yanzu saboda Allah da kudin nan duka zaka basu babansu? Ai macire ko dari biyu ne." " tunda kin cire ai shikenan karkuma kidameni da mita, ina Aicha din take mutafi bara." Sama da kasa suka nemeta agidan hakan ya tabbatar musu da ta gudu makaranta sosai mama tayi masifa."
Shikenan ni rayuwata ta kare a jahilci cikakken kwanaki guda asati dakyar ake barina nake zuwa makaranta idan ma zanje a makare karatun ma bana fahimtarsa bana gane masa saboda rashin mai da hankali. Taɓata akayi ta baya haƙan yasata saurin zabura tana faɗin " Amini menene haka?" " Ke kuwa ina kika shiga? Inata nemanki." Hararta Aicha tayi tace " Ai kinsan gidan mu idan nemana kikeyi ko?" " Rufamin asirin inji gidanku so kikeyi mamanki ta zaneni kin manta kashedin da tayimun kwanaki idan takara ganin kafata sai ta ƙaryata tunda ni nake zugaki." Dariya sosai Aicha tasaka tace " Kuma wallahi tsaf zata iya ba kijimunfa wani alhaji yazo yabada kudi fa yace Nadaina bara wai su baba yanzu muka fara bara." " Ohh Ashe da gaske ne daman ance angamki a motar wani alhaj ashe gaske ne kice munyi sabon masoyi." " Tabbijan gulmar yan garin nan abar tsoro kice har An sanar miki." " Kema kina wasa ai sun sanar dani tuntuni ingayamiki abun dariya har da Allah yasa ba yaudararki zaiyi ba." "Kema dai kya faɗa ta'ina wannan kyakyawan lafiyayyan dan masu kudin zai soni har da wai nayi masa sata, ke dai bari Nikaina nasan yaudarata yakeyi dan iyayen sa basu barinsa aurena." " wai ke Aicha me kika dauki kanki? Menene baki dashi da zaiki sonki? Shifa Allah babu ruwansa da wannan idan mijinki ne sai kiga ƙin auresa." " Mubar zancen kinga mun karaso makaranta banason yaudara wa zai auri jahila kiduba fa kiga aji biyar har yanzu nakasa kammala sa."
**********
A ɓangaren Alhajin da keson Aïcha kuwa zaune yake tare da yaransa yana faman hucin bakin cikin rashin samun biyan buƙatarsa gareta da baiyi ba, wanda hakan yasa shi ɗaukar alwashin sai ya ɗau fansa akan mahaifinta duk ranar da suka sake arangama, haka itama sai ya wulaƙanta rayuwarta takowace fuska, babban yaronsa ne yace, "Ya Alhaji kawai ka aikasu mana har lahira, idan ka bamu umurni akwai sauran ragowar hodar nan yanzun nan muje mu cika masu aiki." Ɗago kai Alhaji yai yana kallonsa yace, "Kesto kuje na baka wuƙa da nama kuyi duk abinda ya dace akansu, ina so gobe naji labarin mutuwar su amma kutabbatar banda yarinyar dan ina son naga rayuwarta ta lalace yanda sai tazo ta nemi taimakona da kanta, a lokacin ne zan cimma duk wani buri da nake dashi akanta"
"Sai Alhaj, kawai ka ɗauka angama dan Aicha ta riga tama zo hannunka"
Tun bayan sallar magariba da tadawo daga makarantar tasamu guri ta zauna mama dake fitowa ce tace " Sannu ƙinji sai yanzu kikaga damar shigowa gidan?." " kiyi hakuri mama bazan kuma ba." " dallah yimun shiru kitashi kibar kasan nan kamin ƙi kassara kanki nagayamiki kishige daki yau bakida abinci." murmushi tayi sannan ta miƙe tsaye dan sai data tsaya taci abincinta agidan su amini kamin tadawo. Ko data shiga daƙinsu babbar yaya na kan sallaya ƙur'ani a hannunta tana karatu dan shiriya tazo mata tun ranar data fahimci iyayen nasu amfani kawai sukeyi dasu dan tara abun duniya ba tare da sun damu da zunubi da suke kwasa ba ko kuma halin da zasu iya tsintar kansu na cuwurwutan zamani anan gaba, "Aicha ina kika shiga ke kuwa bayan kinsan halin mama, yau faɗan yamma duka akaina suka juyeshi." Dariya Aïcha tasaka tana matsowa kusa da'ita haɗe da cewa, "Wallahi makaranta naje daga nan nayi gidansu Amini bakiga lefenta ba ankawo" kallon kanwar tata tayi tana jin acikin ranta haɗe da kallon shigar jikinta kafin tace, "Yanzu Aïcha haka kika shiga cikin yan kawo lefe?" Turo baki tayi kafin tace, "kefa kikace kinsan shigar ɗamammun kaya babu kyau kuma kayana duka sune mama ke ɗunka mani".
