Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels *MUTALLAB ASAD MUTALLAB* (MAM) NA BILLY S FARI & NANA DISO *SHAFI NA DAYA.* _RUBUTUN ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU._ _TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA_ *KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?* *INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?” *KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.* Mun gwada mun gani 💯 Mun gani mun shaida 💯 Anyi mun gani 💯 MAGANIN SANYI MAGANIN NONO MAGANIN HIPS MAGANIN SLIMMING MAGANIN NANKARWA GYARAN AMARE GYARAN MAIJEGO MALLAKAR MIJI KO MATA SUBULU DA SCRUB MAYUKA NA GYARAN JIKI TURAREN WUTA MATSI MAGANIN NI'IMA MAGANIN TSUMI INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯 08142800199 07068558096     Garin a lullume yake da hazo, ga wani irin iska dake kaɗawa, wasu na tafiya aƙasa yayin da wasu suke tafiya akan keke mai ƙafa biyu da uku wasu kuma suna tafiya ne da ainahin ƙafafuwan da Allah ya halittawa kowane cikakken mutum, yayin da iskar dake kaɗawa sai manne musu tufafi takeyi duk da yalwar sutura dake sanye da jikunkunansu, haka yasa wasu suka sake ƙawata saman jikinsu da rigunan sanyi don samun cikakkiyar kariya daga bayyanar sauyin yanayin garin da aka samu da muke kira bazara ko kuma hunturu dake ɗauke da wani irin matsanancin sanyi da kowanne mutum ke ƙoƙarin bawa gangar jikinsa da kuma lafiyarsa kyakkyawar kulawa da zata iya bashi kariya daga wannan Sanyin da akeyi mai tsanani. sai dai duk da hakan kamar yanda kowa ya sani tsanantar yanayin da ake ciki bai hana mutane Yin wani kai da kawo na yau da kullum ba da ke tsakankanin rayuwa da kuma mutuwa a kowace safiya.    *ALHAJI ASAD MUTALLAB STREET* Abunda aka rubuta kenan a jikin wani ƙarfe dake bakin wani babban layi. Ko ba'a sanarmaka ba kasan gidaje ne na masu faɗa aji a gomnati ko kuma manyan-manyan ƴan kasuwa da sukayi fice da kuma zarra akaf faɗin garin, daga gefen hannun hagu a jerin ƙayatattun gidajen wani babban gidane da kallo ɗaya zai tabbatar maka da cewa mamallakin wannan gidan na ɗaya daga cikin waɗanda Allah yayiwa ni'ima da saukar tarin arziki mai yawa a tattare dasu, duba da yanayin tsaruwarsa, tsananin girmansa da kuma yanda aka ƙawatasa tun daga kan tsarin ginin har zuwa abubuwan da aka ƙawatasa dasu aciki, gidane dake ɗauke da rassa daban-daban wanda hakan ke tabbatar maka da yalwatuwar iyali da kuma zuri'a kamar yanda tarin arziƙi ya yalwata acikinsa, budurwa ce da bazata haura shekaru goma sha biyar zuwa sha shidda ba tafe cikin  uniform ɗinta na makaranta da duka-duka sket ɗin kayan kaɗan ya rufe guiwowin ƙafafuwanta, sai doguwar safar kafa dake cikin takalman makaranta dake jikinta, a samanta kuwa ɗan mitsitsin hijab ne dako ƙirjinta bai ƙarasa rufe wa ba duk da zunzurutun sanyi da kuma iska dake faman kaɗawa, school bag ɗin ta kuma na rataye akan kafaɗarta  ta nufo ɗaya daga cikin jerin danƙara-danƙaran motocin da kowace ke zaune a muhallin da aka tanadar mata acikin farfajiyar gidan ta ƙaraso da sauri saboda ganin suna ƙoƙarin makara, dai-dai lokacin da takai hannunta a jikin marfin motar tana ƙoƙarin buɗewa taji saukar muryarsa cikin wani irin coolness  yana cewa, "Ina ƴar uwarki ne Jiddah