Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dama batayi auren ba ta zauna gidan iyayenta gabaɗaya. Shi kuwa yana fita kai tsaye shago ya nufa ya shiga office ɗin dake ciki wanda anan ya samu ruwan tea ya karya don dama akwai komai acikin daya danganci kalar kayan tea ɗin da yake amfani dasu, haka kuma akwai electric cup da nan take zai jona ya haɗa ruwan zafi, sai daya gama haɗa tea ɗin yasha sannan ya fito yana duba kayayyakin da aka sauke masu na kayan ɗinki da suka fara kawowa. Ita kuwa tafi mintuna arba'in awajen har bacci ya soma ɗaukarta sannan ta miƙe tana ƙunƙuni taci gaba da gyara gadon, wasu mintunan goma ta sake ɗauka tana sake gyara masa gadon kamar yadda ya buƙata amma ta kasa, Rai a ɓace ta ɗauki filullukan dake kai ta aza tabar gadn a haka don kada taci gaba da ɓata lokacinta agun har ya dawo ya tadda ita batayi komai ba. Toilet ta shiga taga ba wata datti da yayi amma zai wani sata gyaran sa, ruwa kawai ta ɗiba ta kwara acikin kwalbar sannan ta watse sauran a ƙasan barthtube da kuma ƙasan toilet ɗin ta fito tayi tafiyarta ba tare data damu da ta share cikin ɗakin ba balle kuma mopping uwa uba kuma ta tsince kayan dake ciki. Bata bi ta kan ɗakin ta ba ta sauka ƙasa tana ƙwalawa mai aikinta kira, "Zubaida..Zubaida wai kina ina ne nake ƙwala maki kira kika ƙyaleni?" "Gani Aunty". Matar zata kai shekara ashirin da takwas ta faɗa tare da duƙawa a gabanta duk data girmeta, don duka duka shekarunta ita baza su wuce ashirin da uku ba zuwa ashirin da huɗu ba har yanzu, cikin nuna isa tace "Ki haura sama ki gyara mun ɗakina sannan ki gyara ko ina acikin gidan duk da naga baida wani datti kawai matsin lambarsa ne." Har ta miƙe zata tafi Meenal tace, "Zo nan, saura idan ya dawo ya tambayeki kice ke kikayi, na rantse da sai kin bar gidan nan ba sallama, tashi maza ki tafi". Ta ƙare zancen tana dawo cikin falon tare da neman ɗaya daga cikin kujerun dake ciki ta zauna tana kallon tv. Sallamar ƙawarta Zee dake shigowa falon ya sata miƙewa ta cike da farinciki tana faɗin. "Oyoyo ƙawata, yau kece agidan namu?" Dan dama shekaranjiya dasu Sarsy zasu zo sun faɗa mata cewa tace tana nan zuwa Ummanta ce bata da lafiya shiyasa basu zo tare ba. Zee tayi murmushi tare da cewa, "Ai ke ɗince ba mutunci Meenal, idan na biyewa halinki Allah zumuncinmu lalacewa zai yi". "Haba Zee dena faɗar hakan, kwata-kwata auren nawa wata nawa ne da zan fara yawon fita, wata ɗaya kacal fa da kwana ɗaya, Ya Mutallab ma bazai barni ba shiyasa ban ma taɓa gwada tambayarsa ba koda muka fita dan iya karmu gidansu muka dawo." "To ai shikenan matar aure, Asha zama lafiya ai ni gani nazo ganinki". "Hmmm bari kawai, wane lafiya Zainab tun ina da kwana ɗaya labari ya canza tsakanina da Ya Mutallab sai kace ba auren soyayya muka yi dashi ba. Wlh Zainab da nasan haka auren yake Allah bazan yi ba". Ta ƙare zancen tana matso ƙwalla, Da mamaki Zainab ke kallonta ganin irin ɗaular da Meenal take ciki amma take faɗar haka, tun daga waje ma tsarin gidan nata abun kallo ne balle kuma an shigo ciki, wani kallo tayi mata mai cike da tambaya tana cewa, "Subhanallahi, me kike nufi Meenal? Bangane wannan maganar taki ba, yanzu duk wannan ni'imar