"kwantar da hankalinki zan rama maki itama taji yadda kika ji." Nan ma ɗin dariya sukayi Dada ta miƙe tana cewa, "kai dai kasani bari nasa yarinyar can takawo maka ruwa". Afrah tamiƙe itama ta bi bayanta, wayarsa ya ciro yaiwa Meenal transfer ɗin five hundred thousand kamar yadda ya alƙawarta sannan ya shiga email ɗinsa ganin anturo masa saƙo yana dubawa, bakinta ɗauke da sallama ta shigo cikin ɗakin a take Mutallab yaji sautin bugawar zuciyarsa ta sauya a hankali ya ɗago kansa sai dai kanta sunkuye yake a ƙasa, hakan yasa ya ɗan ja tsaki tare jin haushin kansa na ɗagowar da yai yana sake maida kallonsa ga wayarsa har ta duƙa a gabansa ta ajiye ƙaramin tray ɗin dake ɗauke da gorar ruwa da kuma lemu da cup, cikin muryarta mai sanyi da tuni rayuwar yau da gobe ta sake sanyayata tace, "ina wuni?"d'agamata hannu yayi ba tare da ya amsa ba hakan yasa tamik'e ta nufi hanyar fita, ɗago kai yai da sauri da zimmar son ganin fuskarta jin yadda sautin muryarta yake sake hauhawar da bugawar zuciyar sa, sai dai kash! Bayanta kaɗai ya iya gani don har takai bakin ƙofar fita, a can kitchen kuwa kallon Dada Arfa tayi bayan Aïcha ta haɗa ruwan da zata kaiwa Mutallab tace, "Dada ina kuka samo kyakkyawar yarinya haka? Wow gaskiya ta haɗu Dada." "Wai Aïcha! kin ganta nan marainiyar Allah ce, iyayenta sun rasu sanadiyar gobara da sukayi suka barta ita da ƴar uwarta bayan sati Uku itama ƴar uwar tata ta haɗu da tsotsayi ta rasu sanadiyar haɗarin mota, yanzu ita kaɗai ta rage kaf ahalinta, shekaranjiya naje can gidan ƙanen mahaifinta da take zaune na ɗaukota a hannun matarsa dake nema ta lallata mata rayuwa da talla." Afrah da tuni labarin Aïcha ya sata ƙwalla saboda tausayi ta kalli Dada haɗe da cewa, "Allah sarki Dada tabani tausayi wallahi, uwa kaɗai muka rasa Dada mukasha wahalar rayuwa balle ita data rasa duka a halinta, gaskiya na jajanta mata wannan rashin." "Ai Afrah in Sha Allahu tagama shan wahala, amana na karɓota gina ƙanan mahaifinta dan haka bazan bari wani abu ya sake cutar da ita ba, akwai wani tanadi da nakeyi mata azuciyata kawai ki tayani addu'a Allah ya tabbatar, dani da kakarta data haifi mahaifiyarta da kuma shi kawonku na niarmy uwa ɗaya uba ɗaya muke, kinga kuwa keda ita duk matsayinku ɗaya a wajena bazan iya bari wani abu ya cutar da ita ba matuƙar ina raye." "Yawwa Dadata shiyasa nake sonki, Allah ya cika maki burinki." Tafaɗa haɗe da rungumota tabaya tana dariya, daidai lokacin Aïcha ta dawo cikin yaren faransanci ta cewa Dada ta kai masa ruwan ko za'a haɗa masa da abinci ne? Dada tace, "A'a Aïcha ga dai ƴar uwarki nan Afrah ki zubo mata taci kema kuma ki zuba naki kici, bari nake muyi magana da Mutallab ɗin."
