Allah zansa yazo ya bada haƙuri shima kuma ya ɗauki matarsa." Wata doguwar ajiyar zuciya Dady yayi haɗe da kallon Alhaji Sidi kafin yace, "Allah ya sawaƙe Alhaji, amma yaron nan idan ya gaji da ƴata ya aiko mata da takardarta, ace ya kama yarinya yana duka har ɗan cikinta ya zube dan zai ƙara aure, fisabilillahi wannan aikin zarafi ne." "Adai yi haƙuri Alhaji ai baza ayi haka ba, duk da bana tsammanin haka daga wajen Mutallab, amma ko meye zan tuntuɓesa zan kuma tsawatar dashi kada ya sake haka ta sake faruwa, ayi haƙuri." "Allah ya kyauta." Dady ya faɗa sannan Abba ya kashe wayar yana jin zafin abinda akace Mutallab ɗin yayi duk da wani ɓangare na zuciyarsa ya kasa gasgata hakan, Dady kuwa kallonsa Alhaji Sidi yai haɗe da cewa, "Kaji abinda nake faɗa maka cewa ba lallaine ma yasan meke faruwa ba tunda ba waje ɗaya suke zaune ba kuma yakamata a taushi zuciya abata haƙuri, yaron nan ka tuntuɓesa kaji ko meya haɗasu, anan ne yakamata ka yanke hukunci idan har karɓarwa ƴarka takardarta zakayi." "Shikenan Alhaji sadi zanyi haka in sha Allah." Daga haka suka shiga wata fitar akan abinda ya kawoshi kafin yai sallama yatafi.
**********
Mutallab kuwa yana zaune a babban palournsa dake sama yana latsar waya cike da kewar Aïcha da tunda safe da sukayi breakfast ya barota a ƙasa saboda baƙin dake ta shigowa sai ga kiran Abba ya shigo, wata irin kunya ce ta rufesa don bai samu ya kirasa ba tun jiya da suka wuce bayan gama ɗaurin aure, cikin girmamawa ya ɗaga yana jin duk jikinsa a mace, "Abba barka da rana ya kuka isa jiya?" "Lafiya kalau Mutallab ya iyalin naka da kuma hidima? An watse taro lafiya dai ko?" "Eh Abba, ina ta cewa zan kiraka naji ya kuka sauka.." bai ƙarasa ba Abba yace, "Karka damu tunda muna tare da Jalil, ya bamu cikakkiyar kulawa." Murmushi Mutallab yai cike da jin daɗin hakan kafin can Abba da yai shiru yana tunanin ta yadda zai fara kamo bakin zaren lamarin, so ɗaya nisa jin Mutallab yace, "Abba ko akwai wani abu." Sannan yace, "Eh dama maganar matarka ce Meenal akace mani tana gidan iyayenta, banji daɗi ba ko kaɗan shiyasa nakasa jurewa gudun kar mutane su fassaraka nace bari naji me yasa ka aikata hakan?" Take yanayin Mutallab ya canza dan ko maganar Meenal ɗin baya son ji saboda hasarar gidan Jininsa da tayi masa, sai daya ɗan ciza leɓensa na ƙasa yana jin zuciyarsa nayi masa wani zafi tunawa da hakan kafin yace, "Abba ta cancanci taje gidansu ne shiyasa..." Nan ya kwashe duka abinda yafaru tsakaninsu akancikin kaɗai ya faɗa masa, shi kanshi Abban yaji ba daɗi zubar da cikinsa Meenal tayi, amma duk da haka dannewa yai tare da cewa, "Tabbas ta cancanci fiye da wannan hukunci amma duk da haka kayi haƙuri idan kadawo kaje ka ɗauko matarka, sannan ka tsaya tsayin daka akan matarka saboda sam alaƙarta da Ummanku Ni ban yarda da ita ba, koma meye nasan akwai sa hannunta aciki tunda tare take da ita, dan haka itama nakorata gidansu har sai ranar daka je ka dawo da matarka sannan tadawo". "Amma Abba.." "A'a Mutallab kada kace wani abu, ai duk wanda kaga Abba hakuri to an cucesa ne, saboda haka kayi hakuri kaji ko?" "To Abba Shikenan." "Yasu Dada?" "Duk suna lafiya?" "To madallah ya zancen dawowar taka yaushe ne?" "Eh Abba da wata ɗaya naso yi kafin nadawo saboda ina so naga yadda karatun ita Aïcha zai kasance kafin nadawo nan." "A'a Mutallab! Indai ba wata matsala yakamata kadawowa harkokinka nan da sati biyu tunda ga wasu iyalin anan kabari." Bazai iya jayayya da mahaifin nasa ba don haka ya amsa mashi da "toh." Duk da har ga Allah baya da sha'awar komawa ƙasar yanzun saboda Meenal, so ya yi sai ya koya mata darasi kafin yakoma amma ko yanzu ba damuwa, zai banbance mata tsakanin da da yanzu don bazai koma ɗaukar wuɗannan munanan halayen nata ba...