da Allah yayi maki kice wai da baki yima auren ba, wannan wace irin magana ce haka Meenal?" "Baza ki gane ba Zainab, wlh ya Mutallab ya sauya mani, fisabilillahi ace duk girman gidan nan wai ni yake so na rika gyarawa baya son mai aiki tayi, gyaran ɗakinsa da girki wai duk nice zan yi sai kace jaka Zainab? Wlh bazan iya ba kema kin sani". Cire hannunta Zainab tayi akan kafaɗar tata tana ɗan  jan tsaki tare da sauke ajiyar zuciya kafin tace, "A gaskiya kin ban haushi Meenal, ai na zata wani abun ne daban wlh, to yanzu meye abun ɓacin rai anan? Gidanki ne fa ke kika fi cancanta ki gyara abinki ba wani ba, ko kin ɗauka nan ɗin gidanku ne da komai sai anyi maki? To da sake wlh ƙara ki gyara tun wuri don nan gidan mijinki ne babu wanda zai yimaki wannan aikin tunda yace baya son mai aiki tayi." "Cab..wlh sai dai ya haƙura, ita keyi kuma ita zata ci gaba da yi, har ina wannan uban aikin sai kace baiwa, Allah bazan iya ba Zainab har da zancen ƙara aure yake yimani saboda tsabar rashin mutunci, auren namu duka duka wata ɗaya fa cikin na biyu amma tsabar rainin bawan Allah nan yace zai ƙara aure." #Mutallab Asad #Yan Tagwaye #Nana Diso #Billy s Fari SHAFI NA SABA'IN DA BIYAR *MUTALLAB ASAD*      Arewabook:- billysfari       Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.    baƙi tasaki Tana ƙallonta data gama maganar tata sai tace "meenal wai ke wacce irin diyace? Ƙingama da wulakanta mumy yanzu kuma ƙan mijinki kika dawo? Mata nawa ke neman mijin aure yanzu? Wanda sukafiki komai daga kyau har nasaba da kudi Amma basu samu ba? Kekuma kinsamu wannan daular kina maganganu marasa ƙan gado ke bakya gyara babu lafazi mai daɗi ko wanda mai ƙai Mutallab komai ba baizama dake ke kadai wallahi tayaya zaiyi maganar aure ba saboda Allah? Ita macce ai ƴar ado da kwalliyace ba'a santa da kazanta da rashin gayu ba, matan yanzu dake bin mazan suyi soyayya dasu Amma ke ƙintsaya kina shirme da shirirta Nidai gaskiya zangayamiki wallahi kikarasa Mutallab ba baki nayimiki bakyasamun wanda yafishi, kina dai jin labaran aurukan yanzu daga duka sai rashin ciyarwa sai cin Amana dadai sauransu." " Kinga Zainab bance kiyimun wa'azi ba, kee kiyimana order din abinci yau fried rice da pepper za'a siyo kuje da driver ki dauki atm aƙan mudubina." Jikin mai aikin nata narawa tace " Tohm hajiya." Har tayi gaba meenal takara cewa " kingyara masa daƙinsa ko?" " Eh na gyara hajiya har bandaƙinsa na wanke masa..." " Good kamar yadda nake gayamiki kullum idan yatambayeki wanene yagyara kice masa ni idan kika kuskura baƙinki yayi suɓutar baki kikace kece to tabbas zan baki ticket na sallama." " Hajiya bazan fada ba." " Better." Zainab kam mamaki ne yakasheta dan haka ta hanzarta faɗin sai anjima duk yadda meenal taso ta zauna tace Sam Sam itafa bata zama dam ko ta zauna faɗa zasuyi Da harara dai meenal tabita saboda haushi suna ciƙin haka sai ga ƙanwar mamah tazo duk da basa shiri da meenal Amma tayi Alkawarin zuwa ta dubata. Da murna sosai meenal ta Tarbeta kallonta tayi daga sama har kasa kayan jikinta ko mai aikinta Nata yafi kyau duk dai inda ta duba acikin gida sai a hankali ita matar gidan babu tsafta atattare da'ita idan har hancinta