Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sannan kema kiriƙe mutuncinki kiji tsoron Allah Sarsy kafin ranar nadama tazo maki, ace kina macce amma ke kike neman namiji ya keta maki haddi? Akan me Sarsy bayan wannan abun shine darajarki da kuma kimarki? Idan aure kike so yakamata kisanar da iyayenki kidena wannan ɗabiar don Allah Sarsy". Ajiyar zuciya Sarsy ta sauke tare da kallonsa tace, "Ban taɓa tunanin kana da ilimin addini da tsoron Allah haka ba Kamal, ka godewa Allah wallahi amma ni bazan iya aure yanzu ba maganar gaskiya, ban dai hana ko nan gaba ba". #Mutallab Asad #Ƴan Tagwaye #Nana Diso #Billy S Fari MUTALLAB ASAD MUTALLAB      (labari mai taɓa zuciya) Na Billy s fari Nana diso      RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU.    TAFIYAR BIYU TAFI DAYA   SHAFI NA ARBA'IN DA HUƊU. Yadda ta dire maganar cike da tsiwa yasa mà père sake ɗauke ta da sabon marin da yasata yin gum tana shashekar kuka, "Ya isa haka kubarta". cewar mà père, "karku lahantamin ita nazo na rasa ta ina zan fara zuwa bara, ku ƙyaleta ai ko yanzu taji ajikinta idan Alhaji yakara zuwa nasan zata bishi ai". Mà mèrè tace, "Kadama taje ɗin, shashasha maza tashi ki share gidan nan ki wanke kwanukan can tunda haka kike so, ga kayan mu nan na jiki idan kin gana sai kiyi wanki, ai jiki magayi da kaifin ƙafafuwanki zaki je kiyi yanda muke so ko kin dinga bautuwa kenan acikin gidan nan dan ita kaɗai ce hanyar da zamu moreki tunda kinƙi waccan ɗin". Sai da taci kukanta sosai kamin ta miƙe ta nufi inda suke ɗebo ruwa, robobin gidan tafara cikawa taf sannan tayi wanke wanken ta gama, wani sandararren tuwon da akayi tun safe tunda dama abinci sau ɗaya akeyi da mà mèrè ta bata ta zauna tana ci, tana gamawa tayi arwala tayi sallolin dake kanta da bata samu tayi ba saboda takurar mà mèrè data tsare ta kasa sai tagama mata aikinta, kasancewar har dare yayi ta kunna aci bal bal ta hau wanke masu kayan ta shanya sannan take tayi sallar isha da shafa'i da wuturi ta kwanta, kwanciyarta ke da wuya bacci ya kwashe ta. Washe gari Mà mèrè dake zaune da mà père suna fira tace, "Nifa da zaka bi ta shawarata idan Alhajin yazo kawai kace yabada sadakinsa ka bashi aurenta". "Ai kinsan halin yarinyar tamu ko? Dole abi komai a sannu yanzu tunda tasan ranki yaɓaci kuma batason ɓacin ranki, nasan yau zata saki jikinta tayi shiga mai kyau idan zamu fita". "To ai shikenan sai kayita biye mata tana ɓata mana rai, nawa ce Aïcha ina ko shekara ashirin bata haɗa ba? Allah sai na kakkaryata idan tace bazata bi abinda muke so ba". "Mudai bita a hankali" yafaɗa yana lalubo sandarsa, dai-dai lokacin Aïcha tafito sanye da doguwar riga over size don tayi mata faɗi sosai, mà père na ganinta ta zaro idanuwa tana rafka samari tare da tafa hannuwa kafin tamiƙe tayo kanta, hannunta tana rai aɓace suka shige ɗakin kwananta ita da yayarta ta janyo buhun kayanta ta shiga zazzagesu, wasu riga da sket data taɓa ɗunka mata bukin yayar Amini mà mèrè taciro tamiƙa mata tana cewa, "ungo ki saka wannan yanzu kicere wannan shegiyar rigar kafin narufeki da duka". Turo baki Aïcha tai zatayi magana mà mèrè ta buge mata bakin ta hau yin masifa da ita, dole Aïcha na kuka ba dan tana so ba takarɓi kayan ta saka, duk da ba wani haskene dasu ba amma kasancewar sunyi zaune