#Mutallab Asad
#Ƴan Tagwaye
#Nana Diso
#Billy s fari
SHAFI NA CASA'IN DA BIYU
*MUTALLAB ASAD*
Arewabook:- billysfari
Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.
Sai da suka ɗan taɓa fira da mahaifin nasa kafin sukayi Sallama dashi, aje wayarsa keda wuya sai ga Afrah da Aïcha sun shigo ɗauke da warmers a hannunsu, da idanuwa Mutallab yabi Aïcha da kallo yana amsa gaisuwar da Afrah keyi masa wanda hakan yasa Afrah na ajiye warmers ɗin hannunta tafice daga palourn da sauri, shi kuwa har Aïcha ta ƙaraso ciki idanuwansa na akanta ta nufi wajen dining table ta ajiye kulolin dake hannunta da sauran kayan data shigo dasu, juyowa yai ta saman kansa dai-dai lokacin data baro wajen haɗe da miƙa mata hannu alamun tazo gareshi, cike da jin kunya ta miƙa masa hannunta daya sha jan lalle kanta na a sunkuye a ƙasa ya zagayo da ita gabansa yana jin duka jikinsa na amsawa, saman cinyarsa ɗaya ya yimata masauki tare da kallon cikin idanuwanta da mayatattun nasa idanuwan da lokaci ɗaya suka ƙanƙance masa saboda yanayin da yake ciki, sosai yake da buƙatuwa da ita amma yadda yaga ta kasa sakin jiki dashi da yadda ta nuna bata sonshi tun farko yasa yakasa kusantarta adaren jiya, har ga Allah baya son zuwa gareta sai ya tabbatar tafara son shi da kanta shiyasa ya yanke shawarar haƙura da ita ba tare daya kusance taba don ta tabbatar soyayyar da yakeyi mata ta gaskiya ce ba jikinta kaɗai yake so ba, cikin wata irin kasalalliyar murya yace, "Baby haka ake kula da miji kin barni anan ni kaɗai kinata sabgarki da baƙinki har yunwa na neman kawo mani hari." Bata ce komai ba ta shiga wasa da yatsun hannunta tana jin wani irin baƙin yanayi atattare da ita jinta ajikinsa, bata ankare ba taji ya tura hannunsa cikin rigarta haɗe da sauke shi saman cikinta da sauri tayi wata irin zabura tana neman zillewa daga saman jikinsa yace, "Why Aïcha am I not your husband? Ki kwantar da hankalinki ba abunda zanyi maki har sai kin fara sona da kanki, a wannan lokacin ne zan amincewa kaina dana bari wata alaƙa ta auratayya ta shiga tsakaninmu tunda bakya sona." Ba tare daya bata damar yin magana ba ya sake cewa, "Kinci abinci kuwa?" Ta girgiza masa kai tana faman mutsumutsu akan cinyar tasa ta kasa zama waje ɗaya saboda yadda yake yawo da hannun nasa asaman cikinta, wanda hakan ba ƙaramin sake jefasa cikin wani irin yanayi yai ba, "Tashi muje muci dan da alama cikin nan naki shima yunwa yake ji." Ya ƙare zancen yana ɗagata cak zuwa dining table ɗin dan so yakeyi ya saba mata da jikinsa sosai saboda yana da sha'awar haka, ita kuwa cike da ƴar shagwaɓa ta turo baki tana cewa, "Namu fa nacan wajensu tánte zan je muci tare." Bai tankata ba har sai daya direta akan ɗaya daga cikin kujerun dining table ɗin haɗe da cewa, "Waya faɗa maki haka akeyi? Yanzu tare zamu riƙa cin abinci su kuma suci nasu su acan." Ya ƙare zancen tare da wucewa can gefen dining ya buɗe dishes wadrobe dake wajen jere da dishes farare