ƙara dake alamta saukar mari daidai lokacin da hankalinsa ya gama daidaituwa a gangar jikinsa, juyowar da zaiyi yaga drivern napep ɗin baya ciki yana ɗago kansa yayi tozali da kyakkyawar fuskar tata dake a fusace riƙe da wuyan rigar mai napep ɗin tana zuba masa balbalin bala'i, lumshe idanuwansa yay haɗe da buɗesu lokaci ɗaya ya saukesu akanta, ga dukkan alama itace cikin mintunan da basu wuce uku ba da faruwar abun tafito ta ɗauke mai napep ɗin da mari, sai dai koma meye bata kyauta ba tunda baida laifi ƙaddara ce kuma Allah ya tsare ba abunda ya faru.
Duk masifar nan da takeyi bai fito ba fuskarsa na akan tata fuskar da kallo ɗaya ta fizgesa, baiyi yunƙurin fitowa ba har sai da yaga ta tura mai napep ɗin da ƙarfi ya bugi napep ɗinsa ta baya ya dawo gaba yana ƙoƙarin faɗuwa da sauri yafito ya taresa, ita kuwa tuni cikin rashi damuwar abinda zai iya samun mai napep ɗin data ture ta juya ta nufi wajen Motarta, da kallo Mutallab yabi bayanta yana ƙureta da idanuwa, saye take cikin wasu matsattsin kaya riga da wando da suka ɗameta tun daga samanta har ƙasa, gaba ɗaya surorin jikinta babu inda bai bayyana ba lungu da kuma saƙo musamman mazaunanta da wandon ya bala'in kama, dan zaka ɗauka da tayi motsi kaɗan zai iya yagewa saboda yanda yake ɗame da fatar jikintatana wani ɗan iskan taki hade sai da murzasu suna marin juna, yayin da ƙafafuwanta ke saye cikin wasu takalma masu mugun tsini sai kanta daya sha attach ta yafo ɗan yalolon mayafi akai, atake Mutallab yaji jikinsa ya amsa saboda yadda take motsa jikin nata duk wani mai cikakkiyar lafiya sai yaji wani abun da sauri ya ɗauke idanuwansa daga kanta yana ta'awazi saboda munin shigar tata da idanuwansa suka gama gno masa komai, ɗan tsaki yaja dan a duniya ba bunda ya tsana kamar yaga mace na bayyanar da surar jikinta haka, koda kuwa da kalar ɗunkunan hausawanmu ne da ake matse jiki balle kuma irin waɗannan kayan da kai tsaye zai iya kiransu na yahudawa, dan kallo guda zakayi mata kace ita ɗin ba ƴar musulmai bace saboda munin shigar. Dan da ƙaunar shi ce ita tayi wannan shigar yau ba abinda zai hana ya ɓaɓɓallata.
Meenal da batasan ma me yakeyi ba tana kaiwa bakin motarta bayan ta buɗe ta juyo tana nuno mai napep ɗin da hannu, cike da gargaɗi take cewa, "Next time idan ka koma gigin shiga gabana takaka zanyi kawai in wuce, yadda idan akace ka sake hawan titi any how tunda ba irin na ƙauyenku bane da jakuna kaɗai ke hawa baza kayi hakan ba, baƙauyen banza da wofi". Taƙare zancen tare da zura ƙafarta cikin motar ta shige ta tayar taja tabar wajen ranta a ɓace, haƙuri Mutallab da haushin abinda Meenal ɗin tayi ya gama cikasa ya shiga ba mai napep ɗin tare da taimaka masa ya shiga ciki ya tayar sukabar wajen kafin mutanen da suka zagayesu suma su shiga watsewa da ɗaɗɗaya da ɗaɗɗaya.
**********
Meenal kuwa da dama da ɓacin rai tafito gida dan kwana biyu ranta dagule yake akan abinda AAB yayi mata, tadena fita ko nan da can saboda yanda ta tsorata da abinda AAB ɗin yayi mata sai take ganin idan tafita ɗin zai iya bibiyarta ya sake ƙoƙarin aikata mata abinda yayi niya, bata taɓa tsammanin Bestie ɗin nata tataccen ɗan iska bane sai daya yimata wannan abin, sosai ta goge duk wani abu daya shafeshi a rayuwarta ta kuma ji ta tsanesa tsana mai tsanani, Dadynta na hankalce da sauyawar tata yayi tambayar duniya har ya gaji tafaɗa masa meke damunta amma taƙi, sai ya ta'allaka hakan da dawowar Mommy data je ya ɗauko saboda takurata ɗin da takeyi, but Alhamdulillah ya lura ma tunda Mommyn ta dawo tafita duk wata harkar Meenal ɗin tare da zuba mata idanuwa.
