Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
faɗo tare da sake fashewa da wani kukan tace, "Umma sakina Aliyu yayi ya kuma lakaɗamin dukan tsiya sannan ya koroni wai na barmasa gida kuma kada nazo masa da yara". "Buhun bu....uba dama waye zai karɓar masa yaran ko kin zo dasu tunda ba dasu kika je gidan ba". Umma tafaɗa tana haɗiye wani abu a zuciyarta kafin taci gaba da cewa, "Tirƙashi! Ni za'a yiwa wannan wulaƙancin saki da duka kuma akoro mani ƴa cikin dare? Ai wallahi sai ya gwammace uwarsa bata haifesa ba yi shiru ki share hawayenki kije daƙina ki kwanta ki huta zuwa safiya zamuyi magana". Taƙare zancen tare da miƙewa takoma ɗakin Abba, yayin da Jiddah tabi Aunty Asiya da harara tana faɗin, "Yanzu za'a zo duk a wani takura mutum, mtsssss". Taja tsaki  tana miƙewa ta wuce ɗakinta. ***********     Mutallab kuwa Zamansa kenan abangarensa yana faman lissafin kayan da suka sauka yau da yadda zai kasaftasu, Aryan ne ya shigo ɗakin nasa hankali a tashe yana faɗin, "MAM meenal fa babu lafiya tana asibiti an kwantar da ita, yanzu nake jin haka wajen ƙwarya matar Sadiq da yake naje gidan, pls dan Allah ka shiga lamarin yarinyar nan ka sota, soyayyarta ta gaskiyace MAM so nada zafi sosai nasan baka san hakan ba tunda baka taɓa yi ba, na rantse maka kafin Afrah ta furta mani kalmar so bayan na sanar da ita ba ƙaramar wahala nasha ba, na jigata fiye da tunaninka MAM kazo muje mu dubata kota samu sassauci a zuciyarta". Wani mugun kallo Mutallab yayi masa kamin yaɗauke kansa daga gareshi yaci gaba da lissafi da, kamar bazai yi magana ba can kuma sai yace, "Nagode Allah ɗaya sa bansan lokacin da kayi jinyar soyayyarka ba, da ace na sani da kaina zance ka haƙura da Afrah ɗin tunda ba ita kaɗai bace macce da zata wahalar mani dakai ba, sannan kadena irin wannan shirmen Aryan sam bai kamata ba ƙara kariƙa kama kanka and this will be the last da zaka sake yimani zancen yarinyar nan! Bana so Please and please kadena na gayamaka". Yana rufe baki yaji muryar Abba da Umma taje ta sake zugewa ya kasa haƙuri ya nufi ɗakin nasa na cewa, "Dama na sani yanzu tunda kaga kayi kuɗi ba mutunci kowa kake gani ba, kuɗinka kuɗin banza da wofi da har zaka nemi ka tozartani, wato kai marasa tarbiya da mutunci kaje har gidansu yarinya ka wulaƙantata saboda ban isa dakai ba Mutallab? To indai akan wannan arziƙin naka da faɗarsa kawai akeyi ni ban ganesa a ƙasa ba kake wannan iskancin tare da don nuna mani ni ba kowa bane a wajenka ka tattara kabarmin gidana kaje can da tsiyar arziƙin naka, nace kaje can da arziƙin naka da ba'a san tayaya kayi ba mutumin banza kawai". Yadda Abba ke faɗan cikin hargagi jikinsa har na wani ciccira yasa su Umma fitowa. Tun kafin ma taƙaraso cikin zuga take cewa, "Ai na gayamaka Alhaji wallahi yaron nan ba ɗan mutunci bane bai san girman mutane ba, kamar Alhaji Abdulmalik Mu'azzam zai ce zai bashi auren ƴarsa ya tsaya yana wannan iskancin, ai ko ba komai yasan amininka ne bai kamata yayi haka ba, kuma idan har baka ɗaukar masa mataki ba nan gaba sai yayi abinda yafi haka ko ma yace ai shi ya haifeka bakai ka haifeshi ba". Fizgo kai Mutallab yayi ya kalleta lokacin data ƙaraso wajen ta wani haɗe rai tana komawa gefe saboda wani irin kwarjini da yayi mata, amma