yaya tace, "Kin gani babbar yaya dama nafaɗa maki bazasu yadda mu zauna wajensu ba, kawu kuma kinga yariga daya gama maganarsa shima ni kawai inaga mu koma gidan da muke ciki mu zauna abunmu har Allah yai ikonsa akanmu, kinga tunda dama akwai kuɗin da za'ayi gyara gidan a hannun Bello magini sai mu nemesa muyi masa magana ya gyara mana gidan kamar yadda sukayi alƙawari da mon pèrè ko ya kike gani". Murmushi babbar yaya tayi dan har ta manta da zancen kudin iyayen nasu dake hannunsa haɗe da cewa, "Eh Aïcha kin kawo shawara kuwa, mutafi mu nemesa". Ta riƙa hannunta suka tari keke napep suka hau suka wuce, sai dai ko da suka tafi inda suke tsammanin ganin Bello magini basu isko shi ba, haka suka ƙarasa wunin suna zaman jiransa kafin ya iso, bayan sun gaisa ne suka bijiro masa da maganar dake tafe dasu wajensa, nan ya hau ƙefe-ƙefen idanuwa yana yimasu rantsuwa wai an sace kuɗin tun washe garin ranar daya amso kuɗin tare da basu haƙuri, ba suda wani zaɓi a lokacin daya wuce su barshi da Allah dan ko sunce suyi rigima dashi basu da wata shedar da zata sa a yadda dasu tunda daga shi sai iyayensu suka san da zancen wannan aikin, jiki a sanyaye suka miƙe suka nufi mataccen gidan nasu da yanzu ko rufin kwano babu aciki balle silin, ɗakinsu suka nufa da ƙofarsa bata canye ba haka ma rufinsa suka buɗe suka shiga ciki, dukkansu kuka suka fashe dashi mai tsima zuciya tunowa da mahaifan nasu, tabbas duniya makaranta ce dake cike da tarin wajen ɗaukar darussa kala-kala. Sai da sukaci kukansu mai isarsu kafin babbar yaya ta miƙe ta ɗauki kudi cikin kuɗin da suka samo taje ta siyo masu ledar ruwa da abincin da zasu ci, kafin tadawo Aïcha tasa takalmanta ta tutture dattin dake cikin ɗakin waje ɗaya yayi haske sannan ta fiddo zannuwansu biyu ta shimfiɗa masu a ƙasa dan har ankira sallar magrib, bayan ta dawo suka ɗauki ruwan suka wanke jikinsu suka ɗauka arwala sukayi sallah, tunanin makomarsu suka shigayi ba tare da kowanensu yayi magana ba har akayi kiran sallar isha suka tashi sukayi sannan suka zauna sukaci abinci, da yake akwai gajiyar yawon da sukayi basu jima da gama cin abincin ba suka fara jin bacci, miƙewa babbar yaya tayi ta rufe masu ƙofar ta saka sakata sannan suka karanta ƙula ƙuzai da ayatul kurziyu da amanar Rasulullah da sauran addu'o'in neman kariya sannan sukayi kwanciyarsa....
#Mutallab Asad
#Ƴan Tagwaye
#Nana Diso
#Billy S Fari.
SHAFI NA SITTIN DA DAYA.
*MUTALLAB ASAD*
Arewabook:- billysfari
Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.
