kallon yadda Mutallab ke sauke ajiyar zuciya yana ƙoƙarin ƙarfafa kansa kafin cikin muryarsa data dashe yafara cewa, "Aryan Abba ya koreni agidansa, Afrah bata lafiya yanzu haka, ya zanyi? Meye makomar ƴan uwana? ina zanje nabarsu? Niger wajen dangin mahaifiyata? To wanasani acan? Ya rayuwar Afrah zata kasance a hannun mutanen da basu damu da rayuwarta ba, a hannun yayanta mai matuƙar zuciyar da zata iya saka a cutar dasu, a'ina zanje na barta Aryan?" Ya sake fashewa da kuka da kuka tamkar ransa zai fita, ba abinda yake hangowa sai yanayin da Afrah ke ciki da shine ke sake karyar mata da zuciya, ganin yanda Mutallab ke maganganu tamkar ba'a hayyacinsa ba yasa Aryan dafa kafaɗarsa haɗe da cewa, "Enough Mutallab and Stop crying, am here for you MAM ko kowa ya gujeka ni bazan gujeka ba, saboda haka kayi haƙuri muje muyi tunanin abinda yakamata". Daga haka ya tada motarsa yaja suka bar wajen a hankali Mutallab yashiga Ambatar sunan Allah yana karanto addu'a.
اَللّٰهُمَّ لَا سَهْلَ إِلَّا مَا جَعَلْتَهُ سَهْلاً، وَأَنْتَ تَجْعَلُ الْحَزْنَ إِذَا شِئْتَ سَهْلاً .
Sai da suka hau titi kafin Aryaan yafara magana, "Dan Allah ka saita kanka MAM, bana son wannan kukan naka yajawo maki wani abun, kayi haƙuri Allah yana gani kuma yana sane dako menene ke faru dakai, duk abinda kake gani a duniya yana da farko kuma yanada karshe". Juyowa Mutallab yayi yana jin wata natsuwa na saukar masa haɗe da cewa, "Aryan dole nayi kuka, sata fa Abba kecewa nayi masa ta miliyan kuɗi ba ɗaya ba ba biyu ba har kusan miliyan uku, ina zan saka kaina da wannan tashin hankalin Aryan". Zaro idanuwa Aryan yayi shima cikin tashin hankali yace, "miliyan uku MAM? To kayi me dasu ba tare da anganeka ba? Mtsss wannan shirin ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba na matan mahaifinka ne, Amma koma meye kayi haƙuri ka barwa Allah da sannu gaskiya zatayi halinta, waya sani ma ko wannan ɗan iskan Jamil ɗin dake ɓatawa yaran mutane rayuwa ne ya ɗauka aka ƙala maka". Baice komai ba ya shiga sauke ajiyar zuciya har suka ƙaraso gidan su Aryan maigadi ya buɗe musu gate suka shiga suna, da Ummie sukaci karo tarako ƙawarta tana ƙoƙarin juyawa ta koma ciki, tsaye tayi har sai da Aryan yayi parking suka fito shi da Mutallab, murmushi ta saki ganinsu tare don ita har ga Allah tana don Mutallab haɗe da tausayin halin da suke ciki, annurin fuskarta ne ya ɗauke da sauri taƙaraso wajen ganin yana yin da Mutallab ke ciki da kuma jikkata hannunsa da Aryaan ya fiddo a bayan mota tana cewa, "don lafiya? Meke faruwa da Mutallab naganshi a haka?" tafaɗa tana karasawa haɗe da kamo hannunsa".
"Ummie mudai shiga ciki tukuna yafara yin buɗa baki don na tabbata azumine abakinsa".
"Ok muje ciki Mutallab". Tafaɗa tare da wucewa gaba, duk da Mutallab yaso yafara yin Sallah don kada su rasa jam'i amma Aryaan yaƙi yace lallai yafara zaunawa yayi buɗe baki sannan yaje wajen sallah shi kuma yanufi masallaci,
Aminci mai rai da lafiya Ummie ta jere masa agabansa tasa mai aikinta take ta gyara masa fruit ta yanko masa, sai data bashi magana akan yayi haƙuri yacire komai a ransa yaci abinci ya kuma yi addu'a Allah sassauta masa komeye damuwarsa sannan itama tawuce ɗaki don tayi sallah.
