ya sakeyi haɗe da cewa, "kai nake jira kabarni a tsaye, ina fatar dai Lafiya ko?" Mutallab ya sake jeho masa wata tambayar kai tsaye, daburcewa Jamil yayi haɗe da cewa "Uhm uhmm daman magana ce akan kasuwar nan taka nace dan Allah kagayamin tsakaninka da Allah inda kake samun kuɗin nan, kaga nima sai naje abani tunda..." Hannu Mutallab ya ɗaya masa yana yimasa wani irin kallo haɗe da cewa, "Ya isa haka malam ya'isa, kamanta lokacin dana buƙaci aiki a ƙarkashinka ko Abba mekace mani? Cewa kayi naje nayi dako ko ba haka ba? To naje nayi dakon kuma Allah yabani daga falalarsa ya kuma sakamin Albarka aciki, dan haka idan har zaka iya dako to sai ka shirya da safe na rakaka inda nafara". yaƙarasa faɗa yana mai shigewa ɗakin nasa tare da rufo ƙofarsa". Mamaki ne yakusan kashe ya Jamil hakan ya sakashi kaɗa kai zuciyarsa na masa zafi yawuce part ɗin da dake can gefe.
Tunda Mutallab yashiga ɗakin nasa kasa attaka komai yayi ya samu gefen katifarsa yayi zaune tare da dafe kai, yajima a haka kafin yamiƙe ya rage kayan jikinsa, wanka ya farayi kamin yasaka gajeran wando da singlet wanda yanzu suka zame masa kamar kayan bacci, baƙin cikin maganar da ɗan uwan nasa yayi masa da safe da wadda mahaifinsa yayi masa yanzu sune suka taru suna yimasa yawo acikin ransa, a ɓangare ɗaya kuma yarasa yadda zaiyi da Meenal dake nema ta shige masa hanci, Amma yasan abinda zaiyi, mirginawa yayi haɗe dayin rubda ciki sai yaji wayarsa tayi ƙara shigowar message, kamar bazai ɗaga ba sai kuma yamiƙa hannu ya lalubo wayar a mazaunin da take ajiye, ɗago kansa yayi kaɗan yana buɗe saƙon.
_'Da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun masoya a wannan duniya. Da a ce zan tsunko kowanne fure na baka shi a hannunka, hakan bai isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ka ba. Kaine murmushi na, kuma kaine farin-ciki na. Ina sonka cee mee in your dream'_
Yana gama karanta saƙon yakai hannu zai goge sai ga kira yashigo, ƙin ɗagawa yayi ya kife wayar nata ruri har tagaji ta bari ɗan kanta dan baisan lambar ko waye ba, Meenal kuwa data karɓi lambar ya Kamal ta tura masa saƙon naganin yaƙi ɗaya kiran tafashewa Kamal da kuka, kamar zai maketa yace, "Dallah Malama kiyi mani shiru, ko nine bazan ɗaga kiran nan ba saboda bana ɗaukar sabuwar lamba, balle shi daya san kina daman bibiyarsa, ance Asiya maki wata wayar kin nace sai dai a gyaro maki taki bayan kinsan kin baro layinki aciki".
"Ya Kamal pics ɗin sa fa suna ciki, taya kike tunanin zan iya haƙora na sauya wayar". Meenal tafaɗa cikin kuka tare da faɗawa jikin ya Kamal ɗin, lumshe idanuwa yayi yana shasshafata yana lallashinta tayi shiru, kamar wacce aka tsikara tamiƙe da sauri tana cewa ya banyi sallar la'asar da magrib ba gashi har anyi isha, bari naje nayi ya Kamal Mommy tace zai soni". da kallo Kamal yabita har ta haye sama yana matakin meye haka ke damunta...
#Mutallab Asad
#Tagwaye Biyar
#Billy S Fari
#Nana Diso
*MUTALLAB ASAD*
*PAID BOOK #500*
*TAGWAYE BIYAR.*
NA
*NANA DISO**
&
*BILLY S FARI*
30.
