wani ɓangaren yaga laifin Afrah saboda baiga dalilin da zaisa ta tsaya ta saurari wani ba bayan tasan Aryan zai zo a wannan lokacin, amma idan shi kuma Aryan yai tunani ai yasan Afrah yasan tarbiyarta kuma yasan abinda zata iya da wanda bazata iya ba, me yasa zai bari zuciya ta ɗebesa haka ya aibantata?, Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya shiga sake gaida tánte Sajida tare da tambayarta babu dai wata matsala komai lafiya ta amsa masa da "ehh" sannan yamiƙe yafice daga ɗakin, dama tuni tánte ta jere saman dining da abinci kafin yafito ɗin don haka kai tsaye ya nufi can Afrah na biye dashi, bai ce mata komai ba har sai da tagama zuba masa abincin yaci ya ƙoshi ya taso ya dawo palour ya ɗauki remote ya kunna kallo sannan ya juyo yana kallonta yace, "Auta bazan goyi bayanki ba saboda kema baki kyauta ba, banga amfanin saurarar wani ba tunda kinsan kina son Aryan kuma dashi kaɗai zuciyarki ta amince, kada ki sake aikata hakan domin ko nine abunda zan aikata kenan"
"Bazan sake ba ya Mutallab kayi haƙuri".
"Shikenan kije ki huta kema tunda yanzu kika dawo". Jiki a sanyaye ta amsa mashi da "toh" sannan tabar palourn.
Tana barin wajen wayarsa tayi ringing, dauƙa yayi yana sallama yaji muryar Meenal tana cewa,"Yayana sannu da sauka da fatan kasamu kowa lpya?" Sai da yai murmushi cikin wani irin sanyin murya yace, "Sorry Meenal ban kiraki ba ko?."
"Eh Yayana amma ba komai tunda ka iso lafiya, na jika wani iri lafiya dai ko?" Sai da yaja numfasa sannan yace "Gajiya ce sai kaina danaji yana don fara ciwo." "Kasha magani pls?"
"Ai nasha tunda gashi ina jin muryanki, Nasan ita kaɗai ta wadatar in Sha Allahu". Wani daɗi yakama Meenal tana lumshe idanuwa tace,
"Duk da haka ka daure kasha sai ka kwanta ka huta anjima sai muyi waya ko?".
"To Shikenan nagode da kulawarki, kema ki kula mani da kanki sosai kinji ko". Sautin dariyarta ne ya bayyana cike da farincikin data kasa ɓoyewa tace, "zanyi haka yayana, akwai sako zan bawa ya kamal yakawo maka".
"A'a Meenal nagode basai yakawo ba." Cike da shagwaba tace, "Dan Allah yayana kada kace haka, saboda kai fa nayi." "Tohm sai yazo." Mutallab ya faɗa yana kashe wayar jin tana shirin jefasa cikin wani yanayi, Ko da yakare wayar juyowar da zai yi yaga Jalil tsaye abakin ƙofa cike da mamaki, murmushi ya sakar mashi kafin yace, "ƙaraso mana andawo?" Yana kafewa da idanuwa ganin yadda ya ɗan sauya.
"Gaskiya ranka ya daɗe ka shammacemu, tafiya haka ba sanarwar yallaɓai?" Dariya Mutallab yai haɗe da cewa, "Ba gashi nayi maku bazata ba? ko na koma abina bakuyi farincikin ganina ba dan auta ma haka tace". Jalil daya ƙarasa shigowa ciki ya zauna a saman kujerar dake kallon tasa yace, "Wa munan ranka ya daɗe mu da mukayi kewarka ba kaɗan ba! Ba shago ba ba gida ba duka mun matsu kadawo".
"To gani na dawo kafin kuma na koma, Hope dai ba wata matsala ko?".
"Babuta ranka shi daɗe".
"Alhamdulillah amma ya akayi naga kamar ka ɗan faɗa".
"Ciwon dana faɗa maka kwanaki ina fama dashi ne ya ɗan kwantar dani ana alhamdulillah tunda gashi na warke". Idanuwa Mutallab ya tsura masa yana sake hango ramewar da yai duk da yaɗan murmure ma yanzu akan da kafin yace, "Me yasa baka sanar dani ba har ciwo ya kwantar dakai haka?" Mutallab yai maganar cike da damuwar da dama gidunta yasa suka ƙi sanar dashi zancen rashin lafiyar.
