Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ɗáuka ka isa da ɗanka ne, nazata shiɗin ai ɗan tarbiyane amma ace tsabar rashin mutunci yashigo har gidana yace ɗiyata batada tarbiyar da zai aureta? Duk rashin tarbiyarta ai bata bin maza? Kamar ni da arziƙina da kuma mutuncina ace anzo har cikin gidana an wulakanta mani ƴah? to wallahi kagayamasa duk wani abu yasemeta bazan taɓa haƙura ba sai na ɗauki mummunan mataki akansa, aikin banza kawai". Yana magana yakashe wayar, ji Abba yayi wani irin jiri ya ɗebesa zuciyarsa nayi masa ba daɗi. "Lafiya Alhaji?" Umma tafaɗa tana ƙoƙarin riƙasa ganin yana ƙoƙarin miƙewa tsaye tare da cemasa ya zauna kada ya faɗi, sai da Abba yana ajiyar zuciya sannan yace, "Yaronnan ne ke nema ya tozartani, yanzu ace Alhaji Abdulmalik Mu'azzam zai nemi yaje yaga ƴarsa ya aura masa ita saboda tana sonsa amma sai yaje ya wulaƙanta yarinyar mutane wai bazai aurenta ba batada tarbiyar?" Hannuwa ta shiga tafawa haɗe da cewa, "Shi Mutallab ɗin? Kaji ɗan iskan yaro to shi tarbiya ne dashi da zai daɗi haka, banda yana ɗan iska ma me zai gwadawa yarinyar duk da bansanta ba?" "Nima shi nagani Hajiya". "To Alhaji idan bai sonta ga Jamil nan sai ka turashi su daidaita, shine amfanin haihuwar ƴaƴa da yawa, nasan dai bazai wuce ɗan hasken fata da kyan fuska da yake dashi ba take sonsa, to ko Jamil ba'a baya ba dan baƙar fata ma tafi quality". Shi dai Abba bai iya cewa komai ba har ta gama suruttanta tafita..... #Mutallab Asad #Tagwaye Biyar #Billy S Fari #Nana Diso *MUTALLAB ASAD* *PAID BOOK #500* *TAGWAYE BIYAR.* NA *NANA DISO** & *BILLY S FARI* 38. Janye jikinsa yayi yana faɗin, "ke babu abunda kika iya sai son jiki, ke da zaki saita kanki kidinga dan tutturo gaba yanda zaki ɗauki hankalin masu kai da komowa saman titin nan ko Allah zai kawo yau musamu babban rabo". Mà père yafaɗa yana yawo da rufaffin idanuwan nasa da ba gani sukeyi ba akan titi. Cikin takaici takalle sa batare da tace komai ba sai daga can kuma tace, "Mà père wallahi Allah te regarde (Abba wallahi Allah yana kallonka)". "Aïcha! Wai malama kike son zama ban saniba? Nace malama kike son zama? Idan bamuyi abunda zamu samu kuɗi ba uban me zamuyi? Kajimin ja'irar yarinya". Batare da tabashi amsa ba ta ɗauke kanta tana matsara ƙwalla, can taji wani yana faɗin, "ke yarinyar nan karɓi". ya miƙo mata kuɗin dake hannunsa, cikin hanazari taje ta karɓa tana fara'a duba dashi baice zai taɓa jikinta ba. Mahaifinta dake gefe ya shiga miƙa mata hannu yana dariya haɗe da cewa, "Yawwa Aïcha ƴar albarka, muƙamin nan nawa ne ya bayar?" "Mà père cinq cent ce fa (Abba ɗari biyar ce) kuma shi bai taɓani ba yana bani yayi tafiyarsa". "To Aicha Menene idan ma yataɓaki?" Cuno baki tayi kafin tace, "Mà père haramun ne fa". Taƙare zancen tare da taimaka masa ya tashi sukaci gaba da tafiya ba tare daya kulata ba tunda dai yayi arziƙi ta amshi kuɗin ta bashi. Cikin