Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yafe mana baki ɗaya". Ɗago kai tayi cike da mamaki tace, "ka yafe Mani Mutallab? Nifa na sace kuɗin nan da sukayi sanadiyar mahaifinka ya koreka a gidansa Mutallab! Anya na cancanci saurin yafiya daga wajenka?" Wani abu Mutallab ya haɗe na baƙinciki tunowa da lokacin da irin zugar da sukayiwa mahaifinsa, sai dai mukammu muna yiwa Allah laifi ya yafe mana balle ita data cire girmanta na matsayin uwa tazo taroƙesa yafiya, duk girman laifinta a wajensa bai kai wanda ƴan uwan Annabi Yusufu a.s.w ba sukayi masa kuma alokaci ɗaya ya yafe masu da suka gane kuskurensa suka roƙesa gafara, hakan yasa yai ajiyar zuciya tare da ɗago kai yace, "ba komai Aunty har shi duka na yafe maku dama wanda ban sani ba, baki ga wannan korar ta zame Mani alkhairi ba tunda gashi nima na tsayi da kafafuwana na kuma mallaki gidan kaina? Wace ni'ima ce Allah beyi mani ba da zan kasa yafe maku? Alhamdulillah ba komai kuma komai yawuce awurina, sai dai yakamata ki tashi tsaye da addu'o'i aunty, azkar ɗin safiya da marece, na kwanciya bacci na warwarewar sihiri da sauransu duka ki dage dayi, a kiyaye sallah kan lokaci Aunty da lizimtar karatun alƙur'ani, sukaɗai zasu iya fiddake acikin wannan yanayin, abbama haka ko acikin abincinsa ne kiriƙa karantawa kina tofa masa da sannu za'a samu sauƙin lamurran nan da kuma waraka, zan ba Walid littafin husnil Muslim ko zuwa gobe ne ya kawo maku, tare da takardar addu'o'i akan yadda zaki warware sihiri idan ma akwaishi ajikinki, (kuduba addu'o'in a pages ɗin baya da tánte Sajida tasa Afrah tayiwa Jalil). Godiya tayi mashi sosai kafin ya shiga bata labari akan gidan da Walid ɗin zai zauna da har ankusa kammalawa dan makudan kuɗi ya zube sosai da za'a riƙa aikin ba dare ba rana yadda za'a samu a kammalashi cikin wata ɗayan da aka ɗiba kafin lokacin hidimar bikin nasu tayi. Suna zaune Afrah tafito cikin farfajiyar, tana ganin Aunty Amarya ta haɗe rai tare da juyawa, hannu Aunty Amarya tamiƙa tana faɗin, "Afrah". Hakan yasa Mutallab juyawa yaga tana ƙoƙarin komawa ciki, dakatar da ita yai tare da kiranta yace taƙaraso wajen. Ba don ranta yaso ba ta juyo ta  iso wajen ta tsaya bayansa ba tare data kalli inda suke ba. "Afrah baki ga Aunty Amarya bane da baki gaisheta ba". Turo baki tayi ta gaisheta can ciki-ciki Aunty Amarya ta amsa tana cewa, "Daina Allah Afrah keyi haƙuri kiyafe mani, duniya ta koya mani rayuwa na canza a yadda kika sanni da". "Dama ai haka rayuwa take kaɗan ma kuka gani.." kafin taƙarasa Mutallab ya daka mata tsawa haɗe da cewa, "Afrah yaushe kika koma haka?". "To yaya kamanta da duk abubuwan da tayi mani ne, har fa manya take cemani wlh ba wani tuna ko nadama da tayi kawai tunda taga Allah ya rufa maka asiri ne kawai.."  