"To Dada." Aïcha tafaɗa tare da nufar abincin dake cikin wata babbar warmer ta ɗauki plate tana cewa Afrah, "me zan zuba maki?" Saboda abincin kala biyu ne sukayi dan itama Dada akwai nata da ake dafa mata daban, takowa wajen Afrah tayi tare da jingina wa ajikin carbinan ɗin kitchen tana kallon Aïcha, cikin yaren turanci take sake yabawa kyan da Allah yaiwa Aïcha ɗin duk da ita ɗin ma kyakkyawa ce ta ƙarshe, ɗari kai Aïcha tayi tana kallonta dan bata fahimci ko me take cewa in banda kalmar beautiful data iya fahimtar me take nufi, ɗage mata gira Afrah tayi haɗe da cewa, "1-1 ina kema yanzu kika gama juyewa Dada baki dan kinga bana jin yarenku ko?" Murmushin daya sake ƙawata mata fuska ta saki haɗe da cewa, "Yi haƙuri Adda ba haka bane kawai bakin ne ya riga daya saba ko a'a ne sai mun haɗa dashi." "Ai Shikenan zuba mana tare muci." "A'a Adda kibari na zuba maki mako." "Aïcha zango jin daɗi ki Kur'ani da Afrah saboda shine sunana ba Adda ba." "Ai bazan iya ba kuma sai dai ko babbar yaya tunda kin girman." Tayi saurin sadda kanta ƙasa hawaye na cika mata idanuwa tunowa da ƴar uwarta da tayi, hannunta Afrah data lura da hakan ta riƙo haɗe da cewa, "Sorry Aïcha, Dada tabani labarinki na kuma tausaya maki, ni da yayuna kuma mun rasa mahaifiyarmu tun ina da shekara biyu a duniya, babu wahalar da bamu sha ba amma gashi yanzu komai ya zama tarihi in banda pain din rashin uwa, shima aduk lokacin da muka tuna muna binta da addu'a sai muji sanyi a zuciyarmu, saboda haka krma ki riƙa yin addu'a aduk lokacin da kika tunosu kin ji ko?" Aïcha ta ɗaga mata kai tana share ƙwallan da suka sauko mata a fuska, karɓar plate ɗin hannun nata tayi ta zuba masu abincin duk da Aïcha sai ƙoƙarin karɓar takeyi amma taƙi, anan kitchen suka zauna suka ci Afrah nayi mata hira dan tashi ɗaya taji tana ƙaunar yarinyar aranta.
Dada kuwa koda ta shiga ta isko Mutallab na waya da ƙawu ƙanen mahaifin Aïcha da sukayi zasu haɗu yau dan zuwa wajen da Aïcha ɗin take ba tare daya san ma yana waje ɗaya da ita yanzu, nan kawun Aïcha ke sanar dashi cewa tun safe yafita saboda wani aiki da zaiyi acan cikin garin gashi yanzu yafito kuma yana kusa da anguwar ta mariƙiyar Aïcha, dan haka inba damuwa su haɗu a can, sunan anguwar Mutallab ya tambaye shi ya sanar masa yace masa yanzu haka shima yana cikin anguwar dan haka kawun yace to ba damuwa ya jirasa anan idan yaƙaraso zai kirasa sai yayi masa kwatance gidan da zai tambaya su haɗu acan.
#Mutallab Asad
#Ƴan Tagwaye
#Nana Diso
#Billy s Fari
MUTALLAB ASAD
(labari mai taɓa zuciya)
Na
Billy s fari
Nana diso
RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU.
TAFIYAR BIYU TAFI DAYA
SHAFI NA SABA'IN DA TARA.
Kallonsa Dada tayi haɗe da cewa, "kai da waye?" "Ƙanen mahaifin kishiyar da zan rama maki ga Meenal ne." Ya bata amsa ataƙaice yana dariya, zaro idanuwa tayi haɗe da cewa, "Mutallab! Wai da gaske kake wannan batun." "Eh Dada da gaske nakeyi dan tun wancan zuwan da mukayi na haɗu da yarinyar, ina ga Mahmoud ma ai yasan da zancen na kuma zata zai kwarmata maku." Hannuwa Dada ta shiga tafawa tana sallallami kafin tace, "Auren naka na nawa ne Mutallab da kake so ka kwasarwa kanka mata biyu, anya kana ganin zaka iya kuwa?" "Dada kamawa takeyi shiyasa." "Ikon Allah shine kuma ka ƙetare ƴar uwarka Zainabu duk da yadda take sonka kaje ka ɗauki bare? Nasan ba wata cikakkiyar tarbiyya ne da ita ba amma ai da gidan wani ƙara gidanka ko?" "Dada har ga Allah ni ban taɓa jin son Zainabu araina ba, Kinga kuwa babu yadda za ayi na iya rayuwar aure da ita a haka."
