dai-dai lokacin motocin mahaifin nata suka kutso kai cikin farfajiyar katafaren gidan, suna yin parking sautin ƙarar data saka ya dira a kunnensa, kafin kace me tuni ya ɓalle marfin motar tun kafin guards ɗin da su buɗe masa kamar zai tashi sama ya nufi cikin gidan...
Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only
Zaki biya ta wannan account ɗin👇🏻
0020428430 Ishaq Fatima A GTBank
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
#Mutallab Asad
#Tagwaye biyar
#Billy S Fari
#Nana Diso.
*MUTALLAB ASAD MUTALLAB*
(MAM)
NA
BILLY S FARI &
NANA DISO
*SHAFI NA UKU.*
_RUBUTUN ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU._
_TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA_
Cikin azama ya bankaɗo ƙofar palourn da ƙarfi ya shigo yana faɗin Meenal..Meenal me yake faruwa? me ya sameki? a jajjera ya jefo mata tambayoyin cikin tsananin tashin hankali, ba tare data amsa ba ta ɗauki wani glass flower dake kan center table ɗin ta ƙara fasashi tana kallon yadda jikin mahaifin nata yake rawa yana riƙeta. " Yi haƙuri Meenal faɗamun waye ya taɓaki yanzun nan ya haɗu da fushina saboda akan ɗiyata babu wanda bazan hukunta ba!" ya ƙare zancen yana kallon Mommy data kasa motsawa daga inda take tsaye tana kallon ikon Allah ganin yanda yake faman ɓaɓɓata rai. duk da tasan komai zata faɗa masa bai isa ya zamo hujja a wajensa ba da zatasa ya sassauta mata akan hukuncin da ako yaushe baya gajiya da yanke mata akan Meenal ta sauke ajiyar zuciya ranta a ɓace itama tace "Yanzu Alhaji ba nida ikon yiwa Meenal faɗa kenan? Kawayenta fa takawomin har cikin falona suka ware kida sunata rawa sai kace club....".
Sai daya watsa mata wani banzan kallo haɗe da ƙoƙarin dakatar da ita daga maganar da takeyi sannan yace, "Daƙata malama! so what don tayi hakan gidanki ne? Ko kuma waninki ya gina min? Ɗiyata ce fa kuma gidan ubanta ne don me da baza'a barta tasamu nutsuwar da take buƙata acikinsa ba? Look! Masha gayamiki cewa Meenal tafi kowa iko da duk wani abu dana mallaka a gidan nan koda kuwa yayanta ne balle ke, don haka wannan ya zama shine karo na ƙarshe dazan kara yimiki magana akan nunawa ƴata iko da duk wani abu daya zamo mallakina domin ita ɗin rayuwata ce kuma farincikina". ba tare da Mommy tayi mamakin zafafan kalaman nasa da yayi amfani dasu akanta ba taci gaba da kallonsa, tsaki ya ja sannan ya sake cewa, "Finally you have to apologise her yanzun nan!" Da hanzari Mommy ta ɗago ido tana kallonsa kafin ta maida kallonta ga Meenal data saki wani makircin murmushi tana kallonta sama da ƙasa, wani irin takaici ya tasowa Mommy domin idan da tasamu haihuwa ta tabbatar ɗiyarta tafari sai ta girmewa Meenal, amma tsabar wulaƙanci ace itace zata bata haƙuri duk da Meenal ɗin ce tayi kuskure, Muryarsa taji a tsawace yana cewa, "Bakiji me nake cewa bane?"
"Am sorry". Mommy tafaɗa ranta na matuƙar wani irin zafi ta juya tabar wajen ta shige daƙinta.
