asanar da MAM."
Ko da zance ya isa Abba sai da gabansa ya buga jin abunda yafaru Amma dayake umma na kusa dashi sai ta canza masa tunani tafaɗin " Ai daman dukiyar haram bata ƙarko, zaaje adawo ne sai ta lallaci nifa ko tausayinsa daya banji ba, to yanzu kudin mutane da ya haɗa naga ta yadda zai biyasu." Abba ne yace " Shiyasa nace masa babu ruwan saboda biyar dina bazanyi belinsa ba." Ita dai Anty amarya batace komai ba duba da yanzu abban bayason koda maganarta ne shiyasa ta kwantar da kanta agurin umma dantaga idan tabiyewa zuciya tsaf zai tafa mata taƙardar saƙinta ahannunta."
****
Kasancewa daga siyayya suke sunje jidda sannan sunje wasu kasuwannen sun dai danyi siyayya inda Afrah tace yasarar mata zanin gado itama sai ta siyar yace to badamuwa duba da itama amal tana taba kasuwanci, ko da suka dawo haka kawai yaji gabansa na yawan faduwa duk da hannunsa dauke yake da carbi yana tasbihi dan baccin da yayi gefen gadonsa ne yasashi tashi a firgici yana kallon umar dake kusa dashi. " MAM lafiya kuwa umar yafada yana kallonsa?" " bakomai kawai mafarki nayi mara dadi ne." " To kayi addu'a yanzu mana." Shiru yayi yashiga karanto addu'oin." Wayarsa ya buɗe shigar da zaiyi yaga BBC sun dora abu ganin sunansa yasashi saƙin wayar jiƙinsa na daukar rawa umar Naganin haka yayi saurin Nufoshi ganin zai wadi yace " Lafiya MAM dauka yayi yasaka salati Jin sautin kukan afrah tana buga daƙin yasaka mutallab kokarin mikewa Amma yakasa hakan yasa umar budewa Afrah tashigo tana kuka sosai shima bashida zabi awannan gabar da ya huce yayi kukan ko zai samu sanyi cikin ransa, innalilahi wainna illahirrajiun yake ambata Nan yashiga kiran sunayen yana fadin
اَللّٰهُمَّ لَا سَهْلَ إِلَّا مَا جَعَلْتَهُ سَهْلاً، وَأَنْتَ تَجْعَلُ الْحَزْنَ إِذَا شِئْتَ سَهْلاً
Itace addu'ar da tashiga maimaita har sai da umar yasamu yayi musu wa'azi sannan Afrah tayi shiru shikuwa Mutallab zazzabine ya rufeshi mai zafi dan acikin daren ma sai da duka Nufi asubuti.
*********
Washegari haka manyan kasuwa dakejin haushin mutallab suka shiga gurin madam Kate yar china nan suka shiga sukar Mutallab ta'inda indai ta dauki sukar to tabbas zata kwabe musu ita dashi wani daga cikinsu yace " Madam ai mungayamiki watarana yaronnan sai yaci amanarki yanzu gashinan har container dinki sun kone ance kuma sunyi 50. Mamaki bai cikata sosai ba dan takarancu halinsu sosai sai cemusu tayi " Bana bin Mutallab asad ko ficika saima kudinsa dake agurina Mutallab gabadaya kasuwannin ku yana da shago hatta waken suya yana fitar dashi daga kasar nan da zobo kuma yanada rumfuna acikin kasuwar ba sana'a daya yakeyi ba, idan bakusaniba yau kusani wannan Yaron Allah yariga ya kafashi idan da hannunku ma a wannan abun to tabbas bazaku iya karyashi ba." Sosai hankalinsu yatashi cike da borin kunya suka bar offices dinta.
****
Sosai yawada yayi sanyi Amma addu'ar da yayi yasanya masa Nutsuwa da yadda aryan da jalil ga umar dake kwantar masa da hankali ga Afrah da ya lura ciwonta nason tashi ganin sa cikin damuwa shiyasa yayi gefe da komai idan ya keɓanta yasha kukansa yana gayawa Allah.