yajimata kamshi ma ko body odour bata saka ba. Cikin murna tace " Dukan ku kuka ki zuwa sai yanzu." Ni kinga daga school nake bani abinci yunwa nakeji." " Antafi siyowa bata dawo ba mai aikin?" Bangane menene kike Nufi ba abinci nace miki ba kayan abinci ba." " To ai dagani har mai aikin bamu iya girki ba oder mukeyi a restaurant." " ke kuwa kinsan me kikeyi?" Kallonta meenal tayi tace " Nasani mana tafaɗa taba cuno baki. To bari nayi sallah tafaɗa tana shiga dakinta da ya tsaru da pop Amma kuma zanen gadon ko ina a lallace kallon meenala din tayi tace " Tunda ke baki iyaba itama mai aikin naki kuma fa?" " Yanzu fa tagama gyara nasa idan tadawo zata gyara nawa," batare da tace mata komai ba kawai tadaga ƙanta tana mai shigewa tayi Alwala tana fitowa tayi Sallah Daga suka koma palour ta zuba mata abincin. Sai datagama ci sannan ta kalle meenal ɗin tace "Meenal kenan! Ai babban kuskurene agareki ace kina ƴa macce maccen ma mai miji lafiyayye ɗan gaye haɗaɗɗe da mata ke ribibi da kuma mafarkin samu ace kin kasa kula da kanki har ace kina fama da warin hammata? Bayan komai na buƙatuwar rayuwa da jindaɗinki mijinki ya tanadar makishi, Fisabilillahi kalli yadda kika lallata ɗakinki? bedsheet wannan kin kasa iya sarrafa shi yanda zai ƙawatar akan gadonki, ki kalli Abincin da kika kawo mani wai dashi zaki tarbi mijinki bayan a kallo ɗaya zai gane cewa Order kikayi bake kika girka da hannunki ba! Tabbas akwai gyara a lamarinki domin ko kaɗan baki cancanci amsa kalmar matar aure ba, idan kuma har kin amsheta to ke ba isasshiya bace sai dai akiraki ballagaza, duba da yadda magana kaɗai baki iya furtata yanda ya kamata awajen mijinki ba, kuma duk a haka kike yaƙin ƙwatar ƴancin soyayyarki a wajensa? to ta ina bayan kin kasa natsuwa ki gyara matsaltsalunki, sai hauka kikeyi, daman Nasan Akwai ranar da zatazo irin haka shiyasa sangarta batada Amfani ko kadan mumy din da kukaki tsaya ku bi dakinbita da ƙindace Amma ko kadan wannan bashine gabanki ba sai fitsara dubeki azo aganki kina matar aure matar babban mutum mai kudi kanki duk ya tsufa kina matsawa sai kace wani gardin kazamin ne ya matsa,to bari kiji gaskiya zan faɗa maki wallahi MUTALLAB na mugu-mugun haƙuri dake, saboda haka tun wuri ɗauki hanyar gyara kafin lokaci yaƙure maki!, kinga tafiyata Wallahi bana ganin takaicin nan." Tsaki meenal ta doka tace " Aikin banza abunda kuka iya kenan bakin ciki da hassada." Mai aikinta kuwa dake kitchen ta buɗe kulolin abincin ta barbadesu da magungunan da Umma ta bata. Nan meenal din tazube tana bacci har wajejen azahar har Mutallab yashigo su tante sun shirya tana bacci sauran kayansa ya haɗa ya ajiye mata Atm da kudi aƙan mudubin ta kamin kuma yadawo palour din yashiga yashiga tashinga. Miƙa tayi tana kallonsa wai yanzu zaka tafi ne?" " Ai na sanar miki 4 flight dinmu zai tashi ko? " mikewa tayi tace " kwana nawa zakayi?" " yadanganta zan iyayin 1month ko kasa da haka shiyasa tun farko nace miki kishirya mutafi tare ko?" Nafagayamaka babu inda zanje katafi sai kadawo." Wani kallo yayi mata na takaici kamin kuma yace " Bazaki rakani ba." " Nifa bacci Nakeji kaje kawai malam." jin muryar su tante yasakata biyo bayansa