"Nafa warke ya Mutallab" Jalil yafaɗa yana shafa kansa saboda wani kallo da Mutallab keyi masa, nan dai ya nuna masa bai ji daɗi ba kuma adena ɓoye masa irin wannan saboda sunfi komai muhimmanci a wajensa. Sune fitilarsa kuma duk wani abu da yakeyi yanayinsa ne har dasu, haƙuri yai ta bashi kafin ya samu ya haƙura ɗin haɗe da miƙewa ya wuce ɗakunan ya watso ruwa ya sauya kaya yazo yaci abinci shima sannan ya dawo palourn suka shiga tattaunawa akan yadda kasuwar ke tafiya yanzu.
Suna cikin tattaunawar wayarsa ta sake ɗaukar ƙara yakai hannunsa yadaga yana mai karawa akunnensa bakinsa kuma ɗauke da sallama. Cikin wata murya mai ciƙe da shagwaɓa data nemi rikirkita Mutallab tace. "Yayana ya jiķin naka gashinan zan bawa kamal yakawo maka salon, dan Allah kaci harda kunun aya Nayi maka Akwai wani maganin ciwon kai da Dady ke siyo mana a Egypt Nasaka maka acikin pack din Please kasha." Wani sanyi yaji aransa yanajin Meenal ɗin har cikin ransa, Yanayin miƙewar da tsigar jikinsa tayi ya sashi ajiye remote ɗin hannunsa akan center table yayi baya yana ɗan kishin giɗawa ajikin kujerar haɗe da lumshe idanuwa yace, "Ina matuƙar godiya da wannan kulawar Meenal, amma meyasa kika bani kulawa haka? ga kayan daɗi kin haɗa mani ga kuma magani?".
"You deserve morethan that yayana, da za'a kwantar dani ace lallai sai nafaɗi dalilin haka da nakeyi ko a yanka ni to tabbas za'a yankani saboda ban sani ba, abu ɗaya na sani tun a waccan ranar dana fara ganinka na jarabtu da sonka, kuma da zuciya ɗaya nake sonka yayana kuma na tabbata har na mutu bazan dena ba."
Yanayin shauƙin da Jalil yaga ya'yan nasa ya shiga ya sashi miƙewa ya silale yabar palourn yana masa dariya, sau da rana ɗaya bai taɓa tunanin ya'yan nasa zai saurari Meenal ba balle har yafara soyayya da ita haka, dan ko makaho ya kalli yanayin da yayan nasa ke ciki a halin yanzu zaisan ya gama kamuwa da cutar so har da daɗin ƙauna akai, "Thank you ƙanƙara". yafaɗa ciki da kosawa dajin muryartata saboda yadda take haifar masa ajikinsa, yasan idan baiyi wasa ba take labarin zai cansa masa yanzu. A hankali yake jin soyayyar Meenal yanzu tana ratsa masa zuciya tare da kara jin Meenal din har cikin ransa duba da irin yadda take damuwa dashi haɗe da bashi kulawa.
A ɓangarenta kuma tana gama wayar ta kalli ya Kamal tana marairaice fuska, "ya Kamal Dan Allah katashi kaje tun ɗazu fa yakamata kaje amma sai faman latsar wayarka kakeyi". Banza yayi mata har sai da Mommy tace, "Yanzu kai kamal bazaka taimaka ba kaje ka kaimata duk magiyar nan da maƙe Muryar da takeyi maka?" Ɗago kai ya yi ya kalli Mommy dake maganar sannan yace,
"Mommy yarinyar nan fa ta renani da yawa, fisabilillahi yanzu Mommy kamarnni Ina yayan Meenaluwa zata aikeni wajen kaiwa saurayinta saƙo? Saboda Allah fa ayi maganar gaskiya ai wannan sai taja yarainani". yafaɗa yana ƙare zancen da dariya ganin yanda ta wani marairaice fuska, murmushi Mommy tayi haɗe da cewa "To ai taci albarkacinki Kamal tunda na saka baki ko kuwa? Kayi hakuri ka kaimasa please."
