Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kiraka nace katuromin Mutallab amma kaƙi". "Abba kamanta korarmu kayi ne? Taya zamu riƙa shigo maka gida tunda idan ma munzo da ɓaci rai zamu fita na aibatamu da kakeyi". Sai da Abba ya kalli ƙofar shigowa yaga ba mai zuwa sannan yace, "Haba Jalil ka taɓa ganin an raba ɗa da ubansa?" Ya ƙare zancen yana sake waiwayawa bayansa gudun kada Umma ta shigo taji me yake faɗa ranta ya ɓaci, ya rasa meyasa a ɗan lokacin nan yake yawan mafarkan yaran da kuma tuna rashin kyautawar abubuwan da yayi masu (Ai addu'a makamin mumini ce) ɗan kuwa hakan baya rasa nasaba da addu'o'i inda Mutallab yai tayi zuwa su Saudiya shi da Afrah, ita kanta ma bata gushe ba sai data roki ubangiji ya daidaita soyayyarsu a zuciyar Mahaifinsu da sauran ƴaƴansu dan tana sonsa kuma tana kewarsa, ganin babu kowa yasa Abba sake cewa, "Jalil yanzu A'ina kuke zaune?" Jalil da mamaki ya gama kashewa yace, "Anan bayan gidanka kaɗan Abba". "Ikon Allah, ashe dagaske akeyi da akace gini Mutallab yayi muku kai dashi?" Da mamaki Jalil yace " Eh Abba a wajen wa kaji?" Girgiza kai Abba yai cikin sanyin murya haɗe dayin ƙasa da ita yace, "Mubar wannan zancen anan Jalil kuma Dan Allah kada ku gayawa kowa agidannan inda kuke kar aje a cutar mani daku,". Ya ƙare zancen yana sake waiwayawa tare da share ƙwallon da suka zubo masa. "Abba wai menene? Kana cikin damuwa ne?" Da sauri ya girgiza kai tamkar yaro yana kallon ƙofa kafin yaci gaba da cewa, "Injin gobarar da akayi bata dai taɓa masa dukiya sosai bako?" Mamakine ya sake kashe Jalil ganin Abban nasu na goge ƴan ƙwallad da suka zubo masa agefen idanu da yadda yake magana kamar bashi ba, ajiyar zuciya ya sauke kafin yace, "Abba ta taɓa masa kayansa masu yawa sosai gaskiya". "SubhanallahiAllah yabashi dubunsu kuma yamayar masa da waɗanda suka gudu, dan Allah kace masa yakirani nayi masa kaje, ina Afrah?." "Sunje Niger ai duk suna can tare".  Jin muryar Umma na shigowa yasa Abba yafara abubuwa kamar wani marasa gaskiya, "kai da waye haka nake jin murya ƙasa-ƙasa?" Tafaɗa tana ƙarasowa cikin palourn, tana ganin Jalil ta haɗe rai tare da cewa, "meye haka Alhaji? Meya kawosa nan?" Cikin daburcewa Abba yafara faɗin, "meya kawoka nan, tashi katafi Umma yimasa magana kar yazo ya dameni, tashi kifitarmun gida nace wlh baruwana kawai naga ya shigo ne Umma, kiyarda dani ba ruwana dasu Allah". Jalil najin haka yayi saurin miƙewa yafice daga ɗakin cike da tausayin Mahaifinsu, tabbas yanzu ya sake yarda cewa ba acikin kansa yake yi masu wasu abubuwan ba, wasu ƙwalla ne masu zafi suka zubo masa a fuska ya kife kansa a stearing wheel ɗin motarsa daya buɗe ya shiga yana jin tsanar Umma acikin ransa mai ƙarfi". Tsaki Umma taja bayan ta raka Jalil da harara kafin ta maido idanuwanta ga Abba daya wani sinne kai ƙasa kamar mai jiran ta ƙaddamar masa da hukunci tace, "Ai gashi nan yaranne gaba ɗaya ka bari sunfi karfinka sun zama yan iskan kansu, kaga idan fa ba rabuwa kayi dasu ba har abada ka sanya tsinuwa a tsakaninku baza subarka ka huta ba sun riƙa bibiyarka kenan". "Kiyi haƙuri Hajiya ai ankusa kaiwa ga hakan, duk wanda ya sake dawowa cikinsu Allah tsone masa zanyi". Yayi maganar yana nuna mata tabbas ransa a ɓace yake zaiyi abinda yafaɗa ɗin matuƙar suka sake, harara