naga driver na ƙoƙarin tayar da motar banga tafito ba?" Ɓata rai tayi tare da sakin murfin motar tana turo baki gaba sannan ta juyo haɗe da cewa, "Ya MUTALLAB bata tashi ba kuma mun makara". Ba tare daya kalleta ba ya nufi sashensu yace, "Ki koma ki tasheta ta shirya sannan kufito kuwuce". Sanin baya magana biyu yasa ta fashe da kuka tana bubbuga ƙafafuwa haɗe da ƙunƙuni ita baza taje ba kuma ba zasu tsaya jiranta ba wallahi. yaran dake cikin motar tun ɗazu su biyu ƴan maza suna zaman jiran yayun nasu suka fito suma daga cikin motar suna kallon sashen da ya'yan nasu ya nufa, ɗaya zai kai shekaru goma sha biyu ɗaya kuma bazai wuce shekara bakwai ba, tamkar wasu manya suka bishi da banzar kallo sai kace ba yayansu ba kafin Khalil da shine mai shekaru sha biyu ya maido kallonsa gareta yana gyara stocking ɗin wandonsa cikin ɓaci rai yace "Aunty Jiddah gaskiya idan muka makara aka dakeni Allah ya isana bazan yafe ba tunda da gangan kuka ki shiryawa da wuri". A hasale ta juyo tayo kansa zata kai masa duka ya goce ya balla mata harara, dai-dai lokacin mahaifiyarta mai suna Hajiya Zainab tafito daga sashen daya kasance mallakin mahaifinsu tana cewa, "A.a.a.a meye haka Jiddah wai har yanzu baku tafi ba? Kun san ƙarfe nawa kuwa yanzu?" "To Ummah ba ya Mutallab ne ya hanamu tafiya ba wai sai mun jira Afrah kuma ko tashi daga bacci batayi ba". "Me ne? Yau she yasamu wannan matsayin acikin gidan nan, ita Afrah ɗin waye ya hanata tashi ta shirya da wuri? Ai kuwa bai isa ba maza ku shiga a kaiku, idan taga dama ta fito sai ta nemi abun hawa ya sauke ta, dama meye haɗin tsintsiya da ragga in ba dole ba". Ta ƙarashe maganar cikin ɓacin rai tana rufe masu motar bayan sun shiga tare da dallawa sashen su Mutallab ɗin harara, wanda hakan yayi dai-dai da fitowarsa zai shiga sashen mahaifin nasu gaishesu, duk da yana jin maganganun da take yi bai tanka mata ba sai ma gaisheta da yayi cikin girmamawa ya wuce gaba abunsa ba tare daya tsaya saurarar amsar da zata fito daga bakinta ba, wata uwar hararar ta sake dalla masa haɗe da cewa,"munafurcin banza munafurcin wofi da ban tashi ba zaka ganni ne". Sannan tabi bayansa tana ci gaba da yaɓa masa maganganu don tuni driver yaja motar ya wuce. Cikin girmamawa ya gaida mahaifin nasa dake kishin giɗe akan wata lallausar darduma dake cikin falon nasa daya gama tsaruwa ya amsa masa ba yabo ba fallasa, miƙewa yayi da zimmar fita Ummah dake tsaye gefe cike da takaicinsa na rashin tankata tace, "Alhaji ka jamasa kunne akan yaran mu tunda baya ƙaunar a zauna lafiya kullum burinsa ya raba ɗaya biyu". Ɗan ɗauke fuska mahaifin nasa yayi kafin ya kallesa tare da dakatar dashi daga ƙoƙarin ficewarsa da yake shirin yi, maido kallonsa ga Ummah yayi sannan yace, "Me yake faruwa?" "Ai kasan halinsa da nuna banbanci tsakanin yaran nan Alhaji sai kace duka ba ƙannensa bane, idan ba haka ba akan me ƴar uwarsa zata je tayi kwanciyar bayan tasan suna zuwa makaranta har lokaci ya ƙure kuma yace dole sai Jiddah ta koma ciki ta jirata bayan makara zasuyi? To nidai gaskiya bazan lamunci a takurawa Jiddah ba tana jamata duka a banza a makaranta, ban sani ba ko ita Amarya zata iya haƙura aci gaba da dukar mata yara a banza saboda laifin ƴar uwarsa, don haka