Reading TABARMAR KASHI 1&2 complete by SAFIYYA HUGUMA Chapter 48 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni zan ci gaba da kula da hakan" a bazata maganar tazo mata,har hakan yaso ya rudata amma ta daure

"Haka ma zaka ce dani toufeeq? yayi kyau shikenan, kaje kawai" ya dauka ya kawo qarshen maganar, amma sal ta sake cewa

"ya kuke ciki da meenal?,dazu ta dawo tana kuka,ta bata lokaci tana bada direction na abincin da za'a dafa maka,sai kuma naga da takai maka babu abinda ka taba a ciki,me yake faruwa?" Idanunsa yadan rufe kadan,a yadda ya fuskanci yanayinta ko meye zai fada mata a yanzun zata bata masa lokacine ta qara masa hayaqi akai, saidai duk da haka yana bugatar ya datse dabi'ar daukar abinci takai masa company,alhalin suna da kitchen, sannan kowanne kalar abinci yakeso yana daga office jibril zai iya masa order dinsa

"Mun fita da madam dauko fadeela daga school" idanu tadan bude da kyau tana kallonsa. Tunda suke dashi bata taba jin ranar da ya zarce daga office dauko fadeela makaranta ba sai yau,yau din kenan har hakan ta fara?, har yarinyar taci nasarar juyar masa da hanakali da sauya masa ra'ayi da tsari?,duk kuwa da tarin taurin kansa da kafiyarsa akan tsarinsa?, wanda ko ita ba kasafai takecin nasarar canzashi ba?. Bata gama wannan mamakin ba ta ganshi ya miqe sannan yace

"So please hajiya ki fahimtar da ita basai tayi wahalar kawomin ba,i will be alright, bazan rasa duk abinda nake bugata ba" mamaki ya hanata cewa komai,shi sam baima wani zurfafa dubanta ba bare ya gane ya dora mata

"Zan wuce ciki.da wuri nakeso na kwanta"

"Jacob baya nan,ko a kai maka dinner?" Ta sake garfin halin fada tana ritsashi da ido tare da son tabbatar da zarginta akan säahar . Hannu yasa ya shafi tattausar sumarsa

"No, ba damuwa,i will get something to eat" sai yayi mata sallama yana ficewa. Labiba da haseena, tabbas yana gab da yi musu mummunan warning din da ko sunansa sukaji zasu san nayi,yana musu kara da alkunya ne kawai saboda iyayensa, hajiya qarama da dr jarma,don kwata kwata baya saka mansura a lissafinsa.

Yana shirin fita a sashen adama na isowa, hankalinta yayi gaba sosai don haka bata lura da shi ba har sai da yayi dab da ita, cikin zafin nama ta kauce masa abinda ya sanya ta bugi bango ledar dake hannunta ta. yage,magungunan ciki suka zubo qasa. Cikin tsananin rudewa tare da tuna kakkausan gargadin da hajiyan tayi mata wajen kula da maganin har zuwa sanda zata kawo mata shi,sai ta sulale a gurin tana tattarosu tana zabga salati.

Kansa ya dauke yana ci gaba da tafiya. Har ya gota yá dawo da baya sakamakon wani tunani da ya darsu a ransa. Akwai masu aiki a gidaje kamar haka da suke ta'ammali da kayan maye qwayoyi ba tare da iyayen gidansu sun sani ba,wasu ma idan aka samu tsautsayi har su koyawa yaran gidan

"Ke.. zo nan" kiran da ya sanya hantar cikin adama juyawa,ta dawo da hanzari ta zube a gabansa

"Wadan nan magungunan fa?"

