Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 34 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daya tana fashin sallah,a haka bacci yayi nasarar daukarta.
Da zumudinta fadeela data gama shirinta tsaf ta shigo dakin,tana tsammanin ganin sãahar ta shirya,sai ta sameta akwance tana bacci, zuciyarta a karye fuska a jagale ta koma falon

"Ta gama shiryawa?" Nadeeya ta tambayi fadeelan tana qoqarin cire wayarta daga chargy
"Sister nadeeya,bacci ma fa anty N din takeyi"

"Bana tunanin lafiya qalau take gaskiya, kamar na fahimci bata da lafiya" baaba ramatu ta fada fuskarta na nuna alhini. Take damuwa ta bayyana saman fuskarsu gaba daya

"Rabu da ita fadeela muje,may be ma jiyan bata samu isashen bacci ba.na fuskanci kamar tana da zurfin ciki"

"Alamu sun nuna kam" baaba ramatu ta maidawa nadeeya amsa sai suka fice baaba ramatun na rakasu da addu'a. Har sai da suka garasa ficewa ta dauke idanunta tana girgiza kai sai wasu qwalla masu dumi suka biyo kuncinta,ta saka gefan yalwataccen mayafin jikinta ta goge sannan taci gaba da abinda takeyi cikin falon.

/
*******Cikin tarin nutsuwa kamewa da kuma kwarjinin nan nashi yake saukowa daga cikin jirgin tare da jerin matafiya da suke jerin first class.
Ba abinda zaka fara hangowa sai
kyakkyawar farar fatarsa din nan me surkin ja ja,wadda bata cika wani fari me yawa sosai ba saboda surkin jaa din da take dashi.

Sanye yake da button up shirt me dogon hannu cream color dake da maballai gun metal color hakanan slim fit trouser din jikinsa me sulbi ya kasance kalar button din rigar tasa,wasu lafiyayyun loafers ne a gafarsa kalar trouser din jikinsa,nannunsa daure da tsadajjen agogon rolex daya fito sosai sakamakon tattare dogon hannun rigar tasa da yayi kadan ya rage yakai gwiwar hannunsa.

Kwantacciyar sumarsa da tasha gyara take a kwance luf cikin wani tsari da gyara me daukan hankali sai glowing takeyi,hakanan eye glasses din da yayi amfani dashi ya sake fidda kyawawan qwayoyin idanunsa dake da wani yawa.

Ko sau daya bata daga qafa ba wajen sauke tata gafara a duk inda ya ajjiye tasa ba,tana yi tana shagar qamshin lallausan turarensa daya zama abu na farko da ya fara jan hankalinta game dashi,duk bayan wucewar kowacce daqiqa sai taji kamar zuciyarta zata narka a kansa, tsahon awannin da suka dauka kadai a jirgin a tare tana jin kamar zata zauce a kansa,duk da cewa ko kalmar ZO bata hadasu ba,hasalima bata zaton ya ganta. Tana yawan ganinsa a shafukan MEENAL YA'AQOUB
AJI,amma batasan cewa hotuna rage masa kyau da kwarjini sukeyi ba sai yanzu data ganshi physically


"Hi mr man" ta fadi tana dan qara sauri don ta cimmasa,ganin baiko san tana biye dashi ba. Wani faduwa gabanta yayi lokacin da ya waiwayo ya zube mata idanun nan nasa dake da wani irin kwariini da maganadisu "How can I help you?" Kalmar sai tayi mata nauyi,taji kuma ta muzanta,abinda yasa tadan diririce kadan kenan,tayi gyaran murya sanda yake juyawa zaici gaba da tafiya ganin bata da abin cewa

"Mmmm..... ammm,kamar nasan fuskar nan taka,idan ba damuwa....may i get your phone number?" Wani irin haushi da takaici ne ya kamashi,ya tsaya cak har ta cimmasa,ya waiwayo yana dubanta