"Ai Shikenan Allah ya tabbatar da alkhairi yasa ba gudun gara kaje kayi ba kamar na farkon, dan ko matar taka a tsaitsaye ni nake ganinta babu alamun kunya tattare da ita shiyasa ma naso zaunawa a garin lokacin bikinku har sai naga ya kamun ludayin zaman naku zai kasance amma wancan ɗan ya hanani." Cewa da mahaifin Zainabu ƙanen mahaifiyarsu, Mutallab bai iya cewa komai ba ya buɗe gorar ruwan ya tsiyaya a cup yakai ga bakinsa, sai da Dada taga ya shanye ruwan tas ya ajiye cup ɗin sannan taci gaba da cewa, "Dama akwai zancen da nake so muyi dakai akan ɗan uwan nan naka Mahmoud, tunda dai Allah ya hore maka ka taimaka masa shima yasamu yai auren nan ga mata nan na sama masa." Kallonta Mutallab yai cike da mamaki kafin yace, "Dada Mahmoud ɗin ne za'a yiwa zaɓen mata? Kar fa azo a samu matsala shi yana da wacce yake so zumunci ya koma samun matsala, kina dai gani har yanzu kawu bai daina fushi dani ba akan kin amincewa da zancen Zainabu da nayi saboda na faɗa masa ina da zaɓina." "Bana don muguwar fata Mutallab, idan kai baka amince da sabon da akayimmasa ba sai kace shima bazai amince ba? Ai ba Mahmoud ba ko kaine bazaka ki wannan zaɓi da nayi masa ba yarinya kyakkyawa da ita ga tarbiyya da kuma natsuwa, ina ka ganta dan itace nasa takawo maka ruwa." "Ban kula da itaba amma Allah ya sanya alkhairi yasa zai sota kuma itama zata so shi ɗin." "Amin in Sha Allah ma zata so shi kuma shima din zai sota." Daidai lokacin wayar Mutallab ta ɗau ƙara da sauri ya ɗaga cikin girmamawa, "Gani a anguwar ka tambaya kace a kawoka gidan marigayi malam bulama." "To Shikenan kawu bara nafito". Mutallab yafaɗa yana miƙewa haɗe da kallon Dada yace, "Dada bari naje kawun yarinyar ne ya iso zamu je can ida ake riƙon yarinyar ya gabatar dani wajensu kuma muyi magana da yarinyar idan ta amince sai atura su kawu su nema mani aurenta." "Ikon ALLAH Mutallab, wai abun dawuri haka?"
"Eh anan ma cikin anguwar take gidan.." kafin yaƙarasa wayar Dada ta ɗau ƙara hakan yasa yafice dan kar kawu yaita jiransa da yasan idan Dada tafara waya ba yanzu ba sai ta jima tana yi, ganin lambar kawun Aïcha ya sata cewa, "to shi kuma wannan ko lafiya? Yarinya dai ce bazata sake komawa gidan nan nasa ba in Sha Allah tariga tazo aure kaɗai zai rabani da ita." Sai data gama surutunta wayar ta tsinke ya sake kira sannan ta ɗaga, gaisawa sukayi kafin kuma ya sheda mata gashi ƙofar gida, "lafiya dai ko malam Bello?" Dada tafaɗa tana fitowa daga cikin palourn, "lafiya kalau Dada wata magana ke tafe dani kuma bani kaɗai ma bane." "Ikon Allah to bari naturo ƴar taka ta shigo dakai dama nima akwai maganar da nake so muyi dakai mai muhimmanci." "To masha Allahu ba damuwa Dada." ya faɗa yana kashe wayar dai-dai lokacin da Mutallab yafito daga cikin gidan, Dada kuwa Aïcha ta ƙwalawa kira tace taje ta shigo da kawunta yana waje. Da mamaki kawun Aïcha yabo Mutallab da kallo ganin yafito daga cikin gidan, haka shima Mutallab ɗin mamakin ganinsa yakeyi a ƙofar gidan kakannin nasa kafin yace, "kawu dama kasan ina cikin gidan nan ne?"
