ta kafin tace, "Abunda nake fata kenan alhajina, wato sanyawar albarkarka, kwana biyu nayi missing naka shi yasa nace tabbas yau zanyi yaƙi da tarin Laifuka a dake haifar da hakan wajen faranta maka da kuma rarrashi ka don ka saka mani albarka, kuma alhamdulillah alamu sun tabbata kwalliya ta biya kudin sabulu" Murmushi yayi yana jinsa sama tamkar su kaɗai ne ke yawo a sararin samaniyar duniyarmu, zai yi magana yaji bugun kofa alamar ana knocking, muryar Meenal suka biyo na kuka haɗe da faɗin "Dady, Dady nakasa bacci tsoro nake ji, pls Dadyna Mommy tazo ta tayani zan kwana tare da ita a ɗakinta." cak Mommy taji zuciyarta ta tsaya mata lokacin da Dady yayi saurin cireta a jikinsa jin abinda shalelen nasa ke faɗa haɗe da miƙewa ya nufi bakin ƙofar, yana buɗewa Meenal ta daɗi jikinsa tana kuka cikin yanayin firgici da tsoro tamkar da gaske, "Sorry Babyn Dady nothing will happen to You matuƙar ina raye kinji ko, yi shiru" Dady ya faɗa yana goge mata hawaye, sai da yaji ta natsu sosai acikin jikinsa kafin ya ɗago yana kallon Mommy dake zaune gefen gado tamkar ruwa sun cita yace, "Mansurah taso kije ku kwanta da ɗiyar taki kinji tsoro take ji, baby kodai har da rigimar taki ce ta motsa?" ya faɗa yana maido kallonsa ga Meenal data wani sukurkurce masa, Cikin taushe duk wata damuwa da Mommy ke ji haɗe da sanyin murya tace, "Alhaji kamar Meenal zan je na kwanta da ita saboda Allah, itama ba ƙaramar yarinya bace shekarar nan zata cika shekaru ashirin cif a duniya, taje tayi addu'a ta kuma saka karatun ƙur'ani a wayarta, hakan zai taimaka mata sosai don nasan batayi ba, amma ni babu inda zan je da mijina zan kwana".
"Dady ka jita ko?". Meenal ta faɗa tana sake fashewa da kuka haɗe da juyawa zata bar ɗakin, a take hankalin Dady ya tashi ya riƙota da sauri yana bata haƙuri sannan ya juya wajen Mommy cikin tsawa yana cewa, "Mansura wai me yasa wani lokacin bakya da tausayi? tsoro fa yarinyar nan tace tana ji idan ke kika haifeta zaki kyaleta ne kice anan ɗin zaki kwana? bana son irin wannan mugun halin da kikeyi fa wani lokacin?". jiki a sanyaye Mommy ta miƙe ta maida hijabinta haɗe da cewa, "Shikenan Allah ya baka haƙuri, tazo mu kwana a nawa ɗakin Allah ya kyauta". sannan tafice ranar ɗakin, Dady ko kallonta baiyi ba yaja hannun Meenal ya rakata har ɗakin na Mommy yana lallashinta, sai daya ga ta shiga sannan ya juya ya koma sashensa ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya tare da lumshe idanuwa yana shaƙar daddaɗan ƙamshin da Mommy ta tafi yanar masa...
*******************
Ciƙin Nutsuwa da haiba irin tashi yasaka kai yafita daga gidan, tafiya ce da aƙallah takai ta mintuna bakwai daga cikin harabar tsakar gidan nasu zuwa waje inda yaje ya tadda aminin nasa, tsaye ya samesa a ajikin motarsa yana dannah wayarsa, ƙarasawa yayi bakinsa ɗauke da sallama ya miƙa masa hannu suka gaisa, murmushi Aryaan yayi haɗe da cewa, "MAM how fa?". sai da Mutallab ya ɗan shafa kansa shima yana jinginawa a jikin motar fuskarsa ba yabo ba fallasa sannan yace, "Fine ya gidan, yasu Mamma?" Murmushi Aryaan ya sake sakar masa yana mamakin miskilanci irin nasa kafin ya buɗe motarsa ya shiga yana cewa, "Su Mamma lafiya kalau shigo daga ciki ko?". ba musu Mutallab ya buɗe gefe ya shiga tare da sauke ƴar ƙaramar ajiyar zuciya yana zaunawa akan kujerar ba tare daya san yayi ba saboda yanda tarin abubuwa suka haɗu waje ɗaya suka tarar masa azuciya tare dasa tayi masa wani irin nauyi, juyowa Aryaan daya jingina jikinsa akan kujerar da yake zaune yayi yana kallonsa jin yanda yayi ajiyar zuciyar haɗe da cewa, "MAM ya naganka haka lafiya dai ko?"