"What amount do you need?" Hannayenta ta harde a girjinta,tana dan ware idanunta kadan akan fuskar sa,cikin zuciyarta tana jin wannan din dama ce me kyau a gareta,don haka ta saki murmushi kadan

"Five hundred thousand to one million" waiwayawa yayi yana duban jibril,hannunsa daya a aljihun trouser dinsa

"A bata" va dawo da dubansa gareta

"Wannan va zama shine lokaci na farko kuma na garshe da zaki yarda magana ta sake hadamu" daqa haka ta kewayeta yayi gaba cikin qasaitaccen takun nan nasa,ransa yana sake baci,zuciyarsa na motsuwa,yana in tsanar mata da halinsu gaba daya,ya gama yarda kudi yana gaba da komai a wajensu!,kuma tabbas zasu iya aikata komai akan kudi. Yaja tsaki har baisan adadi ba,zuciyarsa na sake quntata a duk inda ya gifta ya tsinci idanuwansu suna binsa da kallo duk da bawai kallon nasu yakeyi ba,amma yana ji a jikinsa, kyakkyawar fuskar yarinyar na dawo masa

"Ya tsani mace me kyau,hadari ce,ya yadda da wannan" ya sake jaddada maganar can qasan zuciyarsa.
*HUGUMA*

* TABARMAR KASHI_*

68

Tun daga nesa da ya hangi angel dinsa bacin ran ya fara narkewa,saidai wannan miskilar fuskar tasa na nan a hade,murmushi bai kubce mata ba sai da yayi hugging fadeelan,wani sanyi da nutsuwar ruhi na saukar masa,hancinsa ya zuqi daddadan turaren sãahar da take amfani dashi,qamshin ya cika masa zuciyarsa da kwanyarsa gaba daya. Zamewa tayi sannan ta duga har qasa tana gaidashi tare da yi masa maraba da zuwa,sosai murmushi ya wadaci fuskarsa,yasa hannu ya kamota yana amsawa da lallausar muryarsa dake nuna zallar gaunar diyar tasa "Waye ya koya miki angel?" Murmushi ta saki

"Anty N"

"she taught her a lot" nadeeya dake tsaye tana dubansu ta qara masa haske ita kanta tana jin alfahari da sãahar din.

Miqewa yayi tsaye yana kallon nadeeyan,fuskarsa a dan hade,saita langabe kai tana dubansa,abinda yasa ya zare hannunsa daga aljihun wandonsa ya miqa mata,dariya ta kubce mata itama ta bashi sukayi musabaha, she's very proud with him,ta yarda yayanta miskili ne na qarshe,yana da wuyar sha'ani wasu lokutan,musamman idan kayi masa bahaguwar fahimta,amma kuma mutum ne me tsananin kula da damuwa da duk wanda yake alhakin hakan yana rataye a kansa,a yanzun tasan fushi yakeson ya gara nuna mata,amma ta karya lagonsa. Haka suka jera su uku,sun sanyashi a tsakiya,yana riqe da hannun kowa a cikinsu sun baibayeshi da surutu. Duk da rashin son magana da hayaniya irin nashi amma yana qoqarin bawa kowa hankalinsa,har suka isa inda motocinsa suke jiransa,daga daga cikinsu BMW sabuwar qirar shekarar Jason ya bude musu suka shiga ya maida murfin ya rufe.

Har yanxu hannunsa na cikin na fadeela yana mamakin yadda tayi kumari,ta ciko sosai ta murie, ta gara haske gashinta ya qara kyau da tsaho,komai nata ya canza sosai

"Abby baka tambayi anty N ba....bata jin dadi,tana bacci ma muka fito, sister nadeeya tace a ayaleta wai" saita karyar da kanta gefe bayan ta gama bashi labarin. Kanta da tun jiya sãahar ta gyareshi tsaf ya shafa

"That's right ‚ku barta ta huta,she will be okay in sha Allah" sai ta magaleshi da kyau tana murmushin jin dadi.

"ya kamata ayi doubling salary dinta ko?" Yayi
maganar yana duban fuskokinsu. Murmushi
nadeeya tayi tana gyada kai
"Yaa salary din da har yau ba'a taba karbarsa
ba?"

