ko kanwa) me isa kika biye musu? Me isa kika aikata? Me isaka kika lallata rayuwarki soeur? Saboda me?." Da dan hanzari aicha ta dago tana kallonta da mamakin jin furucin yayartata, dafata yayartata tayi tace " me isa kika yarda ? Shikenan kin rasa mutuncinki kema?." " Yaya kece kike wannan lafazin ?" " Kinyi mamaki ko? Ai duk lallacewata ba abun kirki nake aikatawa ba da zanso yasamu ƙanwata babu abunda yake cikin bariki sai kazanta da danasani, wallahi banason abunda nake aikatawa banaso Aicha Nasan haramun ne Amma rabuwa da iyayena lafiya nakeso nayi." " Amma yaya kinsan ba'ayiwq iyaye biyayya a sabawa Allah ko?." " Lokacin da natashi tsananin mama yafi wanda kika tarar wallahi bansan kalar iyayen mu ba bansan irinsu ba Amma sukam sun kasance mutane marasa alkhairi agaremu tafada tana fashewa da kuka ina miki rantsuwa da Allah kaf cikin samarin nawa babu wanda zai iya aurata Wallahilazim kinsan Alhaji Bashir da na cemasa yafito sai cemin yayi yaya zai daukeni ya nunawa iyayensa? Bayan kowanne lokaci suna addu'ar yasamu macce tagari shi bazai iya aurena ba kamilar macce yakeson aure, indai zauna a matsayin yarinyarsa amma gaskiya baya iya aurena. Tundaga ranar nakara fahimtar na kassara rayuwata na lallatata, kuma dalilin biyewa umarnin su har suka dorani a keken ɓera saboda talaucin da muke ciki ki duba gidan mu da amma kinga da kudin da nake samo akeyin yar kwaskwarima da kuma abinci ina tausayin iyayena ina kuma tsananin tausayin ƙanmu da muka tashi A hannun da ba na gari na.sai na tuntunbi ayoub shikuma zai yacemin shifa bazai taba iya haɗa zuri'a da mahaifana ba kokuma na taba ganin ɗan bariki ya aure yar uwarsa yar bariki? Wannan kadai sun hanani zaman lpya tun jiya Aicha banji dadi ba ban..." kukan da takeyi ta dan tsayar ta kalli yayartata da tausayinta gaba daya ya nannadewa zuciya tace " babbar yaya ban aikata komai ba guduwa nayi wallahi kinga ta nuna mata inda ya karceta afuska wanda kikaji ya kawoni taimakona yayi,wallahi bazan taba aikata abunda sukeso nazama ba da yardar Allah bazan kasance mai son zuciya ba." Murmushi yayar tata tayi tace Alhamdulillah Aicha kinga har naji dadi wallahi DanAllah kada Rudin zuciya yasa ki amince musu." " Yaya bazan taba amince musu ba ai ba'a yiwa iyaye biyayya da saɓawa Allah dan haka karki damu danAllah kema kidaina abunda kikeyi ki tuba yaya." " Na tuba Natuba aicha bazan kara ba da yardar Allah." " Maganar me naji kunayi kasa kasa yau kuma ku biyun ke shiri? Kodai wani munafurcin kuke haɗawa?." Babar yayace tace " Bakomai mama kawai ina lallabata." Dariya mama tayi sosai tace kaji ƴar banzar yarinya ko sannan tasaka dariya tashigo tanata lallashin Aicha haɗe da yimata tambayoyi ke dallah rabani da wannan kallon naki kikarbi lemon nan can naje gidan salamatou da kaina na haɗomiki shi saboda ya gyara miki jiƙinki." " To wai me kika haɗa aciki Nifa karki ban abunda zandinga zawo kina ganin masan mu ya kusan ruftawa." " To uwar Na iya da shegen baki kamar Na tsirya Ganyen Na'a Na'a ne da kanin fari kadan da lemon tsami daya da citta na markadomiki na tace nazuba miki sukari ke idan kinashan wannan hadin duk wasu kananun sanyi dake jiƙinki sai sun barki ga karin lafiya." To mikomin nasha tafaɗa jin bata banka wannan magungunan nata ba." " To yaushe yace zai dawo Aicha?" Kallonta tayi tare da yin gefe da kofin sannan tace " Bansaniba dan bai sanar mini ba." " To yanzu dai kisamu ki huta dan gobe idan kikaji karfin jikinki kinga zakuje bara." Kallonta tayi tace to dan tayiwa kanta alkawarin daina jayayya dasu.
