Mike tace " Ke kuka baya yimiki yawa dama Allah Yakawo mana isah da munyi tunanin nan? Komai zan siyo mana har hijjabi." " Ko nazo na rakaki?" " kinga kayanki Aicha har gwara nawa duk sun yage baikamata kina fita haka ba bari naje nadawo kinji." Daga mata kai tayi tazauna a kasa hawaye na wanke mata fuska.
******
Kasantuwar Gobe dauren aure yasa anata hada hada ƴan Niger ma sun iso duƙansu suna gidan Mutallab, kasancewa yace nan zasu sauka dukansu bangaren baki matan kuma suna bangaren tante suke yanzu ma shigowarsa kenan a mugun gajiye yake, sai da yafara duba part din meenal da aka gama jera mata kayan daƙi nagani nafaɗa ko ba'a sanar maka ba kasan ɗiyar wasu ce karatu sosai yayi asashen nata sai dayaga anfara kiran la'asar yafito daga nan yakoma bangarensa, yana sallama yaga tante da afrah azaune. " Afwan tante nabarku kuna jira naje masallaci ne." " To gatanan narasa yadda zanyi da'ita tunda kaga yau gidan amaren zasu fara shaanin su tunda sai gobe za'a daura nace jidda ta gayyaceta dinner dinta taje kada ace bakin ciki take musu ko?." " Yaya danAllah kace mata ta gidan Antyna zanje ni banson zuwa tasu umma." Batare da yace komai ba yamiko mata muƙullin motarsa karama gashinan kije dinner din idan bazaki iya driving ba ai naga samari agidan sai su kaiki ko?" To yaya tafada tana karbar mukullin tafita." Sai asannan ne tante ta miko masa tea flask ta miko masa ga wannan Mutallab kayi kokarin shanyeshi zuwa gobe garin habbatussauda ne ake dafashi da zuma saboda maganin sanyi ga Namiji." " Nagode Allah yasaka da Alkhairi." Kunhaɗu dasu kawu kuwa?" " Eh yanzu ma nalekasu kamin nashigo." " To danAllah kakula da kowa kaga shi yaso ka aure diyarsa yaga kuma kaki amincewa bance zasu cuta maka ba ban kumace bazasu cuta maka ba sai dai kuma banda tabbas kan daya dan zuciyar danadam batada kashi, kuma ku kula da karbar kudi gurin kowa." " Inshaa Allahu tante zan kula." Tohm bari naje kada su dada su nemini."
Sai alok'acin ne yaga text din sarsy data tutturo masa bai tsaya karasawa ba yadannawa numbarta blocking. Ganin kiran meenal ya tuna masa da tace shi zai dakkota gurin kwalliya Allah yasani bayason zuwa event dinnan ko kadan Amma bari ya dakkota in yaso yasa driver ya maidata. Wata Ash din shadda yasaka da black hula yayi masifar kyau sannan ya dauki mukullin motar range rover dinsa ya sauka kasa, kulle ko'ina yayi dan yaga Alamun rubutu ta daya bangaren Ko zuba masa akayi koma me akayi Allah kadai yasani. Kawu dake gefen motartasani yace " MashaaAllah Zakaje taron amaryar ne." " A'a kawu zan kaitane." " To ko zaka tafi dasu zainab tunda sun shirya." " A'a akwai mukullin mota gurin afrah sutafi tare yafada yana shigewa batare da yakara cewa komai ba. Cike da baƙin ciki yakauda kansa yana kallon babbar motar da Mutallab din yashiga. Jan kwafa yayi yafita." Cikin wani blue lace tashiraya kanta tayi masifar kyau bayan kwalliyar dake fuskarta dan su home services akayi musu head dinta ya dauru yadda yakamata daukar wayar tata tayi tace " Hello kazo?" " banason kawayenki ko daya meenal su hau motar dana aiko yafada da iko." " Tohm tafada." Sarsy dake gefenta tace " Nifa amotarku zantafi." " yace ku hau ta abokanansa shi." " Kamar yaya?" Kanwar mamah ce tace " Kamar yadda kikaji mana." " Okay tace tayi shigewarta ta fita tana kwafa." Faɗar haduwar da meenal tayi bata bakine su mama sundaɗe da hucewa daman iya su goma kadai suka rage gidan. MashaaAllah yafaɗa sanda ya sauke idanuwansa kanta har ta buɗe motar tashiga, zamanta keda wuya ya riko hannunta yana aika mata da wani fitinan nen ƙallo dayasata jin kunya lokaci guda."askim tafada tana dora hannunta ƙan daya hannun nasa." " oumm soulmate kinyi kyau da yawa anya zan iya barinki zuwa taron nan yafaɗa yanayin jiƙinsa na kokarin janzawa." Zaro idanuwa tayi tana faɗin " Are you playing?" Da wata ƙalar kasalalliyar murya yace " Uhmm." " DanAllah kayi hakuri muje kaga duk motocin sun tafi mutane suna jiranmu." Cikin sanyin murya yace " ina ƙaunarki meenal gayunki yana rikirkitani."