"Like how?, Ya mata kadan ne?" Kai nadeeya ta
girgiza

"Bana tunanin haka,tunda mommy qarama ma
kafin tayi tafiya last week naji tana tambayarta
tana bugatar qari ne da taqi karbar salary
dinta? amsar dai kawai No ce,tace bata bugata
ne a yanzun,tafi sha'awar kula da fadeela
kyauta,wannan ya qaramin qaunarta da ganin
girmanta sosai yaaya" ta qarashe maganar
tana kallon fuskarsa. Shuru yayi yana juya
maganar nadeeya a ransa,zuciyarsa sai yaji
sam bata aminta da tsarin ba

"She must collet her salary,coz banga muhallin kulawa da ita a kyauta ba,we can afford all her needs da abinda muka mallaka,basai anyi mana aiki kyauta ba" dan murmushi kadan nadeeya tayi,ta karanci har yanzu akwai wannan zafin cikin ransa bai gushe ba

"Kyautatawa ce fa yaya" waiwayo yayi ya kalleta,kamar zaice wani abu sai kuma ya fasa ya maida hankalinsa ga hanya,cikin ransa da zuciyarsa ya soke tsammani ko ganin kyautatawa daga dukkan wata macace muddin ba wadan nan jinin nasa ba.

Kamar ko wanne lokaci idan ya dawo tafiya irin haka,yakan dauki wasu mintuna a farfajiyar gidan,saboda dukka ma'aikatan gidan masu masa barka da dawowa,ya bincika wasu abubuwan ya tabbatar komai haqqinsa ne ya sansu sannan ya wuce ciki nadeeya jibril da fadeela na biye dashi. Jibril ya ajjiye duk wani abu daya danganceshi ya sallami jibril din don shima yaje gida ya huta,su elyas zasu kasance dashi nadeeva ma sai ta wuce sashensu don ta kammala masa komai don yace abinci zai fara ci,yau kam tace nasu zaici,tacewa jacon yau duk abincin daya shiryawa ogan nasa saidai yayi haquri,yana dariya kasancewarsa me saugin kai, kuma yasan barkwancin nadeeya yace babu komai

"Amma madam,ya za'a yi da abincin?"

"Kaie dashi kuci kai dasu Jason kafin su wuce" cikin farinciki ya dinga juye musu abincin yana fita dasu,duk da cewa dukkan wani dake aiki a qarqashin gidan yafi qarfin ci sha da kuma suttura masu kyau,toufeeq yana daga parlor dinsa yana jinsu,baice komai ba,amma kuma zaiga wacce rigima ce ta sanya nadeeva bayar da kyautar abincinsa bayan yunwar da yakeji,kuma tasan baya son missing abincin
Jacob din,ya yarda dashi da girkinsa,expert ne sosai ta wannan fannin,shi yasa salary dinsa yake na daban. Sai daya sallami fadeela da wasu daga cikin tsarabarta dole saboda yadda ta matsa masa ta bashi guri ya samu ya shige bedroom dinsa din ya watsa ruwa kafin ya zauna cin abincin.

Kowa taqi kulawa a gidan da tarin kayan wasanta da bata gajiya da tara shirginsu,ta wuce kai tsaye dakin säahar.
A nutse ta maida murfin gofar ta rufe,ta qarasa gefan gadon ta ajiye kayan tana kiran sunanta,ganin bata motsa ba sai ta haye saman gadon tana janye duvet din data qudundune a ciki

"Anty N,abby is back,kinga abinda ya siyamin,yace sai ya huta zai daukomin sauran" wata miqa tayi tana jin dukka jikinta yana mata ciwo,dole ta yaye bargon ta miqe ta zauna tana karbar kayan wasan.