Baison yayi masu gardama sam don yunwar dake cikinsa tuni ta kama gabanta shiyasa ya zauna ya tsattsakuri abincin dan sam bayayi masa daɗi sannan yamiƙe ya nufi ɗakin Aryaan yayo arwala yafito ya nufi masallacin dake jikin wani gida a layinsu Aryan ɗin, yana zuwa angama sallolin Aryan na tsaye tare da wani maƙwabcinsu suna gaisawa don haka ya shiga yayi Sallah, sosai yayi addu'o'i tare da roƙon Ubangiji yayi masa mafita acikin lamurransa sannan yafito har lokacin Aryan da yaga wucewarsa na tsaye yana jiran fitowarsa suka wuce gida.
#Mutallab Asad
#Ƴan Tagwaye
#Billy S Fari
#Nana Diso.
*18*
*MUTALLAB ASAD*
Arewabook:- billysfari
Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.
# ƳANTAGWAYE BIYAR
#MUTALLAB ASAD
NA NANA DISO &
BILLY S FARI
________*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?*
*INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?”
*KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.*
Mun gwada mun gani 💯
Mun gani mun shaida 💯
Anyi mun gani 💯
MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
GYARAN MAIJEGO
MALLAKAR MIJI KO MATA
SUBULU DA SCRUB
MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
MAGANIN TSUMI
INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯
08142800199
07068558096
Maigadine ya taɓo driver yana ɗan turo idanuwa ganin abinda Meenal ke ƙoƙarin yi yace "kai malam yahaya wallahi bantaɓa sanin yarinyar nan batada tarbiya ba sai yau, ciki fa take ƙoƙarin shiga da ɗan iskancan ko baka kaga irin kayan dake jikinta ba, shikuma yaron kallesa kamar sabon tuba amma a haka zata kaisa cikin gidansu". Dariya sosai malam yahaya ya shigayi kafin yace, "To saboda Allah kaima ina tarbiya anan bayan yadda ubanta ya sangartata, yanzu don Allah wane namijin zai iya zama da ita haka? Koda yake ba tada laifi idan ma tashiga dashi ciki, dama tasamu!". Sai daya sauke ajiyar zuciya sannan yace,
"Allah dai ya kyauta Malam Yahaya amma kam akwai matsala ga lamarin yarinyar nan, kuma tunda take ƴar masu kuɗi za'a iya samun mai iya aurenta tsaf amma fa ɗan uwanta sagartacce irinta ƙila, kaga sai suyita sangartarsu yadda sukeso, sai dai fa maganar gaskiya wallahi yarinyar nan batada tarbiya ko kaɗan?" Malam Yahaya yace, "Uhmm kuma fa nan da sauƙi saboda Hajiya na tsawatar mata tunda iya mai ma'aiki tace min Hajiyar gidan tana iya kokarinta gurin ganin ta ɗorata akan dai-dai mahaifin nata dai ne kawai ke sakata tana abubuwan fanɗarewa haka, kuma wallahi wannan yarinya sai ta zama lamba ɗaya a lalacewa idan ba'ayi hattara ba, yanzu fa ana kwaɓarta kenan amma kaga kamar batayi to inata da ace kuma gabaɗaya ma ba'ayi? Sannan a haka wani zai zo ya zage Hajiyar akan yarinyar don rashin adalci".
"To ai ni zangaya maka haka Malam Yahaya, rannan fa kusan ƙarfe ɗayan dare Alhaji yakoreta akan yarinyar tayo dare tayi mata faɗa, har zata fita gate sai kuma naga yazo ya lallasheta suka koma ciki".
"Tanama ƙokari wallahi don yarinyar nan rashin tarbiyarta da rashin kunyar da take nuna mata yayi yawa, badon tanada haƙuri ba da tuni ta tafiyarta tabar masu gidan".
"Aikam dai, amma kam duk wanda ya aureta ya aurawa kansa wallahi dan babu abun dubawa arayuwarta takowane ɓangaren".