ta maka masa tare da cewa, "rufamun baki dallah ai ba iyawa kakeyi ba, ka shige muje ga Jamil can ba babu lafiya wai ƴan damfara sun damfaresa sun kwashe masa karin daka bashi shine fa yake shirin ɗorawa kana damuwa". "Innalillahi yarufa mani asiri yayi haƙuri kar wani ciwon yazo ya kamashi, indai jari ne zan bashi wani, yanzu muje na duba shi ina so zanje gidan mai naga cinikin da akayi sai na karɓo tunda babu kuɗi a hannu, ga Walid ma yana shirin rubuta jarabawarta ta kammala secondry ayi maganar shiga jami'a ban biya kuɗin ba". Harara Umma ta maka amsa haɗe da cewa, "Sau nawa ne zance kabar batun su walid ɗin nan wai?" "To nabari Hajiya kiyi hakuri na daina tunda bakya so, muje naga Jamil ɗin" ya wuce gaba ita kuma tabi bayansa tamkar wata mahaifiyarsa ta tasa shi gaba har zuwa sashen nasu Jamil ɗin. Jalil ko koda yafito daga gidan parking ɗin motarsa yayi gefe ya shiga rera kuka sosai, addu'a ya shiga yiwa mahaifin nasu acikin ransa yana cewa, "yaa Allah ka kawomana ƙarshen zaluncin nan daya tashi daga kanmu yanzu ya koma kan mahaifinmu, Allah kana ganin yanda matarnan ta mayar da Abba kamar wani kwarkwar sai abunda tace masa tukunna yakeyi, Allah ka dubi lamari mu baki ɗaya". Sai daya gama kukansa mai isarshi sannan ya ciro wayarsa ya kira ya Mutallab, yana ɗagawa ya fashe masa da kuka yana cewa, "i'm scared Yaya danAllah kudinga yiwa Abba addu'a, juya yakirani a waya yace yana nemana, shine da zan fita kasuwa na biyo wajensa, yaya baka ji yanda muke magana da Abba ba cikin kulawa da soyayya har yana tambayata ya kuke ya kasuwar saboda shi kaɗai na samu a ɗakin, amma Umma na shigowa Abba ya ruɗe gabaɗaya yafara korata wai wayace na shigo masa gida, yaya kaga yadda Abba yake jin tsoron Umma kamar ita tahaifeshi? Wlh ko da muna magana dashi kafin tazo yanayi yana juyawa kada tazo taganshi, maganar ma a hankali yake yi ɗan kar ta kusa wannan wane irin zalinci ne haka da ɗaukar alhaki". "Relax Jalil, ai dama nasha gaya maka wasu abubuwan wallahi ba yin kan Abba bane". "Wallahi na yarda ya sam babu tsoron Allah a zuciyar matarnan, baka ga yadda take juya Abba ba da kallo kawai, yabani tausayi yaya sosai" "Allah ya kyauta addu'a dama ba dainawa mukayi ba, kayi haƙuri kadena wannan kukan haka kada kanka yayi ciwo". "To yaya yana ce nace ka kirashi" "Zanyi hakan" Mutallab yafaɗa yana miƙewa daga zaunen da yake don gama shiryawarsa kenan zasu je wajen haɗuwar da zasuyi da shugaban ƙasa.. #Mutallab Asad #Ƴan Tagwaye #Nana Diso #Billy S Fari MUTALLAB ASAD   (Labari mai taɓa zuciya) Na Billy s fari Nana diso    RUBUTUN ƳAN TAGWAYE KARO NA BIYU      TAFIYAR BIYU TAFI DAYA SHAFI NA HAMSIN. Da daddare Mutallab bai koma ba sai daya yakammala komai sannan yadawo gidan, sosai aikin nashi yake gudu tunda ya zube kuɗi sosai, hakan ba ƙaramin daɗi yayi mashi ba ya kuma ƙara godiya ga Allah bisa da wannan ni'imomi da yai masa wanda yana da tabbacin kaɗan daga cikin ni'imominsa ne yai masa, sai da ya zauna agurin kawu suka gaisa yayi masa bayyanin komai kamin kuma ya tambaye inda Mahmoud ya shiga, sai a sannan ne kawu ke kasanar masa ai yashiga can doha amma zai dawo gobe, nan yayi masa fatan dawowa lafiya kamin kuma ya miƙe ya wuce cikin gidan nan ma gaisawa sukayi Jaddi kafin tace, "Nikam Mutallab shigo daga ciki