Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Batare daya faɗa masa gaskiyar abinda yasa yaje ɗin ba. Murmushi Abba yai haɗe da cewa, "Dama nasan ai bazaka ƙi yarinyar ba mutallab, ɗan haka kayi kokari ku gama daidaitawa duk abinda ya dace kayi ka gama tunda Allah yasa kana da arziƙinka ba sai na tallafa maka da komai ba yanzu dai kaga girma ya kamani kuma kana ganin asarar danayi tunda Allah yasa kayi karfi yanzu ai sai ka ragemun hidimar da nakeyi ko da kuwa da kayan abinci ne ko?". Mutallab bai ce komai ba dai har Abba yagama maganarsa sannan Yace " inshaa Allahu Abba zanyi iya kokarina." yamiƙe yayi masa sallama, mamaki sosai yakeyi a ransa na zancen Abba duk da shi ba aure agabansa yanzu, amma hakan na nufin ko auren zaiyi Abba bazai iya taimakonsa takowacce fuska ba bayan yana kallo auren ya Jamil ba abinda yayima kansa duk shi yayi masa, kama daga kan sadaki, lefe gidan da zai zauna, kayan daya saka wajen biki, abincin da akaci da duk wasu kuɗaɗe da amarya zata buƙata duka shiya bashi bayan kuma zaune yake acikin shagunansa yana yanda yake so, Sai shine zai cewa haka sai kace dukansu bashi ya haifesu ba? Wasu hawaye yaji na ƙoƙarin zubo masa yayi saurin maidasu lokacin da zai fito sashen, Afrah ce ta taso tare da nufowa wajensa tace, "Ya Mutallab ara mani wayarka nayi browsing assignment aka bamu kuma gobe zamuyi submitting". Ganin yanayin fuskarsa yasa tata fuskar sauyawa tana tsuresa da idanuwa cike da don sanin menene ya ɓatawa yayan nata rai, murmushi ya sakar mata tare da ciro wayar yamiƙa mata yana cewa, "Kema nakusa saya maki wayarki ko dan irin haka tunda Allah baisa aka samu wanda zai tunawa Abba ya saya maki ba kamar yanda ya sayawa ƴar uwarki ko ɗan lalurar makaranta ki gayamin wacce ake yayi sai anjima ya jalil ya siyo miki". Ya ƙare zancen cike da son maidawa matan mahaifin nasa magana saboda a yanzu wani irin zafinsu yake ji a zuciyarsa, saɓanin shekaru baya da duk abinda sukeyi baya jin damuwarsa a zuciyarsa sosai kamar yanzu. Muryar Umma yaji tana cewa, "Sannu ɗan ƙaruna idan akwai abinda ma yafi waya ka siya mata, marasa mutunci banza da wofi kudin naka da ba'a san ma taya ka samesu ba". Bai rabata da ƙanzil ba yasa kai ya wuce abinsa dan gurinsa ya cika tunda saƙon daya aika ya tafi dai-dai inda yake son zuwa". Aunty Amarya kuwa wani mugun kallo tabi Afrah dashi haɗe da cewa, "Munafuka ai kamata yayi ace kin tambayi ƴar uwar taki Jiddah ta ara maki bakije wajensa kice ya ara maki ba, salon ya siya maki ke kaɗai dan munafucci". Dariya Umma tayi haɗe da cewa, "Au to Ina ruwanki Ina yayanta ne ko? Meye abun munafucci ai kowa ya iya allonsa ya wanke". "Ai ko baki faɗa ba Malama, kina zaune zan biya maki allona shafi-shafi nakuma wankesu tas agabanki dan babu yanda zakiyi dani na zame maki ƙadangaren bakin tulu, idan kuma kina ganin kuma zaki iya to muzuba mugani". Dariya Umma tayi har da shewa haɗe da cewa, "ki kwantar da hankalinki yarinya, me kike tauna na baka na zuba? Ni ai murucin kan dutsi ce, kuma kabewar kan kabari wallahi, daga ke har ƙananan ƙwarin da suke ganin sun isa acikin gidan nan da sannu zan jefa rayuwarku a garari, da AKWAI SIRRIN dana tanadarwa kowanenku, shiyasa na zaɓi a yanzu na zame maku KURMAN