ikon Allah yau dai sunfito da sa'a sai gashi wasa wasa suna ƙoƙarin haɗa dubu biyar. "Mà pére kaga yunwa nakeji kuma fa yanzu uku takusa zanje makaranta ya kamata mutafi gida haka in yaso gobe sai mu dawo da wurwuri kaga yau mun samu kuɗi sosai". "Aïcha wai bazaki haƙura da makarantar nan ba?" "Wallahi bazan haƙura ba mà père, dama ana haƙurine da ilimine! Allah idan baka daina hanani zuwa makaranta ba zan daina kawoka wajen barannan kaina, kuma kasan dai yafemme bazata taɓa takoma ba" tafaɗa cikin jin haushin maganarsa, Jin abunda tafaɗa yasa dole ya bita suka kama hanyar gida wata irin jiri na ɗibarta saboda yunwa tunda ya hanata kuɗi su sayi abinda zasu ci. A hanya ma sai da suka dinga karɓar sadakar abun takaicin ta daya mahaifin nata yanzu ya haɗa jarin da ko bai kula da idonsa ba to tabbas zai iya kama sana'a Amma ta rasa wacce kalar masifa ce wannan kullum kara san kudin yakeyi, yamakasa daina barar. Ko dasuka karasa kofar gidansu Sun tarar Da hammad ɗan gidan mai unguwarsu. " Baba sannu da yini". " murya kamar hammad Baba yafaɗa." Murmushi hammad yayi yana ƙallon Aicha yana wani kanne mata idanuwa kamin yace " oui, c'est moi (eh Nine) " " kaga yaron kirki ke Aicha sai kije Ni bari Na karasa gidan ko?" Kallon hammad din tayi da takaici sannan tace " yau ma tattabanin zakayi? " " Haba Aicha Nifa sonki Nakeyi da Aure." Manyan idanuwanta ta zuba masa tana takaicin wannan hali Na iyayenta kowa yasan hammad har ciki yataba yiwa wata yarinya Amma duba da babansa yanada maiko yasa babu ruwansu suke turata." A hanƙali ya riko hannunta yana faɗin "Aichata."  Harara ta dallah masa saboda takaici kamin ta fizge hannunta tace " Arrête de me toucher (kadaina taɓani)." Shiru yayi yana kallonta har tayi tafiyarta, aciƙin ransa kuma yana ayyana ranar da zai kama yarinyar nan sai yayi mata kaca-kaca yarinya kamar ba yar garinsu ha ita matsatsun kayan da su attachment duk baya gabanta hmm. Ko sanda ta kusan isa gidan Nasu taji karat disco yana tashi Alamun yau ma yayar tata ta aro waya kokuma tasamo speaker, gabadaya yanayinta sai yakara sauyawa, Sallama tayi tashiga tana ganin Mama da baba suna gefen yayar tata kallon su tayi taje ta kashe speaker din. " grande soeur (babbar yaya) wannan ƙidan yayi yawa." Mama ce ta kalleta tace " ke me isa ƙinfoya fitsara Aicha dan kidan da mukeji dan mu samu Nishadi shine zakije ki  kashe mana ince yayar taki sa'arki ce." " Kazamar banza da wofi babu abunda kikeyi sai wari, dubi kayanki saboda Allah Duk sunyi muni gasu manya idan Nabaki kaya kice ke bakyaso haka zaki kare dan babu namijin da zai soki bai tabamiki jiki ba." Mama ce tace " grande soeur ( babbar yaya) gayamata dai ga kyau dai Allah yayi mata da sura Amma ba'a amfani dasu." " Mama kyaleta da kyanta na banza ne tunda ba shigar kirki takeyi ba kayanki fa take sakawa?" Baba yayi caraf yace " haka dazu fa manyan mutane suka kiramu