Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 72 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauri gain sun kai qarshen hallway din suna gab da shiga parlor, ga kuma muryar yaran tana jiyowa

"Ai madam tuhumarki nakeyi fa" ido ta fiddo

"Dame?" Sauketa yayi ta tsaya cak da qafafunta, idanunsa cikin nata yace

"Jiya naji wani gagarumin sauyi,ina suspecting ban ruwana yayi kyau‚na jefa kyakkyawar qwallo a raga"

kunya taso kamata amma saita waske

"Bansan wannan zancan ba"

"Ki rantse" ya fada yana takowa zai risketa,a yadda taga yana kallonta tsaf zai iya cewa zaisha mintinta,don haka da sauri tace

"Na rantse ina kyautata zaton haka ne" tsintarsa tayi kawai yayi sujoodush shukr, koda ya dago hawaye ne cikin idanunsa

"Ya rabb, baiwar da ka yimin na gode,ya Allah kasan inason baiwar nan taka, Allah kaci gaba da yiwa rayuwarta dama rayuwar duk abinda zata haifa albarka" r jikinta ya qara sanyi, zuciyarta na qara cika da soyayyarsa.

He's strong man, amma akanta a nan weakness nashi yake,dole ne tayi duk me yiwuwa wajen kyautata masa shi da mahaifiyarsa,ta kuma kula da tarbiyyar yaransa,wannan shine abu daya da zata saka masa dashi.

Ita ta taka ta dagashi, ta riqe hannuwansa tana duban idanunsa

"'Duk kalmar da zanyi amfani da ita wajen maka godiya sai naga tayi kadan" murmushi ya saki yana dora yatsansa kan lebanta

"Kici gaba da kasancewa dani har garshen rayuwarmu"

"'Nayi alqawari" kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai muryoyinsu asad ya fara dososu

"Anima zamu fita mu maidawa maji su as'ad,daganan zamuje Sr raheema ta dubamin lafiyan baby girl dina" dariya ya bata sosai

"Baby girl kuma?"

"Yes in sha Allah, twins baby girls"

"Maami zata haifa?" Muryar as'ad ta shigo da tambayar.

Harara sãahar ta jefa masa,sai ya dan tsaya ya Rama kunnensa duka biyun yana kebe baki

"Am sorry bazan sake ba maami, amma inason baby girls don Allah maami ki siyo mana a kasuwa,ni banason Teddie's din nan‚masu magana nakeso" dariya ya basu gaba dayansu, har fadeela data bivosu zata kamasu ta maidasu parlor

"Ka fara shirin zuwa suna hanya in sha Allah" toufeeq ya fada yana kama kumatunsa qaunar yaran da suke debo tsananin kama dashi tana sake mamayeshi kwatankwacin yadda yake qaunar mahaifiyarsu maami sãahar.


. Tammat Alhamdulillahi rabbil Aalamin_


-*Dukkan yabo godiya da jinjina sun tabbata ga Allah madaukakin sarki, tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu annabi muhammad*


*ina miga matuqar godiya da jinjina ga dukkan kafatanin masoyana,wadanda basa gajiya da bibiyar labarina, basa gajiya da bibiyar gamayyar marubutan zafafa biyar, Allah ya qara dangon gauna da soyayya yasa wanna tarayya

tamu ta zame mana silar alkhairi da samun tsira*
"Mun gode*
"Mun gode*
* _zafafabiyar na godiya_*
*Haqiqa SAI DA KU* AARO
_ina fatan sagon da nakeson isarwa va isa kurakuren dake cikin wanann rubutu Allah ya yafe mana,ya taramu a ladan_
• "Bazan rufe ba tare da na ambaceku ba jama'ar ZAUREN TABARMAR QASHI,na gode qwarai da hadin kanku*
_sai mun sake haduwa a littafi na gaba idan me duka ya bamu aron rai lafiya da kuma dama_
_subhanakallahumma wani hamdika,ashahadu an la'ilaha illa anta,astgafiruka wa' atubu ilaika_




Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment