da Mahmoud ɗaya kaisu airport ɗin, suna isowa gida saƙon massage ɗin Meenal na shigowa wayarsa ya shiga karantawa.
_Tabbas da zan iya cire soyayyarka a zuciyata ya Mutallab da nayi hakan saboda na tabbata baka sona har cikin zuciyarka, sai dai bazan iya ba saboda da zuciya ƙwaya ɗaya nake sonka, Allah ne ya jarabceni da soyayyarka kuma na tabbata har na mutu kamar yanda mahaifiyata ta mutu jiya bazan dena sonka ba, ina yimaka fatan nasara ya Mutallab tare da fatan alkhairi acikin rayuwarka, ba lallaine kadawo ka iskoni a raye saboda ina jin nima tamkar zanbi mahaifiyata ne namutu nima._
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun". Shine kalmar da Mutallab yafaɗa yana jin tausayin Meenal a zuciyarsa a karo nafarko rayuwarsa, yasan ɗacin rashin uwa, ya kuma san mukin da ake ji a zuciya tunda shima ya rasa tashi mahaifiyar, hakan yasa ya lalubo lambar Aryan, bugu ɗaya ya ɗaga yana zolayarsa kamar yanda ya saba da babban yaya, murmushi kawai Mutallab yai kafin yace, "Da gaskene Meenal tarasa mahaifiyarta?"
"Sosai Mutallab naso nakiraka nafaɗa maka wallahi amma sanin da nayi baka buƙatar maganarta yasa ban sanar dakai ba, idan kaga yarinyar nan yanzu Mutallab wlh su ka tausaya mata, she need support from everywhere wlh".
"Allah yajiƙan iyayenmu da dukkanin musulmi".
"Amin ya rabbi MAM, ya matata.." kafin yaƙarasa Mutallab yace, "Ai tun ɗazu nayarda ƙwallon mangwaro yau nahuta da ƙuda, Flight ɗin su bai jima da tashi ba dan daga wajen dawowa kaita muke".
"Woo..gaskiya am happy ka biyani, fisabilillahi nayi kewar masoyiyata har nagaji amma saboda rashin tausayi ka riƙe mani ita sai yau"
"Ehm, inaga kamanta da babban yaya kake magana, sai nafasa bada auren ƙasar yawa naga yanda za'ayi tunda abun babu girmamawa". Mutallab yafaɗa yana murmushi, haƙuri Aryan ya bashi kafin sukayi sallama, sau uku yana kai hannunsa ga lambar Meenal zai kira amma yakasa, sai ana hudu ne ya daure ya danna lambar, bugu ɗaya ta ɗaga tana fashe masa da wani irin kuka mai tsima zuciyar duk wanda ke sauraro, kukan damuwoyi biyu ne ke fitowa daga ƙasar zuciyarta, nafarko na rashin mahaifiyarta, na biyu kuma kewar Mutallab dake nuna mata rashin so da kuma kulawa, runtse idanuwa yai yana jin kukan cikin ransa da hango irin tashin hankalin da take ciki, kafin cikin taushin muryar da bai taɓa tunanin yana da ita ba yafara magana ta sigar lallashi da kuma ban haƙuri ga wanda akeyiwa maganar.
"Dukkanin mai rai mamaki ne Meenal, mutuwa ƙaddararriyar abuce da babu wanda ya isa ya kauce mata aduniya, dake dani da kowa ma duk ita muke jira, nasan akwai zafi da ƙuna da raɗaɗi marar misaltuwa game da rashin mahaifiya domin nima na rasa nawa, amma ina so ki ɗauki hakan jaraba rayuwarki ne Ubangiji yayi ta hanyar ɗauke maki ita, kiyi mata addu'a sosai, ki kuma kaucewa yin duk wani abu marasa kyau dazai iya janyo atada ita anuna mata abinda ƴarta keyi, sorry for the lost Meenal, Allah ya jiƙanta ya kuma gafarta mata".
Bata iya amsawa ba sai kukan da takeyi kawai tana sauraronsa har ya gama ya kashe wayar saboda kasa amsa mashi ɗin da tayi...
#Mutallab Asad
#Ƴan Tagwaye
#Nana Diso
#Billy S Fari
MUTALLAB ASAD
(Labari mai taɓa zuciya)
Na Billy s fari
Nana diso
RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU
TAFIYAR BIYU TAFI DAYA
SHAFI NA ARBA'IN DA TAKWAS.
Tunda ya ajiye wayar gabaɗaya sai yashiga tunanin lokacin da shima ya rasa tasa mahaifiyar, bai samu mai rarrashin sa ba sai shine yakasance mai rarashin ƴan uwansa. Sautin kukan nata dake fita a ɗazu ne ya shiga dawo masa cikin kunnuwansa, wayarsa daya ajiye agefensa ya kallah yasa hannunsa ya sake ɗauka yana mai ƙara dialing ɗin number ɗin meenal, bugu ɗaya ta ɗaga cike da farinciki dan abune da bata taɓa tsammanin faruwarsa ba ko a mafarki daga garesa, ganin kiransa na farko yasa duk wani bakinciki da damuwar da take ciki kwana biyu ya kawar mata, cikin sanyin muryar da tagama gauraya da kuka tace, "Yayana dan Allah kayi haƙuri idan na dameka.." bata ƙarasa maganar tata ba yaɗan lumshi idanuwansa sannan yaja iska a hankali yace, "Is ok Ƙanwata ba damuwa?" cikin farinciki ta amsa masa da "To yayana nagode." "Ba komai amma wannan kukan naki bashida amfanin yi musamman ga wanda ya mutu, kiyi haƙuri kicigaba da yiwa mamanki addu'a shine abunda take bukata agunki." "Ina sha Allah nadaina bazan koma ba yayana." Sake kwantar da Muryarsa yau ta sigar rarrashi haɗe da cewa, " kinci Abinci?"
"Ai bazan iya cin komai ba yayana".
"No daurewa zakiyi ai, yanzu kitashi ki haɗa ko tea da bread ne kisha anjima da daddare zankiraki". Faɗar murnar datake ciki bazata taɓa iya lissafuwa ba hakan ne yasata amsa masa cike da godiya yai murmushi kafin ya katse wayar yana ganin tabbas yanzu yayi abu mai kyau dan duk wanda yace yana sonka tofa yagama maka komai acikin rayuwa, ganin lokaci yana ɗan ja yasashi miƙewa yayi wanka dan zaije yaga ginin da yafara anan yau, dan kawunsa da Mahmoud sun bashi shawara akan yai ginin yafi masa sauƙi tunda yana da hali akan ya ɗauki hayar shaguna ya kuma zauna shima yai nazari yaga haka ɗin yafi masa sauƙi.
Meenal ko tun daga saman benen da take saukowa take ƙwalawa Mommy kira, Dady dake aiki a system ɗinsa Kamal na a gefensa zaune yana masa bayanin fara kasuwancin da yake so zaiyi sukajiyo ihunta, hakan yabasu damar duk juyawa suna kallonta tare da jin wani sanyi cikin zuciyoyinsu saboda farincikin da suka hango kwance akan fuskarta, dan rabon da Meenal tayi irin wannan murnar har sun manta, Mommy ce tafara miƙewa tana faɗin, "Babyta menene?" Rungumeta Meenal tayi tana cewa, "Mommyna Mutallab yakirani yanzu yayi mun gaisuwa, kinsan me Mommy ya bani kula a wannan lokacin sosai fiye da tsammani, he even called me ƙanwarsa ya kumace na daina kuka, kin san me yafi farantamun Mommy". Mommy da fuskarta ke cike da farinciki ta girgiza mata kai tana murmushi, kwantar da kanta Meenal tayi a saman kafaɗarta haɗe da cewa, "yace nasamu naci abinci anjima zai kirani" Cikin jindadi Mommy tace, "Masha Allah, kice yau mun tashi da sa'a Meenal, da alamu kuma Addu'ar mu ta karɓu a wajen Allah".
"Wallahi Mommy, zan ƙara dagewa da addu'a na kuma sake maida hankali ga ibadata".
"Hakan yayi sosai Meenal, amma ina fatar ko ba dan ki samu soyayyar Mutallab ba zamuci gaba da kiyaye ibadarki ko?
"Sosai Mommy, kinga addu'ar ma da kika bani ta istikhara nayi tun kafin Mahma na tarasu, sai naji na samu natsuwa sosai wlh"
"Masha Allah my Baby Allah yasa da gaske kikeyi". Mommy tafaɗa tana tsureta da idanuwan dan tabbatar da gaskiyar lamarin, murmushi Meenal tayi haɗe da cewa, "da gaske fa Mommyna, bari ma nakaranta maki ita saboda zaunawa nayi na haddace ta,
اَللّٰهُمَّ إِنِّيْ أَسْتَخِيْرُكَ بِعِلْمِكَ، وَأَسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْأَلُكَ مِنْ فَضْلِكَ العَظِيْمِ
فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلَا أَقْدِرُ، وَتَعْلَمُ وَلَا أَعْلَمُ، وَأَنْتَ عَلَّامُ الْغُيُوْبِ
اَللّٰهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هٰذَا الْأَمْرَ
(SAI AAMBACI BUKATA ADAIDAI NAN WALAU MIJI KIKA SAMU KIKESON KIYI SAI KI AMBACI SUNANSA KOKUMA KASUWANCI ZAKI FARA KOMA DAI MENENE NAN NE DAIDAI GURIN AMBATAR BUKATA)
) خَيْرٌ لِيْ فِيْ دِيْنِيْ وَمَعَاشِيْ وَعَاقِبَةِ أَمْرِيْ، فَاقْدُرْهُ لِيْ وَيَسِّرْهُ لِيْ ثُمَّ بَارِكْ لِيْ فِيْهِ
وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هٰذَا الْأَمْرَ شَرٌّ لِيْ فِيْ دِيْنِيْ وَمَعَاشِيْ وَعَاقِبَةِ أَمْرِيْ فَاصْرِفْهُ عَنِّيْ وَاصْرِفْنِيْ عَنْهُ وَاقْدُرْ لِيَ الْخَيْرَ حَيْثُ كَانَ، ثُمَّ أَرْضِنِيْ بِهِ
Allah Mommy naga amfaninta sosai dan duk da banji soyayyar Mutallab tafita cikin zuciyata ba tunda addu'ar naji cewa koda Mutallab bai amince da soyayyarta ba akaro na biyu zan iya haƙura dashi, amma soyayyarsa har ina mutu bazata fita a zuciyata ba da kuma tuhuma, shiyasa yanzu ma na daina addu'a ina fadin Allah ka mallakamin Mutallab sai dai nace Allah ka tabbatarmin da Alkhairinsa saboda yafini sanin yadda nakeson Mutallab, nakan roƙesa nace idan ba Alkhairi bane kuma arayuwata ka ciremun sanshi gabaɗaya, nayiwa Allah alƙawarin na daina rashin kunya Mommy dama komai in Sha Allah, kuma kema ina riƙon ki yafemun abubuwan dana yimaki Mommy?"
Ajiyar zuciya Mommy taja ta sauke tana girmama hukunci da hikima irin ta ubangiji, tabbas mai haƙuri yakan dafa dutse har yasha romonsa, wai yau Meenal ce da bakinta ke roƙonta ta yafe mata! Murmushi tayi tana yiwa Allah godiya acikin zuciyarsa kafin tace,"Ya Allah Nagode maka daka shirya mani ƴaƴan bisa kyakkyawar tarbiyar da kake so, na amince shiryarwa a hannunka take ba a hannunmu ba, ya Allah kacigaba da shiryar mana da al'ummar musulmi baki ɗaya, Meenal na yafe maku har abada dan dama can ban taɓa riƙeki ba a raina, duk fushin da kike ganin ina nunawa saboda naga kin fahimci duniyarki da inda gobenki zata kasance." Dady dake sauraronsu ne wani farinciki na rufesa yayi saurin goge hawayen da suka zubo masa yace, "baby abinci fa".