ƙal da suka bayyana kasancewar marfinta na glass ne ya ɗauko plate ɗaya haɗe da spoon ya nufi wajen sink dake can gefe duk cikin palourn ya wanko sannan ya dawo ya ajiye agabanta yana cewa, "Wash! nagaji Baby taimaka ki zuba mana muci ko?" Dariya Aïcha ta saki ganin ɗan aikin da ya yi amma har da su faɗin wash tana cewa, "Lallai ya Mutallab, yanzu ɗan wannan aikin har ka gaji? To ni zan iya dafa abinci na gyara ɗaki nayi shara da mopping duka ban gaji ba." Taƙare zancen tana dariya tare da buɗe kular ta shiga zuba masa abincin, kallonta yakeyi har sai data gama sannan yace, "Da gaske duk kin iya wannan aikin?" "Eh mana, ka tambayi Dada." tafaɗa tana rufe kular tare da tura masa abincin agabansa, maƙe mata kafaɗa yai tamkar yaro yana langaɓe kai irin bazai ci ba." Murmushi ta saki tare da cewa, "kai ya Mutallab, kai fa kace na zuba maka!" "Eh amma ai baki jira nafaɗa maki sauran aikin ba kika turomun abincin ko?" "To kayi haƙuri, me zanyi maka yanzu." "A baki zaki bani.." Saurin rufe fuskarta tayi da hannu tun kafin yaƙarasa cike da jin kunyar abinda yakeyi mata, karatun mama Yabi ta tuno dashi da tace mata shi namiji kamar yaro yake, indai kina so ki mallakesa dole sai kinyi masa duk abinda yake so tare da shanye duk wata rigima tashi, a lokacin ne ke kuma sai yadda kikayi dashi musamman kina haɗawa da hanyoyin faranta masa ta hanyar kwanciya da kuma daɗaɗan kalamai, cikin jin kunya ta duƙar da kanta ƙasa ta ɗauki spoon tare da ɗebo abincin tana kai masa abaki ba tare data bari sun haɗa idanu ba, a hankali ya buɗe baki ta saka mashi abincin yana kallonta cike da so da kuma ƙauna kafin ya lumshe idanuwa ya kuma sake buɗesu akanta, har ta sake ɗebo wani abincin zata kaimasa abaki sai taji ya haɗe spoon ɗin tare da hannunta ya kaimata a nata bakin, ɗago kai tayi da sauri tana kallonsa ya yimata alama da idanuwansa yana cewa, "haa.. mana." Ta fahimci ko me yake nufi dan haka ba tada zaɓin daya wuce yin yadda ya umurce ta buɗe bakinta shima ya bata abincin taci, haka suka ci gaba da ciyar da junansu tana bashi yana ci shima yana bata har suka ƙoshi, bayan sun gama ta kwashe kulolin ta ajiye a gefe sannan ta tattare wajen ta kwashe ta goge shi ƙal sannan ta nufi hanyar fita da kyan da suka ɓata da niyar wa kowa, ba'a fi mintuna biyar ba ta dawo ɗauke dasu tasa tissue ta goge sannan ta mayar dasu inda taga ya ɗauko su, duk wannan abubuwan da takeyi idanuwansa na kanta har ta kammala ta nufi hanyar fita, "Amma.. Aïcha." Taji yakira sunanta cikin wata irin murya, juyowa tayi yace , "zo mana." Ya faɗa yana miƙa mata hannu lokaci ɗaya kuma yana ƙoƙarin kunna tanƙamemiyar tv dake laƙe ajikin bangon palourn, hannunta ya riƙo ya sanyata ajikinsa yana cewa, "Zauna ki huta tare da mijinki, baƙin nan sun isa haka." Ya kwantar da ita saman kujerar da yake zaune yayi mata matashi da cinyarsa, wani indian film ya kamo masu a tashar Bollywood suna kallo yana yi yana wasa da jelar gashinta