Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 38 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bake bake a bakin gofar,kwarjininsa ya daketa da wani qarfi,ya sanya wannan magnet din sosai a kanta da ya sanya ta kasa duban idanun nasa a yanzu.

Nasa kallon ya dauke daga kanta yana zaro complimentary card dinsa,yayi taku biyu zuwa inda take,abinda ya kusa dauke numfashinta kenan,saboda bata ga card din hannunsa ba,saura qiris tace masa ya dakata, Allah yasa batakai ga fada din ba ya zura mata card din a gefen jakarta dake maqale a hannunta

“Idan kin canza shawara you are always welcome,zamuyi aure don ki kula da fadeela kawai, wannan shine manufar,ni kuma zan baki dukkan 'yanci da mafakar da kike nema" daga haka ya juya a cikin nutsuwa da kamewa ya fice.

A qalla sai da yabar gidan ta motsa daga gurin,ta gama tsorata da yadda ya kafeta da kallomsa,batajin ya taba mata irin wannan kallon kai tsaye,yadda ya nufota kanshi tsaye baya ma ko tsoron ya muhyiddeen ya dawo ya ganshi ya bata mamaki. Tsaiwarta ta gyara tana kallon card din, butter milk color da aka yiwa ado da ruwan gold. Tsaki taja,ta sanya hannu ta zaro card din ta watsar a wajen. Wai ta aureshi saboda ya raina mata wayo,shi baisan ko bashi bama ba zata iya auren kowanne namiji ba? ta rasa ma wa zata aura saishi? har abada,Allah yayi mata tsari.

Dukka ta gama wadan nan maganganun cikin banbami a ranta ita daya,ba tare da tasan gaddara tana sauya komai cikin qasa da sakanni ba kamar dai qiftawar ido. Kusan hakance ta sameta,bayan ta samu yaa muhyiddeen kamar yadda ya umarceta,ya kuma shaida mata a satin nan mahmud zai turo magabatansa da komai nasu,aurenta duka duka bazai wuce watan gaba ba,so basa son mata auren da bataso,idan tana da wanda takeso tayi gaggawar gabatarwa da abban nasu. Tashin hankali,shin a dazu ta gayawa toufeeq wannan maganar kenan da harshen malaiku? ,wata gudan data ambata shine ke neman tabbata a kanta cikin mintunan da basu wuce talatin ba?.

Fadin irin mawuyacin halin data fada ma bata bakine idanunta suka soye sai qirjinta dake zafi, batasan me yasa suka dage sai sun aurar da ita ba,bayan har yanzu bata gama healing ba,tana buqatar lokaci sosai,a galla shekaru goma ma a gaba idan sun bata dama.

Ita dava cikin dakin,qarfe biyu na dare tazo ta risketa ba tare da bacci ya ziyarceta ba,sai tarin fargaba da kalmar auren da yaa muhyi ya furta mata daketa yawo a saman kanta. Ta wacce hanya zata samu ta kubcewa wannan qaddararren auren?,dama dukkan wani aure a nan gaba har sai lokacin da taji zuciyarta ta gamsu ta aminta da aure?.

"Akwai" taji zuciyarta na gaya mata,amsar da taja hankalinta ta kuma sanyata neman baasin maganar

"zamuyi aure don ki kula da fadeela kawai wannan shine manufar,ni kuma zan baki dukkan 'yanci da mafakar da kike nema" kalamansa suka dawo tarwai cikin kunnuwanta,kamar a sannan yake furta mata
SU.