Kwanakin su Nashiga washigari suka baro kasar saudia daga nan suka suka wuce kasar Niger, bakaramin kewar su Amal sukayi ba bama Umar da suka shaku sosai yanzu shima, a babban birnin ƙasar wato Niamey suka sauka a babban filin tashi da saukar jirage na Diori Hamani International airport, suna sauka ya tari mai taxi, duƙo da kansa mai taxi yayi cikin yarensu na ƙasar dan a kallo ɗaya zaka ɗauka suma haihuwar ƙasarne ya tambaye su inda zasu je, " où vas-tu " shiru Mutallab yayi kamin ya buɗe wayarsa ya duba address din da yarubata ya nuna masa. Mamaki mutumin yayi dan inda zasuje din fitattacene akasar tasu dan yataɓa siyasa tunanin address ɗin da Tante Sajida ta bashi kafin can yace, . Yanda ya faɗi sunan cikin ƙwarewa ba ƙaramin kyau yai da bakinsa ba, mutumen yai murmushi tare da fitowa ya karɓi kayansu ya buɗe Boot ɗin motarsa ya saka sannan ya buɗe masu baya suka shiga, Afrah kuwa sai faman washe baki takeyi tana jin wani irin matsanancin farincikin ganinta a mahaifar mahaifiyarta da bata taɓa zuwaba a hankali tasa hannunta ta laƙamo na ya Mutallab daya jingina kansa a bayan kujerar da yake zaune ya rufe idanuwansa yana tunano labaran da mahaifiyarsu ke bashi akan ƙasar tasu, kama da kyan wuraren cikinta har zuwa tsarin garuwa da gine-ginen dake ciki da sauran al'adunsu, tabbas batayi ƙarya ba ko akan cikin filin jirgin da suka sauka har zuwa kan haryarsu da suka kamo ya tabbatar da hakan, musamman yanzu da ko ina ya sake ƙawatuwa da samun gyara fiye da shekarun baya lokacin da tana raye, kanta ta ɗora a saman kafaɗarsa tana rumƙe hannunsa sosai data saƙalo acikin nata haɗe da cewa, "Ya Mutallab how i wish tare muke da Mamie da Ya Jalil adaidai wannan lokaci, na tabbata da zamufi samun farinciki sosai Ya mutallab danAllah karkayi mun fada danAllah kadaina tunani zuciyata tana mun ciwo idan naganka a damuwa inshaa Allahu wannan iftila'in da yasamu dakai sai yazama alkhairi" .
"Everything happened for a reason Afrah, saboda haka kada mukasance masu tuhuma ko kuma ganin Allah bai yimana dai-dai ba cikin rayuwarmu, haka da Allah ya tsaro mana shine mafi alkhairi, ɗan haka muci gaba da yiwa Mamie addu'a kin ji ko? Sannan batun shagunana Allah yafini sanin daidai da banidasu yabani yanzu dan yakarba sai na kasance jahili? Allah ke bayarwa ke hanawa ina rokonsa A kullum da yakareni daga sharrin mutum da aljan yakuma karamin tsoronsa Amma maganar shago wallahi harcikin raina naji sanyi saboda Addu'ar da bayin Allah nagari sukemun ga kuma Nima inayi, Allah yana jarrabar bayinsa da yafiso ne.Jalil kuma zaizo shima za kuma musake dawowa dukanmu idan Allah ya bamu Aron rayuwa inshaa Allahu saudia sai da zame mana kamar gida albarkacin Alkur'ani.".
Sake kwantawa sosai tayi akan kafaɗar tasa haɗe da cewa, "Amin worldbest mama father brother". Yayi murmushi yana sauke ajiyar zuciya tare da matuƙar jin tausayinta acikin zuciyarsa na rashin yin rayuwa da mahaifiyarta wacce da yanzu itace abokiyar shawararka. Suna isa karɓa yai ya duba haɗe da kallonsa cikin yaren Hausa data zauna abakinsa sosai yace, "Kai ɗan gidan malam Bulama Sa'udu ne?"