ALLO, amma mujuri zuwa rafi yarinya". Umma ta ƙare zancen haɗe da miƙewa ta nufi ɗakinta tana ƙwalawa Jiddah kira, tsaki kawai Aunty Amarya tayi tare da ɗora ƙafarta ɗaya akan ɗaya taci gaba da kallonta duk da yanda kalaman Umma ɗin suka dakar mata zuciya. *********    Sosai Meenal taci kukanta har ta godewa Allah kafin bacci mai nauyi ya ɗauketa, bata farka ba sai bayan sallar isha ta tashi idanuwanta sunyi luhu-luhu saboda kukandata sha, ƙasa ta sauko daidai lokacin maigadi yayi sallama Mommy dake zaune palour ta amsa mashi yace, "Hajiya wai ga saƙon Hajiya ƙarama daga campaning magu phone store". Meenal dake ƙoƙarin zaunawa saman kujera sai tafasa ta nufi bakin ƙofar ta karɓo saƙonta tana dallawa maigadi harara, a zuciyarsa kuwa cewa yakeyi Allah ya baki haƙuri ai bani nakar zomon ba sannan ya juya yayi tafiyarsa. A nan palour Meenal ta zauna ta buɗe ledar da aka kawo mata sauƙin taciro wayarta da Ya Kamal ne ya kaimata ita acan kamfanin na magu phone store akayi mata customizing ɗinta, duk da damuwar dake zuciyarta bata san lokacin da tace, "Wow!" Ba saboda yadda wayar takoma mata super clean sai wani ɗaukar idanu takeyi tamkar sabuwa, jujjuya wayar ta shigayi tana murmushi dan a yadda ta tarwatsata bazaka taɓa yadda cewa ita bace, kallon Mommy tayi da idanuwanta na akan tv tace, "Mommy dubi wayan nan?" Sai a lokacin Mommy takalli gefen da take fuskarta da murmushi ba yabo ba fallasa tace, "Kai amma tayi kyau, sabuwa ce aka siya injin?" Dariya Meenal tayi tana kunna wayar tace, "A'a Mommy wayata ce da Ya Kamal ya kaimani gyara a magu phone store, shine fa sukayi customizing ta dawo haka, gaskiya wurin nan bana jin akwai na biyunsu a kaf faɗin ƙasar na". Tana rufe baki Ya Kamal yaƙaraso wajen yana faɗin, "Ai na faɗa maki Meenaluwa mutanennan ƙarshe ne, duk tsufa waya ko lalacewarta haka zasu maida maki sabuwa, kinsan Allah maida tsohuwa yarinya suke yiwa waya". Ya ƙare zancen tare da zaunawa yana ƙoƙarin ɗaukar wata haɗaɗɗiyar kundum ɗin wayar da suka haɗo mata dashi". Wani kallo Meenal tayi masa sannan ta tattara kayan wayar da komai da komai ta komawarta sama abunta ba tare daya kulashi ba saboda fushi takeyi dashi sosai. "Meenaluwa". Yai ta kiran sunanta tayi masa banza, miƙewa yayi zai bita Mommy ta sauke ajiyar zuciya haɗe da cewa, "Ina zaka je Kamal? dawo kada kabita inaga wani ya ɓata mata rai kar kaje ta sauke shi akanka". Cije leɓensa yayi na ƙasa cikin ɓacin rai haɗe da cewa, "Momcy yarinyar nan ta rena mutane wlh, ɗazu fa akan gayen nan ta kwaɗa mani mafi agaban ƙawayenta, shine kuma yanzu zata wani yarfani a gabanki Momcy? I love Meenal saboda ita kaɗai ce ƙanwata amma wlh sai na tattakata yau in yaso tayi fushin dani dai-dai, banda tana ƴar rainin hankali ma Momcy ina ita ina wannan gayen, kin ganshi kuwa sai kace jinin larabawa zata wani name masa saboda mugun san kanta kuma tace baza a faɗa mata gaskiya ba dan batada hankali?" bai rufe baki ba Meenal dake jin duk abinda yake faɗa ta shiga jefosa da duk abinda ta samu dake ɗakinta tana faɗin, "I hate you, I hate you ya Kamal". yanayi yana tarewa har ta gaji ta juya ta koma cikin ɗakinta ta zauna gefen gado ta dafe kanta, kallon Mommy Kamal yayi haɗe da cewa, "Kin gani ko Momcy, Allah