sani ya Mutallab, wai kullum sai kayita tambayata ina Afrah sai kace ita wata ƙaramar yarinya ce". Dama ita gaba ɗaya fitsararriyace ba shiba kowa ma tagama renawa sai taga da gaske yakeyi take ɗan jin tsoronsa, don haka ta bashi amsar kai tsaye tana wani haɗe fuska, zazzafar iska ya fitar ta bakinsa yana shafa goshinsa tare da son rarrashin zuciyarsa dake neman hasala, musamman kukan su Khalid daya cika masa kunne da sukeyi akan ya hana su barin palourn ya ɗago kai a hankali yana cewa, "Ke ba ƴar uwarta bace Jiddah? Meye laifi idan na tambayeki ita? Ko kina da wacce tafita ne da kike buƙatar na tambaya sama dake?" Cikin rashin kunya Jiddah tace, "Tabɗijan..". tana mere baki tamiƙe da sauri tana barin wajen cikin ƙunƙuni take cewa, "Meye haɗina da ita ni ina ƴar mowa ita kuma ƴar bora? komai Afrah sai kace ita kaɗai ce mai lumfashi adoron duniya, ni bansan inda take ba kaje ka tambayi wata, na gode Allah ma da Abba ya raba mana makaranta, ko a haka kaɗai ansan akwai tazarar banbanci tsakaninmu da ita, ta ƙarasa maganar tana shigewa part ɗin Aunty Amarya dake ƙoƙarin fitowa jin kukan yaran nata, yana ganin ta nufo palourn tana tambayar yaran ubanwa ya taɓasu ya ɗauke kansa kawai ya haura sama zuwa ɗakin Afrah, yana jin Aunty Amarya na masifa tare da lailayo zagi tana ɗura masa yayi banza da ita yayi tamkar ma bai jita ba, cikin natsuwa ya ja ya tsaya daga bakin ƙofar ɗakin Afrah haɗe dayin knocking, Afrah dake kuka tayi saurin goge hawayen ta tamiƙe taje jikin ƙofar tacire key ɗin sannan ta buɗe masa tana raɓewa gefe, kallonta ya tsaya yi na sakanni yana karantar yanayin da take ciki kafin ya shigo cikin ɗakin har lokacin idanuwansa na akanta, gefen gadonta ya fara ƙoƙarin zaunawa idanuwanta suka sauka wajen data tashi tayi steaming ɗinsa da jini, zaro idanuwa tayi da sauri ta rugo ta shiga gabansa ta maza ta zauna wajen tana kiran sunansa, " Yaya..." Sai kuma tayi shiru ta kasa ci gaba saboda hawayen da suka fara sauko mata, "Me yafaru Afrah?" Ya faɗa yana zuba mata idanuwansa da suka ɗan sirka da ɓacin ran da yake ciki saboda abinda yafaru kafin ya hawo saman cike dakewa da jarumta da kuma son danne abinda yake ji acikin zuciyarsa don kada ta fahimta, sinne kanta ƙasa tayi ta kasa amsa mashi sai hawaye dake sake saukowa akan kyakkyawar fuskar tata, iska ya furzar gefe tare da kausasa muryarsa yana cewa, "Wai menene Afrah? Kina so ki tayar mani da hankali ne da kike wannan kukan?" Cikin sheshshekar kuka tashiga girgiza kafin tace, "Ya wai Aunty Amarya ce muna zaune a palour ta koroni wai naje na bata waje ina ƙureta da idanuwa kamar na mayya..." Kafin ta ƙarasa Mutallab dake tsaye ya janyo kanta zuwa jikinsa yana runtse idanuwa saboda baya son saurarar sauran kalaman da aka jefeta dasu yace, "enough wannan ai ba wani abu bane, a kaf gidan nan babu wanda yayi kyawonki Afrah watakil shiyasa Aunty amarya ke faɗar hakan, kiyi haƙuri ta faɗa ne kawai amma ai ke ba mayya bace ko". Ya ɗago kanta yana kallon fuskarta dake jiƙe da hawaye, ɗaga masa kai kawai ta iya yasa hannu ya goge mata hawayen sannan yace, "Yanzu faɗa mun meye yasa kika hanani zama a bakin gadonki? Kinyi wani rashin gaskiyar ne?" Ya ƙureta da idanuwa don son gano dalilinta nayin hakan, sadda kanta ƙasa tayi ta kasa magana saboda da kunya, ji take kamar bazata iya faɗa masa ko meye ba amma sanin batada wani sama dashi dazai jiɓinci lamurranta yasa dole tasanar masa da gaskiya, itama bata ma san wajen ya lalace ba data gyara kafin ya shigo, jin ta yimasa shiru ya sashi tsuke fuska tare dasa hannu zai miƙar da ita tsaye tayi saurin noƙewa tana cewa, "Am Sorry yaya don Allah kada ka tayar dani zan faɗa ma, nayi steaming ne agun". Taƙare maganar tana duƙar da kanta ƙasa cike da jin kunya, shi kuwa cikin rashin damuwa da hakan yace, "And so? Meya hana ki gyara kanki yadda hakan bazata faru ba?"
