maza sai mu gangara gidan." Aicha dataji kirjinta yadan buga tace " Allah yabashi lafiya ." Amin tafaɗa tana barin gurin.
****
Wallahi baka isa ba nace baka isa ba Meenal take ta faɗi ayayin data rarumi mukullin motarta taja tafice daga gidan tana danna wani uban horn ga masu gadin " ko data kira mumy kuka tafashe mata dashi kamin tagayamata.
Dariya sosai Umma takeyi tana kallon Asiya tace " Ke sai yanzu babanku yake gayamun wai Mutallab zai kara aure. " da mamaki Asiya taxaro idanuwanta tace " aure kuma,." " Ai ni hakan dadi yayimun shigeyar yarinyar nan ai kinga shikenan daman bata tsinannin da komai tunda sperm din takasa samo mana to ina take da amfani. Kamar daga sama sukaga meenal tashigo tana kuka kamar ranta zaifita " menene diyata wannan kukan fa? " umma wai aure zaiyi" " Wannan wani kalar wulaknci ne aure ? Magana zai jawo mana duk duka ma yaushe yayi auren? Ai shiyasa nagayamiki kikawomin wannan abun da yanzu angama magana." Cikin kuka tace " yanzu yaya zanyi umma? Yaya zanyi inasonsa wallahi inason mutallab." " Au ke har yanzu karatun maza bai gama shigarki ba? Har yanzu zaki tsaya masa agidane kina masa gadi gashi can da masoyiyarsa wallahi maza maza kigama gabanki idan yanasonki ai zai biyoki naga maza ai haka suke? Nima haka nayi da gaske ubansa haka yake da son matan tsiya idan shi yayi Ai ba laifi baniba." Jan jakarta tayi tafita daga palour tana kuka zuciyarta cike da damuwa. Dariya asiya tasaki Tana fadin gaskiya umma kinyi arayuwa Wallahi shikenan kin tayar mata da hankali." Dariya umma tasaka tace " Gaku gabana ina kallonku shine zanje ina daga hankalina akan wata banza makiyana yadda banson mutuwata haka natsani Mutallab kuna ganin akwai wani abunsa da zanso so nake yasaketa ma takara gaba." Jidda dake gefe guda taja tsaki tace " Ai wallahi Umma dama ba yayana baniba da cikin daularcan zan shiga kamar yaya mutallab idan nasameshi aduniya ai nagama samun nutsuwa da jindadi umma zafa a iya kiransa da masu kudin kasarnan wallahi." " Ke dallah yimun shiru bakwa yabon yan uwanku sai dan uba uban wanene yasan kudin anasa namenene? Dakata malama ki kama bakinki kamin yayi shiru kinyin aure kamar bakiyi ba kullum kina gabana dake da dan iskan mijin naki da babu tarbiya a tattare dashi gwaragwara ma nakeji tunda ita Afrah har yanzu babu tsayayyan daman boka yacemun itada aure sai dai tagani anayi.
Menene haka Aryan bana hanaka wannan tunanin dakake zama kanayi ba yanzu saboda Allah menene Allah baiyi maka ba? Menene baibaka ba? Dan matarka taxauna acikin gidan nan menene wancan part din ko mata biyu zai dauka kuma kaga gudunmawar da mutallab yabaka anyi lefe anyi gyaran guri dasu ai kaga sai mu godewa Allah ko?. " ummy event dinnan duk sun cinyemun kudi wallahi banida dubu dari takaina yanzu fa." " Ai shiyasa kullum nake gayamaka amfanin adani ko? Wannan salary din ba abun a yarda dashi bani bako? Kaduba kaga dagani har mahaifinka shekarar mu nawa muna aiki Amma karshe dai abokinka ya taimaka mana da yanzu kana dam ajiye wani abun kaima kayi ginin nan ai ko?." " ummyna kudinne basuda Albarka wallahi kuma ahaka dan albarkan abokina MAM kinga yana taimakamin ta ko'ina yanzu ma banason na tambayesa kina ganin kusan 6m yabani gudunmawa kuma ma fa laifan rabi shiyayimun duk kayayyakin nan masu tsada wallahi shi yayimun su Ummi." " Allah ubangiji yayi masa tukwici da aljanna yabiyasa yanzu karbi zobena kaga zaiyi 500k ai ko kaje kasiyar sai kabani 100k nayi hidimar yini kaikuma kareki sauran yar gudunmawar dana samu sai nahadamaka nabaka Ni nafison kakama sana'ar hannu banason Aikin nan wallahi." " Tohm Ummy Allah yasaka da Alkhairi. Ameen tace.
