Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Amma Alhaji Mutallab Naji Ance kayi gini acan? Kai da ba zama kakeyi acan din ba?" Murmushi yayi yace " Tante inada halin yin haka ne idan Allah ya saka Nasamu wata iyalin acan ai ƙinga sai mufara zama."murmushi itama tayi tace " Ai sai nagani kamar hanƙalinka zai rabu biyu ne, tunda ga wancan bangaren sai ka hadesu anan ɗin." " Adai tayamu da Addu'a." " Anatayi kuma za'aci gaba." ******** Zaune take daƙin shirgi datake kwana faɗar bacin ran datake ciki bazai misaltu ba, bat taba ganin mutane masu ɗan banzan son zuciya ba kamar ahalin nan nata, yaronku yayi kokarin yimun fyade Amma kujani kuyimun ɗan banzan duka. Gefen hannunta takallah yadda ya kwarzane mata da batada baki da shikenan ya cuceta yagama da'ita har Abada. " Wai kukan ne har yanzu kwana nawa da magana ta mutu Aicha? Wallahi ko da wasa kika rayiwa ɗana sharri to kinajina sai na saɓamiki wallahi Allah yarinya sai kafirar karyar tsiya Wai bakya kallonki a mudubi ne? Har ke mukhtar zaiyiwa fyade yarasa wacce zaiyiwa sai ke kina fama da tsamin jiki da wari shigeyar yarinya butulu dangin uwarki ma sunki Daukanki Ni Na daukeki Amma kina mini Iskanci? Wallahi Nakarajin maganar nan Sai na koreki kin koma can gidan hajiyar da kuka tare kije can kiyi barikinki tunda ke bakisan halacci ba." Cikin kuka tace " Wai mama zanyi masa karyane yau kwana nawa baidawo gidan ba yanzu da yayimun ma shikenan ya cuceni." Buge mata baƙinta tayi tana faɗin " Kicigaba da jawomin magana dan ubanki ina magana kina jina bakya shiru munafuka kawai." Mikewa tayi ta fita daga gidan dan idan ta zauna to tabbas zuciyarta zata buga saboda wukancin datake fuskanta yanzu ma yaron maman yasace jarin shiyasa basa kosan basa abincin, tana fita kofar gidan tatarar da isah mai shaye dauke da jakar bakko kallonsa tayi tace " Yaya isa ƙaine." " Aicha Qu'est ce qui ne va pas avec toi (meke damunki?)" Kuka tafashe dashi sosai." Kallonta yayi cike da tausayinta yace " arrête de pleurer s'il te plaît ( ki taimaka ki bar kukan nan)." " Yaya isah daman haka maraici yake kowa son zuciyarsa yayi masa yawa da kaunar yaransa da kansa shikenan narasa iyayena zan kasance cikin baƙinciki da damuwa?" " Aicha kidaina jam'u kiyi hakuri Allah nasane dake ina miki Addu'a ubangiji Allah yanki miki wahala yabaki miji ya aureki." " To wai yaya isa wanene zai aure jahila saboda Allah dubeni ko almajiran garin nan sunfini gata." murmushi yayi haɗe da mika mata jakar Gashinan angama atamfa ce kala biyar sai mayafi kala biyu da lasi kala uku har abaya nasiyo miki ta gwanjo kuma suma guda 5 ne har takalmi da hijjabi danAllah karki kara saka wannan kayan ga canjinki nan dubu goma kyarike ahannunki." Kuka tafashe masa dashi tanafaɗin yaya isa wannan duka Yaya isa Allah yarabaka da duniyar nan lafiya bantaba ganin kamarka ba kuma bazan taba mantawa dakai ba." " banason godiya danAllah yanzu dai inking shiga sai kice mata dangin mamanki suka aiko miki dashi, kamin ma takarasa magana sai ga mama tana fadin wai Aicha jiranki zanyi kamin muci Abincin?" " Ganinan mama tafaɗa tana kin kimar jakar tashigar da'ita ciki, tsayawa mama tayi tana kallonta una kuma kika samo wannan? MUTALLAB ASAD   (labari mai taɓa zuciya) Na Billy s fari Nana diso      RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU.    