Mutallab kuwa daya kasa bacci yamiƙe zaune tare da janyo wayarsa yakira lambar da Meenal takirasa ɗazu bai samu ba, hakan yasa ya juya akalar kiran nasa ga lambar da aka turo masa da saƙo mintunan da suka wuce yakara akunnensa, Meenal da bata daɗi da gama sallolin data ranka ba ta haye kan gado tana karanta wasiƙar jaki ya Kamal ya turo ƙofar ɗakin nata bako sallama ya miƙa mata wayar shima yana faɗawa kan gadon nata tare da ƙoƙarin janyota jikinsa, wani kallo tayi masa haɗe da yashi zaune tana karɓar wayar, ganin lambar Mutallab ya sata zaro idanuwa jiki na rawa ta ɗaga tana komawa saman bedside ta zauna, da wata irin sanyin muryar dake nuna tsantsar mamakinta na kiran da Mutallab yayi mata tace, "Hello my love". Mutallab dake cikin wani irin yanayi ya lumshe idanuwansa tsigar jikinsa na mimmiƙewa wani irin feeling na sake taso masa, ko kaɗan baiyi tsammanin Meenal ɗin nace da sam bai kira wayar ba, cije baki yai tare da runtse idonsa yana ambaton sunan Allah sannan yayi mata sallama. Batare datasan mahimmancin sallamar ba tace, "My love kaine kakirani? Daman Mommy tace inyi addu'a Allah zaisa kaima kaji kana sona sannan sai ka kirani".
"Baki iya amsa sallama bane ba?" Cikin farin ciki tace, "Waalaikassalam". Shiru yayi ya rasa ma me zaice mata saboda har ga Allah bai san me zaice mata ba, da yasan itace bazai kira lambar ba. Kamar anfizgo kalmomin a bakinsa kawai taji yace, "Ki turomin da address ɗin gidanku zanzo na sameki gobe".
"Wayyo Allahnah Are you serious Mutallab?" Tafaɗa cikin ruɗewa tana yarfi da hannuwa saboda tsananin jin daɗi,
"Sai da safe" yafaɗa yana katse wayar yana komawa kwance haɗe da dunƙulewa waje ɗaya, shi kaɗai yasan yanayin da yake jin kansa aciki saboda jikinsa har rawa yakeyi, haushin kansa yaji tare dayin tsaki yana jin tsanar yarinyar cikin ransa, ɗan ako yaushe yana ta'allaka yanayin da yake shiga da farkon fara ganinta da yayi cikin ƴar iskar shigar daya tsani ganin macce aciki,sai dai duk da haka baya jin zai iya aurenta tunda baya sonta.
