Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tafiyarsa shima. Jalil da Afrah kuwa cikin Sa'a koda suka shiga gidan ashe Umma bata nan, hakan ya basu damar zaunawa suka gaisa da Mahaifinsu cikin natsuwa duk ɗaya ayi yana regen ƙofa, yadda yaga Afrah na faman ɗaɗɗaure fuska bayan ta gaishesa ya sashi kwantar da murya cikin sigar rarrashi yana bata haƙuri dan yasan dalilin fushin nata, kuka ta saka mashi kamar zai yi kuka ganin tana ɗaga sautin kukan nata kamar mai tsoron aji wani abun yafaru sai kace ba ƴaƴansu ba, daƙyar ya samu tayi shiru bayan ya gama nuna mata cewa abun ne ya rasa yanda zaiyi shiyasa bai da wani zaɓi daya wuce fita rayuwarsu, da mamaki take kallon Abban nasu kafin ta maida kallonta ga ya Jalil dake zaune gefe ya zuba masu idanuwa ba tare daya samusu baki ba, "Ya kana jin Abba fa, wane irin fita rayuwarmu bayan shine mahaifinmu kuma duk duniya ba muda kowa sama dashi? Abba me kake nufi da wannan kalmar?" Sai dai kafin ya bata amsa ƙarfe biyar ta buga dan haka yana gani tunda dama yana hankalce jikinsa ya soma rawa, cikin matsanancin tashin hankali ɗaya ziyartosa yake cewa, "Jalil tashi kaka Afrah kuwuce ta kusa dawowa, bana don ta ganeki ranta ya ɓaci tunda bata son ganinku acikin gidan nan!" Wannan karon ba Afrah kadai ba har Jalil mamaki kamawa yayi ganin yadda jikin Abban nasu ke rawa da maganganun da yakeyi, ganin sunƙi tashi yasa ya kamo hannuwansu suka miƙa ya shiga turasu yana cewa, "maza kutafi Afrah kada ta isko ku, kutafi nace Jalil dan Allah in ba so kuke raina ya ɓaci ba, Allah yai maku albarka". Ya ƙare zancen yana sake turosu waje tare da ɗaya masu hannu, Fuskar Jalil jiƙe da hawaye yariƙo hannun Afrah da tayi tsaye tana kallon mahaifin nasu itama hawayen na sauko mata afuska yana ja suka fice daga palourn, cike da tausayinsu yabi bayansu yana ɗaya masu hannuwa alamun ban haƙuri sai ga motar Abba da ayanzu ta zama mallakin Umma ta shigo gidan drivernta ya ɗauki ta daga wajen bukin wata ƙawarta data je dan har drivern kanta gareta yanzu, Abba na ganin Umma tafito yai wata irin zaburahade da juyawa zai koma ciki da sauri Umma ta daka masa tsawar data kusan gigita hatta su Jalil da suka kusa kai bakin gate zasu fita, Abba farko ya ɗauka Jamil ne ya shigo bakinsa na rawa ya shiga faɗin, "sannu da dawowa Hajiya". Wani banzan kallo tayi masa kafin ta nuna su Jalil fuskarta a haɗe suna jinta tace, "su waye wuɗan can idanuwana ke gani!" "Wlh bani nakirasu ba, kawai ganinsu nayi kuma yanzu yanzu suka taho nace su tashi sutafi bana son kizo ki ganesu ranki ya ɓaci, zaki iya kiransu ki tambayesu ma". Yai maganar cikin wani girmamawa da ƙasƙantar dakai tamkar ba mijinta ba, juyawa tayi cikin ɗaga murya da isa takira sunan Jalil da har ya aza ƙafarsa zasu fita cikin gidan, runtse idanuwa yai yana jin wani ɗari ƙasa ransa na yadda mahaifinsu yakoma cikin gidan yayin da Afrah jikinta ya ɗau rawa dan tuni ta rasa duk wani kuzari nata, kamar bazai kulata ba sai kuma yaja hannun Afrah suka juya suka koma ciki, cikinƙwarin guiwa yake takowa zuwa gabanta yayin da Afrah ta shiga togewa dan ko ganin umman bata don yi, sai da suka iso gabanta suka tsaya sannan ya amsa