Kusan dukka basuyi mata ba,saboda yanayin lafiyar fadeela da take kiyayewa,ta zabe wadanda basuyi ba a ciki tace mata

"Wannan ki ragesu ki ajjiyesu ba yanzu zakiyi amfani dasu ba,saikin qara samun lafiya da kyau soon in sha Allah" kayan tabi da kallo,da alama tanason kayan,to amma tana bin maganar sãahar qwarai,duk yadda tace mata tayi abu ko ta bari tofa zata bi ne. Dole ta miqe suka wuce dakin fadeelan,ta tayata jera na jerawa,sannan ta dawo dakinta ta sauya pad dinta,ta daura alwala yadda zataji dadin jikinta ta fito parlor dinsu.

Da baaba ramatu da nadeeya duka suna kitchen suna kacaniyar hada komai yadda zai dace da tsarinsa,a can ta taddasu

"Yauwa anty N,yanzu nake shirin shiga naga ilkin naki"

"Karki damu,alhmdlh,naji sauqi" ta fada tana karbar shirya abincin,nadeeya ta koma baya tana kallonta,har ta kammala shirya komai tsaf,cikin burgewa nadeeyan ta kasa shuru

"Wow.ma sha Allah,anty N,anya ba catering kikayi ba?" Murmushi ya qwace saman fuskarta data dan canza kadan saboda baccin
da tayi

"Aikin maama na ne da anty farheen"

"Nice name" nadeeya ta sake fada tana
murmushi, zuciyarta kuma na mata kokwanto
akan sãahar. Kota wanne bangare a waye take
matuqa,kuma ta iya komai fiye da yadda ita
din zatayi,ta zarta a abubuwa da yawa,bataga
wata alama ta bugatar yin aikin nanny ba sam tattare da ita, komai nata na nuna wayewarta
da zurfin iliminta,to amma she's very kind,suna
in dadin zama da ita dukkansu,sai sukejin
kamar wani gibi ne dake cikin rayuwarsu aka
cike musu shi da ita,she's nice person,batason
tayi mata wata tambaya da zata bata mata
rai,ko tayi silar da zata tafi ta barsu.

Ba yadda nadeeya bata juya ba akan
tazo suje su gaisa da abby din koda ba zata
zauna cikinsu suci abinci ba ta girgiza kai

"Saurin me kikeyi sister nadeeya? munafa gida daya,kuma yau yau ya dawo shima,yana bugatar ya samu isashen lokaci daku,zamu gaisa ne" da haka ta doje tayi zamanta kitchen tare da baaba ramatu dake shirye shiryen yi musu tuwo yau,hakan ya yiwa sãahar dadi,don ita kanta tayi missing dinsa kwana biyu

"Yadda kike maqalewa wannan bagin abun,ban zaci kina iya cin tuwo ba ai" baaba ramatu ta tsokaneta sanda take kunna gas tana dora ruwan tuwon a tukunya. Janye coffee din tayi daga bakinta tana murmushi

"Inaci sosai baaba,tuwo abincine me sirri al a cikinsa"

"Tabbas,amma mutan gidan nan basu sani ba,zuwanki yasa fadeela ta fara ci,amma ada idan nayi saidai naci abina ni kadai,ya kamata ki rage shan wannan bagin abun ko zakiyi kumari" murmushi ta sakeyi

"Na iya kalolin tea baaba,amma nafi jin dadin wannan din,kamar wata jarrabawa" baki ta tabe tana murmushi

"Jarrabawar ne ma,dake da baban fadeela bansan wanda yafi wani ba" a wannan gabar batace komai ba,sai taci gaba da sipping coffee din har ta kammala ta kamawa baaba ramatu wani aikin,daga bisani da zuwaira ta shigo saita sakar musu,ta dauki wayarta
kuma.

Karo na uku nadeeya ta iso masa da coffee din cikin wasu qawatattun kofuna da butarsu a tsakiya masu ruwan gold,bakinta dauke da addu'ar Allah yasa wannan ya zama na garshe.