"Nothing" ya bashi amsa cikin basarwa yana jingina kansa a jikin kujerar da yake zaune...
Mutallab Asad
#Tagwaye Biyar
#Nana Diso
#Billy S Fari.
_
Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only
Zaki biya ta wannan account ɗin👇🏻
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*MUTALLAB ASAD MUTALLAB*
(MAM)
NA
BILLY S FARI &
NANA DISO
*SHAFI NA SHIDDA*
_RUBUTUN ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU._
_TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA_
Meenal kuwa Dadynta na juyawa ta saki Murmushi tare da ƙarasowa cikin ɗakin ta jingina a bakin ƙofa tana ƙare masa kallo ɗaya bayan ɗaya, dai-dai lokacin da Mommy data shiga toilet ta rage cikinta tafito tana goge ruwan arwalar bacci da tayo dake fuskarta, Murmushi ta sakarwa Meenal data naɗe hannayenta akan ƙirji tare da harɗe ƙafafuwanta tace, "Ah Meenal me kikeyi a tsaye kuma? ƙaraso daga ciki ki kwanta mana". Mere baki Meenal tayi tana takowa a hankali cikin ɗakin yayin da Mommy taci gaba da shirin kwanciyar baccinta hankali kwance ba tare data bari fuskarta ta nuna ɓaci ran da Meenal ta dasa mata ba, a gaban mirror Meenal ta tsaya tana ɗaukar turarukka designers dake kan madubin ɗaya bayan ɗaya tana dubawa kafin ta juyo ta sake naɗa hannayenta akan ƙirji tana kallon Mommy dake ƙoƙarin hayewa kan gadon tace, "Mom da gaske kikeyi zaki iya kwana tare dani".
"Me zai hana Meenal? Wannan wace irin tambaya ce haka?" Ƴar dariya Meenal ta saki kafin tace, "i thought kawai zakiyi hakan ne saboda Dadyna yayi maki dole, but ko yanzu nasan there's something behind wannan shirun naki, but anyway hakan bai dameni ba, yanda kika ɓatamun rai yau shiyasa nima na saka araina zan yimaki fiye da hakan, maganar gaskiya babu wani tsoro da nake ji a ɗakina kuma babu wani tsoro da naji, kawai bana ra'ayin ki samu farinciki da Dadyna kamar yanda kika hanani samun farinciki da ƙawayena a ɗazu, don haka kada kiyi tsammanin zan iya haɗa lumfashina tare dake balle har na iya kwana kwana waje ɗaya dake, saboda haka bye kiyi bacci mai daɗi". Ta ƙare zance tana juyawa tare da ɗaga mata yatsu biyu.
Murmushi Mommy tayi don dama ko Meenal bata faɗa ba tasan hakan ne bata so shiyasa ta shirya wannan makircin, taso mayar mata da martani masu zafin gaske akan kalamanta na ƙarshe amma sai tayi shiru, ko ba komai tana sane da karin maganar malam bahaushe dake cewa TAFIYAR DAMO..Tamai haƙuri ce, a jiyar zuciya ta sauke daidai lokacin da Meenal ta ƙarasa ficewa daga ɗakin sannan ta ɗan zame kaɗan ta gyara kwanciyarta tana karanto addu'o'in bacci, tunanin abubuwa da dama da suka faru tsakaninsu da ita suka shiga dawo mata a ƙwaƙwalwa kafin bacci yayi awon gaba da ita.
Meenal kuwa kai tsaye ta haye sama abunta ta shige ɗakinta tana dariyar ƙetar yanda taga Mommy ta kwashi ado ta nufi ɗakin mahaifinta, sai gashi cikin mintuna ƙalilan ta tarwatsa komai tabarta da kwanan baƙi ciki a ɗakinta ita kaɗai, kan gadonta ta faɗa ta janyo wayarta ta kira ƙawayenta na ɗazu ta haɗasu conference tana labarta masu abunda ya faru yanzu, dariya suka saka su duka suna sake fasa mata kai akan tayi dai-dai. "kin mun dai-dai Meenal, ai na daɗe ina faɗa maki matan ubannan sam ba kirkine dasu ba, wlh kana yin sanyi zasu rabaka da mahaifinka daga ƙarshe ma susa zaman gidan ubanka ya gagareka, ai yanda na tsani mutuwata ƙawa haka na tsani matar mahaifin ki". Sarsy ce ɗaya daga cikin ƙawayen nata tafaɗi hakan cikin sigar son sake zuge Meenal, sai da Meenal tayi dariya sannan tace, "Kibar shegiya ai sai nasa ta gudu da kaifin ƙafafuwanta, sai na nuna mata ni Meenal ba kanwar lasa bace, duk wani kirkinta da biyayyarta bazasu taɓa yin tasirin da zai sa mahaifina ya dena so na ba ko kuma ya koreni, takun saƙa kuwa yanzu aka fara shi ni da ita, ku dai ku zuba ido ku gani". Yanda Meenal tayi maganar cikin izza ya sasu sakin shewa da dariya, sun san tunda ta daɗi haka to tabbas ƙurar na tafe kuma wasar yanzu aka fara. "Hello Zee wai bakya online ne? Ya naji shiru bakya magana?" Meenal tafaɗa tana ɗan ɓata rai jin tunda aka fara maganar ita batace ko uffan ba, kamar dai ma bata online ɗin, ɗan sauke ajiyar zuciya Zee da gaba ɗaya ke saurarensu tayi kafin tace, "Ina jinku Meenal na rasa abinda zance ne, amma maganar gaskiya hanyar nan da kike tunani ba mai ɓullewa bace kawai ki canza tunani, nace Mommy tana yimaki daidai ba ko kuma akasin hakan tunda ba tare nake daku ba, sai dai ina so kisani itama uwace! K.." kafin ta ƙarasa Sarsy tayi saurin dakatar da ita, "Wait Zee! Don Allah karki ɓata mana rai, so kikeyi ta zauna matar uba na mulkanta tana hanata iko da gidan ubanta? Ai kema kinsan wannan ba mai yiyuwa bane wlh, dama nasan ke baza'a taɓa abu ki gane yanda yake ba, matar uba fa akace! Mtsss kawai katse kira idan bazaki tofa abinda zai faranta mana ba bama son haka".
"No Sarsy barta, na rantse da Allah zan iya haɗawa har ita ɗin saboda itama tasan wannan soki bututun nata ba shigata yakeyi ba, kuma bai isa ya dakatar da ƙudurina akan waccan matar ba.." nan fa Meenal ta nemi maido masifar duka akan Zee, tana jin haka tace, "Allah ya baki haƙuri". Tare da kashe wayarta, Zee itace babbar ƙawar Meenal da suka taso tare tun suna ƙanana, tasan komai akan yanda Mommy tarayu tare da Meenal tun tana ƙarama har zuwa girmanta, sau da dama idan tayi wani abun tana ƙoƙarin lurar da ita amma masifarta kesa ta kama bakinta tayi shiru, a yanzu tana ji Meenal tayi girman da zata iya faɗa mata gaskiya komai ɗacinta akan matar mahaifin nata shiyasa ako yaushe take againsing ɗinta ga wasu abubuwan idan tayi, wanda hakan yasa a yanzu sam basa jituwa da ita ko kaɗan duk da har yanzun suna atare kuma komai tare sukeyi, Meenal najin Zee ta katse wayarta itama ta katse tata cike da ɓacin rai tana jifa da wayar gefe, tafi mintuna biyar a haka kafin ta miƙe ta shiga toilet ta watso ruwa, su Sarsy, Nasmah da kuma Ruky takaici ne ya kashesu ganin yanda Zee ta watse masu plan, ba dan haka ba sun tabbata gobe Meenal zata haɗa masu casu na musamman da zasu raƙashe su kuma samu farinciki.