"Hakane Allah ya kyauta".
"Amin ya rabbi". Yafaɗa tare da miƙewa ya zagaya, (Ƴan uwa mukula a rayuwa, duk abinda zakayi kayishi tsakaninka da Allah ba don neman yardar wani ba hakan zaisa mutane su yabeka ba tare da saninka ba saboda ka tsarkake zuciyarka kanayin komai saboda shi).
ko da suka shiga har lokacin Mommy na ɗaki tana gyara wardrobe ɗinta, kai tsaye wajen dining suka nufa tana ƙwalawa mai aikin kira, bayan tazo tasa ta zuba masu abincin ta kuma ce ta gyaro masu fruit ta kawo masu, ita dai iya mai aiki sai faman jinjina kai kawai takeyi tana mamakin rashin ji da tsagerancin Meenal, tayaya zata shigo da wani ɗan iskan yaro da gajeran wando haka? to ita ko idonta ne taga kamar ma harda sarka wuyansa? Ko bata gani daidai bane, iya tafaɗa tana jan numfashi ganin tunanin nata bai da wani amfani taci gaba da gyaran fruit ɗin ta kammala ta kawo masu, bata sake shan mamaki ba sai bayan sun kammala cin abincin da AAB yacewa Meenal zai wuce bacci yake ji saboda jiya bai runtsa ba, kawai taji tace masa yazo su je ɗakinta ya kwanta ya huta kafin ta a kare ba kunya AAB tafa sun nufi benen yana biye da ita baya suka haye sama zuwa ɗakinta, gaban iya mai aiki ne ya faɗi ta dafe ƙirji tana zaro idanuwa, karfa atafka wata abin kunyar suna cikin gidan Mommy bata sani ba, tafaɗa tana faman kai da kawo tare da regen saman benen tana sake dafe ƙirji, so takeyi tayi wani abu don gudun afkuwar Abinda ke iya faruwa tsakanin namiji da macce amma har ga Allah tana tsoron zuwa ta faɗowa Mommy magana tazo tafita daga baya ace daga bakinta akaji Alhaji ya koreta gidan tunda tana ganin ko matar gidan ba tsira tayi ba akan wannan Shalelen tasa. Don haka da sauri ta gargaɗi kanta tana kama baki tabar falon taje taci gaba da aikace-aikacenta.
Mommy kuwa bata gama gyara wardrobe ɗinta ba sai kusan ƙarfe biyar sannan tafito ta nufi sashen Dady da niyar gyara masa tashi shima, kamar daga sama ta jiyo hayaniya da dararraki a can sama gefen ɗakin Meenal, har zata wuce don ta ɗauka ƙawayenta ne sai kuma tadawo baya jiyo murya kamar ta namiji, gabanta ne yayi wata irin muguwar faɗuwa lokacin data tabbatar da muryar namiji ɗin ce a ɗakin Meenal har bata san lokacin data soma haurawa saman ba tana haɗa steps da sauri da sauri sai dai ta ganta abakin ƙofar ɗakin jikinta na rawa ta tura ƙofar.
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun". Shine abinda yafito daga bakinta ganin ƙato a saman gadon Meenal ɗin daga shi sai gajeren wando da riga armless suna ƴar jefaffa da filoluwa suna dariya, dama ko daya shiga ya kwanta fira suka ɗora shi da Meenal ɗin dake zaune saman bedside tana latsar wayarta, daga haka ne ganin yaƙi baccin sai kallonta yakeyi tace masa gulmamme dama yayi baccinsa jiya ba wani bacci da yake ji, shine fa rigimar ta kaisu har kan gado yana maka mata pillow itama tana maka mashi suna dariya. (Tirƙashi!🤯 Anya biri na mai Babyn Dady?🏃)...
