Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zuciya Mutallab yayi da russunawa agaban mahaifin nasa ya riƙa, Anty Amarya dake jin kamar ta tashi ta rufesa da duka saboda tsana taji zuciyarta tayi wani irin motsawa, duk da awani ɓangare na zuciyarta tana yabawa natsuwarsa sosai don duk yanda aka kai ƙololuwa wajen ɓata masa rai sam baya barin natsuwarsa tabar gangar jikinsa, hakan yasa wasu lokutan ma saboda kishi take ƙoƙarin ɗora nata yaran a irin turbar don kada yafisu, cikin Muryarsa mai sanyi dake cike da natsuwa yace, "Kayi haƙuri Abba, dama nima wannan zaman ya isheni da zaka samarmin aikin kowane irine da nayi murna ko da kuwa matsayin yaron ɗaya daga cikin shagonka ne zan ƙarɓa". Bai ƙarasa rufe baki ba Umma daketa make masa harara ta ƙasan ido tun ɗazu tace "Kamar ya Mutallab! Yau she kasan yanda ake sarrafa kasuwanci da har za'a kaika shago a ajiye? Ko so kake kajawowa mahaifin naku asara tunda komai anayinsa ne da ilimi". Dafarko bai so tankata ba amma sai yaga bai kamata ya ƙyaleta ba a wannan gaɓar dole tana buƙatar ya bata amsa dai-dai da tambayar da tayi, don haka ya ɗago kai yana kallonta fuskarsa ɗauke da murmushi yace "Umma kin manta ne bussiness Admistration na karanta? Ai inaga gwargwado a karatun da nayi kowane irin kasuwanci zan iya riƙesa na kuma sarrafa shi fiye da tunanin ƙwaƙwale". Kauda kai tayi fuskar nan a haɗe wani abu na sake taso mata tare da tsaya mata awuyanta tunawa da tayi Mutallab ɗin yayi karatu har zuwa matakin jami'a, wani haushi ne ya sake kamata data tuna ɗaya Jamil daƙyar ma suka samu kammala sakandire. Duk da haka nisawa tayi cikin ko oho tana cewa, "Oh! hakane fa to amma kam ƙara ai afara samamaka ko dako ne aga ya kamun ludayin ɗan bokon yake sannan ayi zancen baka shago?" Murmushi ya saki don yasan da nufi tayi wannan zancen don kada mahaifin nasa ya bashi ɗaya daga cikin shagunansa, sai dai shi ko hakan ne zai samu yana da buƙata akan wannan zaman nasa da sukeyiwa laƙani da zaman kashe wando ko kuma zaman banza, cikin girmamawa ya kalli mahaifin nasa haɗe da cewa, "To Abba kaji ko dakon ne ina so zanyi". Batare da Abba ya kallesa ba yace "Banida lokacin samar maka aiki kaje can kasamu ko ma wane irine, in ma dakon kake so haka ga waje tunda kasan hanyar kasuwa ai yanzu ni ina busy nemawa ɗanka Saqeeq University of Oxford dake London bazan iya haɗa abun biyu ba". Shiru Mutallab yayi yana mamakin kalaman da mahaifin nasu keyi wani irin ɗanyen baƙin ciki na taso masa daga ƙasan zuciya amma sai yayi saurin danne hakan tare da cewa, "Shikenan Abba ba damuwa Allah ya taimaka, in Sha Allah zanje dakaina ɗin na bincika zanje na bincika ina baran adduarka". Cikin rashin damuwa da zancen nasa Abba yace, "Allah yasa dagaske kakeyi". Mutallab ya amsa da Amin kawai tare da miƙewa yana cewa, "Na barka lafiya". Sanna yafita yana jin wani zafi aransa na halin ko inkula ɗin da mahaifinsa yayi dashi, duk abubuwan dake faruwa dashi a gidan bai taɓa karaya akansu ba sai wannan da shine na farko da sashi zubar da hawaye yana jin matsanancin maraicin uwa atare dashi, duniya kenan yana kallon matan uban nashi da suna jin me Abba ɗin ke faɗa amma saboda shiɗin bai zama jininsu ba aka rasa