Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zaton Alkhairi, wannan mutumen daji babban mutum ne taya zaki gaya masa haka, na faɗa miki tashi kije idan har ni mahaifinki ne". Turo baki tayi sannan ta nufi bakin motar Alhajin daya koma ciki tayi tsaye tana faɗin, "Gani". Cike da tsiwa "Haba ƴar budurwa, mayi magana anan? Ai ba girmanki bane masoyiya, ina ga da alama dai amaryar tawa dai tafiye rigima ko maganar mahaifin nata bata son bi". Ɗago manyan idanuwanta tayi ta saukesu a fuskarsa cikin fushi, hakan yasa take yaji wata sha'awarta ta ƙarar masa saboda yanda fushin yaimata kyau". Buɗe motar yai yana cewa ta shigo daga ciki ba musu ta shiga ta zauna tana ayyana irin abinda zatayi masa a zuciya. "Gaki kyakyawa gaki mai cikar halitta ga kyanjiki ga diri amma kina yin bara? Bayan duka tarin ni'imar nan da Allah yayi miki wacce zaki iya amfani da ita kisamu abubuwa da yawa, ki yarda dani zan siya miki mota, zan bawa iyayenki gida da duk wani jindadi, wannan barar zakuyi bankwana dashi har abada indai kika amince min". Dakewa tayi duk da tsoron da take ji ta kalleshi tun daga sama har ƙasa, tana da tabbacin idan ba'a ƴar aikin gidansa ba zai ɗauketa to tabbas babu haɗi tsakaninsu, duba da irin tarin arziƙin dako ba'a faɗa maka ba kasan yana dashi, jin bata ce komai ba ya sashi cewa,  "kinyi shiru masoyiya, nasan fa kema ƴar harka ce dan nasan kinsan maza, taimaka maki ne zanyi amma kin tsaya kina kallona kamar baki sani ba, bayan ni nawa zaman da zamuyi ɗaukaki zanyi dan zan maidake babbar yarinya sosai zaki zama yarinyata." Cikin sautin kukanta daya cika motar tace, "Kallon da kakemun kenan ni ƴar iska ce dan ina bara ni da mahaifina? To bari kaji wlh rashin mafita yakaini bara ba wai dan na aikata sabon Allah ba, Allah shaidane ban taɓa aikatawa ba kuma bazan taɓa aikatawar ba ko babu zata kashemu ni da iyayena saboda yin hakan saɓon Allah ne". Cikin wata fitinanniyar muryarsa yace, "C'est ce que je veux to (shine abunda nakeso to),ban damu ba idan har kina da tabbacin ke virgin ce farashinki zai ƙara hawa kenan, sannan tunda har bakisan harkar ba ni zan koya miki idan mukaje mukayi abunda zamuyi zan baki pad sai kisaka idan antambayeki agida sai kice al'ada kikeyi, ina Shikenan?". Cike da takaici da ganin rashin tsoron Allah tsantsa da kuma lura mutumin nan yayi mugun zurfi akan sabon Allah gashi yanada kuɗi jayayya dashi zatayi mata wahala zai kuma iya sawa a salwantasu ita da mahaifinta  ta kallesa tace, "Ina da tabbacin kanada mata da ƴaƴa, ƙanne da yayye duka kana dasu, idan har abunda kake yimun kana daukarsa abisa daidai to ina rokan Allah yasa ayiwa zuri'aka kuma ina so kasani ni ba ƴar iska bace kaje can ka nemi daidai irinka". Tana kaiwa nan ta hannu ta buɗe motar tafita, hannun mahaifinta ta riƙo sukayi gaba tana sharar ƙwalla, shi kuwa da yaji duk yanda sukayi da Alhajin ya shiga kwashe mata Albarka haɗe da zaginta, bata kula shiba dan ta lura mahaifin nata yayi nisa baya jin kira, kuma idan ta biye masa akan hanya wajen ganar dashi mutane zasu iya zaginta ba tare da sun san dalilinta ba dan tabbas idan ta ta biye ma iyayen nata zasu sakata saɓon Allah, sai da ta ajiyesa ƙofar gida sannan ta sakar masa hannu, da gudu ta kwasa tayi makarantar