"Banda always Yaya kuma na tambayi Aunty ta bani kuɗi nasiya ta hanani wai na nemi ɗan kwalina na saka.." shiru Mutallab yayi tare da fiddo wayarsa yayi Googling yanda ake amfani da always sannan ya kira Jalil sukayi magana ya kashe wayar". A gefenta ya zauna ya ɗauko tissue ɗin dake ajiye agefen gadonta cikin kwali ya ɗibi mai yawa kamar ƙwaya bakwai ya lunkata sau biyu tamkar shape ɗin da yaga always sannan ya miƙamata yana cewa, "A duk lokacin da hakan ta koma faruwa kiyi amfani da wannan tissue ɗin tunda tana da ƙwari kuma ba jimawa zaki barta tayi ajikinki ba ki saka kafin kisamu always ɗin kuma daga yanzu duk abunda kike buƙata ki sanar dani in sha Allahu zan siyo miki na kawo maki, kada ki kuskura goma ga wata yayi baki sanar dani ba idan always ɗin ta ƙare kuma kada kisake tambayar kowa kin ji ko?" Ta ɗaga masa kai tana ƙoƙarin yin godiya ya ɗora yatsansa akan bakin nata, dole takama bakinta tayi shiru batare data iya cewa komai ba, mintuna biyu yana sake bata shawarwari akan yanda zata riƙa kula da kanta idan tana period da tsaftace jikinta, Jalil ne ya turo ƙofa ya shigo riƙe da leda baƙa a hannunsa ya gaida yayan nasa shima Afrah ta gaishesa sannan ya miƙa masa ledar ya fice daga ɗakin, miƙawa Afrah ledar always ɗin Mutallab yayi yace taje ta gyara kanta sannan ya miƙe zai bar ɗakin ta riƙo hannunsa tana cewa, "ya Mutallab wai gobe zanfara zuwa school ɗin da aka canza mani inji ya Jamil, yace zai kawo mani uniform da safe". Murmushi ya saki tare da shafa kanta yace, "Karki damu Afrah Allah yasa hakan yafi zama alkhairi, in Sha Allah zakiyi alfahari da ilimin da zaki samu a makarantar fiye da waccan ɗin da aka cireki kin ji ko" Ta ɗaga masa kai zuciyarta nayi mata wani irin zafi ganin tabbas-tabbas dai an fitar da ita makarantar da ƴan uwanta keyi da take tsananin so zuwa wata dako kwatar kuɗin da ake biya masu awaccan ɗin batayi ba, ganin zatayi kuka yasa ya Mutallab duƙawa a gabanta ya kamo hannayenta yana kallon yanda idanuwan nata suka cika taf da hawaye, shiru yayi naɗan mintuna kamin yace "Kina so nima nayi kukan ne Afrah? Dagaske ganin kina kuka zai iya saka zuciyata taƙi daɗi Afrah saboda ku amanar mahaifiyarmu ne agareni, farin cikin ku shine farin cikina, kiyi haƙuri ba yanda zanyi ne shiyasa nakasa hana hakan faruwa, dake da ni duka ƴaƴane bamu isa mu kaucewa hukuncin mahaifinmu ba". Ganin zallar damuwa akan fuskarsa da cikin idanuwansa yasa Afrah ta goge hawayenta tana ƙaƙalo murmushi don son faranta masa, Murmushin shima ya sakar mata haɗe da cewa, "Yawwa ko kefe! Ɗazu kinyi zancen Aunty Amarya takoroki daga palour, ina so daga yanzu idan hakan tafaru kije gun jalil kuyi fira ko kizo gurina musha firarmu har mu gaji, idan ma bakya son firar ki ɗauki haddarki kibiya, we are all here for you ni da Jalil, so feel free and be happy b'cous you're always princess indai muna raye kin ji ko?"....
Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only
Zaki biya ta wannan account ɗin👇🏻
0020428430 Ishaq Fatima A GTBank
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya
07040402435,
0903 056 9336
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
#Mutallab Asad
#Ƴan Tagwaye
#Nana Diso
#Billy S Fari.
*MUTALLAB ASAD MUTALLAB*
(MAM)
NA
BILLY S FARI &
NANA DISO
*SHAFI NA TAKWAS*
_RUBUTUN ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU._
_TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA_
Mutallab yaƙare zancen yana jan kumatunta cike da son sakata farinciki, haka kuwa akayi take ta saki wani ƙayataccen murmushi saboda yanda kalaman nasa sukayi mata daɗi sosai tare da faranta zuciyarta".
"In Sha Allah ya Mutallab na daina bari komai ya ɓata mani rai saboda nima ina so naganku cikin farinciki." miƙewa yayi haɗe da cewa, "Allahamdulillah haka nake son ji, Allah yayi miki Albarka yasa ki ɗauka a sanadiyar sauyin makarantar da akayi maki, ki samu ki gyara jikinki ki kwanta seda safe, karki manta kiyi addu'ar bacci kuma kira batar kin kwanta da alwala, tare da gyara gadonki kamin ki kwanta". Ta ɗaga masa kai sannan yafice daga ɗakin yana rufo mata ƙofa ita kuma ta shiga toilet don gyara jikinta.
******
A ɓangaren Meenal kuwa da kallo Mommy tabita kafin ta sauka ƙasa fuska a sake tana cewa, "A'ah Dadyn Meenal yau wace irin fara'a ce haka Meenal takeyi har take bangajeni sai kace wacce aka yiwa albishir da gidan aljanna". Ta ƙare zancen tana ƙarasowa wajen Dady daya haɗe fuska ya ɗauki system ɗinsa zai bar palourn, juyowa yayi da dukkan jikinsa yana yimata wani kallo haɗe da cewa, "Koma meye bai shafeki ba tunda irin wannan farincikin ne bakya ƙaunar ki ganta aciki".
"Subhanallahi me yayi zafi haka Alhaji? Tamkar fa ƴata na ɗauki Meenal to me zaisa naƙi farincikinta? don Allah kadena iri wannan zancen sam baida ma'ana". Ta miƙa hannu zata karɓi system ɗin hannunsa kamar abin da yayi ɗin bai ɓata mata ba, saurin janye system ɗin yayi dake hannunsa ya juya ya wuce abunsa Mommy ta bishi da kallo tana ƙara jinjina lamarin da na ganin koda yaushe anyiwa Meenal ba daidai ba, Meeenal kuwa tana gama waya da mahaifiyarta ta tashi ta ɗauki ɗan ƙaramin mayafinta da iyakarsa ya rufe mata wuya ta naɗa sannan ta saka wasu shegun takalma masu matuƙar tsini ta ɗauki ƴar siririyar handbag ɗinta swag ta rataya daga saman wuyanta zuwa ƙarƙashin kafaɗarta, duk da shiga ce tayi wacce bata mutunci ba sosai tayi mata kyau wacce da zata saka kayan da suka rufe mata jiki to da zatafi hakan yin kyau sosai, wani irin farinciki da nishaɗi take ji tare da hasaso yadda shagalin birthdayparty ɗin nata zai kasance, cikin sauri-sauri gudu-gudu ta shiga sakkowa daga benen batare da takalli inda Mommy take ba tana gyara dining area inda Meenal taci abinci, kai tsaye ta nufi hanyar daƙin Mommyn ta shiga ta ɗauko muƙullin motarta data gani kan mirror ta fito da sauri saboda mahaifiyarta da take kira Mamah tace tayi sauri taje ta sameta su tsara yanda shagalin zai kasance a turawa Dady kuɗin yabiya kafin Mommy ta hana, koda ta faɗi hakan murmushi kawai Meenal tayi don Mamah bata san Mommy ɗin bata isa sawa ko hanawa ba akanta in dai a wajen mahaifinta ne, tana ƙoƙarin ficewa Mommy data fito kitchen ta kallet tana cewa, "A'ah!Meenal ina zaki je kuma da wannan shigar? Ko baki ga yadda surar jikinki duka ta bayyana ba?" Wani banzan kallo Meenal tayi mata haɗe da cewa, "Are you to tell me yadda zanyi shiga? Who are you? Wane matsayi kika dashi ko kika dauƙi kanki a wajena da har kike da wannan courage ɗin? Look kina shiga life ɗina da yawa fa!"