Tunda tafito ya zuba mata idanuwansa, ciƙin ransa yaji mutukar sanyi ganin shigar dake jiƙinta sannan hijjabin yayi mata mutukar kyau duba da basaba saƙashi tayi ba, ga fuskarta dake dauke da murmushi cike da taƙunta na yanga takaraso tana murmushin da yasaka zuciyarsa sanyaya, " Assalamu alaikum yayana barka da zuwa." " waalaikissalam kanwata MashaaAllah tabaraka ƙinyi kyau sosai Allah yayi miki Albarka da wannan shiga." Dan gyara tsayuwarta tayi haɗe da juya manyan idanuwanta tace " Farincikin ka shine Nawa yaya Duk yadda kakeson kasancewata haka zan zama." Murmushi mai sauti yayi yace " Nagode Miki Yanzu kuwa zan samu dady?" Da dan hanzari ta ƙalleshi tace " Eh yana ma palour yanzu Na barsa acan." " Idan babu damuwa ko zakiyimun magana dashi?" " Tohm shikenan tafaɗa tana Nufar cikin gidan shi kuma yana ji ginar da jiƙinsa a motarsa sosai yaji ta kara kwanta masa aransa duba da yadda takara Nutsuwa yanzu, Tabbas kamun kai da Nutsuwa wasu ababeni masu daraja agun diya mace. Cikin mintuna da bazasu gaza biyarba sai gata ta fito tanata murmushi Sannan ta karaso kusa dashi bakinta dauke da sallama kamar dai dazu, kallonta yayi yace " Zansamu damar ganin nasa?" Cikin shagwabar data mikar masa da tsigar jiƙinsa tace " yaya.." Kallonta yayi yace " Uhm.." " Idan laifi Nayi danAllah kayi hakuri karkagayawa dadyna." " Laifin Mr zakiyimun dear? Yafada yana gyara tsayuwarsa Muje kinji inada dan ayyuka acikin shaguna. Cike da jin dadi da kuma farin ciki suka shiga zuwa bangaren da mahaifin nasu yaƙe babban palour ne da yasha alatu ga center table din ancikashi da kayan ciye ciye sallama yayi yakarasa gaban dady yana gaishe shi." Da hanzari Abba ya amsa yana faɗin " Dan Albarka ina fatan lafiya dai ko? Ya mahaifin naka?" " Kowa lafiya dady." Ya kasuwan kuma? Naji dazu radio ana faɗin ka buɗe sabbin shaguna na fitar da hatsi waje, Nima dai ina bukata zamuyi magana daga baya yanzu ina sauraronka." " Murmushi yayi yace " Daman dady maganar Meenal ce Nakeson kara tambaya idan ba'a tsayar mata da tsayayye ba inason intro magabata gobe." Har cikin ransa daɗi sai da yaji wani sanyi kamin yace masa" Alhamdulillah mashaa Allahu Allah abun godiya hakan abun murna ne ai Mutallab bamu tsayar mata da kowa ba babu laifi idan Anturo ɗin." Meenal kuwa najin haka ta haye sama aguje tana murna, tsalle tashigayi tana fadin " Allah Nagode Maka yaa Allah nagode maka tashiga rawa, mumy dake gefen dakin nata ne tashigo tana faɗin lafiya?" A guje ta diro daga bed dinta haɗe da rungume mumy tana faɗin " Mutallab xai aureni mumy, mumy ta I love you tashiga rawa tana murna." " Alhamdulillah Allah yatabbatar muku da Alkhairi Addu'a zakiyi bawai ihu ba kinji." Wayarta datayi kara ta dauka ganin mai ƙiran nata " yaune na farko datace masa "Aşkım" (masoyina da yaren ƴan kasar Turkish) " Uhmm that's a nice name love yafaɗa yana murmushi. I love you, I love you, Meenal, I will like you to be my wife, ina kaunarki da duk raina." " Uhmm tafaɗa A hankali tafashe da kuka." " My soul mate what the crying for?" " Aşkim ina sonka danAllah kasoni Nima ko ƙadan ne, bansan ƙauna ba bansan soyayya ba sai aƙanka Aşkim please..." wani deep breath yaja yana dan gyra zamansa amota sautin kukan nasa na tayar masa da duk wani tsigar gashin daƙe jikinsa sosai yajishi yana ƙokarin shiga yanayi haƙan yasashi faɗin" soul mate