Da kallo Dady ya bita kafin yayi kwafa ya maido kallonsa ga Meenal yace "kin haƙura Babyn dady?." Ciƙe da shagwaba ta ƙalli mahaifin nata haɗe da kwantar da kanta saman kafaɗarsa tace. "Nidai Dady kaƙara yimata faɗa gaskiya tadaina shiga sabgata sai..." "Is okay baby jeki ki huta abunki, ko akwai wani abunda kike so?" "No Dadyna, but want pepper soup na kaza kasa tayi mun kuma tasaka spices". Kallonta yayi cike da soyayya irin ta uba da ɗiyarsa yace "zatayi miki yanzun nan kuwa kin ji Dady girl". yana shafo kanta haɗe dayin murmushi, cike da jin daɗi Meenal ta rungume mahaifin nata tace "I love you Dadyna" "Dadynki yana sonki sosai fiye da haka shima".
Daga haka ta hau sama inda ɗakinta yake, ko data shiga tuɓe komai tayi najikinta kama daga mayafin kanta da wandonta, ƴar ƙaramar rigarta har ma da bra ta cillar dasu ƙasan dakin sannan ta faɗa bandaki ba tare da tunanin tayi addu'a ba, ta ɗauki kusan mintuna talatin ciki sannan tafito tasaka towel wanda bai wuce iya gwuiwarta ba, zama tayi akan dressing mirror tafara ƙoƙarin shafa mai sai data gama sannan ta buɗe wardrobe ɗinta. Yadda ta zubawa kayan nata idanu zaka tabbatar tunanin wanda zata saka takeyi. Cikin damuwa ta shiga watso da kayan kasa tana neman wata long rigar da take don sakawa, sai data zubo da fiye da rabin kayan duka sannan ta dakata ta tuna suna ciƙin ɗayar wardrobe ɗin nata, ba tare da damuwa da kuma tunanin gyara kayan data zubo dasu ba ta shiga taka kayan dake azube ta nufi ɗayar wardrobe ɗin ta ɗauki rigar tata tasaka, kasancewar bata da jiki kwatakwata sai rigar tayi luf ajikinta. sake tattaka kayan da suke ƙasa azube tayi tafice daga dakin ta nufi falon sama dan akwai series ɗin da take so ta kallah ba tare da tayi duba da magariba ta nufo ba, ko kaɗan hakan bai dameta ba dan ko sallar la'asar batayi ba, kawai ta saka a ranta za tabari ta haɗa duka da magrib da isha'i da la'asar tayi idan zata kwanta.
A ɓangaren Mommy tsananin baƙin cikin da take ciki acikin gidan nan da kuma cikin ranta bazai iya faɗuwa ba. rayuwar da takeyi agidan babu daɗi ko kaɗan ga daula da tarin arziƙi kama daga kan suttura, abinci da kuma muhalli, komai na rayuwa babu abinda ta rasa saboda Alhaji Abdulmalik mu'azzam mutum ne mai arziƙi da wadata baɗan ƙarami ba, ya sauya mata rayuwarta data iyayenta daga tarin rashin wadatar da suke ciki, duk wanda ya santa ya kuma san yanda tafito daga gidan mijinta na farko yasan cewa tana cikin wadata yanzu saboda yanda ta canza tayi dumurmur da ita fiye da lokacin da tayi aurenta na farko, sai dai duk da haka tana samun tauyuwar farinciki sanadiyar yarinya ƙarama data fitineta, tana yawan jin ana faɗar matsaltsalun yaran miji batasan haka suke ba sai da Allah ya jarrabeceta yanzu da masifar Meenal, yarinyar da sam bata ganin girmanta da ganin mutuncinta duk da hidimtuwar rayuwar da tayi mata tun tana ƙanƙanuwa har zuwa girmanta. Wayarta ta dauƙo tashiga kiran numbar ƙanwarta da take bima, bugu ɗaya ta dauƙa nan ta shiga gayamata abunda yafaru yau tana share ƙwalla. Murmushi ƴar uwar Tata tayi haɗe da cewa, "kiyi haƙuri Aunty domin babu abunda ya bari a duniya, ki roƙa mata shiriya domin idan ɗiyarki ce Aunty ai dole haƙurin zakiyi da ita ko?"