tana faɗin " Zanje gidan umma kaji." " Banyi iziniba ko'ina kije ki zauna agidanki idan bahaka ba zan batamiki." Meenal mu zamu tafi Allah yakaddara saduwa." " To". Shine abunda meenal tace tana kallon matar jalil dake cikin wata super red anmata ɗinkin stonework tayi masifar kyau sai tafawa sukeyi da afrah." " Afrah nidai asiyomun cukwui." " Yaya jalil kaji antyna ko itafa nace tashirya muje shine zata bani saqo." " Haba Anty afrah" itama tafada da alaman roko. Ganin Mutallab yafito yasakata tsgunnawa ta gaishesa hakan yasa yazuba mata ido daya zuciyar tashi kuma takaici yakamashi kalli matar jalil fes gwanin sha'awa amma tashi matar da wani yadi ajikinta fuska duk kwantsa." Matar jalil datagano meenal sai tace " barka da rana ina wuni." Meenal da baƙin ciki yacikata tace " Lafiya." Duk basu kukata ba suka shige mota yau ne karo na farko da yaji kamar ya muzanta sai datakara bude baki tace " Askim sai kadawo." Matar jalil kuma tace " Nidai matsamin Afrah sai na kaiku har Airport." Samun ƙansa yayi da rintse idanuwansa yana haɗeyi wani abu mai zafi yaa Allah ya ambata A alokacin da sukaja motar tayi komawarta gida. ****** NIGER ke danAllah ƙindameni da sintirin wasu banzan kayanki kwashe bakkon ki kije ki ajiye acan dakin dakike kwanciya Dan babu wacce zatayimun aciki ballantana nace kibani kinsan kuma yarana duk maza ne kitashi kiyi maza kije kiyi wanka kizo zan aikike can birni Niamey. " To mah." Tana tashi daƙin datake kwana tashiga ajiyar zuciya tayi da Allah ya kwato mata kayan nan in bahaka ba tasan kashinta ya bushe tsaf yaran mama zasu kwashe su siyar tunda Akwai mai ɗan hali aciƙinsu, itafa tunda aka sace jarin mama sai takejin dadi sosai acikin ranta duba da tasan kamin mama takara hada wani jarin itama zata huta kayan jiƙinta tacire ta zumbula tsohon hijjabinta cikin kayan takara dubawa nan taga macline har da sabon brush hakan bakaramin daɗi yayi mata ba, ita breziyar nan ce ma takejin wani sanyi into kalleta Kai Allah yabiya ya Isa tafaɗa tana mikewa ta Nufi bandaki domin yin wanka tadan jima aciƙi kamin tafito shima muryar Mama ce taji tana faɗin " Uban me takeyi har yanzu da bazata fito ba." A gaggauce tashafa wani karamin lotion da yasako mata tashafa alimun din datagani aciki a hammatarta sai kuma tashafa hoda da janbaki, mayafi kasancewa medium ne yasata sakawa dan bata shiri da guntayen mayafan nan, lace tasak kalar ruwan kasa anyi mata doguwar riga irin dinkinnan na A shape wanda daga sama yadan fidda shape daga kasa kuma ya buɗe tayi masifar kyau wani sai yayi tunanin diyar wasu masu arzukin ce tasaka mudubi ta kalli kanta dan kunne tayi saurin sakawa, jin kiran mama yasata hanzarin ficewa tana faɗin ganinan, mama ce tayi sakaka da baki tana kallonta kamin tace " Ke kuwa diyar nan kinganki ai da shigowa kikayi bazan ganeki ba, wannan suttura ƙyanta jikina tafada tana ƙauda ƙanta saboda takaici " Kin tsareni da idanuwa sai kace mayya ga Naira hamsin nan kya karasa da ƙafarki." Da mugun mamaki ta kalli mama tafiyar da ko dubu daya ba lallai tayi mata ba shine wai Naira hamsin? To mama wazai ɗaukeni a hamsin?." " Ubanki ne fitsararra kintsaya kina kallona sai kace wata Aljana wanna