*HUGUMA*


*_TABARMAR KASHI *


Book 02 Page 06


Wani irin zuzzurfan nazari ta shiga yi,tanason ta yiwa kalaman nasa duba na fahimta,ta kuma nazarci ma'anarsu da kyau.
"Indai hasashenta yayi dai dai,indai ma'anar fassarar tana nufin abinda ta tsinkaya ne.....zai aureta ta kula da fadeela,ita kuma tayi rayuwarta tamkar macen da bata da miji,babu doka,babu oda,babu auratayya,babu sawa babu hanawa...a idanun duniya sunanta matarsa,amma a tsakanin su din bagin juna ne,kowa zaiyi harkar gabansa" wannan hasashe kadai ya haifar da kyakkyawan murmushi saman fuskarta

"Yes... yes" ta fada gasa gasa tana sakin murmushi

"Ta samu cikakkiyar mafaka,ta kuma samu dama irin wadda zata bata damar yin rayuwarta lya adadin tsahon shekarun da takeso ba tare da takurawa ko sanya idanun kowa ba". Sosai taji al'amarin ya kwanta mata,wanann din wata idea ce me kyau. A daren ta fara laluba card din da ya bata cikin jaka,sai ta tuna ta yasar dashi a falon batama fito dashi ba. Ji tayi a daren kamar ta fita ta dauko card din,amma dole ta haqura zuwa safiya.

Haka kawai kuma wani sashe na zuciyarta ke umartarta tayi addu'a. Bata wofantar da wannan shawarar ba,sai ta mige ta daura alwala, don dama ita din gwanace ta wannan fannin,dai daikun darare ne suke wuceta,farinciki ko baqincikinta tana juyeshi ne saman abun sallah, wanda hakan yake qara mata nutsuwa tare da hasken rayuwa,matsalolinta masu yawa kuma warwara take zuwa musu a qanqanin lokaci.

Raka'a shida tayi,tana gamawa taji wata nutsuwa na shiga ruhinta,kamar iskar dadin na dada sanyi da dadi,tana yiwa annabi salati idanunta suna lumshewa,a haka har wani daddadan bacci data jima batayi irinsa ba ya sureta.

Washegari bata tashi da wuri ba,saboda bacci tayi sosai,bayan ta farka tayi brush tare da alwala,ta dawo cikin dakin nata ta sakawa wayarta charge,ta kunnata ta zauna daga gefan gado,ta buda inbox ta turawa afifa sagon da tasan dole ne ta dawo gida koda bata nemeta ba,duk da jiya da magriba ta tafi zooroad

"Bestie aure zanyi"_ abinda ta tura mata kenan ta sauka tabar wayar a charge ta fito falo.

Masu aiki keta hidimar kimtsa gidan,da )alama aikinsu na safe yazo qarshe saina rana dana dare. Cikin sakewa suka gaisa kamar yadda suka saba,baaba rabi ta gaya mata maama tace a shaida mata idan ta farka,ta tafi gidan uncle ismail,yau din za'a kawo lefen zeenat qarfe uku na yamma,idan ta gama komai ta sameta a can saisu dawo tare. Tana amsa mata tana ficewa,tanaso ta samu card din kafin masu gyaran gurin su hada dashi su share.

Sai data danyi dube dube sannan ta ganshi,ta tsugunna ta dauka tana kallon rubutun dake a jiki. Rubutu ne dake cike da tsari da kuma ban sha'awa,full name dinsa email and phone duka a jiki. Dan tabe baki tayi,tana tuna irin izzarsa da jin kansa,wai yama akayi yasan wasu abubuwa haka a kanta?,ya akayi yasan ita din bazawara ce?,ya kuma akayi yasan gudun auren kowanne namiji takeyi?. lya hasashenta bata iya ganewa ba

"Oho masa,shi ya sani" ta fada a fili tana komawa cikin gidan,ta shiga dakinta ta yiwa card din waje,sannan ta shiga hidimar gabanta.


********Sanye yake da long sleeve kaftan thobe button down, wadda daga qasa gefe da gefe yake a tsage,fara ce qal kamar yadda mafi yawa zabinsa kenan a kaya,hannun rigar ya tattareshi zuwa gwiwar hannunsa,yana riqe da mug na coffee kamar kullum yana kurba,idanunsa akan fuskar fadeela daketa faman gogarin zana wani dan tsuntsu.