Lumshe idanuwa Mommy tayi tana kiran sunan Allah acikin zuciyarta tare da jin zafin maganganun da Meenal ke faɗa kafin tace, "Meeenal wai meke damunki ne kwatakwata baki san yanda zakiyi magana dana sama dake ba? Kinfi kowa sanin matsayinsa agunki tunda ni ba sa'arki bace, ni ɗin uwace dako kina so ko bakya so na gyara miki ɗabiunki, tarbiyarki har ma da gobenki?" Ɗibarta Meenal tayi ta watsar gefe tanayi mata kallon sama da ƙasa haɗe da cewa, "Idan haka ne ki dakatar dani ko kuma kiyi maganina in zaki iya mana, da kike zancen wata uwa ai ke ba uwata bace, nan gidan ubana ne dole kibarni nayi yanda nake so kuma ki gaggauta ficewa rayuwata" ta ƙare zancen tare dasa ƙafa cikin fushi ta ture ruwan mopping ɗin da ƴar aiki ke faman goge tiles ɗin palourn suka zube ta ja tsaki yanar wajen, "Meenal.." Mommy ta faɗa da ƙarfi cikin ɓacin rai ganin abinda tayiwa ƴar aikin da tun ɗazu ta taƙarƙare tana aikinta, juyowa Meenal tayi ta nunata da key ɗin hannunta na mota ta zaro glass ɗin idanuwa dake maƙale ajikin wandonta ta maka a fuskarta sannan tace, "Rubbish". Ta juya ta wuce abunta, kallon Mommy mai aikin tayi ganin yanda abun ya ɓata mata rai itama tace, "Kiyi haƙuri Mommy da halin Meenal, nasan sam bata kyautawa amma komai zai wuce.."
"To munafuka, dake ake gulmar ƴata saboda ba kida mutunci ko? to maza jeki kitattara inaki inaki kibar mini gida daga yau na koreki, butulu kawai da batasan halacci ba". Dady da fitowarsa kenan sanadiyar jin yanda Mommy ta kira sunan Meenal da ƙarfi cikin ɓacin rai yaji abinda mai aikin kefaɗa shima ya faɗa, da sauri ƴar aikin ta zube ƙasa tana roƙonsa yayi haƙuri yace, "Ita ta jamaki don haka kitattara inaki-inaki kibar gidan nan kafin a haɗa baki dake a cutar mani da ƴa tunda ba'a ƙaunarta". Yana gama faɗar haka ya juya ya koma cikin ɗakinsa ransa a ɓace, Mommy kuwa wani baƙin ciki ne ya sake taso mata ganin irin ɗanyen hukuncin da maigidan nata ya yanke, cike da tausayi ta kalli mai aikin tata dake faman rusar kuka ta shiga bata haƙuri sannan ta shige ɗakinta ta haɗo mata kaya da kuma kayan kwalliya da kuɗin da zasu isheta taja jari ta bata tace ta tashi ta tafi tare da cemata duk sadda take buƙatar wani abun kai tsaye tazo ta nemeta zata taimaketa.
