Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 47 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gunta

"Labiba gaba daya na kasa gane kanta,yini take ta kwana tana kuka,ta daina fita ko ina,ta daina walwala ta daina magana da kowa"

"Duka akan me?" Yayi mata tambayar yana zama saman stool. Mamaki yadan kama hajiya mansura yadda yayi kamar baisan komai a kai ba, duk da haka ta hadiye cikin lanqwasa murya da karyar da kai

"Akan yayanta toufeeq mana, tunda yayi auren nan ita kuma ta koma haka" idanunta yake kalla kai tsaye,yama rasa abinda zaya fada, baisan me yasa daga mansura har fauziyya kowacce idanunta ya rufe akan batun hada auren toufeeq da 'yarsa ba,duka duka ma yaushe yaron yayi auren da har za'a tsaya rakito masa wani auren?,shi yasan abinda su basu sani ba yadda haseena take zabin fauziyya,labiba take zabin mansura, haka säahar take
ZABINSA, ya riga taoufeeq nema masa auren sãahar ba tare da shi kansa ya sani ba. Bayan ya samu dukkan labarin aurenta da adam daga bakin muhyiddeen,ya tabbatar ya kuma yi imanin SÄAHAR itace macen da tafi dacewa da toufeeq,itace kuma madadin AMEESHA data sanyawa rayuwarsa dafin da yasa yake kallon mata amatsayin ABU GUDA. SAAHAR itace tayi masa kamanceceniya da SHIFA, dabi'unsu suna gogayya da juna,yafi kowa sanin wacece shifa da halaccinta a garesa,wannan ya sanya ya yiwa toufeeq sha awar mallakarta.

"HUGUMA*


_TABARMAR KASHI*


Book 02Page 25

"Yanzu ba zaka sanya baki ba ko don a samu hankalin yarinyar nan ya dawo jikinta?" Agogon hannunsa da ya manta bai cire ba ya soma zarewa

"Bana shiga lamarin da ban isa na hadashi ba, daga ke har fauziyya na gaya muku, toufeeq yana da ido so ba sai an tursasashi ba,ko ni bani da ikon bashi umarnin ya auri wance,idan ya gani yanaso bazan hanashi ba" maganar tasa ta tabata sosai, kuma dama fauziyya tana can tana nata yaqin kenan? ya tabbata ta shirya cin amanarta da gaske,iska ta furzar a bakinta tana gangance idanu

"'Wallahi wallahi wallahi tsautsayi yasa ta yimin kan kara sai nayi mata na itace, idan tana tutiya da ita din gwanace ni uwarta ce a wannan fannin, zatasan ni mansura cikakkiyar KARA DA KIYASHI ce daukan mara sani" abinda ta furta kenan qasan ranta, kafin daga bisani muryar dr mahmud ta mamayi kunnenta

"An samu ticket din? na ranar yaushe ne?, alright zanyi managing na jira ranar" sai ya sauke wayar daga kunnensa a hankali yana furta

"Alhamdulillah" yadda fuskarsa ke nuna annuri yaja hankalinta

"'Wacce tafiya ce haka me muhimmanci zakayi?"

"Ni kadai tafiyar ta shafa,so ba wani abu bane na daban" ya fada yana kashe wayarsa. Binsa tayi da kallo,haka kawai taji jikinta bai bata ba,so amma koma inane zatabi diddigin tafiyar har ta san inda zashin. Hannuwanta ta sake tajuya tana ficewa don dauko masa plate din abincin data manta.

Tana saukowa daga stairs din hajiya qarama na shigowa falon,kallon kallo suka yiwa junansu, kafin hajiya garama ta buda baki da qyar tayi sallama. Kamar yadda tayi sallamar da gyar haka mansura ta amsa mata da gyar tare da dauke kanta, tazo zata wuce ta gabanta tamkar batasan da wanzuwarta a wajen ba. Matuga da gaske abun ya daure mata kai,don bata taba kawowa a duniya akwai lokacin da zaizo mansura tayi mata irin wannan abun ba

"Ina yaya yake?"

"Tunda kinsan kan gidan ai kinsan inda zaki sameshi" ta amsa mata da gatse, tunda ta sani aduk sanda tazo gurinsa itace ke shaida mata yazo din

"Idanma da gatse kika fada yanzun zaki ga cikar aikin irin na fauziyya" tana kaiwa nan ta kama stairs din tana hawa,hajiya mansura ta bita da kallon zallar mamaki baki bude.