MUTALLAB ASAD MUTALLAB
(labari mai taɓa zuciya)
Na
Billy s fari
Nana diso
RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU.
TAFIYAR BIYU TAFI DAYA
SHAFI NA SITTIN DA HUƊU.
Mutallab kuwa koda mahaifinsa ya faɗa masa zancen hadda na Jiddah ɗin za'a haɗa fatan alkhairi kawai yayi ba tare daya ƙara zance ɗaya ba akai. Ana saura sati biyu ɗaurin aurensu aka kammala ginin gidan Walid, gidan dai-dai shi tsarin macce ɗaya sai ɓangaren mai gida yayi kyau sosai har ya gaji, haka ma ɓangaren Jalil duk da baiyi komai ba Mutallab yasa an sake masa fenti an kuma sauya wasu abubuwan amfani kasancewar an zauna acikinsa, wanda hakan yasa Afrah da tánte Sajida suka koma a daya mension ɗin na Mutallab da tuni aka kammalashi, part huɗu ne aciki, ɗaya part din daya fi kowane tsaruwa daga farkon fuskar gidan shine na maigida, sai guda biyu dake kallon juna yanayin tsarinsu da komai iri ɗaya, sai part ɗin ɗaya dake can gefe hannun daman na Mutallab shi kuma part ɗin Afrah ne da tante sajida , sai wani ɗauki dake can gefensa b.q ne, ga gurin shan iska da shakatawa da akayi daga bayan gidan, daga wajen gurin gate kuma ga dakunan masu gadi, sannan ga wata waya data zagaye gidan alamun wayar tsaro ce, sai filin motocinsa Da a yanzu sunyi guda 6 ajere, iya tsaruwa da haɗuwa gidan yayi, dan daga tante har afrah duk ƴan kauye suka zama duba da yadda kayan suka gama haduwa da tsaruwa, kowannen su addu'a ne kaf bakunan su Afrah da tante da suka shiga bangarensa kasa magana sukayi ganin wani irin tsari da haduwa a bangaren ga wasu tafka tafkan gadaje, hatta tv dinsa irin ƴar zaunen nan ce saboda haɗuwa, sai da suka huce bangarensu Nan ma sunsha kallo dan daki guda uku ne kowanne da gado aciki sai palour da babba da bandaki guda biyu akowanne dakuna sai kuma idan kafito wani madaidaicin kitchen da kayan abinci da komai aciki, tante sajida gidannan yagaji da haduwa." " Ni wallahi ƙaina har juyawa yayi saboda haɗuwa duk na gigice ma." Dariya afrah tashiga yimata tana faɗin Aikam dai ya haɗu sosai, ganin wayarta tana ringing yasata jan tsaki takatse haɗe da blocking din Numbar. Tante ce ta bita da ido tace " Ke afrah menene haka wai ke laifi baya hucewa agurinki saboda Allah tunda har yagane kuskuransa akan wani dalili bazakiyi masa hakuri ba bayan kinason yaron nan, nagama dai makarantar a final year kike." " Nifa tante banasonsa bana kaunarsa yanzu wallahi bazan iya auransa ba duk yafitarmin akai." " To Allah yaui miki zabin da yafi Alkhairi kitashi kuje tunda driver yana nan wannan dinkunan namu kikai mana su ko." " Yanzu ma kuwa Umma tafada tana dariya har sarkq da takalmi duk zanbiya insiyo mana." " To ki dauki kudi ajakata." " A'a akwai a hannuna idan basu isa ba nakiraki." " To Allah yakiyaye.