Tunda ya koma gidan bai tadda kowa aƙofar part din nasu ba sai wata yarinya zainabu daya daga cikin yaran kawun nasa ce Cikin girmamawa tace " sannu da zuwa Dan' uwa." Kallonta yayi da kananan kaya ajikinta ga attachment yazubo sosai ga farcenta da yasa jan farce, abun shi har mamaki yake bashi yaran malami ne fa malamin ma babba ga kudi ga ilimi Amma suke shigarnan kuma baidamu ba." " Ko in hada maka ruwan wanka?" A lokacin yajiyo a dan zabure yace " A'a kibarshi Nagode ƙinji ya makaranta? Ya mutan gidan?." Murmushi tayi tace " All fine." " To mashaa Allahu yafaɗa yana shigewarsa ciki, gobe ne flight dinsa zai tashi zaije yakarasa wani aiki acan kamin kuma yakara dawowa. A hankali yace " Aicha? " sai kuma yayi shiru yanajin yadda jikinsa yashiga zubawa, wacece ita? Yakara fada yana zare t-shirt din dake jiƙinsa. Kalmomin da tagaggaya masa ne suka shiga dawo masa acikin ransa. Mahmud ne yashigo yana masa sannu da zuwa. " Ai na ganoka nace lafiya naganka da t-shirt? Inataso kuwa in maka maganar zainabou ko tayi maka kaga sai ayi ta gida." Mamaki sosai ne yakamasa ya lura mutanen nan kudin sa kawai sukeso dan maganar da kawo yayi masa kenan da safe. " Rigar tawa ce tadan samu matsal Allah yaso nasaka t-shirt aciki, wacce Zainabou kake magana kuma?" " Kanwata mana Mutallab." Ikon Allah nace maka inasonta ne?" " To banda abunda shi auran zumunci sai mutum yace yanaso tunda kakasa tsayar da mata ai sai mu mutsayar maka ko?" Murmushi yayi yace " Ai ni ba mata daya ma zanyi ba biyu zanyi zannan zainab matsayin kanwata nake kallonta ba matsayin budurwa ba." " Amma dai kasan tana sonka ko?" " uhm mubar maganar mahmud zan danyi wanka zan fita kaga gobe zantafi." Rashin jin dadin maganarsa yayi acikin ransa cike da takaici yakallesa danAllah yasani yana bakin ciki da wannan ni'imar da yasamu.
SHAFI NA HAMSIN DA BIYU.
*MUTALLAB ASAD*
Arewabook:- billysfari
Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.
Sai da ya tabbatar tashiga motar sannan ya ziro kansa ta motar yace baba zamuje mudawo zanyi mata wata siyayya. " To Alhaji Allah ya kiyaye hanya koda kun daɗe Ni zanyi gida Allah yasaka maka da alkhairi ai kasan gidan namu ko can rarraba lungu gidan kasa kokuma kace gidan masu bara zasu nuna maka." Murmushi yayi yace " To baba Nagode. " Babane yadaga Murya yace " Ke Aicha ina kara gayamiki kibishi wallahi wallahi idan bahaka ba Allah ya'isa Tunda ke bakya neman Albarka arayuwarki bansaniba ko jiƙaki zamuyi mu shanye kinkai min zalin aure kin tsaya sha -shanci. Sautin kukanta dake tashi A hankali a motar ne yasaka Alhaji jiyowa yana zuba mata idanuwa ƙaramin bakinta da yayi jajir da kuma manyan idanuwanta ya kallah wasu tasirin mikar masa da sha'awa sukeyi kallonta yakumayi yana ganin yadda Nonuwanta suka ciko bam ajikin rigar ga tasaman ma har sun dan bayyana. Cikin sanyin murya da Nuna tsantsar