Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 12 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanyin rai da kuma nutsuwa,kawai dai bata iya nutsuwa muddin taga mahaifinta

"Alhamdulillah,mun yini cikin qoshin lafiya" wannan kusan itace amsar da tafi masa kowacce amsa dadi a rayuwarsa,hakan yana nufin fadeela bata hadu da hatsarin da kowacce rana,tun daga bullowar rana zuwa faduwarta zata iya fuskanta ba,lalurar dake sanyawa duk wanda suke tare dashi fargaba,suke kwana su kuma tashi cikinta.

"Hajiya qarama ma ta dawo" baaba ramatu ta fada a ladabce,abinda yasa ya dakata daga tafiyar da yakeyi,sai ya sauya akalarsa zuwa sassan da 'yan aiki suketa kai kawo,da alama suna aikin gyaran sassan ne.

Fadeelan na biye dashi tana ci gaba da bashi labarai,wanda ayanzun ta sauya akalar labaran nata ne kan MOMMY QARAMA,kayan wasan data kawo mata da sauran tarkacen wasan yara.

Daya daga cikin tafka tafkan sashe ne cikin sassan dake gidan,wanda kusan a manne yake da sashen da fadeela da baaba ramatu suke rayuwa a cikin sa.

Kamar kowanne sashe na gidan,shima masu aiki ne mata ke kai kawo tsakanin makeken falon da yayi girman wasu gidajen kitchen,dining area zuwa balcony din da bedrooms din sassan suke a tsare,har ya zuwa upstairs din sassan da nasa falon.

Tun daga qofar falon suke zubewa suna gaidashi,ba tare da damuwa da cewa ko sau daya bai samu amsawa kowa ba a cikinsu. Sun riga da sun saba da wannan yanayin nashi,zasu iya cewa tsahon shekarun da suka dauka a tare dasu,basu taba katarin ganin koda murmushi akan fuskarsa ba bare akai ga dariya.

"Hajiya qarama fa?" Ya tambayi matar data fito a kitchen ta kuma zube a gabansa cikin ban girma

"Tana sama" bai amsa mata ba,ya fiddo wayarsa ya fara kiran wani layi. Bugun farko aka daga cikin qasa da second daya ya amsa da

"Okay" ya maida wayar aljihu,ya zauna saman daya daga cikin kujerun yaja fadeela jikinsa ya dorata saman cinyarsa yana ci gaba da bare mata chocolate din.

Minti daya tal motsi ya fara tashi daga upstair din,kafin daga bisani sautin takalmi dake bada d'as d'as ya biyo baya.

Farar macace doguwa sambal,ma'abociyar tsaho da kuma qibar da batayi yawa ba,koda batayi kama da toufeeq ba,amma tun kallon farko zakasan cewa akwai alaqa ta jini me qarfi a tsakaninsu,dukkansu kuma babu qarya......a duban farko kadai zaka gane ainihin yare da qabilar da suka fito wato SHUWA.

"Marhaban Muhammad" tayi maganar murmushi kwance akan fuskarta,muryarta ta sanya fadeela zamewa daga jikinsa ta doshi stairs din tana murmushin itama

"Basai kin hauro ba,saukowa zanyi UKTIE" dai dai sanda ta qarasa saukowar,saita miqe hannunta duka ta riqe fadeelan da kyau,cikin wani irin duba me cike da zallar so qauna da kuma kulawa.

Kujerar gefansa ta samu ta zauna tana bashi duka hankalinta

"Yanzun kake shigowa?,sanda na dawo ai baaba ramatu tacemin baka jima da fita ba" kai ya jinjina,cikin nutsuwarsa yace

"Barka da dawowa,i hope komai lafiya" murmushi ta kuma sakewa,tamkar kumatunta basa gajiya da fidda murmushin

"Barka kadai jarma,lafiya alhamdulillah,inacan inata kewarku,hankalina gaba daya yana kan uktie,ina fatan tun tafiyata ba'a sake samun wata matsala ba?" Kai ya jinjina yana lumshe idanunsa hadi da budesu,da alama hakan kusan wata dabi'a ce tasa a duk sanda yake magana

"Komai an samu sauqinsa, alhamdulillah" ya furta cike da fatan hakan taci gaba da kasancewa. Zai iya cewa komai na jin dadin duniya ubangiji ya mallaka masa shi,saidai ita rayuwa bata taba tafiyarwa bawa a yadda ya sota dari bisa dari,hakanan bata taba kubuta daga tarin qaddara da jarrabawa,lalurar fadeela na dukka abinda ya sameshi a can baya ya aminta na daya daga cikin qaddarorinsu,kuma sila na samun tawaya daga cikar jin dadin duniyarsa.

