bata nan ba kika shirya wannan uban abincin haka? ".
Sai da mai aikin ta sadda kanta ƙasa sannan tace, "Ranki shi daɗe itace tace a shiryashi haka".
"Ita wa?" Meenal ta tambaya tana buɗe ɗaya daga cikin warmers ɗin dake jere ba tare daya kalli mai aikin ba. Sunan Mommy data ambata ya dakatar da Meenal daga abinda takeyi cike da mamaki ta ɗago kai tana kallonta tace, "Dama bata tafi ba?"
"Eh ranki shi daɗi". Tamkar wacce aka zarewa lakka haka Meenal ta saki marfin kular kamar zatayi kuka tare da ture abincin gefe tace, "Tashi ki tafi". Tana tallabe fuskarta da atake annurin dake kanta ya ɗauke da tafin hannayenta, ko me tatuna dashi sai kawai ta saki murmushi tare da janyo warmer ɗin dake gabanta, cikin ƙeta da mugunta tasa hannu ciki kawai ta soma cin soyayyar fitar dake ciki da aka naɗa da palour tasha kayan haɗi tana ci tana zubar da wata akan dining table ɗin, sai data ɓata ta kafa sannan ta janyo ɗaya warmer ɗin dake ɗauke da haɗin cowleg aciki shima taci wanda zata ci ta ture sauran a gefe ba tare data rufe ba, haka tabi abincin duka ta ɓatashi ta kuma bar sauran abuɗe, tana gamawa Mommy da Dady na fitowa daga sashensa suna dariya, kallo ɗaya tayi masu ta haɗe rai tare da ɗauke kanta tana goge hannunta da tissue sannan ta miƙe, tsaitsaye sukayi suna kallon yanda ta ɓata komai dake kan dining table tayi baja-baja dashi sai kace wata ƙaramar yarinya, kasa cewa ƙanzil Mommy tayi saidai ta rakata da idanuwa har ta iso inda suke tsaye, batare data kalli gefen ba tace, "Dady Good morning". Sannan taci gaba da tafiyar, fuskar Mommy da ɓacin rai ke shimfiɗe akai Dady ya kalla bayan amsa gaisuwar ƴar tasa dake ƙoƙarin wucewa ya tuno abinda ya faru jiya, da sauri ya dakatar da Meenal da step baifi uku daya rage ta ƙarasa hayewa ba yace,
"Zo mana Babyn Dady". Kamar Meenal bazata je ba amma data kalli fuskar Mommy taga tayi nasarar sanyata cikin ɓacin rai sai ta shiga saukowa fuskarta ɗauke da murmushi ta nufo wajen Dady tana cewa, "Gani Dadyna".
"Me yasa kika kai dare jiya?". Haɗe rai tayi tana hararar gefen da Mommy take tsaye kafin tace, "Dady nifa ba yarinya bace". Taƙare zancen tana turo baki haɗe da kallonsa, hakan data faɗa ya ɗan ɓata masa rai don haka a fusace yace, "shutup Meenal! Idan ke ba yarinya bace don me zaki kai wannan lokacin a waje? Kin san illar haka a rayuwarki?"
"But Dady zan iya kula da kaina, bai kamata ace ka biyewa zugar wannan matar ba har kaima kana tunanin ni ƙaramar yarinya ce da bazan iya ba kaina kariya ba aduk inda nake Dady". tafaɗa cikin ɓaci rai itama tana nuna Mommy, lumshe idanuwa Mommy dake saurarensu tayi tana ambaton Allah a zuciyarta, dan yau da ita tahaifi Meenal yanda take mayarwa da mahaifinta maganar nan kaɗai ya isa yasa takusan kasheta.
