da Mutallab suna fira, acikin firar tasu ne Aryan ke cewa Mutallab yana so ya ara masa million goma yana so yafara wani kasuwanci, kallonsa Mutallab yai jin maƙudan kuɗin daya ambata sai kace bai san yanayin yadda kasuwanci ke tafiya ba, batare da yace komai ba ya maida hankalinsa ga wayarsa da yake ƙoƙarin turawa Meenal saƙo sannan ya maido hankalinsa gareshi suyi magana yaji wane kalar business ne kafin ya bashi kuɗin.
Aryan daya gama kaiwa ƙololuwar ɓacin rai ganin Mutallab kamar ya shareshi yace, "MAM Magana fa nake maka kayimun banza." Murmushi Mutallab yayi Yace, "wane banza nayi maka Aryan abu nake turawa ne amma kayi haƙuri, ina ga dai wani yaɓata maka rai zaka huce kaina dan tunda kazo gidan nan magana kaɗan sai naga ka ɓata ranka akai?" "Kaga malam ni ba wannan nake magana ba million 10 nace ka aramun in zaka ara bawai ka mai dani mahaukaci ba." "To naji yi haƙuri amma Aryan wane irin business ne zakayi da million goma?" Cikin ɓaci rai Aryan yace,
"Ban sani ba Mutallab Asad, nace ban sani ba aikin banza da wofi dan kazama mai arzuki shine kake so ka wulaƙantani? Nace shine kake so ka wulakantani Mutallab." Ihun da yakeyi dashi tamkar dama can jiraye yake da Mutallab ɗin yasa Afrah dasu tante Sajida da kuma Jalil da baisan Aryan na gida ba fitowa barandar dasu Mutallab ɗin ke zaune, Cikin ɗan ɓacin rai Mutallah daya fara hasala da ihun da Aryan keyi masa akai yace, "Wai menene haka Aryan? Menene haka nace?"
Aryan yace, "ban sani ba idan bazaka aramun kudin ba kawai ka faɗa mun bawai sai ka wulakantani ba, Arzuƙin ka name? Kamanta lokacin da mahaifinka ke hanaka kudi yana hanaka abinci ni ke ƴammaka? Ko kuma ka manta sanda mahaifin naka ya koreka daga gidan sa gidanmu na kaika? Nayi maka duk wani hallacci a arayuwarka amma Ni kake tozartawa dan katara abun duniya, tir da wanda bazai iya maida fiye da alkhairin da akayi masa ba, ina Motar da ka taɓa siyamun da bata wuce ta million 6 ba itace kaɗai kyautar daka taɓa yimun ko? To dan meye zan zo na buƙaci kuɗi agunka ka mai dani mahaukaci?."
"Subhanallahi Aryan, wai menene haka kakeyi, haba danAllah ba girmanku bane kudena". Jalil da ransa ya ɗan soma ɓaci ya faɗa yana riƙo Aryan, fizge hannunsa yai haɗe da cewa, "Dallah sakeni munafuki, kudin dan uwan naku uban waye yasan na menene! Aikin banza da wofi kawai" cikin ƙaraji Afrah takira sunansa tana cewa, "Aryan karka manta shi ɗin yayana ne? Dukkaninsu ƴan uwanane basu cancanci haka agunka ba". Wajenta ya tako yana kallon cikin idanuwanta haɗe da cewa, "Me kika ce? Cancanta? Ai daga ke har su babu wata kima da kuke da ita a idanuwana da zan kalli cancantarku, daga lokacin dana gano kuɗin butulu ne masu manta alkhairi na fahimci baku cancanci duk wata mutuntawa daga wajena ba dan haka kar bakinki ya sake ambatar kalmar cancanta saboda batada muhalli acikin gidan nan". Ya ƙare zancen tare da juyowa ga Mutallab yaci gaba da cewa, "Kai kuma daga yau bani bakai, kanwarka kuma nafasa aurenta kuje can ku bata ɗan iskan da take bi babu ni babu ita kowa yakama gabansa, wannan shine mukullin motar daka bani dan haka ga tsiyarka nan bana so". yacillawa Mutallab makullin agefen fuskarsa, hakan yasa Jalil da ransa yakai ƙololuwar ɓaci ya shaƙo wuyansa yana kallonsa da idanuwansa da sukayi wani mugun kaɗawa sukayi jajir, "Sakarshi Jalil". Mutallab da tsoron Allah ya kamashi yafada yana kallonsa.