"yanzun nan zanci Dadyna saboda Yayana yace in daure naci.
Domin Dady yaƙara faranta mata yace, "gaskiya mungodewa yayan nan naki sosai dan kuwa kwanan nan biyu yunwa ta wahalarmin da ƴa". Kamal dake gefensa zaune yana latsar waya ya ɗago kai yana cewa, "Nidai Allah ya rabani da wannan irin soyayyar taki Meenal, wannan ai ciwon so ne ya cimmaki ko kuma muce ƙaddararriyar soyayya ke damunki ta son maso wani". Ƙafafuwa Meenal ta shiga bubbugawa haɗe da taɓe baki zatayi kuka tana kallon Dady tace, "Dady ka ganshi ko?" Dady ya kalleshi yana ɗan ɗaure fuska haɗe da cewa, "Menene haka Kamal? kai baza ka dinga jan girmanka bane tare da yiwa ƴar uwarka fatan alkhairi ba?"
"Wallahi Dady abunne da ban tsoro, kaga fa tazama mahaukaciya gaba..." kafin ya ƙarasa Dady yace, "zan ɓata maka Kamal, kai da yakamata kana dinga lallaɓata tare da tayamu rarrashinta kuma kaine mai neman birkice mana ita tare da tsokanarta?" Hannayensa ya ɗaga sama alamun surrender haɗe da cewa,
"Nadena Dady kayi haƙuri bazan koma ba, Meenaluwa ta Mutallab kema kiyi haƙuri kinji ko!" Duk suka saka dariya kafin nan Meenal ta nufi dining domin cika umurnin masoyinta.
*******
Cikin matsanancin kuka Aunty Amarya ke cewa, "Yanzu hajiya haka zandinga rayuwa kullum ina cikin ƙuryar daƙina? Shikenan na zama hoto acikin gidan mijina duk yanda nake buƙatarsa sai dai na haƙura, gabaɗaya banda ikon zuwa na tunkareshi a matsayin mata sai zaginsa hantara su biyo bayansa wannan wane irin bala'ine haka Hajiya? Don Allah bazaki iya wani abu saboda takai takawo fa ko magana bayamin, ga Walid yagama makaranta cigaba yana neman gagara daman haka akeji? Yanzu haka su Mutallab sukayi haƙurin rayuwa? Sai yanzu nake nadamar biyewa matarnan akan abubuwan da mukayiwa yaran su da mahaifiyarsu, ashe a keken ɓera munafukar ta sakani nima tana da mugun nufi akaina da kuma yarana, wayyo Allah na innalilahi wainna illahirrajiun na shiga uku Hajiya ki taimake ni, wallahi rannar da bakin tace idan banyi hankali ba takusa ta sakashi yabani takardar sakina, hajiya wallahi ko motsin kirki bayayi agabanta ta mayar dashi dolo, sauna matsoraci dan yanzu Alhaji yawuce akirasa da mijin tace ko mijin Hajiya dan hatta da numfashinsa sai anga dama ake barinsa yafiddashi daidai, yana kallo abinci ma sai an zuba an ƴan mana amma yakasayin komai, gashi nakoma tamkar ƴar aikinta ba damar in taɓa komai agidan Shikenan sai ta rufeni da faɗa, su walid basuda ikon gaisawa da mahaifinsu tamkar bashi ya haifesu ba, daga Jamil sai Jidda da wannan bazawarar yarinyar data dawo tana zuba iskanci kala kala agida sukaɗai ne yaransa yanzu sai nagidan auren da suma yake jinsi kamar rai hajiya"
"Hazbunallahu waniimal wakeel, Amarya wannan mahaifi sunyi yawa kuma maganar gaskiya bansan yaya zanyi ba wallahi, kina ganin har ƙauye naje miki wajen wani malaminko za'a dace amma abin yaƙi yihuwa, Nifa tun ina daukar lamarin kishiyar nana taki da wasa har abun yafara bani tsoro wallahi, kina gani fa duk mun ƙarar da ɗan kuɗaɗen mu agurin malamai amma abun ba biyan buƙata, ni dai idan zakibi shawara amarya muzubar da kayan yaƙinmu mukoma ga Allah, ki dage da Addu'a mubar batun malaman nan wallahi kadanne na Allah sauran duka sun taɓe abokan taɓewa suke nema da zasu shiga wuta, ni kuma yanzu naji tsoron Allah bazan yarda naci gaba da binsu ba". Aunty Amarya na sharar ƙwalla tace, "Haba Hajiya al'amarin matar nan fa yahuce.."