boko dan daman ta ƙarfe biyu suke zuwa, tana isa ta hangi Amini ƙwarya ta nufi wajenta tana cewa, "Amini kema sai yanzu kikazo?" Da mamaki Amini ta kalleta tace, "Eh Aïcha, kin biya kuɗin makaranta ne?" Girgiza mata kai tayi alamun a'a". Tace "To wallahi kora akeyi bakiga wulaƙancin da malam Nura yakeyi ba". "Innalilahi wainna illahirrajiun Nashiga uku yazanyi yanzu?" Tafaɗa kamar zatayi kuka, tana ganin malam Nura ya nufota yana gayamata tashige tabar musu makaranta dan bata biya kuɗin term ba ta shiga ja da baya, Tasan idan har ta tsaya magiya to karshe wulakanta ta zaiyi agaban student din dan haka ta ɗauko kafafuwanta tafito tana kallon Amini ƙawarta tashige aji, tafiya tayi mai ɗan nisa kamin kuma ta ƙarasa wani layin dake gab da gidansu, layin tashiga tasaka kuka sosai tana tausayin kanta daman waccan term ɗin daƙyar ta haɗa kuɗin makarantar shima saurayin babbar yaya yazo ya bata. Ganin kukan da takeyi ba shida anfani yasa tamiƙe ta nufi gidan da tayowa guduwar shiga saboda tsoron abunda zai faru kanta, ai kuwa tana shiga gidan bakinta ɗauke da sallama mà marè ta jata tashiga dukanta ɗan mà père daya shiga gidan da ɓacin rai  ya faɗa mata duk abinda yafaru, cikin masifa take cewa, "es-tu fou Aïcha?( ke mahaukaciya ce?) Da zaki je ki janyo mana asara irin wannan? Dubi shegiyar shigar da kikayi sai kace mahaukaciya amma bawan Allah can bai ji ƙyamarki ba yace yana da buƙata dake amma kika ƙi, to menene amfanin nononuwan naki da duwawun naki idan bazaki fiddasu yadda yakamata ba ki samo mana kuɗi, Yanzu ace alhajin birni babban mai kuɗi yana sonki kin zageshi Aïcha dan kina marar mutunci, to bazaki fi karfina ba Aïcha wlh tunda ni na haifeki nake kika haifemu ba".... Mà mèrè na faɗan tana cigaba da dukanta, yayarta dake zaune tana faɗin, "Gwara dai taji ajikinta ko zata gyara, ai masu cewa suna sonta ma naga ƙoƙarin su duk da nasan kyan fuskarta ke ɗibarsu, amma wannan ƙibar tata da tumbi  da take dasu ya kamata ta ragesu sanoda tumbin nan maza basa sonshi suke ba, ƴar lukuta kawai"...Duk da yadda ta daku a hannun mà mèrè amma hakan baisa tayi shiru ba sai da tace, "Abarni a haka indai don na saɓawa Allah zaki ce nawani rage, kuma wannan abun da kikeyi ni bazan taɓa yinshi ba ko za'a kasheni saboda ba'ayiwa iyaye biyayya agurin sabon Allah, kuma nafaɗa wallahi ni bazanyi abunda zai lallata min rayuwata ba saboda samun kudin da zasu ƙare, shi kuwa mutuncina har na mutu bazai daina bina ba idan na tsaresa, kuma ki ɗauke idanuwanki akan jikina dan ƙiba da tumbi halittace ta Allah bazan sha magani ko na canza halittata ba, duk namijin da bazai soni a yadda nake ba to ba shine masoyin kwarai ba, kuma ma maza kome zakiyi musu zai hanasu yabon wata ne? Akan maza bazan zama mahaukaciya ba Allah zai kawomin daidai dani a yarda nake ehe". #Mutallab Asad #Ƴan tagwaye #Nana Diso #Billy S Fari MUTALLAB ASAD MUTALLAB (labari mai taɓa zuciya) Na Billy s fari Nana diso RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU. TAFIYAR BIYU TAFI DAYA SHAFI NA ARBA'IN DA BIYU. Rai a ɓace Mahma ta shiga ɗakin Meenal ɗin tare dayin jifa da handbag ɗinta akan gadon Meenal sannan ta zauna gefen gadon tana hura hanci, zaune Meenal ta tashi tana cije baki ta jingina ga kan gadonta cikin