_(🤔Ikon Allah, Dady wannan wane irin ɗanyen hukunci ne haka, daga bada haƙuri sai ka kori mata wato an taɓa ƴar gwal? Mu dai juri zuwa rafi..🏌️)_
Kusan mintuna goma Mommy ta ɗauka tana kallon hanyar da mai aikin tata tabi tafita, wannan wacce kalar masifa ce? Daga wannan sai wancan? Tabbas ta yarda Meenal da ɗan uwanta sune babbar jarabawar ta a duniya, Ahankali ta furta "Allahumma laa sahla illa maa ja'altahu sahla wa anta taj'alil haznah iza shi'ita sahla,Ya Allah kashiga lamarina kada kasa wannan yaran su ƙurar haƙurina har nakai ga gazawa su rabani da gidan aurena".
Ta ƙare zancen tare da juyawa ta koma cikin ɗakinta, tana shiga ta samu wayarta na ƙara ta zauna agefen gado ta ɗauki wayar dake ajiye agefen gado, bin wayar tayi da kallo ganin sunan MY LOVE na yawo akan screen ta shiga tunanin ko lafiya ƴar tata tilo mai suna Asiya ke kira da bazata wuce shekaru ashirin ba aduniya tare da tuna lokacin data barota agidan mahaifinta tana ƙanƙanuwa amma duk da haka bata rasa samun tarbiya mai kyau ba daga gurin mahaifinta danshi baya bari sam soyayyar ƴaƴansa tarufe masa idanu, duk da ba shida hali sosai bai gurɓata tarbiyar yaransa ba ko kaɗan yana sonta tana son shi ƙaddara ce kawai ta rabasu sanadiyar sakacin da yake tunani tayi tabar ruwan zafi sun ƙone masa ɗansa na fari alhalin bata san hakan zata faru ba, yana son ƴaƴansa sosai kuma tsaye yake ga tarbiyarsu sai dai ko kaɗan baya da haƙurin wani abu ya taɓa masa su ko kaɗan, hakan yasaka cikin fushi yace tatafi ya sawaƙe mata wanda har yanzu yana nadamar aikata hakan, a ɓangarenta kuma haɗuwarta da mahaifin su Meenal sai take ganin kamar sakayya ce Allah yayi mata, tana wannan tunanin har wayar da akafi gaba da kira ta tsinke sau biyu ana sake kira, sake shigowar karin akaro na kusan huɗu yasa tunaninta katsewa tayi saurin ɗagawa, runtse idanuwa tayi jin kukan Asiyar tace, "my love lafiya?"
"Mommy mama ce?" Ajiyar zuciya Mommy ta sauke jin ba wata matsalar bace daban tace, "Haba ƴar gidan mama yau kuma meya haɗaki da ita duk tsantsar kulawarnan da take baki". Share ƙwallon Asiya tayi kafin ta ɗan turo baki tace, "Mommy mama tafara nunamin banbanci agidannan, gasu Yaya Shukura a zaune zata ce na tashi naje na ɗora girki, kuma a gabana Baba ya siya masu sabuwar waya da nayi magana a canza mani tace baza'a canza ba ai bazan haɗa kaina da su shukura ba wai sun girmeni nayi haƙuri idan na kai shekarunsu sai acanza mini, Allah Mommy nagaji kofa baƙo su shukura sukayi ni mama ke cewa nayi masa girki na haɗa masa snacks, wlh Mommy mama tafara mugunta". Sosai Mommy ta danne zuciyarta dajin wuɗannan kalaman da ƴarta ke faɗa da batayi tsammanin jinsu a bakinta ba kafin tace "Allah kayiwa mama albarka Asiya, in dai haka shine muguntar da takeyi maki Allah yasa tayi mako fin haka nagode mata sosai". Sai data ɗan nisa sannan taci gaba da magana cikin ɓacin rai tana cewa,"Haka kika zama Asiya ban sani ba? Yaushe kika canza kike nema kiyiwa rayuwarki illa? Fisabilillahi Asiya duk ƙoƙarin da mama keyi akanki bakya gani har kinyi shekarun da zaki fara tunanin tana cutar dake?wace irin hidimace batayi Mali ba a rayuwa wacce koni dana haifeki iya hidimar da zan iya yimaki kenan, sannan da kike maganar irin wayar su shukura ke sa'ar suce? Nace ke sa'ar su ce? Shekara nawa kika san Shukura tabaki, shekara biyar fa Asiya don me baza kiyiwa kanki adalci ba? Wa yake hure maki kunne kika