duk da haka bata fasa cigaba da maganarta ba sai faɗa take, "Gaskiya ce baka so Mutallab kuma sai an faɗeta, wannan take-taken naka na nuna nan gaba ma dukan mahaifin naka zakayi dan ɗan wannan arziƙin naka na banza da wofi, waya sani ko abubuwan zamanin nan kashiga ɗan kaga kafi yayanka ɗauka, to wallahi Alhaji kada ka taɓa ƙyalesa aure ko yanaso ko bayaso dole yayi tunda haihuwarsa akayi, ɗan baƙinciki arziƙin da zamu dangwala yake baƙinciki dashi tunda mu bai ɗauke mu iyayensa ba, banda ma abun yarinyar nan ai ga Jamil nan meka fushi ne?" Sosai kalamanta suka harzuƙa Mutallab ya wani haɗe hannu cike da ɓaci rai Aryan yai saurin riƙo masa hannu yana faɗin, "Dan Allah MAM kayi haƙuri kayi haƙuri kar kace komai Please na roƙeka". A wani hasale Mutallab ya juyo fuskarsa tayi jajir idanuwansa sun wani sauya tamkar ba shiba yana kallon Aryan yace,  "If you touch me again Aryan wallahi sai na gwada maka negative side ɗina". Maganar Abba ce ta katsesa yana cewa, "Allow him Aryan! Barshi ya nuna mana shi ɗan kansa ne ba'a isa dashi ba, Look Mutallab bana magana biyu kafin kowa sani ɗan haka nabaka daga yau zuwa gobe kaje kabawa yarinyar nan haƙuri kuma ku daidaita ko kuma kabarmin gida". Cikin ɓacin ran da dukkansu basu taɓa ganinsa ciki ba daya jima da ziyartar ziciyarsa yace, "Bazan taɓa komawa wajenta ba kuma kamar yanda na faɗa maka bana sonta bazan kuma aurenta ba, i prepared to leave your house Abba akan na aureta nariga na faɗa bazan aureta ba bazan aurenta ba". Yaƙare maganar cikin ɗaya murya yana sake tabbatarwa da mahaifin nasa abinda ke ransa, ita kuma Umma a fusace ya juyo kanta yana cewa, "Ke kuma ina roƙon Allah yayi miki duk abunda kika yimun arayuwata daga ni har ƴan uwana, gurinki ya cika mahaifina ya sake korata gidansa akaro na biyu, zan tafi kamar yadda ya buƙata saboda bazan iya aurowa kaina irinki ba, In sha Allahu babu ni babu gidanga har abada sai ki zuba ruwa a ƙasa kisha, sannan kije ki aura mata Jamil in yakai namijin da zata iya aura, Finally idan har zaki iya kacireni a list ɗin ƴaƴansa alokacin ne zan san lallai bakya sona kuma da gaske kin tsaneni". Bai kai ga rufe baki ba Abba ya ɗaukesa mafi jikinsa na rawa yace, "Matar tawa zaka faɗawa haka? To kaje sai me? Idan har ita bata cireka a list ɗin ƴaƴana ba ni nacireka daga yau bana son sake ganinka kafita kabar mani gida, alhamdulillah ba kai kaɗai na haifa ba akwai Jamil zai iya bani duk wani farincikin da nake buƙata". Anty Amarya da tasan yanzu ne yakamata ace sun mori Mutallab ɗin bai kamata ace yayi nesa dasu ba ko don abun hannunsa da idan wataran basu ci ba wataran zasu iya ci tace, "Abba dan Allah kayi haƙuri bai kamata ka kori ɗan ka daya san ciwon kansa ba, shi wancan da kake zance idan ba hasara ba da neman magana wallahi ba abinda zai ɗauki maka". Tayi maganar dan ta baƙantawa Umma, ai kuwa kamar jira Abba keyi ya dawo kanta yana cewa, "Wallahi sai yabarmin gidana daga nan zuwa safiya matuƙar bazai bi umurnina ba". Mutallab dake dafe da kunci da idanuwansa cike tab da ƙwalla yace, "Shikenan Abba zan barmaka gidanka  In sha Allahu" yaƙare maganar cikin wani calmness voices dake nuni da ya karaya sosai tare da shigewa ɗakinsa dan yana jin maganar Abba ɗazu ya taso ya fito cikin