Dady kuwa da bai ɗauki abun wani abuba tunda dama yanayin faɗan ne saboda ya cikawa Mommy alƙawarin daya yimata jiya cewa zai tsawatar mata yaci gaba da cewa, "Meenal koma dai meye bana son ki sake dawowa cikin gidan nan wucewar ƙarfe goma na dare, idan ba haka ba sai ranki ya ɓaci kuma sai kin haɗu da fushina sosai"
Ya ƙarasa maganar a zafafe cikin ɓacin rai yana nunata, maimakon Meenal ta amsa shi sai kawai ta juya fuuu. tana fashewa da kuka tare hayewa steps ɗin da ɗan gudu-gudu tabar wajen ita alatilas an ɓata mata rai. Sosai yake jin kukan nata har cikin ransa dan haka sai kawai ya juyawarsa ya koma cikin ɗakinsa ya zauna bakin gado ya dage kansa da hannayensa, Mommy kuwa da takaicin rashin haɗawa da faɗan kalar cin abincin da Meenal tayi a saman dining table da rashin gaisheta da batayi ba yasa tabar wajen tuni tawuce kitchen abinta, wata breakfast ɗin mai sauƙi ta sake haɗawa ta iske Dadyn Meenal a ɗaki ta kaimasa haɗe da janyo stool ta ɗora akai ta aje masa agabansa tana cewa, "Kayi haƙuri na tsaya sake haɗa maki wani abun ne tunda ta ɓata wancan ɗin".
Murmushi kawai yayi fuskar nan tamkar wanda aka yiwa wani abun saboda ran shalelensa ya ɓaci, Mommy kuwa bata tsaya bi takansa ba ta zuba masa abincin tamiƙa masa tana kallonsa ya ɗan tsattsakura kaɗan ya ajiye, ruwan tea kaɗai ya iya sha sosai sannan yamiƙe yana cemata yafita dan dama cikin shirinsa nafita yake tun ɗazu. Ko daya fito palourn sai da yayi tsaye yana kallon stairs ɗin yana jin tamkar yaje ya lallashi Meenal don kukan nata ya tsaya masa a zuciya, haka ba dan yana so ba ya juya yafice yana sauke ajiyar zuciya, har bakin mota Mommy ta rakasa tare dayi masa addu'a sannan driver yaja motar suka tafi.
Meenal kuwa tana shiga ɗaki tafaɗa kan gado, sai da tayi kukanta mai isarta sannan ta tashi ta shiga wanka, tana ganin wayarta na haske amma tayi banza da ita, a haka Mommy ta turo mai aiki ta gyara mata ɗakinta ba tare data sake fita daga ciki ba, sosai hankalin Dady ya tashi ƙin ɗaga kiran nasa daya kasa jurewa yayi mata, haka ma ta ɗaya ɓangaren AAB shima ya matuƙar shiga damuwa da Meenal taƙi ɗaga kiran nasa tun jiya, yayita turo mata messages taƙi reply ya bita a watsapp shima ba alamun ta duba saƙon, facebook ya shiga ya duba shima bata online, ya je Instagram nan ma ya ajiye mata sakon amma tun jiya ba amsa, hakan ya sake ɗaya masa hankali dan gabaɗaya kasa runtsawa yayi jiya, haka yaci gaba da kira yana sake turo mata wasu saƙonnin amma ko takan wayar batabi ba balle har taga abinda yake turowa, Nancy yakira ƙawarta ya faɗa mata abinda ke faruwa tsakaninsu da rashin ɗaga wayar tasa da Meenal tayi tace ya jirata, gwada kiran nata tayi itama Meenal taƙi ɗagawa don yau kowa ma haushinsa take ji, laifin faɗan da Dady yayi mata ya shafi kowa shiyasa ta haɗewa AAB biyu, kiransa tayi ta sanar dashi itama bata ɗaga kiranta ba tana ganin kamar dai daƙyar in lafiya.