Ya danyi mamaki da yaji ana knocking,ya miqe ya buda qofar, mamakinsa ya qaru da ganin fauziyya da safen

"Muje falo" yace da ita ha fito ya biyo bayanta. Nan falon saman suka zauna,yana qoqarin zama ta fashe masa da kuka

"Subhanallahi, lafiya me yake faruwa?" Hajiya Mansura da tayi gaggawar dawowa don taji abinda ke faruwa duk da tasan fauziyyan bata taba wata magana me muhimmanci tsakaninta da yayan nata a gabanta ba,ta saci kallon fauziyyan cikin sa'a suka hada idanu

"'Maganace ta ahali yaya,zan samu sarari?" Kai ya jinjina vana karbar plate din daga hannun mansura yana cewa

"Mansura bamu guri"

"Tom" ta fada zuciyarta kamar zata fado daga qirjinta saboda tsananin takaici. Shekara da shekaru har yanzu babu abinda ya sauya a irin wannan abubuwan dake faruwa,a wannan shekarar kadai ta soma gain abinda fauziyya ta nema dr jarma bai bata ba
AURAWA TOUFEEQ HASEENA.

"Me ya faru?" Ya sake tambayarta,sai ta sake sakin hawaye

"Ba shakka yaaya toufeeq ya auro yarinyar da zata rabamu dashi" mamaki ya kamashi

"Kaman yaaya? wai säahar kike nufi?" Kai ta jinjina masa

"Itafa,tun daga lokacin da tazo gidan komai ya canza,shi kansa toufeeq ya sauya,a yanzun ban isa da shi ba,sai abinda tace,hatta da gaisuwa bankai ta shigo ta gaidani ba,saidai idan mun hadu a compound na gidan" Shuru yayi hannunsa saman bakinsa yana mamaki, vasan wanne aure akayi da manufar auren dake zukatansu dukka su biyun,to yaushe hankulansu suka hadu guri guda har suka fara mu'amalar da mutum me taurin kai da kafiya irin toufeeq sahar zata fara juyashi ya soma daukan maganata?

"Yanzun me va faru?" Hawaye sosai ta matso

"Waini yarinyar zata kalla tace daga yau tanamin kashedin babu ni na fadeela, ta soke bata duk wata kulawa da nake bata,ta shiga ta fita ta canza komai har na makarantarta,abinci bata magani,hatta da daukan yarinyar yanzu babu wanda yake da wannan ikon idan ba ita ba,hatta kaita makaranta yanzun ta maidashi wuyanta". Ga mamakinta murmushi ne ya subuce akan fuskarsa yana dan girgiza qafarsa,cikin ransa aminci da gaunar sãahar tana ratsashi

"Banda abinki da rigima irin taki, kefa yanzun kin girma,da meye kikeson kiji? da shekarunki koda kasuwancinki koda kula da fadeela? ina cewa ke sauqinki ne ma,aiki aka rage miki da nauyi ko?" Sosai ta girgiza,amma kuma ba zata saare ba sai taga abinda ya turewa buzu nadi

"Haba yaaya,haba yaaya, ubanta ma nina raineshi bare diyar? ta yaya kawai don an aurota zamu sake mata kula da diyarmu haka sakaka? yadda yanzu duniya ta zama babu gaskiya,sai a hada kai da mutum a cucuka"

"'ah dakata fauziyya,duk ba za'a samu wannan daga sãahar ba ina kyautata mata zato, banda abinki meson naka ai shima naka ne,ki bar musu diyarsu don Allah, ki cire ranki daga wannan qanqanin abun,duka ba damuwa bane"

"Yanzu ba zata tsawatar ba kenan yaaya?" Murmushi ya saki yana girgiza kai

"A'ah ni bazan shiga wanna maganar ba, diyarsu ce, inda ace kina qorafi ne akan nadeeya to itace 'yarki sai kuma inda qarfinta ya qare" Boom 💥 taji wani abu cikin kanta,karo na farko data fuskanci haka daga
gurinsa, bai taba ganin hawayenta ba ba tare daya zartar da abinda take muradi ba. A yanzun shurun da tayi ma
kamar bai fuskanci bacin ranta ba,janta ya shiga yi da
hira yana yi mata tayin abinci

"Alhamdulillah na qoshi, zan wuce gida na baro meenal
ita kadai,kasan kuma baquwa ce har yanzu"

"'Gaskiya ne ya kamata tazo tayi kwana biyu su saba da mamarta da yar'uwarta"

"Zatazo" ta amsa masa a taqaice,saboda ta qagauta ta

fita daga cikin gidan ko zata samu damar yin
kyakkyawan tunani akan yarinyar,sai takejin kamar wata masifa ce ke tunkarota.