kafin takarasa Jalil daya fito daga cikin shima ya mangare mata kai yana cewa, "Koma dai meye ai kin wuce wajen tunda gashi kamar ba ayi ba, ki manta kawai". Yafaɗa yana kallon Aunty amaryar, Dan tuni take bashi tausayi itama saboda yanayin mulkin kama karyar da akeyi mata acikin gidan, kuma matuƙar ta tuba zata gyara halayenta da taimako ga ne kawai zasu iya fitar da mahaifinsu a halin da yake ciki saboda ita take tare dasu waje guda. Kallon Mutallab Afrah tayi tana dafe gun haɗe da cewa, "yaya ka ganshi ko". "Shine dai-dai ke tunda kin fara sauyawa". "A'a Mutallab kubarta tana da gaskiya duk cikinku babu wanda yasha takura da tsangwama awajena kamarta, amma dan Allah Afrah kiyi hakuri kiyafe mun kin ji?" "Aunty Afrah dan Allah kiyi haƙuri". Walid yafaɗa shima yana sosai kai, hakan yasa tacewa, "Allah kayafe mana gaba ɗaya". Wata ajiyar zuciya Aunty amarya tayi tana yimasu godiya kafin su tamiƙe tanayi masu sallama, kuɗi Mutallab yafiddo yabata yana jin tausayin yanayin da kaɗai take aciki, dan duk wanda ya kalleta zai iya rantsewa yace ƴar aikin gidansu ce, haka suka fice yabisu da kallo yana sake jinjina lamarin ubangiji Sarkin adalci da baya zalinci kuma baya bari ayi batare da utum ya girbi duk abinda ya shuka ba, gashi dai ita dake kallon kanta matar so ita da yaranta alokacin su kuma ana kallonsu wulakantacci marasa gata da galihu acikin gidan mahaifinsu saboda rashin uwa itace takoma a wannan matsayin da suke ciki da acikingidan mijinta, rayuwa kenan Allah dai yasa mu dace. ************ A ɓangaren Aryan baby irin saƙonnin ban haƙuri da bai turawa Afrah ba dana soyayya amma tana gani ko karantawa bata tsayawa yi take gogewa, yakirata awaya shima yafi a ƙirga bata ɗagawa daga ƙarshe ta sanyashi blacklist Dan har ga Allah Bata tunanin zata iya sake barinshi cikin rayuwarta duk da har yau tana jin soyayyarsa dake ƙasan zuciyarta na taso mata wani lokacin, hakan ba ƙaramin girgiza Aryan yai ba gashi bai raga Karan susar akaifa ba da zai iya tunkarar Mutallab ko Jalil koma tánte da zancen su shawo masa kanta, a ɓangare ɗaya ya sake shiga cikin wata damuwa ganin yadda aurensu Mutallab ɗin ya taso gadan-gadan har su uku shiyasa yake so a haɗe da nasu tunda ansan da zancensa, dan shi har ga Allah yana son Afrah baya so ta kuɓuce masa, gashi gabaɗaya taƙi sauraronsa balle ya samu su daidaita ahada da bukin nasu, dan alokacin itama Umma ta tada wuta lallai sai an haɗa dana Jidda tunda tuntuni kayan aurenta na ajiye, tasa Jidda takira mata AAB tace masa lallai-lallai in bai shirya auren ba yafaɗa a maido masa da kayansa a karbi na wani dan tare za'a haɗa bikinta dana ƴanuwanta, maganganu masu zafi ba tare da duba surukarsa take son zama ba ta yayyaɓa masa akan zancen, hakan ya sashi amincewa cike da don koya mata hankali domin idan har ita uwar zamani ce to shima ɗan zamani ne, dan haka itama ta shiga shirye-shiryen hidimar auren ƴarta cike da ikonsa kuma gadara dan Abba duk abinda tace cewa yakeyi eh ba tare da ya yi mata musuba.... #Mutallab Asad #Ƴan Tagwaye #Nana Diso #Billy S Fari. MUTALLAB ASAD MUTALLAB      (labari mai taɓa zuciya) Na Billy s fari Nana diso      RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU.    TAFIYAR BIYU TAFI DAYA   SHAFI NA SITTIN DA SHIDA. Murmushi Meenal tayi tana sake jin soyayyarsa acikin zuciyarta kafin ta ɗago idanuwanta tana kallonsa tace, "Kai ma kayi kyau sosai Askim". Ya saki murmushi shima haɗe da tada motar yabar wajen, yana fita sauran motocin da suka ɗauki ƙasashen nata da kuma ƴan uwanta sukabi bayansa, a dai-dai bakin wani katafaren waje suka iso da aka ƙawata, dama isowarsu kaɗai ake jira dan haka suna isowa aka shiga gudanar da programs da aka tsara, sosai wajen ya