"Nasani babu kyau Aicha amma kuma ba'a ce kayi shigar wulakanta kanki ba kinfa zama budurwa saboda Allah ai yakamata ki dinga gyara kanki, ba ina nufin ki saka ɗammmun kaya ba, a'a ki riƙa wanke waɗanda kike son kina lunkesu waje ɗaya, idan sun yafe kina kaiwa ana gyara maki ko kuma kisa allura da zare ki gyara abunki bawai kiriƙa yawo dasu bugujum bugujum ba" Kallon yayar tata tayi tace, "Uhmm to zan gyara, idan kina da Naira 100 ki bani zanje nasiyo sabulu gobe sai nayi wankin tunda bazamu fita bara ba" " kiduba jakata ki dauka kisiyo mana har macline guda daya sai wake gwangwani biyu gobe nayi mana alala".
"Yauwa babbar yaya kamar kinsan ina so sai na tayaki." Tanufi wajen jakar ta ɗauko sannan ta juya zata fita, "Aicha Aicha taji muryar mahaifinsu na kiranta." Da ɗan sauri tafito tana faɗin, "baba gani".
"Yawwa me naji kina faɗa? Gobe ba Bara?"
"Eh baba". Sandar dake hannunsa ya yiyi nasarar ƙwala mata akai haɗe da cewa, "to uwar wa zamu zauna muyi gida bayan agabanki na tattara kuɗin za'a gyara mana gida? Kinga to ki kwana da shiri ba abinda gobe zai hanamu fita bara kinji na faɗa maki" Yana gama faɗar hakan ya wuce cikin ɗaki abunsa yana jinini...
**********
Fushi sosai Aryan ya ɗauka da Afrah, tayi bashi haƙuri ta text messages har ta gaji amma yayi mata banza, kiransa kuwa tayi ba adadi shima yaƙi ɗagawa, hakan yasa ta zuba masa idanuwa duk da abun na matuƙar damunta a zuciya dan ba ƙaramin so takeyi masa ba, shima first love ɗinta tun tana ƙarama har tagirma yana nuna mata ƙauna da soyayya, wannan dalilin yasa bata ganin kowane namiji a zuciyarta idan ba shi ba, shigarta jami'a kaɗai bata saniya adadin maza da suka furta mata soyayya ba amma duka taƙi saurararsu saboda tariga ta zaɓesa sama da duk wani ɗa namiji komai kyansa, komai kuɗinsa kuma komai Asalinsa ita dai shine tauraronta.
Mutallab kuwa a tunaninsa duk abinda yafaru tsakaninta da Aryan ɗin tun ranar ya wuce saboda yasan fushin masoya hutu ne musamman Aryan dake matuƙar son Afrah, haka itama yasan yadda take son shi dole zata bashi haƙuri idan taga yayi fushi sosai, sai baibi takan abun ba tun ranar yaci gaba da al'amurransa saboda shi Aryan don ma yaƙi nuna masa akwai wani saɓani tsakaninsa da Afrah balle yace zai sa bakinsa a lamarinsu, lafiya kalau suke yaɗuwa su gaisa ko kuma suyi waya alamun ba wata matsala, idan ma akwai abunda ke damun Mutallab ɗin yanzu bai wuce halin da aduk lokacin daya je gaida mahaifin nasu yake iskoshi ciki ba, ko ba'a faɗa maka ba kasan akwai buƙatar addu'a dan tuni angama yin nasara akansa takowace fuska acikin rayuwarsa.