mata kiran da tayi masa yana cewa, "gani". Afrah tafara bi da wani mugun kallo ƙololon baƙinciki na taso mata kafin tamaido idanuwanta akan Jalil tace, "me yakawoku gidan nan? Ko kun manta kuɗin korarri ne daga ainahin mamallakin gidan?" Murmushi mai ciwo Jalil yai tare dasa tafin hannuwansa ya goge hawayen dake kan fuskarsa sannan yace, "baki ji yanda kika ce ba? Mu korarri ne daga ainahin mamallakin gidan ba keba, saboda haka matuƙar shi ɗin mahaifinmu ne babu wanda ya isa ya dakatar damu daga shigowa cikin gidansa koda kuwa shi ɗinne da kansa! Ina so ki sani Ubangiji shiya halasta mana wannan gidan tunda muka zamo jinin mamallakinsa, ɗan haka idan duk duniya zata taru domin haramta mana shi wallahi bazasu iya ba, kuma wannan isa da taƙamar da kikeyi na ganin cewa kin mulki kowa don ranki kema rana na zuwa daba mulkarki kaɗai za'ayi ba da ƙarfin ikon Allah har takaki sai anyi, kuma kisa aranki bazamu daina zuwa muga mahaifinmu ba matuƙar kuɗin jininsa ne". Yana ƙare faɗar hakan yaja hannun Afrah suka bar wajen. Kuka sosai Afrah keyi cikin mota tana tausayawa Mahaifinsu halin da yake ciki, sai da taji yai parking alamun sun iso gida sannan ta ɗago fuskarta da tai jajir haɗe da kallon ya Jalil tace, "ya Jalil dan Allah mu ɗaukikke Abba agidancan, wallahi taƙarfi da yaji ake juya rayuwarsa tare da sarrafa ƙwaƙwalwarsa musamman akanmu". "Bazai yiyu ba muyi haka Afrah saboda tare yake da iyalinsa, bayan haka ma shi da kansa bazai yadda ya biyo mu ba saboda tsoron Umma da yakeyi, soyayya ɗaya zamu nuna masa a wannan lokaci muyi masa addu'a saboda ita yafi buƙata akan komai". Jiki a sanyaye Afrah tabuɗe motar tafito suka shiga cikin gida, ko data labartawa tánte Sajida abinda ke faru cikin tausayawa itama tace, "gaskiyar Jalil Afrah Abbanku addu'a yake buƙata, kuma da son samu ne shima a sanar dashi yariƙe ibada da azkar dan wannan lamari nashi akwai asiri aciki, astagfirulla zato zunubi amma yadda muka sanshi jajirtaccen namiji ada wannan yanayi da yake ciki biri yai kama da mutum". Haka sukayi zaune jugum-jugum abun duk yabi ya damesu, da daddare ma kowanensu da damuwar ya kwanta aransa wanda daƙyar suka samu baccin ya ɗaukesu. Washe gari gari bayan Mutallab ya tashi baccin daya koma ya shiga wanka ya shirya yafito suka gaisa dasu kawo da Jaddi yafito ya dauki motar Mahmoud ya nufi babbar kasuwa wajen da akeyi masa aiki, sai daya tabbatar komai na tafiya normal  tare da yiwa masu aikin babbar kyauta kafin yadawo ya biya su kudin aikinsu sannan yai masu sallama akan zaiyi tafiya ya dawo na da kwanaki suka yimasa fatan alkhairi sannan ya shiga motarsa yatayar yabar wajen, bazata yake son yiwa su Jalil shiyasa bai sanar dasu zancen komawar tasa ba dan haka ya ɗauki waya ya kirasa sukayi magna akan harkar kasuwa sannan ya tambayesa Abba dan tun ranar da sukayi waya bainnemesa ba gashi shi kuma yace kada yakirasa indai ba kiransa ya gani ba gudun masifar Umma, "lafiya klw yake jiya ma munje gaishesa ni da Afrah amma." Sai kuma yai shiru saboda yana ganin ba dacewa yariƙa faɗa masa abinda zai ɓata masa rai akan mahaifin nasu, Mutallab ya fahimci akwai damuwa dangane da mahaifin nasu amma sai bai