kwalliyar da kikayi zaki rasa mai daukarki kyauta ne kinajina ni, idan kikashiga Niamey layin minister zaki tambaya sai kice gidan dan kuluka to matarsa kawata ce tun muna primary nasanta kice mata yar ayouba ce ta aikoki taji Ance mijinta yasamu takara kuma yaci ina mata Allah yasanya Alkhairi Nima abani hasafina." Shiru meenal tayi takaici Na neman kasheta aka. Shaanin mama. Dan ubanki kallona Zaki tsyaa kinayi kina ganin yadda ɗan banzan yaronnan yasace jari da ubanku zanci da ku idan bakije dallah tashi kibani guri ƙan naɓatamiki rai sha sha sha." " Sai nadawo tafada tana fita lallai mama batada lafiyar kai. Dan tafiya tayi hanyar isa mai shayi ko dataje babu kowa sai mutum daya ma yana karyawa, Sallama tayi masa tana faɗin " yaya isa sannu da Aiki Allah ya daukakamin kai kaje inda bana tunani tafaɗa tana fara'a da yasaka kumatunta lotsawa manya kuma jirarrun haƙoranta bayyana. Dan zaro ido yayi yace " Ƙanwata Aicha Wallahi banganeki ba Tabarakallah mashaa Allah kokefa yanzu danAllah haƙan baifi ba kallarki fa." murmushin dake mata kyau tayi tace " ai wallahi sakayyarka sai A aljanna." " Yanzu wannan kwalliyar sai ina?" Cike da Nuna girmamawa tace " Birnin Niamey." Zaro ido yayi yace " da yamman nan kine kiyi menene Aicha?" " Wallahi Mama ta aikeni." " To badamuwa kai wada zoka ajiyemun kanwata." " Okay oga A birnin ina zakije?" " Wai unguwar minister." " To muje yafaɗa yana karasa kurbar shayin." Miko mata dubu daya yayi yace ki rike wannan sai ki dawo da'ita." " A'a yaya isa akwai canjin nan nawa fa bantaɓa ba kabar kudinka danAllah." " Idan baki karba ba sai Nayi tunanin ko ƙin rainane." Karba tayi tana masa godiya sannan ta haye mashin suka dauki hanya ba sune suka isa ba sai wajajan la'asar tana sauka tabashi yace A'a tabarshi tayi masa godiya tashiga babban layin attajirai kana shigowa wani sabon gini ke maka welcome duk da babu ginin banza agurin. Rasa wanda zata tambaya tayi sai daga can ta tuna ai layin kannen mahaifiyarta ne kuma kamar wata kakarsu mah pere anan take kamar dad tatuna sanda suka taɓa zuwa sau daya duk da lokacin batada wani way sosai. Sai data fara tambaya dakyar tasamu wanda yasanan sunan dan kowa sai yagyara mata ashe ba wada bani ba shima dataje sai da mai gadin ya wulaka tata dakyar dai yabarta tashiga wata tagani gefe guda tace " danAllah gurin hajiya Nazo kallonta matar tayi tace ta tsaya nan kusan mintuna sama da ashirin gashi ko Sallahh ba, ki kishigo suna shiga tace " Ina kwana hajiya." Batare da ta amsa ba tace mike tafe dake? Nan takwashe saƙon umma ta gayamata sannan yaja tsaki tana faɗin shikenan mutane daga kasamu ƴar daukaka sai suce sun sanka To ni dai bansan wata wacce kike magana ba karbi dubu biyar sadaka taciro ta bata, Aicha tyi godiya ta fito haka nan kofar gidan tana sake saƙen yunwa datakeji ga gidan da tasabi Amma takasa shiga haƙan yasa taga gwara tashiga gidan dada idan Allah yasa tana nan to basai ma idan zata ganeta ba, tana shifa mai gadin yabara izini tana faɗar dada. SHAFI NA SABA'IN DA SHIDA *MUTALLAB ASAD*      Arewabook:- billysfari       Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne. Ƴar budurwa kamar naji ƙin ambaci dada ko? " Eh