zulama da kwadayi haɗe da rashin tarbiya yace " Wash Aicha ƙin hada komai da ɗa namiji zai bukata, rashin bani hadin kai ayau zai iya haifarmin da shiga tashin hankali mai tsanani, Bani hadin kai kamar yankawa ƙanki tikitin arzukine a cikin rayuwarki zai fiddaki inda bakya tunani tun daga million daya zuwa million 20 zan iya mallaka miki Aicha bukatata guda daya ce kizama mai ɗaibemin kewa ki zama mai tayani kula dakaina." Mamakin da Aicha ke cikine ya hanata motsi gaba daya zuba masa idanuwa tayi tana kallon cikin idanuwansa da suka camza daga kalar fari zuwa ja sannan ta kalli yadda jiƙinsa yake rawa akanta? Sha'awa? To daman ita haka take? Musulmine fa kuma wanda kasarta ke alfahari dashi sunansa yafita dayawa ansansa daga jahohi har kasashe kumafa yanada iyalaifa harma da yara amma bataga tausayin ko imani a tattare dashi ba sai tsantsan son kai da rashin tausayi, yara nawa ya lallata? Nawa ne suka bisa domin cikar burukansu? Tabbas wannan itace jarabawa mafi wahala acikin rayuwarta a yanzu ne ta tabbatar da yayarta ce ta samu damar nan babu abunda zai hanata yimasa tayi." Tafiyar da yakeyi da mota a hankali saboda yadda jikinsa yake rawa yace mata " Aicha ki amince mini danAllah ki taimaka min, inada wani guri danake ginawa angama kasan saman ne ba'a gama ba idan kuma kika ki bina ya bude wani guri acikin motarsa yafidda bindiga data daga mata hankali har jikinta yashiga rawa sosai bakinta ma yashiga mazari. Hakan yasashi jindadi sosai yana faka motarsa acikin manya manyan ginin dake kewaye da gurin ko ba'a gayamaka ba kasan na masu kudin garin ne duba da babu kowa agurin na mutane saboda yadda rana ta tsala sosai, cikin tsoratarwa yashiga bata umarnin da tashiga cikin rudani da girgiza tashiga binsa cikin gina ginan gurin takasa magana takasa cewa A'a meke shirin faruwa da'ita. " murmushi yayi Alhajin ganin abunda bokansa ya gayamasa shike faruwa dan kuwa ta kasa magana kwatakwata saima tsoronsa datashiga ji. Cikin sanyin murya yace " Shige nan." Dafari tadan kafe amma murzawar wani abu a hannunsa yasata shiga da sauri wanda idonta yakai kan hannun nasa, amma kwa kwalwarta takasa tariyar mata menene hakan? Addu'a ma takasa ruwar kofar da yayi da mukulli da hankadata kan wata arniyar hadaddiyar kujera dayayi yasata saƙin kara kadan duba da yanayin jikinta da yake da kiba, tan kallonsa yashiga raba kansa da kayan dake jiƙinsa daga shi sai gajeran wando, wannan karon shine karo na farko ta idanuwanta suka runtse hawaye yana zubo mata." " Duk yammatan danake tarayya dasu babu irin Aicha ke din ta dabance ke din kinada wani sirri na dabban nayi miki lallaba kinki amince mini dole na biyomiki ta wani bangare domin kawar da kwadayinki dake dawainiya dani. Yadda ya cafko nonuwanta yasata zabura tana kuka sosai hayan yabashi daman jan numfashinsa yana kara narkewa ajiƙinta wanda ita kuma takasa