ƙarfin hali ta kalli Mahma haɗe da cewa "Mahma meye haka kika shigo ko sallama babu kuma kin zauna kina ɓata rai?" Sai da Mahma ta juyo ta kalli Meenal ɗin rai a ɓace sai kuma ta sassauta fushinta ganin yanda ƴar tata takoma tana cewa, "Meenal so kikeyi kiɓata mani rai kamar yanda mahaifinki da matarsa suka yimani? Laifi ne dan nashigo ɗakin ƴata banyi sallama ba?" "No Mahma, kawai dai naga hakan is good kamar yanda Mommy ke faɗa mani...." Katseta Mamah tayi kafin taƙarasa tana cewa, "ya isa haka Meenal bana son zancen matar can ɓata mani rai yakeyi, idan kuma kinfi so raina yayita ɓaci sai kici gaba". Ya Kamal ne daya shigowa Mahma da akwatinta yace, "Mahma gaskiya baki kyauta ba abinda kika yiwa Mommy, kina gani fa dakatar dake Dady yaso yi ta hanasa amma shine kika faffaɗa mata maganganu masu zafi haka da zasu ɓata mata rai amma kin zo nan kina cewa an ɓata maki rai, is unfair abunda kikayi". Harara ta maka masa haɗe da cewa, "Shashasha fita kabani waje dama ai kai matsalarka kenan, tariga ta gama dakai da uban naka". "Ba haka bane Mahma ita gaskiya a faɗeta duk inda take, ni kaina da kike gani bawai daɗina Mommy take ji ba saboda ba jin magana nakeba kawai haƙuri ne da ita shiyasa nadena ɗaukar zugarku, amma ita gaskiya dole a faɗeta". Yana gama faɗar hakan yafice don sosai yaji haushin abinda Mahma ɗin tayiwa Mommy, da harara Mahma ta rakasa bayansa har ya fice kafin ta juyo kan Meenal tace, "Kinga kalar sakarci nasa ko? Mtsss Allah yai masa magani ya jikin naki". Meenal ta lumshe idanuwa ta buɗe akanta haɗe da cewa, "da sauƙi Mahma". "Allah yaƙara sauƙi yanzu haka wannan matar tabarki kika koma dan ba ita tahaifeki ba Meenal, kinga yanda kikayi baƙi kika lalace kuwa?" Kamar jira Meenal keyi aikuwa tafashe da kuka tana cewa, "Mamah ya zanyi? Wallahi ina sonsa kamar raina". "Ban gane ba Meenal, waye kike magana akansa?" "Mahma Mutallab! Wlh idan ban auresa ba ji nakeyi mutuwa sanyi". Matsawa kusa da ita Mahma tayi ta janyota ajikinta ta rungume tana ɗan bubbuga bayanta ahankali alamun lallashi saboda tasan zafin so sosai, kamar irin haka ne ta tsinci kanta a shekarun baya akan mahaifin nasu Meenal, wanda ba dan tayi da gaske ba wajen mallakarsa to da tabbas bata sameshi ba, ajiyar zuciya ta sauke haɗe da cewa, "indai wannan ce matsalarka Meenal kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki, ina tabbatar maki da cewa takowane hali indai ni na haifeki sai kin samu cikar farincikinki kinji ko?" Cikin kuka Meenal tace, "Taya Mahma? Mutumen daya sheda mani baya sona matsayin abokiyar rayuwarsa? Mutumen da wayata ma daƙyar na lallaɓashi na samu yake ɗagawa, mutumen dako awaya ba'a samunsa taya kike tunanin har zan mallakesa? Ni na sani kawai mutuwa zanyi". Ta sake fashe mata da wani kukan tana shigewa jikinta sosai, haka Mahma taci gaba da lallashinta tare da faɗa mata maganganun da zasu sakata cikin farinciki, duk da Meenal tasan ba lallaine hasashen na mahaifiyarta ya zama gaskiya ba taji ta ɗan samu ƙwarin guiwa sosai akan cewa zata iya samun Mutallab ɗin, a hankali ta zame jikinta daga na Mommy ta koma saman gadonta ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya ɗaya bayan ɗaya saboda kukan data sha. Ɗakin Mahma tabi da kallo komai yana gyare