ƙayatar ɗan kana gani kasan bukin na masu hannu da shin ne, anyi komai cikin girmamawa, tsari da kuma natsuwa kafin akaci aka sha sannan aka watse kowa ya nufi gida, kasancewar dukkaninsu agajiye suke yasa basu tsaya ɓata lokaci ba Mutallab na ajiyeta ya juya ya wuce gida. Murna kam awajen Meenal ba'a magana ganin yadda hotunan bukin nasu ke yawo tamkar wasu taurari a samaniya, duk juya ɗaya sai tunaninta ya hasko mata kyakkyawan kusancin data samu da Mutallab wajen taron da irin kulawar daya bata, wanda hakan ya tabbatarwa da duniya auren so ne tayi da mijin nata bawai na tilastashi ba kamar yadda wasu ke faɗa ai ita ke son shi bashi yake sonta ba, Kyakkyawar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta kalli Nansy ƙawarta tace, "Nancy me zaki ce akan bukin nan nawa?" "Haɗuwar ƙarshe Meenal dan wallahi najima banga bukin daya burgeni ba acikin garinnan kamar naki ba, gashi a kallo ɗaya za'a ga kun bala'in dacewa da Mutallab". Taɓe baki Sarsy tayi haɗe da cewa, "A'ahh fa Nansy wallahi makaho ma yakallesu yasan Meenal wayo tayi masa dan tako ina Mutallab yafita haɗuwa, kawai dai kice bukin ya haɗu ba ƙarya" "What ever dai Sarsy gobe warhaka ina amsa sunan mrs Mutallab Asad Mutallab, wai Ni bari ma na tambayeki anya ba baƙin ciki kike mun ba? Naga fa kin saka mani idanuwa sosai sai kace Ni ɗin koma baya ce a kyau, dubeni fa sama da ƙasa rabbi yai halitta iya halitta da zaki riƙa wani cewa wayau nayi masa". Ta tashi tana jujjuyawa agabansu wanda hakan yasa duk suka kwashe da dariya, Nasmah ta riƙo hannunta tana cewa, "ƙyaleta ƙawata Allah dai ya samu a damshinki yasa muma mu fita wannan layin na marasa aure" "Amin Nasmah, Mutallab ɗin ne ma yaƙi wani saka friends ɗinsa a bukin mau be sai gobe wajen daurin aure ai da baza'a rasa wuɗanda zasu tayaki ba, shima fa daƙyar na samu ya amince ɗazu ya shiga wajen bukin saboda cewa yayi baya so hakan ma yasa bai yo wani shiri ba, ba mamaki saboda irinsu Sarsy iyayen sa ido yasa baiso shiga wajen ba". Duk suka sa dariya cike da takaici Sarsy tayi jifa da gyalenta da jakarta kan gado tamiƙe ta shige toilet tana faɗin, "kanku ake ji". Daga haka dai kowa yai shirin kwanciya Meenal kuma ta sulala ta nufi wajen Mommy da tunda ta dawo basu haɗu ba, cike da ƴan buki palourn Mommy yake sunata hadahadar taya Mommy wasu aikace aikan kafin wayewar safiya, ba tare data damu da gaishesu ba ta ratsa ta cikinsu ta wuce ɗakin baccin Mommy, idanuwa ta zaro ganin Asiya ƴar Mommy data zo da rana zaune bakin gado tana taya Mommy lunke dinkunanta da aka kawo mata tace, "Asy wai dama kunzo shine kike shigowarki nan wajen Mommy baza kike can ba asha fira?" Dariya Asiya tayi ganin yadda Meenal ta saki baki haɗe da zato idanuwa tana kallonta kafin tace, "Sorry Amarsu ta ango, ai naga bakwa nan sai yanzu kuka dawo ko?" Harararta tayi kafin taƙarasa wajen Mommy tayi hugging nata ta baya tana cewa, "kin gata ko Mommy? Ace program daya abukin nawa bata je ba fisabilillahi". "Tsakaninku ne baruwana Meenal, ya gajiyar bukin ashe har kun dawo?" "Eh Mommy, nazata fa zaki je?" Tafaɗa ashagwaɓe tana kallonta, murmushi Mommy ta saki tare da juyowa tana kallonta tace, "bakin dake cikin gidan namu Meenal a barsu wajen wa?" "Ah to! Faɗa mata Mommy tunda