Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
NA TAMANIN DA SHIDA *MUTALLAB ASAD*      Arewabook:- billysfari       Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.      A hankali tace " kayi hakuri bacci nakeji kuma inada makaranta sai da Safe yaya agaida Antynmu." Sosai yashiga ɓacin rai ganin ta katse masa kiransa, rasa yadda zaiyi da ransa yayi sai ya huce bangarensa kawai yana shiga yatarar da meenal baje ƙan gadonsa daga ita sai towel tanacikun gurasa, Wani sanyi yaji Aransa tunawa da yayi ya kusa samun karuwa shima, tsaf ya ƙalleta yanajin yadda jiƙinsa ke zubawa. " Dear gurasar tayi miki dadi? " murmushi tayi masa tace " Tayimun sosai Nama koshi kasamin afreezer sai kayimun warming gobe." Okay yace mata sannan yahuce ya tafi yasaka mata ko da yadawo bandaƙi yashiga yayi wanka sannan yayi sallah kamin nan yakashe fitila din dakin ya kwanta jin yadda ya rungumota ta baya yasata kokarin turje masa haƙan yasashi kallonta yana faɗin " Ya kikeso nayi Meenal ke nafaranta miki Amma ni bazaki faranta mini ba." " To ni nagaji kana takurawa ciƙinnan nawa." " meenal kinsan ni ba rago baniba kawai ina maneji ne but ke ko damuwa bakyayi oya jiyo ki dan tattabani dear." " A'a ni wallahi sai dai kahakura babu wani tabaka da zanyi nagaji." Sautin numfashin da tasaki saka makon yadda ya aza hannunsa aƙan breast dinsa yasa yadan kara shiga ciƙin yanayi sosai yajiyo da'ita yashiga kissing dinta kamar yarabata da baƙin nata cikin mintunan da bazasu gazaba ta firgice gaba dayanta shima yafaɗa duniyar da bazai iya bayaninta ba, duk da yadda take tuttureshi Anma hakan bai hanashi samun nutsuwa da'ita ba ko da ya kammala dogon Numfashi yasaki haɗe da kara rungumarta yana shafa mata cikinta da shi mata albarka. Wacce kalar magana kakeyi boka Abune da bazai taba yihuba ba wallahi Dole a dauki mataki dan kuwa ansamu akasi da kwaryar nan. " Hahhahahahaha nasanar miki indai kika barshi yafara Azkar ko ambaton Allah to tabbas lamarinki zai chabe yanzu ga wannan nan kisaka musu a abinci Amma ki tabbatar kin bar maganin acikin wandonki na tsahon awanne 7 sannan sai ki zuba musu indai sukaci ina tabbatar miki komai sai da izininki zasuyi bazasu taba gaddama gareki ba." " Allah yakara tsine maka boka Ina godiya akwai tukwici mai girma gashi ta ajiye kudin sannan ta tashi da rarrafe tabar inda boƙan yake. Tafiya ce mai nisan gaske kamin ta karasa gida ko data koma tasaka maganin cikin bujenta, ganin ƴan sanda da motarsu harabar gidan yasa hankalinta mummunan tashi. Can tagano Abba yana faɗin " ku tafi dashi wallahi baya zamarmin." Jamil dake faman fiffizgewa yasa wani dan sanda kifa masa mari. Jin shigowar mota yasanya su duka waiwayar gurin ganin Mutallab ne sanye da coffee din shadda shima da mamaki yabisu yana faɗin " Lafiya?" Umma da fitowarta kenan tayi caraf tace " ina lafiya kana gani za'a tafi da dan uwanka wai yandamfarane suka kamashi suka damfareshi har million goma shine fa mahaifinka yake ta tijara." Baice komai ba yace " Allah kyauta Abba barka da safiya da fatan katashi lafiya." " Lafiya lou Mutallab danAllah ko menene zasuce kada kashiga maganar nan." " To Abba yafaɗa yana ayyanawa aransa dan komenene za'ayi to tabbas hima baya