ace munyiwa duka shegun su uku sunbar garin, amma ko yanzu bata ɓaci ba, gobe zanje ƙauyen can naga malam nakan ruwa, dole nayi abunda na daɗe banyi ba koda yankane yake so ayi yadda zan samu biyan buƙata da gaggawa, kai ko sadaukarwa takama nayi zanyi a kawar mana da wannan shegen yaron". Cikin dabara Jamil dake son zuwa yasan malamin shima yace, "Shekenan ai sai nakaiki Umma ko kuwa?" Cikin takaici Umma tace,
"Bana buƙata kaje can da sokancinka ace sai ƙaninka na kusan biyar yazo yayi maka fintinkau". Dariya Jamil yasaka tare da ficewa yana cewa, "bani nakar zomon bada Umma easy". Ta dannan ma bayansa wata harara har yafice tana sake jan tsaki akaro na ba adadi.
Aunty Amarya ma dai itama tana can ɗauki da nata ɗan guntun baƙin cikin, kallon ƙananan yaran nata tayi da take ganin shekaru masu baƙin yawa agabanta kafin sukai matakin da take hango Mutallab ɗin aciki tace, "Kai Walid ba nayi maka magana akan kallace kallacen banzan nan awaya ba? Je ka ɗauki littafanka kayi karatu, ku baza kuyi koyi da Afrah ba? Ko Bakwa ganin yadda Jalil da Mutullab suke? Kullum ina nuna muku kukasance kamar su koma fiye dasu dan bana son sufiku komai". Wani kallo Walid yayi mata yana turo baki gaba kafin yace, "Ni Anty ki ƙyaleni na huta mana? Kin dameni komai dai muzama kamar Ya Mutallab ko Ya Jalil, sai kace su wasu ne da suka fimu". Zaro idanuwa Aunty Amarya tayi waje tana cewa, "Walid! Ni kake gayawa haka?" Banza yayi mata yayi shigewarsa cikin ɗakinsa yana ƙunƙuni dan ya tsani tariƙa kwatantasu da ya Mutallab saboda yanda suka saka masu tsanarsa.
**********
Dady bai samu zuwa gidan su Mutallab ba sai bayan sallar la'asar, Abba na zaune palournsa yana yiwa Jamil faɗa akan wasu kuɗaɗe da aka kirasa a ɗaya daga cikin gidajen mansa aka sanar dashi cewa ya je ya karɓa mai gadi yayi sallama, Afrah kaɗai ce ta iya amsa masa sallamar amma Jiddah dasu Walid naji sukayi banza dashi dan hankalinsu na akan tv da suke kallo anan main palour, cikin ɗan barkwancin baba maigadi yace, "Shalelen babban mutum afaɗawa Alhaji yayi baƙi". da to Afrah ta amsa tana dariya kafin ta juya tanufi sashen na Abba, tana kawowa zata shiga ya Jamil nafitowa ransa a ɓace saboda faɗa da Abba yayi masa akan ƴan kuɗaɗe ƙalilan da yake gani ba komai bane dan ya karɓa, wani mugun ranƙwashi ya sakar mata akai haɗe da cewa, "Munafuka me kika zo yi anan?"
Afrah da zafin ranƙwashin ya game mata a jiki kasa cewa komai tayi ta sadda kai wasu ƙwalla na cika mata idanuwa, "Koma dai me kikaji ni kuɗin ubana naci, yayanki kuma kuɗin haramun ne da bamu san ta inda yasamosu ba". Jamil yafaɗa rai aɓace sai kace ita tayi masa faɗan sannan yabar wajen, share ƙwallan da taketa faman riƙewa da sukayi nasarar zubo mata a fuska tayi kafin ta shiga cikin palourn na mahaifin nasu dake ƙoƙarin shiga bedroom ɗinsa bakinta ɗauke da sallama, juyowa yayi Afrah tace "Barka da yamma Abba, baba maigadi ne yace a sanar dakai kayi baƙi a waje".
"baƙi kuma?"
"Eh Abba".
"To jeki gani nan zuwa".
Ta amsa mashi da to sannan ta juya tafice daga ɗakin, koda tadawo palourn Jamil na zaune shida mahaifiyarsa agefe yana faɗa mata abinda Abba yayi masa, don haka bata tsaya ba ta wuce ɗakinta duk da ƴan uwan nata na zaune har lokacin suna kallonsu.