kidaina kuka inshaa Allahu bazantaba wulakantaki ba kuma kisa aranki mutallab Asad love you so much." " Nagode Aşkim." " Babu godiya tsakaninmu soulmate ki turamin sizes na komai Naki please."" Okay Sai anjima take care." Mumy dake tsaye tana kallonta tace " Ohhni Mumyn Meenal kiransa kikayi kuma" mumy tayaya zan iya riƙe wannan farin ciƙin ni kaɗai?" " babban farin ciƙin da zakiNuna kitashi kiyi sallah raka'a biyu ki godewa Allah sai kizo mu shirya event ko dadynki yace next week zamu fita siyayyan furniture's." Yau zan haɗamiki maganin infection dinnan kifara sha ɗan ke kam meenal sai Nayi da agske akanki kin lallata kanki ta ko'ina. " " Mumyna tunda inadake da inna ai bazanyi kuka ba ni can ma zan koma tagyarani." Dariya mumy tayi tana kallon fitsarar yaran zamani." Yanzu dai Tashi kije kitchen ki dafa maganin nan da kanki meenal kinji." Kallon mumy tayi tace" yanzu mumy ina amaryar?" Lallai yarinyar nan so kikeyi infara fasa miki baƙi ko?" " To inajinki tafada tana miƙewa." Ki dauki tumeric teaspoon daya, citta tea spoon daya,kaninfari teaspoon 1, tafarnuwa teaspoon 1 albasa teaspoon daya, habbatussauda ki dakata fa 1table spoon, sai ƙimba itama 1teaspoon, sai lemon tsami 1 bisa hudu zaki dauka, sai zuma asaka yadda za'a iyasha, zogale ko tsinkensa, sai ki dafasu su dahu sosai, inshaa Allahu indai kakayi wata daya kinasha duk wani nauyin infection zaki rabu dashi ko kina fama da kurajen gaba ko kuma sanyin jiki inshaa Allahu kin rabu dashi, saura kuma ki ƙi maida hankali." " mumyna zan mayar."
Idress Ne yaƙalle shi yace" Ango ango dazu aryan yake tambayata nace ai banda tabbacin dawowarka." " Baka rabo da zolaya Anraba kayan nan kuwa." " har sunsaka kudinsu ma." MashaaAllah kudin zakkar wannan shekarar arabawa yaron shagon nan danAllah yakamata marasa abun hawa su siya da marasa muhalli." Sosai idris yaji daɗin har yana mas addu'oi. " Amma ranka yadade Anya bazaka fara dahuwar shayin maza ba? ( Matan aure kuma zaku iyayiwa mazajenku domin maganin sanyi da kuma saurin gajiya). Kallonsa yayi sannan yace " Bangane abunda kake Nufi ba." Kasan basir duk ya lallatamu yanzu tunda kaga ankusa aure akwai haɗin da mahaifina ya koyamun wanda akeyi domin magance kowanne irin sanyi." " Madallah inajinka to." " yauwa zaka samu citta mai yatsu wato danyar citta, kamar table spoon daya, sai kaninfari tablespoon daya, sai tsamiya sabuwa akeso ba'a son tsuhuwar tsamiua silli biyu ta wadata, sai tafarnuwa kamar guda uku manya, Habbatussauda shima table spoon 3 adafa maka kana sha da safe da yamma kofi daya, wallahi ajiƙinka ma sai kaga sauyi ballantana kuam alafiyar mazantakarka." " Nagode Abokina inshaa Allahu zan gwada
*****
NIGER
kasantuwar karfi biyu ne Nadare ko'ina yadauki shiru duba da yanayi ne na damuna, duƙun kune take ciƙin ya gulalliyar tabarmar ta rufa da wani tsohon bargonta, Yadda tatashi a firgice tana zazzare ido yasata dan zabura da kuma rikicewa Na dan lokaci ko batayi magana ba mafarkin nan ne da ya aureta Kullum da kullum, daga hannunta tayi sama tana neman tsarin Allah haɗe da karanta falaki da Nasi tana tofawa a bangaren data kwanta, taso tatashi tayi sallah Amma sanin ko fitila basu da'ita ga duhu sosai ga kuma shirun da ziyarci ko'ina agidan sai sautin minsharin mahaifinta dake tashi. Kasancewar sosai baccin yake daukarta yasata komawa batare data shirya ba.