shiga dan daga shi ya jamil din har uwarsa ba mutunci ne dasu ba." Daman maganar shagon nan ce takawoni Abba." " Ko baku taimaka masa ba zanyi yadda zanyi infito da yarona kai kuma ta Nuna Abba uhmm muzuba sannan tayi shigewarta daki. Mutallab kuwa ko kallonta baiyi ba abba ma haka har suka gama tattaunawarsu sannan yabar gidan zuwa kasuwa. Kada kikara shigomin bangaren mijina nagayamiki banason rashin mutunci kunzo kun nannade gida sai kace na gyatuminku abarni in samu nutsuwa da mijina Amma bazakuyi ba Nagaji wallahi munafukai kuma kishiya sai dai ke Afrah kishiga gidan mai mata baniba. Batare da Afrah tace komai ba ta ajiye abincin da tashigo dashi a dinning sannan tafita. Hakan bakaramin kona ran meenal yayi ba ganin bata tanka mata ba hakan yasata ihu tana faɗin " Shegiya mijin auren ma ya gagareki duk kyanki ko dayake umma tace haka zaki mutu bakiyi aure ba." Da dan zafi Afrah ta kalleta tace " Au haba ashe ku kuke da rayuwa danAllah malama kiji da kazantar dake damunki da rashin hankalin dake damunki Amma idan kikace zakiyi dani wallahi sai kinji ajikimki tunda Nalura ke ba tarbiya ce dake ba kuma idan nashiga gidan mai kishiya menene ai ba haramun baniba indai bazan zama macce kalarki ba Ai Alhamdulillah." "Ni kike zagi Afrah nace ni kike zagi?" Da zafin kai Afrah tace da abunda zakiyi ne ? Nace da abunda zakiyi ne? Gani gabanki zo muga." Hakan yasa meenal dan tsayawa dan ita sai bakin amma indai ajikine to tabbas cutarta zatayi " muzuba agidannan sai nahanaki nutsuwa da duk wani jindadi.dakike takama dashi sha sha sha kawai." Tsaki tayi ta barmata dakin." Me isa zaki biye mata Afrah tante tafada tana kallonta." Abubuwanta sunyi yawa tante kinga yadda take cimun mutunci wallahi Allah yayana baiyi sa'ar mata ba kiduba fannah ki duba matar walid abun sha'awa kiga yadda muke jituwa dasu sun daukeni kamar yar uwa ita kuwa wannan ballagazar babu abunda tasani sai sakalci." " Allah ya kyauta to Amma gaba karki kara biyemata taci Albarkar yayanki kinji kinga kada taje ta zugashi tace kinyi wani abun da bakiyi ba ko?." " To inshaa Allahu tante. Ke atine idan kingama abincin kiyimun magana akwai maganin da ake zubawa Alhaji aciki. Cike da girmana atine tace to Umma. Ganin umma ta futa yasata saurin nufar bangaren Anty ko dataje taba zaune hannunta rike da carbe alamun lazumi takeyi. Sai da Anty ta idar sannan tace " atine lafiya kuwa?" " To nidai ina tsaye ina girki waccan umman tace idan nagama inyimata magana wai za'a saka maganin da ake sakawa alhaji tsakani da Allah nasan batada imani ballantana tausayi shiyasa nace bari dai nashigo nasanar dake kina ganin wahalar da mukasha wancan karan Allah ya taimakemu abun nata nata koma mata kinga ai bamu bari takara cutarmu." Da dan murna Anty Amarya tace " nagode sosai Atine Hakan yasa zaman amana mukeyi yanzu kinsan yaya zakiyi ki dauki flask dina ki zubaw abba abinci ciki irin nata sai ki bari sai tagama barbadawa sai ki dakko nawa natan kuma ko dabbobi kar abawa sai azubar kawai ashara." " Eh to gaskiya kinkawo shawara ai wallahi sai kindagr sosai dan dazama da mashirukai masifane zama da alwala da zama da dankwali ko.motsi zakiyi anty ki ambaci Allah kinsan su irin matan nan basa gajiya