A ɓangaren Meenal kuwa tuni sun gama daidaita kansu tare da amincewa junansu su zama a ƙarƙashin inuwa ɗaya sai wata irin soyayya mai matuƙar burgewa suke zubawa cike da bawa juna kulawa. Wanda hakan yasa da kansa ya iske Abba ya sanar dashi zancen, kasa tantance wane irin yanayi Abba yayi na farinciki ko akasin haka lokacin daya sanar da umma zancen yaga ta nuna jin daɗinta dan ya tabbata akwai wani abun aranta da take shiryawa, koma dai meye shi burinsa baifi yaga ya faranta mata ba ya kuma yi duk abinda take so. Data sanar da ƴarta Asiya zancen itama murna tayi sosai dan tun lokacin da taga gidan dasu Mutallab ke ciki ta ɗauki alwashin sai ta koma da zama can itama kamar yadda Afrah ke zaune a can, abu daya dama take jira shigowar Meenal gidansa da mahaifiyarta ta tafaɗa mata cewa boka ya tabbatar mata da cewa Meenal ɗin itace zata zama remote control ɗinsa da zasuyi amfani da ita wajen cimma burinsu, kallon Umma tayi tace, "Wallahi Umma na matsu ayi aurensu da ita nakoma can gidan dan ɗan iskan yaron nan yafara ƙoƙarin shigo mun ɗaki".
"Wai Walid? To ai laifinki ne da kikaje kika saka maganin a ƙofar ɗalibai bayan cemaki nayi ki zuba a ƙofar ɗakinsu Mutallab, ai kinmun baƙin ciki yarinyar nan daba a dakin nasa kika zuba ba kafin su tafi, da yanzu shine ke wannan bunsurancin wallahi, gashi boka yace dama sau ɗaya zai bani maganin saboda haɗari dake ciki".
"Cab! Wai Umma da yanzu ya Mutallab ɗin ne ke wannan mugun neman mata haka da Walid keyi?"
"Eh mana to meye namu aciki? Nifa banso ma ace kwata-kwata zai yi aure ba, son nayi kawai yabi duniyar nan ya lalace, yadda yake da kuɗin nan duka su ƙare a neman mata".
"Gaskiya Umma haɗarinki yamafi na bokanki wallahi". Suka kwashe da dariya haɗe da tafewa sai kace ba uwa da ɗa ba.
A ɓangaren Jamil kuɗi sun fara taso masa tako ina kamar yadda boka ya faɗa masa, sai dai fa bayada ikon yin duk wani alkhairi da kudin ko kuma kyauta dasu dan ko Umma baiba sisi aciki gudun kada ya saɓawa sharaɗin boka daya ce yana saɓawa ɗaya daga cikin sharuɗɗansa zai karɓi hukunci dai-dai dashi.
#Mutallab Asad
#Tagwaye Biyar
#Billy s fari
#Nana Diso
SHAFI NA HAMSIN DA SHIDA.
*MUTALLAB ASAD*
Arewabook:- billysfari
Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.