ɗas ajikinta sai sukayi mata kyau, murmushi mà mèrè tayi cikin yarensu take cewa, "macha Allah, Aïcha kinga kyan da kikayi? Shige muje mahaifinki na jira kuwuce, kuma ɗan kwalinki kaɗai zaki aza ga kai kada ki sake ki saka mayafi ko hijabi". Tayi gaba Aïcha ta bita a baya, suna kaiwa bakin ƙofa da sauri Aïcha ta dawo ta ɗauki Hijab ɗinta tayi maza takaishi bayan kyauren ƙofar gida ta ɓoye sannan ta dawo wajen mà père fuskarta a ɗan sake dan talura idan bata nunawa mà mèrè ɗin tata zatayi yanda take so ba tsaf zata sake jibgarta kafin su fita, da haka ta riƙowa mà père sandarsa tana gaishesheshi sannan suka wuce ma mèrè nayi masu addu'a Allah ya bada Sa'ar bara. ******* Yau tunda ya tashi zirga zirgar zumunci sukayi, hakan yasa suna dawowa bayan sallar la'asar ya samu ya ɗan yi wanka, ganin wayarsa na haske ɗan silent take yasashi saurin miƙa hannu ya ɗauko yana kallon screen ɗin wayar, Jalil ne ke kiransa ya ɗauka haɗe dayin sallama, bayan sun gaisa yake tambayarsa kasuwa da Tànte yace masa duk lafiya kalau suke, "Ya naji maganarka tayi low Jalil lafiya kake kuwa?" "Yaya kwana biyu haka nake jin jikinsa ba daɗi, na samu naje asibiti  amma dai har yanzu weak nake jin jikin nawa musamman dai yau". "Subhanallahi to kayita Addu'a dan Allah Jalil kada ka bari wayar nan da muke fama da ita yanzu dake canye lokuttanmu ta hanaka azkar, in Sha Allah Afrah ma zata dawo zuwa gobe saboda makarantar ta". "Nima daman tunanin da nakeyi kenan makarantarta kada tasamu matsala". "No wannan ai duk ba wata damuwa bace ba". Mutallab ya bashi amsa kafin sukayi sallama, har zai ake wayar su kuma yaga ta sake yin haske alamun an sake kiransa ya ɗauka ya kara akunnensa bakinsa ɗauke da sallama. "Alhaji Mutallab barka da yamma". Yaji mahaifin su Umar da Umar ya haɗa shi dashi tun suna Saudiya yafaɗa, Cikin girmamawa Mutallab duk da baya kallonsa yace, "Barka da wannan lokaci Dad" "Barka dai, dama nakiraka ne nayi maka jajen abunda yafaru, bayan dawowrsu Umar yayimun bayanin abinda ya faru kuna can, abun baiyi daɗi ba kam ubangiji Allah ya mayar da alkhairi" "Amin Dady nagode". "Yawwa to dama nayi tunanin yimaka wani taimako ne anan niamey tunda Umar ya faɗa mani kana can, duba da mahaifinka mutumin kirki ne nasan shago bazai maka wahala anan ƙasar tamu ba, amma kaga anan Niamey tunda shine babbar birni ƙasar duk wasu masu ƙusar kuɗi ko gwamnati anan suke, so nayi tunanin anan yakamata ace ka buɗe shagon naka shiyasa nayi magana da wani babban aminina ɗan kasuwa da ƙasar ke alfahari dashi aka haɗa maka appointment da shugaban ƙasar gobe, ina fatar kana da lokaci tunda ban tuntuɓeka dawuri ba saboda banyi tsammanin za'a samu damar ganin nasa gobe ba". Da hanzari Mutallab ya miƙe tsaye cike da mamaki yana faɗin, "Dad shugaban ƙasa fa kace?". Don gabaɗaya baiyi tsammanin hakan ba shiyasa jiya yayi magana dasu malam Bulama da Mahmoud akan zancen saboda yasamu inda zai kama ƙafa, sai gashi sukutum da guda Allah ya bashi doguwar kafar da zai kama da shugaban ƙasar baki ɗaya, Dadyn Umar dake sauraronsa yace, "Kwarai da gaske Alhaji Mutallab, ni kaina na jinjinawa Alhaji souley da wannan namijin ƙoƙarin daya yimana, akwai ɗunkunan da mukayi magana dakai guda biyu da nace ayimun, to nashi ne sai kaima ka ƙara da wani abun kaje masa dashi, na