"Haba Saddiƙa ya zakice nayi haƙuri shikenan nayita haƙuri yarinya ƙarama tana takani agidannan? ko autar gidan mu fa tafita shekaru saddiƙa, wlh ban taɓa ganin inda ake sangarta yaro ba kamar gidannan, haba! Wannan wace itace masifar ce haka? tun tana ƙaramar nake faman tufƙa yana yimani warwara akan tarbiyarta gashi yanzu har ta girma tana ganin cewa ni da ita girmanmu ɗaya, A fili mahaifinta ke nuna akanta babu wanda bazai iya takawa ba hatta mahaifiyarsa da data haifesa, gaskiya ni bazan iya ba na fara gajiya".
"Subhanallahi Aunty kada kice haka, wannan wacce irin magana ce kikeyi?"
"Hmmm bazaki fahimta ba Saddiƙa, wlh Allah da gaske nake miki babu wanda Meenal take gani da mutunci har kakar tata, sun gama lalata mata tarbiyar da nake ta ƙoƙarin ganin na bata, sangarta kuwa sai kin gani da ido ki, Allah dai kashiryar da ita su kuma ya ganar dasu, amma nikam haƙuri na ya fara ƙarewa Saddiƙa, nagaji nagaji da Auran nan kawai gwara nafito ai talauci ba hauka bane."
"A'a kidaina maganar fitowar nan dan Allah Aunty, koma meye mijin nan naki ya gyara mana rayuwar iyaye hatta gidan ƙasan da suke ciki sai da ya canza musu, kidinga tunawa fa hatta abincin da akeci acikin gidanmu kece kike kawo mana da taimakonsa, ko don haka dan Allah kiyi haƙuri aduk lokacin da ranki ya ɓaci kina tunowa da wannan alkhairin nasa agaremu, ki ƙara jan yarinyar ajikinki kina lurar da ita in Sha Allah watarana zata daina kuma ki kauda kanki ga abubuwan da kika san zasu iya jawo Mali wannan damuwar matuƙar basu taka kara ba" Hawayen fuskarta ta goge tana jin ta ɗan samu natsuwa a zuciyarta tare da amsa wa ƴar uwar tata da "shikenan saddiƙa nagode". tana ajiye wayar taga ƙarar kiran ƙawarta hajiya Binta, sai da ta ɗaga suka gaisa sannan ta shiga labarta mata abinda ke damunta sanadiyar tambayar data jefo mata jin Muryarsa ba daidai ba, nan ta kada baki tace da ita "to shikenan zama zakiyi kina kallon yarinyar nan tana buɗe Mali shafin iska ci kala-kala? Bari kiki wallahi idan tayimiki kici ubanta, shegiyar yarinya jiki kamar na muciya kidaina dauƙar wulakancin nan nagaya miki tunda ba ita kike aure ba, ina mijinki yana sonki ba shikenan ba".
"hajiya binta kenan, bakisan soyayyar da Alhaji ke yiwa yarinyar nan ba kenan da zaki ce haka" cike da takaici Hajiya Binta tana tsaki haɗe da cewa "to ina ruwa ki da wannan, shi da yaji zai iya tunda ƴarsa ce, amma ke akan me zaki zauna tana takani don ranta don mutukar... sufa ƴaƴan miji idan bakiyi da gaske ba wallahi sai sun fiddake." "Haba ƙarara Allah dai ya kiyaye".
"To ai kece da kayan takaici bakisan sharrin su bane, yanzu ba gashi ba guda ɗaya ce sai kuma yayanta amma sun hanaki zaman lafiya? gantalalle wai yana ina shi na dena ganinsa?"
"ya je Egypt wai ciwon ciki ke damunta kwana biyu shine mahaifinsa ya turasa can adubosa".