ɗakin. Aryan da yaji dama bai zo gidan ba ya ɗari kai yana kallon Abba haɗe da cewa, "Abba kayi haƙuri dan Allah". "Kaje ka sauya aboki". Abban ya faɗa tare da juyawa yabar wajen, shima Aryan brin wajen yayi yakoma cikin ɗakin Mutallab, zai yi magana Mutallab ya ɗaya masa hannu alamun baison jin komai, hakan yasa Aryan ficewa yabar gidan gabaɗaya." Umma kuwa har lokacin bakinta baiyi shiru ba tabi bayan Abba tanaci gaba da faɗin, "yaro ya maidakai sa'arka dan yana ɗan iska mara mutunci ubansa na magana shima yanayi". Anty Amarya dake cike da ita tace, "Ke dai wallahi sai kin gamu da Allah kuma Jamil menene bayayiwa Alhaji naga har zaginsa ya taɓayi agidannan, shikuwa Mutullab kullum biye yake dashi sau da ƙafa har kice baida tarbiya, ai dai wallahi wutarki daban ta shiga tsakanin uba da ɗan da, makira kawai ina nan tafe kanki wallahi daga ke har Abba sai kunyi dana sani". Cikin ɓacin rai Abba yace "Au ni kike cewa haka amarya? Wai shin ina ruwanki acikin wannan maganar? To kema kitafi gidanku gobe". Wani bugawa ƙirjin Aunty Amarya yayi tashiga zare ido tana ƙara saita kanta ko badaidai taji ba. Dariya Umma ta fashe da ita haɗe da cewa, "Me nafaɗa maki yarinya? Wannan bugun lamba ne". Sannan tawuce abunta zuciyarta cike fal da farinciki a wannan daren, duk da data tuna dawowar Asiya gida sai taji wani abu ya taso ya tsaya mata a ƙahon zuciya... **************   "Dadyna zan mutu, zuciyata wani irin zafi takeyi Dady dan Allah ka aura mani Mutallab" Meenal dake kwance saman gadon asibiti na Aminity ward tafaɗa hawaye na sauko mata a fuska. Dady da shima hawayen yakeyi bayan gama wayarsa da Abba ya kalli ƴar tasa haɗe da cewa,    "Kiyi haƙuri Meenal ko dukiyata zata ƙare duka sai na tabbatar na aura maki yaron nan ko yana so ko baya so". Yafaɗa yana riƙo hannunta tare dasa ɗaya hannunsa yana shafa kanta, lumshe idanuwa tayi ta buɗe wasu hawayen suka sake zubowa kafin tace, "Dadyna kakiramun Mutallab kaji, Allah indai zai aureni zan daina duk abunda bayaso, Zan gyara halayensa da ɗabi'una duka zuwa yadda yake so su kasance". "Babyna ba wannan ce damuwar ba, dama yaron nan bai jin magana kina ganin yadda ya wulaƙantaki, me yafiki ne? Kyau, ilimi ko kuma dukiya? Idan kuɗi yake taƙama dasu daga shi har mahaifinsa nafisu su, ke dai ki kwantar da hankalinki har ki samu lafiya, idan har yasan wata ai bai san wata ba". "A'a Dadyna da gaskiyar Mommy, attitude ɗina su suka saka Mutallab tsanata, but i'm willing to change Dady". "Meenal.!" "No Dad..." Tafaɗa da karfi tana ƙwace hannunta tare da juya fuskarta gefe taci gaba da cewa, "Just go away from here Dady, kaje kawai ka kawomin Mommy ita zata fahimceni". Ganin yadda ƴar tasa tafita hankalinta gabaɗaya yaga kamar sabbatune ta koma tanayi yasa hawaye bin fuskarsa haɗe da cewa, "Meenal bansan wace kalar soyayya ce kike yiwa yaronnan ba, bansan ya kike ji ba a zuciyarki da nace dan Allah ki hakura dashi." Juyowa tayi tana kallon mahaifin nata haɗe da cewa, "Dadyna Mommy tafaɗa Mani cewa addu'a itace garkuwa kuma maganin kowace matsala, a maimakon wannan tunanin da kakeyi na nahaƙura dashi me zai hana kayimun Addu'a Allah yasa shima yasoni? kakira mani Mommy tazo takwana dani zan bata haƙurin duk abubuwan da nayi mata,  na