Yadda takarasa gidan nasu tana danna uban horn haɗe da ihun mai gadi yasaka masu gadin tasowa asukwane suna buɗe mata ko datayi parking din motar kallonsu tayi cike da masifa tace " uban wanene yahanaka buɗemun? Nace uban wanene wallahi sai na sallameku yanzu yanzun nan Aikin banzan kawai asararru." Sakin baki sukayi da mamakin ganin halayyanta nada suka shiga bata haƙuri itakuma tashiga cikin gidan tana ihu da masifa." " Tunda inada gidan ubana sai nadawo ai wallahi bana zama da kowacce tsinanniyar yarinya da umma tacemun yar mabaraci ce." Da mamaki mumy da Kamal dake zaune suna hira suka kalleta " Meenal sai da kika zo bayan nagayamiki basai kinzo ba anjima zanshigo." " saboda ba diyarki za'ayiwa kishiya ba ai kyafaɗi haka gidan ubanane naga ko? Ko banida right din shigowa ne sai kin bani izini tunda ke kika haifeni." Da mugun mamaki mumy ta zuba mata idanuwa sannan tace " Ban hanaki zuwa gidan ubanki ha gakima aciki fitsararki kuma ki tsaidata akanki karki kuskura kice zakiyimun lamarinki kuma indai ni haifaffiyace bana kara shiga." " To daman nace kishiya ai kema makiyata ce nasani idan diyarki ce datuni kun bazama malamai.. saukar lafiyayyan marin dataji asaman fuskarta yasata saurin dago kanta tana kallon kamal da ransa yagama baci." " Ke dai ko shaidan yana kaunarki meenal halinki babu nakwasa Wallahilazim tunda har kike kallon mumy kina mata maganganun nan matar data maidake mutum ta daukeki kamar diyarta." " Wallahi Allah ya'isa ban yafeba nayi mata rashin kunya sai uban Me." Zai kara marinta mumy tace " kamar kyaleta kabarta da duniya rigar kowa ce wanda bai satabama jiransa takeyi." " Mumy yarinyar nan batada tarbiya ko kadan wallahi in banda kaddara irin ta Rayuwa ina mutallab ina yarinyar nan babu abunda ta'iya mumy sai fitsara ga kazanta ga rashin iya magana ai wallahi yayi kokari koni da idanuwana suka bude bana aurenki wallahi Ita macce itace rabin jindadin duniya idan karasata kuwa ai akwai masifa wallahi." "Bakin ciki shi zai kasheku gidansa ne na barsa na dawo gidan ubana naga wanda ya'isa ya hanani zama idan ya isa." Mumy dai da wani abu ya tokare mata wuya kasa cewa tayi komai sai daƙinta datashiga ta fashe da kuka mai tsanani dan har ga Allah bata fatan kara zama da meenal wallahi dan yarinyar batada hali ko na miskala zarra ina dalili, kamal da yaturo dakin nata yace mumy kuka kikeyi?." " Dole nayi kuka kamal Al' Amarin meenal yafara bani tsoro wallahi me yarinyar nan tarasa?." " uhmm danAllah manta da'ita shirya muje kiga sabon shagona kyaleta da halinta ai yanzu dady dai dai yake da'ita." " Tohm kamal bari nayi sallah sai muje ganinan fitowa tafada tanajin sanyi acikin ranta.
SHAFI NA TAMANIN DA DAYA
*MUTALLAB ASAD*
Arewabook:- billysfari
Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.
Oga wannan ɗan uwan naka muna wahalar dashi fa wannan karan boka yatabbatar mana sai ya kwanta aiki yayi kyau sosai. " Dariya sosai mutumin yashigayi yana faɗin " banason ya kwanta so nakeyi ya mutu gaba daya bana kaunar ganin mutallab bana kaunar sauraron sunansa, so nakeyi boka ya dakushar da duk wata daukakarsa ina fatan wannan karan kwanciyarsa tazama ta jana'izarsa." " ameen yaaa ogah." Dukansu suka saka dariya kowanne yana saka abunda yake son yafaru aciƙin zuciyarsa.