Daga sama sama suka fara jin ihu Na mutane Amma duba da mafarkin data saba yi yasata tunanin ko acikin mafarkin ne? Ihun yayarta baba tana faɗin " Aicha Fire Tm (wuta)." " DanAllah ki kyaleni yaya bacci nakeji." Ihun mutane dayakara karaɗe gurin suna faɗin " s'il te plaît, je devrais sortir (ku mutanen gurin nan ku fito). Wutafa tana cimuku dakuna hakan yasata Aicha mikewa afirgice babbar yaya taja hannunta sukayi waje dakyar aka taimaka musu saboda tafaracin kofar cikin gidan sai da suka fito sannan sukace ina Mama da baba? Nan fa akashiga taimakonsu Amma ina wuta tagama kona daƙunansu duk yadda aka kai da rike Aicha Amma haka tashiga fizga akan iyayen nata." Kubarni naje na mutu nima ma mère et mon père (mamata da babana) wayyo Allah munshiga uku innalilahi wainna illahirrajiun Tunda yayarta ta suma makocinsu yasa akayi gida da'ita Aicha kuwa kuka tashigayi mai tashin hankali. Haka wutarnan ta cinye musu iyaye da komai nagidan tas dakyar samarin garin suka taimaka ta mutu. Duk wani mai tausayi sai ya koka musu ace iyayenka sun kone kurumus aciƙin wuta amini dake tawowa tana kuka itama rike Aicha tayi dake tsugune a kofar gidan juyin duniya anyi anyi da'ita ta tashi taki tama daina kuka wani ƙunji take saki. " Aicha danAllah ki miƙe a kofar gidannan ki duba kiga kawunanki kowa sai magana yake miki, kiyi hakuri ki dauki wannan kaddarar da jarabawa danAllah kidaina wannan ƙunjin, ko motsawa batayi ba yayarta data farfado daga suman ce tafito tanata kuka rungume aicha tayi suka cigaba da kukansu mai radadi da taɓa zuciya. " oncle leur parle (kawu kayi musu magana) " matarsa ce tashiga lallabasu tana basu baki suka tashi suka nufi gidan kawun nasu yaran gidan da kowa akayi ƙansu wannan mutuwa ta girgiza duk wani iyalan babansu har ma dana mamansu da akaje aka sanar dasu shine ma suka Tawo gidan kawun dan anan ne za'ayi musu Jamaica duk wani mai imani idan yaga gawar tasu yadda suka zagwanye sai ya koka musu, Nan manyan malamai suka haɗu akayi musu sallah haɗe da Nufar gidansu na gaskiya wanda hakan yakara tayar da hankalin babbar yaya da Aicha dan sai lokacin Aicha ta suma.
***********
Washegari yakamata Laraba haƙan yasa tun karfe 9 su kawu sukayi haramar fita domin zantawa da iyayen amaran, sai da Aka fara zuwa gidan su fannah tuƙunna aka saka rana haɗe da sadaƙinta. Ita kuma imam kasancewa su kawun ne dai zasu karba suma haka akayi saka rana da sadaƙinta, Sannan akayi gidan su meenal suma hakan yakasance an saka rana da kuma kudin sadaƙi inda biƙin yakama nan da wata daya, suk iyayen amaren sun amince cike kuma da murna da godiya da fatan Alkhairi.
Yau grandma da kannin mamanta gidan suka wuni duk da grandma bata sake da mumy ba Amma babu laifi ba kamar da ba kiyayyar sai da yamma kamal da kansa ya maidasu gida, dady dake fitowa daga palour dinsa ne yace " Meenal gobe ne tafiyarku fa dake da mumy da kamal naso naje amma inada tafiya nima." Dariya meenal tasaka.tace " dady Allah yakara girma." " Ameen." Nan fa meenal tashiga sanar dasu su sassy bikinta wani watan aka shiga tsare tsaren abunda za'ayi. " Meenal" mumy takirata tana zaunawa. " Nidai da anbar tafiyar nan nafara koyamiki girki meenal babu abunda kika iya dafata sai ruwan zafi wannan mijin naki ba kamar yaran zamanin nan baniba kinaji yace miki shi bayason snacks." Murmushi meenal tayi tace " mumy girkifa ba matsala baniba danAllah kibar maganarsa mana mumy." " A'a meenal girki kuwa shine babbar matsala wallahi." " DanAllah mumy ni kawai a gyarani shine abunda nadi bukata." Duka mumy ta daka mata sannan tace " Allah yashiryamin ke."