tabbata ba dan zafin soyayyar da Mommy keyi maka ba da tuni abubuwan da nayi mata sun sa ta haƙura dakai". Shiru Dady yai yana kallonta, wai yau Meenal ce soyayya tasa tayi laushi haka take son ganin laifinta akan abubuwan da sam batada laifi aciki? Wannan wace iriyar soyayyace haka mai ban haushi da takaici?. **********    Yayi kuka sosai mai cike da maraicin uwa tamkar ƙaramin yaro, wani irin kewar Mahaifiyarsu yakeji tattare dashi, lokaci ɗaya maganganun da sukayi da ita na ƙarshe tana gab da rasuwa suka shiga dawo masa arai tare da yimasa amsa kuwa acikin ƙwaƙwalwa.     _'Mutallab ka kasance mai haƙuri kuma ka girmama mahaifinka, duk abinda zai saka kayi masa ko rinka baya so zakaga alkhairi acikinsa, ku saka aranki cewa komai zaiyi maku ba lallai ne yayisa acikin saninsa ba, ko bayan haka ma zai iyayin maku da sanin nasa saboda ya isa daku, kuyi duk abunda zai sakaku ko baku kuyi indai bai saɓa koyarwa musulunci ba sai kaga Albarka a rayuwarka, ba lallai nayi rayuwa mai tsaho daku ba, ɗan haka bayan natafi ku dinga kallon Abbanku amatsayi ko wane bangare guda biyu na rayuwarku, wato mahaifiya da kuma mahaifi wanda idan kuka ɓata masa Allah zaiyi fushi daku, kujurewa tsananin rayuwa kowane iri ne sannan kubishi da addu'a, in sha Allah albarkata na atare daku'_ Kukan nasa ne yayi ƙarfi sosai, a yanzu yana buƙatar inda zai shimfida fuskarsa yaji sanyi a rarrashesa akan wannan damuwar, sai dai ina yarasa hakan, cikin kuka yafara ambaton Allah yana cewa,     *'Allahu Allahu rabbi laa ushrik behi shai'a, hazbiyallahu laa ilaaha illa anta alaihi tawakkaltu wahuwal rabbul'arshil azheem'* "Innalilahi wainna illahirrajiun, me nayi kenan Abba yana faɗa ina fada?  Ammie na koyi haƙuri ba nida zaɓi da yawuce nayi hakan, bazan iya aurar wacce ƴaƴana bazasuyi alfahari da ita ba, bazan iya ba Ammie" a daren baiyi bacci ba sallah yariƙa yi yana kaiwa Allah jikansa kan tafiyar dashi a wannan damuwa kuma yayi masa zaɓi na alkhairi a rayuwarsa har aka kusa kiran sallar asuba sannan bacci ɓarawo ya kwashe shi, A cikin baccin yafara wani irin mafarki mai rikitarwa da kuma tsoratarwa na wata yarinya tanata gudu cikin daji tana miƙa masa hannu ya taimaketa, kuka takeyi tana kiran, 'Mutallab ka taimakeni..'  yana miƙa mata hannu zai riƙota a zabure ya tashi baccin yana shafa fuskarsa, daidai lokacin kuma aka fara kiraye-kirayen sallar asuba yamiƙe daƙyar bayan ya karanto addu'oi a bakinsa sannan yashiga bandaƙi ya kama ruwa haɗe da ɗauro alwala yawuce masallaci... #Mutallab Asad #Tagwaye Biyar #Billy S Fari #Nana Diso *MUTALLAB ASAD* *PAID BOOK #500* *TAGWAYE BIYAR.* NA *NANA DISO** & *BILLY S FARI* 33. Washe gari da wani sabon kukan Meenal ta tashi saboda sake kiran wayar Mutallab da tayi be ɗauka ba, hakan ya masifar ɗaga mata hankali ganin kalaman da yayi iƙirari na shirin tabbata, kafin kace wani irin zazzaɓi mai zafin gaske ya rufeta, dama Dadynta baya nan yayi tafiya Egypt sai jiya cikin dare misalin ƙarfe biyu jirgi su ya sauka ya tsaya a hotel ya kwana, wannan dalilin yasa washe gari safiya na wayewa ya nufo gida cike da ɗokin shalelen tasa da yayi ta mafarkai dan yayi kewarta ba kaɗan ba, yana shigowa gidan ita yafara nema Mommy na kitchen suna haɗa breakfast ita da mai