Sai daya balla mata harara sannan ya sauki qaramin cup din butar yakai bakinsa,kurba yayi ya hadiye,sannan ya dago dubansa yana kallonta bayan ya dora cup din saman tray din

"the taste is still not good,lemme ask you" ya fada yana ritsata da idanunsa da gwara yasa bulala ya zaneta akan irin wannan kallon nasa

"Don kinje karatu sai kika daina girki gaki yar gata?,wanne mutum zaki jewa a haka kuma kice sunanki mace?" Owalla ce ta cika mata ido,shifa yaa toufeeq damuwarta dashi kenan,akan tsafta da girki yanzun nan za'a ji kanku dashi,sannan baima tsaya yaga abinda ta dafa masa ba iarabar shan coffe dinsa ya motsa masa yace shi zai fara sha,ita sam ba ruwanta da wani coffee,bai dameta ba,shi yasa ma bata damu da iya hadashi yadda ya kamata ba

"Am sorry yaa,nifa coffee kasan am not a big fan of it" sake wurga mata harara yayi

"C'mon,come and serve me" yayi furucin yana duban siriryar wayarsa da yakeson maido network din gasar nan.

Sai data gama serving nasa din sannan ta mige da sauri,

"Ina zuwa yaaya" yasan bita da kallo,baice komai ba yaci gaba da danna wayar tasa yana jiran Jacob yazo ya hada masa coffe din har ta
fice.

Da kadan kadan qamshin shinkafar yake shigar masa hanciwani irin aroma da yasan bana Nigeria bane,tun baiyi niyyar kallon abincin ba har ya maida dubansa kai kallon farko girkin yaja hankalinsa,sai ya maida dubansa ga wayar yadan qara hanzarin don ya kammala abinda yakeyi din ya taba abincin yaji ko ya dace da taste dinsa.

Da sallama cikin hanzari ta isa kitchen
din

"Madam coffee, zan samu coffee?" Ta tambaya sãahar dake goga kubewa a grinder
"Yau kuma sister, lafiya?"

"Me zanyi da wannan bagin abun naku" ta fadi tana dariya cikin salon tsokana

"Yaa moha ne zai sha"

"Eheenn,kinji ko?,yanzu na gama zancan,itama yanzu ta gama sha,Allah dai ya taqaita muku" cewar baaba ramatu,nadeeya ta tayata da

"Ameen dai baaba" murmushi kawai tayi ba tare da tace musu komai ba,ta matsa gaban mini coffee maker din ta juye masa sauran ta hada a wani madaidaicin vacuum tumbler me rige zafi ta miga mata

"Yauwa,thank you anty N,nasan zaiyi dadi duk da bansan dadinsa ba,amma qamshin was so perfect" ciki jin dadi ta juya ta fice.

Yana gama aikin da zaiyi din Jacob na isowa da coffee din,ya rusuna cikin girmamawa ya ajjiye masa
"Thank you" yace da Jacob,wanda sosai yakejin nauyinsa idan ya gode masa bayan ya masa hidima,shi a ganinsa shi ya cancanci yayita gode masa har qarshen rayuwarsa,sai
Jacob din ya juya yana barin wajen bayan ya gyarawa fadeela kujerarta wadda ta bada hankalinta dari bisa dari akan game din da takeyi a sabuwar game din daya hado mata a kayanta

"Ajjiye kici abinci angel" ya fadi yana qoqarin bude coffee din

"Da anty N yanzu nakeci abby,kuma ma na goshi,ta bani abinci sosai kafin mu tafi airport" idonsa ya lumshe yana qara jin dadin yadda alamu ke nuna irin tsantsar kulawar da take samu.

Ya sake yunqurawa zai bude nadeeya ta iso,kai tsaye ta dora tumbler din saman table din tana murmushi
"Here's your coffe yaaya" duban kyakkyawan tumbler din yayi sannan ya maida kallonsa ga fuskarta

"Daga ina?"