hanashi komai. Kokarin keta mata rigar dake jikinta yashigayi ganin layar hannunsa na kokarin takura masa yasashi ajiye wanda yayi daidai da zaburar Aicha haɗe da faɗin " Innalillahi wa'inna illahirrajiun nashiga uku DanAllah kabari tafada duk da rigar tata takai gurin yagewa. Amma halin dayake ciki bai barsa ya tsaya ba sai ma kwanto mata dayayi. " Allah ya'isa na Allah ya isana ubangiji yahanaka dukkan wani farinciki yasa yadda kake lallatamu mu yaran talakawa a lallata maka zuri'a tafada tana jin yadda yake kokarin jan siket Dinta, hakan yabata damar hankadashi Amma ko da wasa bai motsa ba kwata kwata." je te supplie d'arrêter ça si tu aimes ton dieu (Ina roƙanka da kadaina wannan abun idan Kana ƙaunar Allah)." Dariya yayi mai cike da wani salon gurnani yana kokarin saka baƙinsa akan nata, gaba daya jiƙinsa ya mutu ya manta da maganar da boka yace masa wannan layar ita kadaice zata hanashi musa masa. je ne peux pas te vivre aujourd'hui, nous devons le faire ( bazan iya barinki ba yau sai munyi fa yau dinnan). Jin bakinsa kan saman kirjinta yasata sakin kuka tana kara tana fadin " Dangirman Allah kabari kadaina danAllah babu kyau Allah yana fushi dakai haramun nr kanada zuri'a bazakaso ayi haka da iyalanka ba." Jin yaki yadaina abunda yakeyi haƙan yabata damar daukan flower vase ta buga masa a gefen hannunsa hakan ya bashi damar gangarawa gefen kujerar ita kuma ta miƙe jikinta na mugun rwa tashiga buɗe kofar jin muryarsa yana faɗin " Aicha mahaifinki yabani damar yin duk abunda yakamata inyi dake yakuma yimiki Allah ya'isa abisa bijiremin akan bukatata, so kikeyi bukatarki ta kasheni wayyo Allah fubi hannuna kin cakamin kwalba danAllah kizo to kamin yakarasa miƙewa ta fita da guda har jiƙinta na mugun rawa sosai mai gadin kamfanin da yaga hakan yasashi bude mata yana faɗin " Allah yasoki yarinya ƙinsha dakyar da haka kema zai lallata miki rayuwa kamar yadda yake lallatawa sauran yammatan dayake kawowa ince yau baiyi Amfani da tsafin nasa ba dan ance da ya dannah laya to babu ke fa babu kara iya korafi akansa dole ne kibashi haɗin ke, ko dayake harda ku shegun yara masu dan banzan buri da shegen kwadin tsiya to in ba kwadayi ba iyaye na fama kace kaima sai ka samu ka shigo gari." Ita dai Aicha batabi takansa ba sai kuka da takarayi jin Alhajin yana biye daita aguje sai tafita tashiga cikin gine ginin dake gurin jin sauti. Sunanta da yaketa ambata yasata shiga ambaton Allah tana kuka sosai ga gaban rigarta dake adage ga kuma gashinta da yazubo yayiwa kafadarta rufa jin sautin muryar mutane yasata Nufar gurin a guje ta baya taga wani mutum sanyi da farar shadda da Alama nuna musu guri yakeyi hakan yabata damar rungumarsa tana kuka kamar ranta zai fita, Alhaji kuma jin sautin mutane yasashi fashewa da kuka yana fadin " Shikenan tayimun Asara in karasa asirina ya Tonu." Hakan yasashi komawa.