****
Tunda suka shirya tasaka abaya baka wacce ta amshi jiƙinta sosai abunka da macce mai ƙugu ga kuma cikar halitta na kirji tayi kyau sosai duba da yanayin da ake ciki ba hazo yasata daukar face mask tasaka kamar yadda taga dada duk inda zataje sai dashi. " Aicha zaman mekeyi haka?" Fitowa tayi tana faɗin " Dadata afuwan na tsaya nayi walha ne tafaɗa tana fitowa." " Ai sai gani nayi ƙingyara gurin kin dafa gandar ne?." " Eh dada nagama komai har ruwan shayi nasaka acikin fridge." " Kallonta dada tayi tace " Wannan duwawukan naki wai nawanene mudai kinganmu caras damu bamuda wannan garun jikin hala na dangin mahaifinki ne." Murmushi tayi tana rufe hannuwanta da fuska. Ko da suka fito sai da suka gaisa da sauran mutan gidan kamin su bude gate au fita tafiya ce da bazata gaza mintuna biyar ba takawosu wani tamfatsetsen gida da duk layin ko unguwar idan baizo na daya ba to tabbas nabiyu zaizo. Masu gadin ne suka bude musu gate din suka shiga. Duba da dada tagane kan gidan yasata Ta nufi babban bangaren datagani abude tundaga kasa take sallama har suka ɗane gadon suka shige. " Aicha dubamin gidan nan kamar na aljanu girman sa baiyi yawaba." Dariya aicha tasaka ganin abunda dada takeyi itakam da bata taba zuwa irin gidan nan nagayu ba kanta ne ma yake kokarin yimata ciwo." Haka suka haye sama nan ne sukajiyo mutane Alamu mazane sai kuma su afrah ita tana falo a tsaye idanuwanta sunyi jajir da Alama kuka tasha." Dada data ƙalli idanuwanta tace " ke diyarnan kalleni dakyau kuka kikayi? Nace kuka kikayi lafiyar sa kuwa nazata dan zazzabeni." Afrah da kuka ke kokarin cin karfinta tace " Dada tun jiya fa yana kwance baisan wanda yake ƙansa ba tafada tana kara fashewa da kuka. Cikin hanzari ta nufi daƙin nasa tana faḍin " Nashiga uku sajida shine kuka barsa gida kai Mahmoud bakuda hankali?." Tante ce tace " Sannu da zuwa dada wallahi likitoci sunfi biyar sunzo sungansa." Mahmoud kuma yace babban likita ma yanzu yafita dada kowanne sai yace lafiyarsa kalou Amma ko ruwa yasha kinga sai yadawo." " Innalillahi wa'inna illahirrajiun sannu Mutallab ubangiji yadubeka dan sayyadina rasulilahi (saw)." " Ameen sukace baki daya bari naje tante idan yafarka kiyimun waya akwai saƙonnin mutane dake hanuna yanzu." Amsa masa tayi tare da godiya. " Kidaina kuka kinji kidaina kuka Addu'a zakiyimasa zaiji sauki inshaa Allahu Kinji." Kallon Aicha tayi tace " Shikadai ne damu." " Allah zai bashi lafiya kinji. " jin dada nakiran Aicha yasata shiga daƙin har kasa ta gaidar da Tante sajida cike da fara'a ta amsa mata." Kinga ko abun kari bamuyi ba dada bari Naje na haɗa." " Tante zan hada miki ina kitchen din. " " A'a kuyi zamanku bari naje nahaɗa mana." To ko ayimasa abinci mai ɗan romo romo ko? Sai yasamu yasha." Basu karasa magana ba sukaga yana kakarin amai sosai cikin tashin hankali dada ta nufeshi sosai yashiga kakarin Amma babu abunda yake fita duba da babu komai acikin ciƙinsa Afrah kuma da gudu tashigo tana kuka tana kiran sunansa ga yaya jalil nan zuwa. Tante ce tace " Yanzu Afrah sai dakika daga masa hankali ko?" Shiru tayi batayi magana ba dada data rikoshi tace " Nashiga uku wannan zafin jiƙinfa? Yayi yawa wallahi