"A'a da kabarni na sauke masa karamin haukan dake kansa." Aryan ya faɗa tare da fincike hannunsa dan tsabar zuciya Jalil ma yakasa cewa komai, wani kallo Aryan yaiwa Mutallab yana cewa, "kadai faɗa masa ni ba sa'arsa bane duka nafi karfinku ƴaƴan bora kawai wanda ubansu ya koresu daga gidansa saboda bakin halinsu ke kuma na fasa auren yar iska kawai mayaudariya".
Dariya Afrah tayi cike da takaici tace, "Ka kwantar da hankalinka wallahilazim ko baka fasa aurena ba ni bazan aureka ba wallahi ko kaine autan maza, kaje can kasamu dai-dai dakai dan duk wanda ya wulakanta mani yayana bazan iya aurensa ba, Allah ya kiyaye umma ta gaida aisha."
"Sai me? Kyanki na banza da wofi babu ni babu ke kuma billahillazi ko hanya naganku kun kulani sai na tozartaku." Ita dai tante kasa magana ma tayi tana gefen barandar a zaune, har ya fice daga gidan kowannensu na cikin damuwa, Mutallab kuwa tashi yayi ya ɗau key ɗin motarsa ya fita daga gidan, ko da yafara driving kasawa yai ya samu gefe yayi parking, abunda bai taɓa tunani daga wajen Aryan ba wai sai gashi yau shi yayi masa shi, menene baya yimasa daya cancanci irin wannan wulaƙancin haka? Kwanaki ma daga shi sai Allahn shi yabashi million 5 data kirasa yace babansa ya samu karayar arziki yace ya bashi yaja jari, gaba zai dawo Nigeria ma ya aro million biyu a hannunsa kuma har yau har gobe bai dawo masa dasu ba yanzu kuma dan ya tambayeshi mai zaiyi da kuɗin daya sake tambayarsa sai abu yazama tashin hankali da damuwa? Meke damun Aryan ne shi sam bai sanshi da irin wannan halin ba, a zatonsa duk yadda yakai ƙololuwa wajen ɓata masa rai bai cancanci irin wannan zagin daga wajensa ba, bai cancanci tozarci da gori kala-kala agunsa ba saboda shi abokinsa ne, amininsa daya ɗauka tamkar ɗan uwansa na jini, "ya Allah!" Ya faɗa cikin wani karyewar zuciya hawaye na sauko masa.
Yaɓata kusan rabin awa kafin ya tada motar ya nufi titi, tsintar kansa yai da zuwa gidan su Meenal, bayan yakirata a waya yace tafito gashi bakin gate ya kwantar da kansa a saman kujerar da yake zaune haɗe da rufe idanuwansa tamkar mai bacci, a haka Meenal taƙaraso ta sameshi tana zuba wani uban ƙamshi da take cikin turarukkan Mommy ta shafo, buɗe gaban motar tayi ta shiga bakinta ɗauke da sallama, a hankali ya ɗago kansa tare da buɗe idanuwansa ya zuba mata, atake yaji kaso arba'in bisa ɗari na cikin damuwarsa ya tafi, yadda Meenal taga idanuwansa sun kaɗa yasa atake annurin fuskarta ɗaukewa, cike da damuwar da nan take ta bayyana a fuskarta tamkar zatayi kuka tace, "yayana me yasa meka haka? Waya taɓa mani kai?" Taƙare zancen hawaye na saukowa akan fuskarta, Murmushin da iyakacinsa akan fuskarsa ya sakar mata haɗe da cewa, "meye haka Meenal? Kuka fa kikeyi?"
"Yayana wallahi bana son ganinka cikin damuwa ko ɓacin rai, ko meye kayi haƙuri pls kaji ko?"
"To shikenan na haƙura, yanzu biyani kwalliyata da kika ɓatamun da wuɗannan hawayen naki". Ya miƙa hannu kamar zai lakuto hawayen cike da jin kunya tayi saurin rufe fuskarta, dariya yai yana danne abinda yake ji ƙasan zuciyarsa na ɓaci ran da Aryan ya saka mashi tare da cewa, "ya kike yasu Mommy da Dady?"
"Duk lafiya kalau, ina wuni". Cikin sigar zolaya yace, "gashi nan tare damu..."