Babbar yaya dake zaune tana shafa kayan kwalliya taga baban nasu yashigo yana dan bubbuga sanda. Mama dake gyaran wake agefe ce tace " A'a babansu yanaganka kai daya ina yar jagoran taka." Dariya yasaka fuskar nan tashi cike da fara'a yace " Ungo nan ku kirga kuga nawa ne nan." Babar yayace tace " Ai ko ban kirga maka ba baba wannan dubu dari ce cus." Mama ce tatashi ta ɗan taka tace ai ko baka faɗaba Nasan yau diyata tana ciƙin dauka da Ni'ima kai wannan karan dole in shi mata Albarka Allah yasa yasota kamar yamutu." Ameen Ameen dai ai dakyar tabishi fa sai da nayi mata kamar na tsine mata tukunna kinga lokaci daya yabamu dubu dari gashi yace zai bamu gida da mota ai arzuki mukuwa yazo." Wannan ne karo Na farko da babbar yaya ta kalli iyayen nata cike da baƙin ciki, wannan labari baiyi mata dadi ba duk da ta dade da banzatar dakanta Amma wannan magana taƙasance mata wani dafi aciƙin ranta, hawaye take taji ya zubo mata hakan yasata fasa futa ta koma daƙi tana Allah wadai da wannan dabi'a ta iyayenta yanzu shikenan itama Aicha tashiga sahun karuwai tafada sautin kukanta naɗan tashi cike da Namadar abunda takeyi, yaaAllah karka bashi damar jawo hankalinta yaAllah Aicha ta kasance mai tunasar damu Azabarka da haramcin abunda ka haramta yaaAllah karkasa ta rasa mutuncinta tafaɗa kuka nacin ƙarfinta." Sautin muryar Mama ce tatashi tana fadin " Yunzu kamin tadawo bani Naje Na hado mata ganyen magarya da alimun da kaninfari da dan kumaso, da ƴaƴan bagaruwa in dake mata su adafa tashiga kamar sau biyar kaga daga nan zata matse tayi gam abunta." " Ba jiya na baki dubu ashirin ba kije ki hado mata dasu mana, to zata zauna ne batare da anhada mata tsumin kabewa ba ? Dole nasiyo kabewa ko ta cent nairas (Naira dari) in hado da kanin fari da masoro da citta da MINANNAS ayo mata haɗin nan dan ruwan jikinta yadawo." Baba ne ya raba kudin kaso biyu ya miko mata yace " Ƙarbi Nan sai ki ajiye rabi a hannunki." Dariya tayi tace " Shiyasa bana maka bakincikin addu'a kullum fatana kasamu dan komai kasamu rabamana kakeyi Allah yakaimu makkah da madina tare." " Ameen yaa Allah Ni yanzu dai ta gidan nan nakeyi Mu samu Mu canza ginin nan kinga dai damuna tashigo ina tsoron kada ginin nan Namu ya rufta mana kina ganin bara yadda muka sha wahala kullum a tsaye muke bacci." " To ko nabaka wannan kudin mukira magini yaduba." " To ai na kirashi ba yace wannan gidan sai dai azubdashi asake wani ko kwaskwarimar da muka saba yimasa mukayi sai ya kara rufawa." Nanne jikin Mama yayi sanyi kuma." Ke kuma bazakiyi kiyi ki fita ba? Ko baizo baniba, da fari zatayi mata banza sai daga baya kuma tace " Yace yayi tafiya." " kayyasa banji dadin maganar nan ba kice yau babu cin jan naman nan mai dadi." " Kuma bazaki kira wani cikin Alhajin naki baniba? Nifa yau ko mai ciki Nan tabarni da kwadayi wallahi, wannan shinkafa da waƙen badan rainane nakeyinta ba, kinga fito ki karbamana ɗan kifi fa kabeji mana Nifa wannan kwalliyar taki banaso tatafi a iska tsakani fa da Allah." Cikin rashin mafita da Girmama iyayen nata ta Mike ta dakko karamin mayafinta ta yafa."
Tunda yaji saukar kirjinta akan bayansa yasaka jiƙinsa shiga rawa duk wata Nutsuwar da yake takama da'ita gaba daya tashiga yimasa barazana hakan yabashi damar jiyowa yana kokarin tureta daga jiƙinsa jikinsa na rawa yashiga kokarin kifa mata mari Amma kuma idonsa yayi tozali akan kirjinta dake abayyane tanata kuka haɗe da fadin " s'il te plaît, aide-moi, il veut me violer ( Kataimaka min yanaso zaiyimun fyade) haka tashiga Nuna hanyar da tabiyo duk yadda idonsa yayi kasa kansa yashiga juyawa sautin ma'aikatan gurin yaji suna faɗin suke kuga wanene haka yake kokarin tozartata hakan yabasu damar miƙewa gaba daya suka fita bin hanyar da tafada shima