." Isah mai shayi ya faɗa yana ƙoƙarin barin wajen, saurin dakatar dashi Mutallab ya sakeyi tare da cewa, "Amma to don Allah ya zanyi na sameta yanzu?" "Ai tana gidan ƙanen mahaifinta ne yallaɓai gashi ni ina akan bakin aikina balle na kaika wajen." "Ba komai zaka iya yimani bayani idan har ba damuwa." Sanin ba lallaine ya iya fahimta ba koya misalta masa gidan da kawun nata yake yasa yace, "Anya! Anguwar nada wahalar kwatance yallaɓai, amma kabani  mintuna goma idan ba damuwa naje wajen sana'a ta kaga gun can nadawo sai na kaika, ai Aïcha mutuniya tace tana da hankali da natsuwa sosai." Wani abu Mutallab yaji ya dakar masa zuciya mai kama da kishi yai saurin danne zuciyarsa haɗe da cewa, "Ga motata can bara naje na jiraka aciki." Yaƙare zancen tare da wuce ba tare daya jira me zai ce ba. Sai da Isah yaje ya haɗa wutar dahuwar shayinsa ya fidda komai ya daidaita su saman trader ɗinsa sannan ya kira wani ƙanensa yace ya zauna ya tsare amsa shagon kafin yadawo sannan ya samu Mutallab suka wuce gidan kawun Aïcha yana faman raba idanuwa cikin motar da tunda yake bai taɓa haɗawa da mota mai kyau irinta ba. Sunyi Sa'a kuwa koda suka isa kawu na zaune ƙofar gida shi da wani abokinsa, bayan sun fito cikin motar suka nufi wajen da kawu da abokin nasa ke zaune sun zubam motar idanuwa suna kallo, cikin girmamawa Mutallab ya duƙa yana gaishesu Isah kuma ya shiga yimasu bayani, dukkaninsu baki sake suka bi Mutallab da kallo kafin kawu yace, "in jin dai lafiya yaro kake nemansu ko?" "Lafiya kalau kawu dama akwai ƴar wajensu mai suna A'isha dana gani kwanakin baya kuma na sameta mukayi magana da ita da kuma mahaifinta da sunan idan na sake dawowa zamu zauna muyi magana dashi sai gashi na samu labarin cewa Allah ya karbi abunsa." "Haka ne." "ALLAH ya jiƙansu yai masu Rahama." "Amin ya rabbi." Shi Mutallab yai ya kasa ci-gaba da magana har sai da kawu yace, "to gashi kuma Aïcha ɗin bata nan ɗazun nan wata daga cikin dangin mahaifiyarta dake zaman kaka wajenta ta ɗauketa, maganar da nakeyi maka yanzu haka takoma can wajenta da zama." "To kawu idan ba damuwa ina so kayi mani izini naje na ganta." Shiru kawu yai kamar mai wani nazari kafin yace, "Shikenan ba damuwa, kaje gobe da safe kadawo na haɗaka da wanda zai kaika ko kuma ni da kaina na kaika wajenta saboda ita mariƙiyar tata ba daɗine da ita ba, bana tunanin idan kaje kai tsaye zata bari kaga yarinyar nan, amma kafin nan me yasa kake son ganinta?" Cikin jin kunya Mutallab ya sadda kai ƙasa haɗe da cewa, "Kawu ina so ne na nemi yardarta idan har ta amince zan aureta". Gabaɗayansu zaro idanuwa sukayi har da Isah jin abinda ke fitowa daga bakinsa da basuyi tsammani ba, Muryar kawu na rawa yace, "Kai yaro ina dai ba yaudarar yarinyar nan kazo kayi ba ka gudu? Inba haka ba ina kai ina ita." "Ko ɗaya kawu wallahi da aure nake sonta, wannan ne ma dalilin daya sa nafara zuwa naga mahaifinta mukayi magana kafin na bijiro masa da wannan zancen sai gashi Allah yayi nasa iko." Ajiyar zuciya kawu yai yana jinjina kai tare da mamakin ikon Allah yana tambayar kansa har ta ina Aïcha ta haɗu da wannan kyakkyawan matashi mai arziƙi