tabbata komai ka gayamasa dangane da batun shagunan da inda kakeson kamawa nasan za'a shige maka gaba kasan gwamnati bakamar mutum yayi kai tsaye bane ba". Cikin jin daɗi da farinciki Mutallab yace, "Allah yasaka da Alkhairi Dady Nagode sosai." "Babu damuwa anjima komai zaizo hannunka sai ka gaidamin da kawun naka". "Zai ji ina sha Allah" Mutallab ya faɗa tare dayin Sujjada ta godiya ga ubangiji kamin kuma yadan kishin giɗa ya huta kafin can ya koma lissafin wasu order ɗin daya saka da zasu fitar waje, na zobo da waken suya. A can baranda gurin da kawunsa ke karatu ya nufa, sai da yasamu guri ya zauna kamin yace, "Bonsoir mon oncle (barka da yamma kawu)."  "Barka Mutallab har ka fito? Ai nazata gajiya bazata barka ka fito ba zaka ɗan samu kayi baccin la'asar ka huta." Murmushi mutallab yayi yace, "Ai dayake ma kawu banjin daɗin bacci a lokacin duk da dai ba laifi bane ko a musulunce shiyasa ban kwanta ba, gajiya kuma ina yin wani naji takama gabanta". "To masha Allah yanzu magana zanyi maka akan aure Mutullab yakamata ace yanzu ka samu  iyali kaima kayi aure ga shekarun naka sai ƙaruwa sukeyi, izuwa yanzu kaima gaskiya yana dakyau ace kayi auren kasamu nutsuwa, ina tunanin hakan shine daidai tunda Allah yai maka sutura da rufin asiri, a yanzu kai lema ne ga wasu ma balle kuma kanka". Sosa ƙeyarsa yayi yace "c'est ce que je souhaite maintenant (shine abunda nake fata yanzu) matan ne kawu kowacce dan kuɗi ko kyau suke nuna soyayyarsu, abun har tsoro yake bani wallahi kullum cikin abu ɗaya suke". "To banda abunka Mutallab wannan ai bakomai bane ba idan Allah yasa kasamu diya mai tarbiya mai kuma mutunci sai ka zauna kanemi zabin Allah idan har kayo istikhara kuma kanemi shawarar mutanen kwarai insha Allahu sai kaga an dace ko?." "zanyi haka kawu". "Yakamata kayi hakan gaskiya, sai batu nagaba naji zancen  buɗe shago da kake son yi ƙasarnan kasan abun dole sai da manyan utane da kuma kamun ƙafa". Murmushi Mutallab yayi kafin yace, "Eh alhamdulillah ma munsamu hanya yanzu har an haɗa mana appointment da shugaban ƙasa gobe ina sha Allah zamu je muganesa." Cikin mamaki kawun nasa yace "Shugaban ƙasa Mutallab, anya Dagaske kake?" Dariya abun ya bawa Mutallab yanda yaga kawun nasa ya ɗan girgiza da zancen haɗe da cewa, "Dagaske kawu insha Allahu zuwa goben ma sai muje tare". "Masha Allah gaskiya kazo da sa'a, ai sai mutafi har mahmoud ko?". "Daman ban zuwa ni ɗaya ai insha Allahu tare zamuje bari naje zamu zaga da Mahmoud". ko da suka fita shi da Mahmoud ya sanar dashi zancen ba ƙaramin farinciki ya taya shi ba, kafin can yaɗan kwanta ajikin kujerar da yake zaune yana lumshe idanuwa jin wani irin yanayi na buƙatuwa na taso mashi. Kamar ance Mutallab ya juyo da fuskarsa ta gefen gilashin motar kawai yayi tozali da wata halitta da tunda yake duniya bai taɓa ganin kyakkyawar halitta cikin halittu da lokaci ɗaya tayi saurin ɗaukar masa hankali ba, take yaji jikinsa ya wani amsawa yanayin da yake ciki ya sake tsanantar masa, da idanuwa ya bita da kallo har motarsu ta wuce su da sauri ya juyo ya kalli Mahmoud haɗe da cewa, "pls broth juya da sauri mu dawo wannan hannun". Dan sun riga sun kawo wajen junction balle yace yai reverse, "lafiya?" Mahmoud ya faɗa yana karyowa ta ɗaya ɓaren hannun yana kallon Mutallab, kasa