shagwaɓarta bazata barta ta tuna dasu ba, kuma da take zancen naje buki Mommy bafa ta gayyaceni ba". "Lallai ma Asy, yanzu Mommy Dan Allah bukin nawa ma sai na gayyacesa?" "Tambayeta ai gatanan gabanki, kinci abinci?" "Na ƙoshi Mommy". "A'a Meenal, kije kitchen a fridge ki ɗauki sauran haɗin kazarki kiyi warming ɗinta ki canye, nasan halinki dan haka bana son gardama jeki kiyi abinda nace, kuma ina kin gaida baƙin dake palourn da kika shigo ko?" "A'a Mommy". Kallonta Mommy tayi haɗe da cewa, "wace irin ɗabia ce wannan Meenal? Duk da wanda kika gani gidan nan saboda ke yazo, meyasa har yau baki san girmama manya ba? Haka zakiyi agidan mijin naki?" "Kai Mommy to kiyi shiru mana kada su ji, zan gaishesu idan zan fita yanzu". "Da dai yafi maki, Allah ya kyauta". Mommy tafaɗa tare da juyawa tabar ɗakin suka fice tare da Meenal ɗin nacewa Asiya ta sameta a ɗakinta tunda ƙawayenta na can. ************* A ɓangaren Aïcha kuwa har Babbar yaya zata fita sai tadawo tariƙe hannunta tana cewa, "Aïcha kinga yanayin gidan nan da zamu zauna da alamu maza ma anfi mata yawa, dan Allah ki zauna a ɗaki karki fito har nadawo, sannan nasanki da tsiwa koda wani zai zo maku da iskanci kada ki kulawa ki ƙyalesa, ki kama kanki ki kuma sare mutunci kinji?" "To babbar yaya sai kin dawo, Allah ya tsare hanya". "Amin ya rabbi". Babbar yaya taƙare zancen tare da ficewa, ksncewar dama bacci bai ishi Aïcha ba yasa ta ɗan zame jikinta a ƙasan ta kwanta tayi matshi da ledar kayan jikinsu tana jiran dawowarta, kimanin mintuna arba'in da fitarta can cikin bacci Aïcha taji ana sallallami haɗe da ihun Christian ɗin dake cikin gidan suma suna haya, a zabure tafarka tafito dan ta ɗauka wutace takama cikin gidan, sai dai ganin barbar yaya da tayi kwance a tsakar gidan cikin jini numfashinta na ƙoƙarin ɗaukewa yasata jin wani abu tun daga tsakiyar ƙafafuwan ta kafin tafara gani dishi-dishi, girgiza kanta ta shiga yi haɗe da ƙarfin halin ƙarasawa wajen ta durƙushe akan ƙafafuwanta sauti fuskarta, jintayi duniyar na juya mata tariƙo hannun babbar yaya data ɗago tamiƙo mata cikin karyewar murya tana cewa, "ki..kiyi ha..haƙuƙuri Aïcha". Tana gama faɗar hakan taga jikinta ya saki hannun nata yafaɗi ƙasa, kanta Aïcha ta tallabo ta ɗora a saman cinyoyinta tana girgiza kai dan gabaɗaya takasa magana sai bubbugar fuskar yayar tata takeyi tana so ta tashi, tabbatar da cewa yayar tata ta mutu ya sata sakin wata irin ƙara haɗe da somewa wajen nan take, da sauri Hajiyar gidan ta kira Isah mai shayi ta sanar dashi halin da ake ciki kafin tasa wasu mata hausawa dake tsaitsaye wajen cikin tashin hankali su janye Aïcha a yayyafa mata ruwa, Babbar yaya kuwa da aka tabbatar ta mutu akasa zane aka rufeta kafin Isah mai shayi daya kawosu gidan ya iso, cikin mintuna goma ya iso gidan akiɗime, nan wani Christian mai suna Elips ke sanar da Isah cewa suna zaune ƙofar gida suna kifi ne suka hango babbar yaya ta dawo da kaya a hannunta da alama sayayya ce tayo masu dan suna zaune bayan fitarshi itama tafita, a ƙoƙarinta na wajen tsallakowa titi dake nan gaban gidan wata mota tazo aguje ta kaɗeta sai dai sukaji ƙarara, kafin su ƙarasa wajen kuma har mai motar ya gudu, shine suka je suka ɗaukota suka shigo da ita kafin nan Allah