Basu daɗe da dawowa daga tafiyar da sukayi na yanzu ma tana zaune gaban dady yana masu magana akan event din da zasuyi. " Nifa dady bazanyi dinner ba Zandaiyi mother eve da kamu kadai sai yini da za'ayi." " To hakan ma ai daidai ne Allah yataimaka kayan naku sunzama ready." Mumy ce tace " Komai sun iso dady hatta takalman mu sun iso, Nace ko zakayiwa can gidan kakannin nata magana sai suyi jeran?" Kallon mumy yayi yace " Banason rigima da kananun magana Akwai kamfanin da yayimana na gidan nan suna can na sunfara haɗa mata komai duk yadda naso kayan su wadata sai dana kara mata da set din kujeru anan." " Gidan babbane kenan?" " Babbane sosai Munji da kamal da safe Naga komai dan haka kudai kucigaba da shirye shiryenku." Meenal ce tace Dady mungama komai fa babu abunda bamu gama ba." Sai alokacin ne dady yasa aka shigo musu da kayan lefen daga can store da ya adana kasancewa sanda suka kawo basa kasar. Mumy ce ta saki baki tana kallon ikon Allah set ɗin akwati biyar ta lissafa kamin meenal tawani daka tsalle tana fadar " wow this is fantastic duk nawane dady?" Dariya dady yayi yace duk Nakinr meenal gasunan." Aikamin yarufe baki tashiga snapping din akwatuna, a wannan lokacin ne mumy taji zuciyarta tadan tsaya har tanawa diyarta fatan samun miji Nagari da har yanzu shiru itama." " Allah yasanya Alkhairi dady yabasu zaman lpya bari Naje Nakarasa da masu event dinnan sai nazo mu bude, Meenal kikira gidan kakanninki kisanar dasu kokuma akai musu sugani ko?" " Su dai zo sugani zaifi mumy." Ba karamin dukiya ya narkar acikin lefen ba yazuba kudi sosai da sosai, kayane masu mugun tsada karamar atamfa babu manyan jakunkuna da lace haka ya dankaramata su, murna a wajen Meenal ba'a magana nan take ta shiga kiransu Sarsy da Nucy dasu Zee ta sanar dasu akan ankawo lefen ta fa, nan ma tagayawa su grandma kamin kace komai gidan ya dinki da mutanen arzuki kowa yazo sai sambarka da fatan zaman lafiya wasu daga cikin ƴan uwan kuma babu abunda suke faɗi sai Wazata aura ne?. Da yamma kuma masu gyaran jiki sukazo kasancewa jibi ne za'a fara biƙin." Mumy kuma sai data gama komai sannan tashiga kitchen ta dakko budurwar kazar da tasaka aka siyo mata ta wanke ta tas sannan sai ta dakko ridi(kantu) wankakke gwangwani daya ta zuba aciki, ta dakko nonon rakumi rabin gwangwani tasaka, tasaka attaruhu da Albasa da tumatur da tafarnuwa sannan tazuba, MINANNAS cokali 1 table spoon, tasaka sassaken bagaruwa cokali daya sannan sai ta haɗa da saiwar malmo cokali daya table spoon tasaka tasak kanin fari guda uku citta kadan, cinnamon shima cokali 1 table spoon ta zuba sannan ta saka manja cokali 1 ta zubq wadataccen ruwa ta rufe ta bar kitchen din. Sama sama dai grandma tayi hira da'ita kamin suma su fice sai kannen mama kadai da suka zauna sai angama biki zasu tafi." Mai saukin kan aciƙinsu ce tace " Mumyn meenal yarinyar nan taki fa sai kin kara gyarata ko girki bata iyaba haka za'a kai masa ita?." " wai me ruwanki ne? Nagayamiki ai nadingayin order." Mumy ce tace " Babu yadda banyi da'ita ba wallahi taki yarda wai ita amarya ce tayaya zata shiga kitchen tun kamin mutafi nake fama da'ita." " kyaleta mumy tunda zata dinga order." Hararata