Yau ma tafito ne saboda kiran da Kamal yayi mata taje ta ɗaukosa airport yayi masu saukar bazata, shine fa tafito dan batayi niyar fitowar ba tana wannan uban saurin saboda tun ɗazu ya takurata da kira sai gashi sun haɗu da wannan tsautsayin, ko data iso airport ɗin ta hango Kamal jaye da trollybag ɗinsa yana ƙoƙarin tare taxi tayo cikinsa da motar, wani irin tsalle yay ya koma gefe, a fusace yay kan motar gani ta tsaya sai yaga Meenal tafito daga ciki tana dariya, ihu ya saki tare da sakin trolly ɗin ya buɗe mata hannuwa, da gudu ta ƙaraso ta shige ya ɗagata yana juyi da ita dukkansu suna dariya cike da farincikin ganin juna. "Wow Meeneluwa! Kece kika ƙara girma haka?" Ya Kamal ɗin yafaɗa bayan ya sauketa yana jujjuyata a gabansa". Duka takai masa a ƙirji tare da maka masa harara tana cewa, "dole kafaɗi hakan tunda ka tafi ka manta dani".
"No Meenaluwa, taya zan manta da my one and only sister? Common zo muje i hv alot of things for you dana yimaki tsaraba, but joke aside faɗa mun me kike ci kika girma haka? me Momcy take baki ne kina ci kika manta dani?" Ya ƙare zancen yana janyota a jikinsa yana sake ƙare mata kallo, cuno baki tayi irin na shagwaɓaɓɓin yarannan haɗe da cewa, "Don Allah ya Kamal kadena yimini zancen wannan matar, Allah bana so na tsaneta serious".
Hannunta kawai yaja ba tare da yace uffan ba dan yasan irin drama ɗin dake tsakaninsu suka nufi wajen motar suka shiga, shiya karɓi tuƙin motar haɗe da tayarwa sannan ya ja sukabar wajen.
**********
A ɓangaren Mutallab kuwa tafe suke bini-bini ya ja tsaki idan yatuna da yanayin shigar da yaga Meenal aciki, musamman da ƙwaƙwalwarsa takasa shafe masa hoton fuskarta data ɗaukar masa acikin idanuwansa, yayi tsaki yafi a ƙirga kafin suka ƙaraso ya ciro kuɗin mai napep ɗin ya biyashi yana sake bashi haƙuri akan abinda ya faru kai ka ɗauka ma shi yay laifin. kayan gwanjonsa ya karnɓa wajen yawale mai shayi sannan ya gangara gida dan ya manta akwai wasu ƙulli daya je dasu yabarsu a dakinsa, hakan yasa ya yayanke shawarar ƙarasowa ya ɗauka Sannan yawuce.
Sai dai yana shiga gidan nasu daya nufi bangarensu yaji gabansa ya daɗi ganin ɗakinsa kamar a buɗe, da saurin taƙarasa wajen ya tabbatar da abinda idanuwansa suka gane masa gaskiya ne yaƙarasa tura ƙofar daƙin yashiga bakinsa ɗauke da sallama duk da yasan babu kowa aciki da zai amsa masa, sai dai ga mamakinsa yana shiga yayi tozali da bankin da yake tariyar kuɗinsa aciki a tsakiyar ɗakin an fashe an kwashe duka kuɗin dake ciki, jikinsa na rawa yaƙarasa wajen ya ɗauki bankin yana jujjuyawa hankalinsa na sake tashi ganin babu komai aciki, don aƙalla yana ƙidaya kuɗin daya zuba aciki sun kusa kai dubu ɗari uku, "Innalillahi wa inna ilaihirrajiun" shine abinda ya iya faɗa tare da ficewa daga cikin ɗakin jikinsa na rawa, daidai lokacin Umma data yiwa ƙawarta rakiya suna tsaye a harabar gidan ke cewa, "Karki damu ƙawata wuɗannan kuɗin soman taɓi ne nabaki dan aikin da kikayi mani yafi ƙarfinsu, kiyi maleji dan daƙyar ma wuɗannan na samesu saboda Alhaji yace baida kuɗi a hannu, ke kuma kince cash kike so amma yayi mani alƙawari idan yadawo gida yau zai bani wasu tunda cash nace masa ina so".