Cikin mintunan da basu fi biyar ba Abba ya fito tare daba maigadi izinin buɗe gate ɗin yace yacema baƙin nasa su shigo, a take maigadi ya wangale masu gate ɗin haɗe da sanar masu da saƙon na Abba,
Abba na tsaye motocin guda biyu suka shigo harabar gidan har sukayi parking, yaran Dady da sukayo masa rakiya ne sukayi saurin fitowa daga cikin motarsu suka tsattsare wadda Dady ke ciki suna wani mazurai da idanuwa kafin ɗaya daga cikinsu yabuɗewa Dady marfin motar yafito, ɗan zaro idanuwa Abba yayi cike da mamakin ganin wanda ke gabansa Dady yaƙaraso wajen fuskarsa ɗauke da murmushin ganinsa shima yana buɗe masa hannayensa suka rungume juna, cikin mamakin da har yanzu bai saki Abba ba ya kalli Dady yace, "Wa nake gani haka kamar hon Abdulmalik Mu'azzam? anya kuwa ba ɓatan hanya kayi ba?" Dan idan Abba bai manta ba sun shekara uku zuwa huɗu basu haɗu ba duk da kasancewarsu abokanan junana tun a secondary kuma suka zo kasuwanci ya sake haɗa su, dan bazai manta haɗuwarsu ta ƙarshe dashi ba a ƙasar china, Dady na dariya ya miƙa masa hannu haɗe da cewa, "Ni ɗin ne da ƙafata nace bari nazo na kawo ziyara wajen ogana Alhaji Asad". Saboda duk da zamansu abokanai Abba ya girmi Daddy nesa ba kusa ba dan ko a secondry ya bashi shekara ɗaya, haka ma wajen kasuwancin Abba ya lunkasa arziƙi sosai kafin wannan asarar da Jamil keta faman janyo masa, tsakanin shi dashi kawai gamon jini ne da kuma soyayya idan tahaɗa...
#Mutallab Asad
#Tagwaye Biyar
#Billy S Fari
#Nana Diso
*MUTALLAB ASAD*
*PAID BOOK #500*
*TAGWAYE BIYAR.*
NA
*NANA DISO**
&
*BILLY S FARI*
31.
Misalin ƙarfe biyar na Yamma Mutallab ya iso gidansu Meenal da taimakon address ɗin data turo masa, Cikin shiga yaƙe mai dauƙar idanu yasaka light blue din gezner da kansa sanye da hula ligh blue takalminsa kuma fari da agogon daƙe hannunsa, lokacin tana zaune tare dasu Nancy da suka zo mata bayan yau da safe takirasu ta labarta masu cewa, ai sun gama dai-dai tawa da Mutallab Asad yau zai zo sufara shirye-shiryen aurensa, shine fa suka zo mata acewarsu gani ya kori ji, turo ƙofar ɗakin ya Kamal yayi tare da kallon ƙawayen na Meenal dake saman gadon zagaye da ita yana wani lashe baki sannan ya maida kallon nasa ga Meenal yana cewa, "Meenaluwa inafa ganin gayennan ne yake kiranki a waya.." kafin ya rufe baki Meenal da tun ɗari take ƙunci ganin har huɗu da rabi tawuce bai zo ba ta dirko daga saman gadon ta nufo wajensa, a maimakon ya bata wayar dake ringing sai ya ɗagata sama yana cewa, "Waɗannan babes ɗin fa?. Tare da ɗaga mata ido, ba tare da tabi takansa ba ta shiga yin tsalle tana ƙoƙarin kamo wayar dan yafita tsayi sosai duk da ita ɗin ma ba gajeriya bace, sai da ya Kamal yaji wayar ta tsinke an sake kira a karo na uku sannan ya sakar mata wayar shima dan idonsa nakan Nancy ita kuma tafice ɗakin da gudu tare da ɗaga wayar takai a kunne tana sauka kan steps ɗin da sauri da sauri. "I'm very sorry my luv wayar na a hannun ya Kamal ne". Idanuwansa a rufe yayin da kansa ke jingine a jikin kujerar da yake zaune yace, "Gani a ƙofar gida morethan 10minute da suka wuce"
"I'm so sorry". Tafaɗa tare da ƙarasowa gaban gate ɗin tana ƙwalawa maigadi kira, da sauri yafito yaƙaraso wajenta yana cewa, "Gani ƙaramar Haji.." bai ƙarasa ba cikin ɓaci rai ta daka masa tsawa har Mutallab ɗin najiyo muryanta.