cemasa uffan Mutallab yai sai sake tattara hankalinsa da yakeyi akan Aïcha ɗin dake tsaye tare da mahaifinta suna bara agaban wasu gungun maza da alama wajen majalisa ce irin ta masu zama da marece ɗin nan, bai ɗauke idanuwansa akanta ba har suka wuce sauti inda suke suka sake zagayowa ta hannun da su Aïcha ɗin suke, "Hasha lillah". Mutallab ya faɗa yana sauke ajiyar zuciya, "Broth wai mey?" Murmushi Mutallab yai idanuwansa nakan Aïcha har lokacin data miƙa hannu zata karɓo sadaka yana cewa, "Halittar Allah mana". Kafin ya rufe baki har Mahmoud da baisan inda zancen nasa ya nufa ba ya sake wuce inda su Aïcha ɗin ke tsaye, "oh my God! Broth Dan Allah ka sake juyawa mudawo wannan hannun, ya akayi kawuce wajen?" Mutallab yafaɗa yanayin baya da kansa haɗe da dafe goshinsa zuciyarsa na wani bugawa da ƙarfi da ƙarfi. "Wai meye haka Mutallab! Juya, halittar Allah, wajen duk nakasa gane waɗannan zantukan ina ka nufa kuma ina kake so mu tsaya ne?" Mahmoud yafaɗa bayan ya karya hannunsa yana kallon Mutallab da idanuwansa ke a lumshe, bai iya ranka masa ba sai da yaji sun sake dawowa ta hannun da suka baro sannan yace, "Matar aurena na gano a daidai wancan wurin majalisar, ɗan Allah idan muka kai ka tsaya wajen ina buƙatar ganin yarinyar muyi magana". Juyowa da kyau Mahmoud yayi ya kallesa kafin ya mayar da hankalinsa ga driven ɗin motar yana mamakin kalaman Mutallab ɗin, to wace yarinya ce ya gani akan titi kuma adaidai gungun da maza suke zaune da manyan motocinsu sun daka a gefe, wanda ko ba'a faɗa maka ba kasan irin masu kuɗin nan ne dake zaman majilisu bayan dawowa office dan rage gajiya. Bai kai ga gama tunanin nasa ba suka iso wajen ya gangara sukayi parking sannan ya kashe motar tare da kallonsa yace, "Gamu mun iso ina yarinyar take?" Idanuwa Mutallab ya shiga rabawa Yana waige-waigen inda zai hangota amma ɓat ta ɓace masa bata ba alamunta wajen, wani bugawa ƙirjinsa yai da sauri ya ɓalle marfin motar yafita yana ci gaba da waige-waigen inda zai hangota sai dai fa bata ba labarinta, Aïcha kuwa dama sun gama baran tunda marece yayi, akan hanyarsu ta zuwa gida ne suka tsaya wajen suka samu sadaka, daga nan suka shiga ta kwantar dake jikin wajen suka gangara can ƙasa zuwa anguwarsu, wannan dalilin ne yasa ko kafin su Mutallab su juyo su dawo wajen su harsun bar gun. "Ya Allah". Mutallab ya faɗa yana jin wani irin jiri na ɗibarsa tare da buɗe motar ya shiga mazauninsa yana sauke ajiyar zuciya, tabbas yau yayi gamo da maccen data motsa zuciyarsa ƙwarai da gaske irin Motsawar da babu maccen data taɓa satayi. Cikin wata irin murya dake nuna zallar damuwar rashin isko yarinyar agun yace, "Muje Mahmoud" yana kwantar da kansa a jikin kujerar da yake zaune.... (Tofah! Yanzu wasar zata soma💃 Gadai Mutallab ya haɗu da zaɓinsa da tayi nasarar motsa zuciyarsa, Ga kuma Meenal can a gefe tana bulayin ƙaunarsa da kuma samun soyayyarsa ruwa a jallo, ko ya wasar zata kaya? Ku biyo mu muje🏃). #Mutallab Asad #Ƴan tagwaye #Nana Diso #Billy S Fari MUTALLAB ASAD      (labari mai taɓa zuciya) Na Billy s fari Nana diso      RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU.    