Idan kace hankalinsa baya gurin bakayi kuskure ba,miskilar fuskar nan na hade kamar yadda take a koda yaushe,saidai sassanyan kyan nan da cikakken gashin girarsa zuwa jajayen lips dinsa zuwa kwantaccen gashin dake habarsa zuwa kuncinsa suna sake bayyanar da cikar kyawunsa tare da gara masa kwarjini.

Shan coffee din kawai yakeyi bawai don yana masa dadi sosai ba,tun wancan ranar da ya dandana wannan coffee din da kuma shayin gaba daya,dadinsa ya dauke dandanon dadin kowanne irin coffee,hatta nasa kuwa da ya tabbatar ya qware sosai gurin iya hadashi.

A nutse ya ajiye mug din,bakinsa na dan fidda tururin ragowar zazzafan coffee din, idanunsa a kafe waje daya. Babu abinda yake masa kai kawo tare da ciwo a rai irin yadda ya zubda dukka makamansa ha gasqantar da kansa ya nema wata diya mace ta aureshi,abinda ya yiwa kansa alqawarin har yabar duniya bazai sake maimaitawa ba,sai gashi dare daya....tazo ta ruguza duk wani abu da ya sanyawa kansa doka da iyakoki a kai. Iska me zafi ya furzar yana dogara gwiwayoyin hannunsa akan qarfen balcony din hadi da fidda zazzafar iska a bakinsa. Ba komai ke sake rura wuta ke zafi a zuciyarsa ba,sai yadda ta tankwabar da tayin da yayi mata. Tana tunanin yana neman wani abu ne daga gareta? ‚bayajin banda fadeela akwai wani abu da zai sanya ya sake kallonta.

Abu daya ya sani,koda bata aminta ba,zaiyi dukkan abinda zaiyi,koda tsiya sai ya dawo da zamanta gidan taci gaba da kula da fadeelan

Karar shigowar saqo a wayarsa ya dauki hankalinsa,wayace da dukka kira ko sagon da zai shigo ya cikinta to me muhimmanci ne a gareshi,wanan yasa ya miqe tsaye ya sanya hannu a aljihun kaftan thobe din nasa,ya zaro wayar yana dubawa.

Sake dafe hannunsa yayi sosai
saman qarfen,tuntuni ya sanya jibril ya nemo masa number dinta,ya kuma yi masa saving nata. Haka kawai yaji yana buqatar zama,ya miqa hannu ya jawo wata kujera guda daya me azabar laushi ya zauna,ya lanqwashe gafafunsa a cikinta sannan ya fara karanta saqon

_I agreed,i will marry you,but under some conditions,idan ka shirya zaka cikasu..
..fine,am ready nima"_ dan garamin tsaki yaja,me ya kaishi irin wannan abunne wai

"Farinciki da lafiyar fadeela kake nema" zuciyarsa ta bashi amsa,sai ya girgiza kar yana gasgata hakan. Baiyi jinkiri ba ya fara tafa mata amsa

_i get the point, duk wasu conditions naki ki rubuta su kawai ki ajjiye basai naji ba,coz i know bani da case dasu,you are going to be my wife for the sake of fadeela,you can do whatever you want"_. Ta kusa a qalla minti guda tana duba amsar tasa,sai kuma ta saki murmushi,saboda abinda takeson ji kenan,zata zama free,zata samu 'yanci. Sauka tayi tana shirin ajiiye wayar wani sagon ya sake shigowa

_"Are you ready for the marriage nan da next week?"_tabe baki tayi,yama raina mata hankali, don ta amince kuma sai yayi mata zancan next week?, kwanaki hudu kacal fa gaba

"Nooo" kawai ta tura masa tana jan tsaki

"Alright,sati biyu kacal na qara,so let's start plan it,ki sanarwa da Dr zan turo magabatana nan da 3days"_. Juya wayar kawai ta dinga yi a hannunta,anya batayi kuskure ba?,anya zai iya cika alqawarinsa?,a yadda maza suke a yanzun?,ba alqawari babu amana. Kai ta girgiza

"Batajin komai zai faru,saboda kowa a cikinsu maradinsa yake karewa yakeson cikawa, kamar contract ne yanzun a tsakaninsu. Da zarar fadeela ta warke zata nemi saki daga hannunsa,shikenan contract ya qare,shi da ita kuma kowa zuwa lokacin ya cimma muradinsa.