mana kullum bama samun zama tsakanin mu kaƙi dakewa sani sai dai kawunanku da ƴan uwanka" Murmushi yayi yacire takalminsa sannan ya shiga ya samu gefen kafet ya zauna yana faɗin ,  "Afuwan Jaddi, aikin nan ne yake dauƙe mun hankali shiyasa kwana biyu bansamun zama dafatan kuna lafiya". "Lafiya kalau muke, nace bamu zauna da jikana ba, dafatan dai Afrah ta sauka lafiya?." Murmushi yayi yace,  "Ta isa lafiya ɗazu ma da mukayi waya dasu sunce a gaidaku." "nous remercions Dieu que Dieu la bénisse (mungode Allah Allah yayi mata Albarka)". Tafaɗa cikin Yaren nasu na Faransa ci da suke dan jejjefawa can baka rasa ba Mutallab yace "Ameen Jaddi". "To yaa batun aure Mutallab, nace ga matanan ƴan uwanka kala-kala gidan kawunanka ka zaɓi ɗaya a aura maka ko kanada wata tsayayyiya ne?" Ɗan sunkuyar da kansa ƙasa yai yana cewa,  "Eh to Jaddi can ma akwai wata yarinya da akayi maganar aurenmu kafin nazo, sannan anan ma jiya naga wata Jaddi". "To masha Allahu, acikin ƴan uwan naka kaganta?" "A'a Jaddi da muka fita da mahmoud ne". "To nidai bazan matsamaka ba dan naga kawun naka kamar yanason haɗin gida, amma dai ina son samu ne gwara kaje can kasamo wata dan gudun taɓarɓarewar zumunci idan aka samu matsala". "To Jaddi insha Allahu bari naje na kwanta agajiye nake jina". "To jikana a dai dunga addu'a duk yanda aka gaji ana kuma sadaka saboda wannan rayuwar damuke ciki ta zama abun tsoro sosai wallahi dole sai ana kulawa da addu'a saboda macuta sunyi yawa". "In sha Allah Jaddi". yafada yana miƙewa tare da saka takalminsa sannan yafito ya nufi ɗakinsa, ko daya ƙarasa ɗakin daya sauka wanka yayi ya wanke bakinsa sannan yasaka daya daga cikin wayoyinsa a caji kamin kuma ya karkaɗe kan gadonsa yana mai yin bismillah sannan ya kwanta jin yadda jikinsa yake amsawa ga tsigar jikinsa tana mimmiƙewa a hankali ya sashi ambaton Allah yana ƙara dan gyara kwanciyar, jin yanayin ƙwancin bai masa daɗi ba ya sashi miƙewa zaune yana tuna alƙawarin da yayiwa meenal na zai kirata". Idan bai manta ba yau yini yai zuciyarsa nayi masa tunanin abubuwa guda biyu, na farko yarinyar daya gani jiya, na biyu kuma tausayin Meenal na rashin da tayi, karo na farko daya tuna da ranar daya fara ɗora idanuwansa akanta, tabbas yaji wani abun game da ita da bazai iya cewa gako meye ba, a yau yana jin irin wannan abun tattare dashi, ya tabbata ba dan ɗabiun Meenal ba a irin son da takeyi masa ba abinda zai hana ya amsheta hannu biyu, wata zuciyar ce tace masa idan ace kaine kake mata wannan soyayyar fa take maka wuɗannan abubuwan Ya zakaji Mutallab? Karka manta kafira ma musulunci yace a aura koda bazata sauka akan addininsa ba balle ita da take musulma, me zai hana kayi tunani ka amshi soyayyarta, wataƙil zata kasance a yanda kake sonta tunda har tana sonka, ƙilan hakan ma zai iya zama sillar shiriyarta daga wasu dabi'un da baka so, ajiyar zuciya ya ja ya sauke kafin ya jawo wayarsa ya kamo numbarta da baiyi saving ba ya fara saving ɗinta da meenal sannan yayi dialing ɗinta kiran farko har ya tsinke bata ɗauka ba sai akira na biyu ringing na farko ta ɗauka tana faɗin, "yayana barka da dare, ina ta jiranka tun ɗazu amma baka kiraba? Da har zan kiraka mommy tace wai nadinga kamun kai mana in bari kakira." Murmushi ya saki jin zancen nata na ƙarshe mai kama