System ya tura mata da tarin wasu ayyuka da zata
tattara masa bayanan guri guda. A nutse take aikin
tamkar ma bata office din, lokaci lokaci tana ji a jikinta
tamkar yana kallonta ne,amma kuma duk sanda ta daga kan nata don ta tantance sai taga idanunsa yana saman system.

Mintuna goma sha biyar kacal suka rage lokacin
break ya cika,har a lokacin bata motsa ko ina ba tana zaune tana gogarin tattara aikin da ya bata hatta da wayarta ma a kashe take, don batason tayi wani abun ma da magana zata shiga tsakaninsu.

A karo na barkatai ya sake satar kallonta, shi kansa
bazai iya tuna wani abu a rayuwarsa da ya yiwa adadin satar Kallon da yayi mata ba ba tare da shi kansa vasan satar kallon yake ba. Dai dai lokacin data zura hannuwanta ta cikin lafayar ta kuma bayan wuyanta tana gogarin tattare gashin data nannade, santsinsa ya sanya ya ware da kansa yake kuma damunta a wuya. Hakan ya baiwa laffayar damar zamewa, lallausan gashin nata dake da wani irin bagi da daukar idanu ya ware a kafadarta ta hagu. Tana qoqarin mayar da mayafin kira ya shigo ta wayar office din. Ta daga kai zata kalleshi suka hada ido, basarwa yayi cikin shan gamshi va kuma hade rai sosai, don bayason ta fahimci tun ba yanzun ba idanunsa ke kanta

"Kin manta aikinki ne?" Ya fada a dake,har ta dan juya
idanunta zata sauke masa harara sai tayi saurin gyara
kallonta,tayi rolling qwayar idanun tamkar me yin fari.
Wani irin ayalli idanun nata suka bada,a dole ya rusunar da kallon nasa daga kanta. Migewa tayi a nutse ta isar ga wayar ta daga,ta kara a kunnenta tare da yin sallama da nutsatsiyar muryarta me sanyi da taushi. Cak ya tsaya daga singing din da yakeyi sautin yana shigar masa kunne

"Idan kuma namiji ne fa?" Yaji tambayar ta fado a ransa,sai ya rige biron a hannunsa yana juyashi tare da son tsinkayo muryar waye a wayar.

"Ma sha Allah, ina fatan Khadija Muhammad girema ce?"

Mamaki ne qwarai ya kama sãahar, ta yaya za'a yi kira a wayar office office din da ba nata ba amma farat daya a kama sunanta?

"Eh itace"

"Good,na buga dai dai kenan.....kina magana da
Ameesha,ex_wife din mijinki muhammad
toufeeq,maama ga FADEELA" sosai ta gyara tsaiwarta ba tare da tace komai ba

" Zuwa yanzu nasan fes kin fahimci wacece ni din"

"Me kike bugata" garamar dariya ta saki

"Naji dadi dana sameki me saurin fahimta,hakan na nunamin bazan sha wahalar fahimtar dake lokaci yayi na dawowata gida na ba"

"Dashi ya kamata ku garasa wanna maganar" tà gintse ameesha din daga abinda ta kira da soki burtsu a waienta. Waiwayawa tayi gareshi bayan ta dauke wayar daga kunnenta suka hada ido dashi, idanunsa zube fes akan fuskarta yana son ya karanci wani abu. Bata bashi dama ba don dauke kanta tayi, ta qarasa gabansa ta rangwafa daga saman table din tana gyara masa zaman wayar a gabansa,wannan ya baiwa ragowar gashin kanta damar qarasa warwarewa,iskar dake shigowa daga window ta buso masa dukkan gamshin dake magale a jikinsa harda tsarabar shafar gefan fuskarsa. Ido ya lumshe a hankali yana jin yadda zuciyarsa take bada wani sautin bugu, sanda zai bude idon harta ja da baya tana sanya takalmanta ba tare data dubeshi ba tace

"'Baguwa keson magana da kai" bata tsaya sauraronsa ba ta dauki hand bag dinta da wayarta ta fita daga office din.