tsaf dan Mommy tsaye take akansa, kullum zata gyara da kanta ko ta saka mai aiki ta gyara mata idan tana wani abun, hakan yasa ako yaushe fes yake baida wani datti, ganin ɗakin bai buƙatar komai yasa Mahma dafa kan Meenal tace, "Baby kinci abinci?" Meenal ta girgiza mata kai saboda bata da sha'awar cin komai, Mommy ma data matsa mata taci kuka ta saka mata dole ta ƙyaleta a zuwan anjima zata sanyata taci ko kaɗan ne, tsaki Mahma ta saki tare da cewa, "Wannan ai rashin kulawa ne da kuma zalinci ace yarinya ba lafiya abinci ma baza'a bata ba saboda an tsaneta ita da gidan ubanta, to bari naje na haɗin maki naga wanda ya isa ya hanani". Taƙare zancen tana miƙewa zata fita, hannunta Meenal tariƙo tare da cewa, "A'a Mahma Mommy takawo mani abinci nice nace bana ci kuma da gaske bana sha'awar cin komai ne". "Meenal ko bakyaci yakamata ace an lallaɓaki ko kaɗanne kinci, ba dole ki koma haka ba ga ciwo ga yunwa". "Mahma.." Meenal tafaɗa cikin gundura da zancen gabaɗaya ta maka mata harara sannan tafice abunta, kai tsaye kitchen ta nufa ta samu iya tabawa na ƙoƙarin ɗora girkin rana, ko gefen da take ta ɗan russuna tana gaisheta bata kalla ba ta nufi wajen da dishes ɗin Mommy ke jere ta ciro glass kettle, tukunyar da iya tabawa ta ɗora akan gas ta ɗauke ɗaya ta ajiye gefe ta ɗora kettle ɗin tare da buɗe drowers ɗin kitchen ɗin tamkar matar gidan ta ɗauko kayan haɗin tea ta zuba, tsaye tayi gefe haɗe da hararar iya tabawa data saki baki cike da mamakin isar Mahma ɗin tace, "Ko kina da magana ne Munafuka?" Da sauri iya tabawa ta girgiza kai, tana tsaye ruwan tea ɗin suka tafasa ta ɗauke ta haɗa gwangon madara dana Ovaltine da suga ta ɗora akan tray tare da cups da spoon sannan ta ɗauki tray ɗin tafice daga kitchen ɗin ta haura sama, tana tura ƙofa ta tadda Mommy da Dady zaune cikin ɗakin yana tambayar Meenal yaya jikinta dan koda suka fito sukaji motsi a kitchen sun aza iya tabawa ce, da kuma suka shiga cikin ɗakin na Meenal basu tadda Mahma ɗin ba sun ɗauka ta shiga toilet, ta gefensu ta ratsa jikinta ba mayafi ta ajiye tray ɗin akan bedside tana ƙoƙarin haɗawa Meenal ɗin tea take cewa, "Yakamta kariƙa saka idanuwa akan lamarin ƴarka, taya tun safe yarinya na ciwo anbarta da yunwa saboda ance taci abinci taƙi ci, halama ba'a san shi marar lafiya dole ana matsa masa yaci abinci ko kaɗan ne saboda sauƙi yafi shiga, yarinya gaba ɗaya banda tarin damuwa da ciwo yunwa tasa duk ta lalace, idan kai bazaka iya magana ba to ina so ka sani ni bazan ɗauki wannan ba yara da gidan ubansu amma ambi duk an takurasu an hanasu sukuni". Mommy dake gefe tasaki murmushi ba tare data kulata ba tajuya zata fita, "dakata Mansura ai tare mukazo ko? Meenal ya akayi bakici abinci ba?" "Dady Mommy takawo mani amma bana sha'awar cin komai nace mata na ƙoshi, yanzun ma bazan iya cin wani abun ba Dady nidai kawai Muryar Mutallab nake son ji". Mahma data gama haɗa mata tea ɗin tamiƙa mata cup tana cewa, "Ki tashi ki karɓi wannan kisha, ko an faɗa mako cewa shi wanda kike son idan ya ganki haka zaiyi sha'awar auren naki ne". Ɓata rai Meenal tayi tana kallon Dadynta ya dafa kanta haɗe da cewa, "Yakamata kiyi mata bayanin irin kulawar da momynki ke baki wacce koni dana haifeki yanzu bana baki irinta kinji