"A'a Mutallab kai zan tambaya dama kasan gidan nan?" Ƙarasawa kusa dashi yai cikin girmamawa yafara gaishesa kafin yace, "ai nan ɗin gidan kakannina ne kawu da aka haifi mahaifiyata aciki." "Ikon Allah! To ai nan ɗinne gidan da mariƙiyar Aïcha take." Yana rufe baki Aïcha nafitowa cike da farincikin daya kasa ɓoyuwa a fuskarta tana cewa, "laa kawu ashe da gaske kaine, sannu da zuwa kawu Dada tace ka shigo ciki." Sake da baki Mutallab ya ɗago kai jin muryar wacce kawu ya kira da Aîcharsa ya kafeta da idanuwa yana kallon yadda takewa kawun nata dariya cike da farinciki, a hankali ya furta kalmar Aïcha! Cikin wani irin salo daya sa Aïcha juyowa har lokacin tana dariya saboda tsokanarta da kawun nata keyi wai akwana biyu kacal da zuwa ta har ta sauya, shi kuwa Mutallab lumfashinsa ɗaukewa yai na wucin gadi ganin yadda ta sauya acikin watannin da bazasu gaza uku ba da rabuwarsu a waccan ranar duk da kuwa tarin ƴan matsaltsalun data fuskanta na rayuwar yau da gobe, tsaye sukayi suna yiwa juna kallon kallo cikin idanuwa mai cike da tarin ma'anoni daga ɓangaren Mutallab, ita kuwa so takeyi ta tuno fuskarsa da inda ta sanshi amma takasa har sai da taji kawu yace, "Alhaji Mutallab ku shigo daga ciki mana ko kuwa Aïcha." Sannan ta iya tunowa dashi da kuma kalamansa a waccan ranar, gaba tawuce tanayi tana juyowa tana kallonsa, shima ɗin ita yake kallo biye dasu cike da wani irin shauƙin so da ƙauna da nan take ke fizgarsa.Kasa motsawa yayi mutallab daga gurin yanagani har suka shige ciƙi take yaji yanayinsa sun sauya gaba daya tabbas ko ba'a gayamasa ba muryarta yaji dazu, Jin Malam bello Na kwala masa kira yasashi Amsawa Da takowa ciƙin gidan. Aicha kuwa samun guri tayi kasa kusa dada tazauna kamar yadda dadan ta faɗi mata " Karaso nan kizauna naji da wacce yazo kuma? Yarinya dai wallahi ban kuma baku ita kuje kuna dora mata tallah kun sata a wani daki kamar na dabbobi yaranku tsaf dasu, Idan ma maganar ta kawoka to wallahi tun muna shiri da juna kayi waje." Murmushi yayi yace " A'a dada ba wannan bace ba ai Aicha kuma tazama taki har Abada." " Ah To yanzu dai naji batu dan in maƙaku a kotu bakaramin abu baniba." Mutallab ta ƙallah tace " kai kuma baƙon naka baizo baniba." Murmushi yayi yana zama yace " Ga baƙon Nawa dada." Mamaki ne yacikata tace " A'a wacece to sabuwar amaryar taka ne?" Cikin zumudi da shauƙin soyayyar da baisan ya furta ba yace " Aicha ce." Da ɗan mamaki itama Aicha tadago ta kallesa sai kuma ta sunƙuyar da banta zuciyarta na bugawa daya bayan daya, Allah yasani bazata iya yarda ta auresa ba saboda yafi karfinta nisa ba kusa ba shahararren mai ƙudin da akeji dashi shine zata aura?." Dada ce ta dan taɓota tace " Ke Aicha daman ƙinsansa?" Cikin sanyin murya tace " Shine wanda Nabaki Labarinsa dada." " Ikon Allah To Ni yanzu banda tacewa malam bello kune iyayen yarinyar nan kuma kune waliyanta Abu daya Nasani kada a tilasa mata idan batasonsa danAllah sannan agayamasa jikata zata cigaba da makaranta dan batasamu cikakken ilimin dayakamata ba." " Babu komai Dada bana ganin hakan matsala Nasan kuma Aicha zatayi mana biyayya koda batasan wanda zamu bata ba gashi kuma ɗan uwanta ne ma." Wani sanyi mutallab yaji dan shima ƙansa sai yanzu yake ganin kamar yaso ƙansa dayawa. Yana cikin tunanin nan yaji Muryar Aicha tana faɗin " DanAllah dada kada ayimun aure karatu nakeso kuma ma Dada Wallahi bana sonsa tafaɗa kai tsaye ganin in har tayi shiru to tabbas zata cutawa ƙanta ne." Da wani mugun firgice mutallab yazuba mata idanuwa yanajin waji abu na kokarin taso masa acikin rai. Dada ce tayi wuff tace " Ahaf Ai nasani to saboda Allah tayaya daga haduwa da mutum kace wai kanasonsa sai aure antaba haka?." Malam bello dayaji kamar