"Dama bakada hankaline da zanyi baƙi kaɓarsa a waje har na tsawon mintuna goma? Ashe kai wawa ne jaki da baisan abinda yakeyi ba mijin da zan aurane fa".
"Ƙaramar Hajiya ayi.." wata ƙarar ta sake daka masa cikin ɓacin rai tana cewa, "Dallah malam rufemun baki kaje kabuɗe masa gate, wawa daƙiƙin baƙauye kawai". Jiki na rawa maigadin yaje ya wangale gare Meenal na gefe tsaye, tana ganin motar ta kunno kai acikin gidan ta wani rungume hannayenta aƙirji tana murmushi cike da farinciki, sai da taga yagama yin parking sannan ta juyo kallonta ga maigadi daya tsare motar da kallo yana so yaga wanene hau ta haushi da zai auri Meenal tana nunasa da yatsa tace, "munafiki me kake kallo ne haka ƴan baƙinciki? Next time idan ya sake zuwa gidan nan kabarshi a waje wallahi bakin aikinka kenan!" Takarasa tana jan wani wawan tsaƙi.
Sannan ta nufi wajen motar tare da wucewa gaban motar kai tsaye tana ƙoƙarin buɗe wa, Mutallab dake kallon duk abinda ke faruwa ta madubin motarsa yana ganin zata shigo masa mota yai saurin fitowa daga ciki, yana mamakin irin tarbiyar da yarinyar nan take dashi, ahakan ake cewa ya aureta, Allah ma yanagani wannan yarinyar tafi karfinsa yafison matar fa zasu rufawa juna asiri wacce tasan mutunci da darajar ɗan adam.hakan ya dakatar da ita daga shiga ciki itama ta zagayo ta gefensa tana tafiya cikin rangwaɗa, kallo ɗaya yai mata ya ɗauke kai dan ko yau ɗin ba shigar kirki ne da ita ba, doguwar riga ce ta wani material ɗinkin fitted gown ya matseta tako ina kanta ba ɗan kwali, sai ƴar ligth makeup da tayiwa fuskarta da pink ɗin janbaki data shafawa ɗan ƙaramin bakin nata, cikin jin daɗin ganinsa ta iso gabansa tana cewa, "My love sai yanzu? Gaskiya har nakusa nayi fushi". Takarasa faɗa tana lumshe idanu da jan wani dogon numfashin jin yadda daɗadden turarensa yadaƙi hancinta.
"Jeki ki sanyo mayafinki muyi magana ko kuma nakoma inda nafito". Yafada kai tsaye kamar bashine yayi maganar ba yashiga danna wayarsa. Kallon kanta tayi kafin tace, "My love kwalliyar ce batayi maka ba?" Ta shiga jujjuyawa a gabansa, saurin kau da kansa yayi yana neman tsarin Allah duba da yanayin tsigar jikinsa ce yaji ta tashi dan Mutallab irin mazan nan ne masu tsananin buƙata da kuma ƙarfin sha'awa, hakan ya sashi saurin juyawa yana ƙoƙarin komawa cikin motarsa, da sauri Meenal tace, "No.pls..pls My love kada katafi dan Allah bara naje na ɗauki". taƙare zancen cikin marairaice murya tana haɗa hannuwa waje ɗaya kamar zatayi kuka, ba tare daya juyo ba yace, "Mintuna biyar nabaki saboda ina da abunyi".
"Ok, Dan Allah kada katafi kaji?". Tafaɗa tare da juyawa da sauri takoma cikin gida, maigadi dake kallonsu ta gefen ido ya ƙyalƙyale da dariya duk da baiji abinda suke cewa ba yace, "Madallah, kiyi mana son ranki yarinya ga alama Allah ya kawo mai rama mana". Dan ko ba'a gayamana ba munga alamun ke kike haukanki shi baya sonki.