A mugun tashin hankali Aryan yaƙarasa ciƙin gurin da suka samu hatsarin, " innalillahi wa inna ilaihirrajiun MAM dafatan dai bakusamu raunin komai ba? Kaga yadda hankalina ya tashi Subhanallahi yakarasa yana dan riko MAM Din. " Bamu samu raining ba aryan Allah ya takaita ga dai motar nan tanata hayaki, kai nane dai yake dan ciwo kadan." Jiyawa yayi ƙan mai taxi din yace " Bawan Allah munafatan dai komai lafiya?bakaji rauni ba? Aryan yafada yana kallonsa ciki da damuwa da kulawa." Ranka yadade babu abunda Naji wallahi Allah dai ya takaita Amma da wani zancen akeyi ba wannan ba inda Allah yataimaka mana na gangaro nan, Ni wallahi ban yarda bama Anya ba turosu akayi ba." Mutallab dake tsaye jiƙinsa babu dadi yace " A'a babu wanda ya turosu tsautsayi ne kuma Allah yatakaita mana." Nan yabawa mai taxi ɗin card dinsa da ƴan canji yasanar dashi a kira mai gyara ya duba motar idan akwai matsala yakirashi yasanar dashi. Nan mai taxi yashiga godiya gareshi. Aryan kuma ya zuba masa kayan nasa duka aciƙin bayan motar suka dauki hanya. " MAM bai kamata kana irin wannan gangancin ba da wadatarka da komai ka kama tsarar taxi saboda Allah? Yanzu da wani abun yasameka fa? Hakan ai ganganci ne Ni gaba daya hankali na atashe yake wallahi." Batare da ya ƙallesa ba duba da ƙansa da ya jinginar a jikin motar ga saramasa da yakeyi yace " zan kula gaba." Baice masa komai ba har suka shiga babban layin nasu Ganin yadda aka kammala ginin Mutallab din yasa Aryan saka karamin ihu yana faɗin " ranka yadade kaga gidanka kuwa mashaa Allah tabarakallah kasan nakwana biyu fa ban shigo nan ba." " A hankali Mutallab ya daga kansa yana kallah dan murmushi yayi haɗe da godewa Allah acikin ransa duba da wannan Ni'ima da yayi masa. Danna horn din da Aryan yayi yasa mai gadi saurin buɗe gate din suka shiga ciki. Saukar idon Aryan a manyan jeep din da ya gani da accord da kuma benz yasashi kara kallon gurin yana fadin " karkacemun duk motocinka ne? Kai Tabarakallah kace munyi mota." Mutallab ne yadan kallesa yace" kaidai baka rabo da barkwanci kamanta nagamaka suna hanya Nace akawosu nan ne kamin agaba settling na can gidan nawa." " Wallahi na manta Amma dai sunyi kyau nasamu ta aro ai." Murmushi yayi ya bude kofar kasancewa babu kowa agidan Jalil yana kasuwa itama afrah tana makaranta yasa yakarasa shiga yaran masu aikin gidan suka shigar masa da akwatunansa. Babu kowa a palour sai tante sajida tana kallo.cikin mamaki tace " A'a babban mutum wa'alaikassalam kace kana tafe? Ikon Allah kuma dazu jalil yadawo kawo wasu kayanka bai sanar dani ba." " sannu da gida Tante sannunki, ai daman Haka nace bazata zan muku ashe ma duk basa gidan? Dafatan nasameku lafiya?." " MashaaAllah Alhamdulillah barka da zuwa Alhaji Mutallab kaga yadda kakara ciki MashaaAllah girman dai ya sauka, basanan kam Afrah lecture din ta yamma ce shikuma yana can kasuwan yanata kokari." " To mashaa Allahu." Aryan bari Nashiga ciki na dan huta ma hadu anjima ko?" " Nima dai zan koma offices idan nataso zan biyu kasamu kasha ko pain killer ne MAM." " Inshaa Allahu zanyi hakan Nagode da kulawa." "Kijishi tante sajida wai godiya yaƙeyimun" "Wannan abota taku Tana burgeni nikaina wallahi Allah yasa har jikoki bari nashiga a dan hada maka abinda zakaci." " tante tuwo miyar taushe nakeso please akwai manshanu ai?" " Tohm shikenan bari nadora.
Ko da yashiga daƙin wanka yayi da ruwan zafi sosai sannan yafito yadan shiga duba wasu kayan da zasu ƙaraso nan da dan lokaci, duba da yadda email dinsa yacika nan ma yadudduba accounts din da zai gabatar da transfer suma haka yayi musu. Yana ɗan kwanciya akan gadon yaji wayarsa tafara ringing gajiyar dake tattare dashi bata bashi damar dauka ba kawai yayi addu'a ya kwanta dan idan baiyi baccin nan ba kansa zai iya tsananta saboda ciwo.