"Kasha kaji yaya,i assure zakaji dadinsa sosai"

"Thanks ajjiye a nan" sai ya maida hankali yana bude wanda Jacob ya kawo masa,ganin hakan ya sanya cikin sauri ta bude masa natan,wanda ta rigashi budewar,take tururinsa da qamshinsa suka cika wajen,qamshin da yaja hankalinsa,ya kuma binne na Jacob har baka iya jin scent din nasan.

Tura masa gabansa tayi tana marairaicewa,hakanan yasa hannu ya dauka, yakai bakinsa yayi sipping. Sam baisan yana lumshe idanu ba,baisan ma sosai yake sha ba har sai daya daga tumbler din yaji ba komai,sai yaji yayi saurin qarewa,nadeeya na gefe cikin jin dadin yadda ya shanye din tas ba tare da yayi qorafi ba,sai kawai ta tura masa plate din abincin,wannan karon baiyi musu ba ya dauki spoon din ya fara ci.
*HUGUMA*

* TABARMAR KASHI_*

69

Tunda ya fara ci din baice komai
ba,cikinsa kawai yake kaiwa,wani dadi da
gardin abincin yana ratsa kunnensa da
kyau,zai iya cewa ya manta rabon da ya
dorawa harshensa abinci me dandano irin
wannan,cike da qamshin ganyayyaki da spices
masu gara lafiya da qamsasa abinci.

"it's delicious ko abby?" Fadeela dake leqen
idonsa ta fada,kai ya gyada kawai

"Anty N ce ta dafa fa,ta iya abinci sosai"
dakatawa yayi da cin abincin,ya maida
dubansa ga nadeeya

"how a nanny turn to a cook?" Cikin gogarin daidata kanta ta masa gamsashen bayani ganin yadda ya hade rai nadeeya tace

"Tafi kowa iya girki a gidan nan,ka tambaya fadeela,coffe din nan ma ita ta hadashi" ransa yadan baci kadan,saboda ba'a kowanne hannu yakeson yaci abinci ba

"Amma.....you know my rules?"

"Am sorry yaaya,ta fimu tsafta da komai da kimai Allah i swear" shuru ya danyi,sai ya ture abincin ya balle gorar ruwa ya zuba a cup ya fara sha.

Ranar har dare suna tare har sai da sãahar ta kira nadeeya a waya fadeela tazo tayi mata shirin bacci

"Kizo ku gaisa saiki dauketa please anty N"
"Sorry nadeeya,ina uzurine ta nan haka,ki daure ki kawomin ita"

"Okay" ta amsa mata tana kashe wayar.

Basu jima ba suka snigo fadeela rungume dia ledojin tarin tarkacenta na cive ciye da wasa,daya hannun nata wata ledar ce, wadda ta tuburewa abby din nata sai daya bawa anty N din tata kyautar doguwar riga,sai wani designer din turare wanda zahirin gaskiya nashine na qashin kansa da yake amfani dashi wasu lokutan ya siyosu don ya ajjiye fadeela ta sanya rigima,to be honest baison sharing personal abubuwansa da mutane,amma fadeela ta daukarma anty N dinta.

Sai data gama shiryata tsaf ta gudu gurin abby din nata tace yau a can zata kwana,ta dawo ta gama shirin nata baccin sannan ta zazzage ledar. Komai na ciki ya dauki hankalinta sosai da sosai,daga turaren har doguwar rigar, kana kallonsu kasan na musamman ne,tayi murmushi tana sake in gaunar fadeelan da yadda itama take sonta,ta yiwa kayan guri ta kwanta.


********Kamar kowacce safiya bayan alfir ya gama ketowa,yayi dukka azkar dinsa da addu'o'in sa,gym yake shiga wanda a nan hantsi yake riskarsa.

Guri ne dake cike da dukka qarafuna da nau'in kayayyakin motsa jiki,wajen yana da girma sosai, kuma an masa tsari me kyau,kamar ba cikin gida aka yishi ba,kai kace daya daga cikin ire iren guraren motsa jiki na alfarma da aka gina ne domin neman kudi.