Meenal kuwa da sauri ta haura sama tana shiga cikin ɗakinta ta iske ya Kamal kwance a tsakiyar gadonta shi dasu Nancy suna fira, sosai abun ya bata mamaki haɗe da ɓata mata rai amma da yake bata son Mutallab ɗin yatafi sai kawai tawuce wajen closet ɗin kayanta tariƙa zubosu ƙasa tana neman mayafin da zata saka, duk wanda ta ɗauko sai taga iya kacinsa ya rufe mata kai dan dama iri irensu ne takeda da kai tsaye za'a iya cewa kawai ƴan kwali ne.
Juyowa ya Kamal da yaji duniyarsa na nema tadawo masa yanda yake so yayi yana kallonta yace, "Meenaluwa wai yaya ne kiketa watso kaya ƙasa haka ko har yanzu gayen naki bai zo bane?" Cikin wani ɓaci rai na rashin samun mayafin da zata rufa ya rufe mata jiki kamar yanda Mutallab ya buƙata tasaki wata irin ƙarar da tasa ya Kamal zubura ya miƙe tsaye.
"Duk kufice mani daga ɗaki wlh bana son ganinku?" Wani banzan kallo Nancy tayi mata haɗe da cewa,
"Da mukayi me? Nifa bana son wannan kalar wulaƙancin naki Meenal?" Buɗe baki Sarsy tayi tare da miƙewa tana cewa, "oho waya sanar mata ko dai dama can ƙarya takeyi ba wani zuwa da Mutallab ɗin zai yi zancen aurenta shine take so taƙare mana da borin kunya". Idanuwanta suka sauka akan mayafin Sarsy ɗin da zai iya kaiwa ƙirjinta, ai kuwa da sauri tafizge shi ajikinta tare da ficewa aguje, hakan yasa duk suka bi bayanta har ya Kamal ɗin suna tunanin anya lafiya take?, Sai dai suna fitowa bakin ƙofar palourn na ƙasa suka hango Meenal ɗin har takai wajen motar Mutallab ɗin ɗin tana haɗa numfarfashi, "I'm sorry love na tsaya neman mayafin ne ban samu ba, wannan ma na ƙawata ne Sarsy". Taƙare zancen tana murmushi tare da nuna masa inda su Sarsy ɗin suke tsaye suna yiwa junansu gulma a kunne ɗan taji lokacin da suka biyo bayanta, ɗan juwa yai kaɗan zuwa sashen data nuna masa ya hangosu har suna ɗago masa hannu, ɓare baki yai haɗe da maido kallonsa ga Meenal aransa yana cewa duk kanwar ja ce ita da ƙasashen nata ɗan basuda wani banbanci saboda suma ɗin ba shigar mutuncin ce ajikinsu ba, ajiyar zuciya ya sauke yana gyara tsayuwarsa tare da ɗauke kansa daga kallon da sukeyiwa juna dan ko yanzu banbancin shigarta data ɗazun shine kanta kawai zuwa ƙasan wuyanta data rufe, amma jiki kam yana nan a bayyanensa takowane lungu da saƙonsa. Cikin wata iriyar murya yace, "Babu amfani ga ƴa mace tariƙa tallata jikinta haka tana bayyanar da surarta ga mazajen daba muharramanta ba but ke nalura hakan ba wani abubane agareki, yanzu kamammiyar macce nutsastiya zata tsaya tana zagin wanda ya girmeta? Hakan tarbiya ce ? Yanzu kina cikakkiyar budurwa kin ruga kin tafi kin kara rugawa ƙin dawo. anyway muyi maganar data kawoni". Shiru yai yana ɗan juya maganganun da yake son faɗa mata abaki kafin can ya sake ɗago kai yana kallonta tacikin idanuwanta da take kallonsa yace, " sincerely Meenal ki haƙura dani saboda daidai da rana ɗaya ban taɓa sha'awar ki zamo mallakina ba ko kuma uwar ƴaƴana, nafaɗa maki wannan kalmar ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba amma kin kasa fahimtata har kinsa iyayenmu sun shiga cikin maganar, to bazan ɓoye maki ba Meenal ni bazan aureki ba saboda bazan iya baki farincikin da kike so kisamu daga wajena ba, shiyasa da mahaifina yasa nazo har na amincewa zuciyata da zuwan dan nafaɗa maki gaskiya ɗaya tilo dake zuciyata, pls ki ƙyaleni kisamu wani wanda ke sanki ki aura ɗan Allah". Ya ƙare maganar yana haɗe mata hannayensa waje ɗaya sannan ya juya zai shiga motarsa.