meenal tayi tana faɗin Mumy yauma zan shiga ruwan zafin?." " Kije ki dora dakanki idan kinason shiga " " wayyo mumyta tayaya amarya zata shiga kitchen saboda Allah mumy ina aka taba haka? Gaskiya A'a nidai." " To sai ki hakuri inji anty dinta tana hararata." Zee ce tace " Bari nadafa mata menene zan hada?" "Yauwa aminiyata kinga zakiga bagaruwa kisa gwangwani daya sai, garahuni cokali 1, sai kaninfari cokali daya, sai sassaken bagaruwa cokali daya, sai salt cokali daya ki dafa ki kaimun toilet aminiyata." " shegen san jikin tsiya anty dinta tafaɗa tana barin daƙin haɗe da jan tsaki." " ko me ruwanta dani." Mumy data ji kitchen ta zubo mata kazar ta ajiye mata akusa da'ita haɗe da faɗin gashinan sai ki cinye yanzu saura ki tsaya shiririta." " mumy babu dadi fa jiya haka kika bani wannan hantar duk tafi daɗi." " To wai meenal ƙintabajin inda akace miki magani yanada daɗi naso ace gidan hajiyata kikaje kika kwana biyu Amma tafiyar nan ta cinye mana lokaci." " Mumy to natafi yanzu mana jibi sai na dawo." Murmushi mumy tayi tace " uhmm ai bakomai yanzu ga wannan garin habbatussauda ne cokali biyu da zuma gwangwani daya ki dinga sha safe da yamma da dare duk wasu cuttuka dake jiƙinki zai miki magani ni na fita." Sarsy dake cike da baƙin ciki da hassadar irin tarin Ni'imar da Allah yayiwa meenal a yanzu dan dakyar ta'iya kallon lefenta ma ga uban kayan arzukin data samu sai yanzu taji duk ta tsani meenal din dan haka zatayi amfani da abotarsu ta lallata mata rayuwa." Sarsy bakya magana tun dazu lafiya." " Ke banajin dadi ne inaji ma gida zan koma nadawo anjima." Harararta meenal tayi tace " Bakida kai abikin nawa." " Sai kiyi." Meenal ta miƙe tace " bari naje na dakko hadin tsumin can sai naci kazar dashi." Ganin haka yasa sarsy saurin daukar wayarta rashin sanin sunan da meenal tasaka wa Mutallab yasa taji babu dadi sai ta koma call log dinta nan taga kira daga askim sosai, hakan ya tabbatar mata wannan ce Numbarsa dan haka tayi saurin kwafa ta ajiye wayar duk abunda takeyi zainab dake bakin kofar tana kallonta kawai tayi sallama tashigo meenal na biye da'ita, bandaki ta tua takai mata ruwan da zatayi sit bath din sannan ta rufe." Sarsy kuwa murna takehi cikin ranta dan kuwa zatayi amfani da damar nan ta hana auren nan wallahi tunda ba ita bata samu mai kudi ba kuma kamal yace bazai aureta ba to tabbas sai tayi duk wani abu da zata hana aurennan nasu. Message tashiga ta rubuta. " Amincin Allah yatabbata Agareka nasan bakasanni ba Amma sunana sarsy kawar meenal tun ta yarinta, A gaskiyar magana wallahi baka dace da'ita ba meenal batada tarbiya gashi mahaifinta ya lallata ta da fitsara da kudi sannan tana bin maza sosai akwai wani Bestie dinta har ciki yataɓayi mata muka zubar, kai kuwa mutumin kirki ne kuma babban mutum da yanzu ake alfahari dashi bana maka fatan auran kazamar yarinyar nan kuma fasiqa shawara tarage gareka, yarinyar da bata ganin mutuncin matan ubanta, bata daraja ƴan aikinsu ga bin maza ina kake tunanin kadace da'ita? Shawara ta rage gareka nidai nafadi gaskiya ta." Sai data gama ta danna send. Daga nan ta dauki jakarta tayi ficewarta dan zamanta anan zai iya sawa zuciyarta ta buga."