Har washegari zuwa wata washegarin ta rasa wa zata tunkara tsakanin Dr girema da kuma maama dinta,ga afifa still bata nan,dole daga garshe gudun kada abban nata yayi bagin da baisan da zuwansu ba,ta dauki waya ta kira afifa tace ta dawo please. Tunda taji hakan tasan akwai wani Issue daya taso masa may be ta gaza warwareshi,don haka tabar komai tazo ta isketa,lokacin zataci abincin rana ne da yammaci,ta garso musu sukaci a tare: Sai da suka kammala,ta gyara gurin sannan ta dawo ta zauna tana fuskantar afifan

"'Bestie na fidda miiin aure" dan dubanta kadan tayi sannan tace

"An fidda miki dai,ko ba mahmud ba?,dama ai saura 3days deadline din da abba ya deba mana ya qare"

"Ba mahmud bane,wanann zabina ne,MT
JARMA" ta fada kanta tsaye tana duban reaction na afifa. Ta fusgi hankalin nata kuwa,don tsaiwa tayi da komai tana kallonta,kalmar na girgiza afifa,hadi da shiga kowanne lungu da saqo na jikinta. Girarta ta dage mata dukka biyun

"'Yes,kina mamaki ne?,nima mamaki naso baki dama kamar yadda kikayimin akan SAJJAD"

Murmushi afifa ta saki tana kauda kanta
gefe

"Sajjad banda kina cikin rudani hankalinki ba'a kammale yake guri daya ba,ya kamata ki fahimta wani abu da kanki.....na miki murna da kika samu zabinki,amma bestie,kome zakiyi ki yishi ba'a bisa kowacce manufa,kin sani.....na sani..... dole na garyaraki zuciyata taqi aminta da cewa MT JARMA shine zabinki, kusan kowa yasan dabin dake tsakaninku,yaushe soyayya ta shiga har kuka fahimci juna?" Sam sãahar batason afifa tace zata hanata aiwatar da qudurinta,a yadda ta tsani maza da abinda ya dnagancesu wannan ne kawai option din da ya rage mata,kuma dama a gareta guda daya da zata rayu cikin salama ba tare da wata alaqa tsakaninta da su ba

"Allah ya sanya alkhairi,kuma ina addu ar
Allah ya maida qogo masaki" bata fahimci maganarta ta qarshe ma,saita watsar,tunda dai bestie din nata bata kawo wani tarnaqi na fine,shikenan.

Afifa ce tayi mata rakiya gidan yaa
muhyiddeen,ta bawa anty farheen sago ta gayawa yaa muhyi din,shi kuma ya isarwa da abba batun. Sakato anty farheen din tayi cike da zallar mamaki tana kallon säahar din

"Yaushe reshe ya juye da mujiya kuma ummin abba?" Dan garamin murmushi ta saki tana kauda kai

"Tsarin Allah,haka qaddararsa take" jinjina kai kawaii anty farheen tayi,don ita kanta bata gama gamsuwa ba. A yadda tasan sãahar sarai da kafiya,bata da sassauci akan abinda takeso da kuma wanda takeqi uwa uba kuma gefe guda ga al'amarin daya sauya zuciyarta zuwa giyayya da gaba daga dukkan jinsin maza.

Sanda sãahar din ta shiga sallah lokacin afifa dake fashin sallah suka tattauna da anty farheen

"'Nafi zaton dukkansu akan wata manufa suka gina auren nan,amma dai koma menene,mu zamu bada gudunmawa waien tabbatuwar komai yakuma dore har abada,so zamu soma shirye shirye,kada ki nuna mata kin fahimci komai" kai afifa ta gyada.