Tun daga ɗakinta take kwalawa Mommy kira tana daka tsalle tafito daga daƙin tana bin matattakala saboda tsabagen murna ko tsaro bataji tasamu bugewa ko gurɗewar kafa take cewa, "Mommy..Mommy yakira waya, wallahi Mommy yakira". hakan yasaka Dady da Mommy dake ɗakinta rigerigen fitowa har suna haɗa baki wajen cewa, "lafiya?" Aguje tazo ta rungume Mommy tana faɗin "thank you, thank you Mommy wlh kinga yakirani yanzu yace in basa address ɗin gidan mu gobe zai zo." Daga dady har Mommy murmushi suka saki, sosai suke jin tausayin wannan soyayya da takeyiwa Mutallab haka mai zafin gaske wacce da zata rasashi basu san halin da zata iya shigaba, hawaye Dady yaji sun tarar masa a idanuwa saboda yawan ba lallaine kota auri yaron ba ya darajata ba saboda wannan mahaukacin don data nuna masa tunda ba'a don ranshi zainaureta ba yayi saurin goge hawayen tare da barin gurin. Mommy kuma cewa tayi, "To masha Allah Allah yatabbatar muku da alkhairi Meenal, haka akeyi aduk lokacin da aka shiga wata damuwa ko tsanani a yawaita karanta addu'a tare da neman agajin ubangiji kinji ko?" Taƙare zancen tana mamakin rungumar da Meenal tayi mata tana kiran sunanta cikin girmamawa, shin kodai da gaske tun farko itace bata biyo matakai masu kyau ba wajen inganta tarbiyar yarinyar nan sai take ganin kamar tsaurarawar da takeyi zaisa tafi jin maganarta tare dayin abinda yake dai-dai? Ko duk soyayyar ce ta maida ita haka alokaci ɗaya, ganin ba tada amsar tambayoyin nata yasa ta sauke ajiyar zuciya tana ƙoƙarin juyawa Meenal ta saki murmushi tace, "sai da safe Mommy". Tana ɗaya mata hannu, Murmushin itama Mommyn tayi sannan tashige ɗakinta. Kamal dake sman step ya haɗe hannayensa yana yiwa Meenal wani ɗan iskan kallo ya shiga saukowa tare da nufo wajenta ya riƙo hannunta yace, "gaskiya wannan guy ɗin yatafi da duniyarki Meeneluwa, tabɗijan wai Mommyn da kike cewa kin tsana bakya sonta yau itace kike wani hugging ɗinta har dasu Godiya kina mata sai da safe, lallai wannan ƙauna da kike masa is beyond the expect".
"Hmm..Ya Kamal idan kaganshi kaima zakace na iya zaɓe saboda one in town ne, ya haɗu ta ko'ina har ya gaji". Wani rungumota yayi tare da cewa, "Haba Meenal! Yakai ya'yan naki?" Kallonsa tayi tare da tureshi tana dariya har tana riƙe ciki tare da dukansa a ƙirji kafin tace, "Ɗan Allah ya Kamal karabu dani da wannan barkwancin naka naje naƙara yin sallah ko shima zai gigice akaina gobe, idan ana zancen Mutallab ya Kamal aikai choose ne". Taƙare zancen tana dariya tare da barin wajen, ko kaɗan ya Kamal baiso hakan ba Dan Yana masifar sonyaji Meenal ajikinsa, amma sai kawai yayi haƙuri ya ƙyaleta yashige sashensa shima yana faman riƙe jikinsa.
WASHE GARI.
ALHAMIS 12:00
Zaune Abba yake yana jiran Mutallab ya shigo bai shigo ba amma, gashi yau Umma tun safe ta sanar dashi zataje gidan yayarta ba lafiya, Anty Amaryama jin haka itama tace zataje gidan mahaifiyarta dukansu bai hanasu ba yabarsu. Yau Afrah ta kawo masa abun karinsa, Jiddah kuma tanada lecture da safe dan haka bata gidan. Yana zaune yana saka yadda zai tozarta Mutallab akan yarinyar nan idan bai amince ba yaji gidan Radio din da ya kunna suna Tallah akan manyan shagunan dake cikin kasuwar singa.
_BARKA DA SAFIYA MA'ABOTA SAURARON GIDAN WANNAN REDIO NAMU, SHIN KO KUNADA LABARIN CEWA MUTALLAB ASAD ENTERPRISES YANA DAGA CIKIN BABBAN SHAGON DAKE KAN GANIYARSA ACIKIN KASUWAR SINGA DAKE KAWO MAKU NAU'UKAN ABINCI NA MORE RAYUWA DA KUMA SAMUN INGANTACCIYAR LAFIYA? IDAN BAKU SANI BA TO ZAKU IYA ZIYARTAR SHAGON MAI LAMBA 77 ACIKIN KASUWAR TA SINGA DOMIN SAMUN KAYAN ABINCI MASU INGANCI DA KUMA SAUƘI DA RAHUSA, SHAGON NA MUTALLAB ASAD ENTERPRISES NA MARABA DA SIYAN ƊAYA KO SARI." Afirgice Abba ya miƙe cike da mamakin yana mai jinsa tamkar acikin mafarki, da sauri ya ɗauki wayarsa ya kira ɗaya daga cikin abokanan sa daya sani a kasuwar yana kashe radion, bugu ɗaya ya ji ya ɗauka yana ƙoƙarin daidaita natsuwarsa yace. "Alhaji Murtala barkan mu da rana dafatan kana lafiya? Ya kokari? Ya komai da komai?"