"Please yaya Kamal ka taimaki ƴar ƙanwarka kasan duk duniya banda kamarka, kayi hakuri dan Allah kakai masa wallahi daga yau na daina yimaka rashin kunya ma".
"Eh ai kya faɗi haka yanzu tunda kina so naje aikenki". Kamal yafaɗa yana dalla mata harara, kyal kyala dariya tayi tace, "Allah da gaske nake, ni kasan ba dan Mommy ta hanani zuwa ba Allah da dakaina zan je na kai masa, so Please kayi sorry kaje kaga ko lafiya ma bashida." Mommy dake kallonsu tace, "Ohh ni ƴasu Meenal ke bakya jin kunya ne wai? Macce fa da kunya aka santa saboda Allah."
"Kema dai kya faɗa Mommy, Dubi yadda take faman rawar jiki akansa saboda ta zaice, Allah ba mamaki idan akace ko rabin son da take yimasa yana mata shi." Mommy ce ta harare shi haɗe da cewa, "Ba bakinka ba gaskiya Kamal, yanzu dai barshi kawai tunda bazaka tafi ba sai naba driver yakai masa ai gidan na Mutallab ba ɓoyayye bane" Tunowa da Kyakkyawar yarinyar da yai ɗazu da yake da tabbacin ƙanwarsa ce ya sashi saurin cewa, "A'a Mommy zan kai masa mana, ai tunda kikayi magana dole naje tasa a sakasu mota bari nafito". Yafaɗa yanayin gaba zuwa ɗakinsa, Meenal kuwa data kasa sake cewa komai jin haushin kalmar daya gaya mata tuni tabar gurin tana jin haushinsa, bai jima ba yafito lokacin Mommy tasa mai aiki takai masa kayan a mota, Ko da yafita bai daɗe ba ya'isa gidan da taimakon address ɗin da Meenal ta tura masa ta wayarsa, Ganin mansion guda yasashi kara duba numbar gidan hakan yasa yatabbatar ba karya takeyi ba, dan sauka yayi daga motar ya isa bakin gate ɗin, har zai ƙwanƙwasa ƙofar sai yaga wasu buzaye guda uku aɗan gefen gidan kaɗan da alamu sune masu gadin ganin ƙaramin cikinsu ya taso ya nufo wajensa yana tambayarsa ko lafiya? Kallon gidan Kamal yai haɗe da cewa, "Ina neman mai gidan ne." "Ka kirashi a waya mana."
"A'a da dai zaka taimaka ka sanar dashi yayi baƙo zaifi".
"To shikenan ka tsaya anan ina zuwa". yafaɗa yana shiga cikin gidan haɗe dayin sallama bakin ƙofa, Afrah ce dake kwance a palour dan tuni shi Mutallab yakoma sama zai tura wasu kuɗi da za'a kawo masu kaya daga Dubai tamike ta fito tana amsa sallamar haɗe da cewa, "Lafiya baba ayouba?" "Lafiya kalau yar masu gida Alhaji ne yayi baƙo ko za'a sanar dashi."
"Tohm ace masa gashi nan zuwa". tafada tana komawa ciki, kitchen tafara shiga wajen a sanar da tánte nan tace, "Anya ba wani abun yakeyi ba tunda kika ga yakoma saman nan Afrah? Inaga kije ki sanar da baƙon yaje yadawo gobe idan kuma saƙone sai ki karɓa masa, saboda idan yasan da zuwan baƙon bazai koma sama ba, kuma shima baƙin daya sanar dashi zancen zuwansa ai zai kirasa awaya."