Meenal da tunda yafara magana taji Numfashinta ya tsaya cak tana ganin ya juya zai shiga motarsa taji kamar anfizgo mata shi da ƙarfi tace, "kada kayi mani haka Mutallab! Wane namijin kake tunanin zan samawa kaina da zaiyi daidai da rayuwata sama dakai! Wlh ban taɓa son kowane ɗa namiji ba idan ba kai ba dan Allah kada ka juya mani baya".
Ba tare daya juyo ba yace, "kada ki yaudara kanki Meenal, ke kin sani bamu dace da juna ba, musamman daya kasance ɗaya ɓangare tsakanina dake baya muradin kasancewarmu tare, a karo na biyu zan sake roƙonki mubar wannan maganar kada nazo nayi maki abunda bazakiji daɗinsa ba".
Meenal da taji wani sabon tashin hankali ya taso mata tasa hannu ta dafe kai haɗe da cewa, "A'a Mutallab! Bazan iya haƙura dakai ba, komai zaka yimun na amince bazanji ba daɗi ba wallahi". Bai tsaya saurarenta ba ya shige motarsa tare da jan marfin zai rufe tariƙe, "pls Mutallab yakamata kayiwa zuciyata adalci, shekara nawa tana dakon sonka? dan Allah kada kawatsa mani ƙasa a idanuwa dan wallahi babu wani ɗa namiji a duniya da zan iya bibiya arayuwata kamarka". Wani mugun kallo yayi mata tunowa da rana ta biyu da fara ganinta da yayi tare da wani namijin har yana tallabota ajikinsa yace, "Allah Meenal? Karki manta dawa kike magana? Mutallab Asad Mutallab nefa da har ajikin wani namijin ya ganeki sannan kice baki taɓa son wani ɗa namiji ba aduniya sai Ni!, Malama kije ki gyara zancenki da kuma rayuwarki hakan zai fimiki akan wannan ɓata lokacin naki da kikeyi". Yana gama faɗa haka ya fizgi marfin motarsa ya rufe ya tayar ransa aɓace yabar wajen, dan bai san abinda yasa duk lokacin daya tuna da waccan ranar sai yaji ɓacin rai ya taso masa tare da jin tsanarta mai tsanani a zuciyarsa.
"A'a Mutallab! ka tsaya nayi maka bayani.." amma ina tuni maigadi ya buɗe masa gate yafice daga gidan, durƙushewa wajen tayi tafashe da kuka, Kamal dake tsaye tare dasu Sarsy suna fira shima tamkar wani macce ya nufo wajen yasa hannuwa biyu ya ɗagota, sake zubewa ƙasa tayi tana rusar kuka tare da cire mayafin dake jikin nata tayi jifa dashi haka ma takalman ƙafarta, Nancy da suka ƙaraso wajen suma suka shiga tafa hannuwa suna taɓa baki tare da riƙe haɓa cike da mamakin yanda take rusar kukan sai kace wacce akayiwa albishir cewa Mamah ta mutu. Kamal daya fara kaiwa wuya da kuka nata rai aɓace yace, "Wai uban me yayi maki kike wannan kukan haka da bazaki iyayin shiru ba? Kin ga Meenaluwa yaroncan kema kin so kanki da yawa, kina ganinsa kinsan ba sa'arki bane wlh dan haka ki haƙura dashi kisamu dai-dai ke.." cak Meenal ta tsaya da kukanta jin maganganun dake fitowa daga bakin yayan nata kafin tasa hannayenta ta share hawayen dake fuskarta haɗe da miƙewa tana yimasa wani mugun kallo, "Ya Kamal me kake cewa?" Tafaɗa tana kallonsa wasu hawayen da suka kasa tsayawa na zubo mata, ya Kamal na buɗe baki zai maimaita abinda yace Meenal bata tsaya wata wata ba ta ɗaukesa mari tana cewa, "Na zata kai ɗin yaya nane da zaka iya tsaya mani takowace fuska ashe kai ɗin maƙiyinane ban sani ba? To wlh bari kaji ko zan mutu bazan taɓa haƙura da Mutallab ba dan yanzu ma nafara son shi! Kuma duk wanda ya nuna baya son tarayyata dashi na tsanesa, na tsanesa irin tsanar da batada iyaka har abada". Tana kaiwa nan tawuce cikin gida fuuu.. tabar ya Kamal dafe da kunci, dariya Sarsy ta kwashe da ita tana kallon Kamal daya gama tsarasu yanzu haɗe da cewa, "Sannu fa yayanmu! Gaskiya Meenal taci kai yakamata ku shiga farautar nemo mata abun yarinya kafinta tada Bama bamai agidan nan". Bata rufe baki ba itama Kamal ya ɗauketa mari sannan yabar wajen, dariya su Nancy suka saka mata itama kafin suyi gaba abunsu ba tare da sunce mata ko uffan ba, dole jiki a sanyaye Sarsy ta ɗauki mayafinta da Meenal tayi jifa dashi tabi bayansu tana jin haushin saka bakinta a maganar gashi ta janyowa kanta mari a banza.