Wannan ya sake tayarwa da AAB hankali ya kasa haƙura, ana kiran sallar la'asar ya nufi gidansu Meenal, lokacin ta gama fushinta ta sauko zatayi lunch dan yunwa ta soma horata mai gadi yayi sallama abakin ƙofa, bata amsashi ba sai cewa da tayi, "Lafiya".tare da jan tsaki ganin Mommy a tsaye gefen gurin, wannan shine karo na kusan biyar da takeyiwa Mommy tsakin tunda tafito amma bata kulata ba tayi banza da ita, don haka ko yanzu gefen da take bata kallaba tashige ɓangarenta ba tare da tace mata uffan ba tana ƙara jinjina rashin tarbiya irin ta Meenal da mahaifinta ya ɗorata akai, wacce da ace tarbiyar da take bata tabari tabi tana da tabbacin baza ta taɓa yin wannan banzan halin ba, don a sonta ta rayu da Meenal tamkar ita tahaifeta da cikinta tayadda duk tarbiyar data bata zata bi tare da girmama nagaba da ita, sanin darajar ɗan Adam da kuma rayuwa cikin ladabi da biyayya, bata san me yasa wasu iyaye ke mantawa da cewa ƴayanmu amanane agaremu kuma duk tarbiyar da muka ɗorasu akai zamuyi bayani agaban sarkin da ya haliccemu, dayawan iyaye suna spoiling (sangarta) yaransu sai rayuwa taja kuma abun yazo yana damunsu bayan su da kansu suka ɓata masu gobensu. Allah ma ya sani har cikin ranta kullum tana tausayin rayuwar Meenal saboda mahaifinta yaƙi bari ta fahimci komai na rayuwa, banda fitsara bata iya komai ba tunda bata as bare cas, ita rashin tsafta, itace rashin iya magana mai daɗi, ga rashin yin girki taki tsayawa ta koya, idan kuma ansta mahaifinta yace ana wahalar masa da ƴa, islamiya tun tana ƙarama bata don zuwa kuma ya ɗauke mata shiyasa ilimin addinin ma bai wadaceta ba, lamarinta ba abinda yake buƙata sai addu'a kawai don wannan halin zai matuƙar bata wahalar yin rayuwa agidan mijinta, dan rashin iya lafazuzzu kaɗai shi kanshi matsala ne saboda Ita soyayya tana ginuwa ne ta hanyar nuna kulawa da kuma tarairaya amma gabaɗaya Meenal bata iya ba, "ohh ni Mansurah Allah ya kyauta ya kuma shiryamana Meenal". Mommy tafaɗa tana sauke ajiyar zuciya lokacin data ƙarasa cikin ɗakinta.
Mai gadi kuwa daya ji muryar Meenal na jefo masa tambayar a hasale ya buɗe baki yana kaɗa kai haɗe da cewa, "Ƙaramar Hajiya kinyi baƙo, yace ace maki ɗan gidan minista ne". Duk da yake hankalinta na akan wayar da sai a yanzu ta ɗaukota tana duba tarin missed calls da messages ɗin da akayi mata wadda na AAB ɗin duk sunfi yawa tana ji yace ɗan gidan minista ne da sauri tace yace masa tana zuwa.
A yadda take daga ita sai wando daya ɗame mata jiki iya ƙwabrinta da kuma t.shet da bata wani kame mata jiki ba ta kuma ɗan wuce mazaunanta kaɗan da hula akanta tanufi hanyar fita batare da tunanin haramcin haka gareta ba ko kuma tunanin shi ba muharraminta bane, haka ta riƙa ratsawa cikin tafiyar nan tata da tayi kama da rangwaɗa a tsakankanin ƴan aikin nasu dake ta zageya a gidan kowane na aikin gabansa, har lokacin ita kuma hankalinta nakan wayarta da take latsawa, jin ƙamshin turarensa yasata ɗago idanuwanta suka sauka akan AAB dake tsaye a jikin motarsa yana latsar waya daga shi sai guntun wando da riga irin armless ɗinnan, kana kallonsa zaka san hankalinsa ba a kwance yake ba, murmushi ta saki dan ita dariya ma yabata, yanzu akan ɗan wannan saɓanin da suka samu shine zaibi ya wani tayarwa kansa da hankali ya jero mata tarin saƙonni da kuma missed call har ya kasa zama sai ya iskota to inata da ranar da zasu rabu kenan! Ko da yake hakan ma bazata faru ba don ko aure bai isa ya rabasu ba, ta faɗa cikin ranta tanaci gaba da takowa wajensa.