sannan ya ɗago kansa yana kallonsa yace, "idan har haka ne kuwa zanfi kowa farinciki itama Aïcha tayi aure kota samu natsuwar zuciya da gangar jiki dan yarinyar nan tawahala arayuwa, taga jarabawa sosai." Nan dai sukayi sallama akan gobe zai dawo su tafi tare gidan Jaddi(Dada) tare dayi masu alkhairi ya amshi lambarsa sannan ya ɗauki Isah mai shayi da jikinsa yai sanyi jin abinda ke tafe da Mutallab suka wuce, dan har ga Allah ya fara sha'awar auren Aïcha saboda ya fidda ita halin da take ciki dan bai san ma takoma gidan Dada ba, amma ko yanzu yana yimata farinciki data samu wanda zai aureta taje ta huta itama, sai da Mutallab ya sauke shi har wajen rumfar shagonsa na shayi da mutane ke zazzaune suna jiransa haɗe da fiddo kuɗi masu yawa dako tsayawa ƙirgawa baiyi ba ya miƙa masa yana godiya, murmushi Isah yai haɗe da karɓa yai masa godiyar shima sannan ya tada motarsa yabar wajen yana jin wani farinciki aransa. **************    Meenal kuwa tunda Mutallab suka tafi gidanta ya koma wata madaddalar daba da ƙawayenta su Sarsy ke zuwa su nake a dafa mai kyau aci asha a ƙoshi sannan a saka kiɗa da waƙa ayita casu, abun na samun Jabir sosai saboda yadda suke samun mutane da kiɗa har lokacin Sallah amma bai taɓa cemata meyasa ba saboda ganin take-takenta akansa, gashi kullum yana ganin yadda Umma ke shiga da fice acikin gidan baya don ya sake yin wani laifi da yayan nasa zaiyi masa faɗa akanta. Sosai ta sake komawa Meenal ɗin asali tasha kitson attach da ƙumba, ga wani shegen haske data sakeyi tamkar ba ita ba, kallo ɗaya zaka yimata kagane hasken bleaching ne banata na asali ba, haka ma duk lokacin da taso fita jan motarta takeyi tafita hankali kwance cikin shigar da duk tayi aya daɗi, bazaka taɓa kallonta ba kace matar aurece dan mayafin da take sakawa sam baiyi kama dana matar aure ba, Mommy tayi faɗa da ita har ta gode Allah amma kamar tana sake zugata dan cewa tayi bata isa ta takurata a gidan ubanta ba kuma tace zata takurata gidan mijinta ba, duniya takoma mata sabuwa ganin koda yaushe account ɗinta cike yake da kuɗi kuma tana damawa yadda take so kasancewar ta amshi sunan matar babban hamshaƙin mai kuɗi acikin garin da babu mai iya takata saboda alfarmarsa data shiga ciki. Yau ma tana zaune ita dasu Sarsy an baje abinci da snacks da drinks a palour suna shan fruit Asiya ƴar Umma ta shigo ita da Jiddah, wani kallo suka bisu dasu Meenal ta miƙe tana faɗin, "Nayi fushi amarya wato sai yau zaki zo gidana." Tayi masu iso zuwa can ɗaya palourn saboda yadda take karramasu saboda Umma da take ganin ta ɗauketa tamkar ƴar data haifa a cikinta, shiyasa take sonta itama da duk wani abun ɗaya shafeta, murmushi Jiddah da tayi wani irin duhu tamkar ba ita ba saboda baƙincikin da take fuskanta a gidan  AAB tayi tana cewa, "Aunty Meenal kenan ai dole na kama kaina tunda bakwai da irinmu talakawa." "Kai Jiddah wannan wane irin zance ne, kema dai ai mai arzikin kike aura balle kice, ya gidan da Ummata." "Duk suna lafiya". Tafaɗa tare da tasowa ta dawo palourn dasu Sarsy suke ta ɗibi snacks dasu drink ta kai masu sannan suka zauna sukaci gaba da fira, da zasu tafi ta budewa Jiddah store tace ta ɗebi duk abinda takeso sannan sukayi sallama tana cewa Asiya da sukayi zancen zata kwaso kayanta ta dawo nan kada ta manta tana jiranta. #Mutallab Asad #Ƴan tagwaye #Nana Diso #Billy s Fari. MUTALLAB ASAD   (labari mai taɓa zuciya) Na Billy s fari Nana diso      RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU.    