Kamar zaman jiran ganin me shiga da fita daga office din saima tayi tana fitowa suna hada ido,saita dauke kai tana nufar living room dinsa dake cikin office din. Ta dora hannunta zata murda handle din living room din sai aka budo ainihin gofar da zata sadaka da sashen saima. Sai ta waiwaya tana duban qofar.

Sanye take da wata gown na Vintage clothing, saman kanta lullube da siririn scarf data nadeshi daga kanta zuwa wuyanta kawai,fiye da rabin fuskarta sun glasses ne ya mamayeshi, sai wani rufaffen takalmi me tudu data sanyawa qafarta, daya hannun na maqale da hand bag yar mitsil, daya hannun kuma wani foldable basket ne da aka shirya qananun warmer's masu kyau a ciki. MEENAL YA'AQOUB AJI kenan,sananniya ga duk me ta' ammali da kafofin sada zumunta,wanann dalilin ya sanya saima miqewa tsaye cak suna kallon kallon a tsakaninsu. Koda batace ba tasan gurin toufeeq tazo,don duk wanda ya santa,yasan ita daya ce tallin tal dake wallafa hotunansa kusan koda yaushe saman shafukanta na sada zumunta. Batayi mata kallo na biyu ba ta murda gofar room din ta shige ta barsu suna kallon kallo tsakaninta da saima.

"Madam ina zuwa haka?" Saima ta tambayi meenal cikin gatse. Dawowa tayi da baya tayi qasa da glasses dinta ta qarewa saima kallo,sai ta saki wata dariyar rainin wayo

"Jealousy"' ta fada cikin nishadi sai kuma ta dora

"Zanyi mamaki gwarai idan kikace wai baki sanni ba…
Meenal ta fada cikin izza da jin cewa ta kai ta kawo ta kuma shirya gogawa da kowa akan TOUFEEQ,tasan da saima already tasan kuma zaman me takeyi a gurin…
*HUGUMA*


* TABARMAR KASHI_*


Book 02 Page 26

.. Anyways, nazo wajen masoyina ne kuma mijina" daga haka ta juya ta nufi office din kai tsaye. Zallar mamaki ya hana saima cewa komai,sai kallon zallar mamakin da ta bita dashi. A cikinsu wace ainihin matar tasa?,ko mata biyu ya aure lokaci guda basu sani ba?.
A nutse take takawa cikin living room din dake tsare da sofas masu tsada da aka sake zubawa,sofas din da kake da ikon lanqwasa su duk shape din da kaso,daga kujera me qaramin table a hannunsa zuwa matsakaicin gado tare da pillows. Jakar hannunta ta ajiye saman sofa din a hankali. Kalaman ameesha ne suka fara dawo mata fes cikin qwaqwalwarta. Siririn tsaki taja gana jin zafi a zuciyarta da matar ta kasance mahaifiya ga fadeela, juma'ar da zatayi kyau tun daga laraba ake ganeta, kuma ita din ba qanqanuwar yarinya bace, dukkan alamu sun nuna zaiyi wahala a samu karamci kamun kai da sanin ya kamata daga gurin matar, kalaman bakinta kawai sun gama gayawa säahar wacace ita din. Sake jan tsaki tayi tana nufar gofar da
aka rubuta Toilet daga samanta da wani irin rubutu
ruwan azurfa. Tura bandakin tayi ta shiga tana binsa da
kallo komai kar kamar ka zuba abinci a ciki kaci. Fitsari
tayi ta daura alwala sannan ta fito ta tayar da salla. Ko'
bayan ta idar zamanta tayi saman lallausar abun sallar
dake ajjiye har guda uku a wajen. Tana azkar kadan
kadan tana tunanin abinda zata ci.


Fuskar haseena dake shigowa da kwanukan abinci
ne ta dawo mata,cikin shigarta dake nuna halittar
sirantakar da Allah yayi mata tako ina wanda wala'alla ita
bata ganin hakan. Gefe daya kuma fuskar saima ta
fado, duk yadda takeson kore tunanin komai daga ranta
amma sai ta gaza aiwatar da hakan?. Wai meye tattare da shi da sauran maza basu dashi suke wannan parade
din a kansa,kamar qarar wayarta shine amsar
tambayarta sai kira ya shigo mata,wanda shine ya zama
silar yankewar tunaninta ta dauki wayar tana dubawa.
Bestie afifa ce, saita saki murmushi sannan kuma ta tura
baki gaba,tabbas sai ta fanshe shakulaton bangaron da
afifan tayi da ita ta daga wayar ta koma saman abun sallar.