"Alhamdulilahi Alhaji Asad ya gidan kowa da komai lafiya ko?"
"Lafiya ƙalau".
"To masha Allah, ai jiya nake gurin ɗan wajenka Mutallab sarin kayan abinci nake cemasa baisanni ba ko? Yace min eh bai ganeni ba nace idan yazo ya tambayi mahaifinsa yace masa Alhaji murtala zai yimasa bayani, yaro Allah ya dafa masa Alhaji yanzu idan baka kira sunansa jerin masu kuɗin kasuwar nan tamu ana farko ba to tabbas zaka kirasa nabiyu, ɗan ta wannan fannin dole a ambaceshi saboda kyawon kayansa da ingancinsa, yaro kam yai gado har ya wuce nake cewa dole yaro yasan sirrin kasuwa dan mahaifinsa cikakken dan kasuwa ne gaba da baya". Mamaki ne yaƙara cika Abba yace "Wai kana nufin Mutallab dai ɗan wajena da naji angama tallata shagonsa a redio shi kake nufi?"
"Eh mana ai ba'a kasuwanci ba har tallafi zaka ji ana yawan faɗarsa agidan redio ya bayar, amma Alhaji karkacemin bakasan yaronka yayi irin wannan shaharar ba?"
"Wallahi banda masaniya Alhaji Murtala saboda yaron sam bai ɗauke i da muhimmanci bai, shiyasa kwanannan dana ga yafara hawan motar miliyoyan kuɗi nafara zarginsa, ashe ni yamayar yana can ya kafa kasuwanci yana yadda yake so". "Uhm To Allah yasawaƙe kaga amfanin jan yaro ajiki ai nasha gayamaka su yaya bakasan wanene zai gajeka agaba ba ko ya amfaneka, adalci ake musu amma gabaɗaya ka karkatar da kanka akan Jamil, yanzu gashinan Jamil babu abunda yake jawo maka sai magana shi wannan ɗin daka wulakanta yazama wani abun, wlh akwai ranar dana ganshi yana dako a kasuwa kamar nace yadawo shagona sai naga mahaifinsa da yafini wadata ma bai bashi shago ba sai ni sai na ƙyaleshi yau gashi yadda Allah ya maida abunsa." Saurin katse wayar Abba yayi saboda yadda yaji zuciyarsa tana huruwa saboda ɗacin maganganun da Alhaji Murtala ke faɗa masa, ba damuwarsa yanzu kamar ace da gaske Mutallab yayi arziƙin da Jamil ɗaya fifita akansa baiyi ba saboda shiya tallafawa ya sanya shi acikin dukiyarsa yayi yanda yake so? Kenan ina yake kai masa kuɗi da da yake kwasa?.
*******
"Aryan.." Ummie takira ɗan nata ya amsa masa da, "Na'am ummie?" "Ni kuwa ina taso in tambayeka wai Mutallab ne yayi suna haka agarin nan ko kuma bashi bani wanine can daban! Naga dai shi har yanzu babu wata alama dake nuna yayi arziƙi tunda har yanzu yana nan zaune gidan mahaifin nasa". Murmushi Aryan yayi yace, "Ai Ummie munyi kuɗi yanzu sai godiya ga Allah, kinsan dare ɗaya Allah kanyi bature" Jijjiga kanta tayi tace, "Ikon Allah sai kallo abun mamaki ga bawa yake ba agurin Allah ba, kuma dama shi mahaƙurci mawadaci ne. Allah ya ci gaba da saka albarka a kasuwancin nasa ya baku mata nagari".