ya kifa mata mari dan takaici da bakin ciki yace " Amma dada za..." " Wallahi Allah babu mai takurawa marainiyar Allah daga ganin mutum kawai kwa dauki diya ku basa? To shi Mutallab din yagayamuku ko watanni 4 bai rufa dayin aure ba? Maganar gaskiya fa muna sakaci da amanar yaranmu daga munga mai maiko maiko kokari muke kawai mukai yaranmu ciki, tashi kije ƴar albarki kinji makaranta inshaa Allah zantsyaa miki har ƙarshen rayuwata." Yadda yaji jijiyoyin ƙansa suntsaya yasanyashi kasa maganar k'omai a hankali yadan kwantar da ƙansa jiƙin kujera dada kuma na tashi ta barmusu gurin.Takaici kuwa gurin kawu bello ba'a cewa komai inbanda rashin hankali na yarinya har takalli mutallab tace bata sonsa." Kada kadamu Alhaji mutallab inshaa Allahu auren nan Alkhairi ne yanzu kabi komai a hankali mugani zuwa wani satin in yaso har dauren auren sai ahada." " Allah ina kaunarta kawu kuma zan kula da'ita bazan taba cuta mata ba." Murmushi kawu yayi yace kada kadamu wannan duk maganar dada ce Allah ya tabbatar muku da alkhairi bari Na huce ni dan yadda kaga dada ta dauki zafi bata kara fito." Jiyayi bazai iya ba He need her, he want to hug her to tell her how much he love her..YaaAllah ya faɗa yana mikewa yashiga kitchen din da yakejin sautin muryarta da Alama da wani take. Mikewa yayi kawai ya tsinci ƙansa da shiga kitchen din Afrah dake kokarin fita tace " Yaya ko kana bukatar wania abun ne?" Da ɗan damuwa acikin fuskarsa yace " Nothing kawai jiki abinki." Aicha dataji kamshinsa ya daki hancinta taja numfashi tana itama kokarin fita, ba karmin tashin hankali yashiga ba ganin zata fita haƙan yasashi fadin " dan Allah ki saurarini danAllah kibani.." cikin sanyin murya da idanuwanta suka ciko da hawaye tace " DanAllah kayi hakuri baka dace da macce irina ba Nima Inaso Nagina rayuwata Nayi yaƙi da jahilci kayi hakuri kaje Kacigaba da zama da matarka.." Ganin idanunsa na ɗan lumshewa ya sakashi faɗin " Aicha Ina kaunarki wallahi bazan wulakantaki ba." " Kadaina tunanin dacewa tsakaninmu Nifa diyar mabaraci ce ƙai kuma fa? Mai kudin da kasata takiji dashi? Mai ...sai kuka yaci ƙarfinta." Jiƙinsa ne yashiga ɓari wani ajiyayyun Numfashi yashiga saki, DanAllah kidaina kukan Nan kada kisa hannuna yakai ga taɓaci Alhalin ke baki hallata gareni baz inajin zafi inajin kamar nacuta maki Ganin kukan nan naki zai iya sakani aikata abunfa bai kamaceni ba , Kiyi hakuri kidaina kuka Mutallab yakara faɗi yana kokarin riko hannunta." " Banda gatan kowa sai Dada Iyayena babu kowa ƴar uwata babu kowa, kanada wata matar kazo ka aureni ku hadu ku wulakantani tunda ni ba yar kasarku bace ba danAllah kada kakara magana akaina Ka taimakeni da barin maganar Aure, Abaya ma bata burgeni ballanta yanzu danasan yadda rayuwar da duniyar take ciki, kabarni Nahada mafarkina Na inganta gobena kamin sauran ragowar lokacina yakaremini." " komai Zanmiki komai zan baki zancika miki burikanki Kibarni na kasance naki kema tawa, Wallahilazim soyayyar danake miki...kamin yakarasa tayi saurin barin kitchen din Afrah dataji komai sai tausayin yayan nata yashiga ranta hakan yasa tabi bayan Aicha da kallo hat ta huce tashige daƙin dada shikuma yayi hanyar barin gidan. Tunda yayi sallah isha'i bai kara fitowa ba Yana kwance ƙan gadonsa ga wayarsa daketa faman kara Amma msata kwata yaki bi taƙanta ganin mai kiran wayar yasashi dagawa haɗe da Sallama.." wai bacci kakeyi?" " A'a meenal ina ciƙin damuwa ne." " Nagayamaka A chat ai period nakeyi ko?" " ba wannan baniba Daman inaso muyi magana dake Akwai yarinyar danakeso....." " Kutmar uban can me kake Nufi Mutallab... " " kikarayimun zagi sai na ci mutunci mara kunya Nace miki aure zankara." " Wannan kuma baka isa ba wallahi kayi kaɗan..