tambayesa ba ganin koma meye tunda yau zai isa ƙasar zai ji ko kuma zai gani da idanuwansa, ɗan haka sai kawai ya basar suka shiga wata maganar daban kafin sukayi sallama. A ɓangaren Aïcha yariga daya gama samun mafita akan lamarin nata, dan haka kai tsaye ya ɗauke hanyar da zata sadashi da gidan nasu, Aïcha na kici tana taya Umma girki daketa faman tsokanarta wai ashe jarumace ita ganin ta ware da safe tana tayata aiki, murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba tana ci gaba da aikinta na talga mata garin tuwo da takeyi sai ga yaro ya shigo yace, "Wai Aïcha tazo ana mata sallama". Ras Aïcha taji gabanta yai wata irin faɗuwa da sauri ta ɗago kai tana cewa, "je kace bata nan". "Yau naji ja'irar yarinya, kika sani ko Alhaji ne yazo dubaki da jiki? Kai ke kace gata nan zuwa". "Kai mama gaskiya ni babu inda zanje". Aïcha tafaɗa ranta aɓace tana rufe tukunyar data gama talgen tuwon, harara mà mèrè data ƙara so wajen da niyar karɓar talgen ta watsa mata tana faɗin, "ai wallahi baki isa ba, zaki je ne ya yagaki jiya a banza bai biyaki ba? Ina ko sisi baki shigo da ita gidan nan ba jiya banda kuɗaɗen da yaba mahaifinki? To maza kitashi ki tafi ko na saɓa maki kinji na faɗa mako". Aïcha na kuka tamiƙe ta shige ɗakinsu ta ɗauki hijabinta har ƙasa tasa hawaye kwance akan fuskarta sannan ta nufi hanyar fita, sai da takai bakin ƙofa ma mèrè ta ɗago ta lura da ƙarin hijabin da Aïcha ta aka, cikin sallami tace, "Aïcha me zan gani haka?" Tabiyo bayanta da sauri Aïcha na turo baki ta ƙarasa ficewarta, ganin har takai waje yasa ta ɗan ɗaya murya tana cewa, "To wallahi kika dawo ba kuɗin nan na murzar da akayi maki jiya sai ranki ya ɓaci, ɗan indai Alhaji zai biyaki to yauma ya ɗauke ki kutafi tunda naga jikin naki da sauƙi ba wata illa yai maki sosai ba".     (Hmm! Anya mama wannan don kuɗi naki bazai kabilu ga halaka ba da kuma dana sani?🤔). *ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 #Mutallab Asad #Ƴan tagwaye #Nana Diso #Billy S Fari. MUTALLAB ASAD MUTALLAB      (labari mai taɓa zuciya) Na Billy s fari Nana diso      RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU.    TAFIYAR BIYU TAFI DAYA   SHAFI NA HAMSIN DA BIYAR. Kukan da Aîcha keyi lokacin data fito ya sashi ɗago idanuwansa daga latsar wayar da yakeyi yana kallonta, cak kukan nata ya tsaya ganin wanda batayi tsammani ba tsaya jingine a motarshi, kasa ɗaga ƙafafuwanta tayi taƙarasa wajen har sai da taga yana gyara tsayuwarsa haɗa da ƙoƙarin ƙarasowa wajenta shi sannan ta ɗaya ƙafafuwan nata ta iso wajen, "sannu da zuwa ina kwana?" Tafaɗa tana duƙar da kanta ƙasa, sai da ya ja ajiyar zuciya ya sauke sannan yace, "lafiya kalau me kike yiwa kuka?" Ya tambaya idanuwansa na akanta duk da kuwa yasan abinda yasata kukan tunda yaji yadda sukayi da mahaifiyar tata, shiru tayi takasa cewa komai hakan ya sashi ɗauke idanuwansa akanta yana cewa, "ki saki jikinki dani ki ɗaukeni tamkar yayanki, banzo ƙofar gidanku ba dan na cutar dake ba sai dan muyi magana dake bisa wani matsayi da zuciyata ke ƙoƙarin baki bayan kin mun sata". Da ƙarfi Aïcha ta ɗago kanta ta zuba masa narkakkun idanuwanta da ruwan hawayen da suka taru aciki