***********
Magana fa Nake tayi maka Abba wai baka isa da yaron nan bane ba? Duk inda yake aciƙin kasar nan yakamata ace yadawo, yara basuda tarbiya sun zama ƴan iskan banza da wofi aikin kawai? Taja tsaki tana karawa da faɗin Allah yasa dai ba tsafi yakeyi ba yatara uban kudin nan, jikin Abba har rawa yakeyi yace, "dan Allah hajiya kiyi hakuri zaidawo kuma zai aure yarinyar da kikace ya aura." Cikin rashin da'a da samun duniya ta daka masa tsawa tana fad'in, "kirashi yanzu yanzunnan kace yadawo duk inda yake", jikin Abba na rawa yashiga ƙiran wayar Mutallab amma akashe dan lokacin yana cikin jirgi, hakan yasa ya kalli Umma yace ," Ƙinji wayar tasama akashe take hajiya." Tsaki taƙara ja cike da takaici dan ta matsu yadawo garin nan ya auri shegiyar yarinyar can data laƙe masa tafara aiwatar da aikinta hannu shi dan ko ita ba sonta takeyi ba kawai dan malam nakan ruwa yace ta hanyarta kaɗai zasu iya samun nasarar da zasu cutar da Mutallab ɗin. Aunty Amarya da tariga tazama abun tausayi acikin gidan yanzu ce tashigo ta gaida Abba." Cikin fada yace, "Kin gata ko Hajiya? Nafaɗa mata bana don ganinta amma tilas sai yazo inda nake". Harara taimaka masa kafin tace, "Dalla rufamun baki munafiki, baka don ganinta wayace ka aurota". Bata ƙarasa magana ba yace, "Yanzunnan ma idan kika ce na saketa Allah sai na saketa, to meye amfaninta? Zaki gaida Hajiyar ne ko a'a" ya ƙare maganar yana watsawa Aunty amarya wani irin kallo ɗaya sata saurin cewa, "Ina kwana Hajiya". Tana danne wani baƙin ciki ɗaya taso mata dan ranta baiso ba, amma sanin idan batabi matar nan ba to tikitin sakinta yana gab da ziyartarta yasa take yin duk wani abu da take so saboda ƴaƴanta da ayanzu ma da take cikin gidan basu samun kulawa dan Allah ma yasa Mutallab ya taimaka mata Walid ya wuce makaranta da batasan yadda baƙinciki zaiyi da ita ba, duk da karatun ma yakasa maida hankali ƙaramin yaro dashi da yanzu shekarunsa basu wani taka kara suka kawo ba amma Shikenan baida wani aiki sai neman matan banza.
Cikin isa da taƙama Umma tace "Lafia, ina kin wanke mun kayan dana fiddo maki ki wanke Mani". Dago idonta tayi da ya cicciko da hawaye tace "A'a ban kai ga wankewa ba na dai gyara ɗakin." "To yanzu zuwa kikayi kisamu agaba kina kallo ko uban me kike zo yi?"
"Yunwa nake ji shiyasa nazo nace miki zan iya ɗora abinci yanzu?" Tana mere Baki tare da sheƙewa da dariya tace, "Wuta! Yarinya ba ke bace, kije ku dora amma ayi mani nawa daban a haɗa mani har da pepper chicken, idan kika gama sannan kizo ki gyara masa dakinsa."
"Toh" Aunty amarya tace tana barin bangaren Abban daya bita da kallo cikin rashin mafita tare da mantawa da matsayinta awajensa ya saukar dasu yana kallon TV dake aiki ajikin bango. Anty Amarya na shiga daƙinta ta rushe da kuka, tarasa gane matsayinta acikin gidan yanzu bata isa tayiwa Umma gardama ba komai tasaka ta yimata takeyi ba tare data tantance ita ɗin mata ko baiwa bace, wayarta ce tayi kara hakan yasa ta gane mahaifiyartace. Dauka tayi ta kara akan kunnenta." Ganinan fa ahanya nace miki zanzo yanzon nan." " DanAllah kada kizo wallahi zata iya sakawa asakeni mama kiyi zaman ki kawai nifa lafiya Lau muke da mijina." " bangane zata saka asakeki ba itace mai gidan ko ita ke aurenki." " Wallahi Mama tafi mai gidan ma iko da matsayi Mijina yakoma sai kace sauna ki taimaka basai kinzo ba yanzu ma tasakani girki kada tayimun fada." " Innalillahi Amarya nashiga uku menene nakeji haka?." Kashe wayar anty Amarya tayi tare da saurin barin dakin nata suwa madafa.