"Na dawo na tarar julia bata nan" ta fadi fuskarta na nuna tsantsar fushi

"Na sallameta" ya amsa mata a taqaice,don shi din mutum ne da bayason doguwar magana sam sam sam

"Shine dai dai hakan da kayi,ta yaya za'a dauki a ninka miki salary dinki na asali sannan ki kasa aiwatar da abinda aka daukoki dominshi?,wannan ai tsantsar yaudara da kuma cin amana ne,naso ina nan,daa kafin tabar gidan nan ba shakka sai na hada mata da hukunci" sumarsa ya shafa da hannunsa daya sannan ya miqe

"Ya wuce"

"Allah ya tsare gaba,zan saka madam Stella ta sake lalubo wata,tsayayya da zata iya kulawa da ita" tayi maganar tana shafa sumar fadeelan cikin kulawa

"Yayi,but idan aka sake samun kuskure kusa dana baya,itama zata rasa aikinta ne kamar su"

"In sha Allah wannan shine karo na qarshe,masu aiki duka babu aminci,kowacce da irin nata sakacin" tayi maganar cikin salon fada. Dai dai sanda labulen daya lullube qofar balcony din dake falon qasa ya bude,budurwa dake ciki ta fito.

Labiba ce sanye da kayan bacci,guntun wandon da iyakarsa cinya,sai wata fingilalliyar rigarsa wadda da kadan ta dara saman cikinta,cup hand ne da ita maqallalle iya dantsen hannunta,kanta baby dankwali,sai gashinta dake daure a ribbons,kusan kowacce sura ta jikinta a bayyane take. Ganin taoufeeq ciki falon sai ya qarasa kashe mata jiki,kowacce gaba ta jikinta ta amsa,amma kuma kallon daya watsa mata ya dakatar da ita daga tahowar da take izuwa gurin,ta tsaya cak tana tuna gamuwarsu ta qarshe,marin da fuskarta tasha da kuma irin zazzafan gargadin da yayi mata.

Bai sake duban inda take ba ya juya ya fice abinsa daga falon a nutse cikin qasaitaccen takunsa.

Wata ajiyar zuciya me qarfi ta sauke,sai daya fitan sannan ta samu sukunin qarasowa,idanun hajiya qarama a kanta har ta zauna

"Lafiyarki ke kuma?" Sake sakin ajiyar zuciya tayi,tana karbar ruwan tea da fried egg da daya daga cikin masu aiki ta kawo mata

"Muhammad"

"Me yasa kullum tunaninki da dukkan furucinki ko yaushe a kansa yake?" Kai ta girgiza tana ajjiye cup din da tayi niyyar kaiwa bakinta ta fasa

"Mommy,wani irin fitinannen so nakeyi masa,ba zaki gane yadda nake jinsa a raina ba,i can't imagine my life without him" wani irin duba na tsanaki hajiya qarama take binta dashi tsahon wasu sakanni ta ajiiye numfashi,sannan ta gyara zamanta.

"Kiyi qoqarin ragewa,kinfi kowa sanin halinsa,bayasin shishshigi bayason kuma a fiya shige masa da yawa"

"Zan kwatanta" ta fada badon tana jin zata iya ba,wani sashen na kwanyarta kuma na tuna mata marin da tasha a haduwarsu ta qarshe. Taji babu dadi amma bataji haushinsa ba,daga qarshe ta tattara laifin ta azawa kanta,saboda tasan kuskure ta tafka ba qarami ba,tafi kowa sanin halinsa,ita kanta batasan zata iya aikata hakan ba,amma SO DA ZUCIYA saidai a barsu kawai.

Sanda ya isa sashensa cook dinsa ya gama shirya table dinsa,gurin kawai zaka dauka wani gurin cin abincin shugaban qasa ko wani governor ne,ya samu sajjad har yayi wanka ya sauya kaya daga cikin bedrooms din dake sassan,a nan yabar fadeela ya haura sama shima don ya watsa ruwan.

Minti talatin da wani abu ya kammala shima ya sauko,cikin fararen pajamas marasa nauyi masu ratsin baqi kadan,mutum ne meson amfani da fararen kayayyaki,kusan first choice dinsa a color fari ne.