suka sauya masu kala tana cewa, "innalillahi wa'inna ilaihirrajiun, sata fa kace! Wlh ban ɗaukar maka komai ba". Haɗe rai ya sakeyi tare da cewa, "taya zakice baki ɗaukar mani komai ba bacin girman abinda kika ɗauka da matsayin da yake dashi a wajena bai barni bacci ba jiya, hakan yasani dawowa yau dan naji meye dalilinki nayi mani hakan?" Kai ta shiga girgiza masa ƙwallon da suka tarar mata a idanuwa na sakkowa akan kyakkyawar fuskar tata haɗe da cewa, "Bawan Allah me nasace maka? Ina rigarka ce kuma kai da kanka kabani, bari na shiga ciki na ɗauki maka kayanka amma ni wallahi banyi maka sata ba". Da ɗan fushi ya kalleta yace, "Kin mun sata mana satar da tafi wannan rigar dana baki muhimmanci domin idan babu wannan abun da kika ɗauke mani bazan iya rayuwa ba". "Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun to ni me na ɗauke maka?" Ta sake faɗa a ruɗe tamakar ta saka kukan gabaɗaya ma tahuta, "zuciyata kika sace Aïcha". Taji ya faɗa wanda hakan ya sata ɗago kai ta tsura masa idanuwa cike da mamakin anya da ita yake?, Jinjina mata kansa yai yana lumshe idanuwa alamun tabbatar mata da zancensa kafin yace, "tabbas kin sace mani zuciya tun akwanankin baya dana ganeki a wani junction Aïcha, sai dai kafin na ƙarasa inda kike kuka yimani ɓatan dabo, kwatsam sai gaki jiya Allah ya sake dawo dake cikin rayuwata bayan na gama fidda ran ina zan sake ganinki, don gaskiya nakeyi maki kuma da aure Aïcha, nayi maki alƙawarin gusar maki da duk wani miki dake zuciyarki akan halin da kika tsinci kanki tun ƙaramcinki har zuwa girmanki, ban damu da sai kin bani amsa yanzu ba akan kina da ra'ayi akaina ko bakida, zan baki isasshen lokaci kije kiyi tunani idan har kina sona ko kuma akasin haka, zuwa lokacin na dawo daga tafiyar da zanyi yau da nake tsammanin zan ɗan yi kwana biyu kafin nadawo". Kai ta shiga girgizawa tana ja da baya, "ɗan Allah kada kazo da zancen da bazai yiyu ba tsakanin ni dakai saboda tazarar banbancin dake tsakaninmu, da gani kai nagartaccen mutum ne ɗan gidan manyan mutane, ni kuma ta ɓangarena ba haka abun yake ba, idan kace zaka taimakemu ne zango yarda akan kace zaka aureni na saboda baka dace dani ba". Taku biyu yai ya ƙarasa wajen da take haɗe da cewa, "taimako wani abune da akeyi ta fuska daban-daban Aïcha, idan har shi zanyi maku to iyayenki zan buƙaci gani kai tsaye nayi duk abinda ya kamata bawai ke ba, amma shi so dole ka tunkari wanda kake yiwa shi fuska da fuska yafara amince maka kafin kagabatar da kanka ga iyayensa, duk da shima ɗin a musulunce iyayen naki yakamata nafara fuskanta kafin nazo gareki, bazan tilasta maki Aïcha ba kije kiyi tunani akaina, sai dai ina roƙonki alfarma kada kisake zuwa baran nan don kada abinda yayi ƙoƙarin samunki jiya ya sake faruwa". "Waye kai kake nema ka hurewa ƴata kunne? Nace waye kai ja'iri marasa mutunci". Mà père da mama taje ta tado tafaɗa masa ga Alhajin dake son Aïcha nan yazo ya taso yafito yake haɗar haka uyana ɗan coccokala sandarsa tare da fuskanto wajensu. "Kaga don Allah katafi mahaifina bazai taɓa amincewa da zancen nan ba". "A'a kibari muyi magana dashi Aïcha ai nima mahaifina ne". Mutallab yaƙarasa wajen ma pèrè