ke kushirya muje asubuti Afrah ai ƙin iya mota ko? Maza ja muje Ke kamomun shi Aicha. Jikinta ne yakama rawa ta kasama gaba ballantana baya. " Bazata iyaba ai dada bati dai ni nakama miki." Afrah kuwa sauka tayi takira mai gadi yazo suka taimaka suka sakashi amota duk abunda sukeyi bayasanin inda kansa yake. Aguje afrah taja motar dada tana mata kwatance har babban asubutin da ake ji adashi a birnin ganin yadda likitoci suka bashi taimakon gaggawa yakara sanyaya zuciyarsu. Daki na musamman aka kaishe daga karshe ma da sukaga abun yana cin tura aka shiga gwaje gwaje." Sai asannan ne dada tace " ina Aicha din?" Tante fa itama sai a hankali tace ai can muka barta." " Ohni ƴasu ciwo dare daya sajida?." " Wallahi dada." Allah yabasa lafiya ya sauwaka masa." " Ameen sun dan jima agurin sukawu sukazo da matansu. Nan suka shiga yimasa addu'a kamin su juya. " Kinsan Me dada Mahmoud yafada ." " Kada kayimun korafi malam kabarni da tashin hankalin danake ciki kaje katawomin da yarinyata nabarta wancan makeken gidan." " Aikam naganta kitchen da Alama ko girki takeyi " " Kinji ko sajida Ai wallahi Yar albarka ce aicha tunda tazo gidan nan tsinke bazangayamiki ina dauka ba baiwar Allah Kullum ciƙin dawainiya dani Allah yabata abokin zama nagari." Ameen sukace. " Kinga dada results suma sunce lafiyarsa kalou." Shiru dada tayi tace " Allah ya maye bakinsu yabasa lafiya." Afrah kuwa najin haka tafita doguwar tafiya tayi acikin motar tashi kamin ta gane gurin almajiran datagani dazu cikin girmamawa ta tambaye malamin almajirin inda aka nuna mata wani tsoho kudin dake jaƙarta ta dakko wanda Akallah zasuyi dubu dari biyu ta ajiye agabansa sannan ta gaidashi. " Ƴar budurwa menene ke tafe dake." " Malam dan Allah ayimana addua yayana ne bashida lafiya to shine asubuti sukace babu abunda ke damunsa amma kuma ko magana baya iyayi." " Allah hakim Allah mai girma bazai huce sihiri baniba kada kidamu inshaa Allahu zai samu sauki Amma ki dauki kudinki Nagode." " danAllah DanAnnabi kakarba malam saboda Allah nabayar ayiwa dalibai sadaka." Nan yakira wani yaro yace " Kaje ka tsinkon yanzun nan ganyen magarya guda bakwai masu kyau." Amsa masa yayi shima ya tafi sannan yakira wani yaro yace ya miko masa alluna." Zan rubuta miki ayoyin karya sihiri sai kije ki dakasu ki zubasu aciƙin bokiti kisa rubutunnan aciki kikara ruwa yadinga sha yana wanka ƙinji Sannan adinga saka masa karatun kur'ani yana saurara sannan adinga karanta masa as'alullahal Azim har zuwa karshe inshaa Allahu zakuga ikon Allah." " Nagode malam Allah yasaka da Alkhairi. Daga asubutin kuma ta huce gida Nan ta tarar da aicha tana zaune palour da alama tsoro takeji." Cikin girmama wa Afrah tace " Anty Aicha munbarki ke kadai ko?" sœur(yar'uwa) yajiƙin nasa? Dafatan yaji sauki?" " Wallahi har yanzu bai farfado ba yana kwance." " Allah yabashi lafiya nayi jallop na abinci da kaza farfesu sai tea da nahaɗa." " Sannu da kokari jirani bari nakarasa sai mutafi." Sai dataje bangarensa ta dauka masa wayoyinsa tatarar da ko'ina angyara acikin dakin hatta bandaki wanda ko ba'a gayamata ba tasan aikin Aicha ne sannan ta hada masa rubutun ta zuye ajarkoki suka tafi.