"Eh... na'am" ta fada a rude tana tuna gargadi na biyu data yi mata,kada ta nuna cewa maganin yana da alaqa da ita ko fadeela

"Uhmmnn" ya fadi yana tsuke fuskar nan tasa me sanya shakka da tsoro a zukatansu

"Ko kin fara shaye shayen muggan qwayoyi?" Ya fada kansa tsaye yana tura hannunsa cikin jallabiyyarsa ganin bata ds niyyar amsawa. Fassarar da yayi matan ta razanata matuqa,har batasan sanda ta daga kai da sauri tana rantse rantse ba

"Wallahi A'ah yallabai,magungunan fadeela ne hajiya tace na karbo daga bakin gate"

"Bakin gate kuma?" Ya tambaya cike da mamaki, saboda yasan duka magungunan da fadeela ke sha ba na nan bane, hasalima order dinsu ake mata na kusan million daya,yana damqasu a hannun hajiya qarama har sai sun qare sannan ya sake yi mata order din da kansa (nasan zakuyi mamaki,maganin million daya?,harma fiye da hakan sukan sha,sannan kamar yadda nace wasu da yawa masu gata a cikin masu lalurar EPILEPSY order magungunan nasu akeyi musu,a qalla a shekara sukan sha maganin million daya din, fatanmu Allah ya rabamu da dukkan wasu cututtukan zamani,ya qaremu da lafiya,su kuma ya basu lafiya,wadanda ya zame musu na
har abada ne kuma rabbi yasa ya zamar musu kaffara

"Eh.. .eh" kai ya jinjina,ko sun qare ne tayi order ba tare data sanar masa ba, sai ya samu kansa da lissafa adadin kwanakin da suka rage su qare din.

Har ya daga qafarsa yaci karo da roba,ya
tsugunna yana dubawa sai yaga daya daga cikin robar
maganin da ya gani ne yanzu,ya waiwaya zai kirayeta
amma tuni har ta bace a gurin,ya juyata a
hannunsa,kwata kwata tasha banban da robar
magungunan fadeela,sai kawai ya jefata a aljihun rigarsa ya wuce.

******Dukka qafafunsa ya zuro waje yana juya zaman agogon hannunsa. Yau din shigar suit ce yayi wadda tayi matugar dacewa dashi,ta fidda kyana kai kace daya daga cikin jaruman Indian films ne. Yau din har da wani extra eye glasses daya mannawa fuskarsa me duhun kala,wannan ya sake qawata fuskar tasa qwarai. Karo na uku va kalli agogon nasa,ya fahimci tunda suka fara ajjiye fadeela a makaranta suke shanyashi,a kullum sai yayi zaman jiransu,duk sanda zata iso kuma tana yine kamar batasan ta sanyashi zaman jiran ba. Kaf duniya idan ka dauke Dr jarma babu wani mutum da yake iya zaman jira,sai ita data karya masa record.


Dago kan da zaiyi suna fitowa daga sassan, kamar kullum tana rataye da school bag din fadeela tana kuma riqe da lunch bag dinta, yarinyar itama na dauke da hand bag din sãahar. Sati kusan na biyu kenan da yake ganin fitowarsu a hakan, amma har yau ya gaza saba ganinsu a irin wannan yanayin,duk lokacin da suka fito din sal sun fisgi hankalinsa qwarai, saidai yau din hankalinsa ya dauku fiye da ko yaushe. Tuni ya sanyawa guards dinsa dokar zama cikin motocinsu a duk lokaci irin wannan har su fito su wuce. Shi kansa bazaice ga dalilin da yasa yayi hakan ba,kawai dai yana ji a jikinsa hakan shine abinda yafi dacewa.

•Yau din kamar murmushi da fara'ar fuskarta ya banbamta da na ko yaushe. Cikin shigarta da ko yaushe take fita zuwa office din da ita ta laffaya. Saidai kuma a yau din laffayar ta musamma ce. Wata irin lallausar farar laffaya ce me yarfin ruwan gold,wadda ta dace da siririn takalmin qafarta me tsinin dunduniya maras tsaho,wanda zara zaran dogayen yatsunta suka kwanta luf a ciki,komai nata a ranar kusan gold colour ne, sai hakan yayi masifar qara mata kyau da wani irin haske,lafiyayyar fatarta ta fita shar.

"Wow" yaji an fada cikin wani mugun zumudi, furucin da yaja hankalinsa aka fusgeshi har cikin kwanyarsa. A nutse ya waiwaya,ba kowa bane tsaye a wajen sai Jamal.

Saidai kuma wayace a hannunsa da alama wani abun daban yake kalla. Haka kawai yaji wani abu yazo ya tsaye masa a wuya. Ba yaune rana ta farko da yakejin kamar shigar bata dace da ita ba,amma sai yake gayawa kansa rayuwarta ce,bai kamata yayi mata shishshigi a ciki ba.