"Ke dakata mun dan Allah kiyi shiru, akwai abunda yafi karfin Allah ne arayuwa? Nifa bazan koma yarda ba ki jawomin taɓewaba ba gaira ba dalili, na gama da aurena ba boka ba malam ace sanadiyar naki auren nazo narabu da Allah, na gayamiki ki koma ga Allah ban iya masifar nan take can taƙarasa ita da Allah, shikenan wai rayuwar aure tazama sai da bin malamai da bokaye? to idan bazaki dage da Addu'a ba kije kiyi da kanki nidai kibarni na haɗu da Allah lafiya a cikin sauran ƴan shekarun da suka rage mani aduniya, ina dalili ko angaya miki jahila nake har yanzu bayan nafarka daga baƙin mafarkin da kika jefani yi a matsayina na mahaifiyarki kinsa sai faman yawon gurin malamai nake sallolina suna ajiye ba'a karɓa fisabilillahi ina dalili, malami ya isa yayimun abunda Allah bai yimun ba ne? To bari kiji ya isa haka, kije kitubarwa Allah ki zauna lafiya a rayuwarki, ta Allah da kike gani shike tabbata karki yadda akan soyayya ki koma ɓata lahirarki abanza a wofi, ita kishiyar taki ki tsaya kiga yadda ƙarshenta zai ƙare mana ita data cire Allah a zuciyarta" sake tashi hankalin Aunty Amarya yai ganin tabbas yanzu bata da wani zaɓi banda haƙuri acikin yanayin data tsinci kanta agidan mijin nata, ɗan haka sai ta sake saka mata wani kukan wanda hakan yasa Hajiya ta kashe wayarta tana bambamin ita kam daga yau bata ba turbar sheɗan da yardar Allah.
********
Idanuwa ya zubawa mutumin dake zaune ne da malummalum yana gyara zaman rigar tashi tare da kaɗa kasar gabansa yana kauda kai gefe. "malam lafiya?" Ya faɗa hankali a tashe yana kallon wanda ke gefensa shima yana wurgowa malamin kwatankwacin irin tambayar daya jefo masa kafin suka maido kallonsu ga malamin atare, wasu duwatsu malamin ya sake watsawa a saman ƙasar dake gabansa kafin yace, "sai dai kuyi haƙuri da yaron nan dan har yanzu abu ɗaya da nake gani idan na buga wannan ƙasar shine nasarar mutumen nan, wannan mutumin bazamu iya aiki akansa ba bayan addini da yake dashi kuma tsaye yake gurin addu'a dan haka aikinmu bazai samu gurin zama ba ajikinsa ba, amma shi ƙarin nasa yanzu da kuka sanar dani na riga dana fara aiki akansa kuma munyi nasara sosai, yanzu haka sanadiyar rashin lafiyar da yakeyi ibadarsa tayi rauni wanda hakan yasa mun haɗashi da aljanar da zata shiga jikinsa tariƙa tsotse masa jini ahankali za'a kasa gane inda abun yake, zasu je asubiti ace maleria daga nan dai zasuyita fama amma su kasa gane matsalar har ya mutu". Dariya sukayi dan sunsan Jalil shine ƙashin bayan kasuwancin Mutallab kuma ɗan uwansa da yake matuƙar so, yana mutuwa komai zai lalace masa akasuwa kuma adawa gane kansa saboda rashin Jalil ɗin balle har yai kasuwanci, kallon malam yai yace Amma malam ka gama biyanmu wallahi ai daman shiyasa nakawo zancen ɗan uwan nasa dan nasan ana taɓasa sai yafi jin raɗaɗin fiye ma damuyi aikin akansa, yanzu ga cikon aikinka ka sauraremu tafe da tukuici". Malam yasa hannu yakarɓi maƙudan kuɗin da suka nuna masa sannan suka miƙe suna jin wani irin farinciki a zukatansu.