kibari nakoya mata hankali". Ya ƙare zancen yana ƙoƙarin sake hawa saman Mommy ta dakatar dashi da cewa, "Ka ƙyaleta mana Kamal ai baka biye mata ba!" Shiru yayi kafin ya juya a fusace yabar gidan Mommy takira mai aikinta tasa ta gyara wajen da Meenal ta jefo yayan nata da abubuwa har wasu suka farfashe. **********    Mutallab na zaune a can cikin ƴar rumfar dake gefe a harabar gidan shi da Jalil suna tattaunawa akan zancen kasuwancin da zai kaisa ƙasar ta Nijar don kusan shine abokin shawarar tasa akan harkar kasuwancinsa sai kuma Idris, da farko dai so yayi idan yaje ya samu wuri mai kyau ya siya ya gina shagunansa, amma sai Idris ya bashi shawara akan yafara kama haya kona rabin shekara ne sannan ya sayi filin  a hankali yanayi yana ginin, kafin wa'adi ya cika na wajen daya kama haya ya gama kammala ginin nasa sai ya koma acan, shine yake faɗawa Jalil saboda yabashi shawara shima, sosai ya nuna masa goyon bayansa ga shawarar Idris tare da bashi misalai da kuma dalilansa na goyon bayan shawarar Idris masu yawan gaske, ɗaya daga cikin wayoyinsa ce dake ajiye a saman siminti daya zagaye ƙarfen dake riƙe da rumfar daga tsakiya ta hau ruri Jalil ya miƙa hannu ya ɗauko ya miƙa masa, ganin lambar Meenal ce duk da baiyi saving ɗinta ba ya sashi sakin tsaki haɗe da rejecting Kiran ya mayar da wayar sukaci gaba da tattaunawa, sake kira tayi akaro na biyu yai banza da kiran har ta tsinke, tana kira a karo na uku ya lumshe idanuwa yana jin kamar ya ƙwalla ƙara tare da furzar da iska a bakinsa, hakan yaba Jalil dariya dan haka yamiƙe da sauri yana yi yabar wajen dan dama sun gama maganar da sukeyi. Ji yakeyi ba dan masu kira daga kasuwa ba daya kashe wayoyin gaba ɗaya, ɗayar wayar tasa ce ta sake ɗaukar ruru yakai kallonsa gareta still dai Meenal ce, kafin yakai ga ɗagawa har ta tsinke ya sauke ajiyar zuciya tare da tattara wayoyin ya miƙe ya nufi ɗaki, sauƙin message yaji ya shigo yai banza dashi dan yasan ita ɗince. Dama shirin kwanciya yakeyi dan haka ya zube wayoyin a gefen pillown sa haɗe dayin rigingine yana kallon saman rufin ɗakin nasa yana naɗe hannayensa akan ƙirji, tunanin mahaifiyarsu ne ya zo masa adaidai wannan lokacin yana jin ina ma ace tana raye, ya tabbata matsaltsalun da suka shuɗe acikin rayuwarsa da wuɗanda ma ke tafe da basu shiga rayuwarsa haka da yawa ba saboda karfin addu'ar da zata riƙa yimasu, Mahaifinsu kuma daya rage baya tunanin a yanda yake nuna masu tamkar su ba jininsa bane zai iya tunawa dasu daidai da rana ɗaya ya sanyasu cikin addu'arsu, wasu zafafan hawaye da yaji sun zubo masa ya sashi mirginawa ya koma ta ɗaya gefen hannunsa na dama a hankali ya lumshe idanuwansa yana karanto addu'o'in kwana har bacci mai nauyi yazo yayi gaba dashi. Meenal kuwa da bai ɗauka ba haka ta  sake zaunawa taci kukanta har ta gode Allah sannan tamiƙe ta ɗauro alwala toilet Dan sai a lokacin ta tuna da batayi sallar magrib da isha'i ba, bayan tafito ta ranka sallolin ta sake saukowa ƙasa lokacin kusan ƙarfe sha biyu, ruwan tea take son sha amma har mai aikin Mommy tariga data wuce gida dan ba'a nan take kwana ba, Mommy kuma tana ɗakinta ita kuma bata san ya zata haɗa ruwan ba, kitchen ɗin ta nufa tayi tsaye cikinta na wani irin ƙugi saboda tun breakfast ɗin safe bataci komai ba saboda zumuɗin tahowar Mutallab, fridge ta buɗe ta ɗauki kwalin hollandia takoma sama tana jin wata irin jiri na ɗibarta tamkar ta faɗi. #Mutallab Asad #Tagwaye Biyar #Billy S Fari #Nana Diso *MUTALLAB ASAD* *PAID BOOK #500* *TAGWAYE BIYAR.