"Ameen Ummie". Aryan yafada yana miƙewa haɗe da cewa shi ya wuce offices daga can kuma zai shiga gurin Mutallab, Ummie ta amsa masa da Allah ya tsare ya kuma gaida mata da shi.
A ɓangaren Mutallab kuma dama akwai tafiyar da yake tsarawa yana son yi, tunda yafita kasuwar ya tara yaransa gabaɗaya ya sanar masu da zancen duk da baisa ranar yin tafiyar ba suka yimasa fatan Alkhairi baki ɗayansu sannan suka koma wajen aikinsu, suna barin gurin Aryan naƙarasowa come da tsokana yake faɗin, "Ranka yadade ubangidana kuma aminina kuma dan uwana Barka da safiya". Dariya sosai yaba Mutallab yana girgiza kai yace, "You're not serious at all Aryan, Ni ɗin ne uban gidanka?"
"Eh mana angon Meenal bada kanka asare". Ɗauke fuska Mutallab yayi haɗe da cewa, "Banason maganar yarinyar nan Aryan kwata kwata wallahi ɗan Allah kadena".
"Kai fa matsalarka kenan! Kaga fa yadda yarinyar nan ke bibiyarka tana sonka over her life amma kana kwafsa mata, Kai kasan wacece ita da girman kan da take dashi amma taƙare da baran soyayyarka ako ina kuma aduk inda taganka? Gaskiya abunda kakeyi MAM babu kyau, ko da yake har da laifin so da beyi mata adalci ba".
Ɗago manyan idanuwansa yayi ya zuba akansa haɗe da cewa, "Aryan kenan! So kake na auri yarinyar mutane bayan bana sonta kuma nazo nakasa bata kulawar daya kamata?"
"To wai kai a faɗa maka dole so ya shiga zuciya lokaci ɗaya, nifa MAM mamaki kake bani bafa yammatan nan kake kulawa ba bafa tsayayyi ce dakai ba ba kuma soyayyar nan kake ba amma kuma ka dage akan baka sonta to wakake so? Ko kafin so ka zauna jaraba nafaman cimma karasa yanda zakayi da ita?" Hararar wasa ya maka masa kafin yace, "Ina nan ina gayawa Allah zaiyimin zaɓi nagari da babu dana sani aciki in sha Allah".
"To ai Shikenan Allah ya amsa mana, amma ina so ka sani ka auri maccen data fi sonka duniya ne wallahi bawai kai kafi sonta ba".
"Mubar wannan zancen, ina tunani zanyi tafiya cikin week ɗinnan Aryan tunda naga kaima yanzu ka iya hawan keken ɗinkin nan ka ƙware me zai hana mutafi tare, ina son buɗe ko shaguna biyu ne acan na ɗinkin ɗan Alhajin maraɗi ya faɗawa mr. Jennifer cewa da zanje can na kafa wajen ɗunki na ire-iren kayayyakin nan namu to da ansamu alkhairi sosai, kaga wata damace wannan da zan samu har nagano dangin mahaifiyata tare da haɗawa da shagunan abinci ko haka gani?"
"Ahhh... Ai ƙafata ƙafarka maigida a 360 ma zan bika". Aryan yafaɗa yana dariya.
"To Shikenan passport dinka yazama ready ɗan kada mu samu matsala"
"Kamar ya MAM bayan baka faɗa mani wace ƙasar ce zamu haura ba".
"Afuwan ai nazata ka gane tunda nayi zancen dangin mahaifiya, kuma nasan dai kasan ita ɗin ƴar Nijar ce". yafada kai yana fita daga shagon Aryan yabisa abaya suna ci gaba da tattaunawa....