Wajejan ƙarfe 9 yakira Meenal akan gashinan zuwa tabashi list din da yasa tayi masa. Har tafara bacci hakan yasata saurin mikewa tashiga ta wanke fuskarta sannan tafito. Mumy da shigowarta kenan ta kalli dakin sai ka rantse dazu ba'a gyara daƙin ba tace " Meenal menene hakan kikeyi? Har yanzu bazaki koyi gyara daƙinki ba? Anya meenal anya kuwa? Dubi yadda kika komar da bedsheet dubi kaya duk kasan dakinki." " Mumy Yaya yazo bari naje nadawo tafada tana zura hijjab dinta sannan tafesa turaren mumy data dakko mata." " Meenal wannan turaren yayi karfi dawo ki canza kaya." Jin haka yasaka meenal rugawa aguje tayi kasa sannan ta bude kofa sai data karasa gate din sannan mai gadi ya buɗe mata, zaune yaƙe acikin motar jin fitowarta yasashi bude lock din motar tashigo bakinta dauke da sallama." Zuba mata idanuwa yayi turaren nata na duƙan hancinsa wani sanyi yaji ransa yayi haɗe da tsigar jiƙinsa data shiga tashi, yaa Allah yace " Badai kinfara bacci ba?" Daga masa kai tayi cike da kunyarsa." " kiyi hakuri dady yacemin gobe zakuyi tafiya Amma shine baki sanar dani ba." " kayi hakuri mantawa Nayi." A hankali yace " Matar Mutallab " dago ƙanta tayi ta zuba masa idanuwanta tana murmushi sannan ta mika masa takardar dake hannunta, haƙan yabashi damar riƙe hannun yanajin yadda jiƙinsa ke Amsa masa kowanne gaba ga tsigar jikinsa dake mikewa." Batasan sanda ta lumshi idanuwanta ba tana jan hannunta shima yayi mata salama yatafi.
Sai wajejen karfe goma sannan Mutallab yakoma gida, Amutuƙar gajiye yashigo.
MUTALLAB ASAD MUTALLAB
(labari mai taɓa zuciya)
Na
Billy s fari
Nana diso
RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU.
TAFIYAR BIYU TAFI DAYA
SHAFI NA SITTIN DA BIYAR.
NIGER
Faɗar irin halin da muke ciki Na baƙin ciki da takaici da damuwa bata baƙi ne Amma ko ƙallon mu kayi kasan muna ciƙin tsananin damuwa da kuma bacin rai. Tunda muka fito daga gidan mu sai muka samu gefen wani ɗan kango da Mai shayi yake zaune muka zauna, kallon yayata nayi tagefen ido sai kawai naga hawaye yana bin fuskarta Amma kuma tana ta kokarin karewa ƙada nagani, Wato su iyaye darajarsu da martabarsu bata taɓa faɗuwa sai har idan karasasu, su iyaye bango ne da ko da yatsage zaka iya jingina dashi. Amma duk loƙacin daya rushe to tabbas babu wani abun da zai maye maka gurbinsa. Duba da yadda mukayita yawo dangin mahaifiyarmu dana mahaifinmu domin su rikemu Amma kowannen su yakasa, wannan wani irin zumunci ne? Wannan zamanin namu kowa babu abunda yasani sai son ƙansa da ƴaƴansa. " Ya Allah" ƙalmar dana furta kenan ina ƙallon ledar da kuka zuba kayanmu da basufi kala uku uku ba. A hankali najiyo Nace " yaya kidaina kuka danAllah hakan yana dagamin hanƙali idan banga juriya agurinki ba yaya zankasance." " Nifa ba kuka Nakeyi ba Aicha kawai idonane yake ruwa." " Yaya ina zamuje?." " Aicha bansaniba kuma zaman mu anan bazaiyihu ba kinga yanzu zakiga masu shan shayi maza sun cika gurin,idan wasunsu nagari ne Aicha wasunsu zasu iya cuta mana ko suyi kokarin amfani damu."bata idda karasa maganarta ba sai ga wata katuwar mota babba baƙa ta faƙa agabanmu. Kallon junan mu mukayi kamin kuma wanda yake ciƙin motar yabuɗe yafito hakan yasani jikina yayi sanyi cikin raina nafara karanta addu'ar wanda kakejin tsoro "اَللّٰهُمَّ اكْفِنِيْهِمْ بِمَا شِئْتَ" sai da yakaraso tukunna sannan