zasuyi mana alheri yarinyar nan tayi caraf tace " Ɗan iska ne." Gaba daya takaicinr ya tsaya mata aranta baƙinciki yana kokarin taso maya Yayar tata ta ƙallah ganin yadda Taci ƙarin gashi ga kayan jiƙinta dakyar take motsi saboda matsewa " Baba kai karbi wannan ta miƙa masa." Dadina dake albarka Amina yanzu duk wannan nawane? Wallahi har cikin raina nafisonki." Ta mikawa Mama nata sannan ta mikowa Aicha tana faɗin " karbi kema ba dan halinki ba, kullum kinki kiwaye sai kace jaka dubi shigarki." " Banaso ki rike kudinki ai bansan ta hanyar da akasamo ba tunda ba sana'a kikeyi ba ba kuma aiki kikeyi ba baza..." bata karasa ba taji Mama ta dauketa da mari tana faɗin " Aicha sois prudent (ki kiyaye) mara kunya kawai." Kuka Aicha tasaka tayi hanyar daƙi." " Ina zaki shiga maza shige kiyi wanke wanke." Jiyowa tayi tafara kuka tashiga wanke wanke duk da lok'acin makaranta yaja sosai. Yanzu tanayin magana karshe a daketa koma ace bazataje ba, sai datagama wanke kwanukan sannan ta sadaddafa kitchen taje taci abincin datagani a kwano tasan na yayarta ne tunda har taga nama guda 5 aciki, yadda tadinga afa abincin zai tabbatar maka da yunwa takeji, cikin ranta kuwa Addu'a taketayi Allah ubangiji karyasa akamata haka kuwa ya kasance dan har tagama cin abincin babu wanda yafito zuwa bangaren dasuke girki. Wanke hannunta tayi ta kalli kanta ganin mahaifiyar tasu tana daƙin kakarta sai tayi maza tashige dakin dasuke kwana ita da babanta wasu tsoffin kayanta ta dakko tasaka rigara ta daura zanin duba da sunyi mata yawa sosai amma ita abunda takeso kenan." Jakarta ta dauka tayi bayan layinsu gidansu Aminiyarta bilki, tana isa taga bilki zaune kan dan daddamalin tsakar gidansu. " Aicha har kun dawo daga barar?" Wannan kalmar tana daga ciƙin kalmomin dake bakanta mata ranta, ko ace mata mai bara ko diyar mai bara. " Nagayamiki bilki kidaina cemin haka ko?" Dariya bilki tayi tace " Allah yabaki hakuri kawata tsokanarki nakeyi.yanzunnan nake maganarki nace idan baki karaso ba tafiyata zanyi." Dallah mata harara tayi kuka na kokarin kwace mata. Tace " Au kema tsokanata zakiyi Amini? Kema kalmar da banaso zaki jefeni da'ita to menene bambancinki da sauran mutanen unguwar?" Hamma ce tafito tana faɗin " A'a A'a wanne shashanci ne wannan? Nace wanni shirme ne wannan amini? Banason kalmar nan taki ita dake zuwa nan taji daɗi idan kika dakko wata dabi'a gurin wazataje?" " Yi hakuri Aicha nifa tsokanarki nakeyi Amma bazan kuma ba kiyi hakuri." Kukan Aicha ne yayi ƙarfi tace " Nima bada son raina kaddarara take ahaka ba, bantaba ganin irin iyayena ba bansan kalarsu ba, amma duk kalar lallacewar da sukayi ai iyayena ne kuma babu yadda zanyi ai dole nadinga yimusu addu'a." " Allah zai sa su gane inshaa Allahu kidaina kuka Addu'a zaki cigaba da yimusu har Allah yaganar dasu, ke Amini zuba mata abinci sai kutafi karku makara." " hamma nagode yanzunnan