#Mutallab Asad
#Ƴan Tagwaye
#Nana Diso
#Billy S Fari
MUTALLAB ASAD
(labari mai taɓa zuciya)
Na
Billy s fari
Nana diso
RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU.
TAFIYAR BIYU TAFI DAYA
SHAFI NA ARBA'IN DA SHIDA.
Kallonta Kamal yai kafin yace "To Shikenan Sarsy, Allah ya kyauta amma ita tuba ba'a jinkirinta Sarsy, sannan duk wani namiji da kike gani a bariki wallah tallahi yana da ilimi ɗaiɗaiku ne kawai jahilai acikinsu akan sani suke aikata komai, fata dai Allah yakawo mana shiriya muduka".
"To Amin Sarsy" ya faɗa yana juyar da kansa zuwa ga sitarin motar yana ƙoƙarin tada ita, ƙarar kiran daya shigo a wayarsa ya dakatar dashi tare da saka hannunsa ya ɗauki wayar dake kan dashboard ɗin motar haɗe da ɗagawa yana karawa akunnensa, "Hello Kamal kayi maza kayi gidan kakannin ka Mahaifiyarka Allah yayi mata rasuwa yanzun nan". Gabansa ne yayi wata irin mummunar faɗuwa ya ciro wayar daga kunnensa yana duba lambar, bai san ma kowaye yakirasa yana yimasa wannan mummunan albishir ba Saboda lambar babuta acikin jerin lambobinsa, a rikice ya kalli Sarsy yana cewa, "Kin ga fita-fita gidan grandama zanje yanzun nan, I can't believe kawai akirani ace wai Mahma tarasu bayan ɗazu nagama waya da ita, fita mana nace". Ya ƙare maganar da ƙarfi ganin Sarsy ba tada biyar fita cikin motar, ba shiri ta buɗe marfin motar tafice shi kuma ya fizgi motar da ƙarfi jikinsa na rawa ya nufi gidan grandama. Yana gab da kaiwa wayarsu tayi ƙara ya ɗaya ganin lambar dadynsa ce, kafin yace komai Dady yace, "Kamal kana ina ne?"
"Gani nazo anguwarsu Mahma Dady kirana akayi wai Mahma tarasu". Ya kasa ƙarasa maganar haɗe fashewa da kuka yana taka wani irin wannan burki ganin ƙofar gidan grandama ɗin tasu cike da mutane, wanda hakan ya tabbatar masa da cewa gaskiya ne mahaifiyar tasu ta rasu.
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun dady da gaskene wlh". Yafaɗa yana saka wata irin ƙara tare da faɗuwa gaban motar tashi daya fito yana ƙoƙarin shiga ciki mutanen dake wajen sukayi kansa aka ɗauke da akayi ciki dashi don ya some.
Mommy dake zaune gefe sai da jikinta yashiga rawa ganin yanda Dady ya zabura yana kiran sunan Kamal ɗin da yaji yai ƙara cikin wayar, a ɗaya ɓangaren jikinta ya mutu sosai jin da tayi Allah yayiwa Mahma rasuwa.