TAFIYAR BIYU TAFI DAYA   SHAFI NA SABA'IN DA UKU. Cikin shiga wani irin yanayi akan ƙaryar da take ƙoƙarin yi da bata saba da ita ba tace, "Um Mama su baffa ne suka aiko mani dasu." Wani kallo Mama tayi mata kafin tace, "Bana son ƙarya Aïcha kifaɗa mani gaskiya kodai sherin da kike yiwa yarona ne kika je kikayi da wani ya siya maki?" "A'a wallahi Mama." Aïcha tafaɗa tana girgiza kai har idanuwanta na kawo ƙwalla, tsaki Mama tayi tana faɗin, "Ai indai kuka ne anan kikafi auki to ni bashi nake so ba ki kwashe kayan ki kai can a ɗakina kwayi amfani dasu keda sauran ƴan uwanki, ina dai kema tare nake maki abubuwa dasu kama daga kan ci da sha har zuwa abun wanki ko?" "Eh Mama." "To kwasa ki tafi can ki ajiye kifito kiyi abinda ke gabanki."ta amsa da to haɗe da ɗaukar kayan ta nufi dakin mama hawaye naci gaba da sauko mata.. ******** A ɓangaren Meenal kuwa Mutallab na fita ta ɗauki wayarta takira Mommy, gaisawa sukayi kafin tace, "Mommy Wai ya zancen mai aikin naji shiru?" "Meenal ai na faɗa mako cewa ni bazan samamaki ƴar aiki ba, duka duka auren naku kwana nawa da zaki nemi mai aiki? Idan wani abu ne ba ƙanwarsa Afrah na nan ba? Ki kirata ta tayaki mana." Turo baki Meenal tayi cike da jin haushi kafin tace, "Nifa bana shiri da yarinyar nan Mommy saboda Mutallab baida wata magana kullum-kullum sai ta Afrah komai dai ita, fisabilillahi sai kace ita ke aurensa." "Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, Meenal! Kina sane fa Ƴar uwarsa ce uwa ɗaya uba ɗaya, ta taso batasan kowa ba sama dasu shine uwa kuma uba agareta, idan har be ambaceta ba wa kike so ya ambata." Mommy tafaɗa cikin sallallami tana mamakin Meenal ɗin, dama mai hali baya barin halinsa sai dai idan arosa yai, faɗa ta shiga yimata sosai akan taraba kanta da shiga hurumin da ba nata ba ta tsaya matsayinta na matarsa ta ƙyalesa da ƴan uwansa ba ruwanta da lamarinsu idan ba an sakata ba aciki. Sam hakan bai yiwa Meenal daɗi ba dan haka rai aɓace suka gama wayar tana baƙin rai, tana ajiye wayar kiran umma ya shigo, hannu tasa ta sake ɗaukar wayar ta ɗaga takai a kunne tana cewa, "hello Umma." "Ƴar albarka kina lafiya?" "Lafiya kalau." Ta bata amsa tana gyara kwanciyarta a saman kujerar da take kwance, Umma tace, "ƴatah lafiya naji muryarki haka ko wani abun yayi maki?" "Ba komai Umma." "To Shikenan dama wata ƙawata ce tazo da irin yaran nan masu neman aiki shine nace bari nakiraki naji ko kina so amma najiki kamar cikin damuwa bari kawai nace tawuce". Ko rufe baki batayi ba Meenal ta miƙe zaune tana cewa, "A'a Umma akawo mani ina buƙata." "Anya Meenal kar fa azo Adamu matsala kifara tambayar mijinki." "Umma ni dai ina har kinga yarinyar tayi to kawai aturo mani ita please." "To Shikenan, Amma marece yayi yanzu mu bari sai zuwa gobe tunda safe sai Asiya ta kawota sannan dubu goma ne kuɗin aikinta duk wata." "Ba matsala Umma sai tazo nagode sosai". Meenal tafaɗa cike da jin daɗi tare da jin soyayyar Umma a ranta tana ganin tamafi Mommy sonta don dama tun can farko ba wani sonta Mommyn keyi ba, a