aikinta ta fito tare da karɓar jikkar hannunsa tana yimasa sannu da zuwa, sama-sama ya amsa yana tambayarta Meenal ta sheda masa tana ɗakinta, kai tsaye saman ya nufa da sauri ya nufi ɗalibta haɗe da tura ƙofa yana kiran sunanta, cikin hanzari ya ƙarara bakin gadon gadon ganinta duƙunƙune cikin bargo jikinta na rawar sanyi, bargon ya fara yayewa yana faɗar, "Meenal lafiya?" Mommy da itama ta biyo bayansa bayan takai masa jikkarsa a ɗaki ta shiga salati ganin halin da Meenal ke ciki ba tare data sani ba, ɗari kai Dady yayi cikin ɓacin rai yace, "yanzu ƴar tawa kika bari cikin wannan yanayin Mansura inma mutuwa zatayi ta mutu? Wace irin ƙiyayyace kike yiwa yarinyar nan haka?" Ya ƙare zancen zuciyarsa babu daɗi yana tattaɓa fuskar Meenal da tayi suntum saboda kuka, kamar jira Meenal keyi taji muryar mahaifin nata ta wani ƙanƙame jikinsa tana sake saka wani kukan tamkar ranta zai fita. "Wai Menene akayiwa ƴata?" Dady yafaɗa cikin ruɗewa da kuma tashin hankali yana kallon Mommy da itama shi ɗin take kallo, ajiyar zuciya ta ɗan yi kafin tace, "Me za'a yimata Alhaji bayan kasan cewa nima yanzu na shigo ɗakin bansan meke faruwa ba? Ni dai a nawa tunanin akan yaron nan ne" "Wanne yaro kenan?" Kafin Mommy ta bashi amsa a hankali Meenal ta ɗago kai fuskarta shaɓe-shaɓe da hawaye tace, "Dady shine! Mutallab ne Dady yace baya sona baya ƙaunata wai nafi ƙarfinsa bazai iya aurena ba saboda bazai iya bani farinciki ba ko ya aureni, Ka taimakeni Dady dan Allah wlh ina sansa, zan iya rasa rayuwata saboda shi Dady wai ko ban haɗu bane? Dady ko banida quality ɗin da zai soni?" Wani irin takaici yasa Mommy kauda kanta gefe ba tare da tace komai ba har Dady ya sake kwantar da ita yana ƙoƙarin ciro wayar da ya kira likita jin yanda jikinta yai zafi sosai ta riƙe masa hannu tana sake fashewa da wani kukan sai ya tsaya yana lallashinta cikin nuna isa da gafara yace, "Ki kwantar da hankalinki Meenal tunda kina sonshi na rantse bai isa yace bazai aureki ba, duk girman kansa bai isa ace da tarin dukiyata da kuma arziƙina da mutuncina ba agarin nan nanemi abu narasa ba komenene kuwa matuƙar na nema zan sameshi, dan haka goge hawayenki bana don ganinsu Meenal hakan na taɓamin zuciya kinji Babyna ko? Kisa aranki maganar Aure  tsakanin ke dashi kamar ma anyi angama". Sake da baki Mommy ke kallonsa tana mamakin irin wuɗannan maganganun dake fitowa daga bakinsa kafin daga bisani tace, "Anya Dadyn..." kafin tsƙarasa ya dakatar da ita yana cewa, " 'Banason jin bakinki ko kaɗan". "Sabida ban isa ba ko kuma dan ita ɗin ba ƴata bace bani na haifeta ba ko? A gaskiya baka kyautawa a lamurran yarinyar nan ko kaɗan, ba tun yau ba nasha gayamaka wallahi wannan sangartar da kake nunawa Meenal da nuna mata duk abinda take so shi za'ayi zai kaina ga nadama wata rana saboda gidan wani zata je, kuma ba kowanne Namiji zai juri haka ba ko kuma ta burge shi da wannan rayuwar daka ɗorata, ka gode Allah anyi sa'a shi yaron da take don mai tarbiya ne da bai tsaya ya yaudareta ba yafito ya faɗa mata gaskiya, ke kuma Meenal idan har so kikeyi yaron nan ya soki to bata hanyar da mahaifinki ke ƙoƙarin bi ba zai sa ya soki, wuɗannan munanan ɗabi'un naki da kikeyi su zaki canza, idan ba haka ba wallahi duk tutiyar nan da