To wannan magana da sukayi da
Anty farheen sai afifa ta saki jikinta,tun a washegari ita da anty farheen suka soma tsara abubuwa da gabatar da shirye shirye. Ta fannin säahar kuwa jin kanta tayi sakayau,ta tsinci kanta cikin wata iriyar walwala mara misali,hankalinta taji yayi mugun kwantawa,tana ji a ranta yanzu bata da sauran matsala a rayuwa. Saidai harkokin gabanta kawai takeyi,duk wani shiri da su anty farheen sukeyi tana gefe ta zuba musu idanu,gani takeyi bata lokacinsu da kuma kudadensu sukeyi,wani abun saidai ta kalla ta tabe baki,amma batace komai ba saboda abune da take ganin tsakaninta ne kawai da toufeeq din,babu wanda ta shaidawa manufar aurensu.

Kwanakin ukun da ya diba matan
baqi na musamman cikin girma daga gidan
Dr mahmud JARMA suka sauka a gidan Dr girema da kudin auren yaransu guda biyu.
Muhammad toufeeq ya bayar da zunzurutun kudin auren Khadija Muhammad girema har naira million daya,yayin da sajjad da ya tsunduma cikin soyayyar afifa tun ganinsa da ita na farko ya bada dubu dari biyar. Sajjad yaso qwarai a qara kudaden sufi haka,amma dr jarma yace sam,hakanma yaso yayi yawa,albarka yake nema musu. Magabatansu sun roqi sati uku kacal,dr girema da gannensa da suka karbi kudin tare basu ja ba,ganin yadda Dr jarma da kansa yaketa roqon ayi masa alfarmar hakan.

Da daren ranar dukka su biyun suna dakinsu,afifa waya take amsawa tsakaninta da anty farheen,duka maganarsu akan yadda shirye shirye zasu guda na ne,sayayyar kayan dakinsu zuwa gyaran jikinsu. Cikin satin takeso yaa muhyi ya samar musu da visa su ukun,china turkey ko Dubai,duk wadda tafi sauri da sauqi,su dora kayan ta sama yadda zayazo da wuri

"Amma ta sama anty akwai kudi fa"

"Karki damu,biyan buqata akeso,indai china ne ma babu matsala,akwai lucky cargo da kayan zasu iso cikin kwanaki galilan har nan kano(me bugatar hulda da amintaccen kamfanin saboda kawo kaya daga china zuwa Nigeria dukka states,sai ya tuntubeni ta wannan number don na hadashi da kamfanin kai tsaye 08187255862)". Sati guda takeso suyi a can,satin da suka dawo kuma sai a fara gyaran jiki da sauran hidimomin da suka shafi amare.

*HUGUMA*

* TABARMAR KASHI *


Book 02 Page 7

Har afifa ta gama wayar idanun saahar yana kan wayarta tana chart,ido tadan zuba mata zarginta yana sake tabbata,yadda sãahar me shakulaton bangaro tare da nuna halin ko inkula da dukka abinda ya shafi bikin ya sake tabbatar mata da zarginta,uwa uba ko sau daya ita dai idanunta basu taba nuna mata kiran toufeeq jarma ba

"Kina jina muna magana amma bakice
komai ba?" Dan duban afifan tayi,sai ta saki
murmushi

"To me kikeso nace?,salon nayi rash-in
kunya?,kuma ma ai kin gama komai,duk
abinda nake bugata ko zance ke kin isar
min,duk abinda ya samu ayi,wanda bai zama
lallai ba ko bai samu ba sai a haqura ko?" Kai
afifa ke girgizawa tana kallonta

"Amma dai ba haka kikayi ba a aurenki da
adamu" ajiye wayar tayi gefe wani murmushi
dake cakude da zallar nishadin da takeji
gasan ranta ya kubce mata ta zuro gafafunta
gasa cikin zummar shiga bandaki sannan ta
amsawa afifa