*************
Washe gari tunda sassafe Mutallab ya nufi sashen Abbansu, da umma ya fara cin karo tafito ɗakin ya gaisheta ba tare data amsa mashi ba ta wuce abunta, kallonta yayi yana mamakin tsananin kiyayya irin tasu, dauke kansa ya karasa cikin daƙin abban ya fara gyara toilet sannan ya hau gyaran ɗakin saboda Abban nasu baya gari kuma yana so yafita wajen aiki da wuri shiyasa ma yazo gyaran ɗakin da sassafe, saɓanin idan Abban nasu na gida baya zuwa gyara masa ɗakin har sai ya gama kammala shiryawarsa yafita sannan shi kuma ya shiga yaje ya gyara ɗakin, bayan ya kammala ne yana ƙoƙarin fita Aunty Amarya ta shigo ya gaisheta cikin girmamawa sannan ya fice.
Ɗakinsa Mutallab ya koma yayi wanka ya nemi wani yadinsa da yaɗan canza saboda tare da nuna alamun tsufa yasaka dan ya lura sauran abokanan kasuwancin nasa babu wanda yake saka kaya masu kyau, sai da yagama gyarawa sannan ya nufi cikin gidan dan yaga ya Afrah ta tashi ko da yaje har tagama shirinta na makaranta, gaishesa tayi ya amsa murmushi ɗauke akan fuskarsa ya amsa kafin ya riƙo hannunta suka sauko yana yimata nasiha akan ta ƙara maida hankali a karatun,ta kuma kiyaye kula duk wasu ƙawayen banza maza ko mata, suna saukowa ta nufi kitchen ta ɗauki abincin da aka zuba mata wanda kana gani kasan saida akaci aka rage mata ba tare data damu ba, shi kuma yakoma daƙinsa ya canzo takalmin ƙafarsa ɗaya anya bai sauya ba zuwa silifas ɗin wanka dake toilet ɗin da sannan ya leƙa ɗakin Jalil yaga har lokacin bacci yakeyi bai tashi ba don jiya aikin printing ya taya abokinsa suka kai dare basu gama ba don haka sai kawai ya ja masa ƙofar, a filin gidan ma sai da yatsaya ya gaggaisa da masu aikin gidan da mai gadin su sannan yafita zuwa bakin titi, tafiya yayi mai nisa dan ragewa kansa kuɗin motar da zata kaishi, dan jiya da suka tawo da Idris ya sake bashi shawarwari akan yadda zai rika tattalin ƴan kuɗaɗensa kafin kowannen su yasamu abun hawa su suwuce, wannan ma wata hanyar adani ne da zaisa kasamu sauƙin kuɗin mota ka kuma tanada kuɗinka, kasancewar yau Alhamis da Azumi abakinsa shiyasa bai tsaya gurin mai shayi ba yashiga cikin kasuwa bakinsa ɗauke da addu'ar shiga kasuwa da tafito daga bakin fiyayyen halitta alokacin da zai shiga *'laa ilaha illallahu wahdahu laa Shari kalahu, lahul mulki walahul hamdu, yuhyi wayumitu wa huwa hayyul laa yumitu, biyadihil khair wa huwa alaa kulli shai'in ƙadeer'*, (wannan addua tanada mutuƙar amfani a yayain da mutum zai shiga kasuwa dan siyayya ko kasuwanci yan uwa kuyi ƙoƙarin haddaceta), ya ɗanyi tafiya sosai cikin layuka kamin yaƙarasa shagon Alhaji Tanimu ya iskesa ana faman jejjere kwalayen abintayyen a bakin shago da kuma kakkaɓe gefen da sukayi ƙura yana magana da wasu customers da suka zo, sallama yayi sannan ya shiga ciki suka gaisa da yaran Alhaji Tanimu ɗin ya samu gefe ya zauna don yau baiga Idris ba, sai da suka gama cinikin da mutanen sannan Alhaji Tanimu ya juyo da sauri Mutallab ya taso ya isa wajensa tare da russunawa ya gaishesa, cikin sakin fuska ya miƙa masa hannu yana cewa, "lafiya ƙalau Mutallab, an fito?"
"Eh Alhaji akwai wani aikin da za'ayi".
"Eh baza'a rasa ba yau Idris bai fito ba ban sani ba ko lafiya? Saboda haka ga wasu nan sunyi sayayya za'a kwashe masu kayan akai masu a waccan ƙatuwar motar sai kaje kayi dan dama Idris ya saba yimasu yanzu kuma baya nan kai sai ka wakilcesa".