wacce zata saka baki ta roƙa masa alfarma koda ƙanƙanuwa ce awajen mahaifinsa sai ma Murmushi daya gani kwance akan fuskar Umma, ƙarama Aunty Amarya yaga kamar ranta ya ɓaci saboda irin kallon da take wa Umma. Abinda Mutallab bai sani ba itama Aunty Amaryar ɓacin ran nata ya bayyana ne dalilin zancen makarantar da Abba yace yana nemawa Sadeeq a London shiyasa ta sauya fuska haɗe da aikawa Umma ɗin wannan kallon dayaga tana yimata mai cike da tsana. Bai tsaya komawa cikin gidan ba yayi hanyar fita ya fice daga gidan, sosai yayi tafiya mai nisa aƙafa sannan ya ɗakko naira ɗari biyar ɗin dake aljihunsa ya nemi mai adaidaita ya hau, a babbar kasuwa ta Abni wacce kaf garin babu kamarta ya kaishi ya ajiye ya miƙawa mai Napep ɗin ɗari biyar ya ɗauki Naira ɗari da hamsin ya bashi ɗari uku da hamsin ya mayar acikin aljihun jallabiyarsa. Sai da ya tabbatar yayi addu'ar shiga kasuwa sannan yayi bismillah yafara tafiya cikin natsuwa yana dubin kowane ɓangare da ɓangare na kasuwar, kasuwace ta masu siyar da kayan abinci ya nufi babban shagon daya fara cin karo dashi ya tsaya ya tambaya ko zai samu aiki, sukace masa a'a suna da yara sai dai ya ƙara gaba, kusan awanni uku kwashe yana neman inda za'a ɗauke sa aiki acikin kasuwar amma bai samu ba, har ya fidda rai yana ƙoƙarin juyawa sai yaji wani Mutum yace masa "Akwai wani aiki idan zaka iya ɗan saurayi amma dako ne zaka riƙa yimani ina biyanka". Cike da farin ciki Mutallab ya juyo yace, ." Eh zan iya Alhaji koma meye". "To Shikenan babu damuwa muje can shagon nawa akwai kayan da za'a ɗakkomin acan babban shagon ƴan china dake canciki ƙasan kasuwar sai ka ɗakko mini". cikin Girmamawa Mutallab yashige yabisa a baya zuwa shafin nasa suna tafe yanayi masa tambayoyi a kansa kafin ya tabbatar masa daya ɗauke shi aikin, sai dai Mutallab ya tsinci kansa da ɓoye masa sunan mahaifinsa sanin kusan kowa yasansa akasar duba da gidajen mansa da shagunansa don kada ya zubar masa da kima. Mutumen yace "Yawwa ya ma kace sunanka?" "Mutallab Alhaji". Mutallab yafaɗa cikin ɗan girmamawa, "To Mutallab ga kurar nan da zaku jido mini macroni katan 50 da taliya katan hamsin ku kawosu nan". Ɗan zaro  ido Mutallab yayi yana kallon kurar tare da jan wata irin ajiyar zuciya, ganin haka Alhajin ya kallesa yana faɗin. "Ko bazaka iya ba Mutallab? Don na lura jikin nan naka daƙyar in zai barka iya wannan aikin. Murmushi Mutallab yayi yana ɗan russunawa haɗe da cewa, "A'a zan iya". Kallonsa Alhaji yayi yana mamakin saurayi irin wannan da kana ganinsa kasan akwai hutu atare dashi anya zai iya wannan aikin? Shi sai ma yake ganin kamar yasan wani mai irin fuskar tashi, wofantar da zancen yayi haɗe da cewa, "To Madallah sai kuje kai idris zonan kutafi." Amsa masa idris yayi kamin nan kuma yayi waje yana bawa Mutallab hannu su gaisa. Tafiya sukayi akallah zatayi ta mintuna 25 kamin su isa ma'ajiyar, idris ne ya gabatarwa da ƴan china Mutallab yana sanar musu ai sabon yaron Alhaji ne, nan suka gaisa da Turancin da hatta idris da ma'aikatan gurin sai da sukayi mamakin yanda Mutallab keyinsa cike da tsari, daga haka Mutallab bai tsaya ɓata lokaci ba suka fara abinda ya kawo su, a katon na farko yaji hannunsa yariƙe masa tunda ba