A yau din duk yadda yaso ya share kaman yadda ya saba sai yaji ya gaza dannewa. Wow din da Jamal ya furta sai yakejin kamar a kanta ne

"Dole ka kare martabar aure, ko ba komai sunnar ma'aiki ce daya kamata ace an tsare kimarta" wani sashe na zuciyarsa yaji yana gaya masa.

Cikin nutsatsen takunta ta iso bakin motar a hankali, kallo daya tayi masa ta janye idanunta tana rage kaifin fara' arta,wanda wanna din wata dabi'arta ce da tuni ya gama ganeta. Hannu tasa a nutse ta budewa fadeela seat din ta daya side din, qasan ranta tana gulmarsa. Zata iya cewa tsahon lokacin da ta dauka dashi zata iya rantsuwar bata taba gain dariyarsa kamar yadda sauran mutane sukeyi ba,wannan baqin eye glasses din da yasa ko yau din kuma tsautsayin kora da sauke kwandon masifar akan wa zai fada?.

Tambayar da ta yiwa kanta kenan, wadda tayi dai dai da saukar sautin muryarsa

"Ji mana" ya fadi yana zube mata zagayayyun idanunsa dake da haske qwarai. A nutse ta juya suka hada ido,a hankali idanun nasa suka sauka akan lips dinta daketa ayallin lip gloss. Tun wancan ranar bata sake maimaita saka jambaki ba,tunda yayi mata wannan abun. Bata fata ya maimaita kusanto jikinta,shi yasa ta daina sakashi kwata kwata a bakinta.

Dubansa ya sauka daga cikin idanunta zuwa lausasan lips din nata,haka kawai yaji ya hadiyi wani yawu. Sai kuma ya fara qoqarin saita kansa yana sake hade ransa

"Wannan shigar bata yi ba,go and change" sosai mamaki ya kamata,sai ta sauke dubanta a nutse ta a kallon kanta tun daga yatsun qafarta zuwa ainihin gangar jikinta,bataga ta inda ake ganin wani abu nata ba. Yana daya daga cikin abinda ya sa take yawan zabar shigar

laffaya saboda yadda take suturta kaso saba'in na surarta

"But......me shiga na yayi,is like fa kana shiga hurumin da ba naka ba" ta fada tana hade ranta da kyau. Wani kallo da ya dago ya aje mata sai da taji tabbas tayi subutar bakin bashi amsar da tayi a yanzun. Bai sake bata damar yin tunani na biyu ba taji kawai ya damqi hannunta,bai tsaya jiran komai ba ya nufi sassansu yana riqe da tsintsiyar hannun nata,yana jin zuciyarsa na wani irin zafi,ba tun yau ba shigar ke tsole masa ido,daga yau kuma ta bar yinta kwata kwata.

"Ka sakarmim hannu mana,kama wuce ga'ida fa" ta sake fada da nata zafin sanda suka isa qofar dakinta. Fusgota yayi ya jefata jikin qofar yana binta da kallo. Take tsoro ya kamata cikin ranta tana mamakin abinda ya Sanya farar qwayar idanunsa sauya kala lokaci guda

"Idan na sake jin bakinki sai na shayar dake mamaki" ya fada da zafinsa shima,sai yasa hannu ya murda handle din dakin ya buda qofar ya tura saahar din ciki. Tamkar kurma haka ta zama,tayi tsaye tana kallonsa sanda ya bude closet dinta yanata debo kaya yana zubawa saman gadonta. Batace masa komai ba har ya kammala,ba tare da ya rufe ba ya tako a nutse ya tsaya gaban kayan

"Ba kwalliyar ki akace kije ki nuna musu ba da zaki dinga sanya wannan abar,tun randa kika fara zuwa aiki har yau,ki cireta ki zabi wasu daga cikin kayan nan ki saka ki fito" Sosai ranta ya baci, ita ko kadan bata taba sanya laffayar da sunan kwalliya ba,hasalima tana sakata ne saboda tsaro, batasan yawan kallo, tana da tarin kaya lace atamfa shaddodi da sauransu kayayyakin qyale ayale na mata, amma duk ciki tafi qaunar sakata muddin zata shiga taron daya hada hadakar maza da mata. Abinda bata sani ba,a duk sanda ta saka laffayar tana yi mata mugun kyau ne,tare da sake nuna zallar dangantakarta da shuwa

"Bazan iya canza kowanne kaya ba" ta fada masa kai tsaye tana dauke kanta daga sashensa zuwa wani sashe na daban hadi da goye hannunta a qirjinta.