"Banda abinki hajiya afifatu,ai kullum dan
adam dada wayo da hankali yakeyi ko?,don
zanyi aure bawai ba hakan yana nufin na
mance da asalin su waye maza ba,ko kuma na manta radadi da daci da suka dasawa rayuwata ba"

"'Anzo gurin" afifa ta fada tana zagayowa gabanta da sauri,ta jawo stool ta zauna akai tana fuskantar sãahar wadda ke mata duban mamaki

"Bestie bandaki zan shiga,yaa haka?"

"Inason nasan gaskiya ne bestie,yau ashe anzo wata gaba da zaki dinga boyemin wani abu a rayuwarki? meye ainihin gaskiyar magana akan aurenki da toufeeq jarma,duk yadda naso na basar nayi kaman ba komai na kasa bestie,ki gayamin gaskiya" murmushi tayi hankali kwance

"Ki barni naje nayi fitsarin mana"

"Na barki" ta fada tana dubanta. A nutse ta miqe ta wuce bandakin,ba jimawa ta dawo ta koma inda ta tashi ta zauna. Komai ta warware mata,abun sai ya sanya afifa murmushi me kama da dariya

"Allah ya sanya alkhairi,abu kuma yay kyau,hakanan hankalina ya kwanta da bayananki,amma ke dashi dukka ku shirya ranar karbar sakamako a tsakaninku"

"Sakamakon me?,kefa wani lokacin kin fiya jaye jaye"

"Lokaci zai bayyana komai". Tasan halin afifan da iya saqa zance,sai kawai tabar zancanta,ta maida qafafunta saman gadon tayi kwanciyarta cikin nutsuwar data jima bata jita cikin ruhinta ba. Yayin da afifa ke duba kiran da ya shigo mata,sajjad ne,migewa tayi ta dauki scarf dinta ta fice a dakin, sãahar data fuskanci meke faruwa ta bita d kallo tana tabe baki

"Hmmm,soyayya manya,mun jima da dawowa daga rakiyarta,mu da ita ko a lahira mun raba jaha" ta fada qasa qasa kamar me qunquni tana gyara kwanciyarta,sai kuma ta tuna zata yiwa maama gyaran wardrobe,don haka ta miqe ta sauko,ta kama gashinta me santsi ta daureshi waie daya,ta dora hula a kanta ta zura slippers ta fice.


********Ya jima a zaune yana juya wayar hannunsa,dukkansu mamaki suke bashi qwarai, nadeeya maji ga kuma mai gayya mai aiki fadeela. Yadda suke nuna tsantsar zakwadi da kuma farinciki akan wannan auren abun daure masa kai yakeyi. A yau sun jima suna waya da majiirin wayar da basu taba yin me tsaho irinta ba,duk da cewa kamar dai ko yaushe itace tayi kiransa bashi ne yayi kiranta ba. Dole bayan ya gama mamakin lamarin ya ajiye wayar gefe,dai dai lokacin sajjad ya shigo gurin bakinsa dauke da sallama.

Guri ya samu ya zauna yana kallonsa yana kwance cikin lounge chair

"'nata jira naji daga gareka" kyawawan zagayyun idanunsa kawai ya daga ya kalli sajjad din

"Game da me fa?" Takaici ya kama sajjad din,kamar bazaiyi magana ba amma ya cije

"Ba aure zakayi bane malam?"

"Aure zanyi sai mene?"

"Bakasan kana da buqatar yin wasu abubuwa ba,mace fa zaka ajjiye cikin gidanka,a ina zata zauna?,ka hada mata lefe?,dinkunan biki da sauransu"

kamar bazaice komai ba,sai ya miqe ya zauna sosal sannan ya zura qafafunsa qasa yadda zaiji dadin zaman,idanunsa akan sajjad din

"Ce maka akayi wani aure ne duk da za'a tsaya masa wannan hidimar? kawai a daura ta shigo taci gaba da aikinta,ni kuma na bata gurin zama da ciyarwa da suttura that's all,duk wadan nan abubuwan da kake jerowa sai ku masu auren farko,tun wani zamani da ya shude muka rufe wanan batun" sai ya miga hannu ya janyo plate din apple da Jacob ya ajiye masa.