manta alkhairi mama awajenki, ta baki kulawa ta siya maki suttura harma da ingantacciyar tarbiyar da nake alfahari dake haba Asiya, ashe gyara kayanka zai zama sauke mu raba?" Cikin shagwaba Asiya tace "A'a Mommy amma...." "shiiii....bana don wannan zancen saboda ba hujja bace a wajena, komai fa iri ɗaya take miki da yaranta to me isa zakiyi tsammanin banbanci daga wajenta?, To bari kiji ni tayi mani daidai kuma Allah yabiyata da alkhairi, maganar ba tada kirki da kike faɗa gayamin ranar data taɓa zaginki? Wallahi kiji tsoron Allah samun mariƙeya irin matar ubanki sai antona, kuma girki dan tace kiyi ai gata tayimiki yau idan kikayi aure bakisan girkin nan kaɗai zai karamiki daraja da ƙima agurin mijinki ba? Kin fiso ki zauna sakaka babu kwaɓa? Kinfiso ku zauna babu gyara? Wallahi wallahi kar nasake ji kar kuma in ƙarajin wannan maganar abakinki, dan kema bazakiji daɗi ba idan yau aka gayawa mahaifiyarki abunda kike gayawa mahaifiyar wasu yanzu." Sosai Asiya tafahimci kuskurenta kuma nasihar mahaifiyar tata ta shigeta, cikin sanyin murya tace, "Mommy kiyi haƙuri bazan sake ba, daman ƙawatace take cewa wai Mama bazata taɓa sona ba saboda matar ubana ce nadaina yarda da ita, wai kulawar da take bani duk na munafurci ne bata ƙaunata." "Innalillahi wa inna ilaihirrajiun, to kar nakoma ji wannan ƙawar banyarda da ita ba a canza ta bana sonta saboda ba mutuniyar ƙwarai bace kinji ko? Mama yau ko dukanki takeyi ta zageki ta gama maki komai tunda ta baki kulawa da tarbiyya, ki bata girmanta na matsayin matar mahaifinmu koda tayi wani son rai daga baya kanta tayiwa kuma ita da Allah, don haka irin lafazin nan da naji abakinki yau kada na sake jinsa har abada kinji ko". "To Mommyna kiyi haƙuri ban komawa, ina Dady yake Rannan ya aiko mana da super nida su yaya shukrah" Da mamaki Mommy tace "yaushe kenan amma ko ki sanar mini?"
"Mommy nazata kin sani fa shiyasa ban gayamiki ba, last week ne ya aikomana da ita".
"To kun gode Allah ya saka masa da alkhairi, nima zan yimasa godiya, ina fatar kuma ba'a biyewa samari ana shashanci ko?".
"Eh Mommy". Asiya ta faɗa tana dariya cike dajin kunyar mahaifiyar tata, murmushi Mommy tayi haɗe da cewa, "Yawwa haka nake so, ki kama kanki ki kama mutuncinki kinji ko? Duk wani saurayin da zaizo yace sai yataɓa jikinki sannan zai soki to tabbas mayaudari ne kiyi nesa dashi, Duk iya shegen fir'auna da kika ji daya tashi aure mata tagari ya aura, don haka kada kiyi tsammanin biyewa saurayi ya ɓata maki rayuwa kuma kisa ran zai yarda ya aureki, Ki zama mutuniyar kirki ki kuma ji tsoron Allah aduk inda kike kinji".
"In sha Allahu Mommyna, zan shiga lecture yanzu inna fito zan kiraki".
"Karki damu ai mun gaisa ubangiji Allah yayi muku Albarka yakuma baki saukin fahimta amakarantar yayi miki tukuici da miji nagari keda ƴan uwanki".
"Ameen Mommyna nagode sai anjima." Asiya ta faɗa tana kashe wayar, shiru Mommy tayi tana mamakin kyautar da Dady yayiwa su Asiya ba tare data sani ba duk da tashin hankalin da suke ciki. (Ai dama a rayuwa duk kalar haƙurin da macce keyi da namiji tako wace fuska yana sane da hakan, kawai wasu abubuwan e dake cikin zuciyarsa ke hana ya nuna mata jin daɗinsa amma zaiyi ta amfani da hanyoyi daban daban ya riƙa appreciating nata, don haka mata mudena ganin haƙurin da mukeyi da miji ko ƴaƴansa ko iyayensu da danginsa kamar yana tashi a banza, wlh amfaninsa na tare damu takowace fuska).