Yaƙare maganar yana nuna masa motar kanta dazai loda kayan aciki. Cikin girmamawa Mutallab yace,
"To Alhaji Nagode, ina kayan suke?" Alhaji ya nuna masa tulin kayan da yaransa suka fitar waje sannan takoma wajen customers ɗin nasa daya sa aka kawowa ruwa da lemu suna sha, kaya ne masu yawan gaske tun daga kan buhunnan shinkafa, gishiri, sugar, jarkokin mai da katin ɗin su taliya da macroni, Ajiyar zuciya Mutallab ya sauke yana furzar da iska ta baki haɗe da game hannayensa waje ɗaya yana murzawa kafin yafara kwasar kayan, tun zuciyarsa nafaɗa masa bazai iya kwashesu ba yana ƙarfafa mata wajen tuno mata da halin da yake ciki shi da ƴan uwansa har yazo ya kwashe kayan tas yana haɗa wani irin zufa tare da sakin numfarfashi ɗaya bayan ɗaya don kusan awa ɗaya da rabi ya kwashe yana aikin, bayan sun bashi sallamarsa ya sannu gefe ya zauna yana ƙirga kuɗin dubu goma ne cif ya sauke ajiyar zuciya sannan ya tura cikin aljihun wandonsa, mai saida ruwan sanyi na leda dake ƙoƙarin wucewa ta gabansa ya gani ya kirasa haɗe da ciro Naira hamsin cikin aljihunsa ya miƙa masa ya ɗauki ƙwaya biyu ya bashi canjin talatin ya maida cikin aljihu, gabaɗaya tuttulesu yayi akansa saboda wani irin zafi da yake ji gashi yana azumi, wata iska mai sanyi yaji tana shigarsa ya saki ajiyar zuciya tare da haɗe labɓansa waje ɗaya yana kallon mutanen dake zirga-zirga a gabansa cikin kasuwar, dai-dai lokacin Idris ya iso suka gaisa da Alhaji nan yake sanar dashi da zazzaɓi ya tashi yau shiya hanashi fitowa dawuri, Allah yaƙara sauƙi yayi masa sannan yawuce wajen da Mutallab ke zaune yamiƙa masa hannu suka gaisa, shima dai ɗin bayani yayi masa dalilin rashin fitowar tasa yau dawuri yayi masa sannu sannan yace yatashi su tafi wajen wankin hulunan tunda ba wani aikin da zasuyi yanzu.
Haka yau ma ya ƙarar da wunin wajen aikin ƙarfi don bayan sun baro can wani wajen Idris ya sake jansa suka tafi, duk wanda yasan Mutallab indai yaga yanda ya koma yau sai ya tausaya mashi saboda tsanin aikatuwar da yayi da kuma gajiya, bai koma gida ba sai kusan ƙarfe biyar da rabi shima sai da yatsaya yasiya tuwo da miya na dari takwas da zai samu yayi buɗe baki dashi sannan ya nufi hanyar titi suna tafe suna fira da Idris, sai da sukayi nisa sosai da gaske kamin su tsaya suyi sallah la'asar abakin hanyar da masallaci yake, suna fitowa ya tsaya ya sayi dabino na Naira ɗari kamin suka samu abun hawa suka hau kowa ya nufi gida, ɗakinsa ya nufa kai tsaye ya wuce toilet ya watso ruwa, yana fitowa ya kwanta wani irin nauyayyen bacci yayi awon gaba dashi.