"Eh mahaifiyata ce ƴar gidan". Ya Mutallab ya amsa masa ataƙaice dan sunan ƙanan mahaifin mahaifiyarsu kenan da zasu sauka gidansa, malami ne sosai kuma yana daga cikin masu kudi acikin garin dan ko daga tsarin gidansa zakasan yatada baya shima, shiyasa Tánte Sajida tafaɗa masa cewa bazasu sha wahalar nemansa ba indai sun shiga garin saboda address ɗin baida wahalar nema, haka kuwa akayi dan labari drivern taxi ɗin ya shiga basu cewa ai yasan malam Bulama Sa'udu saboda a wajensa mahaifinsa ya ɗauki karatu da wasu ƴan uwansa, shima yafara ɗaukar karatu gunsa yau da gobe tasa ya daina yakoma neman nakai tunda yasamu ilimin bautawa Allah dai-dai gwargwado, nan yayita basu labarin ƙanen mahaifin kakan nasu har suka iso ba tare da Mutallab ya rabasa da ƙanzil ba, nawa ne kuɗinsa ya tambayesa amma drivern taxi ɗin yaƙi faɗa sai dai Mutallab ya kwatanta ya bashi dan dama basu taho ba tun a Nigeria sai daya yi chanjin kuɗi har da na ƙasar, babban gidane da kana kallonsa kaga na wani attajirun mai kudin sai kuma ƙatuwar makaranta da aka zamanantar gwanin burgewa da kuma ban sha'awa ɗalibbai sai harmar shiga sukeyi saboda lokacin fara ɗaukar karatun marece yayi, sallama Mutallab yayi a dai-dai bakin gate ɗin gidan mai gadi ya taso yamiƙa masa hannu suka gaisa yana cewa, "Don Allah ko malam Bulama na ciki?"
"Eh yana ciki ɗan saurayi". Mai gadin ya bashi amsa da yarensu dan da Yaren Mutallab ya tambayesa, amsa mashi yai da eh yana nan yanzu ma zai fito, rufe bakinsa keda wuya sai ga malam Bulama Sa'udu ya iso mai gadin yace, "Yawwa gashi nan ma yafito". kallon fuskar sani Malam Bulama yabi Mutallab dashi lokacin daya ƙaraso wajen tare da miƙa masa hannu suka gaisa bayan maigadi ya sanar dashi cewa shi suke nema, yace "Gadai fuska kamar na santa amma nakasa tuna ko ina ne ɗan saurayi? Ku shigo daga ciki". Yayi masu umurnin shigowa ganin Afrah ɗin macce ce bai kyautu abarta tsaye a waje ba, bayan sun shigo cikin harabar gidan ne Mutallab yayi masa bayanin daga inda suke tare da faɗa masa cewa tánte Sajida ce ta bashi address ɗinsa acewarta zasufi saurin gane shi fiye da ainahin gidan kakannin nasu na asali, "Allahu Akbar, ai ba sai ka ƙarasa bayani ba duk wanda ya kalleku zaiga fuskar ƴarmu Mariya atattare daki, sai dai da yake jiya ba yau ba kuma tun bayan rasuwarta mahaifinki bai kawo mana kuba shiyasa banyi saurin gane kuba amma sai naga fuskokin kamar na sanku, musamman kai da duka komai na mareya ka ɗauko, bisimillah ku shigo daga ciki". Ya ƙare zancen tare da wucewa gaba suka bishi a baya, masauki yayi masu a palourn sa kafin yakira iyalansa su biyu, Baaba Raheene da kuma Baaba kaltume su gaisa, bayan sun gama gaisawa ne yayi masu bayanin ƴan wajen marigayiya Mariya ne dake aure suka kawo masu ziyara da taimakon Sajida, sosai sukaji daɗin zuwan nasu tare da nuna farin cikinsu, inda nan take suka kai Afrah masaukinta shi kuma Mutallab malam Bulama yakira ɗansa Mahmoud yace ya saukesa ɗakinsa yafara watsa ruwa sannan yafito yaci abinci.
Fasa fitar da zaiyi Malam Bulama yai har sai daya tabbatar su Mutallab sun samu hutawa sunci abinci sannan yai musu sallama akan zai shiga cikin makaranta sai ya dawo idan anyi sallar magrib sai su tafi can Dosso unguwar da kakanninsu da sauran ƴan uwan mahaifiyarsu suke, hakan yasa Mutallab komawa masauki da aka bashi ya kwanta dan yana ɗan jin kasala atattare dashi, ita kuma Afrah tayi zamanta tare dasu Baaba Raheene da tuni ta saki jikinta dasu saboda yanda suke tsokanarta da wasa irin ta jika da kaka.