"Allah ya raka taki gona ai kuwa huta kafin yadawo.." haka Hajiya Binta taci gaba da maganganunta har ta gama Mommy bata kara cemata komai ba kafin sukayi sallama ta ɗan jingina ajikin gadon da take zaune Ac daƙin na ratsamata jikinta, ta jima a haka kafin ta fito tanufi ɗakin Dady, koda ta shiga yana zaune da alamu bai jima da watso ruwa ba yana shan lemon da tayi masa ta saka masa acikin ƙaramin fridge ɗin dake cikin ɗakin nasa. " Sannu da hutawa Alhaji" a maimakon ya amsa ba tare daya ɗago ba bayan yayi sipping lemun tare da ajiye cup ɗin a gefe yace "Sau nawa zan gaya miki kidaina takurawa yarinyata? pls idan har bazaki dena ba to hakan na nuni da kin gaji da zama dani kenan, don haka ki kama gabanki don ni bazan juri ganin kina ƙuntata mata ba acikin gidannan ba" yanda zuciyarta ke bugawa yasa ta zuba masa idanuwa tana ƙoƙarin sake danne ɓacin ran dake taso mata a karo na biyu kafin a hankali ta sauke ajiyar zuciya tace "kayi haƙuri Alhaji, gobenta nake don gyara mata bawai ina don takurata bane ko don ɓata maku rai."
"waye yasaki? kibarta da gobenta mana ko ke kike da iko akanta". Dady ya ɗago kai cikin ɓacin rai yana faɗar hakan idanuwansa cikin nata ko kunyar faɗar hakan baya ji, "shikenan kayi haƙuri bazan ƙara ba in sha Allah" "zai fi kyau ki kiyaye hakan, me aka dafa a gidan?"
"Abinda kafi buƙata ako yaushe". Mommy ta faɗa tana ɗan sake fuskarta ganin alamun ya fara saukowa,
"Thanks, Meenal nada buƙatar pepper soup, Don haka a hanzarta ayi mata ƙamin nafito."
"Nayi pepper chicken Alhaji kuma itace tace tana so" "To hakan laifi ne idan ta buƙaci a sake yin wani pepper soup ɗin? Ƙarfa ki manta Meenal rayuwata ce dole komai take so a bata tunda akwaishi".
"haka ne, bari in saka ƴan aiki suyimata." "Naki tace tana so don haka ke zakiyi mata mansura". ya faɗa kai tsaye tare da gincirawa gefen gadon yana rufe idanuwansa "Afwan Alhaji bawai bazanyi bane, naga yanzu kadawo kana kuma buƙatar kulawata ko?."
"Yau na yafe kije kiyi abinda zaki farantawa yarinyata hakan ya wadatar." ya kare zancen har lokacin idanuwansa na arufe, Batace komai ba tafice daga ɗakin cike da damuwa, kusan awa ɗaya da ɗoriya tayi kamin ta gama haɗa wani pappe soup ɗin, tana gamawa ta ajiye mata a dinning lokacin suna zaune ita da mahaifin nata da alama wata hirar sukeyi ta kakarta da take kira grandama, kallon abinda Mommy ta kawo ta ajiye agabanta Meenal tayi kafin tace "Gaskiya kin daɗe sosai har yunwa ta soma raunat lafiyata". jin zata iya taso wata rigimar yasa Dady yayi saurin cewa "Karki damu Babyn Dady tunda dai ta haɗa maki duk da ranta baya so". Batace musu komai ba ta nufi hanyar daƙinta, tana jin yanda Meenal ke faman zuba masa taɓara yana faman yimata dariya tayi banza dasu ta shigewarta don inda sabo duka Waɗan nan abubuwan ta saba dasu, zuciya ce kawai ba tada ƙashi shi yasa har take komawa kansu suna ɓata mata rai a banza...
____________
*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?*
*INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?”
*KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.*
Mun gwada mun gani 💯
Mun gani mun shaida 💯
Anyi mun gani 💯
MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
GYARAN MAIJEGO
MALLAKAR MIJI KO MATA
SUBULU DA SCRUB
MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
MAGANIN TSUMI
INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯
08142800199
07068558096
_
Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only
Zaki biya ta wannan account ɗin👇🏻
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*MUTALLAB ASAD MUTALLAB*
(MAM)
NA
BILLY S FARI &
NANA DISO
*SHAFI NA HUDU.*
_RUBUTUN ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU._
_TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA_
*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?*
*INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?”
*KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.*
Mun gwada mun gani 💯
Mun gani mun shaida 💯
Anyi mun gani 💯
MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
GYARAN MAIJEGO
MALLAKAR MIJI KO MATA
SUBULU DA SCRUB
MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
MAGANIN TSUMI
INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯
08142800199
07068558096
Tana shiga ɗaki taji muryar Dady ya ƙwalo mata kira, har ta zauna bakin gado ta maza ta miƙe da sauri don kada tayi laifi ta juya tafice muryar Meenal taji tana cewa "Dady ɗakina yayi datti ka faɗa mata ta gyaramin yanzu." murmushi yayi dai-dai lokacin taƙaraso yace, "Mansura kinaji ɗakin ƴarki yayi datti sai a gyara mata ko". kallon Meenal tayi data kafeta da idanuwa tana jiran taji ko me zata ce, bata tare data nuna abun ya ɓata mata rai ba ko ya dameta ba tace, "To Alhaji" sannan ta juya ta hau benen, abuntakaici gaba ɗaya ɗakin a haukace yake tamkar ba mutum ke rayuwa aciki ba saboda hatta pant ɗinta da bra ta zubar dashi a ƙasa, idan bata manta ba ɗazunnan da safe ta saka mai aiki ta gyara mata shi amma tsabar wulaƙanci dubi yadda taƙara mai dashi, ba don tana kallon Meenal ɗin a matsayin ƴa awajenta ba da bazata cigaba da yimata irin wannan bautar ba da girmanta, sai dai babu yanda zatayi tunda idan ƴar data haifa da cikinta ce komai munanan halayenta dole tayi haƙuri da ita kuma ta hidimta mata a matsayinta Na mahaifiyarta tare da tsawatarmata, matsalar ɗaya ce yanzu ta rasa duk wata cikakkiyar dama da zata iya tsawatarwa Meenal tare da kwaɓarta don bata ingantacciyar rayuwa lura da yanda hatta mahaifiyarta da dangin mahaifiyarta nada sa hannu wajen warware duk wata tubƙa da takeyi akan tarbiyarta, duk wannan dogon tunanin da takeyi tana yine tana gyaran ɗakin, Ƙunshin pad ɗin da taci karo da ita agefen gadonta ya sata saurin ture tunanin nata a gefe tana tafa hannuwa haɗe da Sallallami, ko kaɗan batayi tunanin lalaci Meenal yakai haka ba da zata iya ajiye irin wannan ƙazantar acikin ɗakin baccinta kuma a gefen gadon kwananta duk da yanda ta kwana ta tashi da sanin irin ƙazantar da take fama da ita aɓoye, wacce wanda ya zauna da ita kaɗai zai iya fahimtar hakan saboda a zahiri ita ɗin ƴar wanka ce kuma cikakkiyar ƴar ƙwalisa dake ji da kanta, ba don Allah yasa ma tana shiga lamurranta ba ta ɓangaren ajiye mata duk wasu abubuwan ɗaya kamata a matsayinta na ƴa mace kuma cikakkiyar