dana yara yana sauke ajiyar zuciya a hankali kafin yace, "Yaya bazai amsa maku ba saboda baki yimai sallama ba". "Laaa..Kayi haƙuri dan Allah ƴaƴana, Assalamu alaika barka da dare". Waalaikissalam barkanmu Meenal, ya haƙuri?" "Alhamdulillah Yayana" "Allah yajiƙanta ya gafarta mata ya ƙaramana haƙurin rashi". Ya ƙare zancen yana ƙara gyara zamansa kafin yaci gaba da cewa, "kiyi haƙuri kinji bankira ki dawuri ba, nafita ne kuma ban dawo da wuri ba sai yanzu shiyasa kikaga ban kiraki ba, yasu Dady?". "Suna nan ƙalou yayana, yaushe zaka dawo?" tafada hawaye na zubo mata saboda bata taba tunanin zai saurareta hakan ba har yai mata magana da taushi cikin kulawa, wannan yasa taji tana son ganinsa sosai yanzu, sautin Muryarsa ya katse mata tunani da yake cewa, "kinci abinci? Kinyi sallah?". "Nayi yaya ai na daina wasa da sallah yanzu ka tambaye Mommy kiji". Tayi maganar cike da shagwaɓa, hakan yasa Mutallab jin wata kasalalliyar gajiya na taso masa a hankali ya rufe idanuwansa yana don tunano fuskarta a waccan ranar, ɗan tsaki yaja tunowa da cikin shigar daya ganta yai can ƙasa maƙoshi kafin yace, "To masha Allahu yanzu idan zaki kwanta kiyi addu'a da safe zan kiraki, in sha Allahu kuma next week zan dawo". Cikin farinciki meenaltace "Tohm yayana nagode Allah yafaranta maka ya kuma dawo Mani dakai lafiya, can't wait to see you yayana". "Never mind, nima nagode yafaɗa yana kashe wayar". Tabbas ko yayane kazama silar farinciki ga bawa kai ma Allah zai dubeka, shi har ga Allah baya son macce mara kamun kai tunda yatashi da mahaifiyarsa yatarar da ita macce mai nutsuwa sosai komai nata a nutse takeyi, wuɗannan munanan ɗabiu na saka attachment ko saka ƙumba da sauransu bata taba ba duk da yasan lokacin da su Umma da Aunty amarya nayi, Afrah ma bata taɓa gwada yin hakan ba shiyasa idan yaga macce na irin ɗabi'un basa burgesa, zai iya rantsewa tunda yazo kasar nan baifi sau biyu bani ba yaga masu shigar kirki amma da yawansu shigar matsatsun kaya sai attachment abun mamakin ma sunada gashi sosai amma suke sakawa, hakan ma yasa yayi mamakin yarinyar nan da yagani da shigar hijabi kusan rabin guiwa a waccan ranar ya kuma ji takwanta masa sosai, tabbas su ɗin gajiyayyi ne masu matuƙar rauni amma ita ɗin a yanda ya ganta kamila ce sosai, ko wacece ita? Ko a'ina yanzu zai sake ganinta? Komai dai meye ina jin soyayyarta sosai acikin zuciyata, safe goshinsa yai tare dayin baya ya kwanta yana cewa, "Yaa hayyu yaa Qayyum kayimun zaɓi mafi alkhairi da nagarta". Kafin kuma bacci yazo yayi gaba dashi. "Mommy, Mommy". Meenal kefaɗa da ƙarfi tana yiwa ɗakin mommy da ayanzu take ji ba tada wata abokiyar shawara ko kuma kaiwa kukanta aduniya sama da ita (Ribar haƙuri kenan da Mommy tayi da ita) ganin bata tadda ta aciki ba yabata damar ƙarasawa ɗaƙkin mahaifinta dan tasan tana can. Taɗan daɗe tsaye tana tunanin ta shiga ko uma takoma kafin can ta yanke shawarar shiga ta hanyar yin knocking abakin ƙofar ɗakin tana faɗin, "Mommy, Mommyna Ina nemanki". Kallon Mommy dake zaune Dady yai a hankali yace, "Na lura wannan ƴar taki zata ƙwace mani ke tafiye rigima". Dariya Momy tayi kafin tace, "daman ai ita keda Mommynta" "Ni kuma ni keda daɗina". Yafaɗa yana kashe mata ido, hakan yasa Mommy zaro ido tare da rufe baki tana kallon ƙafa, Dady