Haka sukaci gaba da firarsu cike da so da ƙauna duk don ya kawar da ɓaci ran dake zuciyarsa kafin sukayi sallama yakoma gida.
A palour ya tadda Afrah tana kuka har lokacin Jalil na rarrashinta, kallonta Mutallab yai tare da cewa, "Kiyi haƙuri Afrah in Sha Allah komai zai daidaita kinji ko? Ɗan ɓaci rai ne kawai kuma zai wuce i know him"
"Nifa bazan aureshi ba wallahi yaya ko kun daidaita na tsaneshi wlh dan duk lokacin da ransa yaɓaci zai iyayin fiye da abinda yayi yau, bazan iya ba yaya na tsaneshi" tashiga faɗa tana kuka... Mutallab bai sake cewa komai ba sai ma samun guri yayi ya zauna yana sauke ajiyar zuciya haɗe dayin murmushi, murmushin da yayi ne yasata dagowa ta kalleshi daga ita har Jalil suna mamakin wai shi wace kalar zuciyace dashi haka? Yanzu duk abunda Aryan yafaɗa bai yi tasirin da zai nuna damuwarsa akai ba! A hankali ya ajiye wayar hannunsa yace, "Afrah kukan nan ya'isa haka, banson kuna sakawa kanku damuwa tsakanina ne da aminina, shaidan ne yashiga tsakanin mu na ɗan lokaci kuma inshaa Allahu hakan bazaiyi tasiri ba." Tante sajida ce tace, "Nima dai kam mamaki abun yaban amma duba da Aminintar da babu faɗa mun camfata da zaman munafurci dana ce wannan lamari baiyi daɗi ba Allah dai ya kau da fitina kawai." Jalil ne yace, "yaya bari naje akwai sakon da nake son karɓa na ƴan chinan nan tun ɗazu ake kirana, shi kuma Aryan in Sha Allah nasan sai yai regretting wannan abun da yai." "Ok Allah yakiyaye sai ka dawo." " Afrah kibar kuƙan nan idan baso kikeyi mu ɓata ba." Kallonsa kawai tayi ta daga kai shikuma yashiga ciki dan ya huta."
A kwanakin hakan Afrah ta zama so quite, komai takeyi karfin haline irin nata bakaramin kaunar Aryan take ba tun batasan soyayya ba ya dasa mata sonsa acikin ranta, amma rana ɗaya ya iya tsaya yace bazai aureta ba, innalilahi wainna illahirrajiun ta ambata tana jin radadi cikin ranta bata tunanin zata iya rayuwa batare da Aryan ba Amma a wannan gaɓar ko mutuwa zatayi ta zabi ta hakura dashi har abada. "Kiyita Addu'a kinji Afrah Allah yazaba miki abunda yafi Alkhairi Nasan da ciwo masoyin farko ya gujeka Amma Allah kadai yasan Alkhairin haka." Tánte Sajida tafaɗa ganin yanda ta zuba tagumi tayi shiru "Tohm tante bari nashiga ciki na kwanta". Ta bata amsa dan yau bata je school ba saboda basuda lectures.
Ganin takasa miƙewa daga palon daɗi takeyi zata tashi yasa kawai sai ta zame jiƙinta ta kwanta akan kujerar.
Mutallab kuwa yana shiga daƙin nasa gefen gadon yasamu ya zauna, sai A yanzu ma yafara fahimtar wanene shi Abubuwa da dama sun gefta sun huce wasu ya manta wasu kuma yana sane dasu, yanzu ne lokacin da zai canza yanayin zamantakewar sa da mutane, yanzu ne time din da zai iya mu'amalarsa ga kowa daidai yadda ya mu'amalancesa duba da jiya ba yau ba akwai buƙatar ya farka saboda ba komai bane yanzu ake zubawa idanuwa, wasu mutanen kan shigo rayuwarmu saboda su koya mana darasi wasu kuma sukan shigo rayuwarmu dan su koyi darasi daga wajenmu, da wannan tunanin shima ya kwanta har bacci yai gaba dashi.