kanta daya sha kananan kitso sun fado mata agefen fuska da kuma kafaɗa, wani amsawa A'isha taji jikinta nayi kafin a hankali taji wani irin daddaɗan bacci na kawo mata ziyara, kafin kace wani abu har bacci yayi gaba da ita sai dai Mutallab yaji sautin fitar lumfashin nata dana dai-dai ba saboda yanayin kwancin da tayi, ganin haka yasa ya gyara mata kwanciyarta ajikinsa yadda zata ji dadin baccin sosai tare da rage volume ɗin tv ɗan kada ya sameta. Hannunsa ya miƙa da sauri jin ƙarar wayarsa ya ɗauko tare da kashe ƙarar sannan ya ɗaya, mahaifin Meenal ne daya gama amincewa da shawarar abokin nasa ɗari bisa ɗari yakirasa, dan haka cikin girmamawa ya ɗaga bakinsa ɗauke da sallama yana gaishesa. Amsawa Dady ya yi tamkar ba abinda yafaru haɗe da cewa, "Dama akan zancen Meenal ne data dawo gida kuma banji ka kira kayi mana bayanin dalilin dawowar tata duk da dai munji daga bakinta, shine nace bari ni nakira naji meke faruwa daga bakinka dan yadda naji abubuwan daga wajenta bai mun daɗi ba ko kaɗan." "Haka ne Dady ayi haƙuri amma nace Meenal ta dawo gida ne sanadiyar zubar mani da ciki da tayi saboda zan ƙara aure, na nuna mata kada tayi hakan saboda ina sonta kuma ina don abinda ke cikinta amma sai taƙi wai bazata barshi ba har sai na janye zancen ƙara auren, kuma Abba ina da tarin dalilan da suka sani ƙara aure wanda duk itace ta janyo hakan." Yaƙare zancen tare da miƙewa yana barin palourn, a can barkyard na upstairs ɗin ya nufa yana hango yanayin anguwar da suke ciki daga can sama a ɓangare ɗaya yana saurarar Dady dake cewa, "Subhanallahi, amma ni cewa tayi ka daketa haɗe da ɓarar mata da ciki garin dukan nata bayan cin mutuncin da kake yimata akoda yaushe." "Wallahi tallahi Dady ba haka akayi ba, ita ɗin matata ce Dady taya zan zauna ina dukanta tunda ba haka bace? dan fa ina son Meenal Dady na aureta me zaisa nakoma cimata mutunci..." Nan ya zayyane ma Dady duk abubuwan da takeyi masa na cin mutunci shi da ƴan uwansa, ƙasa tare da takeyi da sauran duk abubuwan da takeyi da baiyi niyar faɗa ba saboda jin ƙaryar data sheƙa masa, wata irin kunya ta rufe Dady dan tabbas duk abinda Mutallab ɗin ya faɗa akanta yasan gaskiya ne tunda yasan halinta ne tun tana gida, ajiyar zuciya yaja ya sauke haɗe da cewa, "Shikenan haka akayi ashe ko? To kabarni da ita Nagode Allah yayi maka albarka." "Amin Dady sai anjima." Mutallab ya faɗa yana cire wayar daga kunnensa cike da mamakin ƙaryar Meenal take tayi masa bako kunya, ajiyar zuciya yai haɗe da cewa Allah ya kyauta sannan yakoma cikin palourn yana sake gyarawa Aïcha kanta dake baccinta hankali kwance, jin yayi shima yana da bukatar baccin dan haka ya kashe kayan kallon sannan ya ɗagata ya wuce da ita cikin bedroom ɗinsa ya kwantar da ita akan lallausan gadon nasa tare da hawowa samansa shima ya janyota ajikinsa yana sauke wata irin ajiyar zuciya. Bai jima ba shima baccin yai gaba dashi cike da tarin mafarkai masu daɗi kala-kala.