"Innalillahi mun shiga uku, a'a Dady wallahi Mamah bata mutuba, ko awa ɗaya fa bamuyi da gama waya da ita ba, taya za ace ta mutu". Meenal da saukowarta kenan tafaɗa tana ƙoƙarin faɗuwa da sauri Dady da Mommy sukayo kanta Dady ya riƙota yana cewa, "Calmdown my Baby mutafi gidan mugani ƙilan ba gaskiya bane kinji ko". Yafaɗi hakan duk da kuwa yana da tabbacin akan mutuwar Mahma ɗin tunda ƙanwarta takira ta sanar masa, Mommy dake faman salati Dady yace ta shiga yaje ta ɗauki wa Meenal hijjabinta itama ta ɗauki nata su tafi, cikin mintuna biyu ta dawo saye da Hijab da wani a hannunta Dady ya taimaka mata tasaka mata sannan suka fita daga gidan da taimakon driver daya tuƙasu Meenal kuwa ta rungume Mommy sai kuka takeyi, sadda suka ƙarasa gidan sun samu har lokacin Kamal daya suma bai farfaɗo ba, haka grandma itama batasan inda hankalinta yake ba, Meenal ɗin ma suna shigowa ta zube ƙasa a some, wannan ya matuƙar tayar da hankalin Dady gabaɗaya yabo duk ya ruɗe, ɗaya daga cikin kanwar Mahma ce tace,
"Wallahi Dadyn Meenal lafiya kalau muka kwana da ita muka tashi, da safennan ma anan ta zauna munata hira da ita sai take cewa bari taje ta huta, Shikenan fa grandma na shiga ɗalinta ganin har anyi sallar la'asar bata fito ba ta iskota a sheme ƙasa babu rai muka ɗauke ta muka je asubuti, likita na dubawa ya tabbatar mana da cewa ta mutu". "Allah yajiƙanta yai mata rahama yasa can tafiye mata nan". Dady da hankalinsa ke matuƙar tashe yaɗa dan hankalinsa nakan yaransa da ake kansu sun some, Kafin kace komai dangi da ƴan uwa da abokan arziƙi da kuma sauran al'ummar musulmi sunyi dandazo a ƙofar gidan, nan akayimata wanka, aka yimata suttura aka sallaceta sannan aka ɗauketa zuwa gidanta na gaskiya, yadda Meenal ke ihu tana kuka tana faɗuwa da za'a fita da gawar Mamah indai mutum nada imani dole sai ya tausaya mata, Kamal daya farfaɗo aka sallaceta tare dashi aka kuma kaita ya riƙata aka sakata a kabarinta suna dawowa ya sake yanke jiki ya faɗi ƙasa a some, ruwa aka yayyafa masa ya farfaɗo yana fadin "astagfirulla Allah natuna, Allah bazan ƙara aikata Abunda ka haramta ba, Allah na dena nayafe mani". Haka yayita maganganu kala-kala yana tubarwa Allah, ganin yadda daga shi har Meenal suka rasa natsuwarsa yasa Mommy ta shiga lallashinsu tare da nuna masu suyi haƙuri tunda akwai mahaifi Allah yabar masu a raye, wasu duka Allah ya karbar masu uwa da uba kuma dole haƙurin sukayi tunda ba yanda zasuyi, ƙanwar Mamah ce da basu fiye shiri da Meenal ba lokacin saboda tana faɗa masu gaskiya ta kalli Meenal tana cewa, "Irin wannan ranar ce nake duba maku Meenal akoda yaushe shiyasa kullum nake nuna maki ki natsu kidaina abubuwan da kikeyi saboda kina da gatar uwa da uba da suka sakantaki, yau gashi nan babu Mamah wacce bakya kauna din itace tsaye tana lallashinki, a rayuwa bakasan gawar fari tsakani ka da mutane, yima dan Adam wulakanci ba abu bane mai kyau ko aibata shi, bawai ina jin daɗin rashin ƴar uwata bane shiyasa nake gaya maku wannan maganar, na tabbata zatafi tasirine a zuciyarki yanzu shiyasa nake faɗa maki ita, kai kuma Kamal da bakada aiki sai ɗaukar mata club da joint ya kamata ka natsu kasamu mata kayi aure idan shi kake so, hakan zai bawa Aunty Maryam salama akabarinta, kada kubari kuɗin zuciya yaci gaba da ɗibarku har ya zama tana dana sanin barin baya da ƙuri da tayi, kuyi haƙuri dukkanmu ita muke jira sannan wannan kukan da kuke yimata ba kyau kudena, Addu'ar ku kawai take da buƙata a yanzu, ku ɗakko kur'ani ku karanta zaku samu zaku samu natsuwar zuciya da salama, ita kuma Allah ya gafarta mata, Meenal data kasa tsaida kukan tace, "Innalillahi wa inna ilaihirrajiun, yanzu Aunty shikenan bazan ƙara ganin Mamah ba? Wayyo nashiga". Taci gaba da kukan gwanin ban tausayi, shi kuwa Kamal ƙarfafa kansa yai ya miƙa yafita waje sukaci gaba da karɓar gaisuwa.