Yana cikin baccin yaji ana buga masa ƙofa da ƙarfi tamkar za'a ƙaryata, daƙyar ya iya motsa jikinsa da saida gabaɗaya gaɓoɓin ƙasusuwansa suka amsa ya miƙe ya nufi ƙofar daga shi sai best da kuma dogon wandon farin yadi dake jikinsa, Abba ne ya gani tsaye da tun misalin ƙarfe biyu na rana ya dawo, kasancewar a gajiye Abban ya dawo yana gama wanka ya kwanta bai tashi ba sai bayan sallar la'asar da yayi Sallah, bayan kuma ya dawo Jamil ya samesa da buƙatar kuɗi ta kusan miliyan 7 da rabi, tsintar kansa yayi da kasa yimasa musu ko kuma tambayarsa abinda zaiyi dasu sai dai yasa ya ɗauko masa check ya rubuta masa kuɗin ya bashi, bayan tafiyarsa ne har zai kwanta sai yayi tunanin duba kuɗaɗen daya ajiye acikin wadrobe miliyan biyu da rabi da niyar yakira Jamil ɗin ya kaimashi su banki, sai dai yana dubawa ba kuɗin ba alamarsu duka an kwashe jakar kaɗai aka barmasa, hankali a tashe yafito cikin ɗakin ya shiga ƙwalawa Umma da Aunty Amarya kira.
"Wa kuka bari ya shigar mani ɗaki bayan tafiyata?" Umma ce tayi saurin karɓe zancen da cewa, "Wa zai shiga ɗakinka kuwa bayan Mutallab, na ganshi da safe yau ya shiga".
"Tabbas nima naga fitowarsa Alhaji lafiya?" Aunty Amarya tafaɗa itama tana ƙarasowa kusa ga Abba da hankalinsa ke matuƙar tashe don hakan bata taɓa faruwa acikin gidansa ba sai wannan karon, cike da ɓacin rai yace, "ina shi Mutallab ɗin yake? Kuɗi na ajiye kusan miliyan uku ban ganesu ba, yana ina ne?"
A tare suka zaro idanuwa suna dafe ƙirji haɗe da cewa, "miliyan uku Alhaji?" Umma taci gaba da cewa, "Mun shiga uku kuwa to wlh a bincikesa Alhaji tunda haka bata taɓa faruwa ba acikin gidannan dan zai iyayin komai ganin ya rasa aiki kai kuma ka hana masa jari". Harararta Aunty Amarya tayi kafin tace, "Amma kuma ai ba yau Mutallab ya saba shiga ɗakin ya gyara masa ba, ya kamata Alhaji kayi tunani akan wannan lamarin gaskiya afara binciko wanda yafara shiga ɗakin".
Tsaf Umma tafahimci me take son cewa dan haka tace, "Sata kam ai bataga wanda yafara shiga ɗakin, sai dai a tsananta bincike ga duk wanda ya shiga cikin ɗakin yau, mudai matan sane ba tun yau yake zaune damu ba, da munayi masa sata da tuni ya gano hakan, amma nan yaron nan yazo ya tsaresa akan ya bashi rumfa ɗaya cikin rumfunansa ya tsare ko kuma gidan mansa, bakya tunanin tunda ba'a bashi ba zai iya cewa ya ɗauka yaje yaja jari"..
#Mutallab Asad
#Ƴan Tagwaye
#Billy S Fari
#Nana Diso.
*21*
*MUTALLAB ASAD*
*KN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?*
*INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?”
*KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.*
Mun gwada mun gani 💯
Mun gani mun shaida 💯
Anyi mun gani 💯
MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
GYARAN MAIJEGO
MALLAKAR MIJI KO MATA
SUBULU DA SCRUB
MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
MAGANIN TSUMI
INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯
08142800199
070685580968.