SHAFI NA TAMANIN
*MUTALLAB ASAD*
Arewabook:- billysfari
Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.
Nace kayi kaɗan takara faɗa da karfin ihu batare da yace komai ba yakara runtse idanuwansa yanajin ƙansa kamar zai tarwatse a hankali kuma yaja ajiyar zuciya yana faɗin " Meenal kiyimun a hankali Nace miki banajin dadi, Maganar aure kuwa kinada tabbacin nagayamiki hakan tun kamin in aureki ko? Sannan tsakaninmu Nataba miki alkawarin bankara aure? Kokuma Nataɓa yimi...." Kaga malam dakata baka iss kace zaka karamin aure ba saboda tsabar wulakanci acema ko wata hudu banyi ba, daman ai maza munafukai ne wallahi baka isaba ba." Runtse idanuwansa yayi zuciyarsa tana kara yimasa zafi ahankali yace " Meenal karki karayimun zagi agabana nagayamiki watch what you're saying am not your mate." " So fucking what idan nayi zagin nayi zagin kutmar uba do your worse Mutallab asad tafaɗa tana jefan wayar gefen kujerar ta. Shikuma yaja numfashi tare da Rufe idanuwansa baƙincikin dayake ciki tabbas zai iyayimasa illah, kasancewa bai akashe wayar ba daga Nisa yanajiyo kukanta haɗi da faɗin " wallahi bai isa yayimun kishiya ba yayi kadan bayan duk yadda umma ke bani maganin mallaka ina zuba masa a gadonsa a kayansa ace zaiyimun kishiya wallahi karyane, a dan tsorace yakara kara Wayar kunnensa yakaraji tace " Ko dayake laifi nane wallahi laifi nane da har Naki kawowa umma sperm dinsa daja kawo da bai isa yakara auren nan ba tafaɗa tana barin gurin. Kirjin Mutallab kuwa yashiga dukawa da sauri da sauri yana kara maimaita Sperm wato umma tana using Meenal ne dan ta illatasa, A hankali kuma yaji wani abun daban yakara tokare masa wuya Nan da nan zazzabi kuma yashiga kokarin rufesa.