******
Mumy dakeyiwa dady sannu da zuwa tace " kaganmu sai yanzu muka dawo yanzu nasamu dora abincin mashaa Allah shaguna sunyi kyau Allah yakara rufin asiri. " " Meenal dake sakkowa cike da murna tana faɗin " Dadyna sannu da zuwa." Banza yayi mata kamin yazauna yacee " Me kikazo yi?" Kuka tasaka masa tace " Nifa nahakura da aurennan dadyna kishiyafa zaiyimun." Bata ankaraba taji ya wanke mata fuska da mari " Ubanme kikazo kiyimun? Nace kizo kiyimun menene? Ke bazaki taba hankali ba? Kinsamu ya aureki shine wulakancin yau daban na gobe daban?" Kuka tasaka tana mamakin yadda dadyn nata ya iya marinta. " wallahi bana zama da kishiya nace maku idan ma ke kikaje kika zugashi munafuka sai dai munafurcinki yakare miki akanki muguwa." Ai saukar wayar da taji jikinta yasata saka kara tana ihu nan dady yashiga zaneta abunda basu taba gani ba daga ma'aikatan gidan har Mumy hankalinsu tashi yayi yau dady yana duƙan ƴar gwal. " Yar iska kikeso ki zamarmin nace rashin tarbiyan taki gaba yayi? Kisamu miji kamar Mutallab kina wulakancin nan? Uban menene kike takama dashi? Nace kigayamun uban menene? Dan ubanki kibarmun gida nabaki daga nan zuwa awa daya ki barmun gida." Mumy ce tashiga bashi hakuri. " Mansurah kina gani da mijin da zai iya da meenal? Bafa sonta yakeyi ba tsantsan biyayyar iyaye yasa ya aureta Amma kiduba kiga wulakancin da take masa akan yace zai kara aure banda taja girmanta yadda wacce zata shigo ɗin zata girmamara idan tazo." " Kayi hakuri danAllah dady." Meenal kuwa kuka tashiga yi taje ta dakko jakarta suna kallonta tabar gidan batace komai ba sai kuka da takeyi, mai dagi kuwa hangota da yayi tun daga Nisa yayi saurin wangale mata gate." " Dadyn meenal da baka daketa ba." " Mansurah a wannan zamanin idan diyarka tasamu miji murna kakeyi mansurah bakamar meenal danasamu ya aure ai sai lallabawa Amma kina gani tanaso takawomin damuwa. "
Yadda ta ware waka acikin motar tana ambatar sai yasakeni wallahi sai yasakeni nafaɗa nakuma fada yasiyawa kansa rashin mutunci kenan.
********
Kwance take a ƙan gado baccin daya ɗan fizgeta yasa taga wani dattijon tsoho yana faɗin " kece yabada sadaka Allah zai bashi lafiya, Asiri ne ajikinsa idan yadage da amfani da ganyen magaryar nan zai warware kigayamasa yadaina zuwa inda yake zuwa aski anan aka hada baki aka saci gashin ƙansa, kigayamasa kullum yadinga sadaka daga falalalar da Allah yayi masa, kigayamasa yadinga zama da Alwala, shine mijinki shine mijinki ...firgit git tatashi daga baccin tana karanto addu'oi dada dake kusa da'ita tace lafiyarki kuwa?." " Bakomai mafarki ne." " To tashi kiyi sallah kiyi addu'a sai kizo ki koma." " To tace mata sannan tatashi."