Tare da tab dinsa ya sauko,ya samu tuni sunyi ready saman dining sai yayi joining dinsu. Yau kam babu laifi a sake yake,hakan kuma sajjad yasan baya rasa nasaba da alamun dorewar lafiyar fadeela.

Suna kammala cin abincin aikin kamfanin da bayanan da jibril ya turo masa na taron yau ya saka a gaba yana dubawa. Shima sajjad din aikin yake ragewa,kowa hankalinsa yana kan na'ura,don haka falon ya dauki shuru.

Sajjad ne ya fara motsawa,ya jawo wata folder ya tura gabansa,ya daga kai yana dubana alamun neman qarin bayani

"Folder din president ce" qaramin tsaki toufeeq yaja,ba tare da yabi takan folder din ba yaci gaba da aikinsa. Tsam sajjad ya dakata yana dubansa

"Wai me kake nufi?,wannan folder din ita ya kamata ka fara dubawa kafin ka duba komai fa"

"Bani da lokaci" ya sake amsa masa a taqaice,sai kawai ya qyaleshi bai sake cewa komai dashi ba.

Ba jimawa bacci ya dauki fadeela,ya tattara komai ya ajjiye,ya dauketa da kansa yabi ta siririn balcony da shi da fadeelan kadai ke amfanin dashi,ya bulla sassansu.

Cikin falon ya samu baaba ramatu,su uku ne,ita da mai gyaran dakin fadeela zuwa sashen wato mabruka,da kuma wadda ke musu girki wato zuwaira,suna zaune suna hira,da alama daukewa baaba ramatu kewa sukeyi.

Shigowarsa a sabe da fadeelan sai duka suka miqe,zuwaira da mabruka kawunansu a qasa suna masa barka da dare,baba ramatu kuma ta qarasa tana karbarta daga hannunsa. Idan da sabo ta saba,muddin yana gari ba kasafai fadeela ke zama suci abincin dare tare ba,yawanci sai dare idan tayi bacci yake kawota,idan kuma dare yayi sosai kwana takeyi a wajensa. Kafin baba ramatun ma ta gama karbarta zuwaira da mabruka tuni sun fece,mugun kwarjini yake musu,girmansa kuma suke gani sosai da har basa iya tsaiwa guri daya da shi idan ba shi ya nema hakan ba.

Da kansa ya rarrage kayan wutar dake falon kafin ya juya ya fice shima.

Inda yabar sajjad ya dawo ya tarar dashi,sai ya duqa ya tattare kayayyakinsa ya wuce daki bayan sunyi sallama.

Saman bedside table ya ajjiye komai dake hannunsa yana dan sauke numfashi na alamun gajiya,ya cire bedroom slippers din qafarsa ya doshi qofar toilet. Alwala ya daura,sannan ya shimfida abun sallah ya tayar da sallahn.

Cikin awa guda ya kammala komai,a maimakon ya hau saman lafiyayyen gadonsa dake lullube da tattausar shimfida,sai kawai ya jawo manyan duvets din dake kai har guda biyu ya shimfidasu a qasa ya sanya pillow,saidai yana kwanciyar yaji kaman ya kwanta akan wani abu. A nutse ya miqe yana duba wajen.

Ido ya lumshe sannan ya bude yana furzar da iska

"Sajjad......inda maye ne ya kamani bazai sakeni ba" ya fada can qasa,ya zaro folder din,har zaiyi jifa da ita ya fasa,ya jawo bedside drawer ya jefa a ciki ya rufe ya maida kansa ya kwanta.

Baiyi cikakken awa uku ba ya farka a firgice sosai,saidai duk da haka bakinsa yana dauke da kalmar

"La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" wani irin birkitaccen yanayi,hautsinannen mafarkin da baya rufa wata biyu baiyi shi ba. Ci gaba yayi da maimaita addu'ar,har ya samu dukka nutsuwarsa ta dawo,saidai jikinsa ya jiqe sharkaf da gumi har ta tsakiyar gargasar dake kwance a hannunsa qirjinsa zuwa qafafunsa,ya miqe a hankali ya doshi toilet.

Alwala ya daura bayan ya kama ruwa,yayi tsaye a gaban madubin bandakin yana ci gaba da watsawa fuskarsa ruwa,sunayen mutum biyu suna masa yawo aka tare da mafarkin daya gama yi yanzun nan a kansu

"Maji,ameesha"


FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*

+22799643131

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥
*H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔
https://arewabooks.com/u/huguma

Page 23

Ya motsa bakinsa a hankali yana maimaita sunan,me yasa yake yawaita maimaita mafarkinsu?,ameesha tuntuntuni ya gama rufe babinta a rayuwarsa.....maji fa?,yasan babu ta yadda zai iya cire jininta daga jikinsa,amma yawaita mafarkin nata a yanayin da yasan a zahiri ba haka rayuwarta take ba shine abu mafi daure kai a wajensa.