yace sannunku. " ina wuni babbar yaya tafaɗa nikuma nayi masa banza ina cigaba da Addu'a kasantuwar shine Alhajin nan dai da yayi kokarin yimun fyaɗe abaya. " Aicha ya hakuri? Rannan nake tambayar wani makaho danake ganinku kuna zuwa bara tare kwana biyu shiru yake cemun ai tsautsayi ne yakifta muku wuta har taci su baba, bakaramin tashin hankali nashiga ba jin wannan maganar dan haka nazo nace yakamata in taimaka muku." " Nagode da gaisuwa da kazo kayimun amma banajin ina neman taimako agurinka." " To Yanzu Aicha kamarke kiganki fa ga kira mai kyau ga kyau najiki kina zama agefen hanya idan wani yayi kokarin cutamiki fa?" Cikin masifa tafara magana tace " Bawan Allah kowane mai irin zuciyarka ta cuta? Nace kowane mai kokarin yiwa ƴar mutane fyade? bana bukatar taimakonka nace." Babbar yaya ce tace " A'a Aicha wannan ba tarbiya bace ba kina zagin mutum da girmansa." " Shi tarbiyace dayaso yayi amfani dani?". Sosai ransa yaɓaci yajiyo ya dauki rafar ƴan dubu daya ya watsa mata afuska yana faɗin " Haka zaki kare rayuwarki a tsiyace idan mu masu dukiya kin hanamu jindadi dake karnukan gari sune zasu kassara rayuwarki fitsarar rar banza da wofi kazantar ko fitsarar ko me kike taƙama dashi? Ta'ina na dace dake ke bari ingayamiki idan naso aɓatarmin dake wallahi yau dinnan magana takare, ina daga miki kafane dan ina kaunarki, kuma daga yau bankara nemanki da kanki idan rayuwa tayi kunci zaki kawomin kanki banza wacce batada galihu." " DanAllah kayi hakuri kayi hakuri yarinyace bata daɗe dashiga shekara 19 ba harda yarinta." Tsaki yaja yashige mota suka figa, babbar yaya ce tayi sauri jiƙinta na rawa tashiga kwashe kudin ita hakan dadi yayi mata ta wani bangaren ganin kudi har kusan dubu dari biyu yasa jiƙinta yana rawa tasaka acikin jakar hannunta data gwagwuye gaba dayanta. Sannan ta ƙalli Aicha dake faman kuka tace " Es-tu fou, il est un homme riche (ke mahaukaciya ce mai kudi ne.)" Yanzu yaya kudin kika dauka." " Idan ban dauka ba mubarshi wasu su dauka bayan kinfi kowa sanin shine abunda muke bukata yanzu, kina dai ganin babu wani mai jin kai a zuciyarsa kowa kansa yasani, Allah ne yakawo mana shi yataimake mu har ya watsa miki, yakamata ki tsayar da zuciyarki da wannan kukan dakikeyi kisani mutanen duniyar nan da yawansu san kansu da kaunar yaransu sune abunda suka sani ki daina kuka dan ɓatattun mutanen da suke ciƙin jarabawar ubangiji wacce dagani harke bamu huceta ba, ba'a jayayya da gomnati ko mai kudi ko sarauta, karfa ki manta mufa ba kowa baniba face masu bin titi yanzu, dangin iyayenmu sun gujemu sun nuna gazawarsu akanmu ki goge hawayenki mu samarwa kanmu mafita kicire tunanin komai Aranki kisani kowanne mutum zai iya yimiki rana ko akasin haka kuma zai iya cuta miki idan yaso hakan." " To yaya ko mukoma gidan kawu." " Kawu bazai taba rike muba kinsani Sarai." Isah mai shayi da zuwansa kenan ya karaso yana kallonsu. " zamanku anan hatsarine danAllah kutashi ku koma gidan naku itafa mutuwa dole ce haka kowannen mu zai tafi amma kuma tafiyar tamu bazata taba tsayar da komai na rayuwa ba." " Isah ina zamu koma mai gidan ne fa yakoromu." " To yanzu ku bakunada yan uwa ba kuje gurinsu mana." Aicha Dake share hawayenta tace " ils nous renvoient ( Sun koremu." Cike da mamaki yakara mai maita kalmar yace " ils t'envoient aller où ? (Sun koreku to kuje inane?)