Aïcha na biye dashi, cikin girmamawa Mutallab ya ɗan russuna duk da yasan ba gani shi zaiyi ba yace, "Barka da fitowa bana ina kwana". Sandar hannunsa ma pèrè ya ɗaga ya taɓo Mutallab da ita tare da ɗan shaƙar ƙamshin turarensa kafin yace, "lafiya klw waye kai?" Har Aïcha zatayi magani tace shine wanda ya kawota jita sai Mutallab ya ɗaga mata hannu tare da kallon ma pèrè yace, "Sunana Mutallab Asad Mutallab baba, ni ɗan Nigeria ne nazo garinnan ne saboda bunƙasa wani kasuwanci nawa sai gashi na haɗu da Aïcha.." bai ƙarasa maganarsa ba yaji ma pèrè yace, "kana da kuɗi yaro?" Tsabar jin kunyar da Aîcha tayi yasa ta duƙar da kanta ƙasa Mutallab yai murmushi haɗe da cewa, "Alhamdulillah baba shiyasa nake so na taimakeku duk da akwai tafiyar data taso mani yau, amma ga wannan" ya tura hannu cikin aljihu ya ɗebo kuɗi masu yawa ya sanya wa ma pèrè a hannu yana cewa, "kuɗine da zasu isheku kuyi lalurorinku kafin na dawo baba muzauna muga abunda yakamata ayi". "To..to kina Ina Aïcha? Bishi kutafi kinji ko? Da alama yana da kuɗi kuma yana da kirki". "A'a baba bashi nake buƙata ba". Sanda ma père ya sake ɗagawa yana lalabo Mutallab jin abinda ya faɗa haɗe da cewa, "yaro bashi kake buƙata ba? Bakaga Aïchan ne ba? Ko akira maka yayarta ne?" Kai Mutallab ya girgiza yana jin wani takaici azuciyarsa haɗe da cewa, "a'a baba ni duk ba wannan nake so ba, alfarma ɗaya dai nake so naroƙeka kayi mani har zuwa lokacin da zan dawo". "Faɗi ko menene yaro zanyi maka". "Dan Allah dana Allah bana kada ku sake fita barar nan, nasan kuɗin dana baki zasu isa kuyi lolurorinku kafin nadawo sai muga me yakamata ayi". Ɓata rai ma pére yai haɗe da cewa, "yaro barar nan fa dashi muke ci muke komai, ba don shi ba ta ina ma zakaga Aïcha ɗin da zaka ce mudena". "Haka ne baba, Amma ai alfarma na nema, kuma na tabbata kafin kuɗin hannunku su ƙare ai zan dawo". "To naji, amma yaro ina kuɗin nan suka ƙare fa baka dawo ba fita baran mu zamuyi, wannan ma dole kayi mani ɗan naga kana da kirki yasa na amince baza mutafi ba". Murmushin jin daɗi Mutallab yai tare da cewa, "Nagode sosai baba Allah ya saka da alkhairi". Yana sake ɗan russunawa alamun girmamawa. Juyawa ma pèrè yai yana cewa, "to Aïcha sai kin shigo, Ja'ira dama ba don zuwa yawon baran kikeyi ba to kya huta kwana biyun kafin ya dawo". Aïcha da fuskarta ke jiƙe da hawaye tabi mahaifin nata da kallo har ya shige gida kafin ta juyo da kanta ga Mutallab dake kallonta, kasa ƙurar kallon nasa tayi saboda abun kunyar da mahaifin nata yai agabansa ta maida kanta ƙasa haɗe da cewa, "mungode Allah ya saka da alkhairi". "Amin Aïcha bari natafi lokacin tashin jirginmu ya kusa, dan Allah Aïcha koda zuciyarki bata amince dani ba kada kifita barar nan har na dawo, taimako a musulunce dolene ga mai halin taimakawa amma ita soyayya ba dole bace, koda bakya sona bazan fasa taimako ku ba dan ganin na kubutar daku cikin wannan halin da kuke ciki". Sai alokacin Aïcha ta ɗago kai ta kallesa dan gasgata maganar da yake faɗa kafin tace, "Mungode sosai Allah ya tsare hanya ya kaika lafiya kuma yadawo dakai lafiya". Cikin jin daɗin addu'ar tata ya amsa mata da amin sannan yai mata sallama ya shiga