Alhajin jin faɗarta yasashi saurin rugawa aguje suma suna binsa. A hankali cikin Nutsuwar da take kokarin gagararsa Yadda jiƙinsa yashiga rawa ya dago idanuwansa da suka canza saboda tsananin masifa ya ƙalleta jikinsa ne yashiga rawa ganin rigar jiƙinta gaba daya yage ga surarta ta bayyana hakan yasa ransa ya bace cike da fizgota yana juya mata baya haɗe da cire rigar shaddarsa mai tsada dake jiƙinsa ya farka gabanta ya mika mata." Kallonsa tayi idonta na zubar da hawaye ta karba shima da bai saba zama haka daga shi sai ƴar t-shirt fara ba yaji yadan tsargu. Batare da yace mata komai ba yaje muje nace ko? Ganin ta kasa matsa daga tsayan da yake, yasashi daka mata razananniyar tsawar da tayi saurin kara fashewa da kuka tana rufe idanuwanta tana faɗin " il veut me récolter, j'ai peur qu'il ait une arme ( Yanaso yayimun fyade ina tsoro yanada bindiga) " cikin wata tsawa da yasata saurin shige masa jikinsa yace " Zaki huce daga nan tsirara ko sai na karyaki bakida hankali." Daya daga cikinsu ne yace oga kayi mata ahankali da Allah kanagani a firgice take kuma munduba ko'ina yagudu danAllah kataimaka mata kakaita gida ." Cireta yayi daga jikinsa yace mai isa ku baku da kunya ina muharraminki ne da zaki rungumeni ko ki taɓamin hannu dubi shigarki dubi kanki abunda yafi fyade ma ai sai anyi miki. Me isa baakwa siturta jikinku?." Jikinta na Rawa tace " Niba ƴar iska bace ba bamtaɓa iskanci ba iyayena suka sani saka kayannan suka sakani binsa... a dan wahale yajiyo yana ƙallonta jin ƙalmat iyaye data ambata.
MUTALLAB ASAD MUTALLAB
(labari mai taɓa zuciya)
Na
Billy s fari
Nana diso
RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU.
TAFIYAR BIYU TAFI DAYA
SHAFI NA HAMSIN DA HUƊU.
"Is ok" Mahmoud ya faɗa tare da miƙewa yafice daga ɗakin. Bayan Mutallab yafito yai shirin kwanciya dan sai da yai sallar isha ya shigo gidan ya haye kan gadon baccinsa, yana buƙatar kaɗaici a halin yanzu saboda yasan meye mafita a sha'anin yarinyar nan Aïcha da zuciyarsa ta kamu da soyayyarta, dafarko ya matuƙar jin zafi a yanayin da idanuwansa suka sauka saman surar jikinta bayan ta rungumesa, ya dauka duka mata halinsu ɗaya ganin ita lamarin nata ma yafi muni akan na Meenal, har suka isa gidan iyayen nata bai gasgata zancenta ba sai da idanuwansa suka gane masa kuma kunnuwansa sukaji munanan kalaman dake fitowa daga bakin mutane mafi muhimmanci agareta da sune yakamata sufara bata kariya wato iyayenta, a iya fahimtarsa a halin yanzu ita ɗin nagartacciya ce, kawai iyayenta na amfani ne da kyakkyawar surar da Allah yai mata da cikar halittarta dan su samu abun duniya, menene mafita agunsa yanzu dan tseratar da ita da sharrin abinda zai rusa mata farincikin rayuwa har ma da tasa rayuwar, wani irin tausayinta ne ya rufesa da har yake jin ya zame masa dole kafin yawuce gobe yai wani abun. Ahankali ya lumshe idanuwansa yayin da nan take ƙwaƙwalwarsa tayo mashi tariyar yanayin daya ganeta aciki ɗazu, "Ya Allah". ya faɗa jin yanda matarsa tawani ƙulle masa kafin yanayin daya saba tsintar kansa aciki yafara taso mashi, ya matuƙar jigata adaren irin jigatar da bai taɓa yiba, dan bai samu baccin ya ɗauke da ba sai bayan wucewar ƙarfe biyu na dare, da asuba ma sai ana kusan tada salloli sannan ya iya miƙewa daƙyar ya shiga yayo wanka saboda ƴar natsuwar daya samu acikin baccinsa data haifar masa dayin wankan. Kasancewar koda yafito har angama salloli sai kawai ya shimfida abun sallah yai sallarsa agida, bayan ya kammala ya janyo wayarsa ya kamo application na complete Qur'an ɗin dake ciki ya shiga karanta suratul baƙara cikin muryarsa mai matuƙar sanyi da kuma daɗin sauraro, bayanta kammala ya karanta azkar sannan ya nemi waje ya koma baccinsa dan sai ƙarfe sha biyu na rana jirginsu zai tashi.