fa da shirka sai sunga kasa ta cika musu baki." " Bakiga ba hatta yaran yanzu duk na dorasu kan ambatan Allah ai rayuwar yanzu babu zama wallahi atine maza kije kar ta fahimci kina nan." Ko da tagama abincin yadda Anty tace bayan tagama abincin haka tayi kuwa ta canza kular batare da umma ta fahimta ba takaiwa Abba shashinsa duba da yau girkinta ne dan tuni ya raba kwana. Ko dayaje kasuwar yadan jima acan duba da ayuka dayatarar sannan akwai transfer da sabbin shagunansa da ake tattaunawa sai wajejen biyar sannan ya isa gida amugun gajiye. Yana zuwa yatarar da meenal sanye da wata doguwar riga milk tana kallo falonsa yayi kaca kaca batare da sannu da zuwa ko wata magana mai dadi ba tace " Nagaji da iskancin kanwarka ni ba'arta bace ba kayi mata magana wannan daƙin mijinane bana bukatar ganinta aciki." " Haba meenal babu sannu da zuwa babu komai sai kitareni da wannan maganar?" " Nidai nagayamaka kashiga tsakaninmu." " Allah yashiryaki yafada yana shigewa cikin dakin nasa ganin pant dinta da bra duk akasa yasashi kwashewa yasamata a gefe guda sannan ya gyara gadon daga nan kuma ya huce toilet shima sai da ya tabbatar ya tsaftace yafito. Duba kan dinning yayi yaga babu komai da dan mamaki ya kalleta ganin tayi amai agefen kujerar amma bata damu ba ga yawo dayaga tana tofarwa anyhow. " " Zan kauda kaina akomai amma banda wannan Wallahilazim kikara tofarmin da miyau saina sabamiki nagayamiki." Turo bakinta tayi tace " To yazanyi yana taruwa abakina ?" " Bakiga tissue ba? Nace bakiganta ba? Me isa kikemin haka ne? Me kika dauki kanki meenal darajar abunda ke cikinki yasa nake daga miki lafa amma wallahi bazakizo bangarena kiyimun kazanta ba kije can naki." Tsaki ta buga tatashi tabar falon tana maganganu bai kulata ba yakira afrah wannan ne karo na farko datace masa kanta na ciwo duk da yasan karya takeyi amma sai ya kyaleta dan ya lura lamarin meenal ne yajawo hakan yasashi tashi yafita domin neman abunda zaici dan gani yakeyi yanzu yafara takura musu ita da tante. **** Kasantuwar suna biki acan maradi hakan yasa dada tasaka driver yakaita duba da dangin mahaifin nata ne, sosai tayi shigar doguwar riga ta atamfa ja tayi mutukar amsar jiƙinta tayi kyau ko dataje cikinsu sai suka dinga mamakin yanayin yadda Ta kara kyau ha diri da Allah yabata ganinsu kawu yayan mahaifinta sunzo suma haka tabisu ta gaidasu babban su babansu ne yace zasuyi magana dan haka sai ta fita can gurin shimfidarsa kasancewa ba'a fara taruwa ba. " Aicha comment vas-tu (aicha kina lafiya). Cikin girmamawa tace " lafiya lou kawu." " Mashaa Allah dazu kawunki yasanarmini maganar Mutallab amma nake ganin Aicha dadai kinyi hakuri kin aureshi duba da shi wannan wanda yabayyanan kamar bada gaske suke ba dan shi kawun nasa ma yayinmun magana amma nasanar dashi akwai wanda yafara neman aurenki, ai ko dan yadda dada ta nuna tsantsar kauna kanki bakya guji jikanta ba duba da yadda akacemun yana mutukar kaunarki yanzu ke yaron kirki kamar Mutallab ai bakya tsaya kina ja'in ja da iyayenki ba kiyi hakuri danAllah kiyi aurenki nasan bazasu hanaki karatunki ba ni kaina yadda nake ganinki dinnan hankalina zaifi kwanciya ace kina karkashin inuwar wani ko kinga kinada garun jiki mashaa