"Haka ne kuma tánte, gashi ma da alama agajiye yake bari naje na gani". Afrah tafaɗa sannan tafice tafara wucewa daƙinta ta ɗauki dankwalin abayar dake jikinta ta haɗa sannan tafito ta nufi compound ɗin gidan, duba da gidane mai girma sai da ta ɗanyi tafiya sannan ta ƙarasa babban gate din tana tura kofar fita, jin ƙarar fitowa shi kuma ya sakashi juyowa yana jefa wayarsa aljihu haɗe da zuba mata idanuwa ganin tana dube-duben inda zata hango baƙon idanuwanta ne suka sauka akan Kamal da yaji lumfashinsa yai skipping na tsawon mintuna, haɗe rai tayi tunawa da tayi kamar akansa fa tasamu matsala da masoyinta tana ƙoƙarin juyawa yai saurin dakatar da ita ta hanyar cewa, "Assalamu alaikum". Sanin daraja da girman sallama yasata tsayawa tare da juyowa ta amsa mashi, jin yai shiru sai idanuwa ɗaya zuba mata ya sata ɗago kanta tana cewa, "Ya Mutallab na wani abu yanzu, zaka iya tafiya ka dawo gobe ko kuma idan saƙone kabayar abashi" taƙare zancen cike da gundura da kallon da yakeyi mata, murmushi ya saki yana gyara tsayuwarsa haɗe da cewa, "Ba damuwa dama saƙone aka bani na kawo masa, amma kafin nan dan girman Allah zan iya sanin sunanki?". cikin ƙosawa da maganarsa da tayi ta kauda kai gefe tana cewa, "ka bayar da saƙon wa masu gadi su shigo dashi". Sannan ta juya tana ƙoƙarin barin wajen, ganin hakan yasa shi saurin faɗin, "DanAllah yi haƙuri ga saƙon nashi daga Meenal" yafaɗa yana buɗe bayan motarsa, baba ayaouba yaji ta kira tace ashigo dasu ita kuma tayi shigewarta ciki....
#Mutallab Asad
#Tagwaye Biyar
#Billy s fari
#Nana Diso
SHAFI NA SITTIN.
*MUTALLAB ASAD*
Arewabook:- billysfari
Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.
Kwala mata ƙira yashiga yi yana faɗin " Ke tsaya mana Nima zan siyo abu idan Allah yasa muka dan samu wata sadakar a hanya Ai Alhamdulillah lafiya lafiya." Turo baki tayi tace " Haba Baba kayi zamanka mana Nifa inaji gudu zanyi Naje nadawo." Fitowa yayi yana fadin idan bazaki rakani ba to ai shikenan." " A'a zanrakaka tafaɗa tana juya masa baya, suka fice daga gidan. Ko da sukaje sun dan dauki lokaci kamin su koma dan sai da baba yasata tasiyo musu shinkafa kwano biyu da masara kwano biyu. Kai kam babansu kafiya biyewa yarinya wallahi yanzu saboda Allah rakata kayi." " To wai mama me nayi yanzu kuma bafa Nice nace masa ya rakani ba shine yaga zai rakani ganin damarsa." " Rufemun baki malama, ke bakyacewa ya hutu?." " Allah yabaki hakuri kema ƙarbi kunun nasiyo miki." Murmushi tayi ta ƙarba tana faɗin saura kije ki kwarawa ƙanki ruwan sanyi da daddaren nan tunda basanin ciwon kanki kikayi ba, sanyi yazo yashigeki a damu mutane da maganin infection." " Saboda Allah Nidaya aka tsana agidan nan kullum laifi kullum." " fais attention avec moi Aicha ( ki kiyayeni fa Aicha) ." Zato idanuwanta tayi tace " To Allah yabaki hakuri mamata Nama fasa wankan Bari Naje Na kwanta." Wannan shine karo na biyu da père (mahaifi) yakirata, jiyowa tayi tace " Nifa kwnaciya zanyi danAllah Mon père ( mahaifina)." Zo nan ki zauna muyi hira kinji." Jin haka yasata tawowa ta zauna tana jinsa yanata bata labarin rayuwarsa tabaya da yadda yayi bara har ta shanye kununta bacci yafara kwasarta, to yanzu dai tayi bacci bari in tasheta taje ta kwanta." " Dakin barta ta kwana cikinmu." " A'a wallahi duk sai ta zanemu da wannan manyan kafafuwan nata." Dariya yayi har ta tasheta taje ta kwanta a tsummar tabarmarta."