mahaifinki keyi a banza ne dan bazai aureki ba kinji nagayamiki, ya rage naka Alhaji kaji tsoron Allah akan yaranka ko akasin hakan, last week na gama faɗa maka abunda Kamal yakeyi agidan nan yayi yawa ka rufeni da faɗa kai kenan baza'a gyarawa yaranka ba komai sukayi daidai sukayi, sai faɗin kakeyi kana sanso amma ka barsu babu islamiyya musamman ita, Meenal zata iya tsayawa ta zagi kowa taci masa mutunci babba da yaro idan an hukuntata kace abar maka gida babu wanda zai takurawa ƴarka, to shikenan gaka ga ƴar taka kuwa ka gwada ka gani ko don da kake yimata da abubuwanda kake taƙamar kana dasu zasu iya samamata wannan farincikin da take buƙata". Tana ƙare maganar yanar wajen cike da takaicin mijin nata, ada tayi alƙawarin saka mashi idanuwa shi da yaransa, sai dai sam bazata iya ba, matuƙar tana zaune dashi bataga amfanin tariƙa boye masa gaskiya ba har ranar nadama tazo masa ya koma yana kuka da ita, ƙara tariƙa faɗa masa ita komai ɗacinta, ta tabbata watarana zai zo ya gane metake faɗa masa ko kuma ya tuna cewa ta faɗa masa gaskiya, Sosai kalamanta suka sosa masa zuciyarsa dan wannan maganar tata wani abokinsa yataɓa gayamasa ita yace, "Indai har baka tsaya ka bawa ƴarka tarbiya ba ka rage sangartatan nan wallahi nan gaba dakai da ita duk sai kunyi kuka saboda ita ƴa macce tarbiya ake ɗorata akai saboda zuri'arta tazama tagari tunda ina wannan rayuwar ce ta rashin tarbiya ya rabaka da matarka ta farko ko nace mahaifiyarta, sannan me yasa kake son wannan matar taka ta yanzu? To tarbiyar da iyayenta suka bata ce tayi tasirin da yasa kake jinta a zuciyarka har kake jin bazaka iya rabuwa da ita ba kuma gashi sama da shekara ashirin kuna tare, dan haka yakamata ka tsayu akan ƴarka, ka iya banbance mata fari da baƙi daidai daba daidai ba". Ajiyar zuciya Dady yaja ya sauke bayan gama wannan dogon tunanin nasa tare daci gaba da rarrashin Meenal yana ganin shi babu wani abu na lalata mata tarbiya da yakeyi kawai sa idon mutanene da bazasu iya gani su ƙyale ba, daga ƙarshe ma sai cewa yai tatashi ta watsa ruwa suke asibiti dan har lokacin zazzaɓin bai dameta ba sai ma wani huci mai zafi da take fitarwa dake nuna zazzaɓin yayi mata zafi sosai. ***********     Umma ce da ayanzu take jin duniyarta zata fara haska mata tare dayi mata daɗi yanda take so zaune a gefen Abba suna fira cikin tsagwaron iya makirci, kissa da kuma kisisina tace, "yanzu Alhaji haka zaka zubawa yaron nan idanuwa duk samun nan da yakeyi bazai iya taimaka maka da komai acikin gidan nan saboda Allah?" Kallonta Abba yayi da niyar bata amsa akan cewa baida hurumi da arziƙin Mutallab tunda da guminsa ya tara abunsa amma suna haɗa idanuwa sai yaji kamar harshensa ya sarƙe, murmushi ya sakar mata haɗe da cewa, "To me kike tunani yakamata ace ya ɗauke mana a gidannan hajjaju?" Sai data juya idanuwa ganin tarkonta ya kama kurciya haɗe da cewa, "Alhaji yakamata yanzu ya ɗauke maka sayen kayan abincin gidannan gaba ɗaya, kuɗin makarantar yarannan suma ya dauƙe maka, saboda shiga yanzu bai san me zaiyi da kuɗin nan ba tunda ba iyalinsa dashi ba, tsabar almubazzaranci ma ɗazun maganar siyawa Afrah waya naji yanayi, kaga kuwa idan da kara sai ya canzawa Jiddah kuma muma yasiya mana ko kuwa?" "Haka ne kin kawo