Har sai da yaji idanunsa suna dan masa yaji yaji sannan ya kulle famfon,ya jawo towel ya goge fuskarsa data qara wani haske,ya fito a hankali daga toilet din zuwa bedroom dinsa,baccin da bai samu ya koma ba kenan,daga qarshe ya matsa ya koma saman sallayarsa ya sake kabbara sallah.....boyayyar rayuwarsa kenan da ba kowa bane yasan hakan.

Washegari da wani irin weakness ya tashi,babu karsashin nan da kuzarin da ya saba wayar gari dashi duk safiya,saidai makara da yayi bai fito lokacin daya saba fitowar ba,don a sanda ya fito din tuni fadeela ta wuce makaranta.

Cook dinsa yana tsaye yana serving dinsa,yayin da shi kuma yake danne danne a wayarsa,sallamar hajiya qarama ta karade falon,sanye take da wani lace na alfarma,wanda ke nuni da zallar tsadar da yake dashi,a kallon farko zaka karanci mutum ce me izza tare da son komai na alfarma da kerewa sa'a,don a iya takun tafiyarta ma kawai ya nuna haka.

Kujera daya taja ta zauna cikin kujeru shiddan dake zagaye da mulmulallen dining table din me wani irin siffa da tsari,a gurguje Noah cook din nasa ya kammala zuba komai bayan ya zube a qasa ya gaidata,ya sauka da sassarfa yana barin parlor din zuwa kitchen don ya tsaftaceshi hadi da kammale komai kamar yadda ya saba a duk sanda ya kammala girkawa uban gidan nasa abinci,daya daga cikin dokokinsa daya kafa masa akan tsafta ne,baya qaunarta sam sam,sai kuma akayi sa'a shima Noah din gwanin tsafta ne dama.

"Kunyi waya da maji kuwa a kwanan nan?" Ta tambayeshi da kulawa,kamar ya dago kansa ya kalleta saboda ambatar sunan da tayi,wanda hakan ya tuna masa da mafarkinta da yayi a daren jiya,sai kuma yaci gaba da diban chips da yakeyi a fork

"Bamuyi ba,bata kirani ba" boyayyar ajiyar zuciya ta sauke,duk da hakan batajin nutsuwa a tattare da ita,shurun maji ta tabbatar bawai yana nufin tabar mata toufeeq bane,hakanan a duk sanda shurunta ya tashi maido da amsa......yana magana ne cikin amo da amsa kuwwa me qarfi,irin qarfin da ita kanta takejin sautin saman jiki da zuciyarta. Ta sani,ba sanin jiya ko yau ba......itadin jarumar macace,wadda bata yarda da faduwa saarewa ko gajiyawa ba,wannan dalilin ne ya sanya har yanzu burinkan mommy qarama ya gaza kaiwa ga gaci,duk da ta cimma nasara da galaba masu yawa a kanta

"Ka qoqarta kayi kiranta" kai kawai ya gyada mata,shuru ya sake ratsa tsakani,tana mamakin yadda har yau bai iya doguwar hira da ita ba,duk da tana data cewa da yawa cikin al'amuran rayuwarsa

"Nace ba" ta sake fada tana fifita masa tea din don ta saisaita zafinsa,qwayoyin idanunsa kawai ya daga ya kalleta ba tare da yace komai ba har zuwa sanda ya janyesu. Janyesun da yayi ne ya qara mata qwarin gwiwa,idanunsa na dabanne,haka kallon dake cikinsu,suna da kwarjini wanda har yau idan ya dubeta tana jin hakan sosai yana tabata

"Yaruwarka HASEENA,nace kuna gaisawa kuwa?" Sosai tambayar tata ta bashi mamaki,ita kanta daya kalleta sai taga tambayar kamar bata hau dai dai ba,tunda tasan kome yake akwai tsakaninsu

"Bani da lokacin biyewa shirmenta" ya amsa a taqaice. Yanason ya bawa hajiya qaraman haske amma kuma shi din bame sanin yadda zaiyi magana me tsaho bane,a ko yaushe yakanyi magana ne a dunqule,indai bamai matuqar muhimmanci ba,shine zai zauna bayani.