* NA *BILLY S FARI* & *NANA DISO* 35. Tun da asuba Umma ta tashi Aunty Asiya ta bata wani ƙullin magani tace maza taje ɓangarensu Mutallab ta barbaɗa kafin ya dawo masallaci, boka ya tabbatar idan har ya tsallaka maganin zai riƙa bin umurninta dashi har matar da zai aura sai yanda taso haka zata yita juya shi tamkar uwarsa data haifa da cikinta, hakan zai bata damar mallake dukiyarsa gabaɗaya sai yanda take so tunda sauran aikin data nema ayi akansa ance bazai yiyu ba. " Cikin magagin barci Asiya tafita sashin tanufi ɓangarensu Mutallab sai dai ba tare data ankare ba takai maganin ƙofar ɗakin dasu Walid ke ciki ta barbaɗe maganin sannan ta koma cikin gida, Umma dake tsaye tana kaida kawo tace, "Yaya? Har kin dawo?" "Eh Umma wai garin yaya kuka bari har duniya tasan da Mutallab haka kullum sai zancensa akeyi haba Umma? Allah abunnan ya baƙanta mani rai me isa baki dunƙushe shi ba tun kafin yakai haka kika bari har sai da yayi kuɗi? Duk Ina bokanyen namu ne?" (Waiyazubillah babu wanda ya'isa yahana abunda Allah yakaddarawa bawa matuƙar bawannan yayi imani dashi, samu da rashi anriga tun farkon halitta an rabawa kowa nashi). Harara Umma ta maka mata haɗe da cewa, "Ke ni matsa kibani waje, ta'ina nasan ya samu kuɗi haka nan saka malam nakan ruwa ya lalata komai ba, kiga yaro munafuki yaki barin ƙafa ko ɗaya da za'a gane yana samun kuɗi, kawai nidai nasan nayi duk yanda zanyi naga Abbanku bai taimakesa ba amma tsabar munafurcin yaronnan sai kace mace daga dako sai arziƙinsa kawai mukaji yafita, amma ko yanzu ba komai kuɗin tamkar mu yatarawa su, wannan shine matakin farko dana fara ɗauka akansa dan ko zanyi tafiya tsirara sai nayi duk yanda zaiyi na tarwatsa rayuwarsa, komai nasa sai ya dawo hannuna ta yadda zai koma asalin faƙirinsa da aka sani tun farko" Murmushi Asiya tayi haɗe da cewa, "da dai yafi Umma, dama ai tun farko nakasashi yakama kuyi ta yadda ko dakon bazai iya zuwa yayi ba amma kuka tsaya sanya, gashinan yana kulla mana baƙinciki a hannu tunda ya tara abunda ba muda shi. Mutallab kuwa bai dawo daga masallaci ba sai da rana tafito bayan yayi azkar da karatun alƙurani ya nufi ɓangaren da Abba yake. Zaune ya sameshi yana shan redio ya durƙusa har ƙasa agabansa yace, "ina kwana Abba?" Ba tare daya iya ɗaga idanuwa ya kallesa ba. banza yayi masa yaci gaba da cewa, "Abba kayi haƙuri da maganar dana mayar maka jiya in sha Allahu hakan bazai sake faruwa ba". idanuwa Abba ya zubamasa kamar mai tunanin wani abu sai kuma can ya haɗe rai yace, "Mutallab bari na faɗa maka gaskiya ba kai ba hatta ƴan uwanka nagaji da ganinku cikin gidan nan saboda na fahimci suma haka zasu tashi da irin hali irin naka, ɗan haka ka haɗa kan yan uwanka duk inda zaka je kuje can  bana don ganinki" "Innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Abba su kuma me sukayi maka? Afrah fa macce idan mu ka koremu munje wani wajen ita ina kake so taje? Laifin me sukayi maka Abba? Don Allah kada