********
Tafiya ce mai nisan gaske Umma tayi kafin ta isa wajen bokanta da take kira malami, danna kallo ɗaya zaka fahimci shi ɗin cikakken mushrikai ne daya amsa sunansa, ko data shiga dajin ba ƙaramin tafiya tayi ba kamin takai bakin wani kogi, nan take taji guguwar da tasaba ji ashekarun baya na karaɗe wajen, wacce ke alamtawa bokan nata cewa yayi baƙi. "Kicire ɗan kwalinki, karki shigo mana a tsaye, kishigo mana da rarrafe". Taji anfaɗa cikin wata irin murya mai ƙara da bata saba jinta ba a lokutta data saba zuwa, cikin rawar jiki Umma tacire ɗan kwalin kanta ta tsugunna tashiga yin rarrafe har ta ƙarasa gurin. Dariya aka shiga kyalkyalawa ana cewa, "munsani basai kin faɗa ba, bazamu iya aiki akansa ba yana addu'a ta neman tsari sosai ko munyi masa sai ya karye, sai dai a yanzu muna da labarin yarinyar dake sonshi, zamuyi anfani da ita mukaɗashi agarari, mu ƙarfafa mugayen halayenta, mu tsananta miyagun ɗabi'unta sannan mu haɗata da aljana yar tsalle da zata sakata bijire masa tako wace fuska". Cikin rawar jiki Umma tace, "Mai gidan nawa baya tani yanzu?"
"Karki damu shegiya hatsabibiya, shima zamuyi masa asirin da sai abunda kikace masa duk abunda zaki sakashi bazai taɓa tsallakewa ba, maganarki zata zamo tamkar zanen dutsi awajensa ko yana so ko baya so".
"Godiy.."
"Tashi la'ananniya bama buƙatar godiyarki, ki ajiyewa aljana ƴar tsalle sadaka sannan kiwuce kina tsallen kwaɗo". boka nakan ruwa yafaɗa yana sake fashewa da wata irin dariya data saka fitsari ya kuccewa Umma, jiki na rawa ta ciro kuɗi tafara tsallen ƙwaɗo har tafice daga dajin
#Mutallab Asad
#Tagwaye Biyar
#Billy S Fari
#Nana Diso
*MUTALLAB ASAD*
*PAID BOOK #500*
*TAGWAYE BIYAR.*
NA
*NANA DISO**
&
*BILLY S FARI*
28.
Sai da ya tabbatar ya ajiyeta a makarantar tare da ƙaramata kuɗin kashewa sannan yayi hanyar gininsa da ake kanyi ya ɗauki aƙallah kusan mintuna talatin agurin kamin yayi kasuwa kai tsaye! Yadda komai yake tafiya acikin shagon nasa yasa ya sake ƙara yin godiyawa Allah. offices ɗinsa dake can ciki yashiga yana duba wasu sabbin biscuits da wani kamfani sukayi masa tallah akan shi zasu fara bawa dilolinsa shikuma yasiyarwa da ƴan kasuwa, Wannan ne karon farko da murmushi ya suɓucewa fuskarsa a take kyansa yaƙara bayyana ƙarara dan yasan baƙaramin riba zai samu da wannan biscuits ɗin ba, duba da last month sun samu na shinkafa mai tsoka, yana tsaka da wannan tunanin ne yaji wayarsa tafara ringing kasancewar sabuwar waya ce a hannunsa sai numbar takasance babu suna ajiki, hakan yasashi share kiran da akeyi alokacin duba da mata da suka addabawa rayuwarsa da kira yaki ina yanzu, abun har tsoro yake bashi wasu ma sungirme masa amma sai ya dinga ganin text ɗinsu na soyayya, abun ma ba'a magana. Bai kai gga gama wannan tunanin ba yaji sauƙin shigowar message.
_Barka da safiya kyakkyawana! my love Ina so ka sani cewa da tinanin ka nake kwana kuma dashi nake karyawa ako wani lokaci. Enjoy your day_.