motarsa ya tayar yabar wajen.. A gurguje ya shiga shiryawa Mahmoud na tambayarsa daga ina yake tun ɗazu yanata nemansa ya amsa masa "daga wani wajen". Ataƙaice yaci gaba da shirinsa lokaci ɗaya yana amsa kiran Meenal dake tambayarsa ko ya iso yace mata gashi nan ma yanzu zai wuce airport ɗin tayi masa addu'a Allah ya saukesa lafiya kafin yakashe wayar suka fito yai sallama dasu Jaddi da kawo sannan suka wuce Mahmoud ya saukeshi a airport, dama a ƙurarren waje suka iso don haka basu tsaya wani ɓata lokaci ba tunda tun safe dama yagama magana dashi akan kula da aikin nasa da zaiyi tare da bar masa duk wani abun da za'a buƙata ya kuma kyautata masa shima Sannan yawuce dan har angama kiran passengers jirginsu ya tashi. *Nigeria* Ana gama kiraye-kirayen sallar azahar ta karfe biyu jirginsu Mutallab ya sauka, wayarsa ya ciro da niyar kiran Jalil yazo ya ɗaukesa sai kuma wata zuciya ta hanashi saboda surprise ɗin da yake son yimasu, Dan haka taxi ya tsayar ya ɗauki drop da zata ajiyesa har gida, bayan angama saka mashi kayansa ya shiga baya driver ya ɗauki hanya yana gaishesa cikin girmamawa tare da mamakin anya wannan ba shine hamshaqin mai kuɗin nan da ake nunowa a tv ba ko kuma dai kamace? Suna kan hanyarsu taƙarasowa gida sai wata babbar mota tazo ta gitta masu wanda ba don tsarewar Allah ba da drivern taxi ɗin dayake ƙwararre yi saurin kaucewa motar suka wuce ta gefen matar tasu ta nufi wani symbol ta tsaya da ba abinda zai hana babbar motar tabugesu suyi cikin daji, Mutallab da hankalinsa yai mugun tashi ya samu ya fito cikin motar daƙyar saboda hayaƙin daya turnuƙe cikin motar yana ambaton sunan Allah ya kuma taimakawa drivern yafito shima yana tari, wayarsa ya ciro dake gaban aljihu yakira Aryan saboda bai so yakira su Jalil ya tayar masu da hankali, bugu ɗaya a na biyu aryan ya ɗaga Mutallab ya sanar dashi inda suke yace yazo yaɗaukesa, yadda Aryan yaji Muryar Mutallab ya matuƙar tayar masa da hankali, cikin rudewa ya shiga jero masa tambayoyi, "Mutallab lafiya? Meya faru? Yaushe kashigo ƙasar? Ko dama kadawo?" "Ni isowata kenan yanzu Aryan, kazo ka ɗauke i". "Ok ganinan zuwa". Aryan Yafaɗa tare da miƙewa ya nufi wajen motarsa, cikin mintunan da basu wuce goma ba sai gashi ya iso wajen duk da tazarar dake tsakani, da alama gudu yai sosai dan koda ya iso wajen aguje ya taka burki tare da fitowa ya nufo wajensu. SHAFI NA HAMSIN DA TAKWAS. *MUTALLAB ASAD*      Arewabook:- billysfari       Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne. A dai-dai lokacin data shige motar Aryan ta kunno kai idanuwansa suka hango masa ita lokacin da take ƙoƙarin shigewa cikin gidan yayin da Kamal ya kafeta da idanuwa yana yaba sura da kuma tsarin da Ubangiji yayi mata tamkar dai ita ta halicci kanta, nan idanuwansa suka sauka akan manya-manyan flaks da ake fitowa dasu daga cikin mota ana shiga dasu cikin gidan, tashin hankali da tsantsar ɓacin rai ne suka bayyana ƙarara akan fuskarsa musamman lokacin da idanuwansa sukayi arba da fuskar Kamal daya juyo yana murmushi bayan sun kwashe kayan ya shige motarsa ya tayar yabar wajen, wani irin dukan stearing wheel ɗin motar Aryan daya dawo da niyar ba Afrah