Ko motsinsa bataji ba bare ta sanya ran yana dakin,har zuciyarta ta fara gaya mata ya fita ne,abun mamaki sai taji hucinsa dab da ita,kafin tayi kowanne motsi taji ya kama daurin lafayar dake qugunta data yiwa daurin zarge ya wareshi,a take ta fara warwarewa daga jikinta.

A mugun razane ta kama laffayar ta cukuikuyeta,don tabbas muddin ta warware din ta gama tozarta a idanunsa,zai ga shape na komai nata ne,don wasu rubber material ne a jikinta me golding masu tsayawa dai dai jikin mutum. Hannu daya ya sanya ya zare laffayar a jikinta qwayar idanunsa cikin nata yana karantar yadda hankalinta yayi wani mugun tashi,yayin da ita kuma ta dage tana gogarin tattarota, wani tashin hankali yana bayyana qarara cikin idanunta. Ko kusa ko alama garfinsu baizo daya ba,tayi imanin idan akaci gaba da haka dukka laffayar zata zame ne ta barta gayanta.

Dole badon ta shirya ba cikin rawar murya tace

"Am sorry i will change it please" yadda tayi maganar da mugun sanyi muryarta na rawa ya karya lagonsa,sai kawai ya sake mata laffayar yana cewa

"Kin dauka ni abokin wasanki ne?, Bayan na biya sadakinki duniya ta shaida ke din kin zama halal din da zan iya yin komai dake ba tare da na zama abun zargi ba shine har kike da zarrar tsaiwa kina fadamin wannan maganar na ina wuce hurumina?" Sake rigeta kawai tayi da kyau cikin tunanin mafita

"Bakisan zan iya mai dake naked ba kuma nace kiyita zama a hakan a gabana?, kuma banyi laifi ba har wajen Allah?" Daga furtawar kawai da yayi sai taji kamar ma ya maidata tsirarar, abinda ya sake mugun razanata kenan ta kasa cewa komai sai karyar da wuya da tayi. Ya gano ta karaya sosai,sai yaja baya yana qara nisan tazarar dake tsakaninsu

"na baki minti daya" ya fada yana sake ja da baya hadi da maida jikinsa ya jingin da mudubi. Cikin rudewa take dubansa,yana nufin a gabansa zata tube ta canza kayan? tashin hankali

"HUGUMA*


_TABARMAR KASHI_


BOOK 02 Page 28

"Don Allah ka bani guri, zan canza" ta fadi kamar zata rushe da kuka, idanunta na fidda wani qyallin hawaye, da gaske dai mutumin nan dan iska ne. Idonsa ya lumshe kana ya budesu,duk sanda hawaye suka cika a idanunta wani irin haske suke garayi

"Zan dawo muddin kika batan lokaci" yana kaiwa nan ya juya yana fita a dakin. Duk da taso tare hawayen amma saida suka silaloAllah ta yarda baki afifa tayi mata

"Aure yana garawa namiji kwarjini a idon matarsa, duk wannan cika bakin da rashin kunyar taki idan baki wasa ba saikin nemeta kin rasa" daya daga cikin maganganun da sukeyi da afifa kenan,wanda ita a nata gurin dai dai yake da tatsuniyar gizo da qoqi.

A gurguje ta cire ta sauya da wata atamfa, plain zani da riga ne, ta dora daurinta ta maida mayafin kayan sannan ta fito. Cikin hallway din ya saka wata kujera yar garama ya zauna. Tana bude qofar yana daga kansa daga danna waya. A hankali take takawa saboda bacin ran da yake cin zuciyarta na irin kama karyar da yakeyi mata. Sati biyun da tayi dashi cikin MT JARMA company kawai tana danne zuciyarta ne, amma kama karya kawai yakeyi mata. A nutse ya sauke qafafunsa qasa daga dora daya saman dayan da yayi, still idanunsa suna kanta, kai ya girgiza

"Koma ki cireta,batayi ba" sai data kalli kanta,kamar zatayi magana amma kuma yadda ya kafeta da kallon nan nasa yasa ta kasa fadin komai,sai kawai ta juya din tana jin zuciyarta kamar zata fashe.