Murmushi hajiya qarama ta saki tana tura masa cup din tea din

"Me kakeso na gayawa daddynka?" Ta sake jefa masa tambayar tana dubansa. Bai amsa ba har sai daya kusa cinye abinda ke bakinsa sannan ya miqe alamun ya gama kenan

"Ya kamata ya fahimceni don Allah" shine amsar daya bata,saiya ciri tissue guda daya ya soma sauka,da kallo ta bishi,sannan daga bisani tace

"A dawo lafiya,Allah ya tsare" taci gaba da kallonsa har ya fita daga dining room din. Dubanta ta dawo dashi inda ya tashin,ta jijjiga kai,sai kuma murmushi ya kubce mata,tadan daki table din kadan sannan itama ta miqe ta fice a nutse cikin qasaitaccen takunta.


***********Kamar kowanne lokaci,yau yadan saba lokacin dawowarsa,don bai shigo gidan ba sai bayan sallar magariba,bayan sun tsaya sunyi sallah a masallacin dake gine daga farkon layinsu.

A kullum itace mutum ta farko da yake fara nema idan ya shigo gidan,yau dinma hakanne,sassansu ya wuce kai tsaye,ya samu baaba ramatu tana gyara kayan ruwa lemo da ice cream kala kala da yake zubewa fadeela a fridge din.

"Barka da dawowa yallabai" tafada cikin mutuntawa,cikin girmamawa shima ya amsa mata,tun kafin ya tambaya kuma ta amsa masa

"Tana ciki ita da hajiya qarama" ta nuna hanyar da zata sadashi da bedrooms dinsu,baice komai ba yaci gaba da takawa da 'yar sasaarfa zuwa dakin,yanajin yadda gajiya takebin gabbansa.

A nutse tare kuma da sallama ya tura qofar dakin,hajiya qarama na tsaye goye da hannayenta,fadeela da sabuwar nannynta na daga bakin toilet,nannyn tana tsane mata jiki da towel.

Sallamarsa kadai ta zaburar da ita,ta watsar da towel din ta tako da gudu,sai ya durqusa mata kamar yadda ya saba,ya bude mata hannayensa ta shige tana fadin

"Oyoyo" murmushi hajiya qarama ta saki

"Shikenan,mun huta da complain din daddy yayi late" siririn murmushin da ba kasafai ake ganinsa akan fuskarsa ba ya saki,wani irin sirrintaccen kyansa ya bayyana

"An dawo lafiya?,ina nan ina sake nunawa nannynta yadda zata dinga kula da abubuwa,bana fatan a sake samun matsala daga kanta" hajiya qarama ta fada,sai ya jinjina kai,yana maida hankalinsa ga fadeela data dauko wani kwali ta miqo masa

"Mommy qarama ce ta bani,kai nake jira ka dawo ka hadamin" karban kwalin yayi hannu bibbiyu

"I hope kince mata kin gode?" Kai ta gyada cike da zumudi

"Good,me zai hana ki bawa mommy ta qarasa ladanta?" Kafada ta noqe,kafin tace komai ma mommyn ta daga hannunta sama

"Inaaa,wannan kuma aikinku ne,nidai na gama nawa tunda na cika alqawari" ta fadi tana dariya gami da nufan qofa

"Allah ya bamu alkhairi tunda tsohonki ya dawo ai kuma shikenan" ta fadi tana ficewa daga dakin.

Duk yadda yaso fa barshi yaje yayi wanka yaci abinci sannan a hada qin yarda tayi,abu daya ta bari akayi,ta kira nanny din nata,tazo ta saka mata kaya,tana riqe da kwalin suka fito zuwa sassansa.

Ta harabar gidan suka sake fitowa maimakon yayi Linkin ya bulla ta sassan nasu,tana gaba yana biye da ita,dai dai sanda qaramar motar da aka gama parking dinta yanzu ke budewa.

Labiba ce ke fitowa,sanye da wani skinny jeans da shirt mai gajeran hannu, high heels ne a qafarta me azabar tsini kamar idan ka takashi da kyau zai iya karyewa,yalolon mayafi ne saman wanda baida maraba da mayafin yaran da shekarunsu ba zasu zarta tsakanin uku hudu zuwa biyar ba

"Hi fadeela" abinda ta fada kenan,idanunta a kansa tana jin wani qunci a ranta,duba daya yayi mata,kallon da bata tunanin ya b'ata second uku yana yi mata shi,ya dauke kansa kamar yaga wani abun qyama