Aciƙin kwana biyunnan bakaramin jigata Mutallab yayi ba yaune ranar da yasamu yace ayimasa alwalah zaiyi sallah duk ya zuge ya wada jalil dake kusa dashine yace " Sannu yaya Allah yabaka lafiya." " Murmushi yayi yace naji sauki jalil ina dada tayomun tuwo." " Wayarsa yadaga yakira dada tace gatanan shigowa ma asubutin ai sunyo abincin kuma tuwon ne daman." Ko da suka shigo cikin asubutin Aicha ce rike da kwandon abincin dada na daddaga kafarta har suka cimma daƙin. Da Sallama tashiga itama tayi sallama tabita abaya. Sai da suka gaisheta kamin itama Aicha tace " Ina wuni yajikin Allah yakara sauki." " Jalil ne yace " Ameen buzuwa." " Tunda kinzo dada bari naje natawo dasu afrah da motar nafito Aicha zuba masa abincin DanAllah." Shiru tayi dan ita harga Allah bazata iya bashiba." Zuba masa tayi ta ajiye masa agefensa shiga jujjuya abincin yayi kamin ya kalleta yace " Ko zaki bani bazan iyaba." Dada ta kallah dada ce tace " bashi kinga lazumi nakeyi." " Tunda ta tsaya gabansa hankalinsa ke kokarin gushewa duk da tsananin zafin da jikinsa yakeyi Amma gaba daya Nutsuwarsa yake kokarin rasawa." " bari kuga naga goro acan nakarbo." " Dada kawo nasiyomiki." " A'a kibarshi Tunda har ansamu yanacin Abincin Ai sai a bashi ko." Fitar dada kenan ya fizgota ya rungumeta yana saukar mata da zafaffan Numfashi, fisgewa tayi tana faɗin " Menene haka jiƙina kakeso kikuma ni ? Ko da yaushe kana kokarin taɓani." Idonsa da yaciko da kwallah sai kuma can yace ke nakeso komai naki komai inaso Aicha danAllah ki aurene..." " Banasonka nace maka." " Astagfirullahi yaa Allah, yafaɗa jiƙinsa na kakkarwa DanAllah kiyi hakuri Ina rasa nutsuwata asanda nake tare dake kada shaidan ya.." shiru kawai tayi atasamu guri ta zauna kawai ta tsinci ƙanta da faɗin" Kadinga sadaka danAllah kadaina barin mai askinka yanayi maka kadinga shan ganyen magarya." To zanyi yafaɗa yana kallonta." Ki kunnamun wayata in kira jalil sai yaciri mana cash abawa mabukata ko?" Murmushin da batasan dalilin sa ba tayi." Ido yabita dasu yana faɗin " Gashi yamiko wayar Duba da itama dada tasiyamata ta iya kunnawa sai ta kunna ta mika masa cikin mintuna da basu gaza uku ba taga anshigo da bakar leda." Usman bata taje tayiwa duk wanda basuda lafiya." Langwabe ƙanta tayi tace Nifa ƙai nakeso kayi musu." " Bazan iya tafiya ba yafaɗa mata." To to sai ka dafani irin yadda Papa yakeyimun dayana raye sai idonta yaciko."
MUTALLAB ASAD
(labari mai taɓa zuciya)
Na
Billy s fari
Nana diso
RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU.
TAFIYAR BIYU TAFI DAYA
SHAFI NA TAMANIN DA BIYU.
Yadda Aïcha taji hawaye na ƙoƙarin sauko mata daga idanuwa ya sata saurin sunkuyar da kanta ƙasa, hakan ya bawa hawayen damar saukowa akan kyakkyawar fuskar tata tana jin wata irin matsananciyar kewar duka iyayen nata nataso mata a zuciya, Mutallab dake kwance ya ɗan jingina da pillown da aka saka masa a bayansa ya duƙo da kansa yana regen fuskarta ganin yadda tayi saurin yin ƙasa da ita bayan sauke kalaminta na ƙarshe, "ya subhanallah! Kuka kike Aïcha?" Ya faɗa yana jin zafin saukar hawayen nata cikin zuciyarsa, fuskarta dake kwance da hawaye ta ɗago haɗe da cewa, "Bani da wani zaɓi sama da haka aduk lokacin da zuciya ta tuno mani da ahalina, musamman Mà père da muka matuƙar shaƙuwa dashi sai naji duk duniyar tayi mun faɗi sosai saboda rashinsa." Mutallab daya tsareta da idanuwa tun data fara magana yana kallon yadda take motsa ɗan ƙaramin bakin nata ya lumshe idanuwa haɗe da buɗewa sannan yace, "Aïcha ba ke kaɗai bace a duniyarki ga wani marayan a gefenki