shawara, da Jiddah da Afrah ai ɗaya suke, sannan ku kuma iyayensa kuke ina har yasan girmana, dan haka zan masa magana Hajiya ai shiyasa nake sonki". Abba yafada yana gyara zamansa. Cikin jin daɗi tace, "Ai hakan shine daidai Alhaji, yanzu ya batun bawa Jamil jarin? Maganar gaskiya kai ma kasan ƙasƙanci da abun gorantawa ne ace yaronka yafi Jamil kuɗi, yakamata kayi haƙuri shima kaƙara masa jarin kar azo ana yada mana da magana a tsakar gid." "Waya isa yayi maki hakan". "Matarka mana". Wani dogon tsaki Abba ya ja yana ɓata rai haɗe da cewa, "Kidena wannan zancen, ita ɗin banza ai da kuwa ta haɗu da fushina, ina dai jari ne ko? To zan ƙara masa yau ɗin nan ba gobe ba, ko ba Shikenan ba?" Murmushi tayi ganin sabon aikinta yaci tare da miƙewa tace, "Godiya mai yawa baban Jamilu Allah yaƙara arziƙi, bari naje na hɗo maka ruwan team ɗin ka da hannuna yau". Saboda ta sake zubo masa wasu surƙullen aciki amma banda haka ai batayi sai dai yasa Afrah ta haɗa masa, da "To sai kindawo". Ya amsa mata yana jinsa wani iri tare da ɗan kishingiɗawa kafin tadawo. Aunty Amarya dake laɓe tana sauraron duk ƙullin da Umma keyi tayi saurin komawa ɗakinta tare da janyo wayarta ta kira mahaifiyarta ta fashe mata da kuka, "Ke lafiya? Kukan menene kikeyi haka? Ni fa bana son irin wannan kiran nasha gaya miki hakan? Ke kenan kina auren mai kuɗi amma kullum cikin kuka tare da tayar mani da hankali? Gaba ɗaya matsalarki tafi takowa acikin gidannan wannan wace irin rayuwa ce? Ina jinki me kuma akayi maki yanzu?" Cikin shesshekar kuka Aunty amarya tace, "Na shiga uku Hajiya wallahi matarnan taƙara cillo masa wani sabon asirin, jiya dana kwana daƙinsa ko son kallona bayayi sai aikin tsaki da yake ta jamin, zancen kuɗinnan ma da yayi alƙawarin yace bazai bayarba, ina masa maganar tafiya karatun walid da yace azaɓar masa ƙasar data dace shima yanzu yace yafasa wai baza ɓata kuɗin da a banza ba yayi asararsu akan yaron da ko secondry bai kammala ba, kuma fa yanzu na laɓe musu naji yana cewa zai sake bawa Jamil jari bayan manya-manyan kuɗinsa da suka sace suka je sukayi bushasha dasu". Taƙare zancen tana sake fashewa da wani kukan, "Innalillahi wa inna ilaihirrajiun, wallahi ban taɓa ganin fitinanniyar macce irin wannan kishiyar taki ba, wannan hatsabibiyar macece yanzu duk uwar wahalar da nasha tatafi abanza kenan! gaskiya hakan da sake amma goge hawayenki nayi miki alƙawarin wani watan zan sake shiga daji, wannan karon zanyi dogon nitso aciki ai ina tasan wata batasan wata ba". "Wayyo Allah na! Yanzu Hajiya har sai wani watan?" "To yakike so nayi? Kin halin Manata ba'a ganinsa sai farkon wata?." "Kai kai nidai nashiga uku Hajiya!" "Dena faɗar haka Allah yarabaki dashiga uku, in sha Allah wannan muguwar matar sai munyi maganinta daga ita har ɗan nata". "Allah yasa Hajiya". Aunty Amarya tafaɗa jiki a sanyaye tana kashe wayar. Abba kuwa yana gama shan baƙin shayin da Umma ta haɗa masa kansa na juyawa wayarsa ta hau ƙara, Umma dake gefensa ta ɗauka ta miƙa masa ya samu daƙyar ya iya ɗagawa yakai a kunne bakinsa ɗauke da sallama, ba tare da an amsa mashi ba yaji Muryar Alhaji Abdulmalik Mu'azzam cikin fushi yana cewa, "Nagode Alhaji Asad da abunda ɗanka yayiwa ƴata, ai da nazo wajenka na

Chapter 21 of 54