*****
Boka kana gani yaron nan babu abunda yayiwa diyata bayan kacemun zaizo ya tambayeni harma yabani kudi. Wani ƙalar ihu bokan yayi sannan ya buga wata kasa haɗe da faɗin " bazamu iya ba bazamu iya ba Tabbas bazamu iyaba shi din mai ambaton Allah ne mai zama da Alwalah yana yawan zikiri ga karatun Al'kurani zokiga ya nuna mata wata kwarya mai ɗauke da jini sai ganin mutallab tayi akan kujera baka kur'ani a hannunsa yace mata " Kingani ko kinagani ko?" To mutum ne mai tsanin Ambaton Allah ya kona mana aljanu sunkai dari nazamu iya aiki akansa ba, Nayimiki aiki akan babansa nayi miki aiki akan kishiyarki amma shi bazamu iya ba kuma duk wanda yace miki za'a iya aiki akansa karya yake miki sai dai idan wani abun za'a amfani dashi ko kibashi kudi ya karba ayi aiki akan kudin kokuma kisamo maniyyinsa kokuma kisamo gashinsa to da wannan ne zamu iya yimiki kokari kokuma inyi miki aiki kidafa jan nama ki bashi." " Nashiga uku boka to ai ko ada baya cin abun hannuna kuma ina zanga gashinsa?." " shiyasa nace miki zamuyi amfani da matarsa saboda kingani yayi wani tsafi sai ga meenal zaune acikin bandaƙi acikin roba, bata addu'a sallah ma haɗewa takeyi yanzu da zan tura mata aljanu yanzu zasu shiga jiƙinta saboda addu'ar bandaƙin ma bata iya ba, Amma kuma naga wani haske agabansa bayan ita wanda har yanzu nakasa gane menene." " To yanzu boka sai munjira yarinyar." Wani irin ihu yayi da haukansa sai ga wasu magunguna sun wado yayi amfani da tsafi suka zama berayi yakarayin amfani da tsafi suka zama kwarya wannan kwaryar daga ranar data tare zaki bude kwaryarnan sai ki ambaci sunanta sau 7, sai ki samu jan nama ki watsashi cikin kwaryar nan zakiga beraye suncinye daga ranar yarinyar zata rasa sukuninta har sai ta ziyarceki daga nan wannan garin maganin ki sakashi a inda zata zauna to sai abunda kika cemata." Murmushi Umma tayi tana dire masa bandir din ƙudi. " Tsinuwa da La'ana sukara tabbata agareka boka." " Kifita da gudu da gudu kada ki soma sallah yau ko gobe sai ranar juma'a kaɗai sannan kada kikara tsarki idan kikayi fitsari idan, muna son jinin hailan yarinyarki zamuyi mata aiki akan mijin nata itama." Murmushi tayi tace " Angama boka zan ajiye maka kusa da kwarya ka aiko akarba kaga ina da nisa da garinnan tafiyar kwana biyu nakeyi kamain na isu.ki ajiye mana shi a bolar gidanki zan aika aljanu su daukamin.
MUTALLAB ASAD MUTALLAB
(labari mai taɓa zuciya)
Na
Billy s fari
Nana diso
RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU.
TAFIYAR BIYU TAFI DAYA
SHAFI NA SITTIN DA UKU.