**************
A ɓangaren Aryan kuwa sai bayan yakoma gida yafara tunanin rashin kyautawar abinda yayi, da daddare bayan sallar magrib suna zaune da Ummie suna fira tace, "Wacce maganar banza nakeji Aryan? Jalil yakirani dazu daman ina jiranka ne kazo? Me kakeson zama? Yanzu Mutallab yacancanci wannan tozarcin daka je har gida kayi masa? Nace ya cancanta? Naga mahaifinkan ka ma gurin aiki sun sallameshi Shine ya tallafeshi da jari, yanzu akan kudin da ba hanaka yayi ba tambaya kawai yayi sai ka zageshi kafito? Yanada arzukin da ko kulleka zaiyi kuma babu yadda muka iya? Haba Aryan haka kazama? Aboki tun na yarinta? Shiru yayi shima yana goge hawayen fuskarsa daga bisani kuma yace " Kiyi hakuri wallahi Ummi bansan me ya hau kaina ba,Ni kaina bansaniba Nayi kuskure kuma zanje nabashi hakuri NaYi masa text babu reply tun safen." " Ni bansanka haka ba wannan ba halin kwarai baniba karna kuma ji Zan kirashi Nima nabashi hakuri ka tabbatar kasameshi, tunawar da yayi motar tashi ma yacillah masa mukullin daman shi yabashi, da data mahaifinsa yake amfani tunda karayar arzukin nan ta samu mahaifinsa sai yazama da albashinsa ake wasu dawainiyar, a hankali ya furta yaaAllah yana jinginar jikinsa ajikin garun filin gidan nasu wannan ne karo na uku da ya tura masa text din ban haƙuri sai yanzu yaga reply " Aryan wannan bada haƙurin Na menene? Nifa banyi fushi dakai ba nasan sharrin shaidan ne ai ko harshe da hakoro ana samun saɓani ballantana kuma aboki da aboki Ban rikeka da komai ba komai ya huce yanzu ma nashiga kasuwa zan kiraka idan na'isa." Murmushi yayi yana share kwallar daya zubo masa a kumatu, Nan ma yashiga dialing wayar afrah itama bata daga ba hakan yabashi kwarin gwiwar anjima zaije yabata haƙuri yasanta da hakuri wuyarta yayi mata wasu zafaffun kalaman yanzu zata sakko."
(Anya zata saɓu Aryan? Jinin Abba ne fa ke yawo ajikin Afrah!🏃)
Mutallab Asad
#Tagwaye Biyar
#Billy s fari
#Nana Diso
MUTALLAB ASAD MUTALLAB
(labari mai taɓa zuciya)
Na
Billy s fari
Nana diso
RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU.
TAFIYAR BIYU TAFI DAYA
SHAFI NA SITTIN DA BIYU.
Kasancewar a gajiye ya shigo kai tsaye ya haye sama ɗakinsa ya fara rage kayansa ya shiga toilet yayi wanka sannan yafito ɗauke da towe, yana tsane jikinsa a gaban madubi da ƙaramin towel ɗin dake hannunsa wayarsa ta dau ƙara, hannu ya miƙa saman gado ya ɗauko tare da ɗaya kiran ya kara a kunne. "Hello Askim". Yaji Muryar Meenal tafaɗa cikin muryar shagwaɓa, murmushi ya saki tare da cewa, "Soulmate bakiyi bacci ba?" . "Eh kiranka nake jira tukuna sai na kwanta kuma sai gashi baka kira ba?"
"Am sorry yau nashiga busy ne sosai shiyasa, ina fatar kin wuni lafiya?" "Lafiya kalau amma zuciyata a wahale tawuni". Gefen gadon ya zauna yana shafo kansa kafin yace, "Ni kuwa meya wahalar munda zuciyar Soulmate ɗina haka?" "Tunaninka Askim, baya barinta hutawa dai-dai dana second ɗaya". "Kusan haka yake a zuciyar Mutallab, duk bayan bugawar kowace daƙiƙa sai tayi tunaninki". Murmushi Meenal ta saki ta janyo pillow ta rungume jikinta tana lumshe idanuwa haɗe da cewa, "ina matuƙar sonka yayana, bansan yadda rayuwata zata kasance ba idan babu kai, shiyasa a kullum addu'a batawuce Allah ya bamu tsawon rai ba".