Meenal dake sakkowa daga sama tana faɗin Mumy shiru har yanzu bai kirani ba kuma fa yacemun suntaso," To meenala idan yasauka aikinsan da gajiya sau ya huta ko? Gashinan dai nagama miki pepper chicken da cake da samosan sai lemon aya idan baizoba ko driver sai ya kaimasa ai." Meenal ce ta bata rai tace " yanzu saboda Allah mumy Driver? Ina laifin kice ni zan kaimasa." " Meenal inaso kigane tarbiyar ki data Mutallab tabanbanta idan kinason samun kansa cikin sauki to sai fa kin aro tarbiyarsu kinyi amfani dashi dan bai kamata ace macce taje gidan su namiji ba amatsayin budurwa haka yake har yanzu kiyi hakuri idan baizo ba ko kamal zan lallaba ai sai ya kai miki ko, Meenal ta amsa da "toh" haɗe da rungume Mommy sannan ta haura sama.
Kamal ne ke tafi amota yana faman lissafin shagon da Dady ya buɗe masa Na yaduka yanzu ma yashigo jami'ar ne zai kawowa wani malaminsa wanda yasiya jiya, juyo da motar da zaiyi yaga yarinya tsaye da alama abun hawa suke jira ko wani, " kai kamar nasan fuskar nan". Yafaɗa Yana sauke window dinsa kasancewar ya saka bakin abun nan babu mai ganin wanda yake ciki. "Sannu ƙannena" Yafada yana yi masu magana ganin ba ita kaɗai nace a tsaye, juyowa Afrah tayi ta kallesa ta ɗauke idonta dan bata sanshi ba, infact batama taɓa ganinsa ba sai yau, Hanan dake gefenta ce tace, "Afrah dake fa yake ." "Kamar ya? Na sanshi ne da zakice dani yake?." Dariya Kamal yayi yace, "Idan baki Sanni ba Ni nasanki tunda kamanninsu basu ɓoyeki daga zamowa ƙanwar Alhaji Mutallab ba da ankalleki". Da mamaki ta dago ta kallesa, koda yake ba abun mamaki bane duk wanda yasan yayan nata zai iya cewa ita ɗin ƙanwarsa ce saboda kamar da sukeyi, ɗan taɓa baki tayi ganin irin kallon da yakeyi mata yana murmushi haɗe da cewa, "Naji bawan Allah amma dai lafiya ko?" "Mau ma kuwa, nace ko zaku shigo na saukeku gida?"
Daidai lokacin motar Aryan daya zo ɗaukarsu tashawo kwana, gabansa ne yai wani irin faɗuwa kafin ya ƙaraso hango Afrah na magana na cewa, "Munce maka muna bukatar kakaimu ne." Cikin zolaya da wasa irin nasa yace, "haba yar fara kyakyawar ƙanwata!" dai-dai lokacin motar Aryan daya ƙaraso wajen yai parking kalmar ta dira cikin kunnensa ransa yayi mugun ɓaci, cikin dakawar tsawa yace "Ke Afrah?." Wata irin zabura tai haɗe da barin wajen ba tare data sake cewa komai ta karasa motarsa suka shiga, ko gama zama batayi ba yafara faɗa yana faɗin, "ke ba kida hankali ne? wannan wane kalar hauka ne da rashin tarbiya zaki tsaya da irin wannan shashashan yaro, dama abinda kike amakarantar kenan kina cin amanata ban sani ba?" Da mugun mamakin kalmomin daya gayamata ta ɗari tana kallonsa, Hanan ce tace "kayi hakuri shine fa ya taddamu wajen ba wai tana kulasa bane tunda bata sanshi ba." "Dole ki kareta tunda baƙinku daya ai, rashin tarbiya take koya yanzu ko kuma daman can da wanda takeso a ranta yaudara ta takeyi" Sautin kukan Afrah ne yacika motar har suka sauke Hanan suka karaso kofar gida tana faman kuka sosai, tana buɗe kofar zata fita taji yace, "Ina fatan baki bari Kamal din ya lallata maki rayuwa ba dan kowa yasan shahararren dan iska ne..." A hankali ta maimaita furta, "lallatawa kuma? Aryan zargina zaka farayi?" Kawai sai ta sake fashewa da kuka ta shige cikin gida aguje, yasan Aryan nda matsanancin kishi amma ko kaɗan bata taɓa sa ran zai zargeta ba atatashi ɗaya akan abinda baida tabbaci dan ɗai ya ganta da wani tsaye". bata shiga ta dakinta ba sai ta zagaya ta dakin tante sajida tana zaune tana linke kaya ta faɗa ajikinta,
"Subhanallahi lafiya Afrah me yafaru?" "Tante na shiga uku"
"Allah ya rabaki da shiga uku Afrah fadamun ke da waye?"