Karo na hudu kenan ta sake fitowar idanunta na mata radadi saboda hawaye,yau din kamar wata wadda kamfani suka dauketa contract na fashion show,ta tsaya a gabansa tana jifansa da harara a fakaice, cikin ranta tayi rantsuwar wannan ce qarshe, muddin yace batayi ba bazata sake komawa ba. Kallon da yayi mata wannan karon yafi na wadancan shigar, duk da abaya ce me sulbi “yar qasar Turkey amma ta fiddata a balarabiya zamm.Janye idanunsa yayi yana miqewa tare da jan sirirn tsaki

"Ba zuwa office yau" ya fadi yana fita a nutse yana barin hallway din.

Hakan itama yayi mata,saboda ita kanta yau ranta a bace yake. Yau din ya raina mata hankali ya kuma bata mata lokaci yadda ya kamata,inda ace sunje office din to bata jin zata yi komai saboda haushinsa da ya cika mata zuciya. Baqinciki ya sanyata yin zaune a bakin gadonta kawai ta kasa fidda rigar ma daga jikinta, tana jin qarar tashin motocinsu,sai kawai ta koma saman gado ta nade abinta ta kwanta tana jan qwafa, kallonsa a kanta yaqi bacewa daga idanunta,babu wani namiji baya ga adam data taba tsaiwa va kalleta har haka saishi, duk da kowacce shiga jikinta yane yake da mayafi, amma har gangar jikinta tana jin kallonsa shi din me zurfine, don ya banbanta da yadda takejin idanun sauran mutane idan suna kallon nata.

Wayarta kawai ta jawo ta bude data tahau online, ta samu afifa kuwa a lokacin

"'Bestie yau ba office?" Tsaki ta tura mata, sannan ta fara bata labarin rainin wayon da yau din toufeeq din yayi mata. Abinda ya bata mamaki dariyar da afifa ta dinga aiko mata da ita

"Banason wulaqanci bestie, idan ba zaki tayani ba ki barni da bacin ran da ya dasa min" sai a yanzun afifa ke sake yarda cewa akwai fa autanci da gaske, da taga gayyar na shirin watsewa sai tace

"Ba shiga sabgar da ba tashi yayi ba, banda abinki bestie duk duniya kallon miji da mata na haqiqa sukeyi muku,kinason ki tona muku asiri ne?, kinga dole yayi komai don ya tabbatar da ingancin aurenku a zuciyar kowa"

"Shi ya sani,bazan sake bari ya rainan wayo irin na yau ba"

"'Nima ina bayanki" afifa ta fada tana boye dariyarta.
Gyara kwanciyarta tayi

"Bestie na fara wani tunani cikin raina,inason kiyimin cikakken bayanin yadda za'a magance epilepsy magani na har abada"

"You mean surgery?"

"idan har ta kama da hakan hakan za'a yi" gyara zama afifa tayi

"Idan nau'in epilepsy dinta yana cikin nau'ikan wanda za'a iya yiwa surgery din zaki iya taking risky na hakan? bayan family dinta ma dake tare da ita basuyi mata ba?" Ido tadan rufe tana tunanin maganar afifa, sannan ta bude tana maida mata amsa

"I can take the risk afifa indai za'a dace.....anjima zamu tattauna akan ciwon if you are available"

"Ba damuwa" ta amsa mata itama, tasan tsaiwa da rashin tsoro da va jima da dasuwa a zuciyar sãahar, indai tace zatayin to zatayi babu fashi.