"Karki damu, In sha Allahu zamu rayu tare har ki haifamun ƴaƴa kin jiki". "Ina fatar haka Askim, me kake yanzu?" "Ehmmm to gani zaune nafito wanka ba ma ƙarasa shiryawa ba sai naga kiranki ya shigo, menene ehm?". "Ba komai bari na barka ka ƙarasa shiryawa dare nayi, thanks for the love". Tafaɗa cikin wani sound daya jefa Mutallab cikin wani shauƙi, a kasalance ya mayar mata da "thanks too soulmate, kiyi bacci mai daɗi". Sannan ya kashe wayar tare da miƙewa ya shafa mai ajikinsa haɗe da turarukka masu ƙamshi ya saka pyjama dinsa sannan ya zura ƙafafuwansa cikin slipper ya sauko ƙasa ya samu abincinsa jere akan dining table kamar dai kullum, kasancewar akwai aikin da yake son yi kafin ya kwanta yasa ya zauna yaci abinsa daidai yadda zai iya ci kafin yamiƙe ya nufi ɗakin tánte Sajida, zaune ya sameta ta kammala sallar shafi da wuturi tana addu'a ya samu kujerar dake gefe ya zauna yana jiran ta kammala,bayan ta gama ne ta shafa addu'ar ta ɗago kai tana cewa, "Ashe kadawo alhaji Mutallab? Ai tun ɗazu ina palour zaune bini nuni ina duba agogo ganin har ƙarfe tara da rabi ta wuce baka shigo ba, ince dai lafiya ko?"
"Lafiya klw tánte Barka da dare kun wuni lafiya dai ko?" "Lafiya kalau wallahi alhamdulillah, "
"Madalla wlh ƴan shirye-shiryen hidimar nan ce suka riƙeni har wannan lokaci, kin san yau aka kai kuɗin aurena da kuma nasu Jalil da Walid, to na tsaya ne a wani ventures da nake so a haɗa duka kayan lefen namu an ne shiyasa nakai wannan lokacin tunda abun ba daukar lokaci zaiyi ba".
"Masha Allahu alhamdulillah ka kyauta gaskiya, ubangiji Allah ya ƙara buɗe maku kuma yaci gaba da haɗe kanku, Allah ya nuna mana lokaci kuma yasa ace ƙara da akayi".
"Amin Tánte, ina mutuniyarki aunta ne?"
"Ta kwanta saboda ko yau data dawo makaranta ran nan nata a jagule yake".
"Allah ya kyauta tánte, nasan auta na son Imran sosa, sai dai duk da haka bazan taɓa tilastataba akan duk wani hukunci da zata yanke masa, abunda yai ɗin bai kamata ba saboda tsakanina dashi ne, zamu iya fahimtar juna daga baya mu daidaita to meye nata aciki da zai sakata, kenan idan ya aureta nazo na ɓata masa rai ko wani abu ya haɗamu sai yace ya saketa tánte? To ni ba ruwana a harkarsu, tsakaninshi da ita ne yanzu, idan tahaƙura sun daidaita zanyi farinciki ta samu wanda zuciyarta ke so, idan kuma tace a'a tánte to nifa bazan mata dole ba, wannan shine kaɗai abinda zanyi akan wannan lamarin". Sai da tánte ta sauke ajiyar zuciya sannan tace, "Gaskiya kam inhar tahaƙura dashi kamar yadda take iƙirari kullum to baza'a ce ayi mata dole ba, ni wallahi har yau sha'anin nasa bai dena bani mamaki ba, abu sai kace mutum na jiraye dakai".
"Ba komai tánte Allah ya kyauta, inaga gobe zan kirasu kawo a can Niger ɗin na sanar dasu saboda sufara shire-shire in akwai wanda keson zuwa saboda so nake natura masu kuɗin jirgi dan abun zaifi sauƙin".
"Haka ne sannu da ƙoƙari kiji?, Allah ya ƙara buɗi ya jiƙan mahaifiyarku, gabaɗaya ɗabiunta ka ɗauko nason ƴan uwa da kuma zumunci da don kyautatawa". Murmushi kawai yai yana amsawa da Amin kafin yamiƙe yayi mata sai da safe, kusan ƙarfe biyu har da rabi Mutallab yakai yana aiki a system ɗinsa kafin ya rufe ya shiga toilet ya ɗauro arwala, nafila yai raka'a huɗu sannan ya zauna yayi addu'o'i masu tarin yawa ga mahaifiyarsa da mahaifinsa dake raye, ya kuma yiwa kansa da kasuwancinsa da auren da zaiyi kafin ya roƙawa Afrah zaɓi mafi alkhairi akan alaƙarta da abokin nasa daya ɓullo masa da wani hali dako kaɗan bai taɓa saninsa dashi ba, daga ƙarshe ya roƙawa ƴan uwansa da sauran al'ummar musulmi baki ɗaya sannan ya kwanta.