TAFIYAR BIYU TAFI DAYA   SHAFI NA SABA'IN DA TAKWAS Bayan ta dawo daga wajen rakiyarsu ne Nancy ta kalleta haɗe da taɓe baki tana cewa, "Sannu uwar son miji! Wai Meenal anya kanki ɗaya kike wani rawar jiki akan ƙannen miji sai kace uwarku ɗaya ubanku ɗaya dasu kina wani washe masu baki". "Barta Nancy Ashe kema kin lura da rawar ƙafar da takeyi akansu mu kuma tabarmu a wulaƙance dan renin hankali, kayan daɗin namu ma duka ta kwashe ta miƙa masu sai kace wadda taga ƙannen su Mahmah." Dariya Meenal tayi bayan taƙaraso wajen ta zauna haɗe da cewa, "kufa ƴan is.. ne wataran, yanzu duk meye na wannan surutun naku? Yaran nan ƴan uwansa ne mahaifiyarsu na soma tare da ganin ta taimakeni, don me ni kuma bazan so yaranta ba?" "Hmm aikuwa indai dangin mijine watarana sai sun saki kuka ɗan wallahi zuciyarsu ba mai kyau bace, kaɗan ne zasu so matan ƴan uwansu da zuciya ɗaya ɗan haka tun wuri ƙara ki farka ki dawo daga rakiyar munafukan banzar." "A'a Sarsy ni dangin mijina ba munfukai bane, dan haka kidena faɗar maganar banza akansu bazan ɗauka ba wallahi." Ta ƙare zancen tana haɗe rai tare da ɗauke masu kai, Zaro idanuwa Sarsy tayi cike da mamaki tana kallonta kafin takalli Nancy su taɓe baki tare cike da mamakin Meenal ɗin tace, "Allah ya baki haƙuri daga faɗar gaskiya". Cikin ɗan fushi Meenal na watsa hannu ke cewa, "To bana so Malama." Hannu Nancy ta ɗagawa Sarsy alamun kar ta sake tankawa haɗe da cewa, "Kinga ya isa haka Sarsy, Meenal yi haƙuri mubar zancen yanzu ya za ayi?" Juyowa Meenal tayi tayi mata wani kallo kafin tace, "dame kenan!" Idanu Nancy ta kashe mata kafin tace, "Wancan zancen mana." Shiru Meenal tayi tana nazari sannan tace, "karku damu babu damuwa bari nakirasa naji". Taƙare zancen tana jawo sabuwar wayarta dal data sake iphone 14, lambar Mutallab tajanyo tayi dailling thaɗe da karawa ga kunnuwa, dai-dai lokacin yafito cikin shirinsa cike da farinciki zai je ya haɗu da Aïcha, dan jiya daya dawo yaiwa tánte bayani akan komai, da farko bata bashi goyon baya ba akan  zancen ko kaɗan duk da tasan tarin matsaltsalun da yake ciki saboda ganin auren nasa duka duka ba'a fi wata biyu dayi ba kuma yanzu ya ɗauki zancen zai ƙara wani auren, bayani ya zauna yayi mata sosai akan dalilansa nason ƙara auren da kuma ko wacece Aïcha sannan ta goya masa baya tare dayi masa fatan alkhairi, hakan ya sashi kwana cikin farinciki cike da tarin mafarkan Aïcha har garin Allah ya waye yana mai ɗokin ganinta da kuma haɗuwa da ita, dai-dai lokacin daya kawo bakin ƙofar shigowa palourn dasu tánte ke zaune suna fira ita da Afrah ya ɗaga kiran yana kai wayar a kunnensa. "Mutallab". Yaji Meenal tafaɗa kai tsaye babu wani saya sunan nasa wanda hakan ya sashi runtse idanuwa yana ƙarasa shigowa ciki ya zauna akan ɗayar kujera