TAFIYAR BIYU TAFI DAYA   SHAFI NA ARBA'IN DA BAKWAI. Alhamdulillah sosai Mutallab yayi nasarar haɗu da shugaban ƙasar dan sun jima suna tattaunawa akan abubuwan da suka kawoshi cikin ƙasar tasa da yake son yi shugaban ƙasar kuma yayi na'am sosai tare da bashi damar idan har akwai wani business da zai ɗora bayan wannan da zai kawowa ƙasar shi cigaba yana na'am dashi tare da bashi takardar shedar tabbatar masa da cikakken ikon ɗaya bashi nayin kowane irin business da yake so acikin ƙasar tashi matuƙar bai taka doka da odar ƙasar shi ba, acewarsa da Niger da Nigeria ƙasa ɗaya muke kuma uwa ɗaya, ɗan haka dole ya karfafa masa saboda kawo cigaban ƙasashen namu da kuma taimakawa samari da aikinyi da yake ƙoƙarin aiwatarwa, haka Mutallab da kawunsa suka dawo cike da farincikin girmamawa da karancin da shugaban ƙasar yayi masu, nan Mutallab yakira mahaifin Umar yasanar dashi yanda sukayi yayi masa fatar alkhairi shima, basu dawo gida ba sai bayan sallar magrib saboda sai da suka fara zazzagaya birnin Mutallab ya duba wajajen da yake da buƙatar fara kasuwancin nasa sannan suka wuce gida, duk da tarin nasarorin ɗaya samu a ginin yau ɗaya ɓangare na zuciyarsa a cunkushe yake da tunanin halittar ɗaya gani jiya data tsaya masa azuciya, duk wani motsi da zaiyi sai tunaninta ya zo masa idan kuma ya rufe idanuwa kyakkyawar fuskarta yake hangowa duk da aibin suturar dake jikinta alokacin, sai da yayi da gaske sannan ya iya ture tunaninta suka gudanar da zaman da sukayi da shugaban ƙasa, yanzu kuwa daya dawo gida ya watsa ruwa sai ya janyo tunanin nata da kansa ya dawo dashi kusa dashi ko zai rage masa raɗaɗin rashin ganinta da yake ji cikin ransa, daf da zai kwanta kuma sai yatuna da Abba dake don yin magana dashi, cikin rashin kuzari dake tattare dashi na dukan da tunanin Kyakkyawar yarinyar daya gani yayiwa zuciya da gangar jikinsa ya ɗauko wayarsa ya shiga nemansa duk da wata zuciyar na ƙoƙarin hanashi kiran ganin dare yayi takan yiyuwa yana tare da ɗaya daga cikin matansa, amma rashin sanin dalilin neman nasa da yakeyi da kuma daraja irin ta mahaifi ya sashi ture tunanin gefe ya kira numbar tashi, kusan kira 4 yai masa bai daga ba hakan yasa ya ajiye wayar tare da ƙoƙarin sake komawa duniyar tunanin daya zamar masa ɗabia tsakanin jiya da yau, gashi kamar kada yayi tozali da wannan yarinyar daya laƙawa suna halitta lalurarsa ta sake tsanantar masa, gashi ko ɗan lemon tsamin nan shi baya sha balle ya samu abun ya kwanta masa, miƙewa yai ya buɗe fridge ya ɗauko ruwan sanyi yasha sannan ya ɗauki wayarsa yafice daga ɗakin, wajen Jaddi ya nufa daya san basu kwanta ba ita da Afrah da duk wani motsinta Jaddi ke kul dashi ya tabbata suna can suna fira don suna jimawa basu kwanta ba, ɗazuma da zai fita ya shiga yana cewa Afrah ta shirya kayanta gobe zata wuce haka Jaddi ta aza masa rigima wai sai dai yanar mata jikarta ba inda zata koma tunda dama Abbansu yace su dawo wajensu, Afrah kuwa ta saka mata kukan ita bazata iya zama anan ba tafi so ta zauna duk inda yan uwanta suke, dole Jaddi takama bakinta tayi shiru don batada amsar basu kuma tunda mai zaman tace bazata zauna ba. Zaune kuwa ya iskosu suna fira da wata ƙanwar mamansu shima ya zauna akaci gaba da firar dashi, Jin wayarsa tayi ƙara ya sashi miƙewa yana yimasu sai da safe tare da jaddadawa Afrah ta shirya dawuri dan goma na safe jirgi su zai tashi, yana fita ya katse kiran ganin Abbane ya kirashi da kansa tare