Nifa banji motsin Alhaji ba tun bayan magariba ko kinga fitarsa afrah? " A'a tante ƙinsan menene?" " badai wani abun yafaru ba." " Wannan yarinyar Aicha ta gidan dada? Kinganeta?" "Eh naganeta." " To ingayamiki itace yaya mutallab keso ashe ita kuma tace batasonsa ko ƙadan inajifa shine yayi fushi bai fito ba." " Subhanallahi Ai ni nayi tunanin sun dade suna soyayya ma ashe shi ƙadai yakeyin abunsa batasan yanayi ba, To bari inje bangaren nasa shirun yayi yawa ko abinci baici ba." Afrah kuwa sai cewa tayi Allah sarki yayana Allah ya saukaka maka. Tante kuwa bayan ta ambaci amin tatashi ta Nufi bangaren nasa duba da dan tafiya da nasu har tashiga bataji motsin komai ba kasancewa daga saman tamkeken palour ne zai kuma dakuna guda uku da bandaki da kitchen sai balcony kusan hudu haƙan yasa ta Nufi wanda yake Abuɗe tana Sallama Jin tayi sallamar sama da sau biyar kuma babu wanda ya Amsa mata yasata kara shiga ciki Nan ta ganshi kwance A aƙan gado jikinsa na rawar sanyi, " Subhanallahi bakada lafiya daman baka kira daya daga cikin mu ba? Haba Mutallab." Duk yadda idanuwansa suka ƙada suka canza zuwa ja ya zuba mata su yana faɗin Akwai magani a drawer ki mikomin nasha please." " Tayaya zakasha magani babu abinci bari nakira afrah tazubo maka abincinka hakan yasa takira Afrah cikin mintuna kuwa ta hado ta kawo Nan dada ta matsa masa sai yaci ya ƙarba dai yayi 2 spoon shima daga Nan sai Amai ya kufce masa Hank'alin su gaba daya sai yatashi kuma Afrah dakko mota Mutafi Asubuti kinga 12 Na dare yakusa." " Babu komai Tante danAllah karku damu zan warware." " kirawo Mahmoud kigayamasa idan ma da likita sai yazo ko?." Nan afrah takirashi awaya yace gashinan zuwa zaizo da Dr Bashir sai ya dubasa tunda yana kan duty yau. A hankali Mutallab yadago ƙansa ya kalli tante Afrah dataga haka sai tabar daƙin dan ta kula magana yakeson gayamata. " Mutallab lafiya dai ko? " " Tante zan rabu da Meenal bazaj iya zama da'ita ba." " Subhanallahi wacce magana kakeyi Mutallab ai mata indai akan kishine fiye da haka ma zasuyi danAllah kayi hakuri." " tante ba akan kishi baniba wallahi idan Nacigaba da zama da'ita rashin yarda zata shiga tsakanin mu kuma zarakaini da cuta mata danAllah kitsaya ki fahimceni inajin zafi cikin raina jikina babu dadi Nayi tunanin Nayi auren da zan rufawa kaina Asiri Amma naga hakan tunanina ne ƙadai ba Tunanin matata ba." " Mutallab shifa bawa baya rabuwa da jarabawa kuma idan kayi hakuri ai ga wata zaka kara idan can babu dadi Nan ai zaka samu Nutsuwa." " Wallahi ban iyawa yafaɗa yana kara kwara wani aman da yayi daidai da shigowar su Mahmoud Dr Bashir ne ya aunashi tare da yan tambayoyi sannan yabashi magani haɗe da saka masa ruwa da Allurar bacci."
Aicha tunda ta kwanta takasa bacci tunda tazo gidan dada daidai da kwana ko awanni bata taba kyararta ko gyamatarta ba, abinci ma tare suke ci yanzu ma gado daya suke kwance suna bacci jin motsin nata yayi yawa yasa dada far-away tana faɗin "Qu'est ce qui ne va pas avec toi (me yake damunki)." Rien dada (babu komai dada)." alors tu devrais dormir, sais s'il te plaît ( sai ki kwanta yanzu kinji) murmushi tayi mata takara gyara kwanciyarta tanajin kamar maganar da tayi agaban dadan bata kyauta ba ga jikanta mafi soyuwa agareta batace komai ba tayi addu'ar bacci ta kwanta dan yau Sunday kuma Monday zata fara zuwa makaranta gobe kuma zata fara zuwa islamiyya duba da aji 5 akakaita a islamiyya boko kuma aji shida.
Washegari da Asubahi Tante takira dada tasanar mata jiya basuyi baccin kirki ba mutallab babu lafiya sosai hankalin tante yatashi. Aicha da tunda tayi Azkar tashiga gyara gidan duk da bawani datti yayi ba sannan ta dora ganda kamar yadda dada tasanar mata ta dora ruwan zafin shayi sai datagama sannan ta Nufi dakin dada tasan azuwa yanzu tagama lazuminta tayi Sallama tashi " Ina kwana dada." " Tafada tana durkushe. " lafiya lou ƴar albarka kinga har ma nayi wanka sajida takirani Mutallab babu lafiya wai jiya bacci kadan sukayi yi wankan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 45 Chapter of 54