"bestie bana yi, bestie kinci amanata" sãahar ta fada
tana harara wayar tamkar dai afifa na wajen

"Don Allah bestie kiyi haquri, wallahi ban taba
experiencing irin wannan yanayin ba a rayuwata" afifa ta

fada da muryarta data gama komawa me sanyi. Ta fahimci maganar afifan, don haka ta sanya hannuita toshe bakinta saboda dariyar da take cinta

"Na miki uzuri bestie, Allah ya bada lafiya"

"Wai Allah bestie, naga rayuwa,sai yau na samu space da hayatee ya taho company" baki sãahar ta tabe, ita kwata kwata wadan nan sabgogin basa burgeta ko kusa ko alama,kafin tace wani abu afifa tace

"Amma bestie lafiyanki qalau kuwa? ,kina cikin hankalinki kike shirin sakarwa mata mijinki?,wannan na ciki wannan ta shigo?" Maganar tadan baiwa sãahar mamaki

"Kamar yaaya? dama na aureshi ne don na kula sa sabgoginsa ko kuma na kula da diyarsa?" Ta jefawa afifa tambayar. Goshinta ta dafe tana lumshe ido, sãahar dai bata canza ba?,a kwanakin d sukayi tare ta dauka komai ya fara canzawa dangane da junansu a zukatansu

"Saahaaarrrr....... please ya kamata ki koma cikin hankalinki,hayatee yazo office dinsa ya taras da hakan, saboda yana kishinsa yana kishinki kuma yana kishina yasa ya gayamin....i was so shocked...
...nasan

ba haka bestie na take ba, aure ai ba abun wasa bane

bestie, ko banza igiya ce me girma a tsakaninku...
...moha
ba normal irin gama garin maza bane,wannan abun da kike na shakulaton bangaro ba komai zai haifar miki ba sai d'a maras ido, ki tsaya kawai kiyi abinda ya kamata ki manta da komai" baki sãahar ta tabe


"Yaushe kika koma me bada shawari?, kinje kin kurbi giyar aure ko?,hmmm sannu farin shiga,to na gode da shawara,amma ni ba ruwana da abinda ya shafi rayuwarsa,wannan shi ya zabarwa kansa,ya auri mata dubu ma ya kula million a yau duka shi yaso, zan wuce gida yanzu lokacin tashi ya kusa,idan na isa zamuyi waya,inason mu tattauna akan wani abu daya fara tunani a kai"

"Allah yasa maji ta aura masa uku tsala tsala larabawan
Algeria"

"And so what!" Ta fada da lafazin da ya sanya fifa shegewa da dariya

"Allah sarki bestie,Allah ya baki lafiya,sannu" mamaki ya kamata,me afifa ke fada?,kawai sai ta sauke wayar ta kashe,taga alama so take kawai ta tuburata.

A nutse ta maida wayar jakarta,ta fidda wata siririyar roba doguwa da bata rabo da ita ta murza turare,ta warware lafayarta ta gyara zamanta sosana ilkinta,ta kuma gyara daurinta,sai gashi ta fito d'ass da ita,wani sirrintaccen kyan amarci da batasan dashi ba yana bayyana saman fuskarta. Jakarta ta dauka ta rataya a hannunta ta fito daga resting room din.

Wayam mazaunin saima yake, ba kowa sai takardu da na'ura a gurin. Kanta ta sanya kai tsaye office din nashi, ta murda qofar ta turata.