Farare qal din sport wear ne a jlkinsa na kamfanin LULULEMON ATHLETICA,da suka fidda qirar jikinsa qwarai,shafaffen cikinsa dake da wani irin tattarar muscles,singalilin qafafunsa dake dauke da gargasa,a tsaye suke kyam suma da alama naman gurin ya saba da zallar gudu da motsa jiki,dantsensa da hannun rigar ya kamashi tsam shima,ya hada zufa sosai amma hakan bai sanya ya rage gudun treadmill machine din ba.

Sai daya gama iya lokutan daya saba yi din sannan ya tsaida treadmill din, vana furzar da iska daga bakinsa yana dan fidda numfashi me kauri ya sauko,ya dauki water bottle dinsa ya bude ya kafa kai yana shan ruwa. Sai daya kusan shanyeshi ya ajiye bottle din,ya zari qaramin towel din dake ajjiye musamman a guri daban yana goge zufar. Ba abinda bakinsa da zuciyarsa ke marari irin dandanon coffee din jiya,duk yadda yaso ya kauda kai yanzun haqurinsa ya tuqe,a yadda ya gama motsa jikin nan shi kadai jikinsa yake bugata,sai ya tsugunna ya sassauta daurin takalmin qafarsa,ya ajjiye towel din ya fita daga gym room din.

Yana tafe a veranda din da zata kaishi sassansa ma'aikatan da suke da aikin safe suna kawo gaisuwar su,da hannu yafi amsa musu sannan ya wuce cikin tsayayyen takunsa dake nuna zallar lafiya da mazantaka.

A falo ya zare takalmansa,ya zura wasu dake ajjiye a gurin ya qarasa shiga cikin falon,hancinsa na jiye masa qamshin girkin Jacob,mudassir da ya kammala gyaran sashen yana feshe ko ina da wani freshener na musamman dake kashe qwayoyin cuta,kafin ya kunna kowacce humidifier dake aiki a lungu da saqo na sassan,ya rusuna yana gaidashi. Dan dakatawa kadan yayi da tafiyar yana amsa gaisuwar tasa,tare da qoqarin karantarsa

"Ya akayi?" Ya jefa masa tambayar,kansa a qasa yana shafa kan nasa

"Sir, matata ce ke labor tun jiya,amma bata haihu ba,so na barosu ne a asibitin inason tafiya da wuri"
agogo ya kalla sannan ya maida dubansa kansa

"Me yasa kazo aiki?,me yasa baka nema excuse ka tsaya ka kula da amanar da aka baka ba?" Ya fada cikin kaurara murya da alamun fada

"Banason ne..”

"Bakason me?,c'mon,saboda baa jikinka abun yake ba?, maza ka yiwa elyas magana,idan kuma saiiad ya shigo kace nace ya maka sallamar da zata isheka" godiya sosai ya zube yana masa,bai tsaya saurarensa ba ya wuce.
Har yayi gaba ya dakata yace

"idan ta wuce awa daya ka canza mata wani asibitin"

"Yes sir,in sha Allah" daga haka ya wuce hanyar da zata sadashi da hallway. Duk da yanayin da rayuwarsa ta tsinci kanta a ciki amma Allah ya zuba masa masifar tausayin mace me ciki,koda kuwa cikin qarami ne,saboda har yanzu idanuwansa suna iya tuna masa wahalar da maji tayi,tun daga farkon cikin nadeeya har zuwa qarshensa,har yau bai manta ba.

Wannan tunanin ya darsa masa ganin dacewar kiran majin ya gaya mata ya dawo,da wannan qudurin ya shiga dakinsa,saidai kafin yakai ga alkatawa sal ya manta menene ma yace zaiyi din,yakai gauro yakai mari amma ya kasa tunawa,sai kawai ya zare kayan jikinsa ya fada wanka.