Tsaki yaja tare da goge message ɗin dan shima lambace babu suna ajiki, sai kace anfaɗa masu abinda yake tunani kenan, wani tsakin ya sake ja akaro na biyu ganin kiran ya sake shigowa da numbar da aka gama kiransa ya ɗauka yana karawa a kunnensa tare da faɗin "Assalamu alaikum." Tun kafin yaƙarasa sallamar ma yajiyo kukan Meenal tana faɗin "Haba Mutallab! Ni bansan me yasa kake wulaƙantani haka ba dan na nuna maka soyayya, kayarda dani wlh soyayyar da nake maka ta gaskiyace, bayin kaina bane nima ko so kakeyi inyi hauka dan Allah? So kakeyi cutar sonka tasa namutu? Ina jin raɗaɗin soyayyarka a zuciyata tamkar zan mutu, na roƙeka dan Allah ya Mutallab kataimaka ko wayata ce kadinga ɗauka". Kasa cewa komai Mutallab yayi yai shiru yana jin yadda taci gaba da shasshekar kukan nata, tsigar jikinsa da yaji tafara miƙewa yasashi runtse idanuwa dan tabbas wannan kukan nata dake cike da shagwaɓa zai iya jefasa acikin wani yanayi, buɗe idanuwan nasa yayi da suka fara sauyawa yai a hankali yafara motsa bakinsa yana cewa, "Look Meenal kike ko?" Jin yai wani murmushi ya subuce mata har yana fita da wani sauti tana ɗaya kai da sauri saboda jin daɗin yakira sunanta, wanda hakan yabashi damar cigaba da cewa, "Bazan taɓa iya wulaƙantaki ba Meenal saboda nasan darajar mace, amma ina so kisani wallahi bana miki kallon masoyiya, ako yaushe kallon ƙanwa nakeyi miki tare da yimaki fatar alkhairi, I'm beg you pls kizauna ki nutsu ki gyara rayuwarki da kuma ɗabi'unki sai kiga Allah yabaki wanda yafini, domin idan nace inasonki Meenal to tabbas nayi maki ƙarya kuma yaudarar zuciyarki kawai zanyi, sannan bazanci gaba da ɗaga wayarki ba ina sauraronki dan ɓata miki lokaci ne zanyi, haka ma idan nayi miki alƙawarin aure to tabbas naci amanarki dan ba auren naki zanyi ba, ɗan haka naroƙeƙi kawai kibarni". Wani sabon kukan tasaki wanda sai da yasakashi ɗauke wayar daga ƙunnensa tana cewa, "If that's what you going to say you're not in love with me! To tabbas zan mutu, zan mutu wallahi ya Mutallab". tafaɗa tana ƙara sautin kukan nata tare da kashe wayar tayi wata irin kida da ita. Wayar kawai Mutallab yabi da kallo jin ƙarar wayar tata data fasa kafin yaci gaba da sabgarsa cike da mamakin Meenal ɗin yana jinsa awani yanayi, dan Allah ma tasani yanzu ba ƙaramin ƙarfin hali yakeyi ba da taka tsantsan akan sha'anin mata, dole sai yabi a hankali da mata dan ko muryar macce yaji sai ya riƙa jin mood ɗin da na canzawa, uwa uba kuma irin kukan da Meenal keyi masa yanzu dake cike da shagwaɓa.