Idanunsa na zube fes akan qofar yana qarasa jin abinda ameesha ta fadiwa sãahar a waya ta a dazun data kira kafin ta ajjiye masa wayar ta fice. Can qasan maqoshi ya amsa sallamar,ta tako zuwa ciki ba tare data dubi fuskarsa ba kamar tasan ita din yake kallo,hakanan bata kalli ko sashen da meenal ke zaune ba,wadda ta ajjiye basket din saman table dinsa ta kuma zauna saman kujeru biyun dake gaban table din nasa,idanunta a kansa tana qoqarin shanye maganar daya gana gaya mata,tana jin zata iya jure koma meye, tunda ta sanshi,ta kuma yi imanin dama bawai zata sameshi ta sauqi haka ba. Dan binta yayi da kallo,sai itama meenal din ta rakashi da kallon, ta kuma janye idonta daga kan sãahar bayan ta tabbatar sãahar din idanunsa suke kalla. Haka kawai wani irin bacin rai ya cika masa maqoshi,yana datse kiran ameesha ita kuma haseena ta sanyo kai da tarkacen kayan abincinta. Can cikin ransa yana jin zafin me yasa zata daga wayar ameesha har ta bashi?,me kuma yasa ta barwa meenal damar shigo masa office da kayan abinci?.

Ido meenal ta qangance, tun daga zuciyarta har ruhinta tana jin matsanancin kishin kyan da säahar ke dashi,yau ne tayi mata kallon fes ta gefen idanu,duk yadda takeji da gayu da kyau sai takejin a yanzun ta muzanta idan aka kwatantata da säahar din. Duk da shigarta shigace ta gargajiya a wajen meenal,don ita bata taba kwatanta sanya suttura full irin hakan ba,to amma ayau sai taga shigar tayi mata mugun kwarjini, abinda bai taba faruwa da ita ba.

"Ina da abunyi so zan wuce gida, inason tsaiwa na dauki fadeela" ta gaya masa tana sake matse agogon hannunta ba tare da ta kalli fuskarsa ba. Zare idanunsa yayi daga kanta a hankali yana dai daita zamansa.

"Tana da abunyi ma take ce masa?,waye bashi da abiny kenan" Bata jira amsarsa ba ta tako a hankali ta qaraso gaban table din nasa amma ta left side dinsa, akwai file da take da bugatar dauka kuma suna ta wajen,abinda ya qara kusanci kenan a tsakaninsu sosai,sassanyan gamshinta na haurawa hancinsa yadda ya kamata,tsaiwar da tayin kuma a wajen ta baiwa haseena damar ganinta sosai fiye da dazun. Zara zaran yatsunta da suka sha lallae tabi da kallo a sace, kamar yadda shima nasa idanun suka sauka akai,launin kalar tana bala'in jan hankalinsa. Hannu yasa da sauri ya dafe wani file da take shirin cirowa,wanann ya baiwa hannuwansu damar haduwa guri guda,take haseena taju zuciyarta
tamkar zata fashe,ta dauke idanunta daga kai tana
migewa.

"Ki koma dasu gida,bana da enough time da zan iya cin
abinci har haka a office" ya bata amsa yana maida file
din tare sa cirowa sãahar din na gasansa daya tabbatar
shi take nema. Tana karba ta soma takawa zata bar
gurin,lokacin meenal ke maida kwanukanta cikin
kwandon tana jin wani bacin rai ranta kamar zai fashe.
Bata taba zaton zai watsa mata gasa a ido ba yace ta
koma da abincin ba,ta hada komai a gaggauce ta nufi
hanyar fita tana qoqarin danne fushinta da hawayen da
ya cika mata idanu,saboda batason matarsa taga
karayarta. Meenal na fita tabi sahunta,saidai kafin takai
ga fita ya amsa mata zancan dauko fadeela daga
school,har yanzu ransa na susa,tare da jin bacin rai da
mamakin yadda ameesha ta samu number wayar office
dinsa bayan yayi blocking nata a dukka wani layi da
yasan zata iya samunsa.

"Fadeela nada driver,so ba buqatar kije daukota,ki tsaya
kiyi aikinki" waiwayowa tayi ta kalleshi sosai,sai lokacin
taga yadda yanayin fuskarsa ya canza da kyau

"Ba dole bane ace driver kullum shike da alhakin
jigilarta,daga yau shima na soke wannan saidai idan da wani dalili me qwari" barin aikin da yakeyi yayi, ya dauke hannunsa yana soke yatsunsa guri guda, idanunsa a kanta. Cikin ransa yana jin kamar ba wannan aikin ya kamata ta bawa muhimmanci haka ba,yayin da wani sashe na zuciyarsa kuma yake son daga martaba da kimar abinda tayin tare da son gamsar dashi

"Zauna muyi magana" yayi furucin cikin rashin son wasa a fuskarsa. Kai tadan dauke, kamar ba zata zauna ba kuma ta dosana kadan a saman kujerar