dayin sallama bayan ya ɗaga yana cewa,"Barka da dare Abba". "Barka Mutallab kashe za fita can waje sai muyi wayar, ka kirani nan da mintuna goma haka kaji". Abba yayi maganar ƙasaƙasa dan kar Umma da tayi bacci tajishi, "To ba Abba." Mutallab ya faɗa yana sake gasgata zancen da sukayi da Jalil. A hankali Abba yamiƙe ganin bacci Umma keyi sosai ya saka silifas ɗinsa yayi hanyar gate ɗin gidan yana cewa mai gadi ba naisa zaiyi ba ya kirasa bakin gare zai ɗan motso jikinsa ne da bayajin daɗinsa, fatan dawowa lafiya maigadi yayi masa sannan shi kuma yafice, sai da yayi ɗan nisa sannan kiran Mutallab ya shigo". Sauke ajiyar zuciya Abba yai bayan ya ɗaga kiran haɗe da cewa, "Kayi haƙuri dan Allah Mutallab da abubuwan da suke faruwa, ban san meke damina ba kwata-kwata na aikata maku hakan, Nakasa samun nutsuwa tunda nace kubar gidannan gaba ɗaya, Kai kuma kayi fushi dani baka kirana kaji halin da nake ciki ba?". "Abba kayi haƙuri nazata zuwan namu ko kuma kiran zai ɓata maka rai ne shiyasa banyi hakan ba". "Mutallab kuna dai lafiya ko?" "Lafiya klw Abba". "A BBC ranar nake gani suna haskawa wai kasamu gobara, banyi bacci ranar naku rasa dalilin da yasa nakasa nemanka, sai ɗari da Jalil yazo na tammbayesa yake cemun akwai kayan acikin shagunan sosai da aka rasa" "Eh  wallahi Abba". "Ubangiji yabaka ninkinsu Mutallab yakuma mayar da alkhairi ya tsare mani ku aduk inda kuke". Hawaye ne suka zubowa Mutallab cike da tausayin Abban nasu shima, a yanda yake jin muryar Abban nasu ya tabbata akwai abubuwa tattare dashi dake samunsa tare da nuƙurƙusar masa zuciya, fitar da iska yai tabaki yana ɗauke hawayen dan baya son Abban nasa yasan kuka yakeyi yace, "Amin Abba na gode". Yana ƙoƙarin sake maida wasu hawayen dake son zubo masa, a ɓangaren Abban ma ƙwalla yakeyi amma cike da juriya ya ƙaƙalo murmushi tamkar yana agaban Mutallab ɗin yace, "DanAllah Mutallab ina so kayi mani wani taimako, duk abun da nake dashi dana juya kansa sai naga babu shi, na rasa komai hatta kadarar tawa duk na siyar naba ɗan uwanka Jamil yaja jari, yanzu gashi masu damfarasun kwashe masa kuɗin business ɗin nasa kaf, ga ƙanenka Walid zai rubuta jarabawar gama secondry nakasa biyan kuɗin, gidanmai na ma daya rage ɗazu naje na tadda babu man sai ɗan neman bashi da ake biyarmu dole na sakashi kasuwa na biya bashin da ake biya". Kukan da Mutallab ke riƙewa tun ɗazu ne ya kucce masa hakan ya sashi kauda wayar gefe tare da ƙoƙarin controlling kansa sannan yace, "Abba kai mahaifina ne babu alfarma tsakanin iyaye da ƴaƴansu, in sha Allahu zan kula da karatun su Walid ɗin daga jami'a har zuwa inda suka gaji suka tsaya, Sannan kuma bashin naka shima zan biya ko nawa ne ka lissafa ka turo mani, gidan mankai kuma kabar abunka kada ka sai da kafin nadawo muga ya za ayi a tayar dashi, kawai dai a sallami ma'aikatan wajen arufesa inaga hakan zaifi, zan kuma turamaka wani abun account dinka sai kadinga cefanen gidan, Ni ɗan ka ne Abba duk abunda kakeso kawai ka tambayeni indai ina dashi zan baka ko meye". Sautin kukan mahaifin nasa yaji yana faɗin, "Ka yafe Mani Mutallab Allah yayi maka albarka Allah yarabaka da duniya lafiya, zan je na kwanta sai da safe amma dan Allah karka kirani idan bani nakiraka ba kada Ummanku tayi fada, bari na koma nafito ne daman kada taji