budurwa da Allah kaɗai yasan ko a bayyanenta yanda zata kasance. durƙusawa tayi ta kwashe tasaka a dustbin tana sake jinjina wannan sangarta irin ta Meenal da gaba ɗaya tayi yawa. da wannan mitar taci gaba da gyaramata daƙin tsaf har ta gama tana mai sake nema mata shiriya a ranta. ko data sauka ƙasa bata tarar da kowa a palourn ba, hakan ya tabbatar mata sun fita tare da mahaifin nata don kusan ko yaushe suna tare da marece kafin sallar magrib, wani lokacin zasu zauna a farfajiyar gidan ne ƙarƙashin rumfar dake can gefe an ƙawata ta da kujeru wani lokacin kuma fita sukeyi da mota, basa dawowa sai ana kiraye-kirayen sallar magrib, kai tsaye ɗakinsa ta wuce don yau tana son taburge maigidan nata ganin yanda kwana biyu rikicin Meenal ya sanya rashin jituwa da kuma kulawa sosai tsakaninsu, kasancewarta mace mai kula da iya taraiyar miji da kuma gyaran jikinta yasa take da tasiri a wajensa da har ta iya saye zuciyar mijin nata, ba don haka ba da tuni irin matsaltsalun da Meenal ke haifar wa tsakaninsu yasa labari sauya wa, don ba shakka adalilinta da tuni ta koma gidansu, sai dai biyayyarta da sauran abubuwa musamman a shimfiɗar aurensu ya matuƙar Sanya shamaki da kuma babbar katangar iya faruwar hakan agareta, Murmushi ta saki ganin yanda tunanin abubuwa ke nema ya zautata kafin ta shiga toilet ɗinsa tafara gyara masa sannan tafito ta gyare masa ɗakin tas ta saka masa turarukka masu ƙamshi haɗe da saita gudun A.c dake aiki, nan take sai ɗakin ya fara fidda wani irin daddaɗan ƙamshi da sanyi dake ratsa zuciya da kuma gangar jiki, duk da tasan wardrobe ɗin da kayansa ke jere a gyare take tsaf don kullum saita gyara kayan dake ciki haka ta ɗauko turaren ƙamari ta turareta sannan ta daidaita zaman kowanensu ta rufe, kallon ko ina tayi taga yayi mata yanda take so sannan tafito ta nufi kitchen, kankanarta ta markaɗa tare da apple ta tace ta saka madara da zuma takai cikin ƙaramin fridge ɗin da dake bedroom ta saka sannan ta wuce ɗakinta ta shiga toilet, cream ɗin shaving ta ɗauka na ta shafa agefen mararta inda gashi yafito ta kuma shafa a hammata don ta ɗan lurah da kyau Alhaji Nason gurun ya ƙasance babu gashi don yana yawan cemata shifa gashi ƙazanta ne kuma yana jawowa macce cutar da bata zato, don haka hatta a ma'amalar aure ni'imar macce tafi fitowa sosai amma idan da gashi wani loƙacin gashin yana maƙalar da ni'imar jikin mace sosai, sai data gama gyare wajen tsaf sannan tayi wanka tahau shiri cikin irin shigar data san yana matuƙar so haɗe da feshe jikinta da turarukka masu ƙamshi bayan ta mulkesa da azababbiyar khumrarta da kwalaccam da ƙamshinsu ke tafiyar da duk wata natsuwar maigidan nata idan ya shaƙa. wannan wani sirrine data yarda cewa yana ɗaya daga cikin abinda ke sata kasancewa aciƙin zuciyar maigidan nata ako da yaushe. shiyasa duk girman laifi da ɓacin ran da zai dasa mata take ƙoƙari taga ta danne tayi masa abinda yafi so don ya cancanci haka agunta, saboda shi mutum ne da babu ta inda ya gaza wajen sauke mata buƙatunta da kuma na iyayenta, sutura komai tsadarta zai siyomata ita, haka idan yau ya canzawa meenal mota ko yayanta to itama zai canza mata, matsalar ta kawai dashi ƴaƴansa da bai haɗa da kowa ba musamman Meenal dako tarin yarinyar bazai juri saurara