yai murmushi abinda yana gyara kwanciyarsa tamkar bashi yai zancen ba, sai data gyara babban mayafin wata doguwar abaya nuni dake jikinta sannan tamike ta nufi wadrobe ɗin kayansa haɗe da buɗewa tamkar tana gyaran wadrobe ɗin tace, "shigo meenal". Ahankali ta tura kofar ta shigo tana fadin, "Dady dan Allah kayi haƙuri zamuyi magana  da Mommy karkace na dameku." "Ai dama yanzu nagama cewa kinkarɓe mani ita ita kuma ta karɓe mani ke kun haɗe mani kai sai dai naji ana ƙusƙusƙus". Ya kare zancen yana kara jin farinciki akan matar tasa dan bakaramin namijin kokari takeyi ba wajen ganin ta sauya Meenal ɗin ta hanyar data dace duk da ɓacin ran da tayi going through acikin gidan nasa dan yanzu kam alhamdulillah kaso hamsin na cikin ɗabi'un Meenal sun canza. "Dady muje?" "Eh kuje ƴar gidan Mommy". "Meenal yaya akayi ne, ko kin kasa bacci ne nazo na tayaki?" Mommy tayi zancen da zuciyarta.  "To ai kince indaina magana agaban Dady ko? Kince indinga jin kunya ko? To kizo muje waje." "Iyyeeee Mommy dama haka kuke mun? Kenan dai yanzu na gane ni ba dan gidan bane shiyasa ake ware ni". Dariya Mommy tayi kafin tace, "No Dady to bari ayi agabanka ɗin".  Meenal dake dariya itama tace, "Yawwa Shikenan ma Mommy alƙawarin kayana da kikace za'a siyamun?" Dady najin hakan yai saurin rufe idanuwansa alamun yai bacci Mommy da taga lokacin da yai hakan ta shiga dariya tana cewa, "Ai kuwa gama tashi zakayi ayi komai dakai, sabbin kaya ƴaƴan keso sai bamu kudi gobe ta sauyosu, infact ni closet din kayan ma nake so a sauya mana gaba ɗaya ko ba haka ba Meenal" "Haka Mommy so nake nadaina saka wayancan ɗamammun tunda ƴaƴana baya so, sannan Dady hadda hijabbai a ɗinkamin pls". "Dady kaji dai buƙatar mu ko?" Mommy tafaɗa tana dariya tare da zaunawa gefensa, cikin jin daɗi Dady ya buɗe idanuwa yana cewa, "Ai sai kuje gobe ku siya zan tura mata kuɗin". "Ni Dady jarida ga account ɗin Mommy itace zata zaɓomun ai". Taƙare zancen tare da matsowa gaban Mommy ta faɗa mata cewa, Mutallab yakirata har da hira sukayi".  Murmushi Mommy ta saki tare da cewa, "Ai tabbas wanda yakoma ga Allah bazaiyi kuka ba Meenal domin shi maji riƙon bawansa ne, kici gaba da Addu'a kinji kada ki gajiya." "To Mommy sai da safe, Dady good night" tafaɗa tare da miƙewa tanufi hanyar fita Dady nace mata, "good night daughter". Aransa yana addu'a Allah ya sakawa Mutallab soyayyarta ya aureta, da tabbas yafi kowa murna da farinciki cikin rayuwarsa". "Abunda Allah yakaddarta shike faruwa Dadyn meenal idan har akwai rabonsu nakasancewa da juna zasu kasance batare da wani ko wata ya buƙata ba, nidai ina roka musu daga ita har Kamal idan sun samu tsayayyu ayimusu auren kawai dan Allah, sannan a matsayinka na mahaifiya kaƙara dagewa da addu'a Allah ya basu abokanan zama nagari." "Inayi wallahi sosai kuma zancigaba dayi in Sha Allah, Allah yayimiki Albarka yarayamiki taki ƴar ya kuma kula maki da ita kamar yadda kika kula da nawa yaran. "Amin Dadyn Meenal". Mommy ta faɗa tana ƙoƙarin gyara kwanciyarta akan gadon. ****** Ƙarfe uku na dare dai-dai. Sautin tashin kukanta ne acikin ragujajjen gidan nasu ke tashi sosai dan masu ƙaramin nauyin bacci zasu iya saurararonta a makota. Yangwalalliyar tabarmar datake bacci take zaune akai tana turkar kukanta, tarasa tayaya zata samu abiya