Ruɗewa Mutallab yay yarasa ina zai nufa ma saboda tashin hankali, baba mai gadi ne dake tsaye yace, "Babban mutum ashe kadawo? In jin dai Lafiya ko naganka a haka?" Idonsa ne da sukcicciko da kwallah ya ɗago yana kallonsa cikin karyewar murya yace "Akwai damuwa Baba, dan Allah waye kaga ya buɗe mani daki ya shiga? Abu na ajiye yanzu na dawo ban ganshi ba". Cike da tsoro Baba mai gadi har yana cin tuntuɓe a maganarsa yace, "A..a..abu Babban mutum? Innalillahi wa'inna illahir raji'un mun shiga uku, to bana ce ga mutum ɗaya da shikaɗai ya shiga ɗakin ba, amma tabbas naga Alhaji bayan fitarka tsaye abakin kofar yazo nemanka, sai Jalil shima naga ya yafito daga cikin ɗakin sannan sai Alhaji Jamil daya zo nemanka shima har yana tambayata yaushe zaka dawo yana son magana dakai".
Juyawa kawai Mutallab yay yakoma cikin ɗakin ya rufo kofar tare da jingina awa ajikinta ya fashe da wani kukan baƙin ciki yana mamakin yadda aka buɗe bankin aka kwashe masa kuɗi kasancewar irin babban bankin nan ne masu ƙwari! Yadda yake jin zuciyarsa na yimasa wani irin luhude sai kayi tunanin zuciyarsa fitowa ne zatayi saboda tsananin tashin hankali, shi kaɗai yasan me yayi going through kafin ya haɗa kuɗaɗen da yake da babban buri akansu, yanzu ta ina zai soma sake tariyar wasu kuɗin bayan waɗannan daya matuƙar shan wahalar tarawa, wanene yayi masa wannan aikin yasan ɗaya kwashe watanni nawa yana tarawa dan rafuwa kansa asiri? Cikin sanyin murya yace, "Allah kafini sanin dalilin faruwar haka agareni, Allah namiƙa maka dukkanin lamurrana kasamar min mafitar da tafi wannan". yafaɗa yana goge hawayen fuskarsa sannan ya ɗakko wayarsa yana neman lambar Jalil da niyar kiransa ya tambayesa duk da yasan ƙanin nasa bazai taɓa aikata masa hakan ba tunda ba halinsa bane, maida wayar yayi ya jiye yafasa kiran nasa ya samu katifarsa kawai ya kwanta zuciyarsa na masa wani irin zafi da kuma raɗaɗi yana rufe idanuwansa tamkar mai shirin yin bacci, Ƙarar da wayarsa tafarayi yasashi buɗe idanuwan tare da janyo wayar ya ɗaga ya kara aƙunnensa ganin sunan Aryan ajiki.
"Hello Aryan?" Mutallab yafada cikin mutuwar jiki ta ɗaya ɓangaren Aryan yace, "Hello MAM ya kake? Ina ka shigene kira har kusan sau uku baka ɗaya ba? Hope lafiya dai ko?" Sai da Mutallab yaja numfashi sannan yace "Lafiya amma ba lau ba Aryan, Ina cikin damuwa da tashin hankali yanzu haka wlh!"
A ɗan razane Aryan dake zaune a office ɗin da yamiƙe tsaye yana cewa, "Ban gane ba MAM! Yimun bayani yanda zan fahimta wani abu yafaru dakai ne? Oh my God ka kirani kasuwar ganina zuwa na daukeka don hankalina ya tashi".
"A'a Aryan bana kasuwa ina gida, calm down ba abunda ya shafi lafiya bane". Wata ajiyar zuciya Aryan yay yana furta kalmar alhamdulillah haɗe da koma saman kujerarsa ya zauna, wannan na ɗaya daga cikin abubuwan da yasa Mutallab kejin ƙauna da kuma soyayyar Aryan cikin jinin jikinsa saboda yanda yake damuwa da damuwarsa kowace irice, can yaji saukar sautin muryarsa yana cewa, "MAM kiranka nayi na gayamaka cewa akwai abokinmu daya shiryamana cin abincin dare ka shirya zanzo na ɗaukeka idan anyi sallar magrib! Wllh bansan da faruwar komai atare dakai ba, faɗa mun damuwarka kasan problems share is a problem solve".