Bayan anyi sallar magrib malam Bulama da ɗansa Mahmoud suka ɗauki Mutallab da Afrah sai Baaba kaltume suka nufi unguwar Dosso dasu, tafiya mai ɗan nisa sukayi kafin suka iso unguwar dan har anyi sallar isha, hakan yasa mazan suka wuce massalaci su kuma su Baaba kaltume da Afrah suka shiga cikin gidan
" Bienvenue Bienvenue (sanunku sannunku) "
#Mutallab Asad
#Ƴan tagwaye
#Nana Diso
#Billy S Fari
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
MUTALLAB ASAD
(labari mai taɓa zuciya)
Na
Billy s fari
Nana diso
RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU.
TAFIYAR BIYU TAFI DAYA
SHAFI NA ARBA'IN DA BIYAR.
A ɓangaren Mahma kuwa mahaifiyarsu Meenal sai da tayi sati biyu a gidan Dady da sunan jinyar ƴarta, duk wata kulawa da wata buƙata ta Meenal takoma ƙarƙashinta ita keyi mata komai, ko da abu Meenal ke so wajen Dadynta zatace mata tabari ta sanar dashi idan ya shigo dubata ba sai tafaɗa masa ba, kai tsaye take nunawa Mommy ita tahaifi Meenal ƴarta ce ba tare da tayi mata kara ba ko sau ɗaya, ita kuwa Mommy ta nuna mata kamar ma bata san yanayi ba, duk abinda kuma takeyiwa Meenal ɗin bata fasa yimata ba sai wanda taga mahaifiyar tata tayi kane-kane akai tare da nuna mata isa sannan take tafitar da hannunta aciki, wannan yaba Mahma damar iya fuskantar Dady aduk lokacin daya shiga duba ƴar tasa da jiki tayi magana dashi don ranta, tun yana yimata banza har yafara kulata, haka Mommy zata shiga cikin ɗakin na Meenal ba tare data sani ba ta isko Dadyn zaune da Mahma da ita Meenal ɗin suna fira, wani lokacin ma har da Kamal, bata taɓa nuna damuwa ko ɓacin rai akan hakan ba sai dai kawai tayi murmushi tata juya ta koma inda tafito.
Hakan yafaru ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba kuma duk tana shanyewa, gori da maganganu kuwa babu wanda bata sha ba awajen mahaifiyar su Meenal, ga isa da take nuna mata kai tsaye cikin gidan amma duk tayi banza da ita, ana haka itama ƴar Mommy tazo mata hutu wanda hakan yaɗan cire mata ƴar damuwar da take ji aƙasan zuciyarta, nan fa abubuwa suka ƙaru kala-kala wajen Mahma har yakai idan Dady ya shiga duba Meenal suka gama fira zata rakoshi har ƙasa benan cike da kissa tana kwasar dariya tamkar itace matar gidan duk ɗan ta baƙantawa Mommy, amma sauda rana ɗaya Mommy bata taɓa bata damar da zata fahimci tana jin ciwon abubuwan da takeyi ba, wannan ya sake jefa mata tsanar mommyn a zuciya sosai, tun Meenal da yanayin kusancin mahaifan nata yafara burgeta bata fahimci me mahaifiyar tata keyi ba har ta soma fahimta, hakan yasa tafara ƙarfafa zuciyarta tare da nuna tasamu sauƙi saboda Mahma takomawarta gidan grandama tare kuma da nuna mata rashin dacewar wasu abubuwan da takeyiwa Mommyn acikin gidan.
Kamal ma ya lura da hakan ɗan haka suka zauna shi da Meenal suka yanke shawarar maida Mahma gida dan har ga Allah yanzu da zuciya ɗaya suke jin soyayyar Mommy dan sun riga sun gano faɗa da takeyi masu na gyara kayanka ne da bazai zama sauke muraba ba, ranar da Mahma tacika sati biyu da zuwa gidan tayi shirin komawa cike da jin daɗin cewa sun fara samun daidaita tsakaninta da Dady, wanda tana sa ran nan bada jimawa ba zai iya maidota ɗakinta, Mommy na kitchen mamah ta sauko Kamal na biye da ita da akwatinta Meenal kuma ta rakosu zata taka masu zuwa mota tace, "To mudai mun tafi sai kuma mun sake dawowa saboda angulu ta kusa komawa gidanta na tsamiya taci gaba da renon ƴaƴanta data bari hannu biyu rabbana, a lokacin ne za'a gane ɗan jaki ma dukiya ne sannan ja da baya ba tsoro bane, bakin rijiya kuma ba wajen wasar yara bane haka kuma ko Giwa tafaɗi tafi ƙarfin atakata dan kuwa wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa, na barku lafiya Meenal".