ɓangaren Umma kuwa dallawa wayar harara tayi bayan sun gama tana cewa, "zaki gane kurenki ne daga lokacin da nayi nasarar shigowar yarinyar nan cikin gidan daga ke har wuɗandake cikinsa." Har ƙarfe biyar da rabi tayi Meenal na nan inda take kwance bata tashi ba sai da taga ƙarfe shida ta marece takusa sannan tamiƙe ta shiga kitchen ta shiga haɗa kayayyakin da take buƙata na tuwo tana yi tana duba wayarta da tayi Googling, tukunya ta ɗauko ba wankewa ba komai ta bude dangi ta zuba ruwa sannan ta kunna gas ta ɗora akai. _Bayan mintuna Arba'in_ Tsaye take agaban gas ɗin da take ta ƙoƙarin gama haɗa abincin da take ganin yinsa tamkar ɗora mata aradu ne acikin gidan sai faman haɗa zufa takeyi a goshi, hannunta dake buɗun-buɗun da garin fulawar da taketa kokarin haɗewa acikin tukunyar da take tuƙa tuwon shinkafar aciki ta ɗago tana goge zufan dake kan goshinta, a daidai lokacin ƙamshin turarensa da tunkafin yaƙaraso kitchen ɗin ya gama mamaye mata hanci tare da alamta mata isowarshi wajen, juyowa tayi da sauri tana washe masa haƙora tana tunanin yau dai tayi abinda zai faranta masa rai, cikin rashin tauna kalaman da zata faɗa masa take cewa, "I have try today, saboda haka no more complain ɗin daka saba yimani kullum ko gajiya baka yi". sai daya naɗe hannayensa akan ƙirji yai crossing ƙafafuwansa yana jingina ajikin ƙofar kitchen ɗin sannan a hankali ya ɗago idanuwansa ya zuba mata yana kallonta tun daga ƙafarta da tayi budu budu da garin fulawa har zuwa fuskarta data ɓaci itama, idanuwansa ya sauke ga rigar daķe jiķinta yana kallon yadda shinkafar tuwon ta ɓata mata ita gaba ɗaya tare da lumshe idanuwansa cike da takaici yana jin tamkar yarufeta da duka, can ƙasan maƙoshi ya furta, "Yaa Allah!" Sannan ya sake ɗari kai yana kallonta, ajiyar zuciya ya sauke yana girgiza kai ba tare daya iya cewa ƙanzil ba ya juya da zimmar fita daga sashen nata. turo baki tayi da sauri tasha gabansa kamar zatayi kuka tace, "kana ganin fa wahalar dana sha saboda kai, wlh Mutallab ba don kai bane ba wanda ya isa ya sani shiga kitchen kuma wai har nayi masa tuwo saboda ni ba iyawa nayi ba, ban saba irin wannan wahalar girke-girken ba agidanmu kuma na gayamaka hakan amma baka yarda ba, yanzu please dan Allah muje ka tayani naƙarasa, Allah tuwon da wahala tun ɗazu nakeyi amma yaƙi tukuwa waje ɗaya sai ma wani ruwa ruwa da yayi mani." Ba tare data damu da irin kallon da yake yimata ba taci gaba da cewa, "kaga fa har fulawa na dama na zuba aciki ko zai haɗe amma yaƙi ya koma kamar wani  fate-fate, ni nagaji gaskiya dan wallahi har Googling na shiga nayi amma duka nakasa!" taƙare zancen cikin shagwaɓa tana wani turo baki, Cikin sanyin muryar data surku da ɓacin ran daya fara bayyana ƙarara a fuskarsa yace, "Ya akayi baki gyara mani ɗaki na ba?" "Ni fa wlh matsalata dakai kenan Mutallab, ana wannan aikin ba'a gama ba kake ɗauko wani! To ni na gayamaka agidanmu ma gyaramin ɗaki na akeyi ko bedsheet ma su suke shimfiɗamun akan gadona balle ayi zancen wani wankin ɓanɗaki, gaskiya bazan ma ƙarya ba nafaɗa maka ni bazan iya duka wuɗan nan aikace-aikacen ba. "Ok to Shikenan, tunda bazaki iya ba ya kike so ayi?" "A nemo ƴar aiki mana Askim." "Ba dani ba a wannan zancen bazan taɓa ɗaukar wata mace tayi mani aiki ba agida bayan ina da mata, sai dai in ke zaki nema kuma bada sisina ba aciki sannan hakan bazai ɗauke maki hakkin dafa mani nawa abincin da gyara Mani muhalli a ba da kanki, idan ba haka ba to zan kawo wacce  zata iya yimani wuɗannan abubuwan da kanta." Cikin ɓaci ran da Meenal bata san lokacin daya taso mata ba haɗe da kishi tace, "Bazai yiyu ba wallahi, wai kai wane irin mutum ne Mutallab da ba'a yimaka dai-dai, nifa na aurena ne saboda na samu soyayyarka da farinciki acikin gidanka ba don na bautu ba da aikace-aikacen da za'a iya saka wani yayi, to akan me zaka takurani." Banza yayi mata ya nufi sashen su tánte ba tare daya sake tankata ba, cikin ƙaraji da ɗaya murya tace, "Na rantse karya kake Mutallab baka isa ka kawo wata mace a gidan nan ba bayan ni, idan ma mafarki kakeyi kadena." Yana jin yadda take suruttanta har ya isa sashen su tánte Sajida, gaisheta yai suka ɗan taɓa fira ɗan Afrah bata nan ta tafi gidansu ilham ƙawarta kafin tamiƙe ta shiga kitchen ta ɗauko masa abinci ta ajiye masa agabansa tana cewa, "da gani akwai yunwa da kuma gajiya tattare dakai Mutallab, ka samu kaci abinci sai ka shiga ka huta." Ya amsa mata da  "toh." Yana bude warmer din data ajiye masa agabansa, best food ɗinsa ne wato tuwo ta taso ta zuba masa da kanta sannan takoma ta zauna bayan ta ajiye masa lemu da ruwa suka ci gaba da firar yanayi yana cin abincin. Bayan ya kammala yamiƙe yai mata sallama ya wuce ɗakinsa yana cemata  su shirya kayansu yana ganin banda gobe zasu wuce dan Mahmoud ya kirasa ya faɗa masa an kammala ginin shagunansa an saka komai shi kadai ake jira ya iso a buɗesu dan su fara aiki ta amsa mashi da "toh Allah yakai mu". A ɓangaren Meenal kuwa tana cikin masifar Sarsy da Nancy suka shigo, mantawa tayi da ɓacin ran da take ciki ta saki wani irin ihu tanufo wajensu da gudu cike da jin daɗin ganinsu Dan tunranar da aka kawota basu koma dawowa ba, kowacen su gefe tayi taƙi bari ta rungumeta ganin yanayin da take ciki suna yimata wani irin kallo kafin kuma su kalli juna su kwashe mata da dariya suna tafewa haɗe da cewa, "Su matan aure manya! Mrs Mutallab Asad Mutallab wai kece a haka?" Suka faɗa suna kama baki alamun mamaki, harara ta maka masu tana cewa, "Kufa ƴan wulaƙanci ne wallahi, ya zanzo da sauri na cike da farinciki saboda nayi missing ɗinku ku aza mani dariya? To meye girki da nakeyi." "Su girki manya". Nancy tafaɗa tana sake kwashewa da dariya, tsaki Meenal tayi haɗe da juyawa takoma ciki tana cewa, "ku dai kuka sani ku wucikke ciki idan kun tashi gulmammi kawai". Taɓa baki sukayi suna sake kallon junansu kafin sukabi bayanta. Kitchen ta nufa da sauri Sarsy ta bita baya ta riko hannunta tana cewa, "ƙawata wai kin ganki kuwa? Kina nufin duk girkin ne haka kika ɓata tun daga kan fuskarki har zuwa ƙafafuwanki da Garin fulawa? Ko dai abun aka cimmaki a kitchen akayi tsabar jindadi kikayi wanka da garin fulawar!" Duka ta naɗa mata a kafaɗa haɗe da cewa, "bana son iskanci Sarsy, tuwo ne fa da Askim yace nayi masa na ɗora masa". Tukunyar Sarsy ta buɗe tana mamakin yaushe Meenal ta iya girki ita dako ruwan team bata taɓa ganin ta ɗora da sunan dadawa ba agidansu, gudajin shinkafar data haɗe gefe da ruwan fulawar daya game sai kace kunu da Sarsy ta gani ya sata buga sallallami kafin daga bisani data sake leƙa tukunyar ta kwashe da dariya, Nancy ce ta biyo bayansu haɗe da cewa, "Wai wace wainar ce kuke toyawa naji ana dariya haka?" "Ba dai waina ba ƙawata sai dai ko tuwon shinkafar fulawar kunu, kuma mrs Mutallab matar aure ke toya abunta ita kaɗai ba dani ba". Ai nan suka tasa Meenal agaba suna kwasar dariya kafin daga bisani su fito fili su faɗa mata gaskiya cewa sam abinda ya dafa bazai ciwu ba balle har asan a cikin wane kalar nau'in abinci yake, ba tare data damu ba ta kallesu tace, "Nancy kunfi kowa sanin Wallahi ban iya girki ba, ya matsa mani ne wallahi shiyasa nayi Googling a waya nace bari nagwada yi". Ajiyar zuciya Sarsy ta sauke haɗe da kallonta tace, "Meenal ai kinyi ragon azanci, tun farko mai aiki yakamata ace kin ɗauka kafin akai ga haka, sannan ko ni ko Nancy duk wanda kika kira kika ce yai maku oder zamu iya yimaki basai kinzo kin tabka abun kunya haka ba, ko ba haka ba Nancy." "Sosai ma kuwa, mintuna nawa ne ga restaurant nan ko ina kowane kalar abinci kike so zaki iya samu, kuma mijinki bazai taɓa gane cewa bake kika yiba." "Hmmm bakusan halin Mutallab bane, shida alallai ko mai aiki baya so na ɗauka balle har ya amince nayi masa odar abinci daga waje." "To waya faɗa maki zaki bari yasan oda kikayo?" Nan suka zauna suka tsara mata yadda zata riƙayi tare da sake ɗorata a tsohuwar turbar da suke akai  tun can ganin yadda cikin kwana biyu da auren nata ta sauya kamar ba Meenal ɗinsu da suka sani ba saboda rashin wanda zaiyi tsaye yai mata faɗa ta gyara kanta kamar yadda Mommy keyi mata lokacin da tana gida, a hakan ma basu sani ba Mutallab na kwaɓarta da yanayin da zasu iskota aciki sai yafi haka.. #Mutallab Asad #Yan Tagwaye #Nana Diso #Billy s Fari MUTALLAB ASAD   (labari mai taɓa zuciya) Na Billy s fari Nana diso      RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU.    TAFIYAR BIYU TAFI DAYA   SHAFI NA SABA'IN DA HUƊU. Nan take suka zauna suka mata list na gashin attachment da take sakawa ada da ƙumba da kayan ciko na hips da breast da zata siya ta dawo asalin ƴar gayu kamar da tare da ɗora nasu kuɗin akai, take Meenal ta cake masu kuɗin sannan sukayi sallama saboda dare nayi azuwan jibi zasu dawo da wacce zata sakamata attached ɗin da ƙumba da sauransu a gyarata, girki kuwa sunkai ƙarshe akan komai Mutallab zaiyi kada ta sake tafasa ɗaukar ƴar aikin da Umma zata kawo mata, a ɓangaren faɗan da sukayi da Mutallab ɗin dan takwashe komai ta sanar dasu shawara suka bata akan ta lallaɓashi su shirya ta samu ta ɗibarwa Umma sperm din takai mata dan hakanne zai hanasa yunƙurin ƙara auren da yakeyi bayan bata mori komai ba acikin amarcin nata tunda suma suna so suriƙa zuwa suna dangwalar arziki sannan suka taimaka mata sukayi ta gyara ko ina suka wuce. Mutallab kuwa bai koma bi takan Meenal ba yai kwanciyarsa yana faman sakawa da warwarewa na ɗabiun nata dake cimasa tuwo a ƙwarya har bacci ya ɗaukesa, washe gari ma baibi takanta ba ya shirya abunsa ya wuce shago duk da ɓacin ran dake zuciyarsa na ganin sabuwar mai aikin data kawo yayi mata kamar bai gani ba, da daddare bayan ya dawo yayi shirin kwanciya ya kirata a waya yace ta sameshi a ɗaukinsa lokacin har ta kwanta bacci ya soma ɗaukar ta dan shikam ya ɗauki alwashin bazai koma zuwa ɗalibta da sunan biyan buƙata ba, sanin sun dauki kwana biyu suna ƴar tsana ya sata miƙewa tana sakin tsaki tare da cire doguwar rigar atamfar dake jikinta tun rana data kwanta da ita ta saka ta bacci ba tare da tayi tunanin ko wanka batayi ba balle akai ga saka turare da sauransu ba, yana latsar wayarsa ta turo ƙofa ta shigo tana cin magani ita ala tilas ya takurata tunda ya tasheta bayan tafara bacci, kawai ba yadda zatayi ne tunda tana son kwasar sperm ɗinsa da ba abinda zata zo tayi masa, ko kallonsa batayi ba ta zagaya ta ɗaya gefen gadon taja pillow tayi kwanciyarta, juyowa yai ya kalleta haɗe da cewa, "Meye haka Meenal? Ba kiranki nayi ba amma shine kika shigo mun haka?" "Nafara bacci ne shiyasa, menene?" Shiru yai jin kalmomin daka fitowa daga bakinta haɗe da girgiza kai ya ajiye wayarsa a saman bedside sannan ya kashe bed lamp ɗin dake gefe ya gyara kwanciyarsa haɗe da janyota zuwa jikinsa yana shasshafata, cikin tsananin buƙata yake ba dan haka ba irin tashin tsamin da yaji jikinta nayi sam bazai iya kusantarta ba, amma ya zai yi? Jarabawarta kenan a gonar da ubangijinsa ya halasta mashi yin shuka a yanzu. Ita kuwa haushinsa da take ji yau bai barta ta nuna koda irin ɗan emotions ɗin dake fizgarta ba tayi kwancenta ƙememe, haka yayi kuɗi da shi kaɗai yayi rawarsa ya gama, da yake bacci ne a idonta suna gamawa ta juya tayi kwanciyarta ta manta da batun sperm da take son ɗiba, babu yadda baiyi da ita ba ta tashi su tsarkake jikinsu amma taƙi, dole ya ya ƙyaleta shi ya shiga yayo wankan sannan yafito ya janyo system dinsa ya soma tura saƙonnin da yake son haɗawa a duka branch na  kamfanonansa da yake aiki kafin lokacin tafiyarsu gobe yayi dan tuni su tánte sun gama shirya kayansu tsaf. Washe gari ma haka yayi ta tashinta da asuba tayi wanka amma yaƙi sai kusan ƙarfe bakwai yana ƙoƙarin shiga toilet lokacin yai wanka sannan ta tashi haɗe da maida rigar baccinta ta nufi ƙofa, bata ƙarasa ba cikin wata husky voice ɗinta dake tattare da ɓaci rai taji yace, "Step ɗaya kikayi ba tare da kin gyara ɗakin nan ba kafin nafito sai ranki ya ɓaci." Yana gama faɗar haka ya shige toilet ransa na yimasa wani irin sululi da ƙuna. Harara ta maka masa tana turo baki haɗe da bubbuga ƙafafuwa kafin taƙaraso gaban gadon ta shiga watso pillows ƙasa da bedsheet ɗin, Kugunsa ɗaure da towel yafito toilet ɗin hannunsa na riƙe da wani ƙaramin towel ya tsaya a gaban madubi yana goge sumar kansa, kusan mintina goma ya ɗauka yana gyarata tare da kallonta ta cikin madubi sai faman haɗa zufa takeyi tana ƙoƙarin gyara makeken gadon dake tsakiyar ɗaki, wanda ta shafe tsawon mintina goma tana wannan aikin amma har yanzu gadon ya kasa daidaita yadda ya kamata balle ya samu kyakkyawan gyaran da zai ɗauki idanuwan wanda ya bata umurnin aikata hakan. Closest ɗin kayansa ya buɗe bayan ya gama shafa mayukkan dake kan madubin da yake amfani dasu ya ciro kayan da zai saka, farar shadda ce ƙal ya fiddo