Ido sajjad ya zuba masa,kaman zaiyi magana sai kuma ya fasa,ya saki qaramin murmushi sannan ya miqe

"Zaka gane kurenka,indai macece ba'a cika musu baki,i pitty you duk lokacin da ka fada tarkonta,saboda haka kabi a hankali,shawarace kyauta na baka" baice masa komai ba sai qaramin miskilin murmushin da ya subuce akan fuskarsa,wannan maganar ta sajjad bata da banbancin da tatsuniya a gurinsa. Banda fadeela,babu abinda zai sanya ya biya sadakinta ta amsa sunan matarsa a bakunan al'umma bare azo gurin da sajjad din ke magana a yanzu.

*********Karo na biyu ya sake gwada kiran qanwar tasa,wannan karon ta shiga sabanin lokutan bava da kiran yake yankewa.

Spoon din hannunta ta ajiiye lokacin da kiran ke shigowa,wani hamshagin murmushi ta saki,yadda yayan nata yake bata kulawa tun daga wancan zamanin zuwa yanzu yana y mata dadi matuga,kuma har yau bata canza zani ba sanadiyyar jajircewarta

"Assalamualaikum barka da warhaka yaaya" hajiya qarama ta fada bayan ta saka wayar a kunnenta

"Yauwa barkanki dai FAUZIYYA" Cikin kulawa suke gaisawa da juna,ya tattambayeta yanayin kayan da taje siyowa a qasar. Tsahon mintuna goma suna tattaunawa sannan ya fara maganar da itace maqasudin kiran

"Kwanaki kusan bakwai ina kiranki na kasa samunki har ina tunanin akwai matsala ne"

"Babu yaaya wani lokaci ajiye wayar nake a nan hotel idan banason yawan kiran"

"To yayi kyau, Allah ya taimaka,amma inajin ai dole ki yanki ticket na dawowa sati me zuwa ko satin sama ma,don yaronki ya tashi aure,Allah ya amsa addu'armu" Wani irin mummunar faduwar gaba me hade da wani tashin hankali ne suka rufto mata,tamkar wadda ake juyewa duwatsu saman kan nata

"Yaron....na? wanne kuma?" Ta fada tana qoqarin boye gigicewar da tayi. Dan murmushi dr jarma ya saki

"Kina da wani d'an ne bayan toufeeq?,inda
'yarki nace saiki tambaya nadeeya ko
HASEENA?" Sarawa kanta yayi da matsiyacin qarfi,wani zazzafan gumi ya karyo ilahirin jikinta ta kowanne sashe,taji kamar an saka allura da zare ana daure kanta,cikinta ya juya take bayan gida ya matsota

"Yaya?,ka manta haseena naketa ajjiyewa toufeeq? tunda anyi na farko ba'a dace ba?,ita kanta yarinyar bata taba kula kowa ba saboda ta sanya ranta akan TOUFEEQ din,ko yanzu haka sati uku ne kacal ya rage ta gama karatunta ta baro hannun babanta ta dawo nan nigeria don su daidaita kansu ita dashi"

"Banda abinki mijin mace hudu ne faidan yaga yana da ra'ayi uku ne sauran da zai cike ma,sannan ita kanta yarinyar bata da matsala,na santa farin sani,itace wadda ta taba rige president na kamfani na,kuma kema kin santa,wadda ke kula da fadeela kafin tahowarki"