sabawa yayi ba amma ganin matasa irinsa ko ajikinsu suna aikin ya sakashi ƙoƙarin ƙarasawa duk da kuwa a kallo ɗaya zaka fahimci ba lallai bane ace jikinsa ya saba da irin wannan aikin, da sauri da sauri ake cillo masa daga motar shi kuma yana cafewa, yana sakawa acikin kurar, Tun yanayi yana jurewa har sai da yakasa ana ƙarshen yana ƙoƙarin faɗuwa. idris ne ya kalleshi yana jin tsananin tausayinsa dan ko ba'a gayamasa ba tabbas akwai ɓoyayyen al'amari don shi kallon ma ƴaƴan attajirai yakeyi masa, sake kallonsa yayi cike da kulawa yace, "Mutallab je kahuta naga kafara gajiya zan ƙara da, daman sai a hankali tukunna zaka saba saboda abun is not easy". Ɗago idonsa a raunace Mutallab yayi da suka sauya saboda gajiya yace, "Nagode Idris Ai nagama munkusa ƙarasawa ko?" "Eh saura katon goma, kabarshi zan ƙarasa" Motsawar da Mutallab zaiyi yaji gaba ɗaya jikinsa tamkar an zare masa lakka, gaɓɓansa kuwa duk sun saki suma sai ciwo sukeyi masa, hannuwansa suma sunyi sanyi sunyi masa jajir, zama yayi kan dutse yaba Idris waje ya ƙarasa sannan suka shiga tura kurar su biyu dakyar suka ƙarasa ya nemi gefen shagon ya tsugunna yana sharce zufa, ganin Alhajin na nufo wajen yasa su miƙewa suka nufi wajensa suna faɗin "Barka da yamma Alhaji mun kammala". Inji Idris Yana ɗan russunawa, kallon Mutallab daya gama jigata Alhaji yayi yace, "Barkanmu Idris sai ku shiga ajiresu aciki ko?" Shiru Mutallab yayi yana kissimawa aransa bayan kwasowa da kawowa har da jerawa zasuyi? 'Ya Allah Sa'idni' ya faɗa acikin ransa kamin kuma Idris ya ɗan taɓosa suka shiga cikin shagon, kowacce guda idan zai ɗauka sai yaji bayansa kamar yacire haka dai yana cijewa yana addu'a ya samu suka ƙarasa, Idris ne ya kalleshi yace, "Idan ka koma gida kasamu ruwan zafi kagasa jikinka sannan kanemi maganin ciwon jiki kasha in sha Allah zaka warware da kuma ka saba shikenan zaka dinga jinka wasai, ni yanzu zanje gurin waccen Alhaji madu ɗin na karɓo masa nasa kayan amma shi ba'a kura baniba a kaina zan dinga dakkowa duba da babu nisa inda ake dakko masa da shagonsa." Cikin gajiya da rashin nuna damuwa da ƙosawa da surutun Idris yace, "Idan babu damuwa zan iya rakaka sai muyi?" Wani kallo Idris yayi masa kamin yace " Babu damuwa indai zaka iya sai muje." Sai da suka jira Alhaji yabasu sallamarsu kowannensu dubu goma goma sannan suka nufi gurin Alhaji Madu shima suka ɗaukar masa nasa suka kai masa Mutallab najin kamar an canza masa duniya, tabbas talakawa na rayuwa cikin wahala, da wannan tunanin Alhaji Madu yazo ya basu kowanne dubu bakwai bakwai sanna yakalli Idris yace, "Na yaba da abokin nan naka Idris, don haka kudinga zuwa tare idan babu damuwa yana riƙa maka tunda gashi yau baka ɗauki wani dogon lokaci ba kun gama". "In sha Allahu tare zamu dinga zuwa Alhaji indai yana buƙata, mungode sosai" Sallama sukayi masa kamin su huce su tafi Idris ya kalli Mutallab yace, "Mutallab ni zanyi gaba can akwai wani aiki da mukeyi na hula zanje yanzu, kasamu mai abinci kasiya kaci sannan kayi yadda nace maka." "Tohm nagode Idris sosai, gobe in Sha Allah idan ba damuwa shima zan riƙa bink". Da mamaki Idris ya bishi da idanuwa kafin yace, "Bazance a'a ba amma zaka iya kuwa". "Zan iya mana Idris". "To shikenan zan sanar da Alhajin idan yace nazo dakai gobe ɗin sai mudinga zuwa kaga wancan layin? Akwai masu abinci kala-kala zaka iya zuwa kasiya". Ya amsa masa daya gode sannan ya nufi layin daya nuna masa yana sharce gumin da yayi a goshi.... #Mutallab Asad #Ƴan Tagwaye #Billy S Fari #Nana Diso .Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only Zaki biya ta wannan account ɗin👇🏻 0020428430 Ishaq Fatima A GTBank KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya 07040402435, 0903 056 9336 *MUTALLAB ASAD* (Labari mai taɓa zuciya) NA *BILLY S FARI* & *NANA DISO* ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU TAGIYAR BIYU TAFI ƊAYA. SHAFI NA GOMA SHA UKU _______ https://www.tiktok.com/@maims_kiddies "Lallai Dr irin wannan kyau haka tamkar kunzo daga ƙasar UK? Gaskiya kayan jikin su Hanan sunyi matukar kyau, amma dai ba'a ƙasar nan kuka siya ba?" Cikin dariya Dr Aisha tace. "A ƙasar nan muka siya, sai dai kamar yadda kika ce ɗin haka ne, duk wannan kayan da kika gani a jikin yaran nan na ƙasar UK ne da *@Maims_kiddie* take sai da su a cikin Nigeria, muma a wajanta muka siya kuma ba tare da munje inda take ba, kayan na gani a Instagram account ɗin ta na *KIDS THRIFTY/OKRIKA STORE.* Kayane masu kyau da kwari daki bari kenan malam Khadija dan tun da na fara siyan kayan yara a wajanta shikenan na dena ganin kyawun na ko'ina. Kema/kuma zaku iya nemanta a Instagram link ɗin dake sama. Za kuma ku iya samunta a WhatsApp ta wannan link ɗin dake ƙasa. Ko lambar wayarta. https://Wa.me//08101378616 ________________ Mutallab shi mutum ne Da baya wasa da Ciƙinsa, Mai son cin Abinci ne, shiyasa ma yakeson abinci mai Nauyi,kada abincin gargajiya yaji labari dan idan akayi tuwo agidan yaƙanjisa cikin Nishida, ya ƙuduri koyawa kansa yin rayuwa aduk yanda yazo masa saboda bayada wani zaɓi daya wuce masa hakan, ko da ya Nufi Gurin masu Saida Abinci, Duba abincin Nasu yayi yaga wanda ya kwanta masa sannan ya zaro Naira duba 1000 ya miƙa musu Ta hada masa Abincin plate daya hadin Naira 800 ya zauna ya soma ci, duk da baya yimasa daɗi haka ya dinga tutturashi har sai daya canye, kamin kuma yace abasa wani haɗin na 500 guda biyu aka saka masa a pack sannan ya nufi hanyar gida. Zaune suke gaba ɗayansu a palour ana kallo ana hira, Jidda kuma sai danne danne waya takeyi Umma na gefe da alama film ɗin da suke kallo ya ɗauki hanƙalinta inda Anty amarya ke faman hira ita da yaranta cike da habaici take cewa, "Ai ku ƴan gata ne Walid, don haka kusha kuriminku sai kun ƙetara ƙasashen waje kunyi bussiness kunyi karatu, dukiya ta ubanku dole ku wala". Maganar takeyi tana dallawa Umma harara da takaicinta ya cika mata ciki, a halin yanzu ta tsani Umma irin tsanar da ko idanu ta ɓuɗe bata son ta ganta agidan, kawai dai babu yadda zatayi da ita ne. Sallamar da Afrah tayi tashigo babban palour ne ya sakasu zuba mata idanuwa, daga nan suka sakamata dariya Umma na faɗin,  "ƴan Academy har andawo?" Sauran yaran ne suka dauƙa suna dariya suna faɗin kaga ƴan Academy suka kara kwashe mata da dariya, Don su Jidda sun riga ta dawowa saboda da ƙafa tadawo gida, Batare da sun amsa mata sallamar data yiba ta ƙara so  palourn tana kallon su