naci abinci ta dakkomin hijjabina Insaka sai mutafi. Ko data ƙarbi hijjabi sai taji wani sabon baƙin ciki yacikata hatta hijjabin ma iyayenta basa barinta tasaka saboda idan tasaka ai maza bazasu ganta su bata kudi ba. taƙaici da bakin ciki ne yataso mata taja hannun Amini suka karasa makaranta, acan dinma sai da akayi rigima da'ita dan wasu kawayensu na ajinsu suka kama zancen mahaifinta har wasu suna cewa Ai matacciyar zuciyace dashi shiyasa. Karo Na biyu kenan tana share hawayen dake fuskarta, " DanAllah Aicha kiyi hakuri." " Yanzu haka zankare rayuwata ana kirana da sunan mabaraciya agabana azagi babana azageni yaya zanyi ne ni Aicha tafada tana kara fashewa da kuka." " Aicha hakuri zaki, yakamata ayanzu ace ƙin karbi kaddararki hannu bibbiyu yakamata ace zuwa yanzu kin amince da kaddararki kidaina kuka kikara dagewa da Addu'a Allah yakawomiki mijinki kiyi aurenki." " Amini babu ranar da bana musu addu'a babu ranar da zatazo batare da naroki Allah yabani miji magari ba banason aure a nan kusa namafison Nisa wallahi, yau shekara ta 5 inayiwa mahaifina jagora ayanzu yaci ace yadaina wannan maular, tunda yasamu abunda yake bukata, amma a yanzu ne nafahimci yakejin daɗin barar. Zuciya ta mutu banda kima da mutunci kiga yadda grande soeur (babbar yaya) take bata mana suna agarin nan tazama yarinyar masu kudi wallahi dazu kusan tashigo da kudi cent mille (dubu dari)". Cikin zare idanu takalli Aicha tace "  êtes-vous sérieux? (Dagaske). Hararta tayi tace " To ina miki karya ne?" " continue de prier pour elle (kicigaba da yimata addua)." Kullum sai nayi mata ai bama ita kadai ba har su baba Muje gidanku kibani sabulunki nayi wanka naji jikina yana dan tsami." " Dan ma kinada tsafta ne wallahi da bakida ita bugawa zakinayi fa saboda rana da kuke shiga." " je mets toujours de l'alim sous mes aisselles pour éviter les odeurs ( ko da yaushe ina saka alimun a hammatata dan na kiyaye kaina daga wari)." " Nima fa ina sakawa kuma ke bakya barin gashi naga rannan ma kisiya reza ai." " Kinsan Mama da tsafta sosai tana kula da komai namu na nan ita tasiya mana alimun din ma." Ko da suka karasa gidan nasu sai datayi wanka sannan ta wanke kayanta da Oman da amini ta bata sannan ta shanyasu dayake daman tatawo da abunta." Aicha baki samo mana wani sirrin ba mu rubuta?" Hmm hamma batanan ko?" " Tatafi biki sai dare can zata dawo." To ingayamiki jiya da ma mère soeur (kanwar mamata) tazo inaji Mama na gayamata wai haɗin tsumin datayi tagyara kanta, wai yana saukar da NI'IMA sosai kuma yana maganin sanyi." " Allah yabarmin ke Aicha wallahi banida damuwa in kina kusa dani, kinga ni bikina saura wata biyar kema Allah yakawo miki miji muyi atare." " Nifa inaso inyi karatu sosai." " Uhmm Amini karatun nan naki fa bazai yihuba wallahi Gwara kiyi aurenki yafi miki." " To ke Amini wanene zai aurene ? Yar masu roko." " Kina mamakin lamarin Allah