Mutallab kuwa daga nan gidansu Aryan ya biya ya gaida Ummie bayan yayi sallar magrib, sun jima suna fira da ita har yake sanar da ita zancen tafiyar da zasuyi da Aryan sai dai bai faɗa mata ko ina bane, shiru tayi kafin tace, "Anya Aryan nada lokaci Mutallab? Ko ka manta aikin office yakeyi kuma hakan zai iya jawo masa matsala". Dafe goshi Mutallab yai haɗe da cewa, "Oh my God, wallahi Ummie namanta, shi kuma bai tuna mani ba". Ya ƙare zancen yana kallon Aryan dake latsar wayarsa yana murmushi dan duk maganar sukeyi yana jinsu, dariya Ummie tayi haɗe da cewa, "Ai kasan halinshi indai akanka ne".
"Ok to shikenan, bari nafara tafiya idan abubuwa sun kamala yanda Yakamata na dawo sai ya ɗauki hutu kona sati ɗaya ne muje yaga yadda abubuwan ke tafiya, kinga Ummie koda ace shi baida lokacin zuwa ya zauna acan zai iya buɗe wuri shima ya samu ƙwararrin ma'aikata ya saka ana biyansu".
"Yawwa wannan a shawara ce ka kawo Mutallab Allah ya taimaka yakuma dafa maku".
"Amin ya rabbi Ummie, Dude tashi' muje ga sallar isha can an kira". Mutallab yafaɗa tare da miƙewa, adawo lafiya Ummie tayi masu tare da cewa Mutallab kada yawuce tacan har sai ya dawo yayi dinner ya amsa mata da to sannan suka fice.
Bayan sunyi sallah sun dawo ne Aryan ke tambayar Mutallab yanda sukayi da Meenal dan ɗazu da safe ɗaya biya ta shagonsa ya faɗa masa cewa zai je wajenta, ajiyar zuciya ya sauke kafin yace, "Mun ƙare wannan maganar da ita saboda munkai ƙarshe nafaɗa mata cewa taje tanemi wani Allah ma yasani bazan iya aurenta ba". Da kallo Aryan ya bishi yana mamakin taurin kai irin nasa, to wai me Meenal tarasa da bazai karɓi soyayyarta ba? Kyau, kuɗi, gayu da sauransu da ake so asamu ƴa mace dasu a zahiri duka ta haɗa, to meyasa zai gujeta?
"Saboda bana santa". Yaji Mutallab ɗin ya bashi amsa lokacinsa suka ƙarasa shigowa palourn ba tare daya san maganar ciki da yakeyi ba tafito fili...
#Mutallab Asad
#Tagwaye Biyar
#Billy S Fari
#Nana Diso
*MUTALLAB ASAD*
*PAID BOOK #500*
*TAGWAYE BIYAR.*
NA
*NANA DISO**
&
*BILLY S FARI*
32.
Aryan bai tankasa ba har sai da Ummie ta zuba masu abinci sun fara ci sannan ya kallesa yace, "To wai kai MAM duk wannan ƙiyayyar da kake yiwa Meenal tame ce? Naga dai duk da kanata furta baka sonta baka taɓa nuna mana hakan azahiri ba".
"Kamar ya? Ai inaga kaine mutum Nafarko da zai fara bada labarin kalar tsanar da nake yimata har a zahirance".