Umma ta gaishesu cikin girmamawa duk da har lokacin basu denayi matadariya ba don har da Umma, Jidda ta kalli Afrah tana taɓe baki haɗe da cewa, "Afrah kin gani kuwa a wani firgice? Allah makarantar nan ta dace dake sosai". Suka sake kwashewa da dariya, cike da takaici Afrah da abun ya ɓata mata rai taja tsaki tana cewa, "To sai me Jidda? Menene idan nayi makaranta ƙasa da taku da kike wata dariya sai kace taɓaɓɓa, ita Abbana ke so nayi don haka banda damuwa akan haka, nagode Allah duk da bana zuwa makarantar da aka canza mani kowanne lokaci ina da ƙoƙari ke kuwa fa? Kin taba zuwa ta ɗaya ko ta biyu? Ke kike ɗaukar ta ƙarshe a aji don haka kanki ya kamata kiyiwa dariya ba ni ba". A hasale Jidda ta ajiye wayar hannunta tayo kan Afrah data nufi stairs ɗin abunta hankali kwance, tana zuwa ta janyota da ƙarfi da kaɗan ta faɗi tace, "Ni kike cewa haka? zagina kika yi?" Tashiga kokawa da ita ba tare data jira cewar Afrah ba, duba Afrah ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba yasa ƙarfi su bai zo ɗaya ba duk da yadda take ƙoƙarin ramawa, Umma dake zaune kuwa yi tayi kamar bata san me akeyi ba saboda tasan tsaf Jidda kecin zalin Afrah haka ba gaura ba dalili balle yanzu data haɗa su, wani ihu Afrah ta saki sabida hankaɗata da Jidda tayi akan ƙarfen benen tana faɗin "banza kawai an faɗa maki ni sa'arki ce, wariya data kasa gane Abba baya sonta da ita har yayun nata, waya sani ma ko ƴaƴan tsintuwa ne ku". Murmushi Umma ta saki saboda Jidda ta tabbatar mata da cewa ita ɗin jininta ce, don da batayi hakan ba ba abinda zai hanata cin ubanta yau yanda taji Afrah ta yayyaɓa mata magana, cikin jin daɗin ganin ƴarta tayi maganin Afrah tace, "Good Jidda, a haka kaɗai kika barta kin nuna mata ke yayarta ce, zo nan ki zauna abunki Allah yayi maki albarka". Duk da rashin son da Anty Amarya ke nunawa Afrah yau sai da yaki tausayinta. Yayin da Khalid da walid suka shiga dariya suna nuna Afrah da hannu haɗe da tafawa, ganin haka yasa Jidda jin tamkar suna zugata don haka ta nufo wajen da Afrah ke kwance ƙasa ta dafe goshi ta ɗaga ƙafa zata takata. "Karki soma wallahi kika kuskura kika takata sai na kikkifa miki mari, Stupid girl" Jalil dake shigowa yafada yana nufar Afrah da ɗan sauri sannan ya ɗagata yana share mata hawaye. "Ka marine? To akan me kasan me tayi Mani? Har ta isa ita ɗin banza..". Wani mugun kallo da Jalil yayi mata yasa ta maƙale sauran kalamanta abaki tana ja da baya, daman shi yafi kowa zafi agidan dan ma Mutallab yana taka masa burki, "Ashe ke ƙaramar ƴar iska ce, ai kece banza wacce ba tada hankali da zaki tak ƴar uwarki saboda sakarci, wato duk haƙurin mutum sai kun ƙureshi to me tayi mako ne?" "To uban ƴan rashin kunya, a gabanmu kake zageta har kana ƙoƙarin dukanta? Me kake nufi kenan". Umma da har jikinta ya soma rawa tafaɗa cikin ɓacin rai, ta jima tana son maganin wannan shegen yaron amma tarasa yanda zatayi dashi, ko kallonta beyi ba ya riƙa Afrah yana cewa, "Na tabbata kina ganin abunda take yiwa Afrah kika saka idanuwa bakice komai ba, wanda da jidda ce Afrah keyiwa hakan ai bazaki yimata shiru ba har sai kin shiga tsakani, amma dayake maiyiyarki ce kuna kallo tana wulakantata anrasa wacce zata tsawatar