kama canza masu wajen karatu tunda bazata iya tashi tana shiryawa da wuri ba ka kaita inda za'a ɗauki wannan shashancin nata". Ga mamakin Mutallab mahaifin nasu bai tsaya yin binciken komai ba kawai  yace, "Shikenan, yanzu ina yaran suke su suje a saukesu?" "Sun wuce Alhaji ita kuma har yanzu ina tunaninma bata fito ba saboda tsabar lalaci dake damunta". Jinjina kai yayi haɗe da cewa "Shikenan ki ƙyaleta zan kaita inda ya dace da ita don bazai yiyu na riƙa banzatar da kuɗina a banza ba". Da sauri Mutallab ya ɗago kai jin abinda mahaifin nasu ya faɗa, ko kaɗan bai yi tsammanin wannan makircin na Ummah zai sa yayi saurin yanke hukunci haka ba, "To mara kunya kallon me kake yimani? Ina Ni na haifesu duka kuma zan iya yanke duk hukuncin da naga dama akan kowanensu". Alhajin ya faɗa cikin ɓaci rai yana kallon Mutallab dake ƙoƙarin buɗe baki yayi magana, wata uwar tsawa ya daka masa tare da nuna masa ƙofa yana faɗin yabar masa ɗaki, ɗago kai yayi ya kalli Ummah ta sakar masa wani irin malalacin murmushi dake tattare da kalar ma'anoni daban-daban. Maida kansa ƙasa yayi yaba mahaifin nasu haƙuri sannan ya juya yabar falon gangar jikinsa a mace zuciyarsa cike da ƙunci da kuma samuwar wannan mummunan hukunci da mahaifin nasu ke shirin yanke wa, kai tsaye cikin gidan ya nufa ya samu Aunty amarya na zaune a falo, kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kansa haɗe da danne duk wani abu da yake ji na ɓacin rai a ƙasan zuciyarsa ya gaisheta tare da wucewa kai tsaye ɗakin daya kasance mallakin ƴar uwar tasa dake can sama jere dana Jiddah, Aunty amarya kuwa da harara ta rakasa har ya janye saman sannan tayi wani mugun tsaki tana jin tsanarsa sosai a ranta. Bakin ƙofar ɗakin ya tsaya ya ɗan bubbuga ƙofar tare da kiran sunanta, jin ba'a amsa ba ya sashi ɗan ɗaya Muryar tasa cikin zafin rai yana cewa, "Afrah..Afrah". Daƙyar ta iya motsa bakinta daga cikin duvet ɗin data tattake aciki tana rawar sanyi tace, "yaya.." sai ta kasa ƙarasawa sakamakon aman da taji ya taso mata wanda ya sata yin wani irin yunƙuri da ƙarfi cike da kakari, jin sautin aman yasa Mutallab tura ƙofar da ƙarfi ashe ma bata saka key ba a buɗe take, cikin tashin hankali ya kutsa kansa cikin daƙin hangota tana ƙoƙarin saukowa kan gadon cikin wani irin yananyi dake tabbatar masa da raunatar gangar jikinta sakamakon rashin lafiyar da take ciki ya tallabota, take tafara kwara amai ga jikinta ya dau zafi sosai tamkar ba a yanayin sanyi ake ciki ba, taimaka mata yayi bayan ta gama aman ya kaita toilet ɗin dake cikin ɗakin nata ya wanko mata bakinta sannan ya fito da ita ya mayar da ita akan gadon tare da Jan duvet ya lulluɓa mata sannan ya cire mata hijab ɗin dake jikinta daya ɗan jike da ruwan data wanko bakinta, idanuwanta a lumshe tace, "yaya.." bata ƙarara ba yace, "ya isa Afrah tun yaushe kike cikin wannan yanayin baki kirani kika sanar dani ba? Sannu meke damunki?" Kanta ta nuna masa da ƙafafuwan ta sai sanyi data sake tabbatar masa da tana ji sosai, wanda hakan ke nuni da zazzaɓine mai tsanani ke damunta. "Ina zuwa". Ya faɗa tare da miƙewa ya fice daga ɗakin, ba'a jima ba sai gashi ya dawo, sai dai a wannan karon su biyu ne, Cikin sanyin Muryar ya kalli wanda suka shigo taren daya ɗan