Dady kuwa da bai taɓa jin kunya ba irin ta yau da nadamar gatan daya bawa Meenal jin tarin matsaltsalunta da mijinta ya lissafo masa ko ɗaya dawo gida bai nuna mata komai ba, lafiya kalau ta tarbesu tana yimasa sannu da zuwa haɗe da tambayarta ko akwai wani abu tace a'a sannan ya wuce ɗakinsa Mommy na biye dashi abaya, ganin yadda fuskarsa take ba walwala ya sata fara ciro ruwa a fridge ta tsiyaya masa ya sha sannan ta haɗa masa ruwan wanka ya shiga yayi, yana fitowa ta kawo masa abincinsa yaci kafin ta kallesa fuskarta ɗauke da damuwar itama tace, "Alhaji lafiya kuwa?" "Lafiya kalau Hajiya Mariya." Ya faɗa yana ciro kuɗi masu ɗan yawa haɗe da miƙa mata yace, kije ki sallami duka masu aikin cikin gidan nan ki faɗa masu zan nemesu daga baya kuma ina sha Allah duk wata zanci gaba dabiyansu salary ɗin su." "Alhaji a sallamesu da kace? Kasan fa gyaran gidan nan nada wahala gashi kai ma kana buƙatar kulawata, ba wai bazaniyayin duka ayukka bane amma za'a iya samun tauyuwar kulawa daga wani ɓangaren." Ɗago kai yayi ya kalleta haɗe da cewa, "To meye amfanin Meenal acikin gidan nan tunda ta zaɓi zamansa, kawai suke zata cigaba dayin duka ayukkan da sukeyi." Zaro idanuwa Mommy tayi dan tasan ko sama da ƙasa zata haɗe Meenal baza tayi ayukkan nan ba, ataƙaice ma yasan bazata iya ba indai ba so yakeyi a zauna da ƙazanta cikin gidannan ba, sanin batada wani iko na sawa ko hanawa ga dukkanin lamurransa da yaransa ya sata yin shiru tare da miƙewa tabar ɗakin tana mamakin sauyawar ra'ayin mijin nata daga matakin da yayi niyar ɗauka shekaran jiya. Kamar yadda mijin nata ya bata umurni haka taje tayi ta sallami duka masu aikin nata sannan ta wuce ɗalibta har lokacin batadena mamakin wannan abun dake shirin faruwa ba acikin gidan.
Da daddare bayan sun gama dinner tare har da Kamal Dady ya kallesa haɗe da cewa, "Kamal ga ƴar uwarka nan ina so kullum kayi mata tuni akan gyare-gyare da aikace aikace gidan nan idan ta manta saboda na sallami masu aikin gidan nan gaba ɗaya, tunda ta zaɓi zama gidan ubanta to yazama dole tayi duk wani abun daya dace acikinsa tunda itama ƴa mace ce, yana kaiwa nan yamiƙe tare da barin wajen, Meenal da lomar abincin data kai bakinta ta sarƙeta jin abinda mahaifinta ya faɗa har saida Mommy ta miƙa mata ruwa tasha ta miƙe da sauri daƙyar tana cewa, "Da..dad.daddy me kake faɗa? Taya zan iya gyaran gidan nan Dady ya yi girma da yawa, gaskiya bazan iya ba kawai amaido masu aikin suci gaba dayi." Kota kanta Dady baibi ba yaƙarasa shigewarsa ɗakinsa, wani kallo ta yiwa Mommy hade da cewa, "Munafuka koma meye dasa hannunki wallahi kuma tsinke bazan ɗauke ba ni da gidan ubana." Cikin ɓaci rai Kamal ya nunata tace da cewa, "Tir wallahi ke kam kinji haushi Meenal, wai Mommy kike