#Mutallab Asad
#Ƴan Tagwaye
#Billy S Fari
#Nana Diso.
SHAFI NA ASHIRIN DA UKU.
*MUTALLAB ASAD*
Arewabook:- billysfari
Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.
*MUTALLAB ASAD*
*PAID BOOK #500*
*TAGWAYE BIYAR.*
NA
*NANA DISO**
&
*BILLY S FARI*
____Darasi Na biyu____
* KANKANA TANA DAGA CIƘIN ABURDA KE SAUKAR DA NI'IMA AJIKINKI.*
* DABINO YANADA TASIRI SOSAI AJIKIN MACCE.*
*KUNGA WANNAN KIRFA DIN DAKUKE RAINAWA MAGANIN MATACE SADIDAN.*
*KANINFARI KAM BA'A MAGANAR AMFANINSA AJIƘINMU.*
*KIMBA MAGANIN SANYI CE SADIDAN KO SHAYI ZAKUYI KUNA JEFATA KO KUNU KO ZOBO KOKUMA DAHUWAR FARFESU MU NAN HAR DAKA YAJI MUKAN SAKANTA.*
*WANNAN SHINE RAIHAN DA LARABCI DA HAUSA KUMA DADDOYA DA TURANCI SCENT LEAF YANA GYARA MACCE SOSAI DAN MAGANIN MATANE SHIMA SADIDAN KO FARFESU KO SALAD ANA JEFASHI.*
_____
Kasancewar tun kafin ya kwanta yake jin jikinsa baɗi saboda wani irin yanayin da yake jinsa aciki da rabon da yaji hakan an kwana biyu, kasancewarsa cikakken ɗa Namijin a yanzu da dukkanin halittarsa ta gama bayyana a yanzu yasa yafara fuskantar wasu baƙin al'amurra tattare dashi batare daya fahimci dalilin hakan ba, cikin dakiya da son jurewa yanayin da yake jin kansa aciki ya nemi waje ya kwanta bakinsa ɗauke da addu'o'i, wani irin wahalallen bacci yayi a daren dake cike da tarin mafarkan da suka bashi cikakkar amsar bayyanar baƙin abubuwa agaresa, da asuba ko daya tashi jikin nasa ya saki sosai, dafe kansa yayi yana jin kunyar kansa da kansa lokacin daya tuna yanayin daya tsinci kansa cikin baccinsa a daren jiya, ƙarfin hali yayi ya miƙe ya nufi toilet yafara yin wanka tare da ɗauro alwala sannan yanufi masallaci, kasa sakewa yayi ganin kamar mutane suna fahimtar yanayin da yake ciki dan haka ya miƙe ya fice daga masallacin ya nufi gida, sai daya nufi wajen kayansa da suka wanke jiya ya ninkesu sannan ya nufi ɗakinsa ɗauke, yana koƙarin shigewa yaji muryar Abbansu yana faɗin. "Kai Mutallab ina kashiga ne yau?" Kayansa ya gyarawa zama kafin cike da tsoron yadda mahaifin nasa yakira sunansa ya ɗago kai yana kallonsa dan bai saba kiransa hakan ba. "Ba dakai nake ba". Abba ya sake faɗa yana nufowa inda yake, sai da Mutallab yayi ƙasa da kansa sannan cikin girmamawa yace, "Barka da asuba Abba".
"Barka, baka ji me nake cewa ba?"
"Ina kasuwa Abba".