"Hi" yarinyar ta maida mata,sannan ta taka da hanzari tabi bayan babanta da yayi gaba tuni tana kiran ya jirata. Tsaye tayi a wajen har suka bace mata,sai a sanann ta samu qwatar kallonta daga kansu,taja wani dogon tsaki

"Yarinyar sai shegen rashin saurin yarda da sabo fal cikinta,ta kwashe halin tsohonta tsaf" tayi maganar cikin salon mita tana maida murfin motar ta rufe,sannan ta saka mata key tana takawa cikin gidan,zuwa yanzu ta fara tuqewa,zuciyarta ta fara gazawa daga yadda ganinsa yake neman fara yi mata wuya,ta jigata sosai da yadda a yanzun ya sake daure mata fiye da baya. A baya koda zai watsar da ita,koda bazai kulata ba,koda bazai kalleta ba amma bazai kyaret ba,bai kuma taba shata mata layin zama inda yake ba,saidai yayi kamar baisan da ita a wajen ba,ita kuma ko babu komai iya hakan ma tasan wata alfarma ce ta samu,wadda dubban matan dake yawo,suke kamar zasu mutu a kanshi basu samu hakan ba,ko babu komai tana samun daman zama ta kalleshi iya son ranta.

Sai daya tsaya ya hada mata komai,ta sake tubure masa sai daya zauna suka fara yi tare sannan ta barshi ya shiga ciki,wanka ya fara yi,ya dawo ya shirya cikin gajerun pajamas.

Yana tsaka da taje kansa wayarsa ta dauki tsuwwa. A nutse ya jawo wayar yana duba me kiran,MAJI shine ya bayyana saman screen din,sai ya ajjiye comb din hannun nasa,ya jawo stool ya zauna akai yana daga kiran.

Sassanyar muryar dattijuwar,dake cike da wani irin amo dake nuna zallar sanyinta koda a yanayi na halitta ma,tayi cikakkiyar sallamar data saka zuciyarsa dokawa,ya lumshe idanunsa yana amsa sallamar tata,tare da qoqarin tuno watannin da ya shafe ba tare daya kirata din ba

"Ka manta dani ko moha?" Ta kirayeshi da sunan da ita kadai ke kiransa dashi,kuma koda a wani guri yaji wannan sautin ya tabbatar ita dince,ko kuma wani dake da alaqa da ita.

Cikin tsananin jin kunya da nauyinta ya motsa labbansa

"Kiyi haquri" ya fada a sanyaye,qaramin murmushi ta saki,ta saba da jin wannan kalmar ta ban haquri daga bakinsa,har batasan iya adadi ba,bada haqurin da kuma ba wai yana nufin ya daina bane,wani abu ne da yake faruwa tsahon shekaru masu yawa,wanda batasan ranar yankewarsa ba,duk da cewa idan har ta bugi qirji ta kuma daga hannuwanta da sunan samun nasara ba shakka batayi laifi ba.

Cikin wani irin rashin sakewa da kuma rashin sabon da baisan daga ina yake taso masa ba a duk inda suke waya ya fara gaisheta,saidai kuma cike da girmamawa ne

"Ina fatan komai yana lafiya?"

"Alhamdulillah"

"Ma sha Allah,kada kayi wasa da addu'a a dukka wani gaba ta rayuwarka,komai yana da lokaci,kuma nan kusa nake fatan samun wani haske da fatahi daga rayuwarmu gaba daya,ina jikata?" Ta tambayi fadeela cike da shauqin son jin muryarta,wata irin qauna me gauraye da tausayi takewa yarinyar. 'Yar halak din kamar tasan ita ake nema kuwa,sai gata ta buda qofar dakin riqe da games dinta tazo kawo qorafi. Kai tsaye ya miqa mata wayar

"Maji ce" ya fada qasa qasa,saita ajjiye kayan hannun nata duka a qasa,ta tako da sassarfa ta karbi wayar.

Gefe ya koma ya harde hannayensa yana kallon yadda suke waya da maji,kamar sun san juna sosai da sosai,duk da batasan maji ba,amma akwai wanda wani irin sabo tsakaninsu qwarai da gaske,tasan maji a baki kamar me. Lokaci kadan tama manta da daddyn nata dake tsaye,hira suke abinsu,kamar ba daga wata qasa maji din ke kira ba,bata jin katinta sam da take yawan qonawa akan fadeela.

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*

+22799643131

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

[8/17, 6:49 PM] +234 806 578 4295: *H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔
https://arewabooks.com/u/huguma

Page 24




Please Login or Register in order to submit comment