"Ehm! To nidai banga alama ba, ɗan daka tsani Meenal dole ka datse duk wani abu da zai haɗaka da ita, a fahimtata kana don Meenal MAM, just that ka tsani ɗabiun da takeyi ne da kuma halayyar ta". Ture abincin dake gabansa Mutallab yai haɗe da cewa, "To hell with loving her da kake zance Aryan, ni ba yaro bane da za'a ce bazan iya banbance me nake so ba da wanda bana so, to accept it or not bana san Meenal". Yaƙare zancen haɗe da miƙewa yana goge bakinsa. Dariya Aryan yai haɗe da cewa, "Easy mana MAM, me kuma yai zafi haka da zaka tashi kabar abincin?"
"Am ok, sai munyi waya". Ya ƙare zancen yana barin wajen tare da isko Ummie dake zaune palour tana kallo yai mata sallama baya ya ajiye mata kuɗi yace ta sayi goro, godiya tayita masa tare da sanya mashi albarka tace ya gaida Afrah sannan ya wuce..
**********
Sanin da Mutallab yayi yau bai je ya gaida mahaifin nasa ba ya sashi yana dawowa kai tsaye yawuce part ɗin sa, ɗan tuni ya janye masa dokar rashin shiga cikin gidansa saboda gyara masa ɗakinsa da yakeyi, abincin gidan ne dai tun wancan lokacin har kawowa yanzu aka dena basa shi kuma bai taɓa nema ba tunda yasan mahaifin nasa ya hana abashi. Bakinsa ɗauke da sallama ya shigo palourn duk mutanen gidan na zaune har Afrah, ko kallon gefen da suke baiyi ba yace, "Umma sannunku da maraici". Yana kallon gefen da Afrah ke zaune tana yimasa sannu da zuwa tare da gaishesa, fuska a sake ya amsa mata yana cewa, "Abba fa?" Ba tare daya damu da rashin amsa gaisuwar tasa dasu Umma basuyi ba, "yana ciki ya Mutallab". Afrah ta amsa masa ya jinjina mata kai sannan yawuce abunsa.
Sallama yayi abakin ƙofa Abba ya bashi izinin shiga dan dama shi yake jira tun ɗazu, tun kafin yaƙaraso Abba yace, "Sannu da zuwa Alhaji Mutallab, yanzu nake cewa idan baza ka samu damar zuwa ka gaisheni ba ni sai naje na gaisheka tunda kana ganin kayi kuɗin da baza ka iya martabani ba yanzu". Jiki a sanyaye Mutallab yaƙarasa wajensa cikin girmamawa ya samu waje ya zauna agabansa yana russunar da kansa ƙasa yace, "Haba Abba, wannan wace irin magana ce kakeyi haka! Kayi haƙuri bana so na sake ɓata maka rai shiyasa ban samu shigowa da safe na gaisheka ba, kayi haƙuri dan Allah Abba, Ina wuni".
"Hmm lafiya lau Mutallab amma ni kagama renani tare daɗaukata ba abakin komai ba, ace ɗan dana haifa zai samu buɗi amma bazai iya sanar dani ba saboda yana tunanin guminsa ne ya manta da cewa nine mahaifinsa! Yanzu duk abunda kazama da ban hanaka aikin ba ai da bakazama ba Ni daman tun abaya gata naƙe ma kasan zafin nema, Ko da yake baka buƙatar tubarrakina tare da sanya maka albarka shiyasa".
"Ba haka bane Abba, amma kayi haƙuri nayi kuskure da ban sanar dakai ba".
"Allah dai ya kyauta, ai ɗan kaga uwarka bata raye shiyasa ka ɗaukeni ba abakin komai ba, Allah dai yajiƙan Mariya dan kam albasa bata biyo halin ruwa ba". Ya ƙare zancen yana share ƙwallon dan har ƙasa zuciyarsa yaji zafin wannan abun da Mutallab yayi masa na ɓoye mashi samunshi sai dai yaji zancen abakin duniya, sosai jikin Mutallab yayi sanyi da ganin rashin dacewar abinda yayi, kina komai shi mahaifinsa ne Yakamata ace yasanar dashi duk wani cigabansa akida kuwa bazai yimasa addu'a da fatar alkhairi ba, hakan yasa yayita bashi haƙuri har ya samu daƙyar ya haƙura kafin ta bijiro masa da zancen zuwa wajen Meenal da yace yayi, bai son ya sake ɓata masa rai a wannan karon ma dan haka kai tsaye yace, "Abba naje".
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 54