"Kasuwa kuma? Me kake yi acan?" Abba yafaɗa yana tsaresa da idanuwa, ɗan sosai kai Mutallab yay kafin yace,
"Ina zuwa wajen aiki ne". Jim Abba yayi kafin yace, "Aiki kuma? Yaushe ka samu aiki acan kuma tukuna farin ma wace kasuwarce ka samu aiki?" Ya jefa masa tambayoyin ajajjere yana cigaba da tsaresa da idanuwa, ba tare da Mutallab yaji ko ɗar ba acikin zuciyarsa akan abinda zai faɗa ba yace, "A kasuwar singa nake zuwa nakwana biyu da fara zuwa can ganin zaman haka baida amfani, ina yin dako kuma ina kasa kayan gwanjo ina saidawa, yanzu haka ma har wajen koyan ɗinki ina zuwa duka". Wani iri Abba yaji aransa amma sai yakasa cewa komai, kamar bazai yi magana ba dan har ya juya da zimmar barin wajen sai kuma ya juyo yace, "Akan yafi zaman banzan da kakeyi ai, Allah yabada sa'a, yanzu wuce muje kagyaramin dakina a gabana tunda baka da hankalin da zakace bari kazo ka gyaramin ƙazanta tako ina na nema tayi mani illa tunda su iyayen naka basa da hankalin gyarawa ni kuma bana buƙatar ƴan aiki su shigar mani ɗaki". Yana gama maganar ya juya yabar wajen, da mamaki Mutallab ya bishi da kallo, shi daya ce kada ko cikin gidansa inda iyalinsa ya koma shiga to me zai sa yabuƙacesa tashiga yagyara masa ɗaki? Bai da amsar wannan tambayar tunda tuni Abba yabar wajen dan haka sai kawai yabisa a baya har suka shiga cikin gidan suka nufi ɓangarensa, ko da suka shiga Aunty Amarya tana zaune kasancewar girkinta ne. Kallo ɗaya tayiwa Mutallab ta ɗauke kai haɗe da cewa, "Alhaji me kuma yaron nan zaiyi a ɗakin nan? Saboda Allah so kakeyi a maimaita abinda ya faru?". Cike da takaici Abba ke kallonta kafin yace, "Agabana za'a maimaita abinda yafaru ɗin bayan gani a tsaye? Ko so kikeyi na zauna da ƙazanta a ɗakina? Ko kuma ƴan aikin da kuka saba suyi muku bauta zakije kituromin su gyaroamin? Dake da ita ɗin tun yaushe nace ku gyaramin kuka ƙi?". Shiru tayi batace komai ba har Mutallab ya gama gyaramasa ya wanke banɗakin tare da gadonsa ya feshe masa ko ina da room freshnass masu ƙamshi sanna yay masa sallama yafita,
Mere baki Aunty Amarya tayi cike da baƙinciki kafin tace, "Wai Alhaji meyasa bazaka saka Jiddah tayi maka wannan aikin ba sai yaron nan, da wani iyayinsa sai kace macce?"
"To kin dai gani matan ma bakowacce zata iya gyaramaka guri kamar haka ba?" Abba yabata amsar da sarai tasan da'ita yake sai kawai taja bakinta tayi shiru. Don akan ƙazanta shikam zai ya sabawa macce duk don da yakeyi mata, gashi dukansu sai dai su gyara jikinsu da wajen zamansu amma nasa sam baida darajar da zasu gyara masa shi idan ma sunyi ba zai yi yanda yake so ba, wannan dalilin yasa ya ɗaurawa Mutallab wannan nauyin sanin mahaifiyarsu ta koyar dasu duka ire-iren waɗannan abubuwan shiyasa yake matuƙar sonta ya kuma zaɓeta haɗe da fifitata acikinsu.
A gefen Mutallab kuwa yana ƙarasawa dakinsa yay saurin faɗawa bandaƙi yay wankansa mai kyau ya wanke ko ina lungu da saƙo dake jikinsa haɗe dayin brush sannan yafito yana goge jikinsa, yana kammalawa kiran Aryan ya shigo a wayarsa, gefen katifar tasa ya samu ya zauna sannan ya miƙa hannu ya ɗauko wayar haɗe da ɗagawa ya kara a kunne.
"Hello MAM gani ƙofar gida". yaji Aryan yafaɗa a ta ɗaya can gefen kuma yana jin muryar mai gadi da suke gaisawa dashi, ɗan lumshe idanuwansa yayi saboda har lokacin jin jikinsa yakeyi tamkar ba nashi ba duba da sabon yanayin daya tsinci kansa aciki wanda lokaci zuwa lokaci idan yatuna sai yaji tsigar jikinsa na zuba haɗe da mimmiƙe masa, abunka da hakan bata taɓa faruwa akansa ba, cikin sanyin murya yace,
"Amm to kashigo ciki mana, yanzu nafito wanka ina kan shiryawa".
"Ok" Aryan ya bashi amsa tare da kashe motarsa yafito yanufi cikin gidan, sashen da ɗakin Mutallab ɗin yake ya nufa yayi knocking ƙofar Mutallab ya bashi izinin shiga sannan ya tura ƙofar ya shige.