mata kuɗin makarantar ta kusan zango guda babu halin taje makaranta saboda rashin biyan kuɗin karatun nata. Yau ma sai data gama musu wankensu tas sannan taje tasamu mà mèrè a ɗakinta, cikin kalar tausayi ta shiga ɗakin akan danAllah tasaka yaya babba ko babansu yabiya mata kuɗin makaranta, amma buɗe bakin mà mèrè tace, "Ni kuwa mai yayi mun zafi Aïcha? Tayaya zan saka abiyamiki makarantar boko tunda ba hauka bane akaina, a haka ma fa yaƙi kikeyi damu balle kin ƙara gaba, ke kenan kullum cikin maida mana da martani kike idan ance kiyi abu, nifa wannan barar taku tafimun komai amfani ko ma samu mai kuɗi ya ɗauke mana ke Aïcha, ko bai aureki ba indai zai riƙa ɗauke mana ƴan lalurorinmu muji daɗin duniyar nan to wallahi yafi mana wannan ilimin boko da kike ta kokuwar samu, in dai rigar nono kika ce na saya maki ko ƙananan kaya zan siya miki amma bana kashe biyar cikin kuɗina akan wani boko naki, ke islamiyyar ma dan kada kicemun kafira yasa nake barinki kina zuwa duk da zuwan nata ma itama yaƙi yakesa kinayi damu, kece damun saki abu sai kice babu kyau ai ni wannan karewar kudin makarantar taki gaba takaini wallahi Allah kuma yayi mani daɗi".. #Mutallab Asad #Ƴan Tagwaye #Nana Diso #Billy S Fari MUTALLAB ASAD   (Labari mai taɓa zuciya) Na Billy s fari Nana diso   RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU   TAFIYAR BIYU TAFI DAYA     SHAFI NA ARBA'IN DA TARA. Wani irin matsanancin ciwo tunda Afrah tadawo Jalil ke fama dashi daya hana mata kuzari ajikita ganin yadda yake matuƙar jin jiki, gashi kuma ya hana a gayawa yaya Mutallab daga ita sai tánte Sajida ke faman kulawa dashi, yanzu ma waya suka gamayi da Aryan tana kuka yace tayi shiro zai shigo yakawo masa wani likita yaƙara duba shi ina sha Allah zai samu lafiya.  Bayan sun gama wayar a hankali ta samu kusa da inda yake kwance ta zauna tare da kamo hannunsa hawaye yana zuba dan har wata rama yayi sosai tana cewa, "Sannu ya Jalil Ubangiji Allah yabaka lafiya". Murmushin da yasaba yimata dan ƙarfafa mata guiwa yayi yana mai riƙe hannunta haɗe da cewa, "Karki damu Afrah zan samu lafiya, duk da dai cikin jikina ina jin wata iriyar azaba da nakasa gane ko menene ke damuna haka Afrah". "Ina sha Allah zaka warke, in Sha Allah Habiby na nan tafe da wani likita zai sake dubaka".  Batakai ga rufe baki ba sai ga tantè Sajida ta shigo ɗakin tana faɗin, "Sannu Jalil, ni ina jin wannan Asiri ne akayi maka ɗan na lura ba tun yau ba yawan mantuwanka da kuma rawan tsorata daka dingayi ko magana akayi bayanka sai ka zabura alamun ka tsorata, tashi Afara ɗakko bokitan nan dake kitchen tunda kin iya karatu ki ciko mana shi da ruwa, mugwada wannan maganin na warwarewar sihiri muga ko Allah zai sa adace". Fara ta amsa da Tohm tana miƙewa tare da ƙarasawa kitchen ɗin tayi yadda tace mata sannan ta kawo ruwan abokiti." "Yawwa ai yanzu ba'a zama haka na gayamuku ba tun yau ba, da yawan fuskokin dake yimaku dariya ba sonku sukeyi ba, Ga ganyen magarya can nasa baba mai gadi ya tsinko mana ɗazu ciro mana guda bakwai yanzunnan ki kawo". Tánte Sajida data karɓi ruwan tafaɗa tana nunawa Afrah inda ganyen magaryar ke ajiye, Miƙewa tayi taƙarasa taje ta ciro ta kawo mata ta sake cewa ta ɗakko ƙaramin turmin daka ta daka ganyen magaryar sosai ta zube acikin ruwan, bayan