Ƙamar dai ita ɗin shima ƙamshin turarenta ya sanar masa da isowarta ya saki wata irin sanyayyar ajiyar zuciya tare da ƙurawa ƙafafuwanta dake sanye cikin Plat shoes idanu yana kallonta tun daga ƙasa har sama, lokacin daya sauke idonsa akan kyakkyawar fuskar tata da babu komai akai sai ɗan fushin da idanuwanta sukayi na kukan data sha ya lumshe idon nasa tare da buɗe su lokaci ɗaya yana sake sauke ajiyar zuciya tare da matsowa da sauri ya riƙo hannunta kamar zaiyi kuka yake cewa, "Am sorry bestie don Allah kada kidena fushi dani haka zai iya sa narasa rayuwata, hukuncin nan da kika yimani yayi tsauri Bestie, gaba ɗaya ya hana mani kwanciyar hankali da natsuwata, pls Bestie am sorry".
Yaƙare zancen tare da niledown agabanta har lokacin yana riƙe da hannunta, murmushi ta saki haɗe da dariya tana rufe bakinta da hannun dake riƙe da wayarta kafin tace, "Shikenan Bestie ya wuce, amma kai kam matsoraci ne har naso inga matar da zaka aura! Daga wannan ɗan fushin sai kabi ka wani tashi hankalinka? Ni dai miƙe haka kar kasa nafara tunanin juyaka son raina".
Sai daya ja ajiyar zuciya ya sauke sannan ya miƙe yana kallon cikin idanuwanta haɗe da cewa, "In ma akwai abinda yafi juyani Bestie kiyi bakida matsala indai baza kiyi fushi dani ba, ya kike?"
"Facially fine bestie, Ina cikin damuwa wlh shiyasa ban kula da kiran da kayi mini a waya ba, matar can ta isheni sosai na rasa yanda zanyi da ita, imagine Bestie yau sai da tasa Dadyna yayi mani abinda bai taɓa yimini ba arayuwata saboda nakai dare jiya ban dawo ba! Ina ruwanta da rayuwata in ba shiga sharu ba shanu ba". Sai da AAB ya gyara tsayuwarsa sannan yace, "Bastie sufa matan uba da kike gani tamkar guba suke, basa taɓa son ƴaƴan mijinsu inba mutuwa sukaga sunyi ba, I think da mahaifiyarki na gidan nan da duk hakan bata faru ba saboda haka yakamata kiyi ƙoƙarin ganin Dadynki ya maidota tunda batayi wani auren ba".
"Yeah Bestie! I will think about that nima, mushiga daga ciki Bestie yunwa nake ji tun safe banci komai ba".
"Same Bastie nima banci komai ba tun jiya, but kina ganin shigata ba matsala bane ga matar Dadynki".
Bata tankasa ba sai data riƙo hannunsa cikin nashi suka nufi cikin gidan sannan tace, "Gidan ubanane Bestie bana ubanta ba, dan haka dole tabarni narayu aciki yanda nake so". Shafa kai AAB yayi yana murmushi don maganar tata tayi masa daɗi.
#Mutallab Asad
#Ƴan Tagwaye
#Billy S Fari
#Nana Diso.
*19*
*MUTALLAB ASAD*
Arewabook:- billysfari
Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.
# ƳANTAGWAYE BIYAR
#MUTALLAB ASAD
NA NANA DISO &
BILLY S FARI
________*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?*
*INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?”
*KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.*
Mun gwada mun gani 💯
Mun gani mun shaida 💯
Anyi mun gani 💯
MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
GYARAN MAIJEGO
MALLAKAR MIJI KO MATA
SUBULU DA SCRUB
MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
MAGANIN TSUMI
INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯
08142800199
07068558096
Sosai wannan bayanin nasu ya kama hankalin Abba don haka kai tsaye ya juya ya nufi ɗakin Mutallab ɗin rai aɓace yana bubbuga masa ƙofa haka, yana fitowa ya riƙo wuyan bes ɗin dake jikinsa tare da fizgoshi waje da ƙarfi ya ɗaukesa mari yana miƙa masa hannu haɗe da cewa, "Bani kuɗina?"