ya amshi abarsa, faɗuwa zaune Isah mai shayi yai haɗe da dafe kai yana cewa, innalillahi wa inna ilaihirrajiun, kaico mu kaico duniya ina zaki damu? Wannan yarinya da kuka gani marainiyace ita da ƴaruwarta, wata ɗaya kenan da mutuwar iyayensu yanzu kuma gashi Allah ya kaɓeta tabar ƴar uwa, Allah ba kada dole mun tuba kayafe mana". Duk wanda ke wajen sai daya tausayawa Aïcha da har yanzu bata farfaɗo ba. Nan Isah yamiƙe yace su taimaka masa a maida gawar Babbar yaya a can ɗakin da suka kama haya dan Aïcha na a ɗakin Hajiyar gidan sannan yafita domin sawo likkafanin da za'a gyarata akaita makwancinta, kai tsaye wajen shayinsa daya baro yafara komawa ya sallami masu jiransa jiki sanyaye tare da basu haƙuri ya rufe shagon, wani maƙwabcin su Aïcha ɗin ne ke tambayarsa ko lafiya? Ya sanar dashi cewa ɗaya daga cikin yaran Ali makaho ne Allah yaiwa rasuwa tare da labarta masa abinda ya sani, sallallami yai haɗe da jima'i kafin yace masa ai kamata yai ya nemi danginsu a sanar dasu halin da ake ciki, nan yai masa jagora suka nufi gidan kawunsu Aïcha aka faɗa masa halinda ake ciki, kuka ya fashe dashi Yana mainadamar korarsu da yai tare da bin bayansu bayan yakira baffansu wato yayan mahaifiyarsu ya sanar dashi shima, kafin kace wani abu maganar rasuwar babbar yaya ta zagaye gari da kuma ƴan uwan iyayen nasu da mutane ke faman Allah yawaddaran abinda suka yiwa ƴaƴan ƴan uwansu. Nan aka haɗu aka yiwa babbar yaya wanka akayi mata sutura aka kaita gidanta na gaskiya sannan kawu yaiwa Isa godiya suka dauki Aïcha da bata um balle a'a sai hawaye kawai dake faman zubar mata a fuska, dan har aka kai yayar tata bata sani ba saboda sumar data dingayi duk lokacin data farfaɗo. Kawo yayi kuka yayi nadama ba adadi akan korar jinin ɗan uwan nasa da yai wanda gashi a sanadiyar haka sun rasa ƴarsa ɗaya, sai gashi tsakanin shi dangin mahaifiyarsu sun koma abun zargi ga junansu na ganin laifin kowanensu da bai riƙe su ba, nan babbar yayar su mahaifiyar Aïcha tace kawu yabata Aïcha ta tafi da ita tariƙe ta hannunta yace a'a su bar mashi ita dama shine dolensu rashin wadata tasashi tunanin bazai iya riƙe su ba, amma yanzu dole yayi ƙoƙarin gyara kuskurensa koda kuwa bara zaiyi ya riƙe Aïcha ya kuma bata kula har zuwa karshen rayuwarsa, haka akayi zaman gaisuwar babbar yaya nan gidan kawu har zuwa kwana uku sannan aka watse shi da dangin mahaifiyar tasu cike da nadamar abun da suka aikata. *********** Washe gari ƙarfe 1:00pm dai-dai na rana aka ɗaura auren MUTALLAB ASAD MUTALLAB da amaryarsa MEENAL ABDULMALIK MU'AZZAM bisa sadaki Naira dubu ɗari biyar, ba tare da ɓata lokaci ba ƙarfe 1:30pm aka wuce aka daura auren JALIL ASAD MUTALLAB da amaryarsa FANNAH UMAR FARUK, Ƙarfe 2:00pm dai-dai kuma aka nufi gidan kawunsu Mutallab Alhaji Kabir mahaifin Imam da shine yayan Abba dan sunanshi ne Walid yaci aka ɗaura auren KABIR (WALID) ASAD MUTALLAB da amaryarsa IMAM KABIR MUTALLAB sannan aka ɗaura na JIDDAH ASAD MUTALLAB da angonta ALIYU ALI BUKULLU (AAB). Bayan kammala duka ɗaurin auren ne Meenal tabuƙaci Mutallab daya zo gida za'ayi hotuna, ba don jinsa da yakeyi yau wani nadaban ba da Allah ya albarka da cikar wata ni'ima daga cikin ni'imominsa da bazai je ba saboda sam shi ba mutum ne mai son