kabari laifina ya shafesu". "Duk inda ma zaku je itama taje can". Abba ya faɗa yana ɗauke kansa gefe, shiru Mutallab yai kafin can ya sauke ajiyar zuciya haɗe da cewa, "Abba dan girman Allah kayi haƙuri kabar Afrah ta zauna, Aryan yafaɗa mani cewa yana so ya turo iyayensa su gaka zance aure su". "A'a ni nayafe kar wanda yazo wajena da wannan zancen nagaji da ganinku a gidan nan kuje can dangin mahaifiyarku ko wani wajen kibarni naci gaba da rayuwata da iyalina cikin farincki, idan auren take so suje can su nemi aurenta wajensu tunda kai mai arziƙi ne sai ka aurar da ita". Murmushin da yafi kuka ciwo Mutallab yayi haɗe da cewa, "Amma wannan ai haƙƙinka ne Abba ba nasu ba ba kuma nawa ba tunda Allah yasa kana da ranka, bayan haka Abba katuna fa da kanka ka hanamu zuwa wajen dangin mahaifiyarmu, hatta waya da mukeyi dasu sai daka hanamu, na tabbata wannan abun ya ɓata masu rai shiyasa suma sukayi watsi damu ina banda má tànte Sajida da wasu lokutan take bibiyar lafiyarmu, ita kuma ba wani ƙarfine da ita ba balle muce zamu tafi can wajenta mu zauna, yanzu haka sun rabu da mijinta Abba to taya zamu kwasar har mu uku muje can bayan ga gidan mahaifinmu?" Cikin ɓaci rai Abba da ganin Mutallab ya haifar masa da ciwon kai ya taso masa da faɗin, "Komai dai meye nafaɗa maka Mutallab ku tattara kubar mani gida bana son ganinki". Wani irin jiri Mutallab yaji ya ɗebesa ya sadda kansa ƙasa ƙwallon da yake ta riƙewa da suka tarar masa acikin idanuwa na zubowa yace, "To  Shikenan Abba zamu tafi, ɗan Allah kayi haƙuri kada kariƙeni arai ka kuma yafemin abisa abunda yafaru jiya saboda nafahimci hakan da nayi kuskurene kuma babban laifi ga duk wani ɗa nagari". "Ni bance nariƙeka arai ba, ban kuma ce banyafe maka ba, kawai so nakeyi dukanku kubar mani gida, ina  buƙatar space yanzu, jiya yayarku Asiya ta dawo gida aurenta ya mutu to da matsalarku zanji ko da Tata? Ka ɗaukesu kawai kuke ni nayi abinda zan iya yanzu suma su ƙarara sauran, in yaso ita Asiya ta zauna a ɗakin Afrah". Har Mutallab zai yi magana sai ga Asiya ta shigo ɗakin, "Abbanamu ina kwana". Tafaɗa tana kifar Mutallab da wani irin mugun kallo mai cike da tsana, take wani yalwataccen murmushi dake ɗauke da farinciki ya bayyana a fuskar Abba tamkar ba shiba yace, "Sannunki yar albarka lafiya kalau, ya kike kin tashi lafiya ko?" "Lafiya kalau Abbanmu ya haƙuri da abubuwa". "Ai komai yaƙare kuma Asiya, Ashe haka abu yafaru ko?". "Eh Abba kuma Allah nidai bazan koma ba tunda ba jaka nake ba". "Karki damu Asiya ko nima bazan barki komawa gida can ba tunda ba jaka na haifa masa ba, ki saki jikinki mahaifinki na tare dake ɗari bisa ɗari zan tsaya miki har sai na ƙwato maki ƴancinki". Murmushin jin daɗi Asiya tayi haɗe da cewa, "Godiya nakeyi Abba a ɗakin Mutallab zan zaunane idan ya tafi?" "Subhanallahi kina maccen zaki zauna a wajen gida ɓangaren maza? A'a ai tare zasu tafi can dangin mahaifiyar tasu shi da Afrah, kinga sai ke ki zauna ɗakinta ai zaifi ko". "Eh Abba gaskiya zaifi, Nagode sosai Jidda ashe har abu ya matso sai yau Umma ke faɗa mani?" "Eh gaskiya yaron a shirye yake shiyasa, ɗan gidan minista Aliyu Bukullu ne, shin ya sunansa ma?" "Kamar Aliyu Ali Bukullu naji Jiddah nacewa sunansa amma AAB ake