Hannu ya miƙawa Mutallab da har ya saka kayansa da yake zuwa kasuwa dasu suka gaisa yana zolayarsa cikin sigar tsokana yake cewa, "Ho MAM ɗan basaja da ɓadda kama, wai kodai nazo mu jone ne?" Murmushi Mutallab yayi haɗe da cewa, "Allah ya tsari gatari da saran shuka Aryan, ai kai kayi gaba tunda Allah yasa kana da aikin yi, ko bayan haka ina kai ina aikin dako? ai bazaka iyaba dan ranar dana fara kamar na mutu nake gayamaka, gaskiya na yarda akwai maza akwai muna maza dan aikin nan sai namiji mai ƙarfin hali, da yake yanzu nafara sabawa sai nake jin jikina ma yafi yimani bakaga daɗi a haka".
Yafaɗa yana dauƙar alimun(Alim) dake ajiye kan wani ƙaramin table ɗin katako dake ajiye gefen katifar yana shafawa ƙasan hammatarsa sabida gudun warin daya ji wasu takwaroran aikin nasu nayi idan suna baki aiki, hakan yasa yake yiwa kansa garkuwa da kasancewa daya daga cikinsu duba da mutane na cutuwa da irin wannan lalurar da wasu ke fama da ita saboda rashin kula ace dole sai an samu shuwa za'a iya kula da wajen, Aryan kuwa dariya ya kasa yana kallon abinda yakeyi kafin yace, "Kaima fa rigima ce kawai MAM amma ka duk san aikin dako ba naka bane, ai kuwa dole kaji kamar ka mutu saboda yafi ƙarfinka aikin, duba wani abu dan Allah MAM wai Alim kake using dashi, ina sure ne ko duk aikin basaja ɗinne?"
"Hohoho Aryan! Abunda kake dashi ai shi kake using dashi, buƙatar hajji dai sallah sure da Alim ɗin ai naga duk warin Suke dauƙewa ko? ya ake ciki?" Ya sake jeho masa wata tambayar cike dason kauda zancen Aryan ya amasa da,
"Lafiya klw, ina Afrah?". Sai da Mutallab yayi masa wani kallo cike da tuhumarsa kafin yace, "Wai nikam Aryan meyasa kake raba ɗaya biyu? Na lura sau dubu idan zamu haɗu ko muyi waya sai ka tambayi Afrah amma bazaka tambayi ƴar uwarta ba Jiddah, ko mantawa kakeyi itama fa ƙanwata ce".
Dariya Aryan yayi haɗe da cewa, "To masu ƙamari Allah ya baka haƙuri ni ba wannan na tambayeki ba, amma kuma idan kaga kare yana shinshinar takalmi ai yana so ya ɗauka ne ko?". Ɗan zaro idanuwa Mutallab yayi haɗe da cewa, "Kamar ya kenan!"
"Kaifa matsalata dakai kenan wani lokacin baka gane abinda ake nufi, Allah da gaske nake son Afrah nakeyi dan jiya daƙyar nasamu tunaninta yabarni runtsawa". Mutallab dake ɗaukar zancen nasa a wasa yana ƙoƙarin janyo bankinsa da yake ajiye kuɗinsa aciki yace, "Haba dai! To kafaɗa mata mana". Yayi maganar cikin rashin nuna damuwa akan zancen, murmushi Aryan ya saki Yana cewa
"No ba yanzu ba MAM sai ta kammala karatunta tukunna". Jin da gaske abokin nasa keyi yasa ya juyo yana kallonsa yace, "Wai da gaske kakeyi Aryan, Afrah fa? She's just a small girl bai kamata ace ka tsaya Bata lokanka wajenjiranta ba, I thought bama zaka wuce shekarar nan bakayi aure ba tunda kasamu aikin da zaka iya riƙe iyali, bayan haka ma.." saurin dakatar dashi Aryan yayi haɗe da cewa, "Hold on please, ya kake wannan zancen kasan shekaru nawa zuciyata tayi tana dakon santa? Ina ruwan soyayya da small girl ni kawai nagani kuma ina so sai in baza'a bani ba".