Kallo juna Meenal da Kamal sukayi kafin suwuce gaba abunsu ba tare da sunce mata ƙanzil ba dan abun ya ɓata masu rai, Mommy kuwa data fito kitchen murmushi tayi haɗe da kallonta tace, "ina tayaki murna tare da fatar alkhairi, sai dai karki manta duk wanda Allah ke yiwa faɗa babu buƙatar yace sai yayi faɗan da kansa, a wajensa nakai kayana dan haka duk wani abinda zai kawo mani acikin rayuwata ina maraba dashi hannu biyu, Allah ya tsare hanya ya kuma saukeki lafiya". Takaici ne yarufe Mahma tayi kwafa sannan tabar wajen tana ji har yanzu bata cire haushin mommyn ba aranta.
A jikin mota Mahma tasamu Meenal ta haɗe rai tare da naɗe hannayenta a ƙirji, "My Baby lafiya?" Ta jeho mata tambayar tana ƙoƙarin buɗe motar ta shiga, ɗan murmushi Meenal ta saki tare da riƙo hannuwan Mahma acikin nata tana kallon fuskarta tace, "Pls Mahma dan Allah wannan abubuwan da kike yiwa Mommy kidena sun isa haka, wallahi Mommy mutuniyar kirki ce, ada nafiki jin tsanarta a raina amma yanzu sam bana jin haka akanta Mahma saboda ɗaiɗaiku ne irinta za'a samu cikin matan uba, ta kula damu lokacin da muke da buƙatar ki, tashanye duk wata damuwa tamu da ɓaci ran da muke sakata aciki mu da Dady, ashe bai kamata yanzu ayimata kyakkyawar sakayya ba? Kiyi tunani akan tarin alkhairanta agaremu ko sau ɗaya ne dan Allah Mahma, zan so idan kun daidaita da Dadyna kidawo amma ba'a haka ba Mahma, bada wannan zuciyar taki da kullum ke nuna maki kiɓata mata ba saboda ni dai na dawo daga rakiyar grandma". Dungure mata kai Mahma tayi haɗe da cewa, "kya faɗi haka tunda kinga kin samu sauƙin".
"Pls Mahma i'm serious wallahi, ni kifaɗa mata ma fushi nakeyi da ita tunda bata zo dubiya ba". Murmushi kawai Mahma tayi tare da shafa kan Meenal tace, "Ki kula da kanki ƴatah sai munyi waya". Meenal ta mayar mata da murmushin tare da ɗaya mata kai sannan ta buɗe mata gaban motar ta shiga ta rufe mata tana ɗaya mata hannu. Kamal kuwa Baice da Mahma komai ba har suka iso gida ya sake ciro akwatinta ya kaimata yana gaida grandama dake washe baki dan tuni Mahma tafesa mata labarin kusancin da suka samu yanzu da mahaifin su Meenal ɗin da take tsammanin nan kusa zai iya sake dawowa jawarcinta, cikin tsokana take kallon Kamal tana cewa, "Ɗan kwal uba gashi nan sati biyu kacal naga har kai ka sauya ka wani canzawa abunka, ashe tsohon naku ya tuno da tsohuwar soyayya? Allah to ya kaimu lokaci kuzo ku ɗauke mani tsohuwar ku ko ma shana muma yanda waccan tsohuwar munafukar dake gidan ke shanawa da dukiyar mahaifinku ita da danginta, ɗan so nakeyi tana shiga takorota waje muga ta ƙaryar fankama da ji dakai". ɗago kai Kamal yai tare da kallon grandama yace, "Hmmm! Grandama kidena irin wannan ba kyau, kuma wallahi idan ma mafarki kukeyi na Dady zai iya rabuwa da ita to ku farka dan ko sama da ƙasa zata haɗe Dady bazai iya rabuwa da Mommy ba, kafin yanzu dana girma nasan ciwon kaina duk wani makircin da kuka san kuna saka mu shirya mata ni da Meenaluwa ada bai taɓa sa Dady ya saketa ba ko sau ɗaya duk da soyayyar da yake mana, babban hukuncinsa da ita yace ta tafi gidansu wani lokacin ma kafin takai ga tafiya zai je ya lallasheta, idan kuma har ta tafi tofa ranar wallahi Dady baya bacci, dan Allah Mahma zan roƙeki kamar yanda naji Meenaluwa ta roƙeki da zamu taho kicire kishin nan da kike yimata aranki kubarta ta zauna lafiya a gidanta, ke kuma muyi fatan Allah yasa ku daidaita da Dady yadawo dake, zamuyi farincikin hakan sosai Mahma, ki ƙyale grandama tsufa yafara sata ruɗewa gabaɗaya".