"Kome zakiyi kiyi qoqarin kare martabar hajiya,saboda ita din kamar maji take a gurinmu" kai ta girgiza

"Ba maji bace,ba kuma zata taba zama maji ba,am sorry to say ban yarda da kowa ba akan fadeela,saboda nayi experiencing wani abu da yaso tarwatsa rayuwata shigen abinda fadeela ke shirin fuskanta daga gurin mutumin da yafi kowa kusanci dani" ta qarashe maganar muryarta tana rawa. Har cikin jikinsa yaji wani abu ya tsarga masa,ta miqe tana qoqarin boye qwallarta,batason zubda hawaye a gabansa

"¡ have to go" kamar bazai amsa mata ba sai taga ya mige,ya tura kujerarsa baya ya fito a hankali daga gurin ya zauna saman resting chair yana maida takalminsa,ya daura agogonsa sannan ya dauki wayoyinsa da system dinsa sannan yace

"Let's go" sosai tayi mamaki, saboda bata taba kawowa zaice suje din ba. Danne mamakinta tayi tayi gaba yana biye da ita a baya.

A hankali take takawa da irin takunta nan qafafunta akan tsari,wanda sai kayi tsammanin tana sane take shirya takun nata daya bayan daya. A hankali a hankali sai taji kamar gafafunta suna neman hardewa wannan va sanya ta sake rage saurinta sannu a sannu har ya cimmata suka dai daita kafada. Kusan a tare suka daga idanu suka kalli juna,sai kuma kowa ya dauke kansa yaba basarwa, itakam harda qarin matsawa gefe.

Ihun murna kawai fadeela tadinga saki sanda taga sãahar harda abby dinta wai sun biyo daukarta,abinda bata taba samu ba kenan. Yana zaune vana kallonsu ta cikin glass din yana jin wani farinciki na ratsashi saboda walwalar da ya gani saman fuskar fadeelan,wai me ya hanashi yin hakan shi tsahon shekarun da suka shude? ya barwa driver komai da komai na hidimar daukota da kaita?. Ido ya lumshe yana jin wani farinciki.

Duk yadda yaso ga dannewa amma ya kasa sai da ya furta

"Thank you"sanda take maida murfin motar tana rufewa.
Cike da mamaki ta kalleshi sai kuma ta basar

"It's my pleasure" ta amsa masa tana dire school bag din fadeela da tuni ta haye jilkin Abby dinta tana cewa yau itama 'van class dinsu sunga abby dinta da mammanta sunzo daukarta kamar yadda ake daukar kowa.

Sanda suka isa gida ko sassanta bata shiga ba suka wuce sashensu, nadeeya daketa zuba idanun dawowarsu ta tarbesu suka dunguma,shi daya ya wuce ciki, sai daya shiga yaga dining wayam sannan ya tuna Jacob fa bava nan, garamin tsaki yaja ya wuce bedroom dinsa. Duk abubuwan daya aiwatar tun daga wankansa canza kaya da fresh milk da yasha ba hakan bai mantar dashi tunanin dake magale a kwanyarsa ba,meye yasa tace bata yarda da kowa ba? me yasa wani irin rashin jituwa yake gudana tsakaninta da hajiya qaraman cikin dan lokaci kadan?,da wannan tunanin ya gama hutunsa cikin sashen,har aka kirayi magariba yayi alwala suka fita sallah shi da jibril. Bayan ya dawo sallar sashen hajiya qarama ya shiga,don bayan ya fito jibril ya shaida masa sau uku tana aikowa kiransa, ba'a gaya masa bane sabida sunsan dai dai lokacin hutawa yakeyi.

Yaji dadi da bai samu meenal ba a sassan,ya samu guri ya zauna yana gaidata

"Ka kusa fin garfina ai toufeeq" hajiya ta fada tana tara hawaye cikin idonta. Mamaki abun ya bashi qwarai

"Me kuma ya sake faruwa,i thought kun gama magana
da Dr ko akan komai?"

*HUGUMA*

* TABARMAR KASHI *

Book 02Page 27

"Amma toufeeq kamar ni?, meye amfanina a cikin gidan idan ban kula da fadeela ba" ido ya lumshe sannan ya bude,ya gaji gaba daya bayason wani daru

"Karki wani damu, tattaromin magungunan ki bani,

Please Login or Register in order to submit comment