yana miƙe ƙafafuwa haɗe da saurarenta ba tare daya tanka taba, "ina son million ɗaya ne akwai bukukuwan ƙawayenmu da zamuyi ni dasu Sarsy kuɗin dake account ɗina kuma basu kai ba." "Nawa ne aciki?" Ya amsa mata ataƙai ce yana danne ɓaci ran dake taso masa, wato Meenal indai ba buƙatar kuɗi take da ita ba bazata taɓa kiransa ba, jin yai tace, "dubu ɗari biyu kacal ne suka rage aciki kuma kasan dole zanyi wasu lalurorin na cikin gida." "Ok zan turo maki five hundred thousand sai ki ƙara dasu." "Kamar ya Mutallab! One million nayi requesting ko naka ji ba ne?" Tafaɗa cikin fushi saboda ganin yana neman rena mata da wayau, runtse idanuwa yai yana murza saman goshinsa kafin yace, "su nake iya bayarwa saboda lalurarki itace dole aguna bata ƙawayenki ba, idan bakya so zaki iya maido mani da abina idan na turo maki". Yana kaiwa nan ya kashe wayar ransa a ɓaci yana jefawa cikin aljihu tare da jan ajiyar zuciya ya sauke, "Mutallab lafiya?" Tánte tafaɗa tana kallonsa, sake sauke wata ajiyar zuciyar yai haɗe da cewa, "Meenal.." bai ƙarasa ba tánte tace, "Allah ya sawaƙe sai ka ƙara haƙuri dama lamarin iyali shi haka yake, akawo maka abinci". "A'a tánte, ina dai ita Afrah ɗin in ta shirya tafito muwuce". Yana rufe baki tafito sanye da wata jar atamfa ɗinkin riga da sket da suka matuƙar karɓar jikinta ta yafo mayafinta a saman kafaɗa, "Barka da rana ya Mutallab". Tafaɗa lokacin data ƙaraso wajen shi kuma yana miƙewa, amsa mata yai fuskarsa ba walwala ya wuce gaba ta bishi baya tana yiwa tánte sallama tare da gyara ƴar ƙaramar handbag ɗinta dake kafaɗarta. Gidan Dada suka nufa dan tun ranar da suka iso garin da suka biya basu sameta ba basu samu damar komawa ba shine yau da safe takirasa tana faɗa ya bata haƙuri akan zasu zo zuwa anjima, shine yasa Afrah ta shirya su fara wucewa can sannan yawuce inda zai je, sama-sama yake amsa firar da Afrah keyi masa dan gabaɗaya Meenal ta riga data gama ɓata masa mood, ganin haka yasa takama bakinta tayi shiru har suka iso gidan Dada ta ɓalle marfin motar tafito da gudu ta shige ciki shi kuma yabo bayanta bayan ya rufe motar, suna shiga ta rungume Dada ta baya tana cewa, "Oyoyo Dada missed you so much." "Ke dalla ni cikani karki ɓallani, wane missing ɗin a kikayi kin je can kin tare abinki gun yayanki ko tunani bakwai". Ɗora kanta tayi ta gefen wuyanta haɗe da cewa, " Kai Dada gidanki fa muka fara sauka bakyanan." "Kudai kuka sani keda yayan naki." Sallamar Mutallab yasa Dada juyowa tana sauke masa harara, murmushi Mutallab ya saki yana sosa kai cikin jin kunya haɗe da cewa, "Allah ya baki haƙuri ranki shi daɗe dama fa yau zamu zo sai gashi kinyi magana." "Kafaɗa ai, sannu ku da zuwa." Taƙare zancen tana masu iso zuwa cikin palounta, bayan sun zauna suka shiga gaisawa tana cewa, "ina kabaro kishiyar tawa ai na aza tare da ita kuka zo." "A'a Dada tana gidana bari kar kice nayi laifi na zomaki da ita". Ya ƙare zancen cikin sigar tsokana irin ta kaka da jika, murmushi tayi sannan tace, "Laifi kuma na nawa tunda ka riga ka aureta, nayi kishi har na gaji na haƙura." Duk suka sa dariya yai gyaran murya haɗe da cewa,

Chapter 44 of 54