hotuna ba, amma zamowar ranar ta musamman ya sashi zuwa aka dauki hotunan aka gama sannan ya juyo suka wuce reception ɗin da Aryan ya haɗa masa na musamman duk ɗan don ganin ya gyara kuskuren daya aikata dan kullum sai Ummie tayi masa faɗa, Afrah kuwa tuni ya dauki dangana ya sakawa zuciyarsa akanta dan gabaɗaya bata saurarensa in ba lokacin bikin nan ma da suke ɗan gaisawa sama-sama ba, inda nan ne ya samu damar roƙonta akan ko bazasu koma yadda suke ba da yana so ta ɗaukeshi a matsayin yaya ko gaisawa ce suriƙa yi, ta yarda da hakan ɗin saboda ta hutawa takura da matsin da yakeyi mata, wanda ta tabbata yanzu daya san babu sauran alaƙa tsakaninta dashi in ba wacce ya roƙa ba bazai ci gaba da takura mata ba. Sosai reception ɗin ya ƙayatar don ba ƙaramin ƙoƙari Aryan yai ba, anci ansha mai kyau an kuma yiwa ango addu'ar zama lafiya tare da zuri'a ɗayyaba sannan aka watse... #Mutallab Asad #Ƴan Tagwaye #Nana Diso #Billy s fari MUTALLAB ASAD      (labari mai taɓa zuciya) Na Billy s fari Nana diso      RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU.    TAFIYAR BIYU TAFI DAYA   SHAFI NA SITTIN DA BAKWAI. Ƴan niger tundaga ranar suka kama gabansu dada taso ta zauna kawu yace samfa bazaiyihu ba gwara yatafi da mahaifiyarsa, dan duk yadda suke tunanin daukakar mutallab din Abun yafi ƙarfin tunaninsu dan haka sai huce da yamma duba da jirgi mutallab din yabiya musu. Sai da yamma tuƙunna Afrah tashirya cikin wata shigarta ta orange lace daga nan ta nufi can gidan Nasu ita da tante domin suyiwa Umma Allah sanya Alkhairi ko da sukaje motoci suncika ta ko'ina na ƴan daukar Amarya, sun gaisa da wasu daga ciƙin dangin abban wasu kuma basuma kulata ba, umma na zaune a palour da alama da wasu take zantawa ganin Afrah tace " Kunga diyar isa da takama sai yanzu zakizo ace ana bikin yar'uwarki amma dan baƙin ciki bazaki iya takowa ba?" " Kinsan Ana bikin su ya Mutallab ban iya barinsu nazo Gurin wacce zata wulakantani kokuma ta nuna batasanni ba sabida Allah ranar dinner banza tayimun ina mata magana harda yabamun magana acikin mutane." Ganin tante tashigo yasa umma canza zancen da faɗin " Tsakaninku ke da ƴar uwar taki." Sai da tante ta zauna kamin tace " barkafa da yamma ya taro, bamu shigo ba sai yanzu dayake can ma munyi taron." " Taro Sai godiya, babu komai hakan ma nagode." " To bari mu tafi Allah yasanya Alkhairi yabasu zaman lpya." Banza umma tayi musu suna fita suka kwashe da dariya sosai suna gulmar afrah, ai ingayamiki boka yagama da lamarin yarinyar nan tun yaushe aka kifar da'ita ai ita da aure sai dai taga anayi duk kyan nan nata." " Kawata bakida kirki." MAM kana ina ne? Motoci fa sun isa Amma fa babu wacce tafito kaga dare nayi." " Ina gida Aryan ban iya fitowa yanzu zan mata magana yanzu yafaɗa yana katse wayar." Tunda meenal ta rungumeshi a gidansu gaba daya ƙansa ya sauka daga charji, karfin sha'awar takai har idanuwansa gaba daya sun canza daga launikan da suke. Tsaki yadan ja sannan yatashi yakarayin wanka yado tare da alwala sannan yafita ta bayan gidan zuwa masalci duba da ƴan kawo amarya sun fara zuwa, sai da suka idar fa sallah sannan ya kira Idress awaya yazo da motarsa, kaji gasassu sukaje suka siyo daga nan kuma ya ajiyeshi suka shiga bashi