**********
Faɗar yanayin dasu Aïcha suka shiga bayan kwanaki da rasuwar iyayen nasu ba'a magana, gabaɗaya rayuwa ta juya masu ta yadda basu taɓa tsammani ba dan mahaifansu nada sati biyu da rasuwa kawun nasu yace su kwashi kayansu su koma wajen dangin mahaifiyarsu saboda sun fisu ƙarfi shi baida halin da zai iya riƙesu har su biyu ya ci dasu ya shada su ya kuma tufatantar dasu, lokacin aurensu yazo kuma nauyi duk yazo yaƙare kansa. Cikin matsananciyar damuwa suka haɗa kayansu suka koma wajen wani mahaifiyarsu kamar yadda kawun nasu ya buƙata, sai dai duk da yana da tarin arziƙi dai-dai gwargwado da zai iya riƙesu kai tsaye yace shima nauyi yayi masa yawa tunda suna sane da cewa matansa hudu yaransa talatin da bakwai kuma duka ƙanana da komai sai anyi masu sunfi yawa, wajen zaman ma da zai basu acikin gidan bai dashi kuma ya tabbata matansa babu wacce zata yadda ya zauna dasu, dan haka suyi haƙuri suje can gidan babbar yayarsu gabaɗaya yasan bazata hanasu zama ba, haka su Aïcha suka kwasa suna hawaye tare da jinjina yadda lamarin zumunci ya lalace a wannan zamanin, shi ɗin da yayan mahaifiyarsu ne uwa ɗaya uba ɗaya haka ma kawu ƙanen Mahaifinsu ne amma cikinsu an kasa samun wanda zai iya riƙesu, lallai duniya nada ban mamaki, cikin karramawa yayar mahaifiyarsu dake auren wani attajiri itama ta tarbesu tana sake jajanta masu rashin mahaifan nasu kafin tasa akawo masu abinda zasu ci sunayi suna fira, sai da suka kammala kafin suka fara sanar da ita abinda ke tafe dasu tare da labarta mata abinda kawo da kuma ɗan uwanta suka ce, a take fuskarta ta sauya tamkar bada ita suka gama fira ba yanzu, cikin masifa tafara faɗa tana faɗin ɗan uwan nata ya rena mata da hankali taya shi da yake da iko akan gidansa zai kasa riƙe ƴaƴan ƴar uwarsu ya turo mata su bayan yasa itama a ƙarƙashin ikon wani take cikin gidan, nan fa ta ɗauki wayarta takirasa cike da sonnnuna masa lallai-lallai sai dai su zauna wajensa dan ita bazata ajiyesu ba acikin gidanta tazo tasamu matsala da mijinta akansu, shi kuma yace lallai shima bazai zauna dasu ba tayi duk yadda tayi ai itace babba acikinsu ya kashe wayarsa.
Haka ta dinga cika tana batsewa tare da haɗe rai agabansu kamar zata fashe, su dai imani da tsoron Allah ya sake sanyaya guiwoyinsu basu ce komai ba har tagama ta ɗago kai tana kallonsu haɗe da cewa, "Ni bansan ya zanyi maku ba saboda maganar gaskiya duk da kuma ɗiyana bazan yadda na zauna daku ba ɗika-ɗikan budare acikin gidan nan azo a samu matsala da maigidana tunda halin mazan yanzu sai su, balle ke.." ta nuna babbar yaya sannan taci gaba da cewa, "da akace yawon banza kikeyi agari, kece yau a ganki tare da wancan gobe aganki da wannan, to ni bazan iya wannan zaman ba dake acikin gidan nan nadawo ina nadama da dana sani, Raihanaah" ta ƙwalawa ƴarta kira sai gata tafito kana yimata kallo ɗaya zaka san yarinyar na hutawa, kallon su Aïcha tayi tace, "Mamah sababbin masu aiki kika ɗauki ne?"