Aryan ya faɗa cikin ɗan ɓacin rai haɗe da ɗauke kansa gefe, murmushi Mutallab ya saki dan shi har cikin zuciyarsa yaji daɗin wannan maganar da Aryan yazo da ita, yasan kowaye Aryan matuƙar Afrah ta aureshi to tabbas zatayi farinciki sosai, dafashi Mutallab yayi haɗe da cewa, "Easy Aryan! Kaima fa Afrah ƙanwarka ce zaka iya kawo mata wani kace ta aura kuma nagoya maka baya balle kuma kai da kanka kake sonta ai dole na tayaka wannan faɗan, ubangiji Allah ya tabbatar mana da alkhairi, sai dai fa girma zai faɗi kana babban wa kadawo ɗan ƙwairo awajen ƙanwarka". Yaƙare maganar cike da zolayarsa yana dariya, juyowa Arayan yay yaɗan hararesa haɗe da sauke ajiyar zuciya yana cewa, "Ba komai indai ta amshi ƙoƙon barana babban yaya". Shima yarama zolayar daya yimasa duk sukasa dariya, da haka Mutallab ya gama ƙirge kuɗinsa daya shigo dasu jiya yasaka cikin bankin da yake ajiyewa daya ɗauko sannan ya mayar yana cewa Aryan ya tashi su tafi Afrah kuma lafiya kalau ta tashi.
Sai da yabiya ɗakin Jalil da fitowarsa kenan shima ya shirya zai fita yana ƙoƙarin zuwa ya gaida Mutallab ɗin, cikin girmamawa ya gaishesu kafin su duka su fice atare, kai tsaye Jalil ya miƙi titi shi kuma Mutallab suka shiga mota dan Aryan yace tabari ya ɗaukesa kasuwar, ganin har lokacin da suka ƙaraso bakin titin Jalil bai samu abun hawa ba yasa suna kawowa Aryan ya tsaya haɗe da leƙowa ta glass ɗin ya tambayesa inda zai je, jin da yay akan hanyar da zasu wuce ne yasa yace ya shigo sai su saukesa su wuce, ba musu Jalil ya shiga saboda ganin ya samu sauƙin biyan kuɗin abun hawa sannan Aryan yaja motar suka wuce suna tafe suna ɗan taɓa fira har suka ƙarasa inda Jalil zai sauka shagon abokinsa dake printing yana riƙa masa, duk da yanzu ma bai fiye zama ba saboda ya koma school sai ranakun da basuda lectures, bayan sun ajiyesa ne suka ƙarasa kasuwa ya ajiye Mutallab sannan ya wuce office.
Yanayin kallon da Mutallab yaga yaran Alhaji Tanimu na yimasa da yanda suka gaisa dasu ya matuƙar bashi mamaki dan ba haka suka saba gaisawa dasu ba, hakan yasa ya ɗan sha jinin jikinsa saboda baisan meke faruwa ba na masifar da Alhaji Tanimu ya gamayi a shagon yanzu akan bazai iya cigaba da zama dashi ba zai sallamesa dan hankalinsa bai kwanta daci gaba da zaman dashi ba yanzu. Gefen shagon ya samu waje ya zauna kamar yadda ya sabayi akoda yaushe kafin ya samu aikin da zaiyi, sai dai ko minti biyar baiyi da zaman ba ya gunduresa don haka yamiƙe ya shiga cikin kasuwar yafara ƴan buga bugar ɗaukar kayan da yakeyi daga shago zuwa wani shagon ko daga shago zuwa cikin mota, bai dawo ba har aka kusa sallar azahar dan sha biyu har da rabi ya nemi wajen wata mai abinci ya saya yaci, yana gamawa wayarsa tahau ƙara yaciro yana kallon wanda ke kiran nasa, Idris ne dan haka yayi saurin ɗagawa, "Hello Mutallab kana ina ne?" Yaji Idris ya jeho masa tambayar hankalinsa a ɗan tashe, yace "ina nan cikin kasuwa mana ka shigo ne?"
"Eh tun da safe naje wani aikine gani ma nadawo shagon yanzu na isko Alhaji yanata faɗa wai customers sun zo sunyi sayayya an nemeka sama da ƙasa kaɗaukar masu kaya ka kai masu a mota an rasa".
"To Idris nazo naga daga Alhajin har yaransa wani kallo sukeyi mini da bansan kona meye ba, naso na zauna amma sai naga bari na ɗan zazzagaya na samu wani aikin kafin ayi sallar azahar, yanzu haka ka gani nan zaune wajen matar nan mai abinci dana siya na gama ci, in Sha Allah yanzu shagon nayo".
"Shikenan to kayi sauri ka ƙara so". Idris yafaɗa yana kashe wayar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 54