Ta jima zaune a daki abinta, har akayi sallar azahar, ta bada farali tana zaune tana duba lokaci.
Batabar gurin ba sai data daidaici lokacin dawowar fadeel daga school ya kusa,sai ta miqe ta ninke abun sallarta, ta sauya kayanta zuwa wata gown sassauqa, don kitchen takeson wucewa kafin su qaraso. Ita ko nadeeya yanzun sun daina cin abincin kowa sai nata. Gown din tayi mata kyau sosai,ta maidata kamar wata baby musamman da gashin kamta ke fake a tsakiyar kanta cikin wani pink ribbon. Gown din me siririn hannu ce, kuma bata gama saukowa ba sai ta dora hijab da ya sauka har gasan gafafunta,ta zura wasu takalma masu laushi ta fito a sashen nata.

Dab da zata isa ga sassansu fadeela hajia garama ta fito. Kamar ko yaushe cikin shigar fariya da alfarma, mayafinta a kafada don ita din ba ma'abociyar yafa mayafi bace. Wani kallo tabi sahar din dashi sannan ta saki murmushi tayi gaba

"A'uzu bi khalimatillahit taammati minsharri ma khalaqa,Allahummakhfinihim bima shi'ita" ta samu kanta da furtawa saboda wani faduwar gaba da saukar mata sanadin murmushin murmushin da ta gani akan fuskarta.

Baaba ramatu ta samu da zuwaira suna hira a falon,ko ina a tsaftace kamar ko yaushe,suka gaisa cikin girmamawa sannan ta wuce kitchen bayan tace da zuwaira da ta mige zata bita suyi zamansu,abu me sauqi zata hada.

Veggies couscous ta shirya tare da egg
souce, tasan fadeela da son kayan zaqi,ba kuma kasafai take barinta vanzu tayi ciye ciyen kayan kwalin nan na banza da wofi ba,sai ta bude freezer ta fidda kankana ayaba yoghurt ta hado da madara ta zuba sugar tayi mata blending water melon smoothie data cikawa madara sosai. Tana juyeshi a wasu madaidaitan drinking glasses masu bamboo lids bayan ta zare glass straw din da suke dashi nadeeya ta shigo.

"Aunty N,yauma akwai special abu da alama, qamshi tun daga compound" tayi maganar tana legen smoothie din da take juyewa

"Abincin faddee ne" dan fuska nadeeya ta bata

"Amma ana wasa tare ci banban, nidai wannan smoothie din za'a tallafeni dashi,yau nasha rana, inajin ajiye aikin nan zanyi" ta fada tana narke fuska. Murmushi säahar ta saki ta maida murfin ta rufe ta zura mata straw din ta miga mata. Zuqa daya tayi ta lumshe ido

"Anty N,bazan iya shan wannan abun a tsaye ba bari na garasa daki"

"A fito lafiya " ta fada tana murmushin santin da taga
nadeeya din tanayi.

Cikin fridge ta maidashi inda sanyi bazaiyi masa
yawa sosai ba,saboda ta saka ice cube qurin blending din so da sanyinsa. Muryarta taji tana qwala mata kira

"Tom an dawo kenan" ta fadi a ranta tana murmushi, a hankali taii sautin nata yana matsowa kitchen din,sanda ta lita dab da gofa saita waiwayo tana murmushi hadi da dan harara a idanunta na yadda ta tafi school bata nemeta ba yau din.

Maimakon fadeela sai idanunta suka hadu da nashi,gabanta ya fadi,ta dauki hannunta tana nadeshi a girjinta saboda yanayin rigar da take sanye dashi, already ta cire hijabinta tun shigowarta kitchen din, saboda tasan babu wanda yake shigowa, daga ita sai baaba ramatu sai zuwaira. Sam bata kawo zai shigo ba,saboda bata taba ganinsa cikin kitchen din ba sam.

Duk yadda yaso yiwa idonsa shamaki a kanta amma hakan ya faskara,sambala sambalan singalalin hannunta dake da lallausar fata me santsi yabi da kallo, a hankali ya zarce da kallon qirjinta data lullube da kyau da singalalin hannun nata,saidai duk da hakan hannun nata bai wadatar ba,saboda cikarsu da tsaiwarsu ya sanya suka fito ta saman rigar fam dasu.