ba, wani mahaukacin so ne da baya misaltuwa adoron duniyar nan yake yimata dako cikakkiyar tarbiyarya ya kasa tsayawa ya bata ya kuma hana wasu su bata, wanda hakan na matuƙar saka mata damuwa dajin cewa ta gaza sosai wajen kula da yarinyar data riska cikin matsananciyar buƙatar uwa tun tana da shekara biyu da rabi ita da ɗan uwanta sanadiyar ya rabu da mahaifiyarsu, itace tasa hannu bibbiyu ta riƙesu bisa jagorancin nasihar mahaifiyarta da ako yaushe ke cewa tayi haƙurin kula dasu tare da basu kyakkyawar tarbiyya tamkar ƴaƴan data haifa saboda itama ɗiyarta nacan a wani wajen tabari kuma zata iya kasancewa kamar Meenal da yayanta a wajen mahaifinta, ma'ana yana yimata irin soyayyar da mahaifinsu Meenal keyi mata, palourn ta fito bayan tayi sallar magrib da tun ɗazu aka gama kiraye-kiraye, tayi tsammanin zata riskesu sun dawo sai gashi har lokacin basu dawo ba hakan yasa ta koma ciki ta soma gabatar da azkar ɗinta na marece kamar yadda ta saba har aka kira sallahr isha'i ta miƙa ta gabatar tana idarwa tayi zikiri sannan ta miƙe ta sauya kayan jikinta zuwa wata doguwar riga ta bacci irin masu sulubin nan tasake shafe jikita da turare sosai haɗe da jefa kaninfari abakinta ta ɗan taubashin saboda gusar da duk wata barazanar bashi sakan iya bijirowa abaki duk yanda kuwa akayi brush, hakan shima wani sirrine ne na daban dake ɗauke duk wani ƙarnin baki. Hijjab tasaka ta rufo ƙofar ɗakinta ta nufi sashen Dady da tun ɗazu taji shigowar su ba tare data lura da Meenal ba dake nan palourn zaune ta baje kayayyakin maƙulashe da mahaifin nasu ya siyo mat ciki kuwa har Dana Mommy ɗin ɗaya bata ta bata ta haɗe gaba ɗaya tana ci.
Ɗago kai Meenal tayi tana watsa mata wani banzan kallon haɗe da taɓe baki ba tare da Mommyn tasan ma tanayi ba, 'Hmmm lallai matar nan, ita alallai nan wajen farantawa dadyna zata je, tab! kin makaro wallahi don yau bake ba barci, duk wannan munafurcin naki a banza zai tashi' Meenal ta faɗa kai tsaye duk da tana da tabbacin Mommyn baza taji ba tunda ta shige abunta.
Sanda Mommyn ta ƙarasa dakin har Dady yakwanta hakan ya sata cire hijjabin dake jikinta take daddaɗan ƙamshin dake fitowa daga cikin fatar jikinta yayi nasarar kaiwa kai tsaye cikin kusurwowin hancin Dady da kwantawarsa kenan ya wani lumshe idanuwa yana sake zuƙa cikin wani irin salo tare da sauke wata irin ajiyar zuciya yana mirginowa fuskarsa na kallon sama, hakan ya tabbatar mata da nauyi bacci ba kawai ya kwanta ne, Murmushi tayi ta zauna kusa dashi a hankali ya buɗe idanuwansa ya saukar a kanta yana sakar mata murmushi shima, hannunsa ya miƙa ya riƙon nata tare da faɗin, "kinyi matuƙar kyau hajjaju shi yasa kullum nake ƙara sonki a zuciyata, baki sani ba! yanda na riski ɗakin nan sai da nace anya nawa ɗakin ne ko kuma naki ne nayi ɓatan kai saboda yanda ƙamshinki ya tarbeni acikinsa, musamman a cikin kayanaa dana zo sauya wa bayan nafito wanka, gaskiya ni ɗin mai matuƙar sa'a ne hajjaju da Allah ya mallaka mani ke, sannu da ƙoƙari Allah yayi makin albarka" ya ƙare zancen yana janyota zuwa saman jikinsa, kallon tsakar idanuwansa da take hango tsantsar soyayyar da takeyi mata wacce duk ƙarfin ta Meenal a zuciyarsa a irin wannan lokaci take danne
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 54