Amina muna nan dake zaki samu miji inshaa Allahu Ai shi aure ba'a Yi masa haka da lokacinsa yazo duk surutun mutane zakiyi aurenki." je souhaite que (ina fatan haka)." " Gayamin haɗin tsumin to." -CARDAMOM 10PC -SASSKEN BAURE 1Spoon -CITTA 1 -KANINFARI 1SPOON -KIMBA 2PC -RAKE -ZUMA 1CUP -MAZARKWAILA 1 -RUWA 10CUP -CINNAMON 4PC -MINANNAS 1TEASPOON -RAIHAN 1TEASPOON -JITA SALAM HALF SPOON -ƳAƳAN BAURE 1SPOON -GARIN DABINO. Ƙinsan har haka naji tace yana wanko ciki sosai sannan yana maganin sanyi, amma banda masu ciki naji tace." " Kai amini ta Allah ya tsundumaki a Aljannah danAllah kicigaba da jiyomana karatu kinsan Mama karshece a wannan gabar." " Ni zangayamiki wallahi da ace zatayi sana'ar kayan mata Allah da ta gyara mata dayawa. Yanzu dai ba wannan ba ingayamiki dazu professeur (malam) farouk yabani wata addu'a dayaga Ina kuka." " Nifa na lura sonki yaƙeyi sosai malamin nan." Kai danAllah daga mutum yadamu daƙai sai soyayya?" " Nidai gayamin addu'ar dan nasan bazaki yarda ba ai."  Yace " idan kasamu kanka a halin damuwa ko wanne kuncin rayuwa, ko Neman aiki ko neman Mijin aure kai koma mai kakeso karkayi kasa agwiwa muddin zakiyi wannan addu'ar Allah SWT zai kawo maka sauki acikin Al'amuran ka, Anaso bawa yayi wannan adduar da iklasin Allah ga addu'oin kamar haka-                   حَسْبُنَا اللَّهُ سُيُؤْتِينَا اللَّهُ وَرَسُولُهُ مِنْ فَضْلِهِ إِنَّا إِلَى اللَّهِ رَاغِبُونَ ☝️رَبَّ إِنِّي لِمَا أَنْزَلْتَ إِلَيَّ مِنَ خَيرٍ فَقِيرٌ - ☝️- رَبَّ إِنِّي مَغْلُوبٌ فَانْتَصِرُ ☝️- رَبَّ لَا تَذَرْنِي فَرْدًا وَ أَنْتَ خَيْرُ الْوَارِثِينَ ☝️لا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللَّهِ الْعَلِيَّ الْعَظِيمِ ☝️- لا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ سُبْحَانَكَ إِنِّي كُنْتُ مِنَ الظَّالِمِينَ Ga addu'oin nan asama kuma yacemin wannan addu'ar kamar magani ne ace anti biotic duk irin matsalar da kike ciki zaki iya karantawa yace idan sansamu ne ma natashi cikin dare nayi sallah sai nayita karantasu zanga ikon Allah da yardarsa. " Kai Amma mungode Que Dieu te bénisse Aicha ( Allah yayimiki albarka Aicha.) Bari kiga inyi isha'i nayi gida nasan idan ba'a dakeni ba to zansha faɗa. #Mutallab Asad #Tagwaye Biyar #Nana Diso #Billy S Fari *MUTALLAB ASAD* *PAID BOOK #500* *TAGWAYE BIYAR.* NA *BILLY S FARI* & *NANA DISO* 37. Yana gama wayar da Jalil aka sake kiransa da wata baƙuwar lamba ya ɗaga dan yana tunanin ko customers ne amma sai yaji wata murya ana magana cikin faɗa, Sallama yayi yana faɗin, " Subhanallahi waye ke magana?" "Mara mutunci daman ai baza ka gane mai magana ba, Mutallab wato kai kana can kana shaaninka ga ƴata kabar mani kwance saman gadon asibiti cikin wani yanayi, kai kam ba kada tausayi ne dan ƴata ta nuna maka so zaka kirata da mara tarbiya? Kai wane irin yaro ne mai taurin kai da zaka zaɓi kabar Mahaifinka kai da ƴan uwanka saboda yace ka auri ƴaƴan?, to bari in gayamaka