Kadan kadan zuciyarta ke bugawa tana duban fuskar fadeela tare da qoqarin waskewa da nuna bata damu da shigowar tasa ba. A kasalance ya dauke idanunsa yana cewa da fadeela

"Sauka angel ki qarasa" saboda dama ha daukota ne a bayansa da kansa yau din. Kafada ta maqale

"Abby ki qarasa ladanka please,ka shigar dani ka kaini
gurin anty N" ta fada tana maqale kafada

"Ya salam" ya furta a ransa,wannan rigimammiyar ruwa takeson ballo masa. Magiya ta dage da yi, hakan ya sanya ya fara takowa da ita cikin kitchen din yana gogarin hana idanunsa kawai wanann gurin da ya zame masa kamar wata jarrabawa akan yarinyar.

"'Matso abby ka gani" fadeela ta fada tana miqewa daga bayan nasa,nufinta ta taka bayansa sannan ta maqalewuyan säahar

"What?, sauko angel" ya fada yana dan daga kansa yana dubanta. Sake marairaice fuska tayi

"Please mana abby, munyi algawari fa kace yau bazan taka qafafuna a qasa ba" kai ya girgiza yana tuna sunyi hakan, amma shi bedroom dinta yace zai sauketa.
Idanunsa ya lumshe ya gara taku biyu gaba yadda yarinyar keso,saahar na tsaye tana murmushi idanunta akan fadeela, saidai can qasan zuciyarta wani mugun gudu takeyi kamar wadda tayi gasar tsere, taku biyunsa su suka hade dukka wani tazara dake tsakaninsu,wadan nan abubuwan da suke tone masa idanu,suka zame masa idanunsa barazana suka samu kyakkyawan masauki saman girjinsa. Yadda yaji saukarsu saman likinsa haka tail vadda girinsa ya tokare nata. Dukkansu jikkunansu suka karbi wani sago me nauyi da bala'in ratsa zukata,yayin da säahar jikinta ya dauki rawar da saura kadan fadeela tasha gasa, banda toufeeq yayi zafin namar taro yarinyar,ya saka dukka hannuwansa ya sauketa a gasa yana duban fuskarta

"She's not brave enough,ba zata iya daukanki ba" ya fada muryarsa tana dan sargewa wanda shi kansa baisan da hakan ba. Itakam fadeela da batasan dawar garin ba dariya takeyi tana sake magale säahar

"Anty N,abby na ya fiki qarfi, amma zamu hada qarfinmu waje daya muma ko?" Kai ta gyada mata a sanyaye tana jin qafafunta babu qwari sam. Tsaiwa yayi kawai a wajen yana duban fuskarta,yadda lokaci daya hankalinta ya tashi fuskarta kuma cakude da bacin rai kadan. Kasa motsawa yayi shima yana qoqarin controlling kansa kafin yakai ga takawa yabar wajen,jikinsa a sanyaye ya ja da baya ya jingina da kitchen cabinet din yana sake binta da kallo sanda take rige da hannun fadeela bayan ta maida hijabinta jikinta.

"Ungo wannan ki fara sha kafin kiyi wanka,kizo kici abinci na gama" sãahar tace da fadeela tana bata drinking glass din. Harda tsallenta, ta dawo gurin toufeeq bayan zuga

"Yummy abby sha kail" ta furta tana miga masa.
Hannunta ya dafe yana girgiza kai,ta fahimci me yakeson cewa saita maqale wuya

"Please mana abby" a nutse ya durqusa ya sanya straw din a bakinsa ya zuqa. Har cikin kwanyarsa dadi da gardin fruit dana madarar ya ratsa masa,ya lumshe idonsa yana jin smoothie din yayi masa matuqa,saidai kafin ya sake sha fadeela ta janye abinta ta kafa a baki.

Su suka fara fita a kitchen din yabi warmers din da kallo daya tabbatar abinci ne a ciki,ya shafi cikinsa yana jin yunwa tana taso masa, tunda jacob yaje gida yake wahalar abinci,tun asali mutum ne shi da bakowanne abinci yake iya ci daga hannun kowa ba, gidan cike yake da masu girki da kuma nau'in abinci kala kala amma bai iya ci ba, da abincin jacob kadai ya aminta. Ba mai yawan ciye ciye bane, amma kuma baya wasa da cikinsa ta fannin abinci, idan ya tashi zaiyi masa ci me kyau,daga nan kuma sai lokaci na gaba. Da qyar ya shawo kansa sannan ya

Please Login or Register in order to submit comment