muna wayar tayimun masifa Allah ya ninka maka Mutallab". "Amin". Kawai Mutallab ya iya cewa har Abban ya katse wayar. Ahankali ya silale gefe guda yana jin wata matsananciyar damuwa akan yanayin da yaji mahaifin nashi aciki, hakan yasa ya shiga karanto addu'o'in yayewar baƙin ciki da kuma damuwa, اللّهُـمَّ إِنِّي عَبْـدُكَ ابْنُ عَبْـدِكَ ابْنُ أَمَتِـكَ نَاصِيَتِي بِيَـدِكَ، مَاضٍ فِيَّ حُكْمُكَ، عَدْلٌ فِيَّ قَضَاؤكَ أَسْأَلُـكَ بِكُلِّ اسْمٍ هُوَ لَكَ سَمَّـيْتَ بِهِ نَفْسَكَ أَوْ أَنْزَلْتَـهُ فِي كِتَابِكَ، أَوْ عَلَّمْـتَهُ أَحَداً مِنْ خَلْقِـكَ أَوِ اسْتَـأْثَرْتَ بِهِ فِي عِلْمِ الغَيْـبِ عِنْـدَكَ أَنْ تَجْـعَلَ القُرْآنَ رَبِيـعَ قَلْبِـي، وَنورَ صَـدْرِي وجَلَاءَ حُـزْنِي وذَهَابَ هَمِّـي A hankali yaji damuwarsa na sauka sosai sai ya rufe da addu'o'in bacci sannan ya kwanta. Ko da Abba yaƙarasa cikin gidan wani irin faɗuwa gabansa keyi, yana shiga palour kuwa sai ganin Umma yayi ttsaye tana kai da komowa rai a ɓaci dan ta ɗauka ma yana sashen Aunty Amarya data hana masa zuwa tun bayan tafiyar su Mutallab, "Daga ina kaje ne Abba?" Ta jefo masa tambayar tana haɗe rai, "Kiyi haƙuri Umma jikina ne babu daɗi shine na fita na ɗan tattaka". "Au to shikenan shige muje na aza sashen waccan sakaran kaje". Tafada tana bin bayansa. Suna shiga cikin ɗakin har zai kwanta Umma tace dakata, "wai ina kuɗinka ne dazu zanbawa Jidda kuɗi banga komai ba adurowar bayan kuma kacemin zakaje gidan mai". "Innalillahi Umma kiyi hakuri mantawa nayi ban faɗa mako yanda akayi ba da naje, amma dai mukwanta gobe zan bata kuɗin, kuma kema zan baki in sha Allahu". Murmushi tayi ranta fes aikin boka yaci uban nada dan yadda take juya Abba yanzu kam abun ba'a magana dan ko Jamil data haifa baya bari ta juyashi haka, tariga data mamaye ko ina ta mayar da Aunty amarya hoto dan yanzu ko dakin Abba bata isa ta shiga ba yadinga yimata masifa kenan har sai ta fita, shi kuma bata barinsa ko ƙofar ɗakin ya kalla ɗan haka dole ne gobe taje taƙarawa boka kuɗin aikinsa dan kuwa yaci yadda yakamata, yanzu abu biyu ne gabanta, nafarko kaɗa ƙeyar su Walid da uwarsu, na biyu kuma tarwatsa rayuwar Mutallab da boka ya tabbatar mata da sai da taimakon matar da zai aura, kuma alhamdulillah tayi nasarar sawa a binciko mata halin Meenal an tabbatar mata da fitsararriya ce, dama kuma kalar macen da boka keso ya ita kenan yanda aikinsa zaiyi tasiri ta hanyarta, abinda ya rage mata shine tasa Abba yasa Mutallab ya aureta, dan haka suna kwantawa tace, "Abba nikam ya zancen auren yaron nan Mutallab da yarinyar nan ƴar gidan amininka? Inaga ka lallaɓashi ya aurota a huta saboda asamu shi kanshi ya natsu, kasan ina saurayi nada dukiya babu kalar iskancin da baya yi". "Kinyi gaskiya to yanzu ya kike so ayi?" "So nakeyi ka kirasa gobe kayi masa zancen, bance kayi masa tsauri ba tunda kasan halinsa kafiya tayi masa yawa, so nakeyi ka lallaɓasa yanda zai amince ya aureta cikin ruwan sanyi". "To Shikenan Umma Allah yakai ranmu gobe lafiya". Ta amsa da Amin wani farinciki na sake lulluɓe mata zuciya. **********    Sai da Mutallab ya tabbatar da jirgin su Afrah ya tashi zuwa ƙasa Nigeria sannan yakira Jalil ya sanar dashi saboda yayi ready ɗin zuwa ya ɗauki ta da zata jirginsu ya sauka, bayan sun gama wayar ya nufi gida cike da kewerta shi

Chapter 27 of 54