." Babbar yaya ce tace " nous ne savons pas où nous allons. (Bamusan ina zamuje ba)." Kai wannan rayuwa abar tsoroce natabbata da babanku ne zai iya rike musu yaransu Amma bakomai nidai shawarar da zan baku guda daya ce akwai gidan danake haya can kasa ashekara muna biyan Naira dubu talatin daki daya ne tak sai wani gefen daki da ake girki mun kai mu talatin agidan, jiya wata mata tatashi mai gidan tace na nemo mata wasu masu kama haya da kuje can ku kama sai kufara sana'a ko aikatau ne kuna ciyar dakanku hakan ina tunanin zaifi bin titi da kukeyi a wannan zamanin da mutanen banza sukayi yawa, êtes-vous d'accord ( kun Amince?)." Aicha datadago da idanuwanta da sukayi jajir tace " oui nous sommes d'accord (eh mun Amince.)." " Hakan dai yafi bazanso inganku kuna mata a gefena bayan mutane kala kala ne suke zuwa gurin shan shayen. Kullin kayan nasu suka dauka sukayi gaba wani yayi tunanin mahaukata ne tsabagen yadda sukayi datti kayan jikin nasu duk ya mutu." Wani babban gidane da suka shiga akallah dakuna sunyi talatin wasu nagefen tsakar gidan wasu kuma suna layin bandaki wasu kuma suna cikin dakunan su sai ihu akeyi." Ko da sukayi sallama babu wanda ya amsa musu sai hajiyar da kana ganinta kaga ƴar duniyar gaske tu attends (ku kutsaya) tafada tana karasowa, kai isa zaka kawomun su babu kudi ne?" je suis désolé, ils paieront plus tard ( kiyi hakuri zasu biya daga baya)." " Es-tu fou? ( kai mahaukaci ne?) Bashi ka dakkomin su." Babbar yayace ta saka hannunta ajakarta ta mika mata dubu talatin din." Aicha kuma tana kallon ikon Allah layin maza da mata a bandaki ga wasu na jan ruwa kowanne kataba jiran masifa yakeyi." Ke taji an kirata." Kinada kyau yarinyar nan Amma sai kazanta hajiyar tafada tana nuna Aicha." Isa ne yace kushige." " Su shige ina ban jamusu kunne ba kunajina wannan gidan da kuke gani gidan nazo kinzo ne babu isa babu takama layin bandaki dole ne haka layin debo ruwa bagidan wa'azi baniba babu ruwanku da abunda wasu sukayi ko suke kanyi ku kama kanku." Aicha ce tace tohm ganin wani katoton mutum ya fito da gajeran wando ajikinsa Babu kunya balantana tsoron Allah. Haka suka shige dan karamin daƙin nasu isah ne ya tsaya yana musu magana. " Yanzu kushiga ku huta zanzo na kawo muku shayi da kwai ko nazata ma bakuda kudi har inafadub idan nayi ciniki yau sai abata wani abun." " Dazu wani yazo yabamu Isah mungode Allah yasaka maka da alkhairi." " Kai babu godiya amina kinga ko dan mutuncin da mukayi da mahaifinku ban bari ku tagayyara bari dai sai nazo." " Mungode cewar Aisha tana kallon dan karamin dakin da babu komai ciƙinsa." Yanzu yaya yazamuyi da Abun kwanciya da girki?" " To aikinga amfanin kudin da muka samu yanzu zanje nasiyo koda kurfoti ne da gawayi da bokiti da buta kinga dai layin bandaƙin da muka tarar dole har fo sai nasiyo mana dan wannan layin yaritsa dakai kashiga uku, har shinkafa da abunda baza'a rasaba zan auno mana kizauna naje nadawo." " Yaya yanzu sana'ar me zamu dingayi?" " abincin siyarwa zamu dingayi aicha zanje can bakin kasuwa muna girkawa musiyar hayar kangon babu tsada sai kiga munsamu rufin asiri ke kuma zan bincika miki koda shara da wanke wanke ne sai kina zuwa kina musu ko?" Kallon yar uwartata tayi zata saka kuka ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 36 Chapter of 54