Da sallama a bakin nadeeyan ta tura gofar dakin fadeela ta shiga,murmushi ya wadaci fuskarta tana kallonsu

"To bama dole kiyi kumatu ba? don Allah ki gani,da safen nan an tasheki ke daya kina cin kayan dadi ke kadai abinki" dariya kawai suka saka mata

"'Ke da baki tashi da wuri waye zai rage miki?"
Saahar ta fada tana goge hannun fadeela da tissue. Hamma nadeeya tayi

"Yanzunma wallahi yaa moha ne ya tasheni don Allah coffe zaki taimaka ki bani na kai masa da sauri,kada yace ya fasa sha nayi jinkiri " kai sãahar ta daga tadan kalli nadeeya tana mamaki a ranta,don anyi jinkiri kawai sai mutum yace ya fasa shan abu?

"Indai sauri kikeyi to yanxun kam sai milk tea wanda na dafawa faddee,babu coffee"

RA
"Ya salam....a zubamin nayi shahada,idan kuma nasha maruka to kin jawomin tare zamuyi jinya" ta fada tana zare ido.

Miqewa sãahar tayi cikin fuskar mamaki

"Maruka kuma? haba dai"

"Allah ba komai bane wajen yaa moha,yaushe ya daina ne? tafiyata karatu fa" maganar sai tadan daure mata kai,to amma batason tsawaitawa tunda ba huruminta bane,don haka fadeelan na biye da ita tana bata labarin tsaurin yaa moha din har suka isa kitchen, itadai tana saurarenta harta gama zuba milk tea din a wani siririn qawataccen silver flask, qamshin flavour din da yakeyi da su cardamom gaba daya ya cika kitchen din

"Yawuna ya tsinke Allah,wannan wanne irin tea ne? don Allah anty N ki ragemin" dariya nadeeyan ta bata,yadda tayi maganar da gaske cikin marairaicewa

"Ya rage miki,bana zaton zai iya shanyewa" dukka ta zaro fararen idanunta waje

"Wa? niii?yaa moha din zance ya ragemin abu?,idan kin ganni a lahira kaini akai" da mamaki ta juyo tana dubanta

"Wanne irin mutum ne shikam haka?"

Abinda takeson cewa kenan,amma saita maida maganarta ta hadiye. Idan ta saba yin hakan da nata yayyun,nan din ai ba gidansu bane,kowa da irin tsarinsa da nasa ra'ayin,so ba huruminta bane.

Yana amsa waya ya fito daga dakinsa,yayi fes cikin wasu fararen kayan still, da alama zabinsa kenan farin abu ko kuma abu me haske,musamman idan ka duba vanavin furniture din dake qawataccen falonsa. Da ido ya tsire tea din har ya kammala wayar,ya kashe ta ya ajjiye wayar a gefe yana hada hannayensa guri daya,kafin ya maida dubansa ga nadeeya

"Me ya hau kanki ne?,wannan yanzu coffee ne?ko dama inashan tea da madara?" Tasan dama tsaf hakan zai iya faruwa,don haka ta sake maida fuskarta kalar tausayi

"Ba wancan yaaya...amma please kasha wannan,idan baiyi ba Allah na rantse, kayimin hukunci"

"Ya isa,Gate out" ya fada calmly,da sassarfa ta juya ta fice tana dafe qirjinta saboda arzigin data auna yau bata shiga ukunsa ba.

Kaman bazai sha ba kamar dai jiya,sai qamshin ya buwayi hancinsa,a daqile ya dauki cup din idanunsa akan TV ya kurba. Kasa wassafa komai yayi a ransa, saboda qamshi da gardin madarar daya kai masa ko ina,karon farko bayan shekaru masu dama ya samu tea din da yafi masa coffe dadi.
_tom,nikam nace tun yanzu MR JARMA?,WAI YA HADUWAR ZATA KAYA NE? KOWA NA YABON DAN UWANSA BA TARE DA YASAN WAYE SHI BA.MUJE ZUWA_
*DON ALFARMAR ANNABI MUHAMMADU
ME FITARWA KIYI HAKURI KIBAR MANA
KAYANMU*

*HUGUMA*

* TABARMAR KASHI *

Page 70

. Baisan ya akayi ba,shidai ya

Please Login or Register in order to submit comment