Allah." Cike da girmama irin tata tace " Kawu indai hakan shine zai faranta muku na amince." " Yauwa yar albarka Allah yatabbatar da alkhairi kinji zuwa wani satin sai ayi magana dasu." " Cike da kuka tabar gurin dan ita harga Allah batason Mutallab duba da abubuwa ko datashiga gidan bata zauna ba saima sallama datayi musu ta nufi gida." " Muhammadur rasulilahi saw ni dada me mutanen nan sukayimiki naga idanuwanki sun cicciko? Ko maganar auren ne bakyaso?" " A'a dada babu komai kawai .." " Kinga aicha karki biyewa wannan dattijayen iyayenaki ki cuci kanki idan baki amince ba wallahi Allah anrufe maganar nan Har abada." " Dada ko dan ke bazanki jininki ba alokacin da mutane suka daukemu kamar rashin zabi ke kika rungumeni nazama zabi gareki dada wallahi koda zan aureshi na cutu ne to tabbas zan zauna dashi saboda ke na amince dada Amma danAllah banason taro ko daya kuma abarni kusa dake danAllah incigaba da makarantata." " Allah yayimiki albarka aichata karatunki sai kin gaji ki ajiyeshi kinji kuma maganar biki ai har dakinki zan mikaki wallahi sai anyi miki gata kamar na kowacce yarinyar kinjini ai dan haka kada kikara fadar haka yanzu dai tashi kije ki huta." ***** Ko data karasa sashenta jitayi bazata iya zama ba saboda datti da kura dan haka ta dawo shashinsa nan ta taddashi yana cin tuwo da miya ga kuma wani takeaway din akusa dashi kallonsa tayi shima ya kalleta sannan ya miko mata ledar hannunsa karba tayi tana zama kusa dashi ta buɗe batare da tayimasa godiya ko uffan ba ta aza abakinta tafaraci wayarsa datayi kara ya dauka kawunsa ne yakirashi dan haka sai ya saka a speaker yace barka da dare babban sarki." Allah yakara maka lafiya yarona " mun daidaita da kawun yarinyar nan mum tsayar da komai zuwa ranar lahadin nan to Mahaifinka ma yace dashi za'aje ina ganin zamu bukaci babbar mota." Wani sanyi yaji haɗe da faɗin Alhamdulillah sannu da kokari kawu zanshigo zuwa da daddare idan Allah yakaimu." " To madallah Mutallab ina saurarenka." " kutmar ubancan me nakeji ai wallahi kayi kadan karamin dan iska kishiya...fadar meenal tana kwara masa miyar tuwo ajiƙinsa wanda yayi daidai da saukar lafiyayyun hannunsa akan fuskarta... SHAFI NA TAMANIN DA TARA *MUTALLAB ASAD*      Arewabook:- billysfari       Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne. Bakaramin gyara Aicha tashaba dan kuwa tundaga kitson da akayimata da kunshi abubuwane da suka kara fidda kyanta ainayi haka kowannen su yadinga yabonta ita kuma tanata jin kunya tasani bazatace tana son auren ba amma kuma bazata taba cewa ta tsane auren ba, duba da wasu sabbin nauyin da take ganin sun hau ƙanta sosai ga kuma wani karin daukaka da take ganin tasamu wai wanda kasarta take yabonsa da kuma bashi lambar yabo na daukaka da wadata yau itace ta zama mallakinsa murmushi kawai tayi tana karasa wanke lallen dake hannunta tanajin dada na kwalla mata kira ta amsa hade ta shigewa bangaren dadan tana faɗin " Uwata maganin kukana ganinan zuwa." Shiyasa dada take kaunarta dan ko haifar Aicha tayi to tabbas karshen kauna da soyayyar da zasu nunawa juna. Rungumeta dada tayi tana faɗin da badan kinfini garun jiki ba da yau goyaki zanyi in hana kowa kallonki dan mashaa Allah tu es