baba gurinta nazo." " Allah sarki to sannu da zuwa Nanɗin ne gidanta kuwa, kimike hanyar can zata ƙaiki babban palour." Aicha ce tayi masa godiya sannan tamiƙe tashige ciki da ɗan far gaba take tafiya har ta isa baƙin palour din nan tashiga sallama, wata karamar macce ce ta amsa mata tana faɗin " Shigo mana." Takalmanta tacire tana kara sallama tashiga dada dake zaune ƙan kujera tace " Muhammadur rasulilahi saw wacece wannan Ƙamar Aicha?" Da ɗan murmushi a fuskarta tace " nice dada Ina wuni." " Daga ina da tsakar yamman nan haka Aicha? Rannan nakeyiwa yaron nan maganarki yacemin ai kawunki ya ƙarbeki nace gani kusa banda abani ke Nida banda kowacce budurwa gabana." Murmushi tayi tace " Mama ce ta aiko ne gidan wata kawarta to shine nace kamar gidan dada nan bari Nashigo mu gaisa." " Kai amma kin kyauta, Kinzama mashaa Allah jiki gwanin sha'awa sai dai kuma shigar taki sai a hankali ita uwar rikon naki tundaga can cikin kauyen ta aiko ki? Saboda Allah da yamman nan to kiyi uban me agidan kawar tata?" Murmushi tayi tace " Wai mijinta ne yazama dan siyasa shine.. nan tabata labarin komai." " Safiyyou kijini da lalatar matar nan, to tayaya bazatace bata ganeki ba danAllah shine ta baki dubu biyar? Ya maganar makaranta kin kusa gamawa dai ko?." Cikin sanyin jiki tace " A'a dada bana zuwa makaranta." " Bangane sandamemiyar budurwa dake ba bakya zuwa makaranta ina kike zuwa to?" Idonta ne ya cicciko da hawaye tace " Ina yiwa Mama kosai da safiya da rana kuma tallan abinci." " Banganeba tallah? Bayan manyan garadan yaranta shine take sakaki? Sukuma sauran yaran gidan mai suke siyarwa?" " Babu mai siyar da komai." " kai wannan rayuwar tazama abun tsoro tunda bazasu iyaba ni sai na karbeki ai amma maganar ki koma ma bata taso ba rayuwar macce ai tana bukatar kulawa." Ke safiyyou jiki ki ƙarbo mata abinci a hada mata da lemo da ruwa kikawo wannan hanya da tasha." Amsata tayi ta fita. " Kinganni nan nasha ana gyara hatsi jikina ne zaizo." Murmushi Aicha tayi. " Dan gidan diyata macce ne ba lallai ki santa ba ita can kasar tayi aure, Bakiga ba Allah ya rufa masa asiri sosai fa kinji Ana MAM GENERAL ENTERPRISES To ai shine jikana zakiji gidan TV da radio suna hirar shagunansa ai shine jikana." Murmushi Aicha tayi tace " Allah sarki." " Bakiga yadda Allah yarufamasa asiri ba uhmm wai yaron can har haushi yakeji dan nace bazan saka baki ba wai ya auri diyarsa yaran fa basuda ɗaa koni basa zuwa su gaisheni kina ganinsa haka shima Sai Allah ya shirya yanzu kuwa kafata kafarki zanje in tawo dake ina zaki zauna babu ilimi." Ciccikowa idanuwanta yayi tana kallon dada tanajin kamar Allah ya amshi adduar datakeyi barana babu dare akan yakawo mata mafita. Yanzu ki zauna kici abincin ƙinji Nikuma zanje inyi sallah sai kishigo ciki ki kwanta." Kasa cewa komai tayi saboda mamaki da yakusa ƙarta, kannin mahaifinta wasu dana mahaifiyarta sunce basu iya riketa to Ina kuma ga wacce suka haɗa kakannni da iyayenta mata yaaAllah mai amsa addu'ar bayi kakara dubana. Duk yadda suke tunanin irin arzuki Na mutallab abun yafi ƙarfin tunaninsu don kuwa ba abune da zasu fahimci komai aciƙinsa ba idan sun ƙallah daidai private jet ne? Har suka