******
Washe gari yakama talata Tunda yayi sallar Asubahi yagabatar da Azkar ɗinsa da kuma zikirin da yakeyi yasamu yakoma bacci. Har yanzu ransa yaki yimasa daɗi akan Aryan to Amma hakan bakomai baniba duba da kowannen su ƴan Adam ne. Wayarsa da tayi ringing yadauƙa yana karawa akunnensa jin muryar mahaifinsa yasashi dan kara zabura yana saita ƙansa." Barka da safiya Baba dafatan kana lapya ya mutun gidan." " Duk ba wannan ta tambayeka ba kayi maza maza kazo ina nemanka ummanku tace lallai lallai asaka biƙin nan da sati biyu dan haka kazo ina nemanka." Mamaki ne yakamashi Amma sanin irin halin da mahaifinsa yake ciki yanzu baisa shi jin komai ba sai ma addu'a da yayi yana kara gyara zamansa sosai haɗe da kashe wayar tasa. Mikewa yayi yashiga wanka.
Afrah haka zaki fita babu ɗan kwalli kokuma ɗankunne? Duk ƙinyi zuru zuru dake? A'a jiki canzo kayan nan sun nuna ramarki sosai. " Tantè tafaɗa idanuwanta na kawo ruwa. " Afrah Addu'ar Nan dai ta neman zabin Allah zaki cigaba dayi idan da Alkhairi sai kiga kuncigaba da soyayyarku da Aryan idan babu alkhairi sai kiga Allah ya hada kowa da mafi Alkhairansa." A hankali ta share hawayenta haɗe da fadin " tante inason Aryan sosaifa Amma wallahi wallahi bazan taba iya auransa ba nakasa cireshi araina jiya kina gani banyi bacci ba." " afrah kenan har yanzu ke yarinyace kiyi hakuri kiji ki fawwalawa Allah komai zaizo miki da Sauki." Dago manyan idanuwanta tayi ta zubawa tante su. Tana ganin yayan nata yafara sakkowa daga bene sai kuma ta tsaya tana kokarin gaisheshi. Cikin wata green din shadda yasakko yayi mutukar kyau kamshinsa ya gauraye ko'ina agurin, kallonta yashiga yi tare da karasowa kusa da'ita yana riko hannunta haɗe da faɗin " Bakida lafiya ne? Naga kin rame." Yaya babu komai kawai banajin dadine." " Afrah kallarni wannan rayuwar fa haƙuri akeyi da kowa da komai, dole Allah zai jarrabaka ta wasu fannonin na rayuwarka bakomai ake dauka fushi ba..bai karasa ba tafashe da kuka tana rungumeshi tana fadin " Zan dauki duka amma bazan taɓa daukar azagarmin ku ko acimuku mutunci ba yayana Wallahi idan natuna da Abunda Aryan yayi maka zuciyata zafi takemin, Yaya koda zan mutu da kaunar mutallab ko sonsa zai kasheni bazan taɓa iya auransa ba wallahi yaya bazan iyaba danAllah danAnnabi (saw) kada ku tilasamin takarasa tana kuka sosai..kune gatana kune komai nawa tunda Na tashi kukazama iyayena kun bani lokacin da baku dashi sannan kun karamin lokacin da kuke dashi sannan ina kallo azo acimuku mutunci, yaya kajifa zargina yakeyi." Sosai kalmomin Nata suka sakawa zuciyarsa rauni dqn gyaran murya yayi yace " Is okay Afrah is okay stop crying shige ki gyara fuskarki kitafi, ga driver nan yana jiranki Ni zan fita, Hannunsa yasaka a aljihu ya irga kudi yace " Gashi kya kara akan najiya." Godiya tayi masa sosai har yafita ta kitchen suna gaisawa da tante sannan ya sanar mata akan gobe zasuje suga can gidan dan an kammala komai yanzu. " Nikam inataso Inyi maka magana akan Fannah budurwar jalil kaga sunata maganar aturo aturo Amma har yanzu shiru." Shiru yadanyi nadan lokaci kamin yace Inshaa Allahu zanyiwa Abba magana yanzu idan naje." " To yakamata dai a tura tunda sunjima suna magana. Ciƙin haiba da kamala irin tasa ya hau bakar motarsa sai da ya dannah horn kamin mai gadin ya buɗe masa kasuwa yafara Nufa, yadan jima acan kamin kuma ya tsaya suka gaisa da Aryan, " DanAllah MAM