mai gajeren hannu iya guiwa ya saka ya ɗau turarukka masu ƙamashi ya feshe jikinsa dasu sannan ya kafa hula ƙube da zata shiga da kayan sosai ta zauna daram akansa, kasancewarsa ɗaya daga cikin fararen mutane sosai dake da kyakkyawar fuska haɗi da daradaran idanuwa masu haske da kuma dogon hanci yasa atake yayi ɗas dashi, ɗago kai tayi ta zubawa bakinsa dake zane akan fuskar tasa da sajen daya zagayeta tana son yimasa magana kamar zatayi kuka amma sai yayi mata wani irin kwarjini, hakan yasa ta maida hankalinta ga abinda takeyi tana turo baki, duk da irin rashin jin daɗin yanayin zaman da sukeyi da ita ƴar ƙibar amarcin da yai bata ɓuya ba sai data bayyana ta hanyar shigewa cikin ɗan tsayin da yake dashi tasa jikinsa murjewa haiba da kuma zatinsa suka bayyana, kallon kansa ya sakeyi a madubi yana shafa sajensa kafinya haɗe fuska tare da juyowa ya zuba mata idanuwa yana kallonta bayan ya jingina ajikin madubin yana crossing ƙafarsa ɗaya akan ɗaya. Sosai ta gaji da gyaran gadon idan ta gyara gefe sai ɗaya gefen ya janye idan ta gyara shi sai kuma ɗaya gefen ya sake buɗewa, sanin ita yake kallo yasa ta miƙe tana dafe kugunta kamar zata yi kuka tana kallonsa, a hankali ya tako zuwa gareta yana sake ɗaure fuska tare da riƙo fuskarta yana kallonta, hawayen da take ɓoyewa na gajiyar da tayi ne suka zubo mata a fuska, har ga Allah yana don Meenal tun ranar farko daya fara ganinta amma munanan halayenta suka sanya ya tsaneta, sai gashi akaro na biyu bayan ta yaudaresa da canza ɗabiunta da suka sashi tsanarta ta sake bijiro masa da wasu ɗabiun da bayada zaɓi ɗaya wuce yayi ƙoƙarin nuna mata kuskure ta takowace fuska duk da yadda yake jin soyayyarta a zuciyarsa har yanzu, wanda hakan ne ma yasa yanzu yake jin zafin yadda hawaye ke zubowa a fuskarta suna ƙona masa zuciya, cikin nuna mata rashin damuwa da hawayen nata yace, "ki tabbata kafin na dawo kin gyara ko ina acikin gidannan, bana buƙatar komai daga mai aiki kama daga gyaran ɗakina da toilet, naki ɗakin da kuma cikin gidana gaba ɗaya, bazan jima a shago ba zan dawo ƙarfe biyu, zuwa lokacin ina fatar na samu abincina akan dining kin kammala, karki manta bana buƙatar girkin mai aiki". Yana kaiwa nan yayi mata kiss a kunci tare da sakin fuskar tata ya ɗauki wayoyinsa dake ajiye a saman side drower ya nufi ƙofa. "Ya Mutallab.." ta faɗa cikin raunin murya tare da saurin rufe baki ba tare data ƙarasa abinda take son faɗa ba ganin yanda ya juyo, yatsansa ne akan laɓɓansa alamun yimata gargaɗi akan tayi shiru kada ta sake yin wata magana baya son ji yana kafeta da idanuwansa, Wanda tsananin kaifinsu da kuma tasirin da suke yi mata a zuciya idan tana kallonsa ya sata sadda kanta ƙasa bayan ta haɗiyi wasu yawu da ƙarfi dan gaba ɗaya yau ya rikiɗe mata tamkar ba shi ba. Murmushi ya ɗan saki ganin yadda tayi sannan ya juya ya fice daga ɗakin ita kuma ta zube akan guiwowinta ta fashe da kuka, wai dama haka gidan aure yake cike da ƙunci, baƙin ciki da kuma takurawa, ita fa hutu da soyayya tazo tayi acikin gidanta gidan mijinta kuma masoyinta ba bauta ba, taya zata zo kuma Mutallab ya nemi ya takura mata fisabilillahi? ta faɗa cikin zuciyarta tana jin

Chapter 42 of 54