girmesa yace, "Jalil ka gyara wajen nan, bari naje na samo mata abinda zata ci tasha magani". Ya ƙare zancen yana nuna masa gun da Afrah tayi amai shi kuma ya fice. Dukkansu kallo ɗaya zaka yi masu ka fahimci  jini ɗaya ne da suka fito daga ciki ɗaya saboda tsananin kamar da sukeyi da juna, musamman Afrah da Mutallab da yanayin hasken fatarsu take iri ɗaya, haka ma zayyanuwar kyakkyawar surar dake shimfiɗe akan fuskokin nasu iri ɗaya ne tamkar an tsaga kara, kawai shekaru da kuma bayyanar jinsin kowanensu zaisa ka iya banbance tsakaninsu, Jalil kuwa duk da suna kama yanayin surar fuskarsa yafi bayyana dana mahaifinsa saboda hatta duhun fatarsa duka nashi ne ya ɗebo, gaba ɗaya shekarunsa basu wuce ashirin ba a duniya, sai Mutallab dake da shekara ashirin da biyar, Afrah kuma tana da shekara sha biyar da watanni don kusan Sa'anni suke da Jiddah, gaba ɗaya baifi wata uku zuwa wata huɗu bane da Jiddah ɗin ta bata. Sai da Jalil ya gama gyara wajen sannan ya dawo gefen gadon ya zauna tare da dafa goshin Afrah ɗin yace, "Sannu tsunkui, Ashe bakida lafiya". Sunan da yake kiranta dashi kenan saboda ba tada wata cikakkiyar lafiya ko yaushe yau ciwo gobe lafiya, hakan yasa ba tada ƙiba sam shi kuma sai yake kiranta da wannan sunan musamman daya fahimci bata so suyita rigima kamar dai yanda kowa yasan yanda saƙo da saƙo suke basa rabo dayin faɗa. Yanzu ma haka ne, duk da tana ciwo hakan bai hanata maka masa harara ba tare da Turi baki tana duvet ɗin har fuskarta ta rufe. "Sorry" ya faɗa yana dariya sai ga Mutallab ya turo ƙofa hannunsa riƙe da cup daya haɗo mata tea a ɗakinsa, "Afrah tashi kisha wannan sai kisha magani". Ya miƙawa Jalil daya tashi ya bashi wurin cup ɗin sannan ya zauna tare da janye duvet ɗin a fuskarta ya taimaka mata ta tashi ta jingina da gado, idanuwa suka haɗa da Jalil ta sake harararsa haɗe da kallon Mutallab tace, "Yaya ka ganshi ko". Ɗago kai Mutallab yayi fuskarsa ba wasa suka haɗa ido da Jalil yayi saurin sadda kansa ƙasa, "me yasa kai babban kwabo ne, tana ciwon ma sai ka tsokaneta?" Zai yi magana Mutallab ya miƙa masa hannu yana cewa, "Ya isa haka, bani". Jalil ya miƙa masa ruwan cup ɗin ruwan tea ɗin ya riƙa bata a hankali tana sha har sai data shanye tas sannan ya ajiye cup ɗin gefe yasa Jalil ya sauka ya kawo masa ruwa ya ɓalle mata maganin ya bata tasha, sannan ta koma ta kwanta ya gyara mata duvet ɗin yana yimata sannu, hannunsa ta riƙe tana kallonsa idanuwanta cike tab da kwalla tace, "Yaya na.." bata ƙarasa ba tayi saurin jan bakinta tayi shiru ganin yanda ya sauya mata fuska nan take saboda godiyar da take ƙoƙarin yimasa. A hankali hawayenn da suka cika mata idanuwa suka fara kokarin saukowa akan kyakkyawar fuskar tata tana jin wata irin soyayya da ƙaunar ƴan uwan nata na yawo a dukkanin magudanar jini da kuma lungu da saƙo na zuciyarta, duk duniya ba tada gata sama dasu, sun zame mata uwa mahaifiya data rasa tun tana ƙarama kuma suka cike mata gurbin mahaifi a tawata fuskar duk da yana a raye shi.... *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya #Tafiyar samo #Tagwaye biyar #Billy S fari #Nana Diso. *MUTALLAB ASAD MUTALLAB*                 (MAM) NA BILLY S FARI & NANA DISO    *SHAFI NA BIYU.