cemasa". Aunty Asiya ta faɗa cikin don cusawa Mutallab baƙin ciki, juyowa Abba yayi ga Mutallab yace, "katashi kuje mana ku haɗa kayanku ku tafi kayi mani zaune ɗan Munafurcin kana sauraren abinda bai shafeka ba". "Amma Abba tunda har ga hidimar Jiddah ɗin ta matso kuma shima Aryan a shirye yake da kayi haƙuri ka haɗe bukin nasu, kaga dai ba muje muka kaiwa kowa nauyi da lalurar auren Afrah ba". "Mutallab karfa ka ƙule ni, nace bazan iya ba ko kai kurmane? To wallahi bari kaji sisina bazan iya kashewa ba auren Afrah da wannan shashashan abokin naka kuma wallahilazim sai kun barmin gida Mutallab". Jin rantsuwar da Abbaya ƙare zancen da ita yasa Mutallab runtse idanuwa kafin can ya buɗe yana cewa, "Tohm shikenan Abba mungode sosai da hidimar da kayi agaremu Ubangiji yabiyaka da dukkanin alkhairinsa". Sannan yamiƙe dan dama zaman da yakeyi tun ɗazu nako zai iya shawo kan Abba ɗin ne bawai dan bazai iya ɗauke ƴan uwan nasa su tafi bane".  Tsaki Abban yaja ita kuma Aunty Asiya ta mere baki haɗe da cewa, "Gaskiya Mutallab ya fiye taurin kai Abba". Sai da Abban yayi kwafa sannan yace, "ai kibarni dashi ni nafisa shi".       (Eh lallai mun gani Abba taurin kai kam Mutallab gado yayi Allah yasa kar ya wuce🏌️). Ko da Mutallab yaƙarasa ɗakinsa yatarar da Afrah da Jalil aciki zaune sun buga uban tagumi haɗe da jimamin abinda yafaru jiya na korar da Abba yayiwa Mutallab ɗin, kowannen su ji yakeyi zuciyarsa babu daɗi kuma a wannan karon ina yayan nasu zai nufa tunda dai sun san bai kammala gininsa ba, kusan atare suka haɗa baki wajen cewa, "Yanzu yaya ina zakaje?" Shi sai abun ya bashi dariya da tausayi da yaji sun jefo masa tambayar, su sunanan cikin damuwar ankoresa basu san yanzu abun har su ya shafa ba, "karku damu da ina zamuje, duk da mahaifiyarmu bata raye Allah yayi mana suturar da bazasu wulaƙanta ba in sha Allah, zamu tafi mubar masa gidansa kamar yanda ya buƙata domin har ku yanzu yace baya don zamanku agidansa saboda abinda nayi masa ya tabbata kuma yimasa zakuyi". Tsayawa yayi ya ɗauke ƙwallan da suka zubo masa afuska da yatsa kafin ya sake cewa, "i'm Sorry na jamaku har laifina ya zo ya shafeku kuyi hakuri duƙanku kunji ko". Kuka Afrah ta saka haɗe da cewa, "Mun shiga uku Yaya ina zamuje yanzu? Meyasa Abban zai yimuna wannan hukuncin ba tare daya tuna da maraicinmu ba?" Janyota yayi ajikinsa haɗe da cewa, "shiii... Afrah kina tare da yayanki fa a wannan karon, ko baki yarda da kibini ba nakoma naba Abba haƙuri koda zai dakeni ne yabarki ki zauna abunki nan". Sosai ta sake rungumesa haɗe da girgiza kanta tace, "zan kasance tare da yayana aduk inda zai je na yarda dashi ɗari bisa ɗari". Ɗagota yayi yana share mata hawaye kafin ya zauna gefen katifa kusa da Jalil yaciro wayarsa, Mà tànte Sajida ya kira suka gaisa, bayan sun gaisa cikin gwarancin hausarta da bata ƙware ba take cemasa yanzu take zancen kiransa tafaɗa masa tananan zuwa ƴan uwa sun haɗo mata kuɗin mota sunce tazo ta duba su, kwana biya kowa sai cewa yakeyi yayi mafarkin mahaifiyarsu, wasu ƙwalla suka zubowa Mutallab yasa hannu ya goge haɗe da cewa, "Mà tánte idan baki kamo hanya ba kibari dukkaninmu muna nan zuwa". Yanda taji muryarsa yasa hankalinta ɗagawa cikin sassarƙe magana take