tagama tánte Sajida ta sake cewa, "Yanzu ki kafa bakinki acikin ruwan sai ki fara karanta suratul fatiha, sannan sai ki karanta Ayatul kursiyyu (aya ta 255 na cikin suratul Baqara), Sai ki karanta Suratul A’araf daga kan (aya ta 106 zuwa kan aya ta 122), Sai ki karanta Suratul Yunus daga kan (aya ta 79 zuwa kan aya ta 82), Sai ki karanta Suratul Kafirun kafa ɗaya sannan ki karanta Falaƙi da Nasi kafa uku- uku. Sai a karanta wannan addu’ar,            *'Allahumma rabban-nas az’hibil ba’as ashfi wa antash-shafi la shifa’a illa shifa’uk shifa’un la yugadiru sakaman” kafa uku.Sannan za’ki iya karawa da wannan addu’a “Bismillahi urkika min kulli shai’in yu’uziyka wa min sharri kulli nafsin Allahu yashfiyka, bismillahi urkik'* itama ƙafa uku saiki tofa". Sai da Afrah tayi ta'awizi da bisimillah sannan cikin natsuwa tafara karantosu dan duka ayoyin na kanta kasancewar ita ɗin mahardaciyace kaɗan ma yarage taƙarasa haddace alƙur'anin, bayan tagama sannan ta miƙa mata tana bata ruwan ita kuma ta taimakawa Jalil yaɗan tashi zaune yasha tasa ya shefe jikinsa dashi, bayan sun gama ta sake riƙasa ya koma ya kwanta tace, "In sha Allahu zaka warware Jalil sannu kaji". Tana rufe baki sukaji Sallamar Aryan gabaɗaya suka waiwaya suna kallonsa, yadda yaga Afrah ta faɗa ya sashi tunkafin ya zauna cewa, "Afrah kema ba lafiyan ne?" Wani kallo tayi masa kafin ta sunkuyar da kanta tana gaishesa, sai daya amsa sannan ya samu guri ya zauna yana gaida tante Sajida yana yimata yamai jiki." Tace, "Ga mai jiki nan jiya bamuyi bacci ba". "Wallahi tánte nima haka tun da nazo dubashi naga yanayin jikin nasa hankalina ya tashi, yanzu dai ga wani likitan nan yazo zai sake dubashi". "To ba laifi, Jalil kam yaji jiki dan haka yai ta ihu da daddaren wai sai yafita, har yau dai ba'a gayawa yayan nasu ba kada hankalinsa yatashi". Da yake shima Mutallab ɗin kwana biyu hankalinsa naga aikin da yaketa son aƙarasa sai ba damu da kiransu ba sanin cewa ba wata matsala tunda ga tantè Sajida tare dasu, Aryan dake yiwa Jalil sannu ya ɗago kai haɗe da cewa, "Daman bai kamata asanar dashi ba hankalinsa zai dawo nan ya kasa yin komai acan tunda kusan dai baida kamar Jalil ɗin gida da kuma kasuwar tasa". "Ai kam dai, Allah dai ya bashi lafiya yaro mai kazar kazar amma dubi duk yadda ya rafke lokaci guda". "In sha Allahu zai warware daman jiki da jini ai sai Allah, Allah yabaka lafiya ƙanin". Aryan yafaɗa tare da cewa, "Afrah ko zaku shiga cikin ya dubashi". Ta amsa da to sannan suka miƙe suka fice daga ɗakin shi kuma ya ciro wayarsa ya kira likitan yace ya shigo, Aryan ya kallesa haɗe da cewa, "Nagode ya Aryan". Yana jinjinawa ƙoƙarinsa wajen basu kulawa tare dajin cewa tabbas Afrah zata samu kyakkyawar kula awajensa idan sukayi aure. *************   Umma ce ke tsaye tana gyara mayafin jinta tare da kallon Abba tace, "To Alhaji ni zan fita kaga ƙarfe takwas na safe ya kusa, gashi kuma ina so naje dubiyar nan na dawo kafin goma tayi, dan haka kada ka sake kafita waje indai ba masallaci ko gidan manka zakaje ba idan har ban dawo dawuri ba kenan, saura idan nafita kaba waccan munafukar matar taka dama tazo gunka ko kai ka kwashi jiki kace zaka je wajenta kaga zallar ɓacin raina idan na dawo dan zan fahimta". Jikin Abba na rawa yake cewa,

Chapter 29 of 54