faɗa wa haka? To wallahi ni dake mu zuba ido acikin gidan nan, kin dai ji abinda Abba yace, tunda kin ki sharar masallaci zakiyi ta kasuwa, wawiya kawai". Ya ƙare maganar yana tura kujerar daya tashi akai da ƙarfi haɗe da barin wajen. Meenal kuwa ta ɗauka da wasa Dady keyi duk da taga ba mai aiki ko ɗaya acikin gidan, dan haka washe gari tayi kwancinta a ɗaki hankali kwance tamkar ma bata san da zancen ba, tana cikin bacci taji an kwaro mata ruwa ajiki cikin kofi, Kamal ta gani tsaye abakin ƙofa fuskarsa ba wasa yace, "Me Dady yafaɗa maki jiya?" Cike da masifa da tsiwa Meenal tace, "Bansani ba bana son haka fa ya Kamal." Tana maka masa harara, saukar marin da taji a fuskarta yasata dirowa daga saman gadon ba shiri, "Uban me kike cewa? Me nafaɗa maki jiya da zaki kwanta har ƙarfe takwas na ƙoƙarin bugawa baki aikata uwar komai ba? Me kikeyi kwance ne?" "Dady.." "Shut up my friend zaki wuce ne ko saina tattakaki a wajen." Jiki na rawa cike da mamakin mahaifin nata Meenal ta fice daga ɗakin tana ganin abun kamar a mafarki, tun Meenal na daukar abun da wasa har taga ashe da gaske Dadyn nata keyi. Dole ta fara aikin tanayi Kamal na maida ita baya, shara kaɗai sai da tayita kusan sau biyar tana sakewa, mopping kuwa tun tanayi a tsaye har ta koma yi a zaune Kamal na sake maida ita baya dan kwata-kwata beyi ba saboda ruwan data shakaka a tsakiyar palourn, aikin da gabaɗaya bai wuce awa ɗaya da rabi ba sai gashi Meenal ta kwashe awa kusan biyar tana yi, dan tun ƙarfe takwas bata samu tagama ba sai ƙarfe sha biyu na rana daidai, tayi baƙin rai da turo baki har ta gaji, da kuma ta nufi wajen dining dan tayi breakfast Dady Dake zaune falo ya daka mata tsawa haɗe da cewa, "Ina jin ke da Mommyn taki duka matan aurene, ita tana zaman gidan mijinta ne tare da hidimta masa domin shine dolenta, ke kuma tunda kin zabi zaman gidan ubanki kin yada na mijinki sai ki shiga kitchen da kanki ki ɗora abunda zaki ci dan bazata koma dafa abinci dake ba na soke haka, haka ma daga yau babu wani mai wanki da zai sake zuwa ya karbi kayanki da sunan wanki, ki wanke abunki dan ke kika yimasu datti da kanki ba wani ba, abu na gaba bana son nariƙa iskoki kina shawagi cikin gidan nan, ki zauna can cikin ɗakinki, Mommy uwa take gareki, Kamal kuma yayanki ne, daga yau kar na sake jin kin ɗaya muryarki akan tasu, dukkansu sama suke dake dan haka dole ki koyi yadda zaki girmamasu cikin mutuntawa, saɓanin hakan zaki iya haɗuwa da fushina ko kuma ki canza gidan wani uban amma bani." Yana kaiwa nan ya rufe jaridar dake hannunsa yana karatu yabar palourn.
#Mutallab Asad
#Ƴan Tagwaye
#Nana Diso
# Billy s fari
SHAFI NA CASA'IN DA UKU
*MUTALLAB ASAD*
Arewabook:- billysfari
Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.