"Ke sallah bana son shashanci je ki ɗauko mani jakata na nan akan gefen madubi". Ba'a jima ba sai ga yarinyar tadawo dauke da jakar tamiƙa mata, kuɗi taciro aciki masu yawa tamiƙa masu tana cewa, "Ga wannan ku tashi kune can wajen kawon naku ai sune dole su riƙe ku su da suke dangin mahaifinku, kwayi amfani dasu bayan wani lokaci idan kunada wata buƙatar zaku iya zuwa na taimaka maku amma gaskiya bazan zauna daku ba, kuma fa mark kuji nace haka kuriƙa yimani go and come bana so kunji na faɗa maku". Aïcha da ranta yagama ɓaci tun ɗazu tana ta don tashi amma Babbar yaya ta hanata sai ƙwalla takeyi ta ɗari kai tace, "Amma umma karku manta kuma fa kuna da haƙƙin riƙemu saboda haka Annabi s.a.w yace, ƙanwar uwa ko yar uwa kamar uwa suke, ma'ana suna zama a gurbin uwa".
"Yau naji fitsara! Aïcha nace maku ba haka bane da zaki titsiyeni da hadisi? Kunga idan bakwa buƙatar kuɗin ku tashi ku tafi dan ni nariga dana gama magana". Ganin tana ƙoƙarin maida kuɗaɗen cikin jakarta yasa babbar yaya saurin miƙa hannu tana cewa, "A'a tánte muna so". Jeho mata kuɗin tayi tana watsawa Aïcha harara babbar yaya tasa hannu ta kwashe sannan ta ɗaya Aïcha da a wannan karon kukanta yai ƙarfi tana cewa, "mungode tánte zamu tafi".
"To a sauka lafiya". Tafaɗa tana ɗora ƙafarta ɗaya akan ɗaya tare da ɗaukar remote ɗin tv ta maida hankalinta akai tana sauya channel. Suna ji suna gani itama suka baro gidanta, suna fitowa itama babbar yaya tafashe da kuka saboda takasa riƙe kukan nata da tun ɗazu ke don taso mata amma tayi jarumtar hana fitowarsa har saida suka fito, kukansu suka sha har suka gode Allah kafin Aïcha ta kalleta tace, "babbar yaya dan Allah mu dakata zuwa gidan kowa yanzu, kada kice sai munje gidan tánte Maryama da tánte zuwaira, na tabbata haka zasuci gaba da tozarta mu, kina da gani ko lokacin da mahaifiyarmu na raye ita da take ƴar uwarsu basu ɗauke ta da daraja ba saboda batada kuɗi tana auren talaka balle kuma mu data haifa". Babbar yaya dake share hawayenta ta kalleta haɗe da cewa, "Aïcha bani nake ji ba domin akwai inda zan iya tafiyata tunda dama rayuwata ta gama lalacewa tun baya, ke nake ji aiicha bana son wani abu yazo ya sameki da zai lalata maki taki rayuwar, shiyasa nake so nasamu muje ko ke kaɗai ce cikin tánte maryamah da tánte zuwairah wata ta ɗaukeki, ni kuma akwai gidan magajiyar dana sani zan tafi can na zauna naci gaba da rayuwar dana taso aciki". "Astagfirullah babbar yaya, karki manta kin tubarwa Allah akan bazaki sake komawa wancan rayuwar ba da zunubinki na baya, kada kibari wannan halin da muke ciki yasa kisake komawa rayuwar da kika baro baki sani ba ko rayuwarmu na gaba da ƙarewa kamar ta iyayenmu ki mutu cikin saɓon Allah, mu tafi duk inda kike so babbar yaya ina tare dake, amma bazan bari ki komawa rayuwarki ta baya ba".
"A'a Aïcha". "Dan Allah yaya kada kice wani abu muje can gidansu tánte Maryamah ɗin idan kina ganin za'a dace".
Haka suka sake kwasa suka nufi gidajen ƙanwar mahaifiyar tasu da ako yaushe take masu iƙirarin suna auren masu kuɗi amma babu wacce ta yadda su zauna wajenta, wanda suna da tabbacin da yaƙin cewa da mahaifiyarsu ce duk takaicin da suke ciki haka tafaru da ɗaya daga cikin ƴan uwan nata baza taƙi ɗaukar yaransu tariƙe ba, tabbas duk lalacewar iyaye su jigone kuma garkuwa ne ga ƴaƴansu matuƙar suna raye, cike da gajiya da yawon da sukayi Aïcha takalli babbar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 35 Chapter of 54