"Abba.." bai ƙarasa ba ya sake jin saukar wani maren da saida ya kusa faɗuwa Jalil da kawowarsa kenan yayi saurin riƙesa yana kallon Abban nasu rai aɓace yace,
"Abba meye haka? Ya Mutallab fa ba yaro bane da za'a riƙa dukansa". Abba yace,
"Jalil na tabbata kasan komai don bakinku ɗaya saboda haka kufito mani da kuɗina miliyan biyu da rabi tun kafin raina yaɓaci". Wani irin juyawa Mutallab yaji kansa yayi daƙyar ya iya motsa bakinsa yace, "Abba miliyan biyu da rabi? a ina nagansu balle na ɗauka Abba? Wlh ban ɗaukar maka kuɗi ba, ka sani Abba tunda ban taɓa daukar maka ba to yanzu me zai sa na ɗauka?" Yafaɗa cikin tsananin damuwa da kuma tashin hankalin daya ziyartosa.
Umma dake bayan Alhaji ita da Aunty Amarya tayi caraf tace, "A'a Mutallab kaji tsoron Allah kafito masa da kuɗinsa, shifa mahaifinka ne duk abinda kaga yaƙiyi maka yasan baka dace da abun nan ba, yanzu fisabilillahi da yakaika rumfarsa ko kuma gidan mansa haka zaka riƙa satar masa kuɗi? Kasan fa ɗazu agabana kashiga ɗakin". Mutallab ya ɗago idanuwansa da suka rine sukayi jajir ya zuba akan Umma kafin can ya kalli mahaifinsa yace, "Tabbas na shiga ɗakinka Abba yau, kuma da izininka nake shiga tunda kaine kabani damar in dinga zuwa ina gyaramaka daƙi, Allah ne shedata banda gyaran ɗakin da nayi babu abunda nayi".
"Kadai faɗi gaskiya Mutallab kafin abunnan yajawo maka matsala, karka manta fa nima agabana kafito ɗakin?" Itama Aunty Amarya tafaɗa tana kallonsa, Jalil ne da ransa yagama ɓaci sai jero tsaki yake yana kallon iyayen nasa kafin yace, "Agabanku kenan ya ɗauka? Wai me yasa gidan nan ba'a adalci, wanda yake satar ma ba'a taɓa masa ƙorafin ya saci kuɗi ba duk da ansan yaniyi sai wanda ko Naira 5 bai ɓaba ɗauka ba, Narantse da girman Allah sai Allah yasaka masa, shikenan masifa daga kun kunna mana waccan sai wannan...?" kafin yakarasa Abba ya daukeshi da mari yana cewa "Dan ubanka ni sa'anka ne? Ko kuma su iyayen naka sa'aninka ne da zaka tsaya kana faɗa mana magana don ranka, wato kanuna mana kai mara kunya da kuma rashin tarbiya ne".
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun". Mutallab kawai ya iya faɗa don yanzu bai san ma abinda zai faɗa ba Abban nasa ya yarda dashi dan sun gama ɗaureshi, Jalil dake jiran yaji Mutallab yace wani abun amma yaji yayi shiru ya kalli Abban nasu yace,
"Abba ina da tabbacin ya Mutallab bai ɗaukar maka kuɗi ba don yau ba'a gidannan ma ya wuni ba, na roƙeka kayi bincike sosai saboda shigarsa cikin ɗakinka bazai zama hujjar da zatasa ace shiya ɗaukar maka kuɗi ba bayan ba yau yasaba shiga ɗakinka ya gyara maka ba". Shuru yayi kafin ya ɗago kai ya kalli Umma yace, "ke kuma da kika cewa agabanki ya Mutallab ya shiga ɗakin, to ke me kikayo acikin ɗakin? Kema Aunty amarya me kika shiga yi cikin ɗakin?" Ganin sunyi shiru sai wani mugun kallo suka aika masa dashi cike da tsana yasa ya maida kallonsa ga mahaifinsa yace, "Abba Idan har ya Mutallab abun zargi ne akan ɗaukar waɗannan kuɗin don ya shigar maka ɗaki to wlh suma abun zargi ne dukansu". Ya ƙare zancen da ƙarfi cikin ɓacin rai yana nunasu da yatsa, "Jalil". Yaji Muryar ya Mutallab cikin sanyin murya ya faɗa tare da ɗago kai yana kallonsa, juyowa yayi suka haɗa idanuwa ya girgiza masa kai alamun yayi shiru ya dena, girgiza masa kai yayi shima haɗe da cewa, "Kabarni nayi magana ya Mutallab ko Abba zai fahimci suma ɗin abun zargi ne.." bai rufe baki ba Mutallab da ransa ya gama kaiwa