tambayarta lafiya? Mai neman kuka anjefesa da kashin awaki! Mutallab najin sautin tambayar da take masa cikin kulawa da soyayya sai kawai hawaye suka dinga wasar ƴar tsare akan fuskarsa, abinda yajima yana nema kafaɗar da zai jingina yayi kuka sosai ko ya samu sanyi da sassaucin nauyin dake dasƙare a zuciyarsa sai yaji tamkar mà tànte Sajida ta bashi wannan majinginar, shiru yayi ya kasa magana ba tare daya damu da kuɗinsa da ake ciba na waya ita kuma bata kashe ba har sai da yaji ya samu natsuwar fara koro mata bayanin duka abinda yafaru. Sosai ranta ya ɓaci ta kuma ji ba daɗi aranta amma sai ta danne ta dinga basa haƙuri tare da ƙarfafa masa guiwa akan ya amshi wannan jarabawar hannu biyu ina sha Allah watarana sai ya bada labari, ta kuma sheda masa cewa kada su zo dama tana saman hanya ne sun tsaya cin abinci ne da kuma sallah. Sosai yaji daɗin hakan tace yabawa Jalil waya su gaisa bayan sun gama yaba Afrah suka gaisa itama sannan sukayi sallama yana mata addu'a Allah ya kawota lafiya. Miƙewa yayi ya bude durowar da yasaba ajiye mahimman abubuwansa ya ciro mukulli ya miƙawa Jalil ita kuma Afrah yaciro iPhone daga cikin leda ya miƙa mata yana cewa, "Kai riƙe wannan ke kuma ga wayar danayi miki alkawari nan amma ina so kiyi karatu sosai bawai ki haye social media ba kina faɗan ɗaukar pic ɗinki kina posting, duk randa na kamaki zan karɓe wayata kuma bazaki koma riƙe waya ba har sai kinyi aure". Cike da jin daɗi ta rungumeshi btana godiya Ya Jalil na tayata tare da yimashi addu'ar da har sai data saka shi ƙwalla, shima dai yayi hawaye na godewa Allah da ya bashi ikon ɗaukar hanya mai kyau duk da challenges ɗin da yayi facing, wannan shine amfanin zama mutumin kirki ko da iyaye basu raye ƙanne da ƴan uwa zasuyi alfahari da mutum kuma suji daɗinsa, da ace yatashi yana shaye shaye ko kuma bai tsaya yayi karatun addini ba bai kuma jajirce ba da yanzu wata maganar akeyi ba wannan ba, wataƙil ma asanadiyarsa suma ƙannen nasa su faɗa cikin wani halin, kallon Afrah yayi dake faman kokuwa da kwalin iPhone ɗin Tata yayi haɗe da cewa, "Afrah tashi kije Jalil ya rakaki ki kwaso duk abunda kike so na buƙatarki ku haɗa da nashi shima ku kawosu a motata, bari na watsa ruwa kafin kufito, miƙewa sukayi tare suka ƙarasa cikin gidan suka nufi stairs zuwa ɗakin Afrah dan babu kowa a nan main palour, sai da suka fara sakko da kayan Afrah da suka haɗa waje ɗaya cikin wani madaidaicin akwati da Mutallab ya siya mata da daɗewa tana saka kayansa aciki sai ga Jidda ta fito daga ɗakinta, kallonsu tayi tasaka dariya haɗe da cewa, "Oh su Afrah fa sai ƙauyen gyatuma aje can asha hwarau-hwarau". A fusace Yaya Jalil yayi kanta Afrah tayi saurin riƙe da tana cewa, "please ya Jalil let her be". tayi maganar kamar zatayi kuka ganin yanda yake ƙoƙarin ƙwacewa ya nufi wajen Jidda. #Mutallab Asad #Tagwaye Biyar #Nana Diso #Billy S Fari *MUTALLAB ASAD* *PAID BOOK #500* *TAGWAYE BIYAR.* NA *BILLY S FARI* & *NANA DISO* 34. Tana fitowa sashen Asiya ƴarta ta shigo gidan tana kuka, da sauri Umma ta ƙaraso wajen tana faɗin, "Ke lafiya?  Me zan gani cikin darennan ni zainabu?" Tare da zama kusa da Jidda da bluethoot ke laƙe a kunnenta tana faman chatting. A jikinta Aunty Asiya ta

Chapter 20 of 54