sai ma dariya da kuka tasa yaranku nayi mata?" Sanin halinsa na fitsara yasa Aunty Amarya da tana sane da gugar zanar daya yimata bata tankashi ba sai Umma ce tace "Taya zaka san an tsawatar masu ko ba'ayi ba kai daka shigo yanzu, wato kai fitsararre mai raba ɗaya biyu shine zaka nuna Afrah itace ƴar uwarki Jiddah kuma ba ƴar uwarki bace ko?" Kallonta yayi yace " Kuma kuka Nuna 'ƴayanku sune gaba akanmu tayaya bazan fifita kanwata da ake nuna mata bambanci ba yau idan mahaifiyarta Tana nan za'ayi mata haka ne gaban wani?" Sanin halinsa narashin tsoron kowa yasata yimasa banza tana huci, kallonsa daya maida ga Jiddah data sha jinin jikinta yana nunata da yatsa yace, "Narantse da Allah duk ranar dana ƙara ganin kin sake saka hannunki a jikin Afrah sai nayi miki shegen duka na ɓaɓɓallaki, ina Abbane taƙamarki ko, to wallahi babu abunda yayi mun zafi zaneki zanyi, ke kuma kika ƙara zama tana ta takaki haka baki rama ba sai na ƙarasa ɓalle wannan jikin naki, ƙarfi a zuciya yake ba'a jiki ba kinji na faɗa maki" yaƙare zancen yana maido hankalinsa ga Afrah sannan ya ja hannunta suka haura sama zuwa daƙinta, Anty Amarya ce tace "gaskiya Jiddah baki kyauta ba idan dake ake yiwa abunda ake wa Afrah a gidannan da tuni kunja Abba ya ɓatawa kowa rai, kin zauna kina rashin mutunci ana ɗaure miki gindi tsabar rashin son gaskiya ga uwar fitsara dake damunki ana mantawa zaki zauna karkashin wani wataran, sauran yayun naki me fitsarar ta tsinana musu? Naga daya ke cikin jindadi agidan mijin kowacce tana kwasar ayarta a hannu ai ba'a sharri wallahi a wanye lafiya". Umma da tama tana kule da take-taken Aunty Amarya kwana biyu tace, "To ƴar bani na iya wani ya tambayeki ne? To baki faɗi ƙarya ba kuma ko yanzu dukkanku zaku haɗu da Abba, ke Jidda shige mutafi za suyi bayani ne" tana hannun ƴar tata suka wuce bangarenta, Afrah kuwa suna shiga ɗakinta tacire hijab ɗinta tana kallon yadda Ya Jalil ke faman sauke ajiyar zuciya ɗaya bayan ɗaya, kamar zatayi kuka tace, "Kayi haƙuri ya Jalil bazan kuma ba bana son naga ranku yana ɓaci shiyasa bana son biye mata muyita faɗa". A hasale yayi kanta kamar zai daketa har yana ɗaga hannu yace, "Sai kuma akace ki zama sakarya a riƙa takaki any how har da ƴan uwan naki?". Afrah da tsoro yasa ta rufe idanuwa tana fashewa da kuka tace, "Am sorry ya Jalil bazan sake ba". cike da tsananin tausayinta ya janyota ya rungume, shi kansa yasan Jidda tafi ƙarfinta don irin kurayen yaran nan ce, ita kuma Afrah rashin lafiyar da take fama da ita tasa gaba ɗaya bata girma, amma ya zaiyi? Dole ya ƙarfafata kada zuciyarta ta mutu da tsoron Jidda, a hankali ya sauke ajiyar zuciya yana cewa, "Am Sorry too tsinkui ɗin ya Mutallab, but dole kisan yanda zaki dinga kwatar kanki idan bama kusa, ki koyi bawa kanki kariya koda ɗaya daga cikinmu baya kusa dake dan Allah Afrah, ba komai ake haƙuri ba dole kina buɗe baki kina mayar musu da martani ki daina shiru musamman idan Jidda ce kar kisa su Walid ma su zo suce zasu takaki". Kallon sa tayi tana goge hawayen dake kan fuskar Tata haɗe da cewa, "Zanyi hakan ya Jalil". tafaɗa ne kawai dan yaji daɗi ganin yanda ransa ya ɓaci, amma ita tasan tarbiyarsu ba zata barta yin hakan ba, shima