hakuri yayi yana rumƙe hannunsa haɗe da ji tamkar zuciyarsa zata fito, wato dama shi Afrah ke renawa hankali ashe tasan wancan yaron? Dama duk kukan munafurci takeyi tare take dashi bai sani ba! Me yayi mata haka zata yaudaresa ita da yayanta dan ya tabbata yana sane dako ma meye, daƙyar ya iya jan motarsa yabar layin yana jin gabaɗaya duniyar bata yimasa daɗi... Afrah tsaye tayi cikin palourn tana kallon uban flask ɗin da aka jere tsakar palourn cike da mamaki, ga wasu jugs masu ɗaukar hankali da ƙyalƙyali har guda uku, kamar Mutallab yasan me ake suna fita ya sauko ƙasa, mamakin ne shima ya kamashi ganin manyan-manyan flask kusan guda biyar da fruit da jug har uku, tante Sajida da fitowarta kenan tace, "A'a daga ina haka aka fito da wannan abun arziƙin". Afrah na dariya tace, "Buduwar ya Mutallab ce takawo masa". "Ahh..to MashaaAllah kice aikin surukar tamu ce? Dama Yanzu nake son na tambayi me za'a dafa da marece nan, "aikuwa kisha zamanki ki huta tánte tunda ga wani ankawo nasan zai wadatar har abayar" "Haka ne to sannunta da ƙoƙari Allah yayi albarka". Baice komai ba yafice daga palourn ya nufi cikin compound ɗin saboda yasha iska kafin lokacin magrib yaƙaraso ayi kiran sallah. NIGER. Aîcha na shiga gida babbar yaya ta kalleta haɗe da cewa, "Aicha ya naga kin shigo kina murmushi ke da kika fita kina kuka?" Sai da tayi dariya sannan tace "babbar yaya bari kawai abun Alkhairin ya samemu, wannan Alhajin ne daya taimakeni jiya yazo ya bawa Baba kudi masu yawa yace kada nakara bara danAllah." Mahaifiyar tasu ce ta kalli baba da ya ajiye wata takarda nannaɗe da kudi yana faɗin "Ina kike zo nan ki kirgamana kudinnan." Ganin damen ƴan dubu dai-dai kusan guda 5 yasata faɗin, "Dubu dari biyar ne baba." Washe bakinsa yayi yace, "Ke kuce dai arzuki yazo? Kunga amfanin barar ko yanzu da bama fita muna zaune uban wa zai ganki yabamu kudinnan Aicha." Mama ce ta dan tattaka tace " kunga kyakyawar diyata mai jinin Arzuki kullum abunda Nake gayamiki kenan Ai kidaina shigar wannan mahaukatan da yanzu mun zama attajirai. " " To ai baba yayi masa Alkawari bazamu sake bara ba." " Ke dallah yimun shiru kikasani ma ko zai sake dawowa? Kawai saboda ya bamu kudi sai mu daina bara yanzu gaba wayasani ko Allah ya kawo mana mai bamu gida da mota."  Daga ita har yayarta saƙin baki sukayi suna kallon ikon Allah." " Gwara ma ki shirya dan anjima ma sai mun fita bara yanzu tashi jiki kiramun habu magini acan gefen zaurensu." Batare datace komai ba ta Mike tafita. Mama kuma tace " Kema naga kwana biyun nan bakison fita kwata kwata ko menene dalilinki." " Bafa najin dadi mama." " Ni dai wannan sakarcin bazan dauka ba bayan ƙinsan da karfinki muke wasu abubuwan agidan." Shiru tayiwa maman batare da tace komai ba." To yanzu ki dakko kudin da muƙe tarawa muga nawa ne sai a haɗa abashi afara gyaran gidan nan ina tsoron damena taci karfi kuna ganin ruwan sheƙaran jiya yaso ya taɓa ginin nan. Kamin yarufe baƙin sai ga Aicha ta shigo ita da habu sallama yayi cikin ladabi ya gaidasu, sai da yazauna suka gama lissafin komai sannan Aka dauki kudi aka bashi shikuma yace akan gobe za'a fara gini sukayi sallama. "

Chapter 32 of 54