Misalin ƙarfe bakwai na safe bayan sunyi sallar asuba sun koma bacci sukaji muryar maza cikin gidan, babbar yaya ce tafara ji tayi sauri tamiƙe tare da bubbugar Aïcha ta tashi, saurin ɗaukar mayafansu sukayi suka saka kafin su miƙe su fito daga cikin ɗakin, daga asalin maigidan har ma'aikatan daya shigo dasu zasu fara masa gyaran gidan yana nunnuna masu wuri ja sukayi turus suna kallonsu cike da mamaki, kallon Aïcha dake faman murza idanuwanta alamun baccin bai isheta ba babbar yaya tayi tana ɗan taɓo kafaɗarta, wanda hakan yasata buɗe idanuwanta akan maigidan dake tsaye har lokacin yana kallonsu da sauri suka ɗan russuna suka gaishesu, sai daya ɗan ɓata rai sannan yace, "lafiya, me kukeyi acikin gidannan? Ina dama ai kuɗinku na hayar sun ƙare kuma mahaifinku bai biya na wannan shekarar data shigo ba har ya mutu". Basu ce komai ba suka sadda kai ƙasa yaci gaba da cewa, "To nasan dai kunsan wannan zancen kawai tunatar daki nayi, dan haka ku tattara naku inaku kubar mani gidana gyara za'a yimun nasamu wasu ƴan hayar na zuba". Ciki suka juya ba tare da sunce masa ƙanzil ba suka ɗauko kayansu suka fice daga gidan tunda dama suna sane da duk abinda yafada, dan haka basu ji damuwar kalaman nasa ba duk da basu taɓa tsammanin zai waiwayi gidan da sauri haka ba bayan iyayen nasu ko wata basuyi ba da rasuwa.
*************
Washe gari bayan Mutallab ya shirya yafita kai tsaye filin da zaya gyarawa Walid ya zauna shi da iyalinsa ya nufa shi da Jalil dake zaman jiran fitowarsa tun ɗazu, koda suka isa wajen tuni ma'aikatan da Jalil ya nemo masa da zasuyi aikin sun iso, dan haka nan take yayi masu bayanin yadda tsarin gidan yake da yadda yake so sufitar dashi, bai bar wajen ba sai daya tabbata anfara aikin sannan suka wuce, kai tsaya shagon daya bayar da kwangilar da za'a haɗa masu lefensu suka wuce, tuni an gama haɗa komai yadda ya buƙata nashi ɗai ne ba'a ƙarara ba saboda akwai wasu kaya da suke kiran su iso daga dubai a ƙarasa haɗa nashi lefen saboda sanin ko shi waye sun san dole ayi harkar girma aciki ta yadda zaai ji daɗi ya yaba kuma su ƙara janyowa kansu customers. Kallon Jalil yai ya nuna masa akwatunan dake jere har set biyu yace ya duba idan akwai abubuwan da yake buƙatar ƙarawa ciki yayi masu bayani na matarsa ne, sai wasu akwatunan agefe set ɗaya amma masu ƙwayar shida da mit ɗinsu ne suma sunji kyau har sun gaji sune na Walid, kallonsa Jalil yai haɗe da cewa, "Wai yaya meyasa kake son kashe kuɗaɗen ka haka? Tun da aka fara zancen auren nan komai kai kakeyi kaƙi bari muyi koda abu ɗaya ne, account ɗina maƙare yake da kuɗaɗe saboda duk abinda na yunƙura zanyi sai naga kayi mani shi, dan Allah ya Mutallab kana bari muna rage abubuwan da kanmu muna". Murmushi yai daga kan kujerar da yake zaune haɗe da cewa, "To meye amfanin kuɗin nawa Jalil idan har banyi maku ba? Ina da wasu ne aduniya da suka fiku?"
"Amma ya..." Kafin yaƙarasa Mutallab ya ɗora yatsansa saman bakinsa yana cewa, "Shiii..ya isa haka Jalil, kawai kayi abinda nace". Duba kayan Jalil yai komai yayi kyau sosai ya kallesa haɗe da cewa, "komai yai ranka ya daɗe".