Meenal kuwa data zube tsakar palour tafashe da kuka da dukkanin ƙarfinta kallonta Mommy tayi da yadda ta rotsa wayar tata aƙasa tana kuka aranta tana faɗin, 'Lallai Allah abun tsoro ne gamai hankali da tunani, daman akwai ranar da Meenal zata kasance cikin soyayya haka? Ko ba'a sanar mata ba wannan yaron da take so sam baya sonta ita kaɗai ce ke haukar sonsa kenan!" Ajiyar zuciya ta sauke duk data daina shiga lamurranta, Cikin sanyin murya tace, "Meenal menene haka kikeyi? Wayarki fa kika rotsa da aka siya maki jiya da maƙudan kuɗi, to da wace wayar zai kiraki kuma idan yafara sanki? Ni anawa tunanin wannan kukan baida amfani kuma zai iya yimiki illah, bai kamata idanuwanki su rufe ba har kizo ki saka kanki a matsala, kiyi haƙuri ki share hawayenki ki tashi kije kiyi karatun alƙur'ani kuma kiyi sallah ki gayawa Allah idan shi ɗin alkhairinki ne ya mallaka maki shi cikin sauƙi kuma yasa yasoki, sai kiga Allah yashiga lamarinki". Da sauri ta juyo ta kalli Mommy da manyan idanuwanta da suka kumbura saboda kuka tace, " Idan nayi sallah nayi Addu'a zai soni mommy? Zai aure ne?"
"Eh in sha Allah matuƙar shi alkhairi ne a rayuwarki".
"A'a Mommy kidena zancen alkhairi, Mutallab ko meye shi aguna ina sonsa kuma zan iya zama dashi a matsayin matarsa".
Da mamaki Mommy ta kalleta tana cewa, "Idan dai Alkhairin ne ai yafi Meenal, kije ki dage da Addu'a sai kiga Allah ya juyo maki da hankalinsa kanki". Tana murmushi ta kalli Mommy tana goge hawayen dake zubowa kan fuskarta tace, "Daman banyi asuba ba bari nahaɗa da azahar sai nayi gabaɗaya".
Murmushi Mommy tayi cike da tausayin wannan kalar rayuwar da takeyi na rashin kula da ibadarta wanda ta tabbata yakan iya zamowa silar faruwar komai akanta cikin sauƙi, A rayuwarta yauce rana ta farko da Meenal tayi mata magana babu fitsara ba rashin kunya duk a sanadiyar soyayya, kai Allah yakyauta tafaɗa aranta tare da tashi tabar palourn, ita kuma ta shiga haɗa wayar tata tana ƙwalawa ya Kamal kira.
**********
Umma data gama shiga tashin hankali bayan sun shiga cikin gida takalli Jamil tace, "Yanzu zamu zuba masa idanuwa ne Jamil muna kallonsa yana samun cigaba da ɗaukaka haka? Wlh mamaki nakeyi yaushe yaron nan ya samu abunyi? Tayaya ya mallaki kuɗi masu yawan gaske haka da har ya iya mallakar zuƙeƙiyar mota bamu sani ba? Tayaya mukayi wannan sake Jamil?" Umma tafaɗa tana ji zuciyarta kamar tafito. " Tayaya zan sani Umma? Malaman nan fa duk ke kika sansu ni kin hanani ko da guda ɗaya nayi ma'amala dashi, sai yanzu kuma tana neman kwaɓewa ki tambayeni garin yaya haka tafaru" Jamil ya jiyi mata maganar cikin rashin tarbiya da rashin ɗa'a. Cije ƙasan baki tayi tana wani girgiza kai haɗe da cewa "Dole mu nemi malamai Jamil kuma mushiga duk inda suke kada mafarkin da nakeyi yakasance gaskiya dan wallahi zuciyata bugawa zatayi, A yanzu ba abinda nake so irin naga Mutallab ya lalace yana bin mata kamar bunsuru, duk abinda ya mallaka yaƙare akansu ba tare daya mori ko sisi aciki ba." Dariya Jamil yayi yace, "To Umma menene dan yabi mata? Ni kawai so nakeyi muyi masa tsuntsuwa yabar garin, dukiyar daya tara ta lallace shi kuma Abba muƙara saka masa tsanarsa, shine babban abunda yakamata muyi kawai!"
"Kai amma Allah yayi maka albarka Jamil, dama kanka naja haka shine baka taɓa kowa mani irin wannan shawarar ba? Ai tuni tsuntsuwar Yakamata
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 54