"Aryan ne tante.." sai kuma ta kas ƙarasawa tana kuka, "Afrah kuyimun magana kin tayar mun da hankali, Aryan ne yai maku me?" Tafaɗa tana ɗagota daga jikinta haɗe da shareta mata ƙwalla, sai data tsagaita kukan sannan ta labarta mata abinda yafaru, ajiyar zuciya tánte ta sauke haɗe da cewa, "Bai kyauta ba amma kuma kiyi masa uzuri kinsan sun fimu kishi, ba abinda ya janyo haka sai ɓaci ran ganinki da wani da yai a tsaye, amma nasan shima daga baya zai yi tunanin bai kyauta maki ba ya baki haƙuri, a lokacin ke kuma kiyi ƙoƙari kiyi masa bayani yadd zai fahimta Dan gujewa sake faruwar hakan kinji?".
"To tánte amma i Yakamata ya yi tunani yasan me zai faɗa kafin ya faɗa mani". Dariya tánte tayi haɗe da cewa, "Ai wannan kishin bazai barshi ya tsaya yai wannan tunanin ba, ni ai hankalina ma tashi yai da kika ce Aryan ne nace bai fa daɗi da fita gidannan ba ya ɗauko yayanki ɗaya dawo". Wato idanuwa Afrah tayi atake ɓaci ran da take ciki na ɓacewa haɗe da maye gurbinsa da ƙayataccen Murmushinta tana cewa, "Tánte wai ya Mutallab kike nufi? Yau she ya iso shine baki kirani kika faɗa mun ba?" Tamiƙe cike da farinciki tabar ɗakin ba tare data jira amsar da tánte ke shirin bata ba ta nufi stairs ɗin inda ɗakin Mutallab ɗin yake asama.
#Mutallab Asad
#Tagwaye Biyar
#Billy s fari
#Nana Diso
SHAFI NA HAMSIN DA BAKWAI.
*MUTALLAB ASAD*
Arewabook:- billysfari
Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.
Tana hawan step na uku shima yafito yana saukowa cikin shigar wando three-quarter da riga armless sai glowing murɗaɗɗen jikinsa keyi aciki, da gudu ta rugo tayi hugging ɗinsa tana cewa, "What a beautiful surprised Yaya! You're welcome home shine baka faɗa mana ba muyi maka kyakkyawar tarba ko?" Murmushi ya sakar mata ya riƙo hannunta sukaci gaba da saukowa yana cewa, "Bakiji me kika faɗa ba Afrah? Ai ba'a faɗar surprised ya studies?"
"Alhamdulillah Yaya gashi nan munata shirin bankwana dashi a huta".
"Allah ya taimaka daga nan sai batun aure ko aura". Yaƙare zancen daidai shigowar su dakin tánte da yazo su ƙara gaisawa". Shiru Afrah tayi haɗe da turo baki Mutallab ya kalleta yace, "Kinyi shiru auta? Kin dai an Aryan yai haƙuri sosai ko? To wannan karon ina sha Allah bazai cigaba da zaman jiraba, kina kammala karatun nan zance ya sake zuwa wajen Abba suyi duk abinda yakamata asa rana ayi bukinnan a huta". Sake da baki Mutallab ke kallonta ganin hawaye akan fuskarta tare da juyowa ya kalli tánte yace, "Kinga halin auta na shagwaɓa ko tánte? Daga wannan ɗan zancen sai kuka?"
"To ai laifinka ne tunda kai ka shagwaɓata haka, amma dai inaga ba wannan zancen ya sakata kuka ba shiri take so ka haɗasu da Aryan ɗin dan yanzu take sanar dani sun samu matsala.." nan tánte ta zayyana masa abinda yafaru kamar yadda Afrah ɗin tafaɗa mata, yaji haushi sosai duk data
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 33 Chapter of 54