wallahi tallahi bakada abunda zaka wulakantata, na baka daga miliyan goma har zuwa ko miliyan nawa kake so kazo ka faɗa mani zan baka indai zaka amince ka auri ƴata saboda akanta babu abinda bazan iyayi ba". Goshi Mutallab ya shiga murzawa da yatsun hannunsa kafin ya furzar da iska tabaki yace, "Kayi haƙuri Dady abun bai kai nan ba, ni ko da ace ina don ƴarka zaka bani kuɗi bazan taɓa karɓar ba saboda ni ba cima kwance bane balle nayi auren jari, to sai kuma aka tasa da sam ƴarka batayi dai-dai da ra'ayina ba da kuma zaɓina ba.." tun kafin yaƙarasa Abba ya katsesa haɗe da cewa, "ƙarya kake Mutallab ƴaƴan tafi ƙarfin kace mata haka! Ko da batayi daidai da tsarin ka ba ya zama dole ka aureta kaji na faɗa maka". Yaƙare zancen tare da jan tsaki yakashe wayarsa, bin wayar Mutallab yayi da kallo kafin Aryan da tun yana wayar ya iso wajen ya ɗagawa, ɗari kai Mutallab yayi dake faman jan numfashi saboda ɓacin ran maganganun da Dady yayi masa yace, "MAM calm down please wannan abun kada yaɓata maka rai, ka kwatanta kanka a matsayinsa Kai kasan dole zai shiga damuwa kuma yace zai yi duk abinda zai yi ɗan samawa ƴarsa farinciki". Kasa cewa komai Mutallab yayi sai dai ya zuba masa idanuwa, ya ake so yayi? Me ake so amaida shi ne? Ya tambayi kansa kafin yace, "Aryan na rasa me ake so nayi? sun gama wulaƙantani da tozartani shine yanzu za'a ci gaba da bibiyata ana caɓa mani maganganu? Shin ni macce ne da za'a ce dole dole sai anyi mani auren da bana so? Me yasa suke mini haka Aryan ko ni ba mutun bane? Gaba ɗaya an hanani nayi farinciki da walwala, daga wannan sai wancan fisabilillahi!". "Kayi haƙuri dan Allah MAM komai zai wuce in Sha Allah, yanzu duk ba wannan ba ina ka kai mani matata?" "Tana gidan Jalil". Ya bashi amsa ataƙaice yana jin zuciyarsa cunkushe, Zaro idanuwa Aryan yai haɗe da cewa, "Rilly? Ashe da gaske Jalil yake yi daya ce in tayasa godiya ka bashi gida da mota". "Ni gida kuɗin da ne nayi masa amfani dasu, mota kuma taimakonsu zatayi shi da matarka ya riƙa sauketa makaranta, banyi tsammanin zamu shiga gidan ba yanzu shiyasa naso nayi maka surprise idan an kammala duka har nawa nakaika ka gani". "Wow Masha Allah, this is the real definition of brother, Ina tayasu godiya Allah yaƙara buɗi, da ace duka ƴan uwa haka suke kamar kai to da duniyarmu ta zauna lafiya, Alhamdulillah mungode Allah MAM Allah yaƙara rufa asiri duniya da lahira". "Ameen Nagode, ina tunanin fa gobe zan wuce kaga akwai abubuwan da nake so naƙarasa can gida saboda haka mu haɗu after magrib". Hannu yabashi suka gaisa sannan kowa ya nufi motarsa ya shiga suka wace. Fitar yaya mutallab ƙeda wuya Afrah taraka jalil sukaje suka siyo furniture set Na Ash colour duk da sunada ɗan kudi sosai daman Afrah tabashi shawara akan yasaka a palour dinsa tunda Allah yasa gaba zaiyi aure ai gidan matar tasa zasu saka Nasuz hakan kuma yayi sai ya dauki shawararta suka