hau suka sauka babu wanda yasamu yimasa magana dan da Alama ma aiki yaketayi. Sau ƙarsu ƙarfe 8 daidai Na dare yadda sukaga motoci da masu tsaro yasa tante faɗar " Lafiya kuwa Alhaji mutallab." Kallon tante yayi Na sakanni kamin yace " Tarbace daga gomnatin kasar kumuje." " Ni wallahi yaya kaina duk ya kulle Afrah ta faɗa tana zazzaro idanuwa." Murmushi yayi ya riko hannunsu suka sauka yana sauka aka karbi jakar hannunsu data hannunsa aka saka a babbar baƙar jep ganin umar gefe yasashi saƙin murmushi yana faɗin " oga barka da zuwa." " Irin wannan suprise umar?" " Dole mu kawo gaisuwa yafaɗa yana bin Afrah da kallo har suka shiga mota." " Kace an gama komai." " Gidanka ai haduwarsa ba'a magana yafaɗa yana murmushi." Nan suka karasa suka huce zuwa babban garin Nasu tsakiyar yamin inda zai buɗe shagunansa daman karfe 9 daidai suka saka hakan yayi daidai da karasawarsu gurin Nan aka bude taro da Addu'a sannan Aka bude shago, daga nan sukayi sauran reshan nasa inda na karshen shugaban kasa da kansa ya bude, arzuki ba abun wasa ba wata daukakar sai Allah Yadda Allah ya daukaka mutallab baki bazai taba bayani ba, security din da aka bashi sukayo har unguwar da zai zauna. Shigarsu wani tambatsetsen gida yasa Mohamud dan jiyowa yana faɗin " MAM Wannan fa?" " Shine ginin da nace maka nayi." Atake yaji wani abu ya sokeshi banda haushin da yasa ji ganin yadda shugaban kasa ya tarbeshi. Cikin wata calm voice " Yace muje mana umar get down yafaɗa yana murmushi. Afrah kam suna sauka ta rungumeshi tana kuka yayana Allah yakulamana dakai yatsaremana kai." " Kishige kuje ku huta akwai ma'aikata gidan abinci ma najiranku." Muhamod kuwa sai yace " ƙaina nadan jiwo MAM bari zandawo da safe." " Okay kawai yace yashige dan Umar nan zai kwana suma su tante ɗin gajiya bata barsu sunfito ba sai sukayi wanka da sallah suka kwanta. Katafaren daƙin dake sama yashiga, wata kalar mika yayi mai Nuni da gajiyar dake tattare dashi, uhumm yace yana ambatar Allah haɗe da raba kansa da kayan jiƙinsa ya ɗaura wani towel iya kugu, Addu'ar shiga bandaƙin yayi yana saƙarwa ƙansa ruwan dumi tare da jan numfarfashi jin yadda jiƙinsa ke amsawa wanda ke Nuni da feeling kenan, ganin yadda Tsigar jikinsa ke miƙewa yasashi gaggauta wanka yafito haɗe da saka light jallabiya yana kiran wayar Meenal, kusan kira uku yayi mata bata daga ba sai ana huɗun tukunna tadaga." Wai menene kaketa kirana haka ?." " bazan kira matata ba." " Bakace aure zakayi ba idan ka isa sai akayi ai kafin kadawo ina tare da baki karka dameni tafaɗa tana kashe wayar." A hankali yanayinsa yashiga sauyawa, ransa kuma yaɓaci da kalaman nata. ***** Washegari sunayin sallar Asubahi dada tasaka Aicha gaba, yunusa driver yatafi kaisu. " Kidaina damuwa ƙinji zan tsayamiki inshaa Allahu indai da abunda yafi karfina na zan tsayamiki, in banda dangin uba sunfi karfi kanmu dangin uwa ai da ko taƙansu bazan biba wallahi yanzu idan muka karasa zamu samu kawun naki ai ko? " Eh zamu samesa dada sai 12 yake tafiya aiki. Ko da suka karasa sallama dada ta rangada nan ta tarar su mama da yara har ma da kawun nata suna zaune." Hegiyar yarinya gidan ubanwa kika tsaya." " Tsuru tsuru

Chapter 43 of 54