Washe gari Meenal bata tashi ba sai kusan ƙarfe goma na safe, har lokacin sauran ɓacin ran da Zee ta sakata a daren jiya bai fita ba, miƙewa zaune tayi a tsakiyar gadon ta saki wata irin miƙa kafin ta zuro ƙafafuwanta ta sauko daga kan gadon, toilet ta shiga ta watso ruwa bayan tayi brush haɗe da fitowa ɗaure da towel tana goge kanta, dai-dai lokacin aka turo ƙofa ta ɗago kai tana kallon wacce ke ƙoƙarin shigowa daga ciki, Mommy ce fuskarta a sake tamkar babu abinda ya faru tsakaninsu jiya ta shigo ciki tafara tsince kayan da Meenal ɗin ta cire jiya data watsar tsakar ɗakin da zata shiga wanka kafin ta kwanta, "Morning Meenal, Dadynki na jiranki a palour". Ta faɗa tare da tura ƙofar toilet ɗin nata da niyar saka kayan a washing machine, wani irin tashi taji yanayi ga kayan baccin data cire suma ta zubar a ƙasan bayin, juyowa tayi da ɗan ɓacin rai a fuskarta tace, "Meye haka Meenal, kayan baccin naki ne a ƙasan toilet gashi sai faman bashi toilet ɗin keyi? Wai wannan wace iriyar ƙazanta ce haka kikeyi? Ko baki san gidan wani zaki je bane?"
Dai-dai lokacin Meenal ta gama saka wani ɗamammen wando daya ɗame a jikinta tare da doguwar riga bodyhug data kusa kai gwuiwarta ta matseta sosai, ba tare data tankata ba ta nufi kan gadonta ta yaye duvet ɗin dake kai ta watsoshi ƙasa tare da pillows ɗin dake kai ta miƙa hannu ta ɗauki wayarta, taku biyu tayi zuwa uku da niyar ficewa daga ɗakin taji Mommy ta daka mata tsawa saboda ɓacin rai, "Ke Meenal ba dake nake magana ba, wai me kike son mayar da kanki ne? Mace kike matar wani uwar wasu anan gaba kuma ita mace da kike gani ƴar gyara ce, dawo ki haɗa waɗannan kayan gadon da kika watso ƙasa don yau ba wanda zai gyara maki ɗakin nan, kije ki gama breakfast ɗinki ki dawo na kama maki bazan iya da wannan takaicin ba". Juyowa Meenal tayi ta kalleta tun daga sama har ƙasa sannan tace, "Ke a wa zaki ce haka?"
"Uwa kuma mahaifiya..." Mommy ta bata amsa don har cikin ranta yau take jin takaicin wannan ɗabi'ar tata da bata da alamun gyarawa, amma kafin ta rufe baki taji Meenal tace, "ba dai tawa ba, sai ki bari aduk ranar da kika haifa taki agidannan kibata wannan umurnin". Tana gama faɗin haka ta juya tabar mata ɗakin, da idanuwa Mommy ta rakata kafin tabi ɗakin da kallo, gabaɗaya ya sake haukacewa fiye da yanda ta riskesa saboda hatta towel ɗin data fito wanka dashi da wanda ta goge kanta da jikinta duka anan ta sakesu, toilet ɗin kuwa ga dukkan alama amfani tayi dashi amma ta kasa tsaftacesa ta hanyar data dace shiyasa yake wannan tashin bashi da kuma tsami, "innalillahi wa inna ilaihirrajiun". Ta faɗa jin zuciyarta na wani zakuɗawa lokacin data ƙarasa shiga daga cikin toilet ɗin, a daddafe ta shiga gyarasa tana toshe hanci kasancewarta mace mai tsafta da kuma ta'ammadi da duk wani abu daya kasance mai ƙamshi, ƙamshi shine kusan best abinda Mommy keso kuma ta ɗora Meenal akan wannan turbar, sai dai bata san yanda akayi ba gaba ɗaya bata iya sarrafa shi inda ya kamata ba in ba ajikinta kaɗai ba.