siya sai set Na gado guda biyu sai set Na labule duba da sunga TV da fridge kusan guda 4 agidan yasa basu siyoba, sai da suka Biya komai sannan sukayi ɗan karamin store suka siya abu da zasu dafa sannan sukayi gidan Haka kuwa akayi ɗan kamin sukarasama har motar kayan tazo tare dai da masu kayan suka haɗa komai da komai MashaaAllah tabarakallah Afrah taketa faɗin duk ɓacin ran da suke ciki sai sukaji ya ƙau. Mutallab dake zaune yana lissafi, apalour duba dashima yasan kamin yadawo angama ginin gidan nasa yasa yake ɗan kasafta wasu kudaɗe da zaiyi order." Afrah ƙin haɗa kayan?" " Yaya Tun dazu na haɗa bakaci abinci ba kuma tundazu aka gama." Afrah wannan girkun sai ku abinci babu nauyi ai bazai ɗaukeni ba." Cikin hanzari tace in maka tuwo?" Dago ƙai yayi ya kalleta yace " Munci abinci tare da Aryan ai nakoshi Nagode." Jalil dake tayasa lissafi yace " Ranka yadade zaka daɗe ne?" " Jalil I don't know kasan halin tafiya zamu fara sauka a Madina ne daga nan muyi 6days muje maka muyi 5days. Ihun da Afrah tayi ne yasasu kallonta. " Ashe mafarkina gaskene makka zanje,yayana Tafada tana kuka.. " Jalil ne yace " Allah yashiryeki Aryan kuma yakara zuba masa ido yace " MAM saudia?" Mà tànte sajida dake lazumi tace ai gwara dai anayi ana hadawa da zuwa ayi ibada Allah yakaiku lafiya." " Aryan ne yayi murmushi yace " Ameen ." Murmushi Afrah tayi masa hakan yasa yakasa fadin komai. Sai da Mutallab yace daga can idan mungama zan sauka a Niger daga nan muyi birnin Niamey gidan ayoub gwongwon Mà tànte sajida tayimun kwatance da bayani sosai ." " Allah yakaiku lafiya yadawo daku lafiya ya MAM abunda kajeyi Allah yasa albarka." Ameen duk sukace. *KASAR NIGER*     NIAMEY Babban birni ne acikin ƙasar Niger, wani raƙwaɓaɓɓan gida ne da ko ba'a gayamaka ba kasan gidan marasa ƙarfi ne kasancewa ginin nasu ginin ƙasa ne, tun daga soron gidan wani dattijo ke zambaɗa masifa, da dukkan  alamu faɗa yakeyi haɗe da kuma ƙaguwa da jiran da yakeyi. tsaye yake cikin wata ƙodadɗiyar riga wacce ta yage daga gabanta ga hannunsa dauƙe da sanda kansa da wata mokaɗaɗiyar hula da dauɗar dake jikinta ta tsananta bayyanar tsufa ta, yadda yake coccokala sandar duk inda ya samu ya tabbatar da cewa shi ɗin yana ɗauke da lalurar rashin gani sosai, cikin ɓacin rai yake ƙwallla mata kira da "Aicha, Aicha". Mahaifiyarta ce ta kalleta tace, "Aicha wai menene kike son zamane? Ba kya jin Má pére (Abba) yana kiranki ne? Ke kullum idan zakuje barar nan sai kin jawowa kanki faɗa kin ɓata masa rai? Menene haka Saboda Allah Aîcha? Ina kuɗin barar nan dasu muke cin abinci har ke? Kesan Allah maza ki tashi kije, Idan baki rakashi ba kinyi masa ƴar jagora ba wacece zataje tayi masa? Yayarki? Bayan gaki yarinya wacce Allah yayiwa kyan jiki da fuska da kowa ke sha'awarta? Haba Aîchan má pére tashi kije kinji ko?" "Má mèrè (Mama)?" Kyakkyawar yarinyar da shekarunta bazasu haura sha