* _RUBUTUN ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU._ _TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA_ *KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?* *INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?” *KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.* Mun gwada mun gani 💯 Mun gani mun shaida 💯 Anyi mun gani 💯 MAGANIN SANYI MAGANIN NONO MAGANIN HIPS MAGANIN SLIMMING MAGANIN NANKARWA GYARAN AMARE GYARAN MAIJEGO MALLAKAR MIJI KO MATA SUBULU DA SCRUB MAYUKA NA GYARAN JIKI TURAREN WUTA MATSI MAGANIN NI'IMA MAGANIN TSUMI INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯 08142800199 07068558096 _________ Ƙarar da wayarsa dake gaban aljihun jallabiyar dake jikinsa tayi yasa shi miƙewa yana ɗaga wayar da sunan ARYAAN babban abokinsa ya fito ɓaro-ɓaro a jiki tare da ficewa daga ɗakin. MUTALLAB ASAD MUTALLAB shine cikakken ainahin sunan yayan nata da take matuƙar ji da kuma alfahari dashi, su uku mahaifiyarsu data kasance mace ta biyu ga mahaifin nasu shahararren ɗan kasuwar da yayi suna lungu da saƙo wato ALHAJI ASAD MUTALLAB MAI TAYA ta haifa kafin Allah yayi mata rasuwa lokacin tana da shekaru huɗu a duniya sai ɗaya yayan nata kuma abokin faɗanta JALIL ASAD MUTALLAB, Mahaifinsu na matuƙar son mahaifiyarsu data kasance cikakkiyar buzuwa data fito daga jamhuriyyar Nijar saboda yanayin kulawa da soyayyar da take nuna masa, wanda hakan ya haifar da matsananciyar tsana tsakaninta da duka matan nasa musamman Hajiya Zainabu uwar gidansa wato Ummah, sun goga kishi sosai da ita duk da kuwa mahaifiyarsu macece mai haƙuri da don zaman lafiya, sai dai fahimtar da tayi kulawarsa ga mijin nata ce ke haifar da rashin zaman lafiyar tasu ta nuna tabbas indai har sai ta dena yin hakan zasu samu zaman lafiya to ashirye take da fuskantar duk wani abu da Hajiya Zainabu zata zo mata dashi, gogaggiyar macece Hajiya Zainabu da tasan kissa da kuɗina da kuma makirci kala-kala sai dai duk da haka rakasa yin nasara akan mahaifiyar tasu Hajiya mariya, hakan yasa tafara bin malamai kala-kala da shiga bokaye don ta raba tsakaninsu, sai dai riko da ibadar mahaifiyar tasu ya shamakanceta daga duk wani kaidi da kuma asirce-asircenta har zuwa lokacin da mai rabawa ta raba su. Duk da haka Hajiya Zainabu bata dena jin wannan tsanar da take yi mata ba ganin yanda soyayyar da maigidan nasu ke yiwa Hajiya Mariya gaba ɗaya ta koma a kan yaranta har sai data shiga tsakaninsa dasu ta kasar masa da hankali akansu tare da kokarin cire masa duk wata soyayya da yake yi masu, lokaci ɗaya suka koma abun tausayi saboda rashin kulawa da kuma banbancin da yake nunawa ƙarara tsakaninsu da sauran ƴan uwansu, a ɗaya ɓangaren itama Aunty amarya tunda ya aurota lokacin Hajiya Mariya nada cikin Jalil taga irin rawar jikin da yake yi da ita da yanda yake nan nan da ita sai kace itace amarya ba ita ba taji ta tsaneta, don kuwa gaba ɗaya bata gabansa baya da zance sai na Hajiya Mariya da cikin dake jikinta tamkar shine na farin, hakan yasa Ummah tayi nasarar shiga jikinta tayita ƙara cusa mata tsanar Hajiya Mariya da yaranta tana nuna mata cewa ai ta asirce Alhaji Asad ɗin ne bai ganin kowa sai ita, bata gasgata hakan ba sai da taga ta kwashe kusan shekara biyar da aurensa ko ɓatan