"Uwarka dai ce ta ruɗe dake nema tabiyewa shirmenku ba niba dan ubanka". Dariya ta bawa Mahma ta riƙo hannun Kamal tana turasa waje haɗe da cewa, "kaga Kamal jeka dan Allah kada ka jawo mani rigima Nagode Allah yai maku albarka, amma ni Mommyn nan takunbazan taɓa sonta ba sai dai nace Allah ya sawaƙe kawai".
"Shikenan Mahma bari naje muna da wani cahasu yau nida friends ɗina".
"Allah ya tsare, ka turo mani kuɗaɗena dana baka ajiya".
"Ba case Mahma zan turo". Ya faɗa yana buɗe motarsa ya shige ya tayar yabar gidan.
Kullum Mahma sai takira Meenal ta sake tabbatar da tana cikin ƙoshin lafiya ko kuma ita Meenal ɗin takira, Dady kuwa dama duk biye mata ɗin da yakeyi yana yine kawai saboda ƴaƴansa, burinshi kawai Meenal tasamu sauƙi Mahma ta tattara tabar masa gida dan har yanzu baya da wata sha'awar son sake yin wata rayuwa da ita, ɗan haka har tayi sati da tafiya bai sake bi takanta ba, itama sai ɗaya takirasa taji yanda ya amsa mata daga lokacin bata sake kiransa ba, zuciyarta kuma na sake tabbatar mata da ko meye yasa yake mata shariya yanzu Mommy ce tashirya shi shiyasa tace har abada baza ta dena jin tsanarta azuciyarta ba.
Kamal da yanzu sun bala'in ɗunkewa tsakaninshi da Sarsy sun zama cingum zaune suke cikin mota suna fira ta kallesa cike da bariki tana cewa, "Ya kamal?"
Ya amsa mata da "Na'am babynbaby?" yana juyowa tare da zuba mata manyan idanuwansa. Idanuwanta acikin nasa tace, "Nikam dan Allah na tambayeka?"
"Ehim ina jinki" yafaɗa yana rage sautin ƙidan dake tashi acikin motar tasa, Sarsy tace "me yasa wai kai baka kwantawa da macce? Nifa i'm need of you har a zuciyata saboda ina masifar sonka." Dariya yai kafin yace, "Haba Sarsy! Duk GP ɗin nan naki kina nufin zaki iya bada kanki ga wani?" "Eh mana in dai kaine".
"Cab gaskiya to GP down Baby! Nifa bazan iya haɗa shimfiɗa da macce ba saboda haramun ne". Zaro idanuwa Sarsy tayi cike da mamaki tunowa da yanda suke romancing juna ita dashi kafin tace, "Wait Baby, Are you serious?"
"Sosai ma, ko kina musu ne?"