shida ba zuwa sha bakwai ba da ake kira da Aîcha ta faɗa tana kuka, mahaifiyar tata tace, "Na'am Aîcha nifa banason kukan nan". "To má mèrè shikenan kullum-kullum kuna sani zuwa Bara nifa bana son zuwa, shi Má pèrè sai yayita aikani gurin maza suyita taɓani dan sunga baya gani, Fisabilillahi yanzu yana da kuɗin da zai iya buɗe shago yakama sana'a ya dena wannan baran amma yaƙi, kuma ai idon nasa yafara gani tunda idan aka bamu kuɗi yana gane ko nawa ne, Allah ni yau bazan je ba  islamiya zan tafiyata, haka kurum ni karatuna sai yana lallacewa saboda bara, bokon nan har yanzu kunƙi bari na ƙarasa duk girmana ace aji uku nake ga ƙawayena tuni sun ƙare secondry, yanzu kuma itama islamiyyar ma so kuke na dena zuwa duka a wuce ni, to da kuke turani baran wanene zai aure ni jahila? Su masu kuɗin da kuke faɗin zasu aurene a cikinsu babu wanda zai yarda ya AURI JAHILA!" Ai bata ankara ba sai dai taji má pére daya biyo sautin muryarta da yake ji yaƙaraso wajen yana mammaka mata sandar dake hannun sa yana cewa, "Aicha Aicha nemavous êtes très stupide? (Aîcha ke bakida mutunci ko?)" Kuka tasaka tana kallon mahaifiyarta tata dake kallonta itama tana cewa, "Kin tsaya kina kuka baki tashi ki wuce ba, ke ko gajiya bakyayi kullum sai anyi dake kamin kitafi barar nan?" Turo baki Aîcha tayi tana maƙe kafaɗa daga inda take zaune mahaifiyar tata ta sake cewa, "Aicha levez-vous et partez (AîchaTashi kuje)" "Haba má mèrè une femme (Ni macece fa kuma dan ina da kyau sai ace ariƙa fita bara dani, kullum sai kina goya masa baya bayan yatara kuɗin nan da zasu rufa mana asiri, Allah kudena abunnan da mukeyi fa haramun ne, kin fiso muƙare a haka shikenan zuciyarsa ta mutu" Saukar sandarsa da Aîcha taji yasata miƙewa tsaye cikin wata barkacacciyar rigarta dataji jiki itama kanta babu ɗankwali tana kuka, muryar má pére taji yana faɗin "Shashasha zo na dafaki mu wuce rana nayi". Jin taƙi zuwa tayi tsayenta a gefe ya sashi cewa, "Aîcha sois prudent (ki kiyayeni ki kula fa)" ɓaci rai na bayyana a fuskarsa, turo ƙaramin bakinta tayi tana kaɗa manyan idanuwanta tace, "Allah nous regarde (Allah yana kallon mu) abunda mukeyi ba kyau kuma tilasta mani kukeyi bana so gani da surar manya amma adinga sakani agaba ana tallah dani dan asamu kuɗi". ta ƙare zancen tare da ƙarasowa kusa dashi ta riƙa sandar shi kuma ya dafata yana faɗin, "Ja'ira shige muje kamin na fasamiki wannan bakin naki da babu komai sai rashin kunya aciki". Daga lokacin bata sake cewa komai ba tafara tafiya tana share ƙwallon da ta zubo mata, mahaifiyar tata kuwa tayi murmushi tana ce, "kunga dirarriyar ɗiyata Aîcha ta má père, gaba acike baya ma cike, ƴar albarka kiriƙa ɗan tutturo kirjin mana ko Allah zaisa mu samu rangaɗeɗen attajiri". bata tankata ba tayi wucewarsa ɗan inda sabo ta saba da wannan mugun kirari da baƙar nasihar da mahaifiyar tata keyi mata waɗanda da ace

Chapter 22 of 54