ƙokoluwar ɓaci ya daka masa tsawa haɗe da cewa bai son ya sake jin bakinsa kuma yabar wajen, "yaya.." Jalil yafaɗa hawaye na sauko masa a fuska don shi kukansa baida wuya Mutallab ya fushi ƙarfin hali da iya haɗe damuwa, juyar dakai gefen da yaga Mutallab yayi yasa dole Jalil ya juya yabar gidan gaba ɗaya, Umma da Aunty amarya kuma dake kukan tuhumar da Jalil keyi masu suka shiga sharar ƙwalla suna cewa Abba yabar yaronsa yaci masu mutunci akan abinda suna da tabbacin idan anyi bincike za'a iya ganinsa wajen Mutallab ɗin, runtse idanuwa Abba yayi tare da buɗe su ya kalli Mutallab yace, "idan har baza kafito mani da kuɗina ba ka tattara inaka inaka kabar mani gida don bazan zauna da ɓarawo ba, kuma ka fita kar ka ƙa minti ɗaya acikin gidan nan ko kuma nakira maka hukuma suje dakai har sai ka fiddo mani da kuɗina". Yana gama faɗar hakan yabar wajen.
Sanin da Mutallab yayi ko shekara dubu za'a bashi ya fiddo kuɗin bazai iya ba tunda bashi ya ɗauka ba yasa kawai ya juya ya koma cikin ɗakinsa ya haɗa kayansa a jikka da duk wani abu da yake buƙata ya rufo ɗakin nasa ya nufi hanyar fita Abba na tsaye daga bakin ƙofa yana kallonsa har ya kusa ficewa, dai-dai lokacin Afrah ta taso daga islamiya ta shigo cikin gidan tana yiwa Walid dariya da yayi dambe da abokinsa aka basu kashi makaranta take annurin fuskarta ya ɗauke hango ya Mutallab ɗauke da jikka, ƙoƙarin sakar mata murmushi yayi don sama mata natsuwa ganin yanda ta ruɗe tun kafin ma tasan da abinda ke faruwa amma ina, don itafa sam bata son ace zaiyi tafiya ko kuma zaiyi nesa dasu, ta dinga ƙunci kenan wani lokacin har da zazzaɓi, musamman lokacin da yayi karatunsa na degree a ABU Zaria, haka akayi ta fama da ita har ya samu ya kammala, "ya Mutallab ina zaka je da jikka?" Yaji tafaɗa jiki na rawa tana riƙo hannunsa, kasa amsa mata yayi don kukan da yake riƙewa zai iya zuwa wajen kokarin yimata magana ganin kalar tashin hankalin daya bayyana a fuskarta sai dai kawai ya shafa kanta yayi gaba, riƙe masa hannu tayi tafashe da kuka tana cewa, "yaya don Allah kada katafi ko ina bana jin daɗin gidannan idan baka nan". Da sauri ya runtse idanuwa jin yanda take kukan shima yana jin wasu hawaye na tarar masa a idanuwa, ba tare daya juyo ba yace, "Afrah dole natafi tunda Abba ya koreni bai son zamana acikin gidansa akan abinda bani na aikata ba, kije Jalil na nan na tabbata zai kula dake fiye da yanda nakeyi kin jiko?". Rirriƙesa tayi tamkar wacce za'a cirewa rai tana faɗin, "Bazan zauna ba ya Mutallab don Allah katafi dani kada kabarni". Abba ne dake tsaya yana kallonsu ya daka masa tsawa yana faɗin, "matuƙar bazaka fito Mani da kuɗina ba ko mutuwa zatayi dole kabar mani gida, Ke kuma Afrah maza sakeshi kowace cikin gida kamin ranki ya baci". Ganin yanda Afrah ta sake riƙe shi tana kuka yasa Abba sake daka mashi tsawa yana cewa, "Wlh Mutallab idan baka sakar mani yarinya ba zan saɓa maka, mai gadi kuzo ku fitarmin da yaron nan bana son ganinsa", hakan yajawo hankalin ma'aikatan gidan suka firfito cike da mamakin jin kalaman dake fitowa daga bakin Abban da zasu taɓa zuciyar duk wani mai hankali da tunani, a zukatansu suna faɗa wato bama Jamil dake iskancin daya ga dama Abba zai koraba Mutallab da duk yaran gidan babu wanda ya kaishi mutunci da sanyin hali! Mutallab bai da ƙwarin guiwar da zai iya dakatar da kansa daga tafiya akan wannan gaɓar jin kalaman mahaifinsa na ƙarshe dake cewa baya don ganinsa.