Akwanaki biyun nan bakaramin tashin hankali meenal tashiga ba dan kuwa kowanne bangare babu dadi ha aikin gidansu kamar yakasheta dan ma mumy tana gyara part din dady da masifun sun mata yawa duk yadda take tunanin abunda sauki Amma kwata kwata bahaka yake ba dan kuwa bakaramin tashin hankali take ciki ba duba da abincin ma dady ya hana mumy ta bata, yanzu ma tsaye take baƙin bandakinta dubawa tayi taga wani kalar datti dayayi hawayen da yazubo mata yasanyata saurin goge fuskarta, tabbas bata iya zaman gidanta gwara ta koma gidan mijinta, ada kanwar mama tana yawan gayamata amfanin taimakawa mumy idan tana aiki sai yanzu ta tabbatar rashin gata tasaka kanta ba gata ba, hatta sharar falo da mopping sai ta mai maita sai uku sannan take ganin ya dawo daidai takusan mintuna talatin a bandaki kamin tagama wankewa samun guri tayi ta zauna gefen gadonta tana kara gwada kiran Mutallab akaro da babu adadi amma kuma bai dauka ba, ga wayar umma kwatakwata bata shiga ma ballantana ta kokarta gurin samar mata mafita, Ga mumy ko kallonta batayi idan ma taganta a falo to itama tana kokarin ganin ta bar mata gurin, yaya kamal ma yana bayan horen da ake mata, jin motsin dady a palour yasanyata saurin sakkowa kasa har tana kokarin tuntube. Dady da yazuba mata idanu zuciyarsa tana karaya da lamarin diyar tasa sai kawai yaji kwallah ta cicciko masa tabbas mumy tafadi gaskiya da take yawan gayamasa ba gata yakeyiwa meenal ba dan ita din watarana mallakar wani ce kuma uwar wasu ce, tabbas yanzu yatabbatar da spoiling din da babu abunda yake haifarwa sai nakasu ga rayuwar yaron, dan ma yana raye yau da baya raye fa? Shikenan rayuwar diyarsa ta lallace babu mai tallafa mata. A hankali yaja ajiyar zuciya yana kallon meenal dake tsaye agabansa " Lafiya kika tsayamin a ka? Har yanzu baki iya ladabi ba ko? Haka kikeyiwa mijin naki.? " cikin sauri ta tsugunna tana faɗin " Kayi hakuri danAllah dady Nasan duk abunda nayi ban kyauta ba danAllah zan koma gidan Mutallab zan kiyaye abubuwan da bayaso zan kuma zauna da matar tasa tafada kuka na kufce mata." Shima hawayen ya goge yana kara kallonta cike da tausayi. " Wancan karan haka kika kalleni kika gayamun zaki canza Amma baki canza ba meenal, kina tare da namiji irin Mutallab kike wasa da damarki? Yaran manya nawa suke auran manya suna musu biyayya sai ke? Ga kazanta ga fitsara? Kina tunanin da Allah ya kaddara yasakeki fa? Har ki iya kallon mumy kina zaginta? Ita umman kishiyar uwar Mutallab din ce ai kinsan halinta?." Saurin taron Abba tayi tace " Wallahi dady umma tanasona kuma bata taba sakani mugun abuba." Sai a Sannan ne mumy ta dan kalleta sai kuma ta kauda kanta." " Naji tana sonki kina sallah akan lokaci? Kina wankan janaba?" Meenal datayi saurin sun kuyar da kanta kasa dan kunya. " Duk inayi dady." " Ban yarda ba dan mai tsaida sallah da cikakken wankan tsarki bazaidinga wannan abubuwan ba meenal duk da haka banki camzawarki ba zan kara baki wani chance din yanzu tashi kije ki gyara dakin kamal daga baya mayi magana zan tuntunbi mijin naki." Da fara'a sosai kan fuskarta tayiwa dady godiya sannan tashige ciki." Dady kuwa da ya kalli mumy sai cewa yayi " Ina gudun anya ba wannan matar uban nasa baceba take zuga meenal?" Mumy dai batace komai ba sai uhmm Allah ya kyauta." Dady da baiji dadin maganar ba yace " Yaya ina magana kina uhmm haba mumyn meenal kome yarinyar nan tayimiki hakuri yakamata kidingayi ni wallahi tausayi take ban ma." " To da bana hakuri dadyn meenal zakaganni anan ne? Ai hakurin yakawo." " To danAllah kiyi hakuri nima naci albarkacin bakinta mumy yau idan bana raye nasan zaki kulamin da yarana Wallahilazim babu kaffara Amma nuna bacin ranki ko fita harkar meenal hakan banajin dady shiru kawai nake miki yau idan diyarki
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 52 Chapter of 54