belle Aicha et tu es magnifique ( kinada kyau aicha sannan kinyi kyau)." Rufe fuskarta tayi tana dariya tace " Kai dada wai kuyita cewa haka ina wani kyau? Kullum mamana kamin rasu sai tacemin kazama yaya babbace mai tsafta." Yabi da da shigowarta kenan tace to ai ba karya tafada ba kazamarce ta bugawa yanzu dai dada ta gyaraki shiyasa ni ƙarbi nan ki shanye." Da ɗan mamaki ta kalleta tace " menene to tana turo baki?" " wannan da kike gani hadin kukane yarinya zaki godemun gaba indai kina hada kuka rabin cokali da ruwa kina damawa ki shanye to bayan maganin da zatayi miki har yan cutukan nan na zamani zakiga baki dasu magani ce babba mu can da muka ganeta shikenan idan miji na nan ka dama ka shanye sha yanzu magani yanzu." Bata rai aicha tayi alamun itafa batasha. Dada data lura da haka tace " ƙarbi kisha yar albarka kinji." Karba tayi ta kafa kanta tashanye." DanAllah mama yabi kibarni da magungunan nan nifa har kaina yafara ciwo." Dada ce tace " Ke rugemun baki ana miki gata bakya gani ni bani guri." Murmushi tayi ta zauna sannan suka shiga yimata kwalliya duba da yanayin tsarin bikin da za'a dan kuwa da autan dada yazo daga Egypt haka yace komai itama sai anyi mata ya yarda banda dinner Amma sai anyi har kamu shiyasa su dada suka hada ayi kamun zuwa dare kawai abunda batasani ba bakaramin shagali dada tasakashi yatsara ba dan babban filin gidan na ajiye motoci nan akayi decoration mai kyan gaske ko'ina ya kawata da yamma lis masu gyara mata fuska sukazo tayi shigar Aurensu baki da raisin kaloli bakaramin kyau tayi ba dan maganar bidiri ma ba'a magana kawayenta na makaranta kuwa kowanne ta gayyata wacce takasance yanzu kamar aminiyar ta humy itace tsaye kan komai ta kawatashi ita yar gidan wani minister ce da suka hadu ta dalilin su zainab da suka taba gayyatarta biki daga nan kuma suka kama kawance duk da ita ba a kasar take ba yanzu ma bikin Aicha ne yakawota shagali akayi na gani nafada sai wajejen karfe 9 sannan aka watse masu kwana kuma kowanne yafara neman makwancinsa can babban palour din da dada da autanta duk da yakai shekara kusan 45 amma auta take cemasa suna zaune suna lissafin kayan dakin da aka jera mata agidan nata. " Yansu auta menene bai cika ba kasan fa kishiyarta yargidan wasu ce bazamu kaita atozarce ba can na aika kudi Mutallab din yasaka an dawomin dashi." Murmushi yayi yana kallon mahaifiyar tasa yace " Ranki yadade babu wani abu da bai cika ba komai da komai ansaka diyarki kuma jikarki ko yar gidan masu kasa zata iya karawa dashi yabi tasiya mata rantsatsun kujeru dan ina tunanin sunyi 1. Gaskiya ga wanda muka saka komai yacika apart dinta Allah yabaku lada." Cike da jindadi dada tace " Allah yayi maka albarka auta yadda kakeson farincikina Allah yaso naka wallahi bazan daina muku addu'a ba dakai da uwar su Mutallab kun bani kamar ba gove Allah yabiyaku da tukwicin aljannah." Murmushi yayi yana amsawa da amin sanna ya amsa sallamar Aicha dake shigowa ta samu gefe guda ta zauna tana kara gaishe da kawu. " Aicha wannan kyau haka anya angon zai ganeki." " Auta adinga hadawa da MashaaAllah kada acinyen diya mana." Murmushi yayi yace " sannu yarinyar kirki angama miki jeran komai kuma kinada sanin wanin satin ne