"Ok anjima sai kuzo kai da Walid ɗin ku kwashe akaiwa tánte tagani sai ku nemi abokananku muje akai tunda naga yanzu haka akeyi ko?". Jalil na murmushi yake sosai ƙeyar kansa haɗe da cewa, "eh ranka ya daɗe mun gode Allah yaƙara buɗe". Mutallab bai jira ya ƙarasa ba yana girgiza kai yamiƙe suka fice suka wuce kasuwa ɗan idan yabiyewa Jalil yanzu ne zai yita sakashi surutu agaban mutane akan abinda issue ɗin su ne na gida. Duk wanda ya samu labarin daurin Auren nasu su uku har da Walid da tuni Mutallab keta shirye-shiryen yadda bukin zai kasance sai yayi mamaki saboda ganin ƙanƙantar Walid ɗin tayi yawa kamar bazai iya riƙe macce ba, musamman da ake ganin ai baida aiki ko sana'ar yi. Aunty Amarya kuwa tayi kuka yafi aƙirga ganin irin hidimar da Mutallab keyi akan ɗanta lokacin da duniya ta juya masu baya, musamman da taga lefen daya haɗa masa wanda da suka ɗauko Walid ɗin yace akai nasa gidan Hajiya wato mahaifiyar Aunty amarya, acan taje tagano lefen, tayi nadamar abubuwa masu yawa da tayiwa Mutallab ɗin da ƴan uwansa wanda take ganin lokaci yayi daya dace tanemi gafararsa, dan haka data dawo daga gidan mahaifiyar tata tace Walid ya kaita gidan Mutallab ɗin, lokacin yana zaune a farfajiyar gidansa saman wata resting chair yamiƙe ƙafafuwansa yana karatun jarida sai kwalin juice da gorar ruwa da kuma glass cup dake gefensa ajiye koda zai buƙata, jin ƙarar an buɗo ƙofar gate an shigo ya sashi ɗago kai, mai gadi ne ya gani ya ƙaraso wajen cikin hanzari ya durƙusa har ƙasa yana gaishesa tare da sheda masa anyi baƙi dan hanasu shigowa yai, izini ya bashi daya shigo dasu ciki, dukkansu baki suka saki suna kallon tsaruwa da haɗuwar gidan mension guda dashi daya haɗa komai na ƙawatuwar gida da zaisa agani ace ya burge dan Walid ɗin ma bai taɓa shigowa ba kawai dai yasan fuskar gidan daga waje kuma yasan cewa na ɗan uwan nasa ne tunda tasamu labari daga mutanen anguwa tunda kusan duk wuri ɗaya ne, garin kallo Aunty amarya da tayi baƙi ta rame tamkar ba ita ba har tuntuɓe tayi sai da Walid ya riƙata, Mutallab na ganin sune yasa mai bayin ruwa dake can ɓangarensa ya kawo masu kujeru, sai daya rufe jaridar ya ajiye fuskarsa ɗauke da murmushi yace, "Aunty sannu da zuwa ku zauna ko". Yana miƙa masu kujeru, cikin tsokana yake kallon Walid yana cewa, "Ango kasha mai". Sosa ƙeyar kai ya shiga yi cike da jin kunya kafin ya ɗan sunkuya yana cewa, "Barka da hutawa ya Mutallab ina wuni?"
"Lafiya kalau Walid ya hidima? Anata shirye-shirye ko?" Ɗaga kai Walid yai yana dariya yakasa zaunawa kan kujerar Aunty amarya kaɗai ce ta iya zama jikinta a sanyaye, "hope babu wata matsala ko?" "Babu ya Mutallab mungode Allah yaƙara buɗi da arziki" "to Amin Walid, Aunty Ina wuni". Mutallab yafada yana maido hankalinsa ga Aunty Amarya da tayi tamkar an tsoma kaza cikin ruwa zafi, ɗari kai tayi idanuwanta cike tab da ƙwalla tace, "Lafiya kalau Alhaji ya kokari da hidima da ɗan uwanka da kakeyi? Allah yai maka Albarka ya saka maka da alkhairi" Taƙare maganar tana fashewa da kuka, "Amin". Mutallab yace yana kallonta tana kukan har tagama tana share hawaye yace, "Aunty ina fatar dai babu wata damuwa ko?"
"Babu Mutallab damuwata ɗaya ce dama yaran nan kuma alhamdulillah ka magance mani ita alokacin da suke gangar lalace mani musamman shi wannan babban, shiyasa nace bari nazo na nemeka yafiyar abubuwan da nayi maku kai da ƴan uwanka, tabbas akwai don zuciya amma har da sharrin sheɗan Mutallab, dan Allah kayafe Mani". Taƙare zancen tana ƙoƙarin zamewa kan kujerar ta durƙusa masa saurin tarota yai haɗe da cewa, "a'a Aunty amarya keɗin matsayin uwa kike agareni tunda matar mahaifina kike, dai-dai da rana ɗaya ban taɓa yimaki wani kallo ƙasa da hakan ba, na yafe maki Allah ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 37 Chapter of 54