dake yin hakan kawai saboda yana da saurin fushi ne da ɗaukar zafi saboda abinda ake yi masu, amma ta tabbata a waje bazai yi hakan ba tunda dukkansu tarbiya ɗaya aka ɗorasu akai shi ɗaya Mutallab kuma itama suka ɗorata akanta, shiyasa ko acikin gidan ma mahaifinsu da ƴan gidan anfi raga masa saboda yasha banban dasu wajen rashin iya sarrafa fushinsa da kuma ɓacin ransa, "Yauwa to zauna ki huta zanje yanzu naga Abba kafin yayi tafiyar nan dan wallahi sai ma ya biya mani kuɗin makarantar nan, sai na gani idan su waɗan can kaɗai ne ƴaƴan agidan nan" Yafada yana miƙewa haɗe da barin ɗakin, Ko da yasauka babu wanda yatarar a palourn hakan yabashi damar fita kai tsaye zuwa sashin mahaifin nasu da bai daɗe da dawowa ba, sallama yayi yashiga yatarar dashi Umma na gefensa da alama wani bayanin take masa. Bai ko kalli inda take ba yace, "Abba sannu da dawowa nazo ɗazu da safe ashe bakanan har ka fita". "Haka ne, Ina ɗan uwan naka ne tun safe ban ganshi ba, ko bai san yau zanyi tafiya ba da bai zo ya haɗamin jakar ba?" Sai da Jalil ya furzar da iska gefe cike da takaicin mahaifin nasu yana ganin meye amfanin matansa da bazasu iya shirya masa kayansa ba idan zaiyi tafiya sai ya jira Ya Mutallab!, Sai daya ɗan sha mit riƙa yace, "Ya tafi neman nakai Abba tunda aikin bai samu ba kuma ya rasa nauyi masa fatan sama masa". Umma da sam bata iya gani ta ƙyale ta mere baki tana cewa,"Wahalar da kai dai yaje yi, ta ina yake da ƙarfin iya samun taro da sisi, tunda aikin nan anyi nema bai samu ba sai ya haƙura da alama bashida rabon arziƙin da yake tunanin yaje ya samu." "Ba Amin ba Umma, ai indai yaya Jamil bai zai haƙura da zuwa kasuwa ba shi da baiyi ilimin ba to shima yaya mutallab bazai dena zuwa nema ba tunda yana da iliminsa akansa, kuma ya kamata idan mahaifi na zance da ƴaƴansu ki dena saka baki kuma ki koyi yin shiru tunda baza ki faɗi alkhairi ba".  Wata uwar tsawa Abba yayi daka masa haɗe da cewa, "Me kake so ne, naga jiya dai na baka dubu biyu Jalil?" "Biyar ne Abba ka manta kuma ina godiya amma yanzu ni Alfarma nazo nema akaro na babu adadi, yau ma ina sake neman wannan alfarmar dan Allah ka biyamin kuɗin registration ɗin nan kafin kawuce, naga dai har jikoki kana yiwa wannan alfarmar balle ni daka haifa da cikinka Abba, daga shekarar nan shikenan na kammala babu wasu kuɗi da zaka ƙara biya fa". Yaƙare zancen cike da don sokawa Umma magana don ranta ya ɓaci kuma cikin ruwan sanyi yayi nasarar yin hak, a ƙufule Abba ya kallesa yace, "Bazan biya ba Jalil". "Akan me Abba? Nifa ɗanka ne kuma naga  har ka biyawa Sadeek shi da yake jika duk da baya fahimtar komai ma kuma har ƙasar London, Abba wa'ec ɗin sama biya akai akayi masa". Umma na jin Jalil zna ƙoƙarin ɓaro mata aiki tayi saurin faɗin, "Haba Abbansu kabiya masa mana dan Allah, nasan bai ji amma ayi masa hakuri". "Naji, Jeka zan aika Jamil yaje yabiya maka gobe, yanzu kai ko kunya baka ji ba ka gama faɗa mata maganganu amma gashi ta saka baki tana roƙa maka alfarma tare da ban haƙuri a madadinka". Shi dai Jalil mere baki kawai yayi bai ce komai ba ya ɗago kai yama cewa, "Nagode Abba." Don Shi kansa yayi mamakin yadda Umma tasaka baki ko da yake ba abun mamaki bane

Chapter 8 of 54