********
Zaune yake ya kasa zaune ya kasa tsaye sai kai da komowa yakeyi, tun ɗaya samu labarin zaman da Mutallab zai yi da shugaban ƙasar Nijar ya shiga wani tashin hankali, tamkar wani zararre yake cewa, "Yanzu duk wannan gobarar da muka haɗa masa sai daya tsallake, shi wane irin mutum ne da baza'a yi nasara akansa ba, taya zamu zauna takowace fuska yana sake bamu tazara sai lunkuwa arziƙinsa keyi? Dubi fa yadda ake zamanantar da shagunansa da muka saka aka ƙone kenan miliyan ɗaya ɗinmu sunje a banza? Ni bazai yiyu ba wlh idan yasan wata baisan wata ba, ba yana da ƙanne ba? Ai nasan sune weak point ɗinsa a yanzu musamman Afrah, dan haka zamu koma takansu mufara taɓa Jalil yanda duk wani ƙwarin guiwarsa zai sace komai ya tsaya cak yakasa cigaba da business ɗin, idan kuma hakan ya gagara to Shalelen tasa zamu salwanta ma da rayuwa mu jefata agararin da duk safiya zai rika jin yana rayuwa ne tamkar matacce adoron duniya". Ya ƙare maganar yana jinjina kai tare da kwashe da wata irin muguwar dariya ganin plan ɗin nasa ya zauna dai-dai yanda yake so.
(Wannan shine sabon maƙiyi a ɓoye? To daga ina yake? Me Mutallab ya tare masa🤔?"
**********
Tun da sassafe kafin yafita yawuce gidan Abbansu, sai da yayi parking ɗin motar sannan ya nufi part ɗinsa, kaɗan ya rage Jidda data fito ta bangajesa yayi kamar bai ganeta ba, yana ganin yadda take jeho masa harara yayi banza da ita dan yanzu da ita da duk wanda ke gidan in banda Abba bayada lokacinsu, dan ita yarinyar tausayi ma take bashi saboda yadda yaga AAB saurayin nata da tunda yabiya sadakinta tare da kawo lefe yake ɗaukar ta suna fita, ya taɓa ganinta a wani hotel zai wuce kan titin sun fito wajen ita da yaron, babbar damuwarsa kada yazo ma ya yaudareta akasa yin komai dan gidan su yaron ba mutunci ne dasu ba, idan kuma anyi nasara ya aureta ɗin shima wata damuwarce dan sai sunyi kuka da idanuwansa sabodo ahali ne da basuda kirki. Sallama yayi ya tarar da Abba yafito a shirye zai fita, ɗan russunawa yai ya gaishesa ya amsa masa haɗe da cewa, "Yanzu Jalil sai kaga dama zakazo idan ina nemanka? Tun jiya nake nemanka baka zo ba na kuma
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 28 Chapter of 54