"Kanbun uba!" Ta fada gasan ranta har bakinta yana motsawa

"Nanny fa yaya!" Ta fadi cikin daukaka sauti

"Ba nanny bace fauziyya,kawai tayi sha'awar aikinne,amma badon ta rasa komai ko kuma bata da gata ba,infact 'yar Dr mamman girema ce,wanda kikaso a baya,kikace matarsa ce ta hanashi sauraro da kulaki" wani bala'in kawai bayanan yayan nata suka qara mata,Dr mamman da baya ganin kowacce mace a gabansa sai matarsa?‚buzuwar nijer,wadda koda wasa mamman din bai taba kallon wata mace ya taya da zummar zai aureta ba saboda yadda ya samu kula biyayya da dukkan wani jin dadin rayuwa da d'a namiji yake bugata da muradin samu daga wajen diya mace? ‚matar data wahalar da ita ta kuma kafa tarihi ta zama mace ta farko da tayi mata shamaki da abinda takeso? bayan tafiyarta toufeeq ya koma gidan,yarinyar tayi amfani da wannan damar kenan ta ja hankalinsa? har sai daya kamu da soyayyarta me zafin da ya kasa sukuni cikin sati uku kacal ya nema aurenta?,to itakam fauziyya tana me? wanne irin sakewa tayi haka?. Kamar dr jarma shima yanason canzawa,ta yaya yake maganar idan toufeeq din yana so?,bata saba jin wannan kalamin daga bakinsa ba a duk sanda ta bugaci wani abu daga garesa, komai tsananinsa kuwa

"Ya kikayi shuru?" Ya jefa mata tambayar. Cikin duniyanci da wayancewa tace

"'Ina lissafin randa zan dawo ne,da abinda ya kamata na taho dashi na hidimar biki,sanann wannan karon abun yayimin banbarakwai ne,ba kamar aurensa na baya ba da akayi komai dani,wanann lokacin labari kawai naji" dan murmushi dr jarma yayi

"Kinsan kowanne aure da yadda yake
Zuwa,amma dai batun haseena karki damu,indai sun daidaita kansu shikenan,zanfi kowa farinciki da wannan,tuwo na,mai na"

rintse ido tayi tana jin zafin abinda yake fadaidan sun daidaita kansu kuma?,ba ruwansa kenan bazai shiga ba bare ya tilasta yiwuwar abun?. Har yanzu batasan me yasa ta kasa bude wata qofa guda daya tal ba,duk da tarin nasarorin da taci take kuma kan ci,amma har yanzu qofar bada umarni ga toufeeq bata kammala buduwa. A duk abinda ta umarta da yayi,musamman abinda ya shafi janibin rayuwarsa akwai yiwuwar yayi ko kada yayi,bata manta lokacin da ta umarceshi da kada ya dawo da Ameesha,sai ganinsa tayi da matarsa a wancan lokacin,ribar kawai da taci shine watsewar lamarin da yayi babu jimawa dutse a hannun riga. Da tana da wannan cikakkiyar damar,to da a yau zata umarceshi da ya dakatar da komal,ya ajjiye batun auren ya saurari zuwan yaruwarsa nan da sati uku masu zuwa.

Gefe guda babu abinda ya sake dagula mata lissafi irin haseena,batasan yadda zata tunkareta da zancan ba,bata iya jurewa tashin hankali,bata da juriya sam ko iya cinye abu,ta tabbatar babban bala'i da tashin hankali ne zai biyo baya. Dole tayi iyakar bakin gogarinta na ganin ta toshe dukka wata kafa da zata zamu labarin wannan auren,kafin sannan ta shirya fada mata tare da yi mata bayanin komai yadda zata fuskanta. Bacin ran haseena dai dai yake da nata bacin ran,ita daya qwal ta mallaka a duniya,tafi qaunarta sama da komai a rayuwarta,kai koda kuwa dukiyarta da take mutuwar so,take tattali da fadin tashin tarawa tsahon shekaru,ai dukka tana yine saboda ita haseena din.


Migewa tayi dole tsaye,tanajin kamar hawan jininta zai tashi ta

Please Login or Register in order to submit comment