Don haka yaci gaba da tafiya har lokacin Afrah na rirriƙe dashi tana kuka, ganin haka yasa Aunty amarya juyawa ta koma ciki bayan taka hannuwansa Khalid da sukayi tsaitsaye suma suna hawaye ganin kukan da Afrah keyi, don tsakanin ɗan uwa da ɗan uwa sai Allah, shi Abba kuwa cewa yayi Umma taje ta riƙo Afrah ta shigo da ita ciki, jiki na rawa Umma da farinciki ya cikata ta nufo wajen tafara ƙoƙarin fizge Afrah daga jikin Mutallab ita kuma tana sake komawa haɗe da rirriƙesa, ƙarfi Umma tasa sosai ta fizgota da ƙarfin gaske, hakan yasa atake Afrah ta saki wata irin ƙara ta faɗi wajen tamkar wacce aka zarewa rai haɗe da sheɗewa alamun Asma ɗinta ta tashi duba da yadda take buɗe baki tana kokuwa da lumfashinta, da sauri ya Mutallab ya juyo shi da Jalil dake tsaye can waje bakin gate cikin ƙunar rai sukayo kanta.
"Kada ka kuskura ka taɓa mani ƴa kafice kabar mani gida kafin nakira maka hukuma suje dakai". Suka jiyo Muryar Abba nafaɗi cikin ɓacin rai haɗe da nunosu, hakan ya dakatar da Mutallab daya gama ruɗewa daga tallabo Afrah da yake shirin yi Jalil ya tallabota yana cewa, "kaje da ita kabata maganinta Jalil, kuma ka kula da ita sosai kaji ko". Sannan ya juya yabar wajen tare da ficewa daga gidan gaba ɗaya, yana jin Jalil dake tallabe da Afrah na cewa, "ya Mutallab ina zaka je?" Amma ya kasa tsayawa yabashi amsa, take yaji wasu hawaye masu matuƙar zafi, ƙuna da kuma raɗaɗi na sauko masa a fuska. yana fita daga gidan wani azababben kuka yaci karfinsa, irin kukan daya daɗe baiyi ba tun bayan rasuwar mahaifiyarsu ganin halin daya baro Afrah aciki ya kuma kasa taimakonta sai ga motar Aryan ta faƙa agabansa. Horn yake danna masa amma ina bai ma san yanayi ba sai shesshekar kuka da yakeyi ya zubu ƙasa durƙushe akan giwoyinsa da duk mai imani daya kallesa a wannan yanayin sai ya tausaya masa. Da sauri Aryan ya kashe motar ya fito ya nufi wajensa cikin tsananin tashin hankali don bai taɓa ganinsa a irin wannan yanayin ba. Jin an taɓo kafaɗarsa yasa shi kara fashewa da kuka Aryan ya ɗagosa haɗe da rungumesa yana cewa, "MAM meke faruwa dakai ne?". Tare da kallon gate ɗin gidansu MAM ɗin dake kuka, "Innalillahi wa'inna illahir raji'un! MAM what's going on please?" Ya sake faɗa akaro na biyu jin Mutallab ya kasa amsashi sai kukan yakeyi, hannunsa ya ja yakaisa cikin motar sannan ya dawo ya ɗauki jikkarsa dake ƙasa ajiye ya buɗe bayan motar ya saka ya dawo ya buɗe gaba ya shiga ya zauna tare da juyowa yana
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 54