ko?" Yaƙare zancen ba tare daya kalli ko gefen da Mahma ɗin take ba sannan yamiƙe suka fice tare da Mommyn, Mahma kuwa kallon Meenal tayi haɗe da cewa, "Dama bakida hankali Meenal? Taya zanyi tufƙa ki warware mani? Wannan fa damace muka samu da zamu yaƙi wannan matar kuma burinmu yacika akanta". "Dama wannan yakawoki gidannan Mahma ba jinyata ba shiyasa kika zo harda akwati?" Gefenta ta zauna ta miƙa mata ruwan tea ɗin haɗe da kallonta tace, "ko kaɗan ba wannan ya kawo ni ba Meenal, amma ki tuna wannan dama ce.." hannu Meenal ta ɗaya mata haɗe da cewa, "A'a Mahma ba wata dama da zaki iskota har cikin gidanta kice zaki yaƙeta, Mahma dan Allah ki zubar da makamanki akan Mommy wallahi duk abinda take yimana saboda mugyara halinmu ne, wataƙil tun farko da mun tashi a yanda take son mu da ban tsinci kaina acikin wannan halin ba.." "Ya isa Meenal! Kiyi ƙoƙari kisha tea ɗin zaki ɗan samu ƙarfin jikinki". Mahma tafaɗa rai aɓace dan sam maganganun da yaran nata keyi yanzu basa yimata daɗi suna ƙona mata rai sosai. Dady kuwa koda suka fito bai cewa Mommy uffan ba tarakasa yafice zuwa wajen wani ɗaurin aure da zai je da aka gayyacesa sannan ta dawo takoma kitchen suka cigaba da shirya abincin da za'a ci da rana, iya tabawa nason ɗaukowa Mommy zancen abinda Mahma ta shigo tayi amma ko kaɗan Mommyn taƙi bata fuskar yin hakan saboda bata so ta shiga abinda bai shafeta ba har azo itama akoreta daga aikinta. ************   Faɗar kalar farincikin da kakar su Mutallab ta shiga na ganinsu ita da sauran baffaninsu da wasu ƙananan mahaifiyar tasu mata da tuni suka cika gidan ba'a magana, haka ta rungume Afrah ajikinta tanata kuka tunowa da tata ƴar da suka sata yi saboda tsananin kamanninsu da ita, duk da Mutallab mutum ne mai ƙaramcin fara'a ayau kasa ɓoyuwa tayi saida ta shimfiɗa a fuskarsa sosai ganin yanda ƴan uwa keta nan nan dasu tare da nuna farincikin ganinsu, wasa-wasa sai gashi ya saki jiki dasu sosai anata fira yana kwasar dariya, da mamaki Afrah ke kallonsa dan tun tashinta bata taɓa ganin yayi koda makamanciyar irin wannan dariyar ba, kololuwarta dashi taga yayi Murmushin da iya haƙoransa zasu iya bayyana sai gashi wai yau da kansa yake dariya haka, wani farincikin itama taji ta tsinci kanta aciki tare dayin murmushi sannan ta maido hankalinta cikin ƴan uwan nata da itama ke zagaye da ita ana fira, su malam Bulama sun jima agidan dan sai da Mutallab yakira tánte Sajida da Jalil ya shaida masu sun iso lafiya ya basu suka gaggaisa da mutane sannan sukayi sallama suma suka wuce Mutallab na tabbatar masu da cewa In sha Allahu zuwa gobe ko jibi zai sake shigowa wajensu. Mutallab sai daya kwanta a masaukinsa kafin yakira Idris sukayi magana akan harkar kasuwancinsa nasa ta ɓangarenshi, sosai idris ya jajanta masa yakara gayamasa kuma akan ya kula sosai da mutane da wanda zaiyi sirri dashi dan shidai yana zargin wannan gobarar data fary akwai saka hannun wasu matane aciki kuma makudantan sa. Sai da suka gama kamin kuma yakira jalil a waya Nan yashaida masa anfara gyaran shagunan har anyi kusan rabi,daga nan shima ya shiga labarta masa irin tarba da karancin da suka samu daga wajen dangin mahaifiyarsu shi da Afrah, tamkar ba sune suka ɗauki zafi tare dayin fushi dasu ba ashekarun