Meenal kuwa da kuka ta sauko ƙasa tunda tafito ɗakinta ta hango mahaifin nata zaune a palour yana amfani da system, bai ji saukowarta ba kasancewar babu takalmi a ƙafafuwanta shi kuma hankalinsa sosai ya ɗauku ga aikin da yakeyi sai dai yaji faɗowar kanta a saman kafaɗarta tana zama kusa dashi, "What! My baby what's wrong with you". Ya faɗa yana ture system ɗin dake saman jikinsa tare da glasses ɗin idanuwansa, cikin muryar kuka Meenal tace, "Dady she hated me so much saboda kasa jiya ta kwana tare dani".
"Baby ban fahimceki ba, she hated you kamar ya?"
Nan Meenal ta kwashe ƙarya da gaskiya akan wai Mommy bata barta takwana a ɗakinta ba kuma yanzu taje tana mata tsawa saboda kawai bata gyara ɗakinta ba kuma yanzu ta tashi bacci, "Share hawayenki Babyn Dady, in har Mansura bata sonki nima bana sonta, idan bata tausaya mako ba tabbas nima zan dena tausayinta, haka kuma matuƙar tace zata riƙa yimaki tsawa a gidan nan to tabbas zata nemi duk wani kwanciyar hankalinta ta rasa, don haka kibarni da ita kin ji ko?" Ɗaga kai tayi kawai tana share ƙwalla kafin yariƙa hannunta ya miƙar da ita yana cewa, "Zo muje kiyi breakfast i have good news for you".
"Gist me Dad pls" tafaɗa tana shagwaɓe fuska, dariya yayi tare da takawa zuwa dining area da ita yana cewa, "Noo har sai kin gama taking breakfast naki tukuna". Ya ja mata kujera ta zauna sannan shima ya zagaya ya zauna wacce ke facing ɗinta.
Da kansa ya zuba mata abincin taci yana yimata fira har ta kammala sannan yace, "Don you know what? Tommorow is your birthday, saboda haka kije ki kama duk inda kike so ke da ƙawayenki kuyi shagali ko nawa ne zan biya da duk wani abu da zaku ci kusha". Ihu Meenal ta saki tare da tasowa tayi hugging ɗin mahaifin nata cike da farinciki, ita gaba ɗaya ma ta manta da gobe ne birthday ɗinta idan ba yanzu da Dadynta ya tuna mata ba, "wow Dady thank you so much i love you". Ta sakesa tare da barin wajen da sauri tana kiran mahaifiyarta a waya, da ɗan gudu-gudu take yawan steps ɗin har mahaifiyarta ta ɗaga wayar, "Hello Mamie tomorrow is my birthday shine baki kirani kika tuna mun ba? Shiyasa nake faɗa maki my Dady is the best tunda gashi shi ya tunatar dani yanzu, don haka akwai shagali sosai Mamie yace na kama duk hall ɗin da yayi mani nida ƙawayena da duk abinda muke bukata zai biya kuɗin". Ta ƙare maganar tana kaiwa step ɗin ƙarshe ita kuma Mommy na kawowa ta gama gyara mata ɗakin tsaf ta kunna bunner da turaren ƙamshi da ita da kanta ta ajiye mata su, amma ga alama data duba bata ma taɓa amfani dasu ba, Meenal na ganinta ta kawo amma ta kasa bata hanya tawuce sai ma tayi kamar bata ganeta ba ta bingijeta da gudu tashige ɗakinta.