************
Jalil na dawowa office wanka kaɗai yai ya kira Afrah yace ta shirya su wuce gidan Abba dan ita gaba ɗaya ma ta manta da zancen, ɗan turo baki tayi tana kallonsa haɗe da cewa, "Wai ya Jalil baka manta ba?" idanuwa ya zaro yana kallonta haɗe da cewa, "Afrah yaushe kika koma haka? Kin manta matsayin Abba ne a wajenmu da kike tunanin akwai abinda ya shafesa da zan iya mantawa dashi?"
"Amma ya Jalil kana gani fa tunda yakoremu bai nememu ba, idan ku maza ne zaku iya kulawa da kanku baya tunanin ni macece ina da raunin da ako yaushe zan iya buƙatar mahaifina atare dani tunda yasan banda mahaifiya a raye kamar sauran yaransa?" Murmushi Jalil yai yana hango damuwarta akan haka cikin idanunta kafin yace, "banda abunki Afrah ai Abba yasan muna tare dake babu yanda za'ayi mubari wani abu yacutar dake, beside ma Abba ya nememu Afrah kuma yana sane da duk wani motsi namu kawai ba yanda ya iyane da abinda yariga yafi ƙarfinsa shiyasa bai nemi mukoma can ba". "Yaya.." hannu ya ɗaya mata tare da cewa, "ya isa Afrah shiga ki ɗauko mayafinki". Ganin babu alamun wargi a fuskarsa yasa ta shiga ta ɗauki mayafin nata suka wuce tana faman haɗa rai, juyowa ya Jalil yai ya kalleta tare da maida hankalinsa ga riƙon da yakeyi, nasiha ya soma yimata akan girman iyaye koda kuwa kafirai ne balle nasu mahaifin da yake musulmi wanda hakan ya ta ɗan sassauta fushinta.
A bakin gate Jalil ya ajiye motarsa sannan suka fito suka shiga cikin gidan, suna shiga sukaci karo da Jidda zaune can gefe saman kujeru suna fira da ABB wanda zata aura dan yanzu auren nasu ma saura wata ɗaya kacal, baki Jiddah ta saki daga ita har ABB suna kallon Afrah, shi yana mata kallon jaraba saboda tsabar yadda kyanta da dirinta suka fizgeshi ita kuma Jidda nayi mata kallon mamaki ganin yadda ta sauya ta wani yi fresh tamkar ba Afrah ɗin data sani a ƙanjame ba, abinda ma ya girgizata haƙoran data hango data saka na Makka abakinta dan tafe suke hankali kwance suna firarsu da Jalil, ABB ne yace "Wow Baby waccan cikar fa? Gaskiya ta haɗu kin ganta kuwa?" Yaƙare maganar yana wani karkace kai tare da regen Afrah da suka wuce abunsu kamar basu ganesu ba agun. Cike da takaici Jiddah ta maka masa harara tana cewa, "Ban gane ba wai kallon meye kake yimata haka? Ƙanwata face?" Ta ɗaure fuska tana kallonsa, murmushi ya saki yana shafo baki haɗe da cewa, "sorry gaskiya ta haɗu Beb! Dama kuma da alaƙa da larabawa ne?"
"A'a da indiyawa dai muke da alaƙa, idan baka ji tsoron ba duk wannan kyan nata da kake gani na ɗan maciji ne shiyasa Abba ya koresu agidan nan saboda mugun halinta ita da yayunta". "Anyway beb ɗin zazzafar ce sosai, how i wish kece ita babyna". Ya faɗa batare da tsoro ba dan ake tasan karce tsakaninta dashi, a hasale tamiƙe tana harararsa saboda baƙin ciki kafin kuma tafashe da kuka tabar wajen aguje dan aganinta ba ƙaramin wulaƙantata yai ba, kiranta ya shiga yi amma tayi banza dashi hakan yasa ya ɗage kafaɗunsa irin i don't care ɗin nan haɗe da miƙewa ya shige motarsa yai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 31 Chapter of 54