ledar yayi yashiga da ita set room dinsa shikuma ya huce bangaren su Afrah. " Ai ni nazata baka gidan ashe kana nan?." Kallonta yayi yace " Yanzu na shigo nace bari nazo na dubaku idan da abunda kuke bukata gobe banjin zan iya fita kaina yana dam ciwo zan huta." " Bama bukatar komai Mutallab yakamata kasamu hutu, shima jalil din yanzu yabar nan ga Afrah can tanata kuka daki nayi rarrashin har nagaji." Mikewa yayi yashiga daƙin nata duk da yadda ƙansa ke masa ciwo sai yaji yakara Sara masa ƙallonta yayi haɗi da sir iriyar sallama yana shigowa zama yayi gefe Ln gadon haɗe da riko hannunta yana faɗin " me isa bakyason in samu nutsuwa da kwanciyar hankali? Yanzu me kuma akayimiki kike kukar nan Har Tante ta baki baki but you still keep crying?" " Kayi hakuri yaya nadaina." " Menene kike kuka?" Wai wata Asma kawar jidda ce ta zazzageni yaya har dacewa an kai kudinta da Aryan." " To me isa zaki biye mata afrah?" " Yaya ban biye mata ba bakaga acikin kawayen mu yadda ta dinga gayan magana ba harda kyauna na banza ne tunda har Aryan yagujeni." " Afrah kefa kikace bakyason aryan babu yadda banyi dake ba inaji? Kika nuna bakyason shi to menene na kuka dan wata tace tanasonshi?" " Yaya wallahi bansonshi kawai maganganun da tagayamun ne suka sakani kuka." " To ki bude kunnenki da kyau Allah nakara ganin kina shashancin nan sai na ɓata miki Aryan ankai kudinsa shekaran jiya ya lallaɓeki ya lallaɓaki amma still dai kince bakyasonsa and what cause all this. " ki tashi ki wanke fuskanki banason wannan kukan." To tace masa tana miƙewa. Shikuma yayiwa tante sai da safe yafita. Nikam mumyn meenal me kuke haka ne da yarinyar nan bazata fito ba ga masu mota can sunata jira? " hajj danAllah adan kara mana lokaci gamunan." " To kuyi sauri." Meenal ƙinyi shaving din?" Mumy yanzu sai nayi askin danAllah?" Wallahi ko kiyi kokuma in ɓatamiki ranki yanzu yanzunnan." To nagama mumy tafito tana faɗa. Nan mumy ta daga hammatar ta tashafa mata sure ta mulketa da perfume oil masu kamshi ta cilla mata kaninfar cikin baƙinta saura ki tsaya shirme kikama kanki kisani rayuwar gidan miji bakamar ta gidan.dadynki bace ba dole kiyi hakuri da abubuwa da dama idan bahaka ba wallahi meenal zakiyi kuka da idonki ki Nutsu ki bar rawar ƙan nan nagayamiki mijinki kamili ne ba irin shakatafin mazan nan baniba maza ki daura lafayya muje gurin dadynki. Ko data daura lafayyar wani sabon turaren khumrah Wanda aka hadashi da ruwan sanyi na bushra da oil na bushrah sai misik kaɗai sai wasu oil perfume da mumy takara masa nan ta shafe mata lafayyar dasu daga nan kuma sukayo gurin dadyn meenal yana zaune a palour dinsa daga kansa da yayi yaga diyar tasa na kuka yasakashi shima fashewa da kuka, haka suka rungume ƙansu suna kuka hajja ce tajata tana fadin kayi maya fada dady." Allah yayi miki Albarka meenal Allah yasakawa Aurenki Albarka kiyi hakuri duk inda kika tsinci ƙanki." Daga nan kuma suka shige mota aka tafi ƙaita. Iya tsaruwa da haduwar gidan sai wanda suka gani kawai kowa yazo yaga gidan da irin dukiyar dake gidan sai anyaba sai da suka kaita gurin tante daga nan akayi part dinta dasu, hajja ce ta dakko wani jug ta miko mata tanafaɗin ƙarbi ki shanye ƙinji wannan haɗin danyen zogale ne da

Chapter 38 of 54