zaki fara makaranta ko? Sai ki maida hankali danAllah ki zauna da mijinki lafiya duk da nasan bakida fitina da kinadashi bazaki iya zama da dada ba nasani amma inaso kiyi hakuri ki kauda kanki akan komai saboda rayuwar duniyarma hakuri ke tafiyar da'ita kinji anzuba q miki komai adakinki komai angama ya nuna dada yace farincikin dada shine nawa aicha kuma kinadaga cikin farin cikinta DanAllah ki zauna da kowa lafiya kinji. " " Inshaa Allahu kawu dada ko ku bazaku taba kuka dani ba kunzame mun tudun dafawa kunzamemun jigon rayuwa kun haska rayuwata da abubuwa da dama Abunda kukayimun Allah yaninka muku shi tsakanina da dadata kuwa sai dai Aljannah da zanta roka mata har nakoma ga Allah tafada tana goge hawayensa." " To nidai ba wannan ba auta ba son Mutallab takeyi ba kayi mata fada soyayya baita bace zaman aure kada tazata abunda take kallo afilm shine ciki." " Murmushi aicha tayi tace " duk abunda dada takeso aicha ma tanasonshi ballantana Masoyinta kamar ya Mutallab." " Murmushi yayi yace " Wanga magana dai tsakanin ku Natura miki dan kudi da mota naso nasiya miki sai dada tace " aa abaki kema a hannunki a kyale motarnan." " Godiya aicha tayi masa sosai da sosai kamin ta koma daƙinta nan tabawa Yabi labari itama tayi mata godiya tasamu ta wanke kwalliya suka kwanta. **** Da mugun mamaki ya saukar da idanuwansa akan abunda ya gani sosai ransa yayi mugun baci jikinsa ne yashiga rawa kansa yana kokarin kwancewa saboda tashin hankalin da yagani jini? Namenene gudan jini a hankali yasaukar da idonsa kan meenal datagama jigata ga uban azabar da da alama ta gushe dan sai ta tsinke kanta da yimasa dariya tana fadin " Nacika alkawari nacre tsinannen cikin dake jikina." Da mugun zafin kai ya kifa mata marin da tayi karar da tante da Afrah dake waje sukayi saurin shigowa dan su sun dade da shiryawa na shi suke jira." Haba Mutallab danAllah sakarta karkayi mata illa bakaganin halin datake ciki ne kaduba fa kaga harda yanzu bleeding." " Meenal kije gida bazan iya zama dake ba yafada yana ficewa sannan ya koma bangarensa da yafashe da wani matsanancin kuka saboda yadda ya kwallafa rai acikin nata menene so to? Menene kaunar da tace masa tanayi? Tayaya dabi'unta sukafi nada muni? Ganin tsaf zai iya kwanciya ga flight dau 1hour su daga sai kawai yafita daga bakin part dinta yace " Ki tafi gidanku nagaji da halinki yakara fada yana buga mata kofa. " afrah dan mamaki fara fita tayi batace kanzil ba. Meenal kuwa da ta cika tayi taf dan ko amafarki bata taba kawowa Mutallab zai iya cewa haka hakan yasata Ta kalli tante tace " Allah ya'isa tsakanina daku kun rabani da mijina kunji dadi ko?" Ganin tante za'a zageta sai tatashi ta shigewarta batace kanzil ba, haka driver yajasu a jeep din Mutallab suka tafi duba ba da jalil zasu samesa acan . Kokari kawai yakeyi dan bayajin zai iya karasawa kasar jinsa yakeyi acikin wata duniya sabuwa mai cike da takaici. Wayarta taja takira umma bugu daya ta dauka tace " yace inje gida fa umma nacre cikin tun jiya da dare dan yaso yagani ne naki tashi daga gurin." Murmushi umma tayi har da dariya " Wannan shine daidai kinga kin hukuntashi ta cikun sauki kikumayi kokari kibarmasa gidansa yayi aurensa idanma sakinki yayi ga mazanan a gari." " Umma banson saki wallahi inasonsa." " Au haba dallah tashi kibar masa gidansa menene cikin gidan? Inbanda jaraba kine can gidan ubanki dakike da ƴanci kiyi yadda kikeso shikuma zamu je kauye saboda shi." Hakan yasa meenal din taji mugun sanyi acikin ranta da dadi. ******* Yau Alkawari yacika An daura auren Mutallab Asad da Aicha inda gangamin manyan masu kudi da yan kasuwa suke shiga da fice cikin masallacin suna masu tayashi murna yana godiya garesu, sanye yake cikin wata shiga mai daukar ido da kyau wato farar shadda haɗe da dinƙin da akayi da ash ko'ina sai zuba kyalle yakeyi da walwali ko ba'a kayamata ba kasan shine angon. Cike gidan dada yake da ƴan uwa da aboƙanan arzuki kama daga dangin mahaifiyar tasu har ma da dangin mahaifi. Mamaki ne yakama kannen mahaifiyar Aicha da yayan mahaifiyarta jin wai mai kudi zata aura yanzu ma suna karamin palour din dada bayan sun gama cin abinci " Nikam dada wannan hadinki ne ko?" Inji daya daga ciƙinsu dake maganar da dan murmushi abakinta. " Wanga hadi yafi karfina ai, ina gayamiki yaro da yaso ya zubemin da ciwo saboda soyayya ai shi Mijin nata kemata son MashaaAllah." Daya daga ciƙinsu da abun ke mata takaici da bakin ciki ce tace " Yanzu shi duk yammatan nan sai yar mabaraci saiji yanaso." Dada ce tayi dan murmushi tace " Har yake kokarin mutuwa saboda kaunarta kinsan shi lamarin aure babu ruwansa da komai na rayuwa da jarabawa yana zuwa anayinsa ne Asanda ubanji ya aminci." " To dada ance ai mai matane ko? Ashe mijin wata zata aura." Dariya yabi tayi akaro na farko tace " Ashe wata na aurar mijin wata? Ai ni wallahi Nazata kowa mijinta take aure? Duba da daga hakarkarin mijin akayita ai mu dayake munada ilimi bamusan wannan ba tunda babu ayah ko hadisi." Babbar yayar tasuce taji ranta yakara baci sai cewa tayi " To mudai dada babu kudi ga wannan dubu ashirin ce muka hada dan kam bazamu iya yimata na kayan gado na gaskiya." Sai da dada tayi musu kallo sosai duk da zuciyarta ta dan sosu sai kuma ta karba tace tabarakallah mashaa Allah hakan ma ai angode kunyi kokari." Dayar cikinsu ce tace " Angayamasa dai ai ubanta baida komai kada yahi tunanin za'a cika masa kaya da gida dan basu bar komai ba." Yabi dada ta ambata tana fadin " Tashi kuje suga gidan aicha ko kamin mazan su shigo." Kowannen su kuwa sukayi hanzarin tashi suka bi yabi ta tasaka mayafi suka Nufi kofar gida ganin basuji ance atafi da mota ba sai suka ce " Mama yabi akafa zamu gidan nata ne harda dariyar su." Batace musu komai ba sai sukaga taba nufar tamfatsetsen gidan da kowa yashigo a estate din sai yakara kallonsa dan babu kamarsa mamaki ne yakamu ganin ta tura wata katuwar kofar alfarma masu gadi sunata gaidata tante dake fillin motocin tasahiga murnar ganinsu afrah nagasige su sukam sunkasa komai ma saboda mamaki. " kinga iyayen aicha ne narakosu zuwa bangaren nata zasu gani." " To mashaa Allahu ku isa bangaren nata sannu ku da zuwa tante ta fada cike da girmamasu." Tunda suka shiga kowacce sai ta raina kanta sauran dame tunanin suna auran masu kudi sai kowaccen su takasa magana daga karshe ma kasa zama sukayi suka fita. Can kuma gidan Bikin aicha ta cakare cikin farin shadda anmata

Chapter 49 of 54