Abba kuwa ko daya kwanta lokacin yana jin zai iya haƙura da Mommy amma sai yaji hakan na nema ya gagaresa don gaba ɗaya ya kasa samun natsuwa akan haka, miƙewa yayi ya nufi shashin Mommyn yakara tabbatarwa da tatafi da gaske ya zauna abakin gadonta yana shaƙar ƙamshin daya zame mata jiki aduk inda take, awa biyu kacal kenan da tafiyarta amma ji yakeyi kamar sun shekara biyu kenan bata cikin gidan, fuskarsa ya shafa a hankali yana ambaton sunan Allah kafin yaja jikinsa ɗaya gama mutuwa ya koma daƙinsa, ɗakko wayarsa yayi ya shiga wajen dialing numbars da niyar kiranta amma sai yaji ya kasa dan tabbas ta ɓata masa rai, miƙewa yayi zuciyarsa na masa wani irin zafi ga yunwa dake ƙunshe a cikin cikinsa don haka yafita zuwa dinning, ga abinci jere akai sai dai sanin bazai samesa kamar yanda aka saba shirya masa shi ko yaushe ba tunda maiyin hakan bata nan yasa yaji abincin yafice masa arai, sashenta ya sake kallo kafin ya tuna da Meenal daya baro ɗazu tana kukan cikinta har bacci ya ɗauketa, da hanzari ya shiga hawan matattakalar benen yana mai nufar daƙinta, sai dai buɗewar da zaiyi yaga wayam daƙin babu kowa aciki, wayar hannunsa ya ɗauka yashiga kiranta bugu ɗaya ta ɗauka tana fadin "Hello Dadyna?" "Where are you baby?" Kaɗai ya iya faɗa yana kallon ɗakin nata, A ɗan shagwaɓe tace, "Dady natafi gurin Bestie nabashi haƙuri, Allah bakaga wulaƙancin da Mommy tayi masa ba". Duk da yaji wani abu aransa amma don kar ya ɓata mata rai sai kawai yace "Okay Baby take care don't come back late please". "Sure Dadyna". Yakashe wayar yana cigaba da ƙarewa ɗakin kallon ko'ina yayi kaca kaca don data sauya kaya anan wajen ƙasa tabar wuɗanda tacire har da wandonta da bra, kansa yafara juyawa tunowa da ƙasa tare mahaifiyarta don tabbas Meenal ƙazantarta ta biyo, girgiza kai kawai yayi haɗe da sauke ajiyar zuciya yafita daga ɗakin yana jin wata irin kewa atattare dashi, duk yanda yake jin zai iya jurewa rashinta sai yaji ya kasa, don haka ya sake gwada kiranta, ba tare daya ankare ba zuciyarsa ta ingiza hannun nasa ya dannawa lambar tata kira har kusan sau uku bata ɗaya ba kuma lokacin wayar na hannunta tana faman jujjuyawa itama takasa kiran nasa, duk da taji daɗi aranta naganin kiransa haka ta ƙyalesa yaci gaba da kiran batare data ɗaya ba irin abun nan namu na mata wato jan aji, cigaba da sake kira yayi har ya sauka ƙasa haɗe da kallon bangaren nata yana jin tsananin kewarta atattare dashi, dole ya hakura jin ana kiran sallar magrib kuma yaƙi ɗagawa ya nufi ɗakinsa yayi arwala ya wuce masallaci, bayan ya dawo wajen sallah yaji da gaske fa tunanin Mommy bazai barshi shaƙat ba har sai yaganta acikin gidan tadawo ya sashi ƙara fitowa ya faɗawa driver ya fiddo mota zaifita, cikin girmamawa ya amsa mashi da to tare da tambayeshi motar da za'a fita da ita ya faɗa masa sannan ya koma ciki yayi wanka yayi shigarsa irin ta manyan mutane tare da feshe jikinsa da turare yafito suka nufi gidansu Mommy, a lokacin ita kuma ta ajiye wayar taje tayo arwala itama Inna ta zubo mata abinci tanaci.
**********
Mutallab kuwa kasa ɓoyewa Ummie komai yayi saboda a yanzu duk duniya ita kaɗai yake kallo a matsayin uwa dake tausayinsa tare da nuna masa kyakkyawar hanyar da zata ɓullar masa, shiru Ummie tayi cike da takaicin matan mahaifin nasa da sam babu tsoron Allah a zuciyarsa, cikin tausayawa halin da yake ciki takallesa tana cewa, "Kayi haƙuri Mutallab jarabawace kuma in Sha Allah zaka bada labari, zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana ha maza ha mata tofa sai yayi, addu'ar nan daka saba kaci gaba dayi, sannan aduk lokacin da kayi ido biyu da bayin Allah nan to kariƙa karanta masu wuɗannan addu'o'in da zan baka na neman tsari ga abokan gaba da kuma wanda keda iko akanka don tabbas mutanennan basa ƙaunarka, shi kuma mahaifinka ba yanda zakayi dashi tunda ya isa gareka".
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 54