************
A ɓangaren Mutallab kuwa duk da yanda ya nunawa Afrah cewa ba komai bane hukuncin da mahaifin nasu ya yanke na canza mata makaranta sosai abun ya taɓa masa zuciya, hakan yasa bayan sallar isha da kansa ya samu mahaifin nasu, cikin girmamawa ya gaishesa ya amsa mashi ciki-ciki, duk da Mutallab yaji kamar ya fasa zancen daya kawosa sai kuma ya basar tare da cewa, "Amm..Abba dama alfarma nazo neman ka idan zata yiyuwa".
"Ina saurarenka meke tafe dakai". Shiru Mutallab yayi yana jujjuya kalaman da zai faɗa ga mahaifin nasu kafin yace, "Akan zancen Afrah ne Dady, nasan cewa tayi kuskure amma don Allah kayi haƙuri kada ka sauya mata makaranta, in sha Allah zata gyara".
Kamar Abba bazai yanka masa ba sai kuma can ya ɗago ya kallesa yace, "Bakin alƙalami ai ya yanke, ko bata faɗa maka Jamil har ya karɓo mata Form a ɗayar school ɗin da zata koma ba ya cike ya gama komai, idan har wannan alfarmarce to kabarta a riga angama, idan kana da wata maganar kafaɗa ina so na kwanta".
Wata gwauruwar ajiyar zuciyar da ba lallai mahaifin nasa ya iya koyo sautin fitarta ba Mutallab ya saki tare da cewa, "Shikenan Abba Allah yasa hakan ya zame mata alkhairi, amma Abba don Allah a samo mata mai lesson hakan zai iya ƙarfafata ya zamana karatun nasu na tafiya daidai dana ƴar uwarta". A wannan karon cikin fushi Abba ya ɗago kai yana kallonsa yake cewa, "Mutallab yaushe kafara zama wanda zai tsara mani yanda zanyi abu acikin gidana, dukkansu ƴaƴanane ina da ikon zartarwa kowanensu hukuncin ɗaya dace dashi, akan me kake tunanin zan nemowa Afrah mai lesson a gidan nan bayan ba haka tsarina yake ba, tafi sauran ƴaƴan nawa ne da kake tunanin zan fifitata akansu? To bazanyi hakan ba kaji ko? In ta so tayi karatu inda na kaita idan kuma taso kada tayi babu wani mai lesson da zan ɗauki mata a gidannan, shikenan ni na zama duk wani nemana da faɗi tashi akanku zai ƙare? Kasan adadin naira miliyan nawa nakashe ga karatunka tun daga kan primary har zuwa jami'ar daka kammala? Wace tsiyar na ƙaru da ita tun da ka gama karatun har kawowa yanzu da kake zaune zaman banza acikin gidan nan? Me samun nagartaccen ilimin naka ya ƙareni dashi? Wace uwar kake tsinana mani da ingantaccen ilimin naka daka samu? Mu koma kan ɗaya ɗan uwan naka Jalil, nawa na kashe masa da sunan samun ilimin ingantacce amma gashi nan gida har yanzu bai kammala ba yana jiran na sake dunƙular wasu kuɗin na bayar, to nagaji da asara dakai da shi ba wanda zan koma kashewa ko sisina, nayi abinda zan iya kuma itama tana kammala matakin j.l.c aure zanyi mata bazan cigaba da ɓannatar da kuɗina ba".
Duka kalaman mahaifin nasu babu wanda ya taɓasa kamar na ƙarshe, aure kuma Afrah, nawa ne shekarun nata gaba ɗaya sha shida fa zuwa sha biyar, ga lalurar da take fama da ita taya zata iya rayuwa a bagiren da baya kusa a tare da ita alhalin bata samu cikakken ilimin da zai iya taimaka mata ba kuma ya iya bata kariya daga ƙalubalen rayuwa da matsaltsalun gidan aure, take yaji wani zufa da damuwa sun lulluɓesa ya ɗago kai daƙyar yace, "Kayi haƙuri Abba ni da ɗan uwana bamu kasa zamowa yanda kake so bane bisa don ranmu, ƙaddararmu ce tazo a haka amma na tabba ta Afrah tasha banban da tamu sosai, ita macce ce iliminta nada matuƙar amfani, don Allah kada ka dakatar da ita.." da zafin nama Abba daya gama kaiwa kololuwar ɓacin rai da kalaman Mutallab ya miƙe yana nuna masa ƙofa, "Get out of here Mutallab". Ya ambaci sunan da ƙarfi duk da kasancewar sunan mahaifinsa ne bai cika faɗar sa ba sai dai ya kirasa da Babana ko kuma babban mutum kafin abubuwa su sauya ya riƙa kiran sunan nasa gatsau ba wani sayi...