baya. Cikin jin daɗi Jalil dake ji tamkar shima yayi tsuntsuwa ya ganesa agarin tare da ƴan uwansa yace, "mashaa Allah ya Mutallab kace ashe nayi missing". "Sosai kuwa ba kaɗan ba Jalil, amma karka damu kaima soon zaka zo in Sha Allah, ɗan ina tunanin idan komai ya kammala anan ɗin kaine zaka riƙe mana branch ɗin, kaga kuwa zama daram damdam kai dasu". "Allah yaƙara kuɗi kuma yanufa, amma nikam bazan matsa nesa dakai ba". "Wasa kakeyi, Allah dai ya taimaka mana". "Amin ya rabbi Yaya". "Ya Abba?" "Yana nan lafiya, ko kirana yayimun Jaje baiyiba, hatta su umman ko ya jamil babu wanda yayimana har abban kuma kasan bayan tafiyarku naje na nuna masa makullan motar daka bani yace wai nadai bi a hankali dan shi yafara tsorata da lamarinka". Murmushi kawai Mutallab yai yana jin wani abu mai kama da miki a ƙasan zuciyarsa na taso masa akan kalaman na mahaifinsa, " babu komai Jalil,Ka kula dashi Jalil sai da safe" Mutallab yafaɗa yana kashe wayar, jin haka yasa Jalil jikinsa yai sanyi yana ji dama bai faɗa masa abinda mahaifin nasu yace ba, message ya rubuta masa.       ' _I'm sorry_' Ya tura masa sannan ya ajiye wayar, yana ajiyewa Aryan yakirasa ya ɗauka cikin girmamawa ya gaishesa, bayan sun gama gaisawar ne nan yake sanar dashi cewa ya sauya layi ne amma yanzu haka suna nigar sun dawo yakirasa zai samesa, haka kuwa akayi suna gama waya yakira mutanan da har ya gyara kwanciyarsa bacci kawai yake jira ya ɗaukesa, haƙuri Mutallab ya soma da bashi dan yasan ko kowa bai nemesa a waya ba shi zai nemesa, shi kuma yayi hakan ne saboda ya samu damar gudanar da ibadarsa yanda Yakamata,  murmushi Aryan yai haɗe da cewa, "Kai ma dai kasan baka kyauta ba, dan kana wahala ga taka soyayyar shine muma zaka wahalar damu? Ina matata?" "Yanzu kam ai nasan tayi bacci amma dai kakirata zaka iya samun layinta yanzu". "Ok to Shikenan, wai sai yaushe zaka dawo ga yarinyar mutane nan na shirin mutuwa akanka MAM, don Allah kaji tausayin Meenal". Lumshe da idanuwansa dake cike da bacci Mutallab da har ya manta da zancen wata Meenal yace, "To idan ka gama gulmarka sai ka kashe wayar, dama shi yasa ka kirani". "Ba haka bane MAM wallah yau da kukan yarinyar nan takira ni tana tambayarka wai tanata neman layoyanka bata samu ba koka canza layi ne saboda ita, shine na shaida mata cewa ai baka ƙasar ne kayi tafiya, ni wallahi bansan ma ina tasamu lambata ba". "Aryan muyi magana gobe bacci nake ji sai da safe". Kafin Aryan yace wani abu ya kashe wayarsa dan yasan halinsa ba lallaine yabarshi yai baccinsa ba har sai ya ɓata masa rai, dariya Aryan yai kafin ya lalubi lambar Afrah, cikin Sa'a ta ɗagadan sallama sallarta kenan ta shafa'i da wuturi taji wayar tata naƙara, "Hello Habiby". Tafaɗa cikin wani sanyin muryar da yasa Aryan ɗan zamewa daga kan gadon da yake zaune ya kwanta a hankali yana rufe idanuwa, a shagwaɓe Afrah ta sake cewa, "Hello Habiby shine ka ƙyaleni". Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace, "ba wani Habiby Habibty bayan kin manta dani, kwana nawa baki jini ba amma ga alama hankalinki kwance, Allah sai na faɗawa Ummie". Ya ƙare zancen shima cikin shagwaɓa kamar yanda tayi, murmushi Afrah tayi haɗe da miƙewa itama ta haye kan gadon Jaddi (kaka) don a ɗakinta zata kwana kuma har yanzu tana can waje bata shigo ba suna fira kafin tashigo. MUTALLAB ASAD MUTALLAB (Labari mai taba zuciya) Na BILLY S FARI NANA DISO RUBUTUN ƳANTAGWAYE ZANGO NA BIYU TAFIYAR DAYA TAFI BIYU SHAFI NA ARBA'IN DA DAYA. Yau suka cika kwana biyar wacce take daidai da kwanakin da zasu huce makkah afrah da Mutallab je ke zubawa tantabaro hatsi inda Amal keta daukarsu hoto shikuma umar yana kallon Afrah anutse har mamakin yadda takeson ɗan uwanta yakeyi, Yadda yashigewa mutallab yazamana yazama na kusa dashi yanzu itama Amal sun dinke da Afrah sosai, karasawa cikin masallaci sukayi dan yau suna so su shiga ziyara wato rauda, Ahankali Mutallab yadaga ƙansa yana kallon yadda lema ke buɗewa tana rufewa ga kuma ruwan dake busowa tajikin lema, kwana biyun nan yarasa me isa yakejin jiƙinsa babu dadi, shiyasa yake hana ƙansa bacci yana dagewa da Addu'a yanzu ma da yakarasa baiyi komai ba sai Karatun Alkur'ani haka shima abokinsa umar, sai da sukayi Sallar La'asar kamin kuma su shirya zuwa makkah a hanya zasu tsaya su dauki Niyar umarah a masjid Nana aisha Anan suka tsaya akayi wanka sannan Aka dauki harama zuwa cikin garin makkah tafiya ce mai dan tsaho, symbols Mutallab yagani na inna yanuna Almasjid alharam wani kuma mina. Shigarsu cikin makkah yasasu fara ajiye kayansu sannan sukayi masjid alharam Nan suka fara gabatar da dawafi sannan sukayi safa da marwa daga nan sukayi sallah rakaa biyu suka sha zam zam sannan sukayi aske Afrah kuwa kuka sosai tayi haka Mutallab sai yaji bakin cikin mahaifiyarsa da bata raye da yakawota har tabar duniyar tana zuwa, kasancewa masallacinsu kusa da harami ne yasa suna gamawa suka sai abinci sukaje suka kwanta. ******* Ihun da ƴan kasuwar sukeyi suna faɗin " Kawo taimako shagunan Alhaji mutallab sun kama da wuta mutane kutaimaka " haka kasuwa ta rikice aka shiga kawo agaji Amma abunka da wutar bakaramin ci takeyi ba yasa aka kasa kashewa har sai da jalil yaje da kansa yakira yan kwana kwana yana kuka duba da container dinsu guda 40 da ko buɗesu ba'ayiba suna ciki. Daga yaron kantinan har jalil innalilahi wainna illahirrajiun suke ambata suna kuka sosai sai kazata yarane. Kuka sosai da addu'oi sukeyi haka itama ƴar chinan sai da ta kuka dan ita kadai tasab irin dukiyar da akayi asara wasu ƴan kasuwa nata faman Allah yakara cikin ransu dan daman gani sukeyi kamar mutallab din yazame musu ƙarfa. Wasu kuwa sunata kokawa duba da tashin hankalin da zasu shiga na rashin mai saukaka musu kaya dan kaf kasuwar nan babu wanda kayansu sukafi nashi sauki. Aryan ma shigowar sa kenan garin yaji labari Nan yashiga kasuwar yadda yaga sabbin shagunan sun koma sai da ya koka sosai jalil kam sai da akayi asubuti dashi saboda tashin hankalin da yake ciki, ko da aka sanar da tantè itama bakaramin tashin hankali tashiga ba duba da masu labarai zancen kawai sukeyi both gidan TV da radio. Jalil muyi hakuri muyi hakuri Allah yafimu sanin daidai." " Tantè sajida kayan da suka koni bakananan miliyoyi baniba " " Allah yana jarraba bawan da yakeso ne jalil danAllah kar asanar masa da wannan tashin hankalin." " Aryan da shigowar sa kenan dakin shima idonsa yayi jajir saboda tashin hankali yace " Anya jalil wannan ba aikin makiya baniba. DanAllah kar

Chapter 25 of 54