"Gaskiya, taya zan yarda kasan haramun baby?." Duk da yaji zafin maganar tata amma sai yayi murmushi yace, "Nasan komai mana Sarsy har taɓakin da nakeyi da sauran abubuwan da mukeyi na masha'armu duka nasan haramun ne, but narasa yadda zanyi ne shiyasa nake amfani da wannan damar ina rage zafi, tun ina da shekara 20 na nunawa Dady cewa aure nake so yace sai nagama karatuna tukuna, Maamah ma dana sanar da ita cewa tayi ban isa aure ba wai nayi ƙanƙanta, daga baya da Dady yafahimci da gaske nakeyi yaso ya sama mani ɗaya daga cikin ƴaƴan abokansa na aura amma Mahma naji tace wai itafa babu maiyiwa ɗanta aure yanzu, a lokacin su ke ganin ƙanƙantata amma basu san irin sha'awar da nake fama da ita ba, shi nefa dana gayawa abokaina halinsa ake ciki sai sukace karna damu babana yanada kuɗi why not bazan dinga jan yammata ba, ni kuma nasan ba abu bane mai kyau saboda Mommy nashan yimani ire-iren wannan faɗan cikin hikima tare da bani labarai makamantansu,waɗan da ni da kaina nasan hannunka mai sanda ne takeyi mani, ire-iren wuɗannan abubuwan na ɗaya daga cikin dalilan da yasa nake sonta kuma bana iya yimata rashin kunya kamar Meenal, ina saurararta duk da bako yaushe ba, ina kuma fahimtarta idan tana lurar dani saɓanin Meenal shiyasa mukafi shiri da ita, Sarsy nasan duk abinda nayi nima za'ayiwa iyalaina shi watarana shiyasa bana zurewa dayawa, wannan ma da nakeyi Allah ya gani ina jin zafi araina amma wannan nafitar kaɗai nake da ita, Sarsy wallahi idan naga macce bana iya controlling kaina, ciwon cikin da nayi shekaru baya hadda wannan lalurar amma sai Dady yakasa fahimtata yaturani waje wai naje naga likita, hakan yabani damar rage zafi da ƴan matan turawa kala-kala ta hanyar romancing da amma wallahi ban taɓa ketawa kowace macce mutuncinta ba, Allah ne shedata Sarsy bana zina kuma bazan fara akanki ba, A shekarun baya ƙoƙarin kaucewa wannan matsalar na fara biyawa kaina sha'awa da kaina saboda zama da wani abokina wanda yake cikin jarrabawar shi yabani shawarar nariƙa yin hakan, amma nakasa samun natsuwar da nake buƙata shima saboda ina fara ɗabiar ciwon kai da zazzaɓi ya aureni, Ni mutum ne mai basira a makaranta amma sai gashi tunda nafara ɗibi'ar nadena gane karatu, ƙwaƙwalwata ta toshe babu abinda nake fahimta, ga yawan faɗuwar gaba da yawan mantuwa, al'amurrana gabaɗaya suka sauya tamkar ba niba". (wuɗannan ɗabi'un suna aurar duk wata/ wani mai wannan ɗabi'a ta masturbation wato biyawa kai buƙata, don Allah masuyi ku kiyaye ku kuma dena don tsira da lafiyar jikinki).
"Ina so nadena wannan halayyar amma nakasa har sai da naji wani wa'azi na wani babban malami a ƙasar nan akan makomar masu irin wannan halayen, da yake na ƙyamaci abun azuciyarta kawai nakasa denawa ne sai gashi Allah ya dubi zuciyata yasa nadaina wannan mummunan ɗabia gaba ɗaya, dana lura kaɗaita ke yawan jefani a halin sha'awa kuma sai yazamana ina ƙoƙarin shiga mutane akoda yaushe tare da yawan yin raha, na kuma saka araina bazanji zina ba bazan koma biyawa kaina buƙata ba domin idan kowa baya ganina Allah da ya halicce ni yana kallona, Sarsy duk da kike ganina haka wallahi Azumin alhamis da littinin baya wuce ni saboda nasake nemawa kaina kariya daga faɗawa mummunan ƙaddarar da zatayita sakani nadama har ƙarshen rayuwa, Mommy da kike gani uwace sosai dan ba donta ba da tuni abubuwan da nakeyi sunfi haka, shiriya ta Allah ce kuma ako yaushe ina roƙon da daya kawo mani mafita ga lamarina domin ni ban isa na shiryar da kaina ba, yanayin da nake ciki kuma na yawan sha'awa dake sakani yin wannan taɓeɓen da mukeyi shima Allah ya dauke mani shi ya sassauta mani ƙarfinta albarkar nabiyyirrahma,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 26 Chapter of 54