daya taso da raɗaɗi irin wanda kike ji na rashin mahaifiya, zan so kibani dama na maye maki gurbin Mà père, mà mèrè da babbar yaya da naji kina faɗa, ina da tabbaci da kuma yaƙini akan zuciyata zata bani ƙwarin giuwar baki cikakiyar kulawa koda tis'in da tara ne bisa ɗari takowane fanni saboda we shared the same pain a zukatanmu na rashin iyaye duk dani nawa mahaifin na raye amma na tabbata hakan zai bamu damar kula da juna, tausayawa juna da kuma amincewa junanmu na har abada." Yadda yake yimata maganar idanuwansa na acikin nata har lokacin haɗe da marairaice murya ya sata sauke idanuwan nata a ƙasa dan bazata iya jurar cigaba da kallon nasa ba kaifinsu yai mata yawa, ajiyar zuciya Mutallab ya ja ya sauke jin bata ce komai ba tare dayin baya ya sake jingina da pillown bayansa yana rufe idanuwansa a hankali yana cewa, "Allah ya jiƙansu da rahama." Ta amsa mashi da "Amin." Ba tare data ɗago kanta ba tana wsa da yatsun hannunta, tsawon mintuna biyar suka kwashe a haka zuciyar kowannensu na bugawa da wani kalar sauti da bazasu iya tantance ko wane iri bane musamman ita dake kallon lamarin dake faruwa tsakaninsu kamar wani wasan kwaikwayo, a hankali ta ɗago kanta haɗe da zuba masa kyawawan idanuwanta tana ƙare wa kyakkyawar fuskar tasa kallo, kamar daga sama taji muryarsa yana cewa, "Wannan kallon fa?" Da sauri ta janye idanuwanta tana ƙoƙarin barin wajen yai saurin riƙo hannunta ba tare daya buɗe idanuwan nasa ba, "ina zaki je baki ƙarasa aikinki ba? Faɗa mun kallo me ne kike yimun haka bayan kin kasa karɓar ƙoƙon bara na, me yasa ba kyajin tausayina Aïcha?" Ya ƙare zancen tare da buɗe idanuwansa yana kallonta, hannunta ɗaya riƙe ta kalla sannan ta ɗago kai ta kallesa, yasan me take nufi dan haka da sauri ya sakar mata hannu yana murza gaban goshinsa haɗe da cewa, "Sorry i never knew i could love someone the way that i love you, your love drive me like crazy Aïcha shiyasa bana iya controlling kaina matuƙar zaki yimun irin wannan kallon da kika gama yimun yanzu, sorry pls". Yana rufe baki Dada na shigowa, hakan yasa Aïcha taja bakinta tayi shiru ba tare data bashi amsar abinda ke zuciyarta ba. Ganin jikinMutallab ɗin daya ɗago idanuwa yana kallonta yai ƙwari ba kamar yadda tafita ta barshi ba yasa Dada faɗaɗa fara'arta tana cewa, "Alhamdulillah kace jikin naka yai sauƙi?" "Eh Dada jikar taki ta iya jinya." Yafaɗa yana maido idanuwansa kan Aïcha, Dada kuwa taɓe baki tayi haɗe da cewa, "kai kasani dama can iyayi ya kai kwanciyar asibitin, Aïcha ɗauki kayan mutafi tunda ga Jalil can naga yakora waje tsabar rashin kunya". Da sauri ya ɗago kai haɗe da cewa, "Haba Dada! Tafiya kuma Fisabilillahi bayan kina ganina kwance rai a hannun Allah." Yafaɗa yana langaɓe kai tare da komawa ya kwanta yana jan duvet ɗin dake kan gadon ya rufe jikinsa dashi, hakan ya bawa Aïcha dariya Dada dake rafka salati tace, "Mugun fata zakayi mana kenan Mutallab? Kagama warewarka yanzu daga magana saikakoma kan gado ka naɗe baka da lafiya?" Dariya Jalil daya sake shigowa ɗakin yai dan ɗazu lamarin yayan nasa daya kasa danne sirrin zuciyarsa agabansa ya sashi fita, ledar kuɗin daya shigo dasu ɗazu dake hannunsa ya miƙawa Aïcha yana cewa, "Ungo wannan riƙe masa, ke kuma Dada zo muje na ajiyeki gida ki huta dan wannan sa'idon naki yayi yawa." Ya ƙare zancen yana dariya haɗe da jan hannun Dada suka nufi ƙofar fita, "Kai ni cikamun hannu dila sarkin wayau, duk wannan abun nasani sarai akan Aïcha yakeyi kuma ni bazan bari ta aureshi ba tunda bata
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 46 Chapter of 54