Mommy na ajiye wayar taji alamun anturo ƙofa, hakan yasata ɗaga kanta tana faɗin, "sannu da gida Dady yanzu make cewa na shiga wajenka.." kafin taƙarasa ya ɗaya mata hannu yana yimata wani irin kallo dake cike da tuhuma kafin yace "Mansurah kenan! da wa kike waya haka naji sai faman shimata albarka kikeyi?" Murmushi tasaki ba tare data kawo komai aranta ba ta amsa masa da cewa, "Asiya muke magana har take faɗa mani ranar ka aika masu da saƙo ban sani ba, angode sosai Allah ya saka maka da alkhairi ya ƙara buɗe ya shirya mana zuri'a kuma yayi masu albarka". Wannan addu'ar da Mommy tayi ita ta hanawa Dady ƙorafi da maganar da yayi niyar yaɓa mata akan ƴarta da yaji tana ta shimata albarka, duk da haka sai ɗaya ce, "Da haka kike sawa Meenal albarka tare da kwantar mata da murya bakya yimata ihu Mansurah ai da baza muyita samun saɓani ba, amma da yake bakya kaunarta banda baƙar magana da kike yaɓa mata a gidannan da yimata ihu ba abinda kikeyi, ɗazu fita zatayi amma saboda ta tare maki wani abun a gidan nan ko Allah yadawo lafiya banji kinyi mata ba abakinki, yanzu kuwa da yake ƴarki ce tun daga cikin naji addu'oi kala-kala da kike yimata, Allah ya kyauta ni nafita". Ko kaɗan Dady bai fahimceta ba amma ako yaushe bata manta Meenal a addu'ar ta kawai faɗa gyara kanki daya fi ganin tana yimasa yake gani kamar ihu ne takeyi matan, cikin nuna damuwarta da tsayar da maganar karta girmama tace "Ranka yadaɗe kayi haƙuri Allah ne sheda ban taɓa bambanta Meenal da Asiya ba a wajena, yanda nakeyi mata addu'a haka nakeyi mata itama, duk wani abu da kaji kamar inayi mata ihu akansa to gyara kayanka ne nake yimata, amma kayi haƙuri in Sha Allah zan kiyaye tare da ƙara yimata addu'ar fiye da wacce nakeyi, Allah ka shiryar mana dasu duka" Kallonta yayi yace, "Himma kamar da gaske Mansura, da dai bansan halinki ba akan Meenal da yanda kika tsaneta, Allah dai ya kyauta". A sanyaye ta amsa masa da Amin saboda yanzu bata san kuma me zata sake cemasa ba, shi kuwa ya kaɗan kai tafiya cike dajin zafin irin rashin son da yake ganin matar tasa nayiwa ƴarsa.
*****
Kana ganin yadda Meenal take driving ɗin zaka fahimci babu Nutsuwa sam atattare da ita saboda wani irin sauti dake tashi acikin motar na waƙar datake ji ta davido tanabi tana ihu sai ka rantse itama mawaƙiyarce, bata fi mintuna ashirin da biyar da fitowa daga gidan mahaifin nata ba ta iso bakin ƙofar gidan kakannin nata ta danna wani mugun horn daya kusa kiɗimar da mai gadi ya shiga yawo a harabar tsakar gidan saboda firgici ba tare daya buɗe gate ɗin ba har sai daya sake jin ta sake danna wani horn ɗin da ƙarfi ba tare data ɗauke hannunta ba sannan ya nufi bakin gate ɗin ya wangale mata ƙofa, da mugun speed ta shiga cikin gidan don da kaɗan ta buge maigadi sai da yayi wani irin tsalle ya koma gefe da sauri, dariya ta saki tana cewa, "village man, ai dama ka tsaya na takaka na taka banza don ba abinda za ayi".
_(Anya Meenal ba abinda za ayi? Sai kace kin take dabba don mahaifinki nada kuɗi, to ko zaki gwada mu gani ne?😜)_
Domin biyan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 54