wata batayi ba amma ko kaɗan abun bai dansa ba, nan da hankalinta ya tashi a lokacin Hajiya Zainabu ta sake haihur ƴar ta ta ta huɗu wato Jiddah, ita kuma Hajiya Mariya ta sake haihuwa ta haifi Afrah wacce sunan mahaifiyarsa ne ya saka mata wato khadija. JAMIL shine babban ɗanɗan Hajiya Zainabu, yanzu haka yayi aure kuma anan cikin gidan yake zaune a can ɗayan part ɗin dake gefe da yaransa biyu Nihla da Sameer, Sai Aunty Asiya itama tayi aure tana da yara uku, sai kuma Aunty Luba da aurenta shekara biyu yanzu, sannan auta Jiddah. Aunty amarya kuwa bata haihu ba sai bayan rasuwar Hajiya Mariya mahaifiyar su Mutallab da shekara ɗaya ta haifo ɗanta yaci sunan Khalil, hakan yasa ta sake amanna cewa mahaifiyarsu Mutallab asiri take yi tunda gashi daga mutuwarta itama ta samu nata jinin kenan asirin ya karye, bayan shekara uku ta sake haifo ɗanta yaci sunan Walid, daga nan haihuwa ta tsaya don har yanzu ko ɓatan wata bata sake yi ba. Wannan shine. ********** Cike da rashin kunya da tsiwa take magana cikin ji da kai da kuma izza, sam babu alamun girmamawa ko kuma mutuntawa acikin kalamanta da take jefawa wacce ta zamo jigo kuma matsayin uwa a gurbin rayuwarsa. duk da bata haifeta ba ba kuma tasan wahalar ɗaukar cikinta ba ta amsa sunan uwa kuma nagartacciya agunta da ako yaushe ba tada wani buri sama da taga ta saita gobenta ta kuma bata kyakkyawar rayuwa, sai dai ita hakan baisa ta zama mai alkunya da kuma nuna karar amsa sunan ƴa a gina ba daidai dana second ɗaya shi yasa take iya kallon tsakiyar idanuwanta ta faɗa mata duk wata magana data fito daga bakinta komai ɗacinta kuma komai muninta don ita ɗin ƴar gata ce kuma ƴar gaban goshi ga mahaifin nata ALHAJI ABDULMALIK MU'AZZAM da ko ƙuda ya taɓa masa ita to tabbas da sai yaji ɗacinsa. "Nan ɗin gidan ubana ne babu uban daya isa hanani nayi yanda nake so, su ɗin kuma ƙawayena ne suna da damar shigowa suyi duk abinda suke so, don haka kija jikin saboda ba kida iko a kaina, haka kuma ba kida hurumin sa mani iyaka a gidan ubana, ki barsu suci arziƙi suma kamar yanda kema kike ci bana son sa ido kin fahimta ko?" "Meenal.." cikin tsawa matar mahaifin nata dake ƙoƙarin tausar zuciyarta akan munanan kalaman da yarinyar data rena da hannunta ke caɓa mata a gaban ƙawayenta da suka zo suka baje mata a tsakiyar falo suka ƙure volume na home theater suna kwasar rawa ihu da kuma shewa ta kira sunanta, wani kallo meenal ta jefa mata haɗe da juyawa tana cewa, "ƙawayena ku ƙara sauti kuyi yanda kuke so, nan ɗin gidan ubana ne babu mai hanamu". Tanayi tana kwasar rawa abinda, don kuwa indai kiɗa ne Meenal baza ta taɓa bashi kunya ba duk inda ta jishi sai takai jiki kuma sai ta taka balle ace acikin gidan ubanta ne kamar yanda take iƙirari. Ran Momy a ɓace ta nufi wajen kayan kiɗan ta kashe sannan cikin kakkausar murya ta shiga ba ƙawayen Meenal ɗin umurni dasu tattara su fice mata daga gida kafin takira masu jami'an tsaro suyi mata gaba dasu, jin hakan yasa jiki na rawa suka shiga ɗibar jikunkunansu da takalmansu a hannu suka fice da sauri Meenal na faman kiransu amma ko saurararta basuyi ba, wata irin ƙara ta saki tare da ɗaukar abun ƙawar dake kan center table na glass tayi jifa dashi ta fashe da kuka,

Chapter 1 of 54