#Mutallab Asad
#Ƴan Tagwaye
#Nana Diso
#Billy S Fari.
*MUTALLAB ASAD MUTALLAB*
(MAM)
NA
BILLY S FARI &
NANA DISO
*SHAFI NA BIYAR.*
_RUBUTUN ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU._
_TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA_
*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?*
*INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?”
*KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.*
Mun gwada mun gani 💯
Mun gani mun shaida 💯
Anyi mun gani 💯
MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
GYARAN MAIJEGO
MALLAKAR MIJI KO MATA
SUBULU DA SCRUB
MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
MAGANIN TSUMI
INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯
08142800199
07068558096
___________
*MUTALLAB ASAD*
*PAID BOOK #500*
*TAGWAYE BIYAR*
NA
*BILLY S FARI*
&
*NANA DISO*
5.
Hakan yasa Aryaan ya tayar da motarsa ya ja yabar wajen, a hankali Mutallab ya buɗe idanuwansa daya lumshe ya juyo da kansa yana kallonsa, duk da baiyi magana ba Aryaan ya fahimci ko me yake nufi, don haka ya ɗag masa kafaɗa haɗe da cewa, "A gun Mamma zan kaika ita sai ta tambayeka kome ke damunka tunda kaƙi sanar mani, ko makaho ya kalleka MAM yasan kana cikin damuwa amma shine zan tambaye ka kace mani nothing, na rasa sai yaushe zaka fara ɗaukata a matsayin dani na ɗauke ka". Runtse idanuwa Mutallab yayi tare da dakatar da Aryaan daga tuƙin da yakeyi, sai daya ji ya tsaya sannan yace, "Kai matsalar dakai kenan Aryaan, sai kace komai saika sanar da Hajiya kuma kasan tabbas baza taji daɗi ba".
"Eh mana, ni an faɗa maka ina jin daɗin ganinka acikin irin wannan yanayin ne? Kai ko tsoro baka ji wani ciwon yazo ya sameka?".
"Meke tafe dakai?" ya jefo masa tambayar har lokacin idanuwansa na arufe, "Ban sani ba". Aryaan ya bashi amsa a hasale yana maka masa harara, wanda yayi daidai da lokacin da Mutallab ɗin ke buɗe idanuwansa akansa, murmushi ya saki yana gyara zamansa kafin yace, "Allah ya baka haƙuri maida wuƙar mana". banza Aryaan yayi masa hakan yasa Mutallab yaci gaba da cewa, "Karka damu kawai matsalar gidanmu ce da a kullum ƙara gaba takeyi, a ɓangare ɗaya ga larurar Afrah da duk safiya nake kwana da ita kuma nake tashi da ita". cike da tausayinsa Aryaan ya dafa gefen kafaɗarsa yana cewa, "MAM kaci gaba da haƙuri watarana duk wannan abun zai wuce har yazama tarihin da kai da kanka zaka bada labarinsa, Afrah kuwa muci gaba da yimata addu'a cuta ba mutuwa ba, wlh ina har muna da rai itama sai ka bada labarin wannan lalurar tata ta yau ciwo gobe lafiya, kuma idan ka lura wannan ciwon nata tamkar ruwan dare ne yanzu, mutane na fama dashi sosai kuma ana samun lafiya".
"Aryaan typoid da athma fa akace lokaci ɗaya ajikin mutum, kaima kasan abin ba mai sauƙi bane da hankali zai iya kwanciya bayan hango tarin barazanar da ako yaushe suke yiwa lafiyarta". "Haka ne amma ai ba abinda yafi ƙarfin Allah ko?".
"Ehmm.
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 54