kayi hakuri Nasan nayi kuskure basan me ya hau kaina ba kayi hakuri." Murmushi Mutallab yayi yace " Bakomai Aryan yahuce ai daman zaman tare yagaji haka Ni zan huce gida." " Ko Na rakaka ne?" " A'a kayi zamanka ina godiya yafaɗa yana fita daga shagon." Shima aryan din fita yayi ya hau adaidaita sahu zuwa makarantar su Afrah. Tundaha baƙin gate yake faman dannah musu horn kasancewa baba mai gadi bayanan babu mai buɗewa sai daga can ne yaga walid ya fito da sauri ya bude kofar gate din." Mamakine yakusan kashe mutallab duba da yadda yaga walid din yadawo ga alumun girma sosai harda kasumba sun bayyana Amma kuma ya rame yazama baƙi kasantuwar da yanada haske sosai. Katse masa tunaninsa yayi ta hanyar faɗin " Barka da rana Ya mutallab. " kashe motar Mutallab yayi haɗe da bude kofa yana fitowa sannan ya bashi Hannu suka gaisa " Walid bakada lafiya ne?" " Ya Mutallab Aure Nakeso." Cikin dan zabura yaƙalle Walid din da yanzu ne ma fa zai shiga jami'a amma yake maganar Nan, " Walid aure kamar yaya bayan karatun ma yanzu ne kasaka masa hannu fa." Cikin yanayi Na tsantsar damuwa yace " Wallahilazim yaya bansan tayaya nima nazama haka ba but bana iya controlling ƙaina aduk lokacin danaga mace and yaya Dana bata rayuwata da bin mata gwara anyimun aurena." " Kanada yarinyar dakakeso ne?" " Eh sunanta imam." " To daga gobe kafara zuwa shagon jalil kaima idan naga ka maida hankali sai nabaka shagon sannan kuma wannan gashin karbi kaje kayi aske makaranta kuma zaka fara zuwa wacce afrah take zuwa." Kuka yafashe masa dashi haɗe da rungumeshi." Bakomai kaji zanwa Abba maganar auren naka sai ahaɗa dana jalil." " Nagode yaya Ubamgiji yayimaka tukwici da jannatul firdausi Nagode yaya." Ko da yakarasa bangaren Abba Umma na zaune gefensa tana tayi masa lissafi.Sallama yayi yana cire takalminsa kamin yasamu guri ya zauna " Barka da rana Abba, sannu Umma dagida yafaɗa babu alamun ko murmushi afuskarsa." " ko baka gaisheni ba babu komai ai tunda tarbiyar taku tayi karanci damar maganar aurenka ne Ansaka sati biyu." " Bakida hurumin sakamin ranar aurena ki tsaya Amatsayinki yanzu ina magana ne da mahaifina." Ganin yadda ya canza lokaci guda sai taji jikinta yayi sanyi ga kwarjinin da yayi mata hakan yasa ta taɓe baki tace " Ai kai sai kayimasa bayani." " To bari Nayi masa bayani, Mutallab maganar meenal Umma tace asaka sati biyu." " Abba karka damu danAllah Bani kadi ba harda jalil da walid, munyi magana da kawu kamin in karaso nan anjima zasuje a kai kudi da saka rana in yaso ko Nan da wata uku ne sai asaka bari dai muji gidan iyayen yaran idan sun shirya." Da mamaki da kuma baƙin ciki Umma tace " Wanne irin walid yaro karami." " Eh shima auren yakeso dan haka zamu kokarta ganin mun karewa mahaifinmu mutuncinsa. " shiru Abba yayi yanason yayi magana yana tsoron Umma hakan yasata fusata tafita tana faɗin bari naje naji idan uwarsa ce ta ƙimtsa masa wannan iskancin." Tana fita Abba yaja ajiyar zuciya yace " To shima jalil yasamu wacce yakeso ne? " " eh yasamu Abba." " kuma naji kace Walid? Mutallab ina walid ina aure baiyi karatu ba gashi ba kasuwanci ko guda daya tayaya zai rike diyar wasu?." " Abba walid da kanshi yasameni yanzu... nan yakwashe komai yagamasa." " To gidan da zai zauna fa kaga nan babu guri kuma sai yayi shiru hawaye yana zubo masa.." " Inshaa Allahu zan bashi gidan zama akwai wani fili dana yanka kwanaki da ina saran ayi masallaci dashi Amma sai Na gina masa kusa yake da gidan Jalil kuma aiki da karatunsa Abba duk zaiyi, ka daina kukan nan." Riko hannunsa Abba yayi yana fashewa da kuka da yasa idon mutallab sauyawa shima."" Abba kukan me kakayi haka." " Allah yarabaka da duniyar Nan lafiya mutallab ubangiji yarabaka da duniya lafiya " jin umma ta shigo hannunta janye dana Anty tace " kut menene haka?" Abbane yayi saurin zare hannunsa yana danAllah kiyi hakuri." To ga uwar walid din tace babu sa hannunta ayiwa danta aure." Mamaki ne yakama mutallab sosai bakinciki yakuma taso masa cike da bacin rai yace " Kuzama cikin shir8 dan kowannen su gobe za'a kai kudin auransa." Jikin Anty dake rawa Umma ta dakawa tsawa tace " Bazakiyi magana ba kice bada yawunki ba?" A dan firgice ta juyo tana fadin.." " Dakata malama Mutallab yafaɗa kidinga azkar safe da yamma kina zama da alwala sannan yayi ficewarsa." " wallahi baku isa ba kaikuma harda rike masa hannu to kujiraye ne tafaɗa tana ficewa tana musu ihu da masifa." Anty Naganin tafice tace " DanAllah Abba kasa yayi masa auran wallahi walid zai lallace idan ba'ayi masa ba." A hankali Abba yace " Zoki dan zauna mana." Kallonsa tayi tace " Idan tazo taganmu fa?" Cike da tsoro yataso yana rungumeta jikinsa har rawa yakeyi hakan yasata fashe masa da wani raunannan kuka da yasata kara rungumesa" Yaya zamuyi Abba? Haka zamucigaba da rayuwa? Cikin..." ke munafuka mikika tsaya yi? Banace miki karki kara mintuna uku anan ba." Jin muryar umma yasaka Abba saƙinta a mutuƙar rikice itama ta rikice tafita daga dakin har jiƙinta Na rawa. Abba kuwa da duk yafirgice yace " Kiyi Hakuri danAllah daman ƙince in gyara daƙincan ko? Bari naje na gyara yafada yana shigewa. Wani guntum murmushi tasaki tace " Asiya zan fita kisamun idanuwanki akansu dan bazan zauna yaron can yana juyani ba duk abunda yace uban baya iyayi masa musu dole Na dauki mataki wallahi." " Baki da damuwa Umma sai ƙin dawo." " Yauwa..
Tunda yafita waje yasa aka sauke duk kayan abincin da yazo musu dashi, Nan yadan tsaya suka gaisa da baba mai gadi dake sanar dashi jidda ce ta aikeshi shiyasa bai taddashi ba. Daga gidan Nasu ya Nufi gidan kawu don su tattauna akan lamarin auren ko da yakarasa yana palon sa a zaune, gaisawa suka farayi kamin yace masa goben inshaa Allahu zasuje dukka gidan matayen nasu. " To Amma kasanar dasu ita matar da zaka aura?" " Ban karasa gurinsu ba kawu yanzu daga nan can zan nufa." " To hakan ba damuwa ita imam din tunda kaga diyatace ai babu wanda za'a sanar sai mahaifiyarta ita kuma fannah yau ma sai da muka gaisa da mahaifinta." " MashaaAllah kawu ga wannan kudin Na jalil Wannan kuma Na Walid Wannan kuma nawa ne." To Allah yasaka albarka yakare fitina Allah yabiyaka kaikuma acigaba da hakuri da Addu'a inshaa Allahu rayuwa zatayi kyau." Sai da yafito daga gidan Nasa ya dauki hanyar gidan su meenal hakan yasa dayazo gate aka buɗe masa daga bisani kuma yakira meenal din, sanin cewa zaizo yasata jan mayafin afterdress dinta ta sakko tana fadin " Ganinan yaya."
SHAFI NA HAMSIN DA TARA.
*MUTALLAB ASAD*